Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan bayan ta kulle gidan ta dawo falon Hajja ta zauna amma gabaWaya bata jin daWi.

Sallamar Bashir ta ji daga gate Win Hajja, ta tashi da hanzari ta je ta ce, "Bashir ya ake ciki?." Ya kalli Didi ya ce, "Didi Ina ya bincikawa, na dawo Goje ya ce min kina gidan nan shine nazo na ji lafiya. Ko akwai wanda ya shiga gidan?."

"Babu kowa. Hajja ta ce na dawo nan na kwana ne saboda gidan babu kowa."
"Haba Didi, muna nan fa, wallahi ko kuWa bazai taSa ki da niyar cutarwa ba." Didi ta ce, "Gwara dai na zauna a nan Win Bashir. Don Allah duk abinda ake ciki ka yi min waya." Bashir ya amsa sannan ta dawo gida wajan Hajja gabaWaya bata da nutsuwa.

Hajja ta ce, "Salma kai ta Wakin Nayla ta huta." Salma ta raka Didi Wakin Nayla da yake shirye tsaf sai khamshin turarenta yake yi. Murmushi tayi tunawa da Nayla, ta zauna a gefen gadon tana kallon kan mudubin Nayla da yake ajjiye da kayan kwalliya kamar a gidan take rayuwa. Murmushi tayi ta kalli Salma da ta kawo mata abinci ta ce, "Salma ni fa ba ba™uwa bace, ki daina hidima haka."
Salma tayi dariya ta ce, "na sani Didi, hutar dake nayi." Didi ta ce, "na gode. Šakin ™anwata Nayla sai ™hamshi, ga kayan kwalliya kamar tana ciki."

Salma tayi dariya ta ce, "Aljanar kwalliya kenan." Didi tayi murmushi kawai bata ce komai ba Salma ta fita ita kuma ta Wauki abincin ta fito ta zauna kusa da Hajja tana ci suna ´ar hira kaWan.

Washe gari.
Abuja.

       "Daddy Ina aka kai Faruk? Daddy a dokance baka da right Win da zaka saka a kulle shi ba tare da ya yi wani laifi ba. Yana da damar da zai kai ka ™ara court kuma dole a yi maka hukuncin aikata haka" Sai kuma ta daidaita murya ta ce, "Dad Ina yake? Don Allah ka faWa min inda aka kai shi" ta faWa tana zamewa a wajan tana kallon mahaifin na ta.

Shi tausayi take bashi sosai, gabaWaya ta fita daga hankalinta ta koma wani iri kamar ba Narma ´ar gayu mai aji ba. Kallon Mum ya yi da take kallon sa kafin ya sake kallon Narma ya ce, "Narma ki nutsu." Narma cikin kuka ta ce, "bazan iya nutsuwa ba Dad, bazan iya nutsuwa ba Ina so na ganshi. Ina kewarsa, don Allah Dad kar ka cutar dashi. In aurena dashi ne baka so zan ha™ura dashi amma kar ka yi masa komai don Allah Daddy, bashi da laifin komai ni ce na fara son sa."

Sen ya kalle ta ya ce, "na ce ki nutsu ko?." Zama tayi tana share hawaye ya kalle ta ya ce, "Ranar monday zaki jinginar da duk abinda ki ke yi zaki tafi London." Da sauri ta Wago kai ta kalle shi murya na rawa ta ce, "Daddy London..? Me zan yi a can?."
"Ina so ki je ki huta hankali ki ya dawo jikinki daga baya za a san abinda za ayi."
"Dad i can't go anywhere without knowing where Faruk is. Where you have take to him?. Dad wallahi bai yi deserving wannan hukuncin ba, it's his fault for falling in love with me?. Kuma Daddy kai ka yi min al™awari zaka bani duk wanda nake so, na kuma kawo maka shi ga sakamakon da ya biyo baya."

Dad kallon ta ya ke yi kamar bata cikin hankalinta, sai magana take yi mara kan gado kamar ba ita ba. Sai ya yi shiru bai ce mata komai ba. Narma ta ce, "don Allah Dad ka taimake ni ka bar Faruk ya tafi, ka ™yale shi na yarda na ha™uta dashi bazan sake cewa Ina sonsa ba." Mum ta kalli Dad sai ta mi™e kawai ta bar wajan jim kaWan sai gata ta dawo. Ba jimawa sosai sai ga wani saurayi ya shigo Mum ta taso ta ri™e Narma ya yi mata allurar bacci.

Mum ta kalli Dad ta ce, "ni na kira shi, na lura Narma ba ta cikin hankalinta. Ya gama lalata min tunanin yarinyata, ya gama cutar da ita. Na rantse da Allah na tsane shi bana sonsa, bana so ya rayu a cikin duniyar nan." Dad ya kalli Narma da tayi bacci a wajan ya kalli Mum ya ce, "sai a hankali zata dawo daidai, ita da ganin sa kuma har abada" yana gama faWa ya fita dan ya zama dole ya canja shiri akan Omar.

Narma bacci tayi na sama da awa bakwai, dan tun safe take bacci har bayan sallar la'asar sannan ta farka da weaknesses joints. Da™yar ta iya wanka ta fito tana kallon kanta a madubi, key Win mota ta Wauka bayan ta shirya ta fita daga gida.

Kai tsaye wajan Wan sanda da ya zo ya kama Omar ta je ta ce tana so ta ga Omar. Da kamar bazai kai ta ba amma ya ga ta dage sai ya saka aka raka ta inda aka ajjiye Omar.

Can ™auyen Abuja ne, cikin wata unguwa da bata taSa zuwa ba, aka buWe mata wani wula™antaccen gida ta shiga ana biye da bayanta. Kallon gidan take yi tana hawaye, wai Omar Win ta ne a cikin nan ba tare da ya yi laifin komai ba.

Da ta shiga waje mai kyau aka ajjiye ta, inda masu azabtar dashi Win suke nan suka bata ta zauna. Bouncers Win da suke gidan kaWai abin tsoro ne, Narma sai kallo su take yi domin kana ganin su ka san basu da imani, in ka shiga hannun su sai sun karya ka. Ita kam ta kasa zama sai zagaye take yi, tana ji an buWe ™ofa da sauri ta kalli wajan. Ajiyar zuciya ta sauke ganin Omar da kayan jikinsa da suka zo amma kayan sun yi ba™i, duk da ba Saki sosai ba amma sun yi duhu. Fuskarsa babu walwala ko kaWan, sannan wahala ta bayyana ™arara akan fuskarsa. Da gudu Narma ta taho inda yake zata rungume shi ya motsa ya Wan ja baya kaWan sai ta kalle shi tana kuka.

Zubewa tayi a wajan ta ce, "im sorry Faruk! I'm sorry!!" Ta faWa tana kuka sosai tana dur™ushe a gaban sa. Bai ce komai ba bai ma kalle ta ba idanunsa a rufe babu abinda yake addabar zuciyarsa kamar Sacin rai, babu abinda yake damunsa kamar halin da Didi take ciki. Zaman inda yake da wahalar da ake bashi baya damuwan sa kamar barin Didi da ya yi a gida ita kaWai. Ya san tana can tana kuka, ya san tana can hankalinta a tashe saboda rashin ganinsa. Wannan tunanin yafi halin da yake ciki ™una da raWaWi a zuciyar sa.

Narma ta ce, "Na yi maka alqawari zan yi duk yadda zan yi wajan ganin ka bar wajan nan, zan yi iyakar iyawata wajan tabbatar da Dad ya ™yaleka. Ni lawyer ce, zan yi duk abinda zan yi saboda kai Faruk." Sam kalaman ta basa kwantar masa da hankali dan gabaWaya ma baya so yaji koda maganarta, ba wai dan ya tsane ta ko dan yana jin haushinta ba, sai da tsantsar ba™in cikin da yake zuciyarsa.

Narma ta sake cewa, "kayi magana Faruk, ka ce wani abun ko zan ji daWi." Sai a lokacin ya sauke shanyayyun idanunsa a kanta, haWa ido suka yi ya kalle ta na sakan biyar kafin ya janye idanunsa. Tabbas ta rame kana ganinta ka san tana cikin damuwa. Damuwarta bata dame shi ba, inda zai iya yi mata magana da ya yi magana akan Didi, amma baya tunanin ko waye yazo a wannan lokaci zai iya buWe bakinsa ya yi magana, shirun shine alkhairi a gare shi.

Omar da kansa ya juya ya koma inda aka ajjiye shi, Narma na kiransa amma ya yi mata banza ko juyowa bai yi ba. Bashi da nutsuwar da zai iya kallon ta har ya yi mata magana shiyasa bai ce komai ba.

Narma da hawaye shaSe-shaSe ta fito ta shiga mota ta fizgi ta da ™arfi zuwa gida. Tana tafiya tana kuka har ta je gida tana shiga falo ta zube a jikin Mum tana kuka mai sauti. Hankalin Mum ya tashi dan ita take nema tun bayan fitarta ta ce, "Narma Ina kika je? Kin san baki da lafiya kika fita ke kaWai?. Me ya same ki ke kuka haka?."
"Mum naje na ga Faruk, Mum gabaWaya an canja min Faruk Wina, Mum Dad ya saka ana azabtar min dashi. Mum abinda nake ji a zuciyata ji nake kamar na kashe kaina. Kinga bouncers Win da Dad ya ajjiye suna dukan Omar, kinga irin azabar da ake yi masa? Kashe kaina kawai zan yi!."

Hankalin Mum ya tashi da kalaman Narma, da hanzari ta dannawa Sen waya Allah ya taimaka bai yi nisa ba ya ™araso gidan.  A lokacim Narma take cewa, "Mum Ina sonsa, Ina ™aunarsa. Mum in Dady bai fitar dashi daga gidan da ya saka aka ajjiye ba ni zan yi da kaina, in aka hana ni zan yiwa kaina illa Mum, zan iya kashe kaina akan Faruk Mum...!" Ta ™arasa faWa tana jan sunan Mum Win tana kuka.

Sen ya ji ta ya ™araso ya tasar da ita tsaye ya rungume ta sai kuka take yi yana rarrashinta. Surutai take tayi masa barkatai akan Omar yana ta rarrashi yana shafa bayanta, sai da ya ga ta Wan yi sanyi sannan ya kalle ta ya ce, "je ki Waki ki huta." Zata yi magana ya ce, "kar ki ce komai Daughter, je ki" ba musu ta tafi zuwa Waki tana share hawaye.

Mun ta kalli Dad a ™ufule ta ce, "Tunda har ka san zata iya binciko inda yake har taje ta ganshi meye amfanin barinsa nan? Meyasa baka kai shi inda baza ta iya zuwa ba?." Dad ya ce, "shiyasa zan tura ta London."
"Saboda shi sai ta bar Nigeria? Kenan shi ya yi riba akan ta ko me?."
"Saboda ta samu peace of mind. Shi kuma zan ji dashi" ya faWa yana hawa sama ya bar Mum a wajan. Dole ya san abinda zai yi akan Omar kafin ´arsa ta rasa hankalinta akansa.

*Kaduna.*

Nayla na zaune sun gama magana da Twiny a waya sai ta kira Salma, tana Wauka ta ce, "Sis ya ki ke? Ya Hajja?." Salma ta ce, "lafiya lau Nayla, ya Mama da Abiy?."
"Kowa yana nan lafiya lau. Kin ga alert?."
"Eh naga kuWi ya zo, na ce Nayla kuWin wa ta saka min." Nayla ta ce, "KuWinki ne, first salaryna ya sauka."

Salma tayi dariya ta ce, "godiya nake ma'aikaciya." Murmushin ya™e Nayla tayi kafin Salma ta ce, "ya ki ke? Ina fatan yanzu babu damuwa ko?." Murmushi ta yi kawai bata ce komai ba dan maganar da suka gama da Jidda kenan. Salma ta ce, "Nayla don Allah ki kwantar da hankalinki, in kina tayar da hankali Abiy bazai ji daWi  ba. Yanzu kin samu magana dashi Win?."

Nayla ta ce, "Salma na faWa muku ni bana so ya san Ina sonsa, gwara ku taya ni addu'a kawai Allah ya kawo min ™arshen ko meye. Bana jin zan iya furta masa kalmar so gaskiya."
"Amma Nayla cutar da kan ki ke ke yi. Ni ki faWa min inda take a faWin Kano naje na same shi nayi masa magana, sai cutuwa ki ke yi a kansa, ba ke kika sakawa kan ki ba Allah ne, meye aibu dan an faWa masa?." Nayla ta murmusa ta ce, "Salma sanin waye bashi da wani mahimmaci, koda yana sona ma aure na dashi bazai yu ba. Na tabbatar Abiy bazai aura min shi ba."

Da mamaki Salma ta ce, "kafiri ne?." Nayla ta ce, "musulmi ne yana sallah kamar kowa, kawai dai aurena dashi na san bazai taSa yuwa ba. Balle kuma ni bazan faWi suna ba, kuma sannan bazan ce Ina sonsa ba." Salma tayi shiru kafin ta ce, "Nayla kar ki cutar da kan ki, ni na san Abiy indai kina sonsa shima zai so shi Nayla." Nayla bata ce komai ba Salma ta ce, "kin yi shiru."

"To me zan ce miki Salma? Asalin gaskiyata nake faWa miki Salma, na san Ina sonsa, Ina ™aunarsa amma bazan iya furta masa ba, kuma bazan iya faWa muku sunansa ba koda zan mutu. ˜ar™ari in na mutu ku ce soyayya ce ta kashe ni keda Jidda. Tabbas in na bar duniya a yanzu da tasirin soyayyarsa a yin ajalina."

Salma ta sake karya murya zata yi magana Nayla ta katse ta ta ce, "Ya Didi? Tana lafiya?." Salma jin ta kawar da maganar sai ta ce, "Allah ya kawo miki mafita, in alkhairi ne a gare ki Allah ya zaSa miki shi ´ar uwa."

Ta amsa da amin kafin Salma ta ce, "Didi tana gida, Wazu dai ta fita daga nan, da yake a nan ta kwana." Nayla ta ce, "ta kwana a gidan Hajja? Lafiya dai ko?."
"Ba ™alau ba dai. Ta™adirin ™aninta ne mana, Wan kuka mai jawa uwarsa jifa." Gaban Nayla ya faWi matu™a ta ce, "Me ya faru?."

Salma ta ce, "Wai ´ar Senator Sagir yake so dan tsabar bashi da hankali, to ko ni zauna gari banza babana ba Senator ba yazo ya ce yana sona ba sai na saka an yi masa abinda har ya mutu bazai manta dashi ba?. Ke ko bani ba, ko wacce bata kai ni rufin asiri ba ya ce yana so sai mun haWu mun hana ta sonsa saboda ba mijin da za a so bane. Wai ™afa ya Wauka yaje har Abuja gidan Kano centaral Senator wai yana son ´arsa Narma. Ki ji fa Nayla, Barr Nass fa wacce ki ke gani a social media yaje neman aure dan tsabar ™arfin hali irin nasa. Tsabar wiwin da yake sha ta taSa masa ™wa™walwa harda kwasar gajojin ´an daban yaransa suka tafi wai neman aure. Ai kam Sen ya yi ram dashi, ya saka an Waure shi yana neman hanyar da zai kai shi prison, kuma ya ce  sai ya yi life in prison."

Dum dum dum dum! Haka ™irjin Nayla yake bugawa, ta zazzaro idanu waje kamar Salma Win tana ganinta. Duk da a.c da take Wakin gumi ya gama wanke mata jiki saboda tashin hankali. An kama Omar? Omar Win ta da ake zancen zai yi life in prison? Omar fa masoyinta.

Salma ta katse mata tunaninta hanyar cewa, "Shine fa hankalin baiwar Allah ya tashi, ta shigo tana kuka abin tausayi. Allah ya haWa ka da Wan uwa irin Omar ma ko ™addara, haka kawai ya saka hankalin baiwar Allah ya tashi. Hajja har Daddy ta yiwa magana ya ce zai san yadda za ayi, za a yiwa Sen Win magana ko zai fito dashi. Gashi an ce bashi da kirki ko kusa, baya Waga ™afa akan komai da™yar ya amince ya bada Omar. Ke ni fa a wajena Omar ya cancanci fiye da haka, tsabar raini da tsaurin ido ya Wauki ™afa ya je har gida wai ´arsa yake so? Ni ban ga laifinsa ba."

Nayla bata iya cewa komai ba domin ™wa™walwarta tafi hutun rabin lokaci. Salma bata damu da shirun ba ta kuma cewa, "jiya da daddare Hajja ta saka ta dawo nan ta kwana saboda gidan babu kowa, kuma kin san ´an daba ´an uwasa masu jin haushinsa zasu iya shigowa su cutar da Didi. Inda mutumin kirki ne ma sai ka tauyasa masa, gwara ma haka."

Nayla hawaye ya gama wanke mata fuska, hawaye na tausayin masoyinta, hawaye na tausayin abin ™aunarta, hawaye na tausayin halin da yake ciki a wannan lokaci. Hango fuskarsa take yi tana tunanin yadda ya koma a yanzu. GabaWaya nutsuwarta ta bar gangar jikinta.

Da™yar ta iya buWe baki ta ce, "Allah ya kyauta" daga haka ta yanke wayar ta toshe bakinta da hannunta fashe da kuka mai sauti. Mama tana tsaye daga bakin ™ofar duk hirarta da Salma taji, girgiza kai take yi domin wannan soyayyar da Nayla ta fara babban makami ne a gareta, tunda gashi har taji tana cewa mahaifinta bazai amince ba, lallai tsuntsu ya faWo daga sama gashashshe.

Shigowa Wakin tayi tana kallon Nayla, Nayla tana ganin ta manta halin da take ciki ta mi™e a guje ta faWa jikinta tana kuka. Mama tana shafa bayanta a hankali cikin rarrashi ta ce, "yi shiru kar ki damu, kwantar da hankalinki."

Kuka Nayla take sosai na tausayi Omar da Didi, jikinta har rawa yake yi saboda tashin hankali da tsananin bugawar zuciya. Mama ta Wago ta daga jikinta ta kalle ta ta ce, "Nayla ko baki faWa min ba idanunki sun faWa min soyayya ce ta saka ki a wannan yanayi, kar ki damu kar kuma ki tsorata ni uwa ce a gare ki, zan shige miki gaba wajan samun duk abinda ki ke so a wajan mahaifinki. Haka ne hasashena?."

Nayla ta yi shiru ta sunkuyar da kai sai hawaye da yake zarya a kan fuskarta. Mama ta sake janta jikinta ta ce, "kar ki damu ki nutsu, Ina tare dake a ko yaushe. Na kuma yi miki alqawari zaki auri wanda ki ke so ko waye shi, kar ki damu da faWa min waye shi a yanzu, ki bari sai lokacin da zuciyarki ta aminta da ki faWa min. Ni kuma a lokacin zan jajirce kamar ko wacce uwa na samar miki da farin ciki. Zan sadaukar da komai wajan ganin mallaki wanda ki ke so, zan iya yin komai dan tabbatar da cikar burin ki Nayla."

Nayla kwanciya tayi a jikin Mama tana kuka tana ji wani Sangare na zuciyarta na tabbatar mata da abinda Maman ta faWa. Ido ta a kulle cikin tausayi da soyayyar Omar..KRB2P003
Arewabooks@nanahaleema11.


Mama sai da ta bar Nayla tayi kukan ta sosai sannan ta Wago ta daga jikinta ta ™arasa da ita kan gado ta zaunar da ita, ta tashi ta kawo mata ruwa a glass cup ta sha ta zauna a gefenta tare da ri™e hannunta tana kallon ta. Nayla sai sauke ajiyar zuciya take yi irin ta wacce ta sha kuka ta gaji. A tausashe Mama ta ce, "ki nutsu, Ina tare da ke a akan duk abinda ki ke so. Mahaifiyarki ni ta barwa amanarki, bazan taSa bari wani abun ya cutar dake ba."

Nayla ™arfin guiwa maganar Mama take ™ara mata hakan ya saka ta Waga kai Mama ta ce, "Sanar dani yaushe kika fara sonsa? Sannan a Ina yake?." Nayla ta rausayar da kai ta ce, "Mama don Allah bana so Abiy ya sani."
"Bazan sanar dashi ba Nayla, ai wannan sirrin uwa da ´arta ne." Nayla ta sauke numfashi ta ce, "A Kano yake da zama Mama, kuma ni ma ban san lokacin da na fara sonsa ba."

Mama ta ce, "ya sunansa?." Nayla ta kalli Mama sai bata ce komai ba. Mama ta ce, "shikenan ba sai kin faWa min waye ba, amma meyasa ki ke cewa Abiy bazai amince ki auren shi ba? Yana da wani hali mara kyau ne ko kuwa ba musulmi bane ba?." Nayla a sanyaye ta ce, "Musulmi ne Mama, kawai dai...." Sai tayi shiru bata ce komai ba. Mama ta ce, "Ina jinki, kawai dai me?."

Nayla ta kalli Mama ta ce, "don Allah Mama mu bar maganar nan kawai." Mama tayi murmushi ta ce, "shikenan Nayla. Ki daina saka damuwarsa a zuciyarki komai zai zama labari kin ji ko?." Nayla ta Waga kai Mama ta ce, "Dama nazo na sanar dake Abiy ya ce zaki yi ba™o yau, sai ki shirya tarbar zuwansa."

Nayla ta amsa a sanyaye Mama ta dafata ta ce, "kar ki damu, zaki auri wanda ki ke so in sha Allah." Murmushin ya™e kawai tayi dan ko amin din ma bata ce ba. To in ta ce amin ta wacce hanya auren zai zo? Na farko dai Omar bai ma san tana sonsa ba, na biyu yanzu haka Omar yana kulle babu ranar fitowarsa, na uku koda yana nan ita dai baza ta ce tana sonsa ba, na huWu Abiy bazai amince ta auren shi ba. Duk da Abiy baya damuwa da lallai sai mai kuWi za a aura, amma yana son good background da kuma good manners wanda ta tabbatar da Omar ya rasa. To akan me zata ce amin? Gwara tayi shiru kawai kar ta faWa da bakin mala'iku.

Mama ta ce, "ki yi ™o™ari ki dinga sakewa in ba haka ba Abiy zai takura ki akan rashin da sakewar nan taki." Kai ta Waga kawai Mama ta fita ita kuma ta koma da baya tana ajiyar zuciya. _Ko ya Omar yake yanzu? Wanne hali yake ciki?. Allah sarki Omar ya haWu da sharrin so, son maso wani kenan, ni ina nan ina haukan sonsa shi yana can ya sadaukar da ™uruciyarsa akan wata. Ko da yake abinda nake ji shima shi yake ji a zuciyarsa akan wata, amma ni bazan iya furta Ina sonsa ba, gwara na mutu....eh gwara na mutu kawai na huta. Bayan a gabana yake yiwa wacce take son sa faWa a waya...? Hmmm ga wula™ancin da Didi ta faWa min ya yi mata a gabanta, me ya kaini cewa ina son Omar?. Gwara nayi shiru kawai na auri wanda suke sona._ tunanin da take yi kawai a zuciyarta kenan ita kaWai cikin yanayi na damuwa da bugawar zuciya.

Sai bayan sallar i'sha sannan aka turo tazo ba™on ta yazo. Da™yar ta samu ™arfin guiwar motsawa daga inda take ta mi™e ta canja kaya zuwa doguwar riga ta slik mai kyau da santsi. Šinkin bubu ne, amma wacce ake yayi, wacce ake Wan Waureta daga ciki. Tayi mata kyau sosai ta saka hular kayan sannan ta yaga mayafi ta fito zuwa falon.

Yau ma dai ba™uwar fuska ta gamu da ita, daman Abiy ya ce mata mutum huWe ne har Abbas, ta zauna da mutum biyu ga na ukun, na huWun kuma Abbas ne daman ta sani. Kamar sauran bata haWe rai kuma bata kore shi ba, sun gaisa da girmamawa ya gabatar da kansa itama ta gabatar da kanta, sun Wan tattauna kafin ya yi mata sallama ya tafi.

Kamar ko yaushe yau ma dai Abiy na zaune a falo ta dawo, shi da Yaya J ne da kuma Mama. Da sallama ta shigo kamar baza ta zauna ba sai kuma Abiy ya kira ta dole ta dawo ta zauna gabanta na faWuwa matu™a. Abiy ya kalle ta ya ce, "Mamana kun gaisa da Lamin Win?." Nayla ta Waga kai ta ce, "Eh Abiy, ya tafi ma."

Abiy ya ce, "To daga kansa zan dakatar da duk mai zuwa neman aurenki. A cikin Omar, Lamin, Abbas da Hashim ki Wauki guda Waya a cikin su. Dukkan su na amince da iyayen su, aikin su, ilimin su, halayen su da sauran su. Sannan ko wanne Wan babban gida ne sun fito daga gidan mutunci da tarbiyya. Babu Waya a cikin su da yake shan koda taba balle a kai ga batun maye ko wani abun. Babu wanda na bawa damar zuwa wajanki a cikin su har sai da nayi bincike a kansu sannan na bari suka zauna dake. Kun tattauna da ko wanne a cikin su, to ki zaSi guda Waya da ki ke jin zaki iya zaman aure dashi. A cikin guda huWu ai na san baza ki rasa wanda ya kwanta miki a rai ba, In kuma Wan uwanki Abbas kika Wauka duk Waya ne."

Nayla gabaWaya kalaman Abiy tarwatsa mata zuciya suke yi, dan gabaWaya abinda yake lissafowa samarinta suna da shi ita kuma hange ta ke yi Omar bashi da ko Waya. Gashi Abiy ya jefa ta a tsaka mai wuya, ta ya ake tunanin zata iya Waukar mutum Waya a cikin su da sunan tana so? To wa take son Win a cikin su...?ita ko kamannin su ma bata tunanin zata iya hange a idanunta balle tayi batun so, ko waya suka kirata bata jimawa take sallama dasu ta kwanta. So Waya take yiwa mutum Waya tak a duniya kuma shine Omar Tiger, ta kuma tabbatar son bashi da wani amfani tunda ba auren sa zata yi ba.

Abiy ya katse ta ya ce, "kina ji ko?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "in sha Allah Abiy. Ka taya ni da addu'ar neman zaSin Allah." Abiy ya murmusa ya ce, "Allah ya tabbatar da alkhairi a rayuwar ku baki Waya." Aka

Please Login or Register in order to submit comment