Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mio mata ruwa ta buWe ta sakawa Nayla a baki ta ce, "Nayla buWe baki ki sha ruwa." Ta Wan sha kaWan ta kifa kanta a kafaWar Mama tana fitar da huci mai zafi.

A lokacin Khalid ya dawo ya araso ya ce, "Bara a yi mata allura kawai" ya faWa yana rio hannunta ya tattare dogon hannun rigar jikinta ya nemi jijiya ya yi mata allurar. Tana jikin Mama a kwance har aka yi allurar bata sani ba dan gabaWaya zafin da zuciyarta yake mata ya fi zafin allurar. Mama ta ce, "ka tabbatar zata samu sauki?."
"In sha Allah Mama, nan da anjima kaWan zaki ga ta warware. " Mama ta Waga kai tana sake kallon Nayla da take jilinta har lokacin.

Abbas ya ce, "Mama a kai ta Waki ta kwanta, in ta samu bacci zata fi jin daWi." Mama ta ce, "Khalid kira min Ummimi ta zo mu kai ta Waki." Khalid ya sau sama sai ga su tare da matashiyar budurwa wacce zata yi sa'ar Jalila anwar Nayla, ta zo suka rie Nayla zuwa Wakin da yake falon aka kwantar da ita. Khalid da Abbas suna bayan su, har Mama ta cire mata hijjab Win jikinta da Wankwalinta saboda ciwon kan, sannan aka kashe hasken Wakin aka kunna mata ac, ba jimawa bacci ya kwasheta dan allurar ta ratsa jininta.

Tare suka fito falo Ummimi ta kalli Mama ta ce, "Mama yaushe ta zo? Daman bata da lafiya ne?." Mama ta ce, "yanzu ta shigo, ban san me yake damunta ba kuma." Khalid ya ce, "da ta farka daga baccin zata samu saui in sha Allah, in ya so sai je asibiti a tabbatar da abinda yake damunta."
"Ni na fi tunanin ko ciki gare ta" Mama ta faWa tana kallon Khalid. Khalid ya ce, "to bana ce ba, shiyasa daman na yi mata pcm saboda gudun hakan."

Abbas ya ce, "ni sai nake ganin kamar tana cikin damuwa ne duba da yadda ta shigo da motar da yanayinta." Mama ta ce, "Sai ta farka zamu san abinda yake damunta. Ku je ku yi sallar i'sha ku zo mu ci abinci" ta faWa tana tashi ta hau sama Ummimi ta biyo bayanta su kuma suka fita.

Omar da tsayuwar Nayla a inda yake da abinda ta ce babu abinda bai ji ba kawai bazai iya magana ba ne, ya yi matuar oari da mamakin kansa da ta tsaya a gabansa yana cikin wannan yanayi ta yi masa magana bai Wauki mataki a akanta ba. A duniya bai taSa jin Sacin rai kamar wannan ba, a lokacin baya haWa auren su da ita ya fi komai Sata masa rai, amma a yanzu wannan shine kan gaba.

Mari fa, in ya tuna marinsa fa Didi tayi akan waWancan wanda basu da wata daraja a idanunsa sai ya ji kamar duniyar zata juya ta kife dashi. Haka yake zaune a wajan shiru bai motsa ba kuma bai yi magana ba, sai arar fankar da take tsaye a falon take juyawa a hankali.

Kiran sallah ne ya miar dashi cikin mutuwar jiki, rana ta farko da ya shiga banWakin kusa da falon ya yi alwala, ya jira masallaci aka tarar da Allah ya bi su a falon dan bazai iya fita ba a yanayin da yake ciki zai iya tashin Kano gabaWaya.

A haka ya idar da sallah ya sake zaune shiru Sacin rai yana nuurusar zuciyarsa, yana ratsa jininsa yana yawo a sassan jikinsa. Har aka yi sallar i'sha yana wajan, a nan ya sake yin sallah ya zubawa waje guda ido abubuwan da suka faru suna sake gilma masa a idanunsa. Shi dai ya san ranar bacci sai dai Sarawo, Sacin rai hana shi bacci yake yi ko ya ya motsa sai ya tuna, balle irin wannan Sacin ran da ya fi komai taSa shi. Baya so ya fita ya haWu da wani ya yi masa magana dan bazai iya tankawa kowa ba, in kuwa ya buWe baki ba abin kirki ne zai fito ba, shiyasa duk sonsa da komawa gidansu ya kasa motsin kirki yana zaune a wajan kamar mai Waukar karatu.

Didi kuwa a gidansu mijinta ya je ya Wauke ta, tun a mota ya fahimci tana da damuwa amma bai tambaya ba har suka je gida. Sai bayan ta ci abinci ta huta ya zauna kusa da ita ya ce, "A yanayin da ki ke ciki saka damuwa a zuciyarki bai kamata ba Aisha, yanzu buatar hutu ki ke yi da kwanciyar hankali ba wannan damuwar da ta mamaye fuskarki har ta nuna a jikinki ba. Don Allah ki sassautawa kan ki wannan tashin hankali, kin shiga third trimester fa, in baki samu kwanciyar hankali ba wanne a yanayi zaki kasance?."

Hawaye ya sakko daga idanun Didi, AbdulHamid ya ce, "kin gani ko? Yanzu meye na kukan? Me ki ka ce min last zuwan ki awo? Kin faWa min an ce jininki ya Wan yi sama kaWan, kin san da hakan kuma kika saka damuwa a ranki har da kuka Aisha?. Ko rasuwar da aka yi ce take taSa zuciyarki?."

"YallaSai Omar ne" ta faWa tana kallonsa da jajayen idanunta. Da mamaki ya ce, "Omar kuma? Shine ya saka ki kukan?." Didi "Damuwar Omar ce ta saka ni kuka yallaSai, Omar so yake jinina ya hau."

A tausashe ya ce, "Damuwar Omar kin saba da ita tun ba yau ba, meyasa zaki bari tayi tasiri a zuciyarki a irin wannan lokacin da ki ke buatar hutu da kwanciyar hankali?." Ta goge idanunta ta ce, "Ka san komai a tarihin iyayen mu, Omar ya i zuwa gaisuwa, nayi-nayi ya ce bazai je ba. acin rai ya ja ni har na mari shi ban sani ba."

AbdulHamid ya wara idanu ya ce, "Aisha mari? Omar Win ki ka mara?." Didi a raunane ta ce, "Wallahi ban san na yi ba, ban san na aikata ba YallaSai. Magana yake ta faWa mara kan gado, in da ban katse shi ba a lokacin tsaf zai furta kalmar saki akan Nayla. Tsaf zai ce ya saketa gashi tana tsaye a wajan, na mare shi saboda na katse shi amma sai na sake tunzura shi."

"Kema kin san dole ya tunzura, marinsa da ki ke yi shine ma zai saka i zuwa gaisuwar. Zai ga akan bai je gaisuwa ba ki ka mare shi, to bazai je ba." Didi ta ja numfashi ta ce, "kamar a gabanka aka yi. Ban san meyasa bakina ya furta saboda mahimmacin da suke dashi a rayuwarsa sune suka karSar masa aure ba, Wallahi ban san na faWa ba, saboda na san furta hakan babbar katoSara ce a gare shi. Wallahi tsawar da ya yi sai da Wan cikina ya motsa."

Duk da halin da take ciki sai da ya yi murmushi jin abinda ta ce kafin ya ce, "Ai ko nan gaba kar ki sake kuskuren marinsa, ke kin fi kowa sanin halinsa in ya shiga bacin rai, yadda ki ka yi losing control ki ka mare shi shima zai iya losing control ya mangareki. Kuma ke da ki ke neman ya je gaisuwa ina ke ina mari don Allah?." Didi ta ce, "ya Sata min rai ne wallahi."

"Ba yau ya saba ba, jurewar da ki ka saba yi dai ita zaki yi akansa. Yanzu da ki ka sako zancen aurensa kuma ki ka mare shi kin samu mafita yaje gaisuwar?." Ta girgiza kai alamun a'a ta ce, "A gaban idon Nayla ya fara dawo da maganar da ta wuce, shi ba sonta ya ke ba, ba son auren ta ya ke yi ba. Kuma ka san a yanayin da zai yi maganar, inda ace a hankali yake maganarsa fa saui, to cikin hargagin da ya saba yake magana. Yana nuna ta da yatsa yana cewa baya sonta baya aunar zama da ita. Harda rantsuwa duk abinda ya fito daga hannunsu baya so ciki harda auren da ita kanta Naylan. Ya juya kalle ta fa, idomta ya kalla ya ce ke bana sonki, bana son zama dake, alfarmar Didi ki ke ci kuma yanzu komai zai are. Ba dole raina ya Saci na mare shi ba YallaSai?."

"Subahanallah! Bai dai furta sakin ba ko?."
"Ciwon arya na fara yallaSai, zama na yi na fara rawar jiki na arya ina juya kai shine ya dakatar da shi. Baiwar Allah, itace ta saka ni a mota ta kai ni har gidanmu ta bani ruwa tana tambayata abinda nake so."

Ya ce, "Ai dole ki yi rawar jikin arya, da kin saka ya furta kalmar saki da ke kika jawo komai, alhakin sakin yana wuyanki. Kin fi kowa sanim halinsa bai kamata ki yi masa haka ba, yadda ki ka san halinsa kamata ya yi ki ci maganin zama dashi ba ta hanyar mari ba Aisha. Da dabara ya kamata ki yi masa magana ya je gaisuwar ba ta wannan hanyar ba. Tunda kin san shi kamar jariri yake sai da lallaSawa, carbin wai ne sai kin nutsu zaki iya jansa lafiya ba tare da ya fashe a hannunki ba."

Didi ta dafe kai ta ce, "ni ban san ma ya suka are da Nayla ba, kunyarta nake ji shiyasa da ta fita ko wayarta ban kira ba. Amma na san duk inda take yanzu kuka take yi. Nayla tana matuar aunarsa, kai ko bata sonsa furta mata kalaman da ya yi amfani dasu a Wazu zai taSa zuciyar ko wacce mace balle ita, wallahi Allah kunyarta nake ji matua."

"Ya kamata ki kira ta kuwa." Didi ta Wauko waya ta kira wayar Nayla har sau biyu amma bata Wauka ba. Ya kalle ta ya ce, "Ki bari zuwa anjima sai ki sake kira. Shi kuma Omar ki yale shi ya sakko da kansa zai zo har gidan nan, baya iya dogon fushi da ke. Amma kema kar ki sake kuskuren marinsa, yadda ranki ya Saci kika mare shi shima Sacin rai zai saka ya bugeki, bugewa Waya zai miki ki sume wallahi" ya faWa yana dariya.

Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Rigamar Omar tafi shekarunsa yawa, babban tashin hankalina ranar Omar ya san a gidan wanda yake zaune. Hmmm in Omar ya san gidan da yake ciki ga daga wajan wanda ya fito ai ina jin sai an yi aramin yai, fetur zai zazzaga min ya banka min wuta na one." AbdulHamid ya yi dariya ya ce, "kuWin haya ma kin ce kin biya ya dawo miki da kuWinki."

Didi ta ce, "Dariya ma abin ya baka? Hmmm baka san tashin hankalinsa ba ne shiyasa. Tun yana shekara sha bakwai yake walagigi dani, har yanzu ban huta ba."

Ya sake yin dariya ya ce, "Yanzu dai ki kwantar da hankalinki, wannan damuwar ce bana so, ki nutsu komai zai wuce in sha Allah." Didi ta ce, "Allah yasa, Allah yasa kuma bai yiwa ar mutane komai ba. Babban tashin hankalina kar ya furta sakin nan wannan wallahi, ban san zuciyar wa Omar ya gada ba, ba haka iyayen mu suke ba wallahi, hauri ne dasu da kuma saurin yafiya."
"Bazai aikata ba in sha Allah."
"Allah ya sa."
"Amin. Ta so mu je ki kwanta" ya faWa yaka rieta zuwa ciki saboda damuwar ce baya so ya ganta a ciki gabaWaya.KRB3P029
Arewabooks@nanahaleema11.

Nayla arfe tara na dare ta farka, tana jiyo hayaniyarsu a falo ta shiga banWaki, da yake ta san ba sallah zata yi bata damu lokaci ya wuce ba. Tana fitowa daga banWakin Mama ta shigo kamar yadda take shigowa dubata akai-akai, ta bita da kallo ta ce, "Nayla kin tashi? Taho falo cikin yayyenki ki ci abinci." Ba musu ta rie hannun Mama suka fito falon duk suka bita da kallo. Zama Mama tayi itama ta zauna Mama ta ce, "Ummimi samo mata abinci."

Nayla a sanyaye tavce, "A'a Mama bana ci." Mama ta ce, "baki da lafiya fa Nayla, yana da kyau ki ci abinci."
"zan sha tea kawai." Mama ta saka a kawo mata aka kawo mata. Mama ta rie shayin a hannunta tana jira ya yi sanyi ta bata. Babu wanda ya yi magana Mama ta fara bata da kanta tana sha har ta sha rabi kafin Nayla ta ce, "ya isa Mama" ta faWa tana sake kwantar da kanta a kafaWar Maman.

Mama ta ajjiye shayin ta ce, "ciwon kan ne?." Ta girgiza kai alamun A'a. Mama ta ce, "babu abinda yake damunki yanzu?."
"Jiri nake ji" ta sake faWa a hankali ba tare da ta Wago ba. Mama ta ce, "Ko dai kina da ciki ne Nayla?."

Duk da halin da take ciki sai da ta Wago da sauri ta kalli Mama da take kallonta tana jiran amsarta, kallon mutanen falon ta yi taga yaran Maman maza guda uku sai Ummimi, ta sunkuyar da kai ta girgiza kai alamun A'a.

Mama ta ce, "to me yake damunki? Ko mu je asibiti?." Nan ma ta girgiza kai alamun A'a. Mama ta ce, "to ki saki jikinki." Ta Waga kai alamun to ta sake kwanciya a jikin Maman. Mama ta sake kallonta ganin hawaye ya sakko daga idonta ta ce, "Hauwa wai ne ya faru ne? Yanzu kika farfaWo daga ciwon kai fa, kukan na meye haka?." Bata ce komai ba sai hawaye da take gogewa Mama ta ce, "meye ya faru?."

Bata iya magana ba ta share hawayenta ta ce, "bana jin daWin a zuciyata Mama, zuciyata zafi take yi min, ki rarrashe ni ta daina" ta faWa tana zaga hannayenta bayan Mama ta rungumeta tsam. Mama ta rie ta itama tana jin bugun zuciyarta a jikinta tace, "to ki daina kuka, ki nutsu ki faWa min damuwarki Nayla." Nayla ta yi shiru bata ce komai ba kuma ba ta Wago daga jikin Maman ba.

Mama ta rasa abinda zata ce mata sai tayi shiru kawai ta yaleta, Nayla ta sake gyara kwanciya a jikin Mama, itama ta rieta dan ta san tana jin Wumin mahaifiyarta ne a jikinta shiyasa duk inda Nayla ta ganta sai ta kwanta a jikinta. A hankali ta tsayar da kukan kuma ba ta Wago ba tana jikin Maman har lokacin. Mama ce ta Wago da ita ta share mata hawaye ta rie hannayenta duka biyun ta ce, "FaWa min damuwarki Nayla. Me ya same ki? Daga ija ki ke kika taho nan?."

Shiru ta yi bata ce komai ba, Mama ta kalli su Abbas da dukkansu jira su ke su ji damuwarta ta kalli Nayla ta ce, "Ko su Yayyenki su ba mu waje ki faWa min?." Jin haka sai Abbas ya mie ya ce, "Sai da safe Mama, Nayla Allah ya ara lafiya."

Mama ta amsa duk sai suka suka fita Ummimi ta hau sama. Mama ta ce, "taso" ta faWa tana rio hannun Nayla suka hau sama har Wakin Mama, Mama ta rufe ofa ta zauna a kusa da ita ta ce, "daga ni sai ke sai Allah, FaWa min me ya faru? Omar ya sake ki ne?."

Kai ta girgiza alamun A'a Mama ta ce, "to meye?." Cikin muryar kuka ta ce, "Mama ni na bar aurensa, ki faWawa Daddy a raba auren" ta faWa hawaye yana sakkowa daga idonta. Mama ta wara ido waje cike da mamaki ta ce, "a raba auren Nayla? Omar Win ne baki so yanzu?."

Nayla ta ce, "ni dai a raba auren kawai."
"To Nayla ana raba aure ne ba tare da a san dalilin da ya kawo hakan ba? Ko shi Daddyn su Salman in na faWa masa sai ya ce meya faru ki ke so a raba auren, in kuwa ki ka faWa min sai na faWa masa gabaWaya, ai babu wanda zai miki dole, abinda ki ke so shi za a yi."

Nayla ta ce, "Mama ba ya son zama da ni, gwara a raba auren a huta." Mama ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Shikenan dalilin?." Nayla ta Waga kai alamun eh, Mama ta bita da kallo tana hango damuwa sosai a tare da Naylan, sannan tana hango soyayyar Omar har gobe a idanunta. Amma tunda har ta buWe baki da kanta ta ce a raba auren tabbas duk abinda ya yi mata ya taSa mata zuciya sosai. Mama ta ce, "Ina shi Omar Win ya ke?."

"Ban sani ba."
"Ya san kin taho nan?." Ta Waga kai alamun e Mama ta ce, "shikenan. Ki kwantar da hankalinki, gobe zan je na samu Daddyn sai na yi masa bayani. Yanzu ki ta shi ki yi wanka zaki ji daWin jikinki." Nayla ta Waga kai ta rie hannun Mama ta ce, "Mama a raba auren da wuri kin ji?." Mama ta rie hannunta itama ta ce, "kar ki damu, Tashi ki yi wanka zan saka Ummimi ta kawo miki kaya sai ki saka."

Nayla ta ce, "Mama na taho da kaya suna mota." Mama ta ce, "to bara na saka a Wauko miki" ta faWa tana fita daga Wakin.

Ba jimawa sai ga Ummimi ta shigo da wayar Nayla da laptop da sauran kayan ta ajjiye ta fita. Nayla tana wanka tana kuka, ta dole ta iya furta a raba ta da masoyinta ba dan tana so ba, ta kai zuciya nesa ta ga kuma abinda ya kamata tayi kenan shiyasa ta aikata. Gwara ta bashi space tunda har ya buWe baki ya ce mata ba ya sonta, ido da ido ya kalle ta ya faWi haka, ya kuma ce har abada bazai so aurenta ba, gwara ta haura duk da son da take yi masa.

A haka ta fito ta buWe kayan ta saka doguwar riga ya zauna a gefen gadon. Wayarta kalla ta ga tana haske, ganin sunan Salma sai ta share bata Wauka ba ta jingina da fuskar gadon idanunta a lumshe.

Ranar da ta fara ganin murmushinsa ta tuna a gidan Didi, da ranar da suke je Kaduna ya yi mata murmushi da ranakun da suka biyo baya. Zuciyarta harbawa take, in ta ce bata son Omar arya take yi amma ya zata yi? Hakan shine mafita a gare ta da rayuwarta.

Ranar tare suka kwana a Wakin da Mama kasancewar mai gidan baya nan. Duk motsin da Nayla zata yi sai Mama ta buWe ido ta ce lafiya, hakan shine yake yiwa Nayla daWi take jin Mama kamar Ummanta da ta bar duniya.

" " " Da safe wanka tayi ta shirya, sai dai kallo Waya zaka yi mata ka hango damuwa da ramar da tayi lokaci Waya. Ummimi ce ta shigo ta kalle ta ta ce, "Yaya Nayla ki fito falo in ji Mama." Nayla ta girgiza kai ta fito zuwa falon a sanyaye ta sakko daga saman. Dukkan su suna zaune wani yana danna waya wani kuma yana shan tea. Kafin Nayla ta arasa sakkowa aka yi sallama aka shigo falon.

Wacce take bin Abbas ce da ake kira da Yaya Zahra da yaranta guda biyu suka. A guje suka taho wajan Mama suka faWa jikinta suna murnar ganin ta. A lokacin Nayla ta sakko daga saman ta ce, "Yaya Zahra sannu da zuwa." Anty Zahra ta kalleta tayi murmushi ta ce, "Naylan Mama."
"Na'am Yaya, sannu da zuwa."
"Yauwa Nayla, lafiya ki ke naga fuskarki ta Wan kumbura?." Mama ta ce, "bata jin daWi ne."

Nayla ta kalli Abbas da Khalid ta ce, "Yaya Abbas Ina kwana, ya Khalid ina kwana." A tare suka amsa Abbas ya ce, "ya jiki? Ina fatan baki kwana da zazzaSin ba." Nayla ta ce, "Eh ban kwana dashi ba, tunda Yaya Khalid ya yi min allura ya sauka." Khalid ya ce, "Amma fuskarki ta kumbura, kuka kika kwana kina yi ko?."

Nayla bata ce komai ba Khalid ya ce, "Nayla kar ki stressing kan ki da yawa fa, ko meye yake damunki ki kwantar da hankalinki ki sanar da Mama in ba haka ba zaki jawowa kan ki ciwo da arancin shekarunki, ki kwatar da hankalinki ki faWi duk abinda yake damu ki bazai gagari iyayen mu ba in shaAllah." Nayla ta Waga kai alamun to.

Yaya Zahra ta ce, "A nan ta kwana kenan, Mama lafiya dai ko?." Mama ta ce, "eh to lafiyar dai zan ce. Abbas in baza ka je aiki ba anjima zaka kaini gidan Daddy." Abbas ya amsa da to amma ya damu da ya san damuwar da ta saka Nayla a wannan yanayi.

Mama ta ce, "Nayla tashi ki je ki ci abinci." Bata musa ba ta tashi sai gata ta dawo da tea a hannunta zama tayi tana sha suna hira a falon sama-sama. Nayla ce ta mie tsaye a sanyaye ta ce, "Mama bara na Wauko wayata a sama." Mama ta amsa mata ta hau saman da kofin a hannunta.

Yaya Zahra ta ce, "Wai ne ya same ta ne? Ba dai sakinta ya yi ba?." Mama ta yi ajiyar zuciya ta ce, "bai saketa ba, amma ta ce sakin take so, ita kar a Wauki lokaci kawai ya saketa ta gama auren, shiyasa zan je na samu Daddy anjima." Yaya Zahra ta ce, "Tofa, ita da kanta ta ce ta gaji da auren?." Mama ta amsa mata Yaya ta ce, "ba a san dalilin ta na faWin hakan ba, tunda har ta furta da kanta gwara a raba auren."

Mama ta ce, "shiyasa zan sanar da Daddy, ta inda aka hau ta nan ake sauka." Yaya ta amsa suka cigaba da hira har Abbas da yake zaune.

Kamar Yadda Mama ta ce bayan sallar azahar Abbas ya kai ta gidan Daddy, ta same shi a falo ta yi masa bayanin yadda suka yi da Nayla. Abin ya bashi mamaki sosai, ya ce aje a kawo masa Naylan. Abbas aka saka ya koma ya Waukota.

Lokacin da ya koma a zaune ya same ta tana waya ita da Salma, ya kalle ta ya ce, "Nayla ta so mu je, Daddy yana son magana dake." Kashe kiran ta yi ta ce, "To bara na Wauko mayafi" ta faWa a sanyaye tana wucewa ta hau sama ba jimawa ta dawo suka tafi.

A falo ta samu Daddy da Mummyn su Salma da kuma Mama. Ta shiga suka gaisa gabaWaya ana tambayarta ya jiki ta amsa musu da ta ji saui. Daddy ya ce, "Hauwa na ji abinda Maman ki ta ce, auren kawai ki so a raba?." Nayla ta Waga kai a hankali kamar mai ciwon wuya. Daddy ya ce, "wani abun ne ya faru?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "Babu komai Daddy." Daddy ya ce, "Haka kawai ki ke so a raba auren babu abinda ya faru?."

"eh daddy." Daddy ya ce, "to shikenan. Yanzu a wajan Maman ki zaki zauna har sai an raba auren?." Nayla ta Waga kai alamun eh Daddy ya ce, "babu laifi, shiga wajan an uwanki ku gaisa." Nayla ta mie ta shiga cikin gidan.

Mummy ta kalli Daddy ta ce, "Jikinta a sanyaye yake duk yadda aka yi dole ce ta saka ta furta wannan kalmar Daddy, kamar ba a son ranta ba." Mama ta ce, "Kamar a gabanki akayi Mummy. Jiya tana faWa min jiya tana hawaye alamun abun yana yi mata ciwo sosai, ni da farko na Wauka ma sakinta ya yi."

Daddy ya yi ajiyar zuciya ya ce, "mu jira mu gani in mijin na ta zai biyo sahu, in dai ya biyo sahunta matsalar ba mai girma ba ce, in kuma bai biyo sahu ba matslaar mai girma ce wacce yake nuni da wataila bai karSi aurenta ba ne har yanzu."

Mama ta ce, "haka ta ce min daman wai baya sonta." Daddy ya yi murmushi ya ce, "shiyasa na faWa miki, in har yazo nemata matsalar ba mai girma ba ce, zai biyota dan ni dai bazan neme shi ba, amma indai bai zo ba za a raba auren kamar yadda Naylan ta nema. Daman dukkan mu ba son zamanta dashi mu ke yi ba, babu yadda zamu yi ne ya saka muka amince tunda tana so kuma mahaifinta ya zartar da hukunci. Zan kira mahaifinta na sanar dashi yanzu dan ya san abinda yake faruwa. Ni dai bazan nemi Omar dan naji abinda ya faru ba, tunda har ya san ta baro gida zan saka masa ido na bashi lokaci naga zai nemeta, kamar yadda na faWa in yazo daidai ne, in bai zo ba ma daidai ne."

Mama ta ce, "hakan ya yi, gwara ma da hakan ya faru ko babu komai ta

Please Login or Register in order to submit comment