Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ce,  Rouhi! Sai bata ce komai ba ta sake komawa jikinsa ya mayar da hannayensa ya rufeta a jikinsa yana jin farin ciki a ransa. Duk abinda zai mata, duk abinda zai bata baya tunanin zai biyata akan abinda tayi masa, shiyasa da ya samu so yake ya faranta mata a ko yaushe.

Da sauri ta Wago ta ce,  Rouhii kalli tawa motar fa, har yanzu sabuwa ce, wata ka sake bani?.
 Girman ki ne ya faWa yana pecking Winta a goshi. Itama a kumatu tayi masa ta bar wajan a guje ta sauka yana ™wala mata kira amma ta sauka. Sai gano ta ya yi ta buWe motar tana zagaye a harabar gidan. Marmerh da Musliha da suke wasa a ™aramin childeren park Win da aka yi musu suka ™arasa wajanta. Ta tsayar da motar ta saka su a ciki tana cigaba da juyawa cikin farin ciki.

Yana tsaye yana kallon su har ta gaji ta fito suka shigo cikin gidan ita da yaran. Barin wajan ya yi yana jiyo takun zuwan su Marmerh da surutun Musliha. Tana shigowa ta gansa a zaune da laptop Winta yana kallon yadda viewers da comments suke ™aruwa a hirar da aka Wora haka . Zama tayi a kusa dashi tare da yi masa pecking a kumatu. Sai kuwa Marmerh da Musliha suka yi irin abida tayi, suka yi dariya gabaWaya ta ce,  Thank you so much Rouhii, na gode sosai, mota ta yi kyau.

 Ta yi miki?.
 Thousand percent ta faWa tana murmushi cikin farin ciki. Murmushi ya yi bai ce komai ba sai su Marmerh da suke ta magana yana biye musu. Da ya juyo sai ya ga shi take kallo, ya Wauke kai ya cigaba da hira da ´a´ansa. Ya kuma kallonta yaga shi take kallo, sai ya tsayar da idanunsa a kanta yana Waga mata gira sama alamun ya dai ´an mata. Murmushi ta yi ta kwantar da kanta a kafaWarsa ya Wora hannu a cikin ta ya ce,  ki ke gudu ko?.

 Farin ciki ne ya yi min yawa.
 Shine zaki salwantar min da ajiyata?.
 Ni na isa? Bazan sake ba tuba nake. Ya kalli fuskarta ya ce,  ba a karSi wannan tuban ba, za a karSa ne in ´a´an ki suka yi bacci, sai mu ga in zan karSi tuban ko bazan karS ba. Dariya ta yi kaWam ta ce,  To shikenan, zamu jira mu gani.

Zuwa dare bayan ta yi shirin bacci, dan ranar tana so ta faran ta masa rai ta nuna masa ta ji daWin kyautar da ya yi mata. Wajan laptop Winta ta ™arasa ta duba ta ga ko Malaysia sun yi replay akan mail Winta, sai ta ga basu yi ba ta kashe laptop Win ta ajjiye. Šakin su Marmerh ta shiga ta tarar da nanny su tana ta dambe dasu wajan saka musu kaya. Ganin Nayla suka taho wajanta a guje, dole ita ta saka musu kayan bacci ta kwantar dasu tare da yi musu addu a.

Lokacin da ta shiga Wakinsa waya yake yi, ya saka wayar a speaker yana magana kamar baya so yana yatsine fuska. Ganin ta shigo ya saka shi zuba mata ido yana kallon ta, da ido ya yi mata alama da tazo inda yake ta taka ta ™arasa ya yi mata masauki a jikinsa. Magana ake masa a wayar amma ya daina ji sai da aka kira sunan sa ya amsa kawai ya ce yana zuwa ya kashe wayar.

 In Ina tare dake bazan iya aiki ba, zaki saka na dinga tafka shirme ne kawai. Murmushi ta yi ya kalle ta ya ce,  kin yi kyau ´an mata.
 Zan yi Wa na uku ka ce min ´an mata?.
 Eh mana, me ya canja? Komai yana nan kamar dai shekaru goma sha nawa ne ma? Ya faWa yana Waga mata gira yana kallon ta.

Ta fahimci lokacin da yake nufi ta yi dariya ta ce,  Nima ban sani ba.
 In ma kin sani ki ka ™i faWa to har yanzu komai yana nan bai canja ba. Nayla ta ce,  Rouhi ka faWi gaskiya dai, ni ai na fara tsufa ka fara gajiya dani. Ya Wago fuskarta ya kalle ta bayan ya haWe fuska ya ce,  Me ki ka ce Jidda? Na fara gajiya dake fa ki ka ce.

Ganin ya Waure fuska sai ta marairaice zata yi magana ya Wora yatsansa akan bakinta ya ce,  kar ki ce min komai Jidda. Ni Omar ni ne zan gaji dake? Yanzu har kina tunanin zan iya gajiya dake Jidda? Kina tunanin akwai inda zamu je a rayuwa na iya gajiya dake?.

Idonsa take kallo kamar yadda yake kallon nata ya ce,  Bana tunanin zan iya gajiya dake daga nan har a tashi duniya Jidda. Ke kaWai nake da bu™ata a rayuwata, sha awarki kaWai nake ji a duniya wallahi, kamar yadda ke ce mace ta farko da na fara sani kece ta ™arshe in sha Allah. Allah bai halicce ni dan na gaji dake ba Jidda, a ko yaushe karsashin son kasancewa dake ruSanya yake a tare dani, ko yaushe shau™i da son raSar ki sake ninkuwa yake a zuciyata. Ki daina wannan tunanin, ki daina tunanin na gaji dake domin kuwa ni Omar bazan iya gajiya dake ba!.

Murmushi ta ke yi ta ri™o wuyansa ta Wora kansa ™irjinta tana ji kamar ta zubar da hawaye saboda ™aunar da yake nuna mata. Shiru suka yi gabaWayan su kafin ta Wago ta kalle shi ta ce,  Bani da kamar ka a duk duniya, ina sonka Rouhi. Murmushin gefen baki ya yi bai ce komai ba sai kallon ta da yake yi. Sun zubawa juna ido suna kallo, Waga mata girar da ya yi ya saka ta murmushi shima ya yi ya ce,  kullum ™ara kyau kike yi Jidda, anya ba daga aljanna ki ka gudo ba?.

Dariya tayi sosai ta ce,  kamar ka san ranar dinner nan da aka saka hoton mu haka wani ya ce, wai anya wannan ba daga aljanna suka gudo ba.
 Ke dai Jidda, ni ai ba komai bane in kina nan.
 TaSWi, da ace ina da irin kyaun ka ai ni ba kalar auren ka ba ce ba, matar manya ce. Dariya ya yi sosai ya Waga wuyansa zuwa sama.

Hannu ta saka tana shafa dogon wuyansa har ya sauke bata cire ba ya ce,  daman ke ai ba kalar auren Omar ba ce, Allah ne ya duba maraicina ya bani ke. Amma in ba haka ba ina Omar ina wannan kyakykyawar halittar?.

 Allah ka fini kyau YaMar. Ya sosa goshinsa kamar yadda ya saba ya ce,  To wai ina kyaun yake?.
 Kai fa halfcast ne, tunda rabin ka Wan chad ne.
 Ni dai banga kyaun ba.
 Ni na gani, ´an mata da yawa ma sun gani. Murmushi ya yi ta Wora hannunta akan girarsa ta ce,  ko iya wannan kyau ne, kalli eyebrows Winka ta faWa pecking Winta.

Ta sake Wora hannunta a saman idonsa ta ce,  kalli idanun ka& . Ta sake yin pecking idon ta cigaba da cewa,  idanu masu kyau da ban tsoro. And, most attractive& . Ta faWa tana Wora hannunta akan bakin sa tare da yin light peck ta ce,  Iya shi kaWai kawai abin kallo ne. Kalli hancinka, kalli gashin kyakykyawar round face Winka.

TaSe baki ya yi yana jin yadda take ta lissafi ita kaWai ya ce,  ni dai bana gani. Dariya ta yi ta haWe goshin su waje Waya ya ce,  me zan samu ´an mata?.
 Duk abinda ka ke so.
 Godiya nake ya faWa a hankali cikin salo na soyayya da ™auna.

After some days& ..

Ready to say goodbye
Ko an™i ko an so na kusa gamawa=ĜƒÜ<Ĝûß>Ĝ#ŬKRB3P127

A cikin kwanakin kamar yadda Nayla ta turawa ™asar Malaysia mail sun yi approving, sun kuma karSi company Tiger a matsayin abokin kasuwancisu wanda zasu dinga aiki dashi. Hakan ya sake kawowa Omar sabuwar Waukaka da girma da arzu™i. Tare suka je Malaysia gabaWaya har su Marmerh, aka yi aka hannu a contract aka cigaba da aiki.

Omar ya zama so busy, in ka gansa a gida dare ne ko wani abu mai mahimmaci ya dawo dashi, amma ko yaushe yana office. A office Win ma ba zama yake yi ba, amsa wayar sabbabin customers kaWai ta ishe sa, balle ga ba™i daga inda bai yi tunani ba suna zuwa. Ba™i daga ™asashen ™etare suna kawo ziyara domin kasuwanci. A cikin kwanakin Omar ya saka zama mai kuWi na gaske, contarct Win da yake samu daga ™asashen waje sune suke sake Waga darajarsa da ta kamfaninsa zuwa sama, wanda bai san sa ba ma yanzu ya san sa saboda yawan ganin hotonsa da ake yi a social media. Kamfaninsa kuma ya sake yin suna, ga yawan tallace-tallace da ake bayarwa na a kafafan yaWa labarai.

A cikin kwanakin Nayla, ta haihu ta haifi Wanta namiji kyakykawa mai kama da babansa, har ya fi Musliha kama da Omar, dan shi irin sak ya Wauko kama da Omar, hatta gashin girarsa irin ta Omar ce. Kwanan ta Waya a asibiti ta dawo gida, a wannan karon da kansa ya je har gida ya nemo alfarmar ™anwar Mamansa akan ta zauna da Nayla. Ai kuwa hakan ya yi mata daWi sosai, ta yi farin ciki ta kuma ji daWin abinda Omar ya yi mata sosai.

Ranar da ta kwana uku da haihuwa tana zaune a falo tana faWa da ´a´anta, a lallai sai sun Wauki sa, ta rufe ido ta fara yi musu faWa cikin tsawa dan sun dame ta. A lokacin Omar ya shigo, jin muryarsa sai suka tafi wajansa a guje suna kuka. Ya ri™esu ya ™araso ya zauna ya ce, "Jidda lafiya? Me ya faru haka suke kuka?.
"Ina fa lafiya, sun zo sun ishe ni sai na basu shi, ina yi musu magana kuma sun ™i ji. Ko ta ya zasu iya Waukarsa oho musu.

Ya kalle ta cikin rashin jin daWi ya ce, "shine kuma zaki yi musu wannan tsawar? Haba Jidda, tun kafin na shigo na ji tsawar da ki ka yi musu, ai sai ki tsorata su, har nawa suke da za a yi musu wannan tsawar?. Nayla ta kalle sa da kallon mamaki baki buWe, dan ta lura sam baya so ayi musu faWa komai sai abinda suke ga dama suke yi, musamman Marmerh da take babba kuma mai ™iriniya, baya so ya ga Marmerh tana kuka ko kaWan yanzu sai ya damu kansa kamar wani babban abun ne ya same ta. Nayla ta kawar xa kai gefe ta ce, "Šan nawa haihuwar kwana ukun zan bawa waWannan yaran? In suka yar min dashi fa? Haihuwarsa na yi fa, ba bacci nayi na farka na gansa a gefena ba. Kawai dan kar su yi kuka sai na basu shi? Sun daWe basu yi ba.

Omar ya Wan yi murmushi ya ce, "Eh na san haihuwarsa ki ka yi ba ajjiye miki aka yi ba, amma ki daina yi musu irin faWa haka, ki duba har kuka suke yi fa. In kika yi musu magana a nutse ai zasu fahimta, tsawar nan tsorata su ki ke yi wallahi. Nayla bata sake magana ba ta Wauke kai ta cigaba kallon Wanta da yake kwance a jikinta. Omar ya kalle su da suke kwance a jikinsa ya ce, "Kar ku daina kuka kun ji, ku karSa ku jr ku yi wasan ku ya faWa yana basu kayan za™in da ya shigo musu dashi, suka karSa suka fita zuwa inda aka tanadar musu domin wasa.

Ya bisu fa kallo har suka fita, ya kalli Nayla da ba shi take kallo ba tare da yin ajiyar zuciya ya ce, "Ban samu mun yi magana ba sai yanzu, bana samun zama sai ta kama. Ta kalle sa fuska babu walwala ta ce, "ka yi busy ai, ni Win ma ba ganin ka nake yi ba" ta faWa tana Wauke kanta daga kansa. Ya Wan shafa kansa zuwa gashin fuskarsa ya ce, "Abubuwa sun yi min yawa ne wallahi, kwana biyu kuma bakya rage min aikin ne shiyasa. Na saba wani abun ke ki ke yi shiyasa abubuwan suka tarar min sosai. TaSe baki ta yi bata ce komai ba. Ya nutsu yana kallon yanayin ta dan sai ya ga kamar fushi take yi ya ce, "wai fushin me ki ke yi ne haka? Ina magana kina kawar da kai kina Waure fuska. Bata kalle sa ba ta ce, "ni ba fushi nake yi ba."
"Amma meyasa ki ke Waure fuska? Maganar ma kamar bakya so ki ke yi, da farko na Wauka saboda yanayin jikin ki, ne amma yanzu na lura kamar akwai wani abun a ranki.

Nayla ta ce, "GabaWaya yanzu ka zama baka da lokacina, ko yaushe kana office baka dawowa sai dare, kuma da ka dawo zaka cemin bacci ka ke ji ka gaji. Abinci ma ba ko yaushe ka ke ci ba, in na ce a aiko maka dashi office ka ce a'a. A haka ka ke so ka ganni kamar daaa?. Kaima ai ba kamar da Win ka ke ba yanzu.

Tunda ta fara magana yake kallon ta har ta gama, ya girgiza kai cike da mamakin rigima irin ta ta ya ce, "Jidda aiki ne yake yi min yawa kin fi kowa sani, ke da kan ki kina taimaka min wajan rage min wani abun. Kuma ina sane nake cewa kar ki aiko da abinci saboda yanayin da ki ke ciki, yanzu kuma kin haihu, in ki ka huta sosai zuwa gaba zan ce a kawo ai. Ta ya zaki ce bani da lokacinki? Ina da wanda zan bawa lokacina in ba ke ba?.

Ajiyar zuciya ta yi tana Wan taSe baki alamun bata yarda ba ta ce, "Haka ne." Ya yi murmushi yana kallon ta ya ce, "baki yarda ba kenan ko? Baki yarda da abinda nace ba?.
"Hmm ni ban ce ban yarda ba, tunda ka faWa ai dole na yarda ko bana so. Amma batun canji ka canja fa, a daa in na Wauki wayarka baka damuwa, har fita ka ke yi ka barta a hannuna, wani lokacin ni ce ma nake aiko maka da ita saboda kar a neme ka. Amma yanzu da na Wauka sai ka ce na baka zaka yi amfani da ita, ko da kaga zan yi amfani da ita sai ka riga ni Wauka kamar wacce take yi maka bincike a ciki. Kafi kowa sanin ba bincike nake yi maka ba, inda bincike nake yi maka a wayar da ka sani. Babban abinda yake tsaya min a rai meyasa baka so na ri™e? Meyasa baka so na Wauka bayan daa baka damuwa?.

"Saboda bana so ki ga abinda zai Sata miki rai ne." Da mamaki ta kalle sa ta ce, "Meye a wayar da zai Sata min rai? Yaushe aka samu abinda zai Sata min rai a cikin wayar?.
"Ba wani abun bane a, amma wayar tana hannunki message zai iya shigowa wanda baza ki ji daWi ba in kika gansa, ta ko wacce kafa messages da hotuna nake samu, ko nayi blocking wani zai zo. Duk da ba amsa nake bayarwa, ba amma in kika gani ranki bazai yi daWi ba, na san halin ki. Saboda haka nake kiyaye Sacin ranki, shiyasa bana so wayar ta jima a tare da ke.

Ta zuba masa ido tana kallonsa, kafin ta janye idanunta ta kalli gefe bata cr komai ba. Omar ya mi™a mata wayarsa ya ce, "karSi." Bata karSa ba ta cigaba da kallon Wanta tana shafa kansa. Ya Wan yi shiru na wani lokaci, kana ya ce, "Jidda kina zargin ina da ´an mata a waje ne ko kina zargin na fara bin matan banza?." Da sauri ta kalle sa ganin so serious ya yi maganar, ta langwaSar da kai a raunane ta ce, "A'a,ni ban ce ba."

"To meyasa ki ka damu dan ina karSar wayataa hannunki? In akwai abinda nake aikatawa wanda bana so ki gani ai bazan ma bari ki Wauki wayar ba ko da wasa. Da rufe ta zanyi na saka mata security wanda baki san sa ba. Na san kuma ba bincike ki ke yi min ba, sai amfanin ki Wauka Win ya zo ki ke Waukar waya. Amma saboda gujewa Sacin ranki da jin babu daWi a zuciyarki ya saka nake karSa. Amma ke naga zargina ki ke yi, zargi ki ke yi ina aikata wani abun mara kyau shiyasa.

Da sauri ta tare shi ta ce, "A'a wallahi, ni ba zarginka nake yi ba, har abada bazan taSa zargin ka ba ta faWa a raunane tana kallonsa. Ya zuba mata ido yana kallon ta kana ya ce, "To me yasa kika damu kan ki har ki ke fushi?." Nayla ta ce, "Kawai zuciyata ta kasa aminta da hakan ne, na riga da na saba da yadda muka fara tun farko, ganin wannan canjin zai saka min shakku a zuciyata.

 Shakku, a kaina Jidda?.
 A kan wayar ba kai ba ta faWa tana rausayar da kanta.  To waye mai wayar in ba ni ba?.
 Allah ba haka nake nufi ba.

Ya Wan yi murmushi ya ce, "Ni dai ina faWa miki, babu abinda zan Soye miki a cikin rayuwata da wajenta. Jidda ko budurwa na gani ina so zan aura you're the first person da zan fara faWawa, ko ya yi miki daWi, ko kar ya yi miki daWi, ni dai na faWa miki saboda kece komai nawa, dan bani da wata bayan ke. Daman ke da Didi ne, to ita bata duniya sai ke kaWai, dole ki jure abubuwan da zan dinga zuwar miki dashi dan wani bazai yi miki daWin ji ba. Ina so ki ri™e wannan, bisa kuskure na aikata wani abun mara kyau wallahi sai na faWa miki Jidda, ko mai muninsa sai kin sani.

Ta yi ajiyar zuciya a raunane ta ce, "balle ma baza ka ga budurwar har ka fara so ba, kuma baza ka aikata wani abun ba." Šan murmushi ya yi kaWan yana lumshe idanunsa akan fuskarsa kana ya ce, "ki kwantar da hankalinki, wannan Omar Win na ki ne ke kaWai in sha Allah, babu wata mace da zata yi miki over taking a wajena. Dan na san duk akan kar ki je ina da wata a waje ki ke wannan abun, to babu Jidda, har gobe da jibi kece kaWai. Abu Waya nake so a gare ki...." ta Wago ta kalle sa kamar yadda yake kallon idonta ya ce, "Yarda! Ki yarda dani kawai Jidda, bazan taSa cin amanarki ba in sha Allah. Yadda kika ri™e min amanar kan ki nima bazan ci amanar ki ba, zan ri™e miki kaina da zuciyata, babu wacce zata shiga zuciyata domin fadar ki ce. Murmushi jin daWi da walwala tayi, ya shafa kumatunta yana ja kaWan ya ce,  keda kishi aminan juna ne. Ta kwantar da kanta a kafaWarsa ta ce,  kai kuma fa?. Bai bata amsa ba ya kalli Babyn da yake jikinta ya ce, "da Abiy zamu dinga kiran sa?."

Da mamaki ta ce, "Sunan Abiy Win ne? Na Wauka sunanka ne."
"Sunan sa ne, in Allah ya kawo wani sai a saka sunan nawa." Ta yi murmushin jin daWin karar da ya yi mata ta ce, "Na gode YaMar." Ya Waga gira sama yana binta da kallo ya ce, "da aka yi me?." Murmushi ta yi bata bashi amsa ba, ta shafa kan yaron ta ce, "Allah ya raya mana Mufty."

Ya bita da harara ya ce, "kin cika iyayi, daga Musliha an samo Mufty. Ko da yake ´ar gayu ce ke, dole ki saka sunayen ´an gayu. Ta yi dariya ta ce, "kuma dole ka faWa ba, haka lokacin Musliha ka ce baza ka faWa ba, sai gashi yanzu shi ka ke cewa har ka sana." Ya yi murmushi ya ce, "zan fita, ki yi lisaafin abinda za a siyo da abinda ki ke so, babu lallai na dawo da wuri. Ta amsa da to bai jima a zaune ba ya tashi ya fita.

_Jiya na yi kuka sosai, na gama editing ina burin yau na yi update gabaWaya na huta, ina shiga naga ya dawo farko=Ĝ-Ŝ over 10k words, haka na gama kukana editing ya dawo farko. Na so na gama uptade yau amma ba zai yu ba, sai zuwa gobe in sha Allah._

P128

Haka aka cigaba da karSar ´an barka, mutane Kaduna zuwan su daban ne musmaman da suka ji sunan Abiy aka saka. An yiwa yaro hidima sosai kuWi da kaya kamar ba a so. Ranar suna aka raWa masa suna Abdallah aka yi hidimar taro kamar lokacin Musliha. Sai dai wannan lokacin an fi Sarnar kuWi, an fi kashe kuWi kamar ba nema ake yi ba, an yi Sarnar kuWi a sunan Mufty, dan sai da ya kai ya kawo duk wanda ya zo sunan bazai tafi ba sai da atamfa da takalmi da mayafi da dubu ashirin na Winki. Ga abubuwa manya-manya na rabo da aka raba a wajan, an yi hidima sosai kowa ya yi farin ciki. (Can na hango ´an Kiran Rabo comments section an hau layin karSar Souvenirs, ´an arewapen har sun fi ´an whatsapp za™ewa, ana ture su suna komawa).

    Bayan suna da kwana sati uku ya kama sati huWu kenan da haihuwar Mufty, Umma Saroot ta shiryata koma gida bayan ta gama shirya Nayla ta gyara ta yadda ya kamata. Dan ta lura Wan nata fitinanne ne, tunda ya lura Nayla ta samu tsarki babu zaman lafiya, har inda Umma take zai zo ya ce tazo, sai dai in taje ta gudo. Shiyasa tayi mata haWin da ba a yi mata a haihuwar Musliha ba, an yi mata gyara mai kyau sosai.

Kyautar mota Omar ya yi mata ban da kaya da kuWi da aka haWa mata, ba dan ya biya ta abinda tayi ba sai dan ya kyautata mata ya saka ta farin ciki. Ai kam ta yi farin ciki sosai, ta ji daWi tayi masa addu'a sosai. Dan a yanzu iyaye yake yi dasu, Umma sama Umma ™asa yake faWa cikin girmamawa da nuna su Win dangin mahaifiyarsa ne, in zai gaishe ta kuwa har ™asa yake dur™usawa. A ´an uwansu babu wanda bai kira sa ya yi murnar kyautar da ya yi ba, shi kansa daWi yake ji a zuciyarsa, daWin alkhairin yake ji a duk lokacin da yaga ya aikata ana farin ciki ana yi masa addu'a, sai yana ji ina ma tun Didi tana raye ya bar komai ya wuce haka da bai san farin cikin da zata yi ba, Allah bai nufa zata gani ba.

   Ranar da Nayla ta kwana arba'in ranar suka bar bar Nigeria ita da mijinta da ´a´anta. A ™asar Canada suka yada zango, a cikin HoneyRose hotel. Babban hotel ne a ™asar, hotel ne da ya yake cikin five star kuma yake cikin top ten a best hotel in honeymoon. Hotel Win yana Sangaren VIP, standard da kuma luxury. A vip suka yi reserving room, suka Wauki one parlor and  two bedrooms, Waya kids room, Waya kuma couples room.

Nayla ta buWe kids room Win, ta ga akwai toys na yara da aka tanada a ciki saboda yara su yi wasa. Nayla da take kallon Wakin ta kalle sa ta ce, "Zaka iya bari su kwana su kaWai Win ne?." Omar da yake bayanta ya yi ´ar dariya ya ce, "ba dole na ba, shiyasa aka tanadi wannan Wakin."
"Daman kaine ai baka so su kwana su kaWai, kamar wani abun zai same su."

A nan suka kwantar da Marmerh da Musliha da suka yi bacci, kasancewar wheather da suka samu

Please Login or Register in order to submit comment