Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko shi ya haife ta sai haka, duk abinda zai samu sai ya siyawa Marmher wani abu, kayan wasa kuwa kamar banza haka yake siya ya kai.

Nayla kuwa abin ba a cewa komai, siyayyar kayan sakawa da tarkace kayan kwaliyya haka zai kawo Nayla. Wani lokacin ya kan rasa me zai siya mata saboda sai ya ga komai tana dashi, shiyasa ya fi mayar da hankali a siya mata kayan ado tunda ya ga tana so.

Omar ya sake yin haske saboda zaman da kuWi suke a hannunsa, ya sake zama mai class na ™arshe, magana ma sai ka zama mai sa a za a yi maka. Dan yanzu harkar kasuwancin sai in ta kuWi masu yawa ne ake maganar dashi, amma komai da Bashir ake yi.

     Kamar ko yaushe yana zaune a falo tana kusa dashi yana ri™e da hannunta saboda ciwon kan da take fama dashi, yana bin tabon ciwon da aka ji mata da yatsansa a hankali ya ce, "Kin san me?." Nayla ta ce, "sai ka faWa."

"Akwai abubuwa da yawa da nake son siya, Akwai machines da kayan ado da za a dinga amfani dashi amma ance sai an je China ake samu." Nayla ta ce, "to ya za ayi yanzu kenan?."

Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ina tunanin zan je China Jidda, amma ance samun visa China yana da wahala sosai, shiyasa kaina ya kulle na rasa ya zan yi. Kuma bana so na tafi na barki, bana son yin nisa da inda ki ke kar a sake cutar min da ke.

Nayla ta Waure fuska ta ce,  ana zancen arzu™i zaka kawo wannan maganar, don Allah ka daina faWar haka komai ya wuce. Ya sauke numfashi ya ce,  to na daina, ina jin ki.

Nayla ta yi murmushin ta ce, "Indai ta visa ne baka da case, akwai wanda Abiy zai yiwa magana a cikin sati Waya za a iya buga maka visa China." Ya ce, "Da gaske?."
"Da gaske wallahi, Indai har zaka je Win kayi passport da komai, zan yiwa Abiy magana."

Ya Wan yin murmushi ya ce, "Shikenan, Gobe zaki raka ni passport office Win sai ayi." Nayla ta rungume shi ta ce, "Allah ya kaimu Rouhii, Allah ya cigaba da saka maka albarka a duk abinda ka saka a gaba." Ya yi murmushi yana shafa fuskarta ya ce, "Amin, ki cigaba da taya ni addu'a."

"Addu'a ko yaushe cikin yi maka mu ke yi." Ya kalle ta ya ce, "Daman ke ´ar baiwa ce ai, addu'arki da wuri karSuwa." Tayi dariya kafin ta yi magana ya ce, "da gaske nake. Tun daga ranar ashirin da bakwai ga watan ramadan na tsorata da lamarinki, kina kuka kina faWawa Allah abinda yake zuciyarki, a lokacin na ji a zuciyata Allah ya sa ba ™arata ki ke kaiwa ba."

Ta kwanta a jikinsa tana dariya ta ce, "kuma na kai masa ™arar ka, a lokacin da ka ke hararata, nace Allah kana ganin bawan ka, ina jin tsoron idanunsa yana hararata. Ya yi dariya mai sauti bai ce komai ba. Nayla ta ce,  Kukana nake kai masa, kuma wallahi Allah ya bani, babu abinda na ro™o wanda Allah bai cika min shi ba a wancan lokacin."

Ya yi murmushi ya ce, "shiyasa na ce ke ´ar baiwa ce ai. Ko zaki raka ni China? Kin ga dai ban taSa zuwa ba." Nayla ta ce, "ai da yawa wanda suke fara zuwa China duk basu taSa zuwa ba, a hankali suke gogewa su dawo ´an gari. Kuma da aka kashe min kuWi a tafi dani gwara ai siyi wani abun da kuWin, kar ka manta ginin gida ake yi."

Ya taSe baki yana kallon ta ya ce, "wai ke irin mai tausayin nan ko?." Tayi dariya sosai ta ce, "eh mu je a haka." Dariyar shima ya yi ta kalle shi ta ce, "zuwa nan da yaushe ka ke saka ran tafiya?."
"In aka samu visa nan da sati biyu ma zan tafi." Nayla ta ce, "lokacin bikinsu Ya J." Ya Waga girarsa ya ce, "Uhum sai ki yi abinda ki ke so ko? Shiyasa ki ke murna." Nayla ta langwaSar da kai ta ce, "ya za a yi na yi murna bayan Rouhiina zai yi tafiya ya bar ni?."

"Hmmm kya ji da shi dai" ya faWa yana murmushi ba tare da ya kalle ta ba. Itama murmushin ta yi kafin ya sake kallon ta su haWa ido ya ce, "Ya ciwon kan na ki?."

Nayla tayi murmushi ta ce, "tunda ka zauna ka ke tambayata, na ce maka na ji sau™i." Ya Wan yi shiru yana kallon ta kafin ya ce, "Šazu Didi ta ce min ina ki ke, sai na ce baki da lafiya, shine ta ce min ko ciki ne dake." Nayla ta Wauke ido daga kallonsa sai ya ja tsaki ya ce, "yanzu sai ki ce na baki kunya ko?." Nayla tayi dariya ta Wago ta ce, "ni bani da komai."

"Ya aka yi ki ka sani?."
"Ka manta ina on period ne yanzu haka? Shine ma ya saka min ciwon kan." Ya Wan yi ajiyar zuciya ya ce, "To yaushe zaki yi cikin? Da Didi ta faWa sai na ji ina so ki yi cikin, sai ta saka min sha'awar ace kina da ciki Jidda. Yaushe zaki yi?."

Ta Wan kawar da fuska bata ce komai ba, ya ce, "Allah ki ka sauke ido ™asa zamu yi faWa dake, ke komai kunya yake baki? Maganar ma kunya take baki?." Nayla ta yi dariya dan ta san yana adawa da wannan kunyar, baya sonta ko kaWan, ita kuma tana ™o™arin ta rage amma wani lokacin bata sanin ta nuna masa ta ji kunya.

Nayla ta ce, "Allah ya baka ha™uri Rouhii, ba kunya naji ba. Dariya ka bani da ka ce yaushe zan yi ciki." Ya harare ta ya ce, "ni zaki faWawa ba kunya ki ka ji ba? Wanne hali ne naki ban sani ba Jidda?." Ta sake yi murmushi ta ce, "Allah dariya ka bani."

"Dole na baki dariya ai, ni ba wasa nake ba da gaske nake yaushe zaki yi ciki?. Yaushe zaki karSi ajiyar Wana ko ´ata Jidda?. Ina so na ga kin haihu, kin ga nida Didi kawai iyayenmu suka haifa, abinda zan haifa da wanda zata haifa shine ahlin mu."

Nayla ta karyar da kai tana kallonsa ta ce, "To YaMar samun ciki ai sai lokacin da Allah ya yi." Ya girgiza kai yana kallon ta ya ce, "haka ne....amma komai da niya ko?" Ya faWa yana buWe idanunsa yana kallon cikin nata ido. Ya bata kunya sosai, amma bata so ta nuna masa sai ta daure ta ce, "To na kusa."

"Yauwa, ki da gagagwa kin ji? Yara nake so da yawa in Allah ya bani, kamar guda goma haka." Ta wara ido waje ta ce, "goma zaka haifa?."
"Zaki haifa min dai."
"Duk ni kaWai?."
"A'a ni da ke."
"Ka san wahalar haihuwa kuwa Rouhii?."
"Ke kin sani ai, tunda kin haihu Win" ya faWa yana kallon ta. Sai tayi dariya sosai shima kansa murmushi yake yi ta ce, "Goma fa da yawa, in na haihu goma ai na tashi aiki."

"Baki tashi aiki ba, ai ni kika haifarwa kuma tare da ni zamu zauna." Nayla ta girgiza kai ta ce, "To YaMar Allah ya bamu masu albarka."
"Amin Ashiq!. Zan yi ™o™arin ganin na baki ajiya  ke kuma sai ki yi gaggawar karSa, in na mi™o miki ki karSa a wannan karon kar ki ™i kin ji?."
Nayla ta ce, "Me zan karSa?."

"Cikin Mana." Ta rufe ido ta ce, "Allah ka bani kunya." Ya taSe baki ya ce, "to bani kayata." Ta buWe ido ta ce, "me?."
"Kunyar mana, kin ce na baki kunya shine na ce ki dawo min da ita."

Murmushi ta yi tana jan gashin fuskarsa a hankali ta ce, "Babu wanda zai ce kana magana haka, in aka ganka sai a Wauka baka da baki nan kuwa saura kaWan ka kai parrot. Sai an zauna da kai ake fahimtar waye kai. Duk da a zama da kai Win sai kaso a fahimta Win, in baka so ba baza a gane ba. Duk da akwai ka da faWa da zare idanu, amma ka ™aro wani class shiyasa ´an mata suke maka layi." Murmushi ya yi mai sauti ya ce, "kece ´an matan ai."

"Don Allah ba a cewa ana sonka?." Ya kalli idanunta ya hango tsantsar kishinsa a ciki sai ya ce, "kema kin san matashi kamar ni ai dole a gani a yaba" ya faWa yana juya idanu kamar mace. Sai kuwa ta Wauke fuska zata bar jikinsa ya ri™ota yana dariya ya ce, "wasa nake miki, ni bani da farin jini ai balle ace ana so."
"Kai Win? Kana kallon kan ka a madubi kuwa?." Ya kwaikwayi muryarta ya ce, "bana gani, ni ai kece madubina Jidda."

Ta kwanta a jikinsa ta ce, "ni dai kar ka dinga kula su, kuma kar ka yi min kishiya, in ka yi min kishiya Allah mutuwa zan yi." Dariya ya sake yi ya ce, "Kina cemin yara goma sun yi miki yawa ba dole na fara tunanin wata ba."

Da sauri ta kalle shi ta ce, "zan iya, ko ashirin ka ke so zan yi, amma kar ka ce zaka yi min kishiya aka ji" ta faWa zata fara kuka. Ya yi dariya ya ce, "wasa nake miki, kar ki yi min kuka, shagwaaSSiya sarkin kuka. Wasa nake yi, ki kwantar da hankalinki kin ji?." Kai ta Waga kamar mara lafiya ta lafe a jikinsa tana sauraron bugun zuciyarsa, itama ta ta tana bugawa saboda kishinsa.KRB3P077
Nana haleema.

     A washe garin ranar kamar yadda ya ce suka ce aka yi international passport, a ranar aka yi aka basu, Nayla ta faWawa Abiy abinda ake so ya ce a tura masa visa page Win Passport Win. Kamar yadda ta faWa cikin kwanaki kaWan aka samu visa ta fito, ya siyi ticket Win ta tafiya duk da taimakon Nayla ake komai tunda itace ta saba.. Ana e gobe zai tafi da daddare ta ishe shi da rigima da shawagaSa, sai rarrashinta yake yi duk ta ruWa shi. Shi kansa sai ya ji tafiyar ta fita daga ransa, dan baya so ya yi nisa da ita kamar yadda bata so.

       Tana jikinsa tana jan numfashi a hankali alamun ta yi kuka ta gama, cikin sigar rarrashi ya ce, "in kina kukan nan ni ya ki ke so na yi? Tafiya zan yi fa, in na tafi ina tunanin na bar ki kina kuka bazan yi abinda ya kai ni ba. Sati uku kawai zan yi, kuma kinga biki za ku yi zaki ga lokacin ya yi saurin dawowa tunda kina cikin ´an uwanki."

Nayla ta Wago ta kalle shi suka haWa ido ya yi mata kiss a goshi yana shafa fuskarta a hankali, ta Wora hannunta a fuskarsa tana shafa gashin fuskarsa ta ce, "Ni ba cikin ´an uwa nake so na zauna ba, tare da kai nake so na zauna Rouhii. Zan yi kewarka, sati uku fa da yawa, Zan yi sati uku babu kai" ta sake faWa hawaye na sakko mata. Omar cikin damuwa ya ce, "kukan ne bana son gani kin san da haka, ki kwantar da hankalinki zan dawo ai." Ganin ta™i yin shiru sai ya sakata shirun ta dole dan kukan na ta yana tayar masa da hankali sosai.

      Ta yi matu™ar ™o™arin bada gudunmawar da zata tsaya masa a rai ya dinga tunawa koda baya nan, ai kam ta yi nasara, dan ya ji yayi tafiyar ta fita daga ransa duk ya bi ya damu baya so ya tafi ya barta. Sai tattalinta yake yi, da ta motsa ya dinga tambayar me ya same ta ko me take so, a haka suka wayi gari. Da kanta ta yi breakfast duk fuskarta da damuwa, a haka suka ci tare yana sake rarrashinta amma ta kasa sakewa yadda yake so.

Bayan sun kammala cin abincin ne ya ri™e hannayenta yana kallon ta ya ce, "Ki yi ha™uri ki kwantar da hankalinki, da na tafi zaki ga lokacin dawowata ya yi." Ta Waga kai ta ce, "Allah ya kiyaye hanya."
"Amin Ashiq. Ta so mu je ki taya ni haWa kayan kin ga lokacin tafiya ya kusa." Babu yadda ta iya tare suka haWa kayan dan jirgin ™arfe biyu zai hau.

       Karfe sha biyu na rana Didi ta zo gidan yi masa sallama, da ta shigo ya yi murmushi ya karSi Marmerh da tayi wayo sosai yana yi mata wasa tana dariya. Ya kalli Didi ya ce, "Gidanki nake niyar zuwa sai ga ki." Didi ta ce, "Dole na fito ai na yi maka sallama." Ajiyar zuciya ya yi ya kalli Nayla, ya kalli Didi ya ce, "ki rarrasheta Didi, sai kuka take yi, kukan ne ni kuma bana so wallahi." Didi tayi murmushi ta ce, "To ai dole ta yi Omar, tafiya zaka yi har na sati uku fa, ta saba da kai dole ta damu."

Ya kalli Nayla da ta sake rau-rau da ido, ya sake kallon Didi a tausashe ya ce, "Ya zaki dinga zuga ta Didi? Yanzu sai ta fara kuka." Didi ta ce, "yanzu zaka tafi?." Omar ya ce, "Sai na yi sallar azahar, zuwa ™arfe Waya in sha Allah." Didi ta kalli Nayla da take tsaye har lokacin ta kalle shi ta ce, "Allah ya nuna mana lokacin."

"Amin, Zan je wajansu Bashir na dawo." Didi ta ce, "to sai ka dawo." Ya kalli Nayla ya ce, "Don Allah ki daina Waure fuskar nan ko kyau bakya yi" ya faWa da tsokana yana kallon ta. Šan kawar da kai tayi bai ce komai ba ya fita da Marmerh a hannunsa.

Didi ta dinga rarrashin Nayla da kalamai masu daWi har ta sake suka cigaba da hirar bikin Salma da Jawad. Ba jimawa ya dawo Marmerh tayi bacci a kafaWarsa ya kwantar da ita ya shiga cikin Waki. Nayla ta tashi ta bi bayansa ta samu ya shiga wanka ta dawo wajan Didi ta zauna. Ba jimawa ta sake komawa ta tarar ya shirya cikin ™ananun kaya wanda suka yi masa matukar kyau sosai. A tsaye ta tsaya a bayansa tana kallonsa shima yana kallonta ta madubi, a sanyaye ta tako ta ™araso inda yake ta rungume shi ta baya.

Juyowa da ita ya yi ya ri™eta ta gaba ya lumshe ido yana ji kamar ya tattara ta su tafi. Sun jima a haka a tsaye kafin ya Wago fuskarta ya yi kissing lips Winta na ´an mintina kafin ya kalli idonta ya ce, "Zan yi kewarki Ashiq!." Ta kalle shi ta ce, "Nima zan yi kewarka Rouhii! Zan yi kewar ka sosai."

Cike da tsokana ya ce, "ki faWa min gaskiya ni zaki yi kewa ko aljanun dare?." Dariya ta yi ta ce, "Duka biyun." Ya Wan buWe ido ya ce, "Ki ce Jidda itama ta zama ´ar hannu, itama yanzu ta zama always available." Kwanciya ta yi a jikinsa cikin kunya, ya yi dariya ya shafa bayanta ya Wago da ita daga jikinsa yana kallon ta. Ya kalle ta ya ce,  Ban da fita ke kaWai Jidda, ban da yawo a mota ko yaushe. Duk inda zaki je ki faWa min, sannan ki saka a kai ki kar ki fita da kan ki. Ganin zata yi kuka ya ce, "Kar ki min kuka, zo mu je" ya faWa yana ri™o hannunta ita kuma ta ta jawo trolly bag Win da zai tafi da ita.

Tare suka fito falo, Didi ta mi™e tana kallonsu tana murmushi cikin burgewa ta ce, "Ka fito?." Kai ya Waga ya kalle ta ya ce, "Na fito Didi, ki taya ni da addu'a." Didi ta ce, "Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya, ya baka abinda ka je nema."

Murmushi ya yi yana kallon ta, ya saki hannun Nayla ya ri™e na Didi duka biyun ya ce, "Amin Yaya Aisha, Duk abinda ki ke so ki faWa min kar ki ce bana nan baza ki faWa min ba, in wani abun ya taso na Marmerh ki sanar dani. Sannan ban da yawo ko ina musamman da daddare, bana so wani abu ya same ki. Didi tayi dariya jin sunan da ya kira ta dashi ta ce, "To Yaya Omar, in sha Allah." Ya kalli Nayla ya kalli Didi ya ce, "ki kular min da amanata Didi, da ke kaWai na yarda na bar ta a hannunki, kar ki bari ta dinga wannan kukan kin ji?."

Didi ta ce, "in sha Allah Omar, zan yi duk abinda zan yi wajan tayata farin ciki."
"Na san zaki yi Didi." Ya shafa fuskar Marmerh da take bacci, ya kalli Nayla da take hawaye ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Yaushe zaki tafi gidan Daddy Win?." Cikin dauriya ta ce, "In anjima" ta faWa murya na rawa sosai. A tausashe ya ce, "Don Allah ina ro™onki kar ki dinga fita ke kaWai, duk inda zaki je in dare ya yi kar ki ce zaki yi driving ki bari a kai ki. Ina so naje na dawo na same ki lafiya, bana so wani abun ya same ki kin ji?.

Nayla ta Waga kai alamun to, ya tako ya zo inda take ya ce, "in kina kukan nan sai na ji kamar na fasa tafiyar nan, gabaWaya tafiyar ta fita daga raina wallahi, a haka kike so nayi farin ciki in kina kuka?. Baki ga Didi bata kuka ba?." Sake shiga jikinsa tayi tana sauke ajiyar zuciya, ya yi murmushi tare da rungumeta idanunsa a kulle kafin ya sake ta ya Wagota daga jikinsa ya ri™e hannunta ya ce, "Zan tafi."

Ta goge hawayen idanunta ta ce, "Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya."
"Amin Ashiq, Ki yi min alqawarin baza ki cigaba da kuka ba."
"Ban yi alqawari ba, ni kaWai  na san me nake ji a zuciyata."
"nima ni kaWai na san abinda nake ji, amma na yi ha™uri kema ki yi kin ji?."
"Bazan iya ba."

Murmushi ya yi ya kai bakinsa kusa da kunnenta ya ce, "Aljanun da suka tashi jiya a wannan yanayin na baki ajiya Allah yasa ki karSa, so nake kafin na dawo na ji an ce ajiyata ta yi ™wari, har Didi ta san na baki ajiya Wanta." Murmushi tayi mai sauti ta rufe ido ya ja hancinta ya ce, "kunyar ce ko?." Murmushi take yi ta ce, "in dai ka bada ajiyar da kyau na karSa, in kuma baka bayar yadda ya kamata ba laifina ba ne."

"Bara na faWawa Didi a ji laifin waye." Ta wara ido ta ce, "Rufa min asiri, kar ka faWa mata don Allah."
"To na rufa miki, amma sai kin yi dariya na gani." Sai kuwa ta yi dariyar ya juyo inda Didi ta ke ya ga bata wajan ya kalli Nayla ya ce, "kin ga kin saka na za™e da yawa a gaban Didi, gashi ta gudu."

Nayla ta ce, "Allah babu ruwana, laifin ka ne."
"Laifin ki dai." Ta kalli agogo ta ce, "Mu je na san su Bashir suna jiranka." Šaukar jakar ya yi ya ri™o hannunta sai ta turje ta tsaya ta ce, "Rouhii!." Ya juyo ya kalle ta ya ce, "Na'am Ashiq! Me ki ke so?." Ta matso kusa dashi ta ce, "to ka Wan rage tsaho ka yi min tsahi da yawa."

Bai ce komai ba ya Wagota jikinsa ya rabata da ™asa, ta yi kissing Winsa kamar yadda ya yi mata Wazu. Idanunsa a lumshe ta kalle shi ta ce, "Ina sonka Rouhii." Ya lumshe ido ya ce, "Ina sonki Ashiq!." Murmushi ta yi ya direta a ™asa suka fito tare, a nan suka tarar da Didi suna hira Bashir ganin fitowa su ya saka suka karSi jakar aka saka a mota.

Didi ya kalla ya yi murmushi itama murmushi tayi, ya kalli Nayla ya girgiza mata kai alamun kar ta yi kuka. Bata yi kukan ba sai ya Wauke kai daga kallon ta, ya kalli manyan yaransa da suka zo yi masa sallama duk suka gaisa sannan ya shiga gaban motar Goje da Tk da sabon yaronsa Mustapha suka shiga baya suka fita daga gidan.

Nayla tare suka koma da Didi, ta yi ™o™ari ta ware suna ta hira da Didi har ya kira ta a waya ya shaida nata sun shiga jirgi zasu tashi. Suka yi masa fatan sauka lafiya daga nan ya kashe suka cigaba da hira da Didi. Amma zuciyar Nayla babu daWi, kewar mijinta take ji amma babu yadda zata yi.KRB3P078
Nana haleema.

    A daren Nayla ta Wauki motarta a gidan Hajja ta haWa kaya ta tafi gidan Daddy dan Salma ma ta koma har Hajja tana can ana ta shirin biki. Suna zaune gabaWaya a falo ana ta shirye-shirye Mummy ta ce, "Nayla ai na Wauka Kaduna zaki gudu."

Nayla ta kalli Salma tana dariya ta ce, "Ai Mummy ina nan, ni ce babbar ™awar amarya ina zan tafi Kaduna?." Mummy ta yi dariya ta ce, "Gaskiya ne. Kuma kin san da yake ma duk events Win a nan ne ba damuwa za a yi da zuwa can ba." Nayla ta ce, "shiyasa ban saka a raina zan je ba, ina za a kai amarya ma tafi" ta faWa tana dafa Salma tana dariya.

Mummy ta ce, "na Wauka baza ki je ba ai."
"Zuwa kai Mummy." Suka cigaba da hirar biki tana yi tana kallon waya dan ta san har lokacin mijinta yana sama suna tafiya.

Haka aka cigaba da hirar biki kamar baza su yi bacci ba, sai dare sosai suka yi bacci. Nayla tana tashi da asuba waya ta duba ta shiga WhatsApp tana tura masa sa™on kewa da sauran su kafin ta cigaba da harkokinta.

Sai da ya kwana biyu da tafiya da yamma tana zaune an gama yi mata gyaran jiki, dan duk abinda aka yiwa Salma sai an yi mata kawai ta ga kiransa ta whatsApp call. Hannunta har rawa yake yi ta Wauka ta saka a kunne ta kasa cewa komai. Daga nasa Sangaren shima bai ce komai ba sai daga baya ya yi murmushi tare da ajiyar zuciya ya ce, "Ashiq!."

Nayla a kasalance ta ce, "Rouhii!." Omar ya ce, "uhum kina lafiya? Ina fatan kin daina kuka ko?."
"Rouhi bazan daina kuka ba har sai ka dawo."
"Ki fara lissafi, har an ci kwana biyu ko?."
"Ka sauka lafiya?."
"Lafiya lau, shigata hotel kenan na kiraki, Na damu na ji muryarki, zuciyata tana faWa min matata tana nigeria tana kuka."

Nayla cikin shagwaSa ta ce, "Baka huta ba?."
"Ban huta ba Jidda, sai yanzu da na ji maganarki zan huta. Na gaji sosai, ina ma kina tare dani da kin yi min tausar nan taki mai saka ni bacci." Nayla ta lumshe ido ta ce, "Ka je ka huta Rouhi, na san in ka gaji sai ka fara ciwon kai, bana so kanka ya yi ciwo."
"Zan huta Ashiq!. Kina lafiya? Kin fara jin alamun ajiyata?." Nayla tayi dariya kaWan ta ce, "Rouhii haka ka ke son yara ban sani ba?."

"Nima ban san ina so ba sai da aka haifi Marmerh, ina so na ga an nuna yarinya kyakyawa kamar ki an ce wannan ´ar Omar ce wacce Jiddan shi ta haifa." Murmushi ta yi ta ce, "Yanzu ka huta tukunna, bana so ka yi ciwon kai."
"Yanzu kuwa Ashiq! Dare ya yi sosai a nan, asuba ta kusa."

"Mu kuma ko sallar magriba ba mu yi ba."
"zan kira ki video call in anjima, ki kasance ciki shiri zan ga abinda na yi kewa, ina nan ina tunani da kewar rashin jinsu a jikina da bacci tare dasu, kin gane ai." Dariya tayi shima haka ya kashe wayar.

Nayla bayan sun gama waya sai walwalarta ta ™aru ko babu komai ta san yana lafiya. Ta cigaba da harkokinta bai kira ta ba sai bayan sallar i'sha ta shiga Waki har da rufe ™ofa ta saka lock ta zauna sannan ta Wauki kiran.

   Fuskarsa ta bayyana akan screen Win sai ta ga ya sake yi mata kyau yayi haske gashin kansa ya kwanta kamar ba shekaran jiya suka rabu ba. Omar ya ce, "Ya dai ki ke kallona, na

Please Login or Register in order to submit comment