Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na rasa yaushe zuciyarka zata yi sanyi Omar, na rasa abinda za a yi maka da zai saka kayi sanyi wallahi.
 Babu, babu abinda zai saka na sakko ™asa Didi. Didi ta ce,  ai shikenan.

 Kawai zan je mu haWu dasu, ayi kare jini biri jini, koni ko su, ko su karni ko na karsu. Abinda nake so dake koda zasu kashe ni, ki tabbatar da Jidda ta kasance cikin ™oshin lafiya, ki tabbatar abinda yake cikin ta ya rayu cikin aminci. In ta haifi namiji ki saka masa sunana, in macece sunanki. Amma ki fara tambayarta, in tana da zaSin suna a saka zaSinta. Sannan ki san duk yadda zaki yi ki tabbatar da Jidda bata auri wani namijin bayan ni ba, ta cigaba da rayuwa a haka har tazo ta same ni mu tashi a aljanna. In ta auri wani bayan ni bazan taSa yin farin ciki ba har abada! Ya faWa so serious yana kallon Didi.

Rauni ya mamaye zuciyar Didi ganin da gaske yake maganar, ta ri™e hannunsa ta ce,  Omar me ka ke faWa haka?.

 Gaskiya nake faWa miki Didi, zan iya sadaukar da raina akan Jidda da abinda yake cikin ta. Marmerh a iya kallo Waya soyayyarta ta cika zuciyata, cikin jikinta kuwa tunda aka ce min an same shi nake jin son ko meye a zuciyata. Da na rasa abinda yake cikinta gwara na sadaukar da raina a huta. Daman ba saboda ni suke wannan abubuwan ba? To in na mutu ba shikenan an huta ba?.

Didi ta fara kuka cikin rauni ta ce,  babu abinda zai same ka, baza ka mutu ba Omar, baza ka mutu yanzu ba in sha Allah. Kuma Omar in ka koma ka Wauki makami dan tsayar da wannan maganar hakan ba masalaha bane, domin wallahi baza su ha™ura ba. Kuma Omar duk Waukakar da ka samu a rayuwarka ka rasa dame zaka sakawa wanda ya yi maka sai ta hanyar cigaba da abinda ka bari!?. In ka yi haka baka godewa Allah akan ni imar da ya yi maka ba, in ka aikata haka wallahi ka butulcewa ni imar Allah, kuma ka bar baya da ™ura, domin baza a taSa daina bibiyar mu ba har abada!. Ka fini sanin illar daba, kai da kanka ka taSa bani labarin wani babban mutum da yayi irin rayuwarku har girmansa, ™arshe har gida aka shiga aka yi masa yankan rago saboda Waukar fansa kawai. Kowa ya san daba haka take, kai zaka aikata laifi amma a kan danginka za a Wauki fansa, matu™ar ka sake komawa ruwa ka gama cutar kan ka da ahlinka. Yadda ka juya mata baya ina so ka sake juya mata baya, ka sauke kai ™asa domin wannan fitinar ta lafa.

Yayi ajiyar zuciya yana shafa goshinsa da yatsunsa kamar yadda ya saba, ya rufe ido ya buWe cikin rashin mafita. Didi ta ce,  ka je ka same su Omar, ba lallai sai ka bada ha™uri ba, ko kuWi ne ka biyasu akan su janye.

 Bazai janye ba, na san halinsa.
 To ku tattara ku bar Kano kai da ita, kana da arzu™in da zaka iya zama a wani garin ba lallai sai nan ba. Ya harare ta ya ce,  kawai ki ce naji tsoro na gudu na bar garin saboda tsoronsu.
 Ba tsoro bane Omar, ja da baya ne.
 Su a wajansu tsoro ne, kuma inaso ki tuna, Omar baya ja da baya.

Didi ta ce,  ni dai bana so ka butulcewa mahaliccinka akan ni imar da ya yi maka, Waukar makami ka je ka ya™e su ba naka bane, Allah ya yi maka suttura bai kamata ka wula™anta kanka ba, Allah ya Waukaka bai kamata ka ™as™antar da kan ka ba. Allah bai duba laifukan da ka yi ba yayi maka abinda baka yi tunani ba, meyasa zata gode masa ta wannan hanyar?. A nutse take maganar hakan ya saka take ratsa shi har zuciyarsa. Ya lumshe ido ya buWe ya ce,  Didi Jidda ake so a kashe fa, abinda yake cikin ta suke so su zubar tun bai zama mutum ba.

 Suna son zubar da cikin jikinta dai ba kashe ta ba, saka maganar da ka yi a ranka shine ya kai ga yin mafarkin za a kasheta. Mafarki kuma ba gaskiya bane Omar. Ka kwantar da hankalin ka, ka je ku yi magana cikin nutsuwa komai zai zama labari.

Yayi shiru bai ce komai ba, Didi ta ce,  Sai ha™uri haka sakayya take akwai ciwo. A haka ma dan kana sallah kana salati, kana sadaka kana taimako shiyasa Allah yake sassauta maka. Abinda nake guje maka kenan tun a baya Omar, babu rabon zaka fahimta sai yanzu. Allah yasa komai ya tsaya daga nan, mu cigaba da neman tuba muna faWawa Allah.

 Astagafirullah! Ya furta a hankali tunawa da ta addacin da suka yi a da. Didi ta sake nutsuwa ta ce,  ka je ka nemi mafita kafin wani abun ya sake Sullowa. Ina Naylan take?.
 Tana gidan Yayarta.
 To ka je ka san abinda zaka yi kafin ta dawo.
 Zan yi Didi.
 Ko ka kira wannan dpo da ku ke shiri dashi ya shiga maganar, ko iyaka ya yi maka da Šan ™auran ai an rage.
 Na gaji da saka hukuma a lamarina Didi, da kaina zan Wauki mataki.
 Ha™uri zaka yi da Waukar matakin nan, dole a saka hukuma a ciki matu™ar kana son zaman matarka da Wan ka lafiya.

Ya sauke numfashi ya kalle ta ya ce,  Koda za a kashe ni ki tuna da abinda na faWa miki dai, ni jikina yana bani gwara naje su yi yadda suke so dani a ku huta da wannan tashin hankalin. A baya in naga mutum ya zubar da makamansa ya bada ha™uri saboda danginsa ina Waukar hakan a matsayin tsoro, kuma ina ganinsa a matsayin wanda ya bada maza. Ashe abinda ake ji kenan& gwara na je ayi ta ta ™are indai zaku zauna lafiya. Didi ta girgiza kai ta ce,  baza ka mutu ba in sha Allah, mutuwarka ba mafita ba ce. Ya kake so mu yi in baka nan? Ni da nake fatan na bar duniya Marmreh tana da kai kuma ka dinga faWar haka? don Allah ka daina, bana so.

Ya lumshe ido ya kalle ta sai yaga tana hawaye, yayi murmushi ya ce,  wai ke irin mai sona Win nan ko? Bakya so na mutu na bar ki. Ta goge ido ta ce,  eh ka Wauka hakan ne, sai na riga ka barin duniya in sha Allah. Na fi so na mutu na barwa Marmerh uba kamar ka, yallaSai mahaifinta, kai kuma ubanta. Yayi ´ar ™aramar dariya da son kawar mata da damuwa ya ce,  To ki mutu Win mana, ai ba Jidda ce zata mutu ba balle na damu ya faWa yana taSe baki.

Didi tayi dariya sosai ta ce,  Nima mijina yana sona, baya so na barshi. Kuma na janye maganata, kaje ka mutu ka ji Omar. Kuma wannan ™aunar da ake mana rawar kai a kanta nice silarta, ko an™i ko anso Aisha ce silar wannan soyayyar.

 Kin ci ™arya kin kwana da yunwa, wannan soyayyar haWin Allah ce, ko da Aisha ko babu Allah ya yi nufin ™ullata.
 Ko mutuwa tana da sila, faWa min waye silar?.

Yayi murmushi ya ce,  Anji kin zama sila, in kin isa ki raba ™aunar.
 Aikin banza, kamar ba kaine ka dinga masifa ba, kana ihu kana cewa ni bana so, ai bance ina sonta, kuma bazan sota ba. Didi in ke kika halicce ni sai ki saka min sonta, wallahi zan yanke ala™a da ita ta faWa cikin kwaikwayon muryarsa tana dariya.

Dariya yayi mai sauti kamar yadda take dariya, ya girgiza kai ya ce,  ni kika yiwa gori ko? Shikenan zan rama. Ta yi dariya ganin ta kawar masa da damuwar kan fuskarsa sai taji daWi. Ya kalle ta ya ce,  Jidda bata san maganar nan ba, kar ki faWa mata, bana so ta damu.

 Daman bai kamata ta sani ba, tsaf tsoro zai saka mu rasa unborn. Ya girgiza kai bai ce komai ba, ta matso ta Wan yi masa side hug ta ce,  Ka je kayi abinda ya kamata, amma kar ka bar baya da ™ura don Allah.

Ya girgiza kai ya ce,  to meye na shige min jiki? Sai kin saka matata taji hakan a ranta? Kamar fa cin amanarta ne. Didi ta Wago tana kallonsa taga ba murmushi yake yi ba alamun da gaske yake, sai ta ce,  ka faWawa matar ta ka, kafin ta shige maka jikin ni na shige. Kuma ka faWa mata ni Win nan dai babu abinda ban maka ba, tun daga kan wanka& . Bai bari ta ™arasa ba ya rungume ta yana murmushi ya ce,  zan rama wannan gorin Didi, ki bini bashi ya faWa yana raba kansa da ita ya fita yana jin damuwarsa ta ragu sosai. Didi ta biyo bayansa sai da ta ga ya tafi sannan ta dawo tana murmushi da fatan Allah yasa ya daidaita dasu komai ya wuce.KRB3P089
Nana haleema.

Sai bayan sallar magrib Didi ta kira wayarsa, a lokacin yana tsaye da key Win mota zai je ya Wauko Nayla. Ya Wauki wayar ya saka a kunne ta ce,  Omar ya ake ciki? Ina fatan maganar ta wuce ko?. Ya ja tsaki cikin Sacin rai ya ce,  bata wuce ba, tarwatsa zaman nayi domin abinda ya nema bazai samu ba. Saboda abinda ki ka ce ne ya saka na amince dpo ya shiga maganar, wai an kira shi ana faWa masa abinda za a yi ni yake kallo yake cewa sai na bashi ha™uri zai ha™ura? Ni Omar ni ne zan bashi ha™uri?.

Didi cike da takaici ta ce,  to meye a cikin bada ha™urin? Ba dai in ka bada ha™urin maganar ta wuce ba?.

 Na fi ™arfin na bada ha™uri. Mutum biyu kaWai na taSa bawa ha™uri a duniya, daga ke sai Jidda. Bana sauke kai ™asa in na kalli sama, shima yana so ya kafa tarihi a kaina shiyasa yake so na bashi ha™uri, dan ya san ba Wabi ar Omar bace.

 Yanzu fisabinillahi meye dan ka bashi ha™uri? Kalma uku ce fa kacal Omar, a cikin kalma ukun nan da zaka furta akwai kwanciyar hankalinka, dana matarka, dana Wan cikinta. Rai uku ne a ™ar™arshin kalmar ka yi ha™uri, kenan ka zaSi a rasa rayuka har uku akan kalmar ha™uri?. Yanzu da baka bada ha™urin ba in suka cutar da ita fa?.

Ya yi shiru bai ce komai ba, Didi ta cigaba da yi masa nasiha cikin kalamai masu daWi da kwantar da hankali, ta hana shi magana tana isar da sa™on da take so ta isar, tana sake faWa masa illar ™in bada ha™urin Nayla za a cuta. Da yake ta san Nayla ce rauninsa tunda take faWar haka sai ya sauke ajiyar zuciya ya ce,  FaWuwa ce a gare ni na bada ha™uri.

 Ba faWuwa ba ce, kowa yaji ka bada ha™uri zai tabbatar da cewa Omar Win baya bana yanzu bane, Omar Win yanzu ya san abinda yake yi. Mai hankali da wanda ya san ya kamata shine yake kwantar da rigima. Kasan adadin mutanen da zai haWa kai dasu a cutar da Nayla? Yanzu ba ta kai suke yi ba, Nayla zasu cutar saboda itace rauninka Omar, duk yadda da zasu bi dan cutar da ita zasu bi. Don girman Allah ka bada ha™uri a wuce wajan.

Omar ya sauke numfashi ya ce,  Didi in na bada ha™uri na faWi, na ja baya, kuma naji tsoro. Ban dace da wannan abubuwan ba, zubina ba na masu bada ha™uri bane. Didi taji kamar ta ziro hannu ta wayar ta zabga masa mari. Didi ta ce,  yanzu zaka koma gidan jiya kenan? Zaka butulcewa ni imar da Allah ya yi maka ko?. Ai shikenan Omar Allah ya taimaka, ina jin sai ka ga gawata, kaga gawar Nayla, kaga ta Marmerh duk an kashe mu saboda bashin da kake Wauka sannan zuciyarka zata yi sanyi. Kar ka bada ha™uri, ka je ka yi abinda ka ke so ta faWa tana yanke wayar. Ajjiye wayar yayi ya Wauki abinda zai Wauka ya fita daga gidan.

Bai je Waukar Nayla ba sai ™arfe tara na dare, yana ajjiye motar ya ganta a ™ofar gida ita da Jidda da mijin Jidda, da Jawad da Salma da alama rakiya suka yo musu. Wani takaici ya mamaye masa zuciya, daman ransa a Sace yake ga wani Sacin ran ya tarar. Ganin Jawad yana kallon Omar yana dariya sai ya daure ya fito daga motar ya ™arasa inda suke. Da Wan murmushi a fuskarsa suka gaisa da Jawad, suka gaisa da mijin Jidda. Salma da Jidda suka gaishe shi ya amsa fuskarsa ba sakewa sosai.

Nayla ta bishi da kallo suka haWa ido sai ta ce,  bara na Wauko wayata a cikin gidan. Ko kulata bai yi ba ya Wauke kai. Yana gani sai shagwaSa take yiwa Jawad yana biye mata, harda ri™e mata hannu ita kuma ta yi masa side hug Salma tana tsokanarta. Yana cikin mota yana kallon komai zuciyarsa kamar zata buga saboda haushi. A haka su Jawad suka tafi ita da Jidda da mijin Jidda suka koma ciki.

Ba jimawa Nayla ta fito ita da Jidda ta shiga motar Jidda tana yi mata sallama suka wuce gida.

Yadda fuskarsa take a Waure haka itama ta ta fuskar ta ke, Allah ya sani yana bata haushi sosai. Ace har yanzu ya kasa sakewa da danginta? Har gwara Jawad yana iya yi masa murmushi amma ko Salma fuska ba yabo ba fallasa yake amsa gaisuwarta. Tana ganin yadda mijin Twiny yake, wasa da dariya ake yi dashi kamar Wan gida amma nata miji kamar fuskar shanu.

 Kafin ki shiga gidan Wazu me nace miki?. Juyowa tayi ta kalle shi taga kamar ba shine ya yi maganar ba. Ta muguWa baki ta ce,  kace na zauna a gidan.
 Amma da nazo a ina na same ki?.
 Yaya J ne fa& ..
 Ki amsa min kawai, a ina na same ki?.
 A waje.
 Yayi kyau. Daga nan bai sake cewa komai ba suka cigaba da tafiya itama bata ce komai ba.

Haka suka ™arasa gidan suna share juna, ta wuce Waki tayi wanka ta shirya ta fito zuwa Wakinsa ta shiga. A zaune ta same shi yana waya, ta ™arasa ta zauna a akan gadon tana danna wayarta.

 Abinci fa? Ya tambaya ba tare da ya kalle ta ba. Nayla ta mi™e ta ce,  me zan dafa maka?.
 Dake nake. Sai ta koma ta zauna ta ce,  naci abinci, sai dai na dafa maka. Bai ce mata komai ba ya cigaba da abinda yake yi itama haka. Gajiya tayi ta tashi ta kashe hasken Wakin tayi addu a ta kwanta. Bai jima ba ya tashi ya kwanta shima, duk a zatonsa tayi bacci ya jawota jikinsa yana shafa ™ansan cikinta yana ji wajan yayi tauri sosai. Ya lumshe ido ya yiwa wajan kiss yana jin ™aunar abinda bai zama mutum ba a zuciyarsa.

Nayla tana jinsa tayi shiru kamar tayi bacci, ya yi pecking goshinta yana sake gyara mata kwanciya a jikinsa.

Washe gari da ta tashi har breakfast ya yi, bayan tayi wanka ta zauna a kusa dashi ta ce,  YaMar. Ya kalle ta sannan ta ce,  zan je gidan Daddy. Ya Wauke kai daga kallon ta bai ce komai ba. Nayla haushinsa ya mamaye mata zuciya, ta mi™e ta bar falon. Ya bita da kallo bai motsa ba ya cigaba da abinda yake yi.

Bata jima ba ta fito ta haWa tea ta wuce dashi Waki bata ce masa komai ba. A haka suka yini shida ita kowa yana jin haushin Wan uwansa. Da daddare da ya shigo ta gama dafa noodles tana zaune tana ci. Yana zama ta tashi ta kawo masa ya bita da kallo ba tare da ya karSa ba. Ta ajjiye masa a gabansa cigaba da cin abincinta. Tana gamawa bata ce masa komai ba ta wuce Waki, ya yi murmushi yana shafa kansa.

Sai da ya gama abinda zai yi sannan ya shiga Wakinta, a banWaki yaji motsinta sannan ta bar ™ofar a buWe. A hankali ya ™arasa sai ya tarar tana amai, duk noodles Win da taci ta dawo. A ruWe ya ™arasa ya ri™ota ya ce,  Jidda baki da lafiya? Me ya same ki?. Ya ri™ota suka dawo Wakin ya zaunar da ita akan gado, ya fita ya kawo mata ruwa tasha ya zauna a gefenta tare da ri™e hannunta ya ce,  yanzu har fushin da ki ke yi dani ya kai baki da lafiya baza ki faWa min ba Jidda?.

Nayla ta kalle shi ta ce,  Nifa lafiyata ™alau, wannan aman kuma ina yi wani lokacin.
 Me yake kawo shi?.
 Unborn ta faWa ba tare da ta kalle shi ba.

 Amma ya kamata ki faWa min, bai kamata fushin ki ya shafi rashin lafiyarki ba. Ta kalle shi kafin tayi magana ya ce,  kin dawo da abinda ki ka ci, me zaki ci yanzu?. Ta girgiza kai ta ce,  bana jin yunwa.
 A a, ki faWa min abinda zaki ci.
 Bana jin yunwaaa! Ta ja ™arshen kalmar hawaye yana sakko mata.

Omar ya dafe kai ya ce,  Jidda meye na kukan kuma? Ya kike so nayi miki? Kina so ki haukata ni ne?. Nayla ta goge ido bata ce komai ba. Ya zamo daga kan gadon ya zauna a ™asa kusa da ™afarta yana kallon fuskarta tana ™ifta idanu ya ce,  Jiddaaa!. Ta Wago ta kalle shi ya ri™e hannayenta ya ce,  laifi nayi miki?.

 Kai na yiwa laifi, kaine tun a gidan Twiny ka ke ta hararata kawai dan ka ganni a ™ofar gida. Kuma tun daga Kaduna Yaya J da Salma suka zo yi mana sallama zasu tafi Malaysia, dan na fito na rako su ™ofar gida sai ya zama laifi?.

Omar ya zuba mata ido yana kallon yadda take maganar da fusata da alama bata ji daWin abun ba, ya sauke numfashi ya ce,  Duk abinda nake yi saboda ke nake yi Jidda, duk saboda lafiyarki nake yin hakan.

 Amma ka san Yaya J ma bazai bari wani abun ya same ni ba, in ma sake ™o™arin kashe ni Win ake yi zai tsaya dan ganin ya kare ni kamar yadda zaka kare ni. Har yanzu ka kasa sakewa da ´an gidanmu, kayi ta Waure fuska in ka gansu. Wai a haka ma kana sakarwa Yaya J fuska shiyasa fuskarka ta tsaya a haka. Amma Salma da Jidda kamar baka sansu ba, ka haWe rai in ka gansu kamar waWanda ba jinina ba.

Omar ya yi shiru yana jinta dan yaga alama abinda yake ranta kenan shiyasa zai bari ta gama. Nayla ta ce,  bana jin daWin hakan ko kaWan, ba haka naga ana yi da mijin Twiny ba, shi sakewa ake yi dashi kamar Wan gidanmu haka yake. Kai kam Yaya J kawai ka ke sakarwa fuska, Yaya Ahmad kuwa ko number wayarsa bana tunanin kana da ita. Yanzu in aka nuna kama Jalil da Jalila ™annena baza ka gane su ba, saboda baka sansu ba. Sati biyu Jalila tazo tayi a gidan Twiny, ni da nace mata meyasa bata zo gidan nan ba cewa tayi tsoronka take ji, kuma tsoron gidan nan take ji kar a shigo a kashe ta. Ni bana jin daWin attitude Win nan naka gabaWaya, lokacin da Twiny ta haihu ni mijinta ya kira ya faWawa, yanzu ni in na haihu ko Jidda baza ka gane a fuska ba balle har ka samu number ta ka kira ta. Balle kuma a kai ga kiran su Mama ko Hajja ta faWa tana kuka sosai.KRB3P090
Nana haleema.

Rauni ya mamaye zuciyar Omar musamman maganar ™anwarta da tace tana tsoron zuwa gidan, ya yi shiru yana jin yadda take kuka kana ta ce, "wanda suke Kano sune a kusa dani, amma kai da na Kaduna ka ke Wan sakewa kaWan."

Omar ya yi shiru yana kallon ta zuciyarsa sam babu daWi, ta ja numfashi ta goge idanunta tana kallon gefe Waya. Calmly Omar ya ce, "ki yi ha™uri." Ta kalli idanunsa jin yadda kai tsaye ya bata ha™uri, duk dai bai Wauki bata ha™uri a bakin komai ba, har mamaki take yi in ta Sata mata rai ya gama fushin kai tsaye zai ce mata ki yi ha™uri. Tana mamakin hakan dan bata Wauka zai iya aikata hakan ba, dan Twiny ta faWa mata mijinta duk bala'i baya buWe baki yace tayi ha™uri, sai dai zai yi abubuwan da zata fahimci ha™uri yake bata. Tayi mamakin bada ha™urin nasa cikin sauri haka, dan ta san sai ya gama fushin sannan yake bada ha™uri. Omar ya girgiza kai ya ce, "nasan a zuciyarki kina regretting aurena, kina ji ina ma baki aure ni ba, da baki aure ni ba da ™anwarki bata ce tana tsoron gidan nan ba. Ki yi ha™uri Jidda!."

Zata yi magana ya katse ta ya ce, "yadda na baki dama ki ka faWi abinda yake ranki ki jira na gama." Ta sunkuyar da kai ™asa ya ce, "Mijin Yayarki da ni ko a sunayen mu muna da banbanci, halinsa daban da halina Jidda. Bani da saurin sabo kin fi kowa sani, ke kan ki sai a hankali muka saba har muka zo yanzu. Bazan iya canja kaina ba Jidda, bazan iya canja yadda Allah ya yi ni ba, amma ni nasan ina ™o™arin ganin na sake da kowa naki."

Ya sauke numfashi ya ce, "Zan koma yadda ki ke so Jidda, zan yi ™o™arin ganin na koma zaSinki saboda kar damuwar halayena su yi miki yawa. Tunda na sauke komai naje aka zauna dani Omar aka yi sulhu saboda ke da lafiyarki babu abinda bazan iya yi domin ki ba. In Allah ya amince babu abinda zai sake faruwa da zai saka ki yi danasanin aurena Jidda, zan yi ™o™ari na koma yadda ki ke bu™ata."

Nayla a sanyaye ta ce, "nifa bance maka ina danasanin aurenka ba, kawai yadda baka sakewa da familyna ne bana jin daWi."
"Yanzu ki ka ce ™anwarki tace baza ta zo gidan nan ta kwana ba saboda kar a cutar da ita, dole zaki ji haushin wannan maganar a zuciyarki, har zaki Warsa da ace bani kike aure ba da hakan bai faru ba."

"Ita tsoron haWe fuskarka take ji ba wani abun ba." Ya Wan yi murmushi calmly ya ce, "kin faWi abinda tace Win ba tare da kin san kin faWa ba. Wata™ila da bani kike aure ba da bata ce haka ba, kalmar tayi miki zafi shiyasa har kika furta min baki san kin faWa ba."

Nayla ta ce, "nidai ban yi danasanin aure ka ba, gwara ma ka daina faWa. Kawai yadda ka ke da familyna ne bana so, kuma na san haka halinka yake, bana jin daWi ne kawai." Yayi shiru bai ce komai ba, jin shirun sai ta kalle shi suka haWa ido ya Wan girgiza kai ya ce, "shiyasa nace ki yi ha™uri Jidda."

"Ni dai ban ce ina danasani ba."
"Nima ban ce kin ce ba, amma kalamanki da fuskarki sun nuna hakan. Kuma baki yi laifi ba, kin cancanci ki yi danasanin ne jidda. Meye abin alfahari a auren wanda aka yi ™o™arin kashe ki har sau biyu?." Nayla ta rufe masa baki da hannunta ta ce, "nidai ban ce ina danasani ba, ka daina faWar haka bana so." Ya Wan yi murmushi bai ce komai ba.

Ya sake kallonta yana cire hannunta daga bakinsa ya ce, "zanyi ™o™arin

Please Login or Register in order to submit comment