Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dare ta dawo gida.

Kamar ko yaushe ranar Alhamis Nayla ta dawo daga wajan aiki tana zaune tana kallo a tv, Didi tayi mata waya take sanar da ita an yi rasuwa a gidan Kawunsu inda suka taSa zuwa. Nayla ta ce, "To na taho yanzu ne Didi?." Didi ta ce, "sai gobe za a yi jana'iza, ki bari sai goben, sai dai kuma zaki je aiki."
"Babu komai zan samu na zo, ai Friday ce. Allah ya jian rai." Ta amsa da amin ta kashe wayar.

Washe gari kuwa da wuri ta shirya kamar zata tafi aiki ta wuce gidan rasuwar dan ta gane gidan. Tun daga bakin layin zaka san anyi rasuwa, dan manyan motoci ne sosai na mutane da suka zo jana'iza. Ta ajjiye motarta shiga gidan ta kira Didi ta sanar da ita inda take aka rakata suka zauna tare.

arfe tara aka yi jana'iza, Didi ta rie hannun Nayla tana kai ta wajan wanda mutuwarta shafa tana yi musu ta'aziya. Har su Kawu sai da ta yiwa, lokacin goma na safe ta yi sannan suka yi sallama da Didi ta wuce wajan aiki a lokacin.

Bata jima sosai ba ta koma gida ta sanar da su Hajja rasuwar dan su yiwa Didi gaisuwa. Tana zaune da yamma sai ga Didi ta shigo, kana ganin yadda ta shigo ka san ranta a Sace yake sosai, ga cikinta ya girma sosai duk ta saka babban hijjabi amma ana gani, fuskarta duk ta canja tayi ja sosai. Didi ta kalli Nayla da take yi mata sannu da zuwa ta ce, "Nayla Ina Omar?."

A lokacin ya shigo falon ya kalle ta ya ce, "gani." Didi ta juya ta kalle shi ta ce, "Meyasa kai wani lokacin baka aiki da tunani ne Omar? Mutuwa fa aka ce, matar Kawu babba ce ta rasu amma ka kasa zuwa ka yi musu gaisuwa. Tun Daren jiya na faWa maka, maimakon ka je ko ladan jana'iza ka samu sai baka je ba saboda wani banzan tunanin ka. Ai mutuwa ta fi gaban wasa, tunda aka ce ta mutu ko meye a zuciyarka sai ka kawar dashi ka yi mata addu'a haka musulmi na gari yake. Kai kaWai aka yiwa laifi a duniya ne ko kai kaWai ne me zuciya!?."

Kallon ta yake yi jin yadda take yi masa faWa shiyasa ya shareta, in ya tanka ofar da yake tsaye a jiki ma ta tanka. Didi ta ce, "Yanzu ka wuce mu je ka yi musu gaisuwa, in har na isa da kai ka wuce mu je yanzu ba anjima ba."

TaSe baki ya yi ya ce, "bazan je ba, da nawa mahaifin ya bar duniya itace ta fara kallona ta ce an rage iri a duniya, dan yanzu ta mutu kuma sai ace na je gaisuwar mutuwarta? Kema kin san wasa ki ke yi."
"Ta riga ta mutu, ko me tayi maka ya kamata ace ka manta dashi ka yafe mata. Kuma ba dan ita zaka je gaisuwar ba, saboda Kawu zaka je da kuma aanta."

Omar ya ce, "Didi babu inda zan je gwara ma ki daina wahala da bakin ki." Didi ta fusata sosai ta ce, "Sai ka je Omar, in dai na isa na faWa maka sai ka je!."
"Bazan je ba, akansu ki ke Waga min murya haka? Su Win su waye a rayuwata?."
"Iyayenka, iyayenka ne ko kana so ko baka so, danginka ne wanda baka da kamar su."

"Iyayen wasu dai amma ban da ni, ba iyayena ba ne kar ma ki sake danganta ni da su!" Ya faWa cikin muryarsa mai amo wacce ta sa Nayla ta toshe kunnenta.

Didi ta ce, "ko kana so ko baka so iyayenka ne, gwara ma ka hutar da kanka ka so. Wannan banzar zuciyar babu inda zata kai sai dana sani." Bai tanka mata ba ya kawar da kai ta ce, "Ko baka so dole ka je ka yi musu gaisuwa, in dai na isa da kai." Ya girgiza kai ya ce, "kin gama yi min dole Didi, kin ga ina yin abinda ki ka ce shiyasa ki ke yin abinda ki ga dama. To ta are!" ya faWa a kausashe yana kawar da kai gefe.

Didi ta matso kusa dashi ta ce, "wai wacce irin zuciya ce da kai?."
"Wacce Allah ya yi min."
"arya ka ke, kai ka sakawa kan ka wannan bain hali ba Allah ba. Kuma zan gani in ina da darajar da zance ka yi abu ka yi, in kuma bani dashi zan gai." Omar a fusace ya ce, "Kina dashi, amma a wannan lokacin bazan yi ba!."

"Iyayenka ne dai ko ka i ko ka so, sune danginka, komai na rayuwarka sai ka neme su, su ne suka karSar maka aure!. Ko gobe zaka sake yin wani abun wajen su dai zaka je, baka da inda ya fi su, kaga kenan dole ka ce da mijin iya baba."

Nayla bata taSa ganin wannan faWan na su ba, ta saba ta ga suna hira da nishaWi da aunar juna, ganin su a haka gabaWaya sai ta damu saboda yanayin da Didin take ciki. A sanyaye ta ce, "Didi don Allah....."
"Ke!!" Ya faWa cikin tsananin tsawa yana kallon ta da idanunsa da suke waje suka kuma koma jajaye. Baya Nayla tayi a firgice, iya tsawar da ya yi mata ma abin tsoro ne balle kuma idanunsa da suke a waje.

Ya nuna ta da yatsa ya ce, "kar ki sake cewa komai a wajen nan, duk ba ke kika jawo ba? Ba ke kika jawo min ake yi min gorin su ne suka karSi aurena ba!?" Ya faWa yana kallon ta kamar ya tsinka mata mari. Didi ta kalle shi ganin ya koma kan Nayla ta ce, "Dani zaka yi ai ba ita ba, ni ce nayi maka laifin ba itace tayi maka ba Omar!."

"Auren da ki ke batun su suka karSar min ni nace Ina so? Ko na ce ina son auren ne? Ba haWa baki ki ka yi dasu aka munafurce ni aka yi min aure ba tare da na sani ba!?."

Didi ta ce, "ko a nan ya kamata ka fahimci matsayin da suke dashi a rayuwarka, tunda gashi kana zaune da auren da su ne suka karSe shi, hatta sadakin auren ba kai ne ka biya ba su ne suka bayar saboda su ne iyayenka!" Ta faWa ido a waje itama tana kallon sa.

"Saboda ke, saboda kin yi min dole ya saka nake zaune da auren nan kema kin sani, ban ce ina so ba kuma bazan taSa so ba. Har abada bazan taSa son abinda ya zo daga gare su ba cikin harda auren nan!. Ke ka yi min dole na karSa, ke kika yi min dole nake zaune a gidan nan, ke kika yi min dole nake rayuwa a cikin gidan, ke kin san ba dan ke ba babu wanda ya isa ya saka na kalli maganar auren nan ma balle na kawo shi cikin rayuwata. Ki goge tunanin sun zama iyayena dan kawai sun karSin auren da ban ce ina so ba, kuma har yanzu ban so!" Ya faWa cikin fusata yana kallon ta.

Didi bata san ta tsinke shi da mari ba sai da ta ga yadda ya sake buWe ido yana kallonta idanunsa sun zama jajaye sosai. Irin fusata da fushin da yake kan fuskarsa ba dan Didi bace zai iya shae ko waye a kusa dashi. acin rai ne yake tasowa daga asan zuciyarsa yana mamaye ilahirin jikinsa, fusata yake ji tana shiga jininsa tana zaga ko wanne lungu da sao na jikinsa. Hannunsa rawa yake yi, hannunsa aiayi yake yi, ba dan Didi ba ce da yanzu ba wannan zancen ake yi ba.

Didi itama fushin ne akan fuskarta wanda bata taSa yi ba a rayuwarta, ta nuna shi da yatsa cikin rashin sanin abinda zata ce sai ta ce, "Kana bani mamaki."

Shi kam ya kasa magana kallon ta kawai yake yi, wai Didi ce ta mare shi, mari akan waWanda baya so da kuma auren da aka yi masa ba tare da yana so ba. Yadda yake huci ya kasa magana kana kallonsa ka san ya gama zuwa arshen Sacin rai, ji yake kamar ya zaro zuciyarsa ya cillar saboda Sacin ran da yake ji. Idanunsa har ruwan Sacin rai suka tara, ya kalle ta yana nuna kansa da yatsa ya ce. "Ni ki ka mara?." Didi tayi masa banza bata kula shi ba, ya girgiza kai sai kuma ya shafa fuskarsa, ya cize baki ya naushi hannunsa guda Waya. Jikinsa har rawa yake yi, cikin tsananin Sacin rai ya ce, "yau na tabbatar da kin fifita su a kaina! Su ki ke kallo a matsayin an uwanki bani ba!."


Didi cikin wani irin yanayi ta ce, "Ban fifita su akan ka ba, abinda ka ke yi ne bana so, kuma ina so ka sani, su ne iyayenka ne ko baka so!."

"Saboda auren da aka yi min ne ya saka ki ke cewa iyayena ne? Kema kin san in da ace da sani na babu wanda ya isa ya aikata hakan ko!?" Yadda muryarsa take fita ya saka ta kulle ido dan ta san ransa ya gama Saci, ta san zai iya furta ko wacce kalma akan auren, ta san zata iya ji ya furta kalmar saki akan Nayla ita kuma ba haka take so ba.

Baya tayi kamar zata faWi, Nayla da ta gama suman tsaye a wajan ta farfaWo ta rie Didi ta ce, "Ki zauna Didi." Kamar ta farkar dashi daga mafarki ya kalle ta cikin tsananin fusata da Sacin rai, hannunsa yana rawa ya ce, "Ke bana son aurenki, ban taSa ji a zuciyata ina son zama dake ba, Ina zaune dake ne saboda Didi, duk abinda nake yi a gidan nan saboda ita ne. To naga lokaci ya yi da komai zai are tunda har abin ya kai ga haka......" Ya dafe kai tare da runtse ido, ya buWe ido ya sake kallon Nayla ya ce,

"A kan aurenki ta Waga hannu ta mare ni, tun ina arami muke tare da ita bata taSa dukana ba koda wasa sai yau, yau Win ma a kanki da waWancan munafukan. To ina so ki san bana sonki kamar yadda bana son aurenki, kina zaune dani ne saboda alfarma, Ina kwana a gidan nan saboda dolen da aka yi min a kan ki. Tunda abin nata ya zama haka yanzu komai zai are, bazan......." Didi ta mie tsaye da hanzari ta katse shi ta ce, "Omar ka dakata!."

"Bazan dakata ba! Bazan dakata ba!. Ni kika Wauki hannu kika mara, tun ina arami baki taSa aikata hakan ba sai yau, tun lokacin da nake ji da tantiranci, nake zubar da jinin mutane, nake Wauko miki magana, ki ke yawo a kan titi kina nemana, ki ke zuwa police station belina, ki ke zuwa prison kai min ziyara, baki taSa Waga hannu kin mare ni ba sai yanzu. Akan su da kuma kan wannan aurenta kika Waga hannunki da kike rarrashina dashi ki ka mare ni ko Didi?!" Ya faWa tana kallon ta idanunsa har ruwa suka tara saboda Sacin rai, jikinsa rawa yake yi haka bakinsa. Jijiyoyin kansa sun tashi, duk wata kafa ta gashi a jikinsa ta buWe, fuskarsa tayi ja matua.

Didi ta runtse ido, saboda tashin hankali har Wan cikinta sai da ya motsa saboda bala'in Omar. Ta runtse ido ta ce, "Babu ruwan auren nan a cikin maganar nan, na sako shi a ciki ne saboda ka san mahaimmacin su a gare ka."

"To bana son auren ai, na faWa miki tun farko ai ko? Tun kafin azo nan na ce miki bana so kuma bazan karSa ba. Amma me ki ka ce min? Dole ki ka yi min ba dan ina so ba kika jawo ni har nake zama a cikin gidan nan. Didi na gaji da dolen da ki ke yi min, bazan sake aikata abinda bana so ba saboda ke!" Ya faWa yana nuna Didi da yatsa cikin fitar hayyaci.

Ya nuna Nayla hannu yana rawa amma Didi yake kallo ya ce, "Kin tuna? Kin yi min faWa a kanta, kin ce min ina shirme a kanta, kin kore ni daga falon ki akanta, kin yi min dole na karSi aurenta, kin yi min dole na zauna da ita, kin yi min dole ina saurarenta, kin yi min dole ina shiga lamarinta, yanzu kin mare ni ta dalilinta. Me zai saka ni na so ta har na so aurenta? Me zai saka ni na zauna da aurenta!?. Cewa ki ka yi in ban karSi aurenta ba babu ni babu ke shima duk a kanta. Didi ko aljanna zan samu ta hanyar zaman aure da ita na yarda ta wuce ni, ai rahamar Allah tana da yawa, hanyar rabo tana da yawa zan samu a wani kiran rabon ba sai ta dalilin aurenta ba!?."

Didi ta dafe kai ta arasa zata rie shi ta ce ta ce, "Omar ka saurare ni...." Ya fizge jikinsa ya ce, "bazan saurareki ba, na gama saurarenki Didi, na gama sauraren maganar ki akan abinda bana so har abada. Wallahil azim bazan taSa son abinda ya fito daga hannunsu ba ciki harda auren nan da ita kanta!. Komai ya zo arshe, komai ya lalace Didi, komai ya are!" Ya faWa can asan maogwaro yana kallonta dan jijiyar kansa har harbawa take yi. Didi dafe kai tayi ta zauna ta fara rawar jiki saboda yadda kanta yake sarawa.

Nayla kuwa ta gama amewa a wajan tun daga kan maganar da ya kalle ta ya faWa, jikinta ya gama yin sanyi zuciyarta ta gama karyewa a lokacin. Hawaye ya gama wanke mata fuska, jikinta ya gama mutuwa gabaWaya. Shiyasa ta kasa koda motsi, dayar ta iya ta rie Didi tana ganin yadda jikinta yake rawa sosai.

Shi kuma dakatawa ya yi da maganar ganin yanayin Didi ya canja, ransa ya riga ya kai arshe wajan Saci, huci kawai yake yi kamar kumurci. Kallon ta yake yi kawai amma ya kasa ce mata komai saboda wutar Sacin rai da unar zuciyar da take ruruwa a zuciyarsa. Wai Didinsa ce ta mare shi, mari akan kuncinsa kuma saboda waWanda ya fi tsana a duniya. in ya tuna hakan sai sai ya ji kamar ya kurma ihu. Ji yake kamar ya bankawa gidan wuta, da shi da Didin da Nayla duk su mutu a huta.

"Didi!" Nayla ta faWa a sanyaye tana daga tsaye. Didi bata motsa ba sai rawar jiki da take yi ta ce, "Didi mu je asibiti, baki da lafiya" ta faWa hawaye na sake zubo mata. Didi ta ce, "Nayla rie ni mu fita." Nayla ta dua ta rieta, ta saka hijjabinta da yake gefe ta rie hannunta suka fita daga falon har lokacin yana tsaye.

Nayla ta buWe gaban mota Didi ta shiga, ita kuma ta arasa gate Win ta buWe ofa tana duba su Bashir, ganin babu kowa a cikin su wanda zai buWe mata sai ta buWe da kanta ta shiga motarta fita ta bar shi a buWe.

Didi ta ce, "Nayla mu je gidan mu kawai."
"Didi baki da lafiya."
"Ciwon kai ne kawai, mu je gidan mu Nayla, akwai key Win gidan a hannuna." Da yake babu nisa ba jimawa suka araso. Nayla ta ajjiye motar ta rie Didi har gidan ta buWe mata ta shiga. Gidan yana nan yadda yake ko ura babu sosai dan yana zama a ciki sosai.

A kan kujera Nayla ta zaunar da ita, ta Wauki ruwa ta bata tasha ta ce, "ki sha ki kwanta ki huta Didi." Didi ta yi ajiyar zuciya tana kallon Nayla da fuskarta ta tayi ja tana tuna abinda ya faru.

Didi ta sunkuyar da kai bata ce komai ba tana shan ruwan. Ajiyar zuciya ta yi bayan ta sha ruwan tana kallon Nayla, ta jingina da kujera bata san me zata ce mata ba. Nayla ta mie ta ce, "Sannu Didi, babu abinda ki ke so?." Kai ta girgiza alamun babu Nayla ta ce, "Ina zuwa" ta faWa tana fita daga gidan.

Motar ta koma ta nufi gidan kai tsaye, ta tsayar da motar a ofar gidan ta tarar da an kulle gate Win ta buWe ofar ta shiga. Yana nan inda yake a zaune ya dafe kai yana wani irin huci har sautin sa tana ji. Wuce shi tayi bata ce komai ba ta shiga Wakinta ta jawo trolly bag tana zuba abinda ta san zata iya zubawa wanda zai yi mata amfani, ta Wauki laptop Winta da tap Winta, ta jawo jakar tan rie da sauran kayan a hannu ta fito.

arasowa ta yi inda yake, ta kalle shi ta haWWiye yawu Sacin rai ta ce, "Na gode da karSar aurena da ka yi saboda Didi, yanzu ina so ka rabu da aurena saboda nima na ce bana so, ina so ka rabu dani saboda bana so ba dan wani ya yi maka dole ba, bana son zaman auren kamar yadda baka so. Na gode da zaman da muka yi da kai matsayin mata da miji. Zaka iya karSar number wayata a wajan Didi ka tura min saki ba sai ka wahalar da kanka ka rubuta ba! Sai wata rana" ta faWa tana jan jakarta fita daga falon, ta saka jakar a bayan mota ta ajjiye komai na hannunta ta shiga gaban motar taja motar ta fita daga unguwar gabaWaya.KRB3P026
Arewabooks@nanahaleema11.

Usman Umar shine sunan mahaifin su Omar, asalin kakanin su an garin Gombe ne amma iyayen su da shi kansa a Kano aka haife su. Yana da an uwa guda huWu har shi biyar kuma dukkan su maza ne dan mahaifiyarsu bata taSa haihuwar mace ba.

Matarsa mai suna Saudat ita kuma asalin su buzaye ne haihuwar asar Chad, iyayen su dukkan su a can aka haife su, kana ganin kammanin su ka san ba an nigeria bane saboda kyau da gashi. Kasancewar mahafiyar su ta yi aure a nigeria hakan ya saka duk aka haife su a Kano suke kuma zaune a Kano. Su huWu ne mata, sai yayan su namiji guda Waya wanda ya kasance shine babba a cikin su.

Tun farkon haWuwar Usman da Saudat Allah ya ulla alaar auna da soyayya a tsakanin su cikin lokaci kaWan, har ta kai ga ta gabatar dashi a matsayin wanda take so kuma zata aura. Dangin Saudat kowa ya nuna sam baya son Usman, dan kallo Waya zaka yi masa ka fassara shi a mutum mara kirki, sannan a kammani da zubin sa ya nuna hakan.

Saudat ta nuna ita dai shi take so kuma shi zata aura, an uwanta da kowa nata ya nuna baya son auren amma ita ta nuna shi take so kuma shi zata aura. Kasancewar inda mahaifiyarta ta fito ba daga nigeria bane da ta ga ta dage akan shi take so bata takura ba ta saki maganar. Dagewar da tayi a kai ya saka dole aka daura musu aure ba dan wani nata yana son wannan aure ba sai dan babu yaddda za su yi da ita ne.

A gidan gado Saudat ta tare, gida ne da dukka su uku suke aure a ciki, harda space Win sauran biyun da ba su yi aure ba. Gida ne mai Wakuna da yawa amma banWaki biyu ne kacal a gidan kuma a tsakar gida yake. Kasancewar iyayen Saudat suna da rufin asiri sam basu ji daWin wannan gida da arsu ta tare a ciki ba.

Bayan auren Saudat da Usman sai asalin halinsa ya fara bayyana, mutum ne mai shaye-shaye, kaf danginsa haushinsa suke ji dan lokacin da aka bashi Saudat har mamaki abin ya basu saboda sun san ba a kintse yake ba. Saudat ta fara shiga damuwa matua, dan baya tashi dawowa sai dare kuma a daren dayar in bai mata duka ba, garin dukan ta da yake yi ta yi Sarin cikin ta ne farko.

Bayan wani lokacin iyayen Saudat suka rasu nasa iyayen su ma suka rasu ya rage basu da kowa sai an uwa. A wannan lokacin Saudat ta haifi Aisha wacce Wakyar aka iya rainon cikin ta saboda wahala, duk da bata rasa ci da sha a gidan ba amma ta rasa farin ciki mai yawa. Bayan haihuwar Aisha kamar ya nutsu ya daina komai, amma sai aikin yiwa yaran mutane ba'a da jafa'i, ko wanne yaro Wan iska yake kiransa kuma mara tarbiyya.

Matarsa Saudat sam bata jin daWin wannan kalaman na sa, amma ya riga da ya saba ko magana zai yi sai ya haWa da Wan iska ko tsinanne. Ita kuma tana gujewa Aisha da ta haifa, kar bakin da yake yiwa yaran wasu ya faWa kanta.

A cikin wannan yanayi Aisha ta taso kasancewar yana matuar son Aisha babu abinda baya yi mata, komai yana siya mata na yara da duk abinda zata buata. A haka ta fara tasawa cikin kula da tarbiyyar mahaifiya. Sai dai kyara da hantarar mutanen gidan, dan zuwa lokacin sauran mazan duk sun yi aure. Matan gidan sai suka haWewa Saudat kai, saboda ta fi su kyau da jiki mai kyau sai suke bain ciki da haka. Babu damar Aisha ta fito tsakar gida koda rarrafe ne sai tsawa da duka.

A haka aka cigaba da rayuwa, Aisha da shekara huWu a duniya Allah ya kawo cikin Omar a lokacin da ba a yi tunanin zuwan sa ba. Da yake Saudat tana fama da rashin lafiya mai tsanani wacce take tashi a kai a kai ba a yi tunanin zata iya sake haihuwa a wannan yanayi da take ciki ba.

Bayan ta haihu aka sakawa yaro suna Omar, sunan mahaifin Usman kenan. Da kanta ta kaiwa an uwata shi amma babu wanda ya iya Waukarsa, har gwara anwar ta Saroot a lokacin bata yi aure ba yarinya ce, ta nuna ya burge ta saboda ya yi kama da an Chad gabaWaya.

GabaWaya ba sa son yaranta, Saroot Win ce kawai ke iya yiwa Aisha wasa har ta Wauki Omar. Haka take zaune cikin yanayi na damuqa kala-kala, ga damuwar miji, ga damuwar zaman gidan yawa, ga damuwar basa sonta, ga damuwa an uwanta.

Tana matuar son Omar, tana aunar Omar saboda yana kama da ita, aunar da take masa ya saka take kiransa da Ashiq ko ta ce Habibi saboda son da take yi masa. A haka ta cigaba da rayuwa yau da lafiya gobe babu. Tun bayan ta yaye Omar ciwo ya matsa mata, yau lafiya gobe babu lafiya haka ta dinga rayuwa kamar baza ta tayi rai ba.

A haka har Omar ya kai shekara biyar zuwa lokacin Aisha tana primary school dan ta girma tayi tsaho sosai. Omar yana da shekara shida a duniya mahaifiyarsu ta bar duniya, an uwanta sun ji mutuwarta sosai, sun kuma sake tsanar mahaifinsu Aisha saboda a ganin su shine silar raba su da ar uwarsu. Kafin rasuwarta ta barwa Aisha amanar aninta, duk da yarinya ce amma maganar ta ratsa ta sosai tana ta kuka tana rie da hannun mahaifiyarta.

Kaf gidan babu mai kula da lamarin Omar da Aisha sai shi mahaifin na su, babu wanda yake damuwa da maraicin su kowa sabgarsa yake yi dan zuwa lokacin mutum biyu sun tashi gidan ya zama saura mutum uku. Hakan ya saka Aisha take rayuwa cikin kaWaici ba uwa kuma babu dangin da zasu ja ta a jiki su nuna mata auna da soyayya. Ita kaWai ke nunawa ananinta soyayya, gashi da rigima ita kaWai take iya rarrashinsa tana kuka yana kuka. Wani lokacin baya daina kuka har sai mahaifinsu ya dawo.

Zaman gidan gabaWaya baya yi musu daWi, ga Wabi'ar mahaifinsu har lokacin tana nan bai daina ba hakan ya saka suka zama marayu na asali wanda basu da wani gata sai na Allah. A haka suke cigaba da rayuwa, Aisha tun tana arama ta iya dafa abinci saboda babu mai damuwa da sun ci ko ba su ci ba, dole ita zata yi ko dan Omar.

A haka suka cigaba da rayuwa har Omar ya shiga primary school da kuma islamiyya. A cikin wannan yanayi ciwo ya kwantar da Baba saboda shan tabar da yake ta taSa masa hunhu, daga nan bai sake samun lafiya ba

Please Login or Register in order to submit comment