Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Win ma haka yake komai yana mahallinsa hatta towel da bathrobe suna ajjiye a inda aka ajjiye su.

Bayan ta gama aikin Didi ta dinga tsokanarta ita kuma kunya take ji. Da yamma ta shirya cikin abaya ba™a wacce ta haskata matu™a ta fito falo ta kalli Didi ta ce, "Didi bara na je wannan store Win na baya, akwai abinda zan siyo zan je dashi aiki gobe."

Didi ta ce, "ma sha Allah Nayla, wannan kyau haka? Wanda bai sanki ba sai ya sauka bakya jin hausa ai." Dariya tayi sosai ta ce, "kai Didi, kamar wata ke."
"Amma dai kin fadWawa mijin na ki zaki fita ko?." Nayla ta ce, "ya bani damar zuwa ko ina ai, tunda ya ce naje duk inda nake so kar na sake tambayarsa." Didi ta ce, "haka ne. Sai kin dawo."
"Yanzu zan dawo Didi, da ™afa ma zan je bazan hau mota ba. Ina so ma na bada motar car wash zan kira Bashir ya kai ta" ta faWa tana fita daga falon.

Wajan mintina talatin da fitar sai gashi ya shigo ko sallama bai yi ba. Didi ta Wauka Nayla ce sai da ta juyo ta ganshi ta ce, "A'a sai yanzu?." Ya kalle ta kamar zai yi magana sai ya yi shiru amma bai daina kallonta ba. Didi da mamaki ta ce, "meye na kallon?."

Girgiza kai ya yi ya Wauke idonsa daga kanta, ya sake juyowa ya ya kalli Didi ya ce, "ki faWawa wannan yarinyar kar ta sake fita koda ™ofar gidan nan ne." Didi da mamaki ta ce, "wacce yarinya kenan?." Wani irin kallo ya yiwa Didi na kin san wacce make nufi ai, sai ta ce, "To baka faWi suna ba ta ya zan gane ta ne?." Ya ce, "koma dai wacece, ki sanar da ita kar na sake ganin ta fita."

Didi ta ce, "Wai Nayla ka ke nufi? To akan me zaka hana ta fita?." A lokacin Nayla ta buWe ™ofar ta shigo tana cewa, "Didi har na dawo, shiyasa na tafi key Win gate saboda kar na tashe ki buWe gate."

Kallon ta ya yi ya ce, "ke! Kar na sake ganin ko da wasa kin fita daga gidan nan." Nayla ta bishi da kallon mamaki kafin tayi magana Didi ta ce, "ba kai ka ce ta dinga zuwa duk inda zata je ba?."
"Ai ban ce ta dinga yawo a kan titi ba!."
"To in bata yi yawo a kan titi ba a kan me zata yi yawo? Wai me take damunka ne Omar don Allah?. Kai ka bata damar fita kace ta fita duk lokacin da take so, dan ta fita sai ya zama fitina kenan?."

Nayla a sanyaye ta ce, "kai ka ce na je ko ina babu ruwan ka." Wara idanu ya yi akanta kamar tayi masa allura ya ce, "yi min shiru a wajan nan!." Didi ta ce, "ba gaskiya ta faWa ba? Ba haka ka ce Win ba?."

Omar a fusace ya ce, "To yanzu na canja, na canja yanzu!. Kuma dole abi abinda na ce in ba haka ba baza a ga daidai ba wallahi!. Kar na sake ganin ta fita" ya juyo ya kalle ta ya ce, "kar na sake gani kin fita, na soke maganar da nayi a baya, duk inda zaki je ki tabbatar kin sanar dani, in ba haka ba ranki in ya kai guda dubu Waya bayan Waya sai na Sata su wallahi." Didi ta ce, "Ikon Allah, me ya kawo wannan canjin kuma?." ˜aramin tsaki ya yi ya ce, "oho kuma" Ya kalli Nayla da idanunsa bai ce komai ba kawai ya fita.

Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta ce, "ni dai bana taSa yi masa daidai a rayuwa." Didi ta ce, "me ya faru a wajan ne?."
"Babu fa Didi, kawai yana so ya dinga yi min faWa ne shine kawai."

BuWe ™ofar aka sake yi duk zaton su shine ya dawo sai suka ga Tk da leda a hannunsa, ya gaishe su ya ce, "gashi in ji Tiger." Didi ta kalle shi ta ce, "me ya Satawa Damisar na ku rai haka? Ya shigo yana ta bala'i shi kaWai." Tk yayi ´ar dariya ya ce, "Babbar Yaya ai wani ne yanzu ya riga Antynmu ™arasowa gidan nan, ya zo ya samu Damisa a tsaye yake faWa masa shi dai yana sonta. Ana haka sai gata tana tahowa, shine ran maza ya Saci. In kinga faWan da yake yi yanzu da ya fita sai ya baki tsoro" ya ™arashe faWa yana dariya.

Didi ta murmusa ta ce, "fushi yake yi mai hujja." Tk dariya ya yi ya fita bai sake magana ba. Ita dai Nayla tana tsaye har lokacin bata zauna ba, Didi ta jawo hannunta ta zauna ta ce, "Ke ashe kasuwa ki ka yi shiyasa ran mijin naki ya Saci har ya soke fitar ki ko na."
Nayla a sanyaye ta ce, "wallahi Didi ban san shi ba." Didi ta ce, "haba meye na wallahi Nayla?. Kawai ya ganki yaji kin yi masa bai Wauka kina da aure ba shine kawai."

Nayla ta ce, "kuma Didi ai bana saka kaya half niked ko?." Didi ta ce, "bakya sakawa Nayla, kina shigar mutunci irin ta masu mutunci."
"Da na sani ma ban fita ba, abinda na je nema ma ban samu ba."

Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, Didi ta ce, "na ce miki Omar kishin ki yake yi kin ce ba haka ba, yanzu meye wannan in ba kishi ba?." Nayla ta Wago ta taSe baki ta ce, "yadda baya sona baya so wani ma ya so ni, shine kawai dalilinsa." Didi ta yi murmushi ta ce, "na gaji da musu dake, mu je a hakan." Nayla ta ce, "Amma Didi ya ce kar na sake fita, kuma zan je aiki gobe."
"Kar ki damu, ki jira ya shigo zuwa dare sai ki sanar dashi, yanzu a dokin fushin ya ke." Nayla ta girgiza kai suka cigaba da hira da Didi bata bari wani zancen kishi ya yi tasiri a ranta ba.

Yau ma kamar jiya Didi ta yiwa Nayla dole na zuwa Wakin Omar, babu yadda bata yi ba amma Didi ta ce sam sai ta tafi, kamar zata yi kuka saboda ciwon da kanta yake yi mata, amma Didi ta ce ta sha magani in ta je can tayi bacci kan zai daina ciwo. Ita tsoro ma take ji kar ta je ya yi mata wani abun tunda ransa a Sace yake kamar jiya.

A hankali ta tura ™ofar ta shiga da sallama. Yana daga zaune a gefen gadon cikin shiga irin ta jiya sai dai yau farar singlet ce a jikinsa. Ita tsoron kallonsa haka take yi, jikinsa kwarjini yake mata bata iya tsayawa ta kalle shi shiyasa kanta yake a sunkuye.

Tunda ya amsa a ciki bai ce komai ba ita kuma bata ™araso ba, Wakyar dai ta iya daurewa ta motsa amma ta kasa ™arasawa wajan gadon saboda yau yana zaune a kai ba kamar jiya ba da yake kan stool ba, Ita kuma ta sha maganin ciwon kai bacci take so tayi, ciwon kan ya dame ta matu™a.

Shi kam yana kallonta bai ce komai ba, tana shigowa abinda ya fara zuwa ransa wanda ya ce yana sonta. Sai ya ji wani irin abu ya daki zuciyarsa, idanunsa har ruwa suka tara saboda yadda ya ji bugun bazatar da zuciyarsa ta yi. Yana mamaki kansa yana so ya san dalilin da ya saka ya damu har haka, tun a jiya yake so ya gano dalilin me yasa ya damu da an yi posting ™afarta ya rasa, ga yau ma ta faru ya rasa gane abinda yake ji.

Nayla ™arfin hali tayi ta ™arasa gefen gadon ta zauna a gefen da ta kwanta jiya. Sai ya zama tana daya Sangarne shima yana Waya Sangaren ko wanne su a zaune yake. A hankali Nayla ta zame ta kwanta idanunta ma kawo hawaye saboda ciwon kan ya dame ta, ga hasken Wakin ya yi mata yawa. Ta juya masa baya hakan ya saka ya juyo ya kalleta ya ganta sanye da hijjabi kamar dai jiya.

Ya jima a zaune ita kuma ta kasa baccin saboda ciwo da kuma hasken Wakin. Tashi zaune tayi, ciwon kai ya saka ta zare hijajbin ta ajjiye ta dafe kai da duka hananyen ta biyu tana hawaye. Kallon ta ya yi kamar zai yi magana sai ya fasa, sai ya ga ta mi™e ta kashe hasken ta dawo ta kwanta a takure.

Yana nan dai bai motsa ba babu kuma abinda yake yi yana zaune ne kawai. Sautin kukan ta yake ji kaWan-kaWan tana kiran wayyo kanta. Kamar ya share ta sai ya ga ta sake mi™ewa zaune ta dafe kai.

"Lafiya?" Ya furta yana kallon ta. Nayla bata Wauka zai yi magana ba, amma jin maganarsa sai ta ji daWi a ranta cikin muryar kuka ta ce, "Kaina ne yake ciwo sosai" ta faWa muryar na rawa. Tausayi ta bashi musamman yadda muryarta take rawa, ya tuna lokacin da bashi da lafiya yadda ta dinga yi masa cikin tausayawa, hakan ya saka ya ce, "kin sha magani?."
"na sha, amma ya ™i ya daina" ta faWa a raunane cikin zafin ciwon kan.
"Sannu" ya sake furtawa can ™asan ma™oahi.

Bai sake magana ba bai kuma motsa ba, Nayla tana zaune itama amma ta ji dadi zuciyarta da ya tambaya har ya yi mata sannu. Kwanciya tayi a hankali saboda jin daWin kulawarsa sai ta ji zata iya baccin ma. Ba jimawa ta sake mi™ewa zaune ta sake ri™e kanta cikin ciwon da yake damunta. A hankali ya mi™e ya ™arasa ya kunna hasken Wakin yana kallonta, kuka take yi bilha™™i tana zaune ta ri™e kai.

Mamaki abin ya bashi, mai neman maganin ciwon kai ina shi ina kuka kuma?. A hankali ya ™araso inda take ya zauna a gefenta a karo na farko a zamansa da ita. Sai da yaji wani irin yarrr dan kafaWarsa ta taSa ta ta kaWan, ya ji wani abu kamar jan wutar lantarki kafin ya dawo daidai. Duk da ciwo yana damunta sai da ta ji wani iri a jikinta da mamaki mai matu™ar yawa.

"Cire hannun ki" ya furta gab da ita hakan ya saka taji maganar a kunnenta. A hankali ta sauke hannun daga goshinta shi kuma ya kai hannunsa goshinta ya ri™e jiijiyoyin kan nata. Yadda suke bugawa da gudu zai baka tabbacin ba ™aramin ciwo kanta yake yi mata ba, sai ta sake bashi tausayi dan ya san azabar ciwon kai tunda yana yi, ga kan nata ya yi zafi.

Addu'a ya fara yi mata wacce annabi Muhammad S.A.W ya koyar damu yayin jin ciwo. A online school Win da yake attending aka sanar dasu addu'ar, kasancewar bata da tsaho karantawa uku ya haddaceta a kansa. Sannan ya ji sheikh Isah Ali ibrahim Pantami ya koyar da ita a wani tafsir Winsa wanda ake Worawa a whatsapp status ko tiktok. Bai taSa gwadawa ba, amma yana ji a jikinsa in ya gwada mata zata samu lafiya. A zuciya yake karantawa hannunsa na ri™e da kanta kusan mintina uku kafin ya zare hannun ya tofa a hannunsa ya shafa mata a goshin a hankali.

(Za a ri™e inda yake ciwo, ko ina ne yake maka ciwo zaka ri™e wajan sannan ka yi Bismillah sau uku, sai ace #9OHR0O (P'DDGP HNBO/R1N*PGP EPFR 4N1PQ EN' #N,P/O H#N-N'0P1A'uzu billahi wa ™udratihi min sharri ma ajidu wa uhadir. Ina neman tsari da Allah da kuma Ikonsa daga sharrin abin da nake ji (na ciwo) kuma nake jin tsoransa. Za a karanta ™afa bakwai. Addu'a ya™ini ce, sai ka saka yarda da ya™ini sannan zaga amfaninta, in ka yi don gwaji ba tare da amincewa ba bazata yi maka aiki ba.).

Nayla tunda hannunsa ya sauka a goshinta ta ™ame ™am saboda gudun da zuciyarta ke yi, ta tabbatar da zai kasa kunne da kyau zai ji yadda zuciyar take bugawa dan ba bugu take na wasa ba, bugu take mai ™arfin da kuma sautin da take iya jiyo shi a kunnenta. Hannun Omar masoyinta akan goshinta ai dole zuciyata buga ko bata shirya ba.

Bata san ya gama ba ta ji ya zare hannunsa a kasalance kamar baya son magana ya ce, "Ki kwanta, sannan ki daina kuka. Ban da shirme me neman maganin ciwon kai meye zai kai shi kuka" ya faWa yana tashi daga wajan.

Nayla ta ja numfashi ™hamshin turarensa ta sha™a lokacin da ya motsa, ta kwanta a hankali a lokacin duhu ya mamaye Wakin dan ya kashe hasken ya ga yana damunta. Cikin mintina da bai wuce biyar ba bacci mai daWi ya Wauke Nayla.KRB3P021
Arewabooks@nanahaleema11.

Omar yana kallon ta har baccinta yayi nisa sosai sannan ya Wauke kai daga kallon ta ya tashi ya dawo kan gadon dan bazai yi kwanan takura irin jiya ba. Kwanciya ya yi a can ™arshe itama tana ™arshe akwai space mai yawa a tsakiyar su.

Kallon gefenta ya yi yana mamakin wai shine kwance da wata mace a kan gado Waya, Allah mai iko mai yadda ya so a lokacin da ya so, in ba dan ikon Allah ba shekaru biyar masu zuwa baya kawo aure a ransa. Juya mata baya ya yi tunani kala-kala yana zuwa ransa dan shi kam ya kasa bacci. ˜hamshin turaren ta ya dame shi, ko ya ya motsa sai ya ji shi a hancinsa.

A haka shima bacci ya Wauke shi da™yar, bai farka ba sai ™arfe biyu na dare ya buWe ido. Kallon inda take ya yi yaga tana yadda take amma ta juya yanzu tana kallon bayansa saSanin lokacin da ta kwanta. Sake rufe ido shima ya yi ya cigaba da bacci bai tashi ba sai asuba. Yau ma har ya yi alwala ya saka jallabiya bata motsa ba.

Tunani yake ya tashe ta ko ya ™yaleta? Kallonta ya ke yi sai yaga ta buWe ido kai tsaye suka haWa ido da ita, ganin haka sai ya janye idonsa ya fita daga Wakin.

A inda ya same ta bayan ya dawo tana wajan kamar jiya, ya zauna akan kujera kamar jiya bai ce mata komai ba. Nayla ta ce, "Ina Kwana." Maimakon ya amsa sai ya ce, "ya ciwon kan?." Nayla ta yi murmushin jin daWi har tsakiyar ranta sannan ta ce, "ya daina ciwon gabaWaya tun a jiya." Bai ce komai ba daman bata yi tunanin zai ce ba ta ce, "na gode."

Nan ma bai ce komai ba sai ™aramin jarbinsa da ya zaro a aljihu yana ja a hankali. Nayla ta ce, "YaMar zan je asibiti anjima, sannan na wuce wajan aiki." Ya jita amma ya share bai ce komai ba, Nayla har ta fitar da ran zai amsa mata sannan taji ya ce, "Shi zuwa aikin dole ne?." Ta kalle shi jin abinda yace amma ga mamakin ta idanunsa a kulle suke kamar ba shi ne ya yi magana ba. Ta ce, "eh."

Shiru ya sake yi bai ce komai ba amma yana mamakin ita da bata da lafiya aikin me zata je kuma?. Nayla ta ce, "Ka bar ni na je?." Ya buWe yana kallon ta cike da mamaki ya ce, "kin ji na ce kar ki je?." Ta girgiza kai ta ce, "A'a."
"Da in zaki tafi tambaya ki ke yi?." Nayla ta bishi ido tana kallon sa shi kuma ba ita yake kallo ba kuWin da yake ajjiye akan table Win yake kalla.

Nayla ta ce, "kaine ka ce ba sai na tambaya ba ai, Amma ka yi ha™uri." Mamaki ta sake bashi jin harda bashi ha™uri, kamar zai yi mata magana sai ya fasa kar ta ga ya za™e da yawa a lamarinta. Tashi tsaye ya yi ya ™arasa wadrobe ya buWe ya Wauki abinda zai Wauka ya dawo inda yake zaune amma bai zauna ba, a lokacin Nayla ta mi™e tsaye ya mi™a mata kuWi ta saka hannu ta karSa ya ce, "ki siyi magani." Nayla ta kalli kuWin ta kalle shi har ya juya ya koma ya zauna. Nayla ta yi murmushi farin ciki, annushuwa tana mamaye mata dukkan ilahirin jikinta da zuciyarta, ta ce, "Na gode YaMar."

Bai motsa ba balle ya tanka, ita kuwa daWi yayi mata yawa da tana da dama da tabbas da ta taka rawa saboda farin cikin da take ji. Agogo ta kalla ta ga har shida ta yi ta ninke sallayar da tayi sallah ta ajjiye inda ta Wauka tana ta murmushi ita kaWai. ˜arasawa tayi bakin gadon ta fara kokarin gyarawa dan in ta fita babu lallai ta dawo Wakin.

Bai ce mata pim ba har ta gyara gadon tsaf ta zo zata wuce shi ta ce, "Sai anjima YaMar" ta faWa tana fita daga Wakin tare da ja masa ™ofar. _Wai YaMar, inda ta iya faWar R Win ma da sau™i, amma wata kalmar take faWa daban a madadin R Win. Na rasa meyasa sunan yake min daWin ji a bakin ta._ abinda yake faWa a zuciyarsa kenan yana murmushi shi kaWai wanda bai san dalilinsa ba. Kawar da tunanin ya yi ya tashi ya kashe haske ya kwanta.

Yau ma ya jima yana bacci sai goma ya tashi, ya yi wanka ya sake gyara Wakin kamar yadda ya saba ya shirya. Yau wankan maroccon yallabiya ya yi marron kala mai shegen kyau da faWi kamar kayan sarakai haka take. Fitowa ya yi falon ya yi karo da Didi a zaune tana sha tea.

˜arasowa ya yi ya zauna ya ce, "Ina kwana." Kallon sa ta yi ta ce, "ka tashi lafiya." Bai amsa ba kamar yadda ta san bazai amsa ba daman.
"Ina ta jiran ka daman, ga abinci nan ka ci."
"Bana jin yunwa." Hararasa tayi ta ce, "ka ci don Allah, ai Nayla bata nan balle ka ce baza ka ci ba."
"Daman na ce miki saboda ita ne bana ci?."
"Baka ce ba, amma zaki fi sakewa ka ci in bata nan tunda haka ka Worawa rayuwarka."

Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba amma yana tunanin ko ta je asibitin, ko me aka ce yana damunta, ko ya ciwon kan nata yanzu bai sani ba. Didi ta kalle shi ganin yayi shiru kamar mai damuwa ta ce, "nima gidan zan kulle, shiyasa na ce mata ta Wauki key dan gidan Hajja zan je, bazan sake dawowa nan ba gida zamu wuce." Omar bai ce komai ba ya sake yin shiru yana sauke numfashi Didi ta zuba masa ido ta ce, "lafiya na ganka kamar mai damuwa?." Ya ce, "lafiya" ya furta kafin ya sake kallon ta ya ce, "Shi zuwa aikin nan nata wai dole ne?."
ÿþ

Didi ta ce, "dole ne mana, dashi ai ka aureta kuma iyayenta sun faWa maka zata cigaba da aikinta." TaSe baki ya yi bai ce komai ba, Didi ta ce, "kana da matsala da zuwa aikin na ta ne?."
"Ko Waya, na ga bata da lafiya ne kawai." Didi ta ce, "ta ce min zata biya asibiti daman yau." Shiru ya yi bai tanka ba Didi tana murmushi da mamakinsa, gabaWaya sai ta ga ya canja, tana kuma da tabbacin ko ba ya son Nayla to yana gab da faWawa, domin alamun hakan sun bayyana a tare dashi.

Maganar abinci da ta sake yi masa tana magiya ya saka shi ya sha tea kawai ya fita itama ta ce bazai dawo ya tarar da ita ba zata gudu. KuWi ya bata ya ce kuWin mota ne ta san hali babu damar ta ™i karSa ta shiga uku da masifarsa.

Nayla ma da ta tashi daga wajan aiki gidan Hajja ta wuce a can ta samu Didi, ta zauna suna ta hira har sai da Didi ta tafi sannan itama ta dawo gida. Bashir ya shigo mata da mota ya bata key Win sannan ta shiga cikin gidan.

Kamar yadda ta yi zato baya nan, ta kunna hasken falon sai ta tuna Didi ta ce ta dinga duba yanayin solar gidan hakan ya saka ta ta je inda Didi ta nuna mata dan ita ba sani tayi ba ma. Ganin da ™arfinta sosai ya saka ta komawa ciki ta yi wanka ta saka kayan bacci ta fito ta zauna a inda ta saba zama tana ta aikin dana laptop saboda aikin da aka turo mata ta gmail.

Bayan ta gama Netflix ta shiga ta fara kallo kafin ta kashe ta shiga application Win da take kallon ball ta saka tana kalla. Sai kuma ta tashi ta kunna tv falon da bata saba kunnawa ba, ta shiga tashar ball a nan ta ga dstv Win subscription ya ™are. Tsaki ta yi ta fara danna waya lokaci kaWan ta tura kuWin, ta tura musu number dstv Win nata aka sako mata kati. Kashe laptop Win ta yi ta cigaba da kallon ball din a tv, yadda ta ke kalla tana fahimtar komai zai baka tabbacin ta saba gani.

Tashi tayi ta shiga Waki ta Wauki maganinta da aka rubuta mata a asibiti ta zo ta sha ta zauna tana cigaba da kallo. GabaWaya kewar Didi ta dame ta a zuciyarta kamar sun jima a gidan haka take ji. Waya ta Wauka ta kira Didin, tana Wauka ta ce, "Wallahi Didi kamar ki dawo haka nake ji, gabaWaya gidan babu daWi." Didi tayi dariya ta ce, "ba kuma zan sake kwana a gidan ba har abada." Nayla tayi dariya ta ce, "kin je gida lafiya?."
"Lafiya lau Nayla, Ashe haka ki ka lodawa yallaSai lemo a bayan mota ban sani ba? Har da su madara."
"To Didi na san in nace zan bayar hanawa zaki yi, ni kuma sun yi min yawa kar ai ta asara. Kinga da azumi ma haka na dinga bayar da kayan saboda kar a yi asara, wa nake dashi in ba ke ba?."

Didi ta ce, "To Nayla na gode Allah ya bar zumunci, Allah ya bar ™auna tsakaninki da Damisa." Nayla tayi murmushi kawai bata amsa ba, Didi ta ce, "baki ce amin ba." Nayla ta ce, "To Amin." Didi ta yi dariya ta ce, "Ina fatan babu ciwon kan ko?."
"Babu ko kaWan, yanzu ma na sha magani."
"Haka nake so na ji, Sai ki tuna da abinda na ce miki." Nayla ta yi dariya ta ce, "Hajiya Didi kenan."
"Zaki ga Hajiya Didi." Sallama Nayla tayi mata ta kashe wayar tana murmushi.

Wai ta koma Wakin Omar da kwana, yo haka kawai ta je yana zare mata idanu? Dan ya yi mata mutunci jiya shi ai kamar wahainiya yake ko yaushe canjawa yake yi. Baza ta je ba, daman dole aka yi mata kwana biyun, yanzu tunda Didi ta tafi ya sha zaman sa.

Sallamarsa ce ta katse mata tunani kamar ko yaushe, Nayla ta amsa dan ta san babu lallai ya ™araso shiyasa bata motsa ma daga inda take ba. Sallama ta sake ji a inda take sai ta kalli inda yake ta ganshi ya shigo har inda take zaune sai ta mi™e sosai ta ce, "Sannu da zuwa." Kallon tv ya yi yana mamakinta, bai taSa ganin mace na kallon ball ba sai ita, yana yawan ganin ta tana kalla.

"Ya jiki?." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Da sau™i."
"Me aka ce yana damunki?." Ba Nayla ba hatta shi da ya yi tambayar sai da ya ji wani iri a zuciyarsa, amma sai ya maze bai nuna ba. Nayla ta sunkuyar da kai ta ce, "na samu low blood pressure ne, sai malaria amma babu yawa, amma sun bani magani." Girgiza kai ya yi ya ce, "Okay, Allah ya ™ara lafiya." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Amin, na gode."

Juyawa ya yi zai bar wajan sai ya dakata bai juyo ba ya ce, "in akwai wani abun zaki iya sanar da ni" yana faWa ya wuce ta bishi da kallo.

Baya ta yi ta kwanta a kan kujera tana jin farin ciki na zaga ko Ina na zuciyarta, wai Omar shine yake tambyar lafiyar ta cike da kulawa haka. Gaskiya yanayin ya yi mata daWi bata san lokacin da ta fara hawayen farin ciki ba, tabbas ta yarda da addu'a, ita kanta ta san addu'ar da tayi a watan ramadan a jikinta take jin Allah ya amsa, gashi kuwa tana ta ganin canji tun ba a yi nisa ba, ko a yanayin yadda take gaisawa da Abiy ta san Allah ya amsa mata addu'arta. Da wannan farin cikin Nayla ta

Please Login or Register in order to submit comment