Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk suka mi™e tsaye ya kalle su da murmushi suka gaishe shi ya amsa kafin ya kalli Nayla ya ce, "Mamana kina lafiya kuwa?." Nayla ta ce, "lafiya lau Abiy, ciwon kai ne tun na jiya har yanzu."
"Kwana biyu ciwon kai yana damunki sosai, ki je asibiti mana."
"Wallahi stress ne aiki na kawai Abiy, da nayi bacci na tashi sai na dawo daidai."

Abiy ya yi dariya ya ce, "kaga sabuwar ma'aikaciya." Tayi dariya Abiy ya zauna yana cewa, "™arfe nawa zaku tafi Kaduna gobe? Ni sai jibi monday zan dawo in sha Allah ." Nayla ta ce, "Duk lokacin ka ce Abiy."
"Saboda aikinki dole a koma gobe gaskiya, zamu gani zuwa azahar sai ku tafi in Allah ya kaimu."

Bata yi magana ba ya kalle ta ya ce, "Maganar Wan daban yaron nan." Ai da sauri ta Wago tana kallonsa a lokacin Mama tazo ta zauna a wajan. Abiy ya ce, "Mun yi magana da Senator..." ya faWa yana duba waya wacce sa™on text ya shigo. Shiru ya yi bai yi magana ba yana duba wayar. Nayla ji take kamar ta ™wace wayar daga hannunsa saboda ya kai ga faWa mata abinda zai ce.

Abiy ya ajjiye wayar ya ce, "mun yi magana ya kuma amince zai ™yale shi, gobe ma ya ce zai sake shi ya dawo gida in sha Allah." Wata irin ajiyar doguwar zuciya Nayla tayi, ta lumshe idanu tana jin wani irin daWi na ratsa zuciyarta. Abiy ya bita da kallon mamaki ganin yadda farin ciki ya bayyana a tare da ita kamar itace Yayar ta sa. A hankali ta buWe ido suka haWa ido da Abiy da yake kallonta, da sauri ta sunkuyar da kai amma murmushi take yi. Abiy ya ce, "ko dai kema ™anwarsa ce ne Nayla? Wannan ajiyar zuciya haka kamar Jawad aka kama za a saki?."

Murmushin ya™e tayi ta ce, "Abiy kawai Ina murna ne in na tuna yadda Didi zata yi murna." Abiy ya zuba mata ido yana binta da kallon tuhuma kafin ya ce, "kin tabbata?." Sai taji tsoro ya shige ta da tunanin Allah yasa bai gane wani abun ba. Ta sake sunkuyar da kai tace, "Eh Abiy."

"To ya yi. Ki sanar mata gobe zai dawo in sha Allah." Da farin ciki ta amsa shi kuma ya tashi ya shiga ciki Mama ma tabi bayansa. Nayla na shiga Waki sai gata ta fito da key Win motar Mama, Salma da Jidda suka kalle ta kafin su magana ta ce, "Gidan Hajja zan je, in zaku je kuzo mu tafi." Salma ta karSi key Win hannunta tace, "bani baza ki sake ™o™arin kashe mu ba." Bata ma ji ba tayi gaba burinta kawai taje ta faWawa Didi. Salma ce ta ja motar suka tafi gidan Hajja.

Nayla na shiga ta tarar da Didi ita da AbdulHamid suna tsaye da alama sallama yake yi mata. A guje ta faWa jikin Didi ta ce, "Didi Abiy ya yi magana da Senator ya tabbatar masa da gobe zai dawo, gobe zai dawo Didi" ta faWa da murna sosai. Didi cikin farin ciki ta ce, "da gaske ki ke? Da gaske ki ke Nayla?."
"Da gaske nake Didi." Didi ta ce, "Alhamdulillah! Allah na gode maka, Allah na gode maka" ta faWa tana sake rungume Nayla da take dara saboda murna.

"Na gode Nayla, na gode Allah ya saka miki da alkhairi Allah ya baki miji na gari." Ciki suka shiga dan Didi ta manta da AbdulHamid da yake wajan. Sai da suka shiga falon Hajja Salma ta ce, "Amin Didi. Dan wallahi itace jiya ta samu Abiy tana kuka kamar zata mutu saboda a fito da Omar, yadda muka bar gidan nan jiya baki ga gudun da ta dinga yi damu a mota ba saboda kawai take ta samu Abiy. Cikin ikon Allah tana faWawa masa ya kira shi a waya ya Wauka, yau suka haWu ya yi masa maganar ya kuma amince" Salma ta faWa tana kallon Didin da ta san aikin Nayla ne yadda ko Omar Win ya fito ya san ita tayi masa hanya ya fito.

Didi ta sake ri™e Nayla tana godiya tana hawaye tana cewa, "na gode Nayla, Allah ya bani abinda zan saka miki Nayla. Na gode sosai." Hajja ta ce, "itama ai ta saka alkhairin da ya yi mata ne Aisha, kin manta abinda ya yi mata?." Didi ta ce, "ban manta ba Hajja, amma wannan taimakon da tayi min ai baza ki haWa shi da wancan ba. Ta ceci rayuwata ta ceci ta Omar, bani da abinda zan saka mata saka addu'a."

Hajja tayi dariya dan ko ita ta ji daWin labarin dawowar Omar. Didi ta ce, "Nayla mu je na yiwa Abiy godiya, mu je yanzu in yana gida." Hajja ta ce, "A'a Aisha, ki bari ya dawo sai ku je ku same shi tare." Didi ta ce, "Amma ya kamata na je yanzu kafin ya dawo ko?." Nayla ta ce, "to sai mu je in anjima, ko kuma ki yi masa waya."

A nan suka baje ana ta hira da nishaWi Didi ji take kamar ta mayar da Nayla ciki saboda son da take yi mata. Sai bayan i'sha suka tafi saboda dinner da zasu je, tare da Didi aka je ta yiwa Abiy godiya ya ce babu komai. Drivern Hajja ne ya dawo da Didi su kuma suka fara shirin dinner. Ko a wajan dinner kowa ya lura da walwalar da Nayla take yi, su dai su Salma fatan samun sasssuci akan abinda yake damunta suke yi mata.

Washe gari ranar lahadi ™arfe goma na safe ta fita daga gida zuwa gidan Hajja. Ta samu Didi ma bata nan ta shiga gida tana aikace-aikace Saboda dawowar Omaar. Salma ce ta shigo tana cewa, "shine ko ki jira ni kika taho bayan kin san Jidda tana gidan ta." Nayla ta ce, "to ba gashi kin zo ba. Matsa min naje gidan Didi." Salma ta ce, "ba da wuri Abiy ya ce zaku koma ba ne? Yana ta faWa ya ce kin san zaku tafi Kaduna ki ka fito yawo."
"Kin ga Ina zuwa" ta faWa tana fita ta shiga gidan Didi Salma na biye da ita.

Lokacin da suka shiga Didi share Wakin Omar take yi, jin sallamar Nayla ya saka Didi ta ce, "Nayla gani nan, shigo." Nayla gabanta ya faWi matu™a, ta kalli Salma da take tsaye sai Salma tayi tsaki ta shiga Wakin.

Nayla ta shiga Wakin a sanyaye da sallama gabanta yana faWuwa, Waki ne babba mai girma dan yafi na Didi girma. Babu tarkace a Wakin babbar katifa ce mai girma da tudu, sai wardrobe mai guda shida a gefe, sai mirror mai irin wardrobe Win a gefe wanda abubuwan da suke kansa basu wuce guda biyar ba.

Didi ganin Nayla sai ta yi murmushi ta ce, "Nayla har kin fito?."
"Wallahi na fito Didi. Kin san fa yau zamu wuce Kaduna." Didi ta ce, "wallahi duk sanda ki ka zo bana so ki dinga zancen zaki koma Kaduna Win nan, bana jin daWi ko kaWan.." Nayla tayi dariya tana cigaba da kallon Wakin da sai ™hamshi turare yake yi mai sanyi.

Didi ta ce, "Ina gyara Wakin mutumin naki, in ba haka ba in yazo da faWa zamu fara kin san baya ™aunar ™ura ko kaWan. Zai iya zama wajan da aka zubar da kaya amma bazai iya zama a waje mai ™ura ba. Shiyasa yake gyara Wakinsa ko yaushe, dan shi baya jin gyaran Waki." Salma ta girgiza kai ta ce, "Ga Wakin nan tsaf dashi kamar ba na maza ba, har so nake na shigo dan naga ™azantar da take ciki ashe Wan gayu ne."

Didi ta yi dariya ta ce, "Ai baya shiri da waje kaca-kaca, kinga tsintsiyarsa a ajjiye ga dustbin"
Didi ta faWa tana nunawa Salma amma Nayla ce ke gani. Salma ta ce, "shikenan ya huta, ko ya yi aure babu ruwansa da sai an gyara masa Waki."

Nayla sai murmushi take yi tana kallon Wakin tana jin farin ciki a zuciyarta. Fita suka yi zuwa falon Didi bayan ta gama gyarawa har da fesa airfreshner. A falon suka zauna suna ta hira Nayla sai kallon ™ofa take yi amma babu alamun Omar ko kaWan.

Duk ta damu ga rana tana yi lokacin tafiyar su yana gabatowa. Suna zaune har azahar tayi Omaar bai dawo ba, a lokacin kiran Abiy ya shigo wayarta tana Wauka bai jima yana magana ba ya kashe, Nayla ta kalli Salma da Didi ta ce, "Didi zan je gida zan haWa kayana zan wuce, sai dai na ce sai na dawo wani lokaci. Wata™ila ma sai bikinki" ta faWa tana kallon Didi.

Didi ta ce, "tafiyar ta tashi?."
"Wallahi Abiy yace na zo zamu tafi."
"Na so kun haWu da Omar kafin ki tafi gashi bai dawo ba har yanzu. Amma zamu zo Kaduna tare dashi mu sake yiwa Abiy godiya sha Allah." Nayla ta yi murmushi ya ce, "Allah ya kawo ku. Salma zo mu je" tare suka fito Didi tana ta yi mata godiya har sai da Nayla ya nuna bata so sannan ta daina suka shiga gidan Hajja. A harabar gidan Hajja ta kalli Salma ta ce, "Salma don Allah ki zauna da Didi in ya dawo ki yi min video ki tura min kin ji?."

Yadda tayi maganar sai ta bawa Salma tausayi a sanyaye ta ce, "in sha Allah zan yi miki, kar ki damu."
"Na gode ´ar uwa." Daga haka suka shiga wajan Hajja tayi mata sallama a gaggaucs saboda kiran Abiy da yake shigowa wayarta. Ta Wauki motar da ta zo da ita ta bar unguwar zuciyarta duk babu daWin rashin ganin masoyinta.KRB2P008
Arewabooks@nanahaleema11.

Didi da Salma tun suna zaman jiran dawowa Omar har suka gaji da zama suka koma gidan Hajja. A can suke zaune har akayi sallar magriba babu alamun Omar. Didi a lokacin ta yi ajiyar zuciya a sanyaye ta ce, "wata™ila bai amince ya sake shi ba ne, wata™ila kuma Omar Win ne ya yi taurin kai ko ya faWi wata magana mara daWi." Hajja ta ce, "ki ta addu'a zai dawo, tunda Abdullahi ya ce zai dawo na tabbatar zai dawo kar ki damu."

"Assalamu alaikum!" aka faWa a ciki ba tare da sallamar ta fito sosai ba tare da shigowa cikin falon. GabaWaya suka juya ga wanda ya shigo suna kallon sa.

Didi wara idanu tayi ganin Oamar Winta a tsaye yana kallonta, sai ta zabura ta mi™e ta ™arasa inda yake ta ri™e hannunsa ta ce, "Omar kai ne?." Kai ya Waga mata ya ce, "eh Didi, ni ne." Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Alhamdu lillah! Allah na gode maka, Allah na gode maka da ka dawo min da Omar cikin ™oshin lafiya."

Duk ta ruWe tana addu'a kamar wacce bata cikin hankalinta, ganin hakan sai ya dafa kafaWarta muryarsa a sha™e ya ce, "Didi ki nutsu mana." Didi ta ce, "na kasa nutsuwa Omar, na kasa. Farin cikin dawowarka ba zai bar ni na nutsuwa ba." Sai a sannan ya kalli Hajja da take kallonsa ya ce, "Ina yini."

Hajja ta ce, "daga nan? Baza ka shigo ka zauna ba?." Didi ta ri™o hannunsa zuwa cikin falon ya tako da™yar dan baya jin daWi gabaWaya. Zama ya yi Hajja ta kalle shi ta ce, "Barka Omar, Ina fatan komai lafiya ko?." Kai ya Waga kawai bai ce komai ba dan maganar ma wahala take masa, ya kalli Didi da take kuka ya ce, "meye na kukan kuma Didi? Ba dai gani na dawo ba? In kina kuka bazan ji daWi ba."

Saurin goge ido tayi ta ce, "na daina Omar, farin cikin ganin ka ne ya saka haka nake kuka amma na daina." Hajja ta yi murmushi tana kallon sa, abinda ya bata mamaki tsaf dashi baza ka ce ya fito daga wahala ba. Duk da ya rame sosai fuskar sa ta Wan yi duhu amma shigarsa da yanayinsa gabaWaya bai nuna haka ba. Yadda ta ce gashin fuskarsa ya taru yanzu duk an rage sai wanda ya saba bari abin ya bawa Hajja mamaki.

Didi ta kalle shi ta ce, "Ka yiwa Hajja godiya, ta silar Hajja da Nayla ka dawo gida yau. Mahaifin Nayla shine ya saka aka dawo da kai gida." Hajja ta katse ta ta ce, "Aisha ki bar shi ya huta tukunna, yana bu™atar hutu sosai. Ku je gida ya huta maganar ta biyo baya." Kamar jira yake ya mi™e dan daman bai so shigowa ba, kawai dan Bashir ya ce masa tana ciki ne ya saka shi ya shiga. Hajja ya kalla ya ce, "Sai da safe."
"Allah ya tashe mu lafiya Omar" ta faWa da murmushi tana kallon sa.

Fita ya yi Didi ta dawo kusa da Hajja ta ce, "na gode Hajja, na gode Allah ya biya ki da aljanna. Duk ta dalilinki Omar ya fito, ta dalilinki ne Hajja. Allah ya sa aljanna ce makomarki." Hajja da Salma suka amsa da amin Hajja ta ce, "kar ki damu Aisha ai a riga an zama Waya, kallon jikata nake yi miki kamar Nayla da su Salma, Kar ki damu ki kwantar da hankalinki. Ki shiga kitchen ki Wauki abinci a nan ki kai masa ya ci ya huta, in zai je ganin likita ma aje a duba shi ya dawo hankalinsa kamar da."

Didi ta ce, "to Hajja. Amma na so Nayla tana nan ya dawo, ban san dame zan sakawa Nayla abinda tayi min ba Hajja." Hajja tayi murmushi ta ce, "kin san bashi da uwa sai ke Aisha, ki tashi ki je ki bashi abinci ya huta sai mu yi magan." Da to ta amsa ta tashi taje ta Wauki abinci a kitchen Win Hajja, ta Wauki hijjabi da wayarta ta fita daga gidan cikin farin ciki.

Hajja tayi murmushi bayan ta fita ta ce, "Allah sarki Hauwa'u sarki tausayi, sai da ta san yadda tayi mahaifinta ya fito da Omaar. Allah ya biyata." Salma ta amsa da amin tana kallon video da ta yi a zuwan Omar tana tunanin ta tura mata ko ta share ta kawai. Kiran Nayla ne ya saka shigowa wayarta, daga tafiyarta zuwa yanzu sau goma sha bakwai kenan tana kiranta, Salma
tayi tsaki ta mi™e ta shiga Waki.

Didi da ta fita a tsaye a ™ofar gidan ta ga Omar shida mutane sa, da hanzari ta ™arasa ta buWe gidan ta manta a rufe gidan ya ke. Sai da ta Wan jima da shiga sannan ya shigo falon tana kallon sa har ya ™araso. Ta ce, "™anina ga abinci kazo ka ci sai ka kwanta ka huta ko?." Omar ya zauna ya ce, "na ™oshi Didi, na ci abinci magani kawai zan sha na kwanta."
"Sannu" ta furta a sanyaye tana kallon sa. Kawai ya Waga kawai bai ce komai ba.

Didi ta ce, "na ganka tsaf ba kamar lokacin da naje na same ka ba." Omar ya ce, "ban shigo cikin gari ba sai da na tabbatar na dawo nutsuwata. Da aka bani wayata sai na kira su Bash suka same ni a wajan gari, har asibiti mun je a ™ara min ruwa an kuma bani magani. Wannan dalilin ne ya saka na jima ban shigo ba sai yanzu." Didi ta ce, "gwara da ka yi hakan ko dan saboda ´an gulma. Amma ka rame sosai Omar, kuma ka yi duhu." Bai ce komai ba ta sake kallon sa ta ce, "to ka sha maganin kafin kwanta sai ka fi jin daWin bacci."

Kallon ta ya yi da kulawa ya ce, "kema kin rame Didi, baki da lafiya ne?."
"Lafiya lau nake Omaar, rashin ka ne kawai ya kawo hakan." Šan murmushi ya yi ya ce, "Sai ka ce in ina na nan Win ba faWa muke yi ba." Didi ta yi ´ar dariya ta ce, "Ko doke-doke muke yi ™arewar faWa ba." Murmushi ya sake yi ya ce, "Kar ki damu yanzu na dawo ai."

Kafin ta yi magana ya ce, "an ce a gidan Hajja ki ke kwana ko?."
"Eh Omar, hana ni kwana anan tayi ta ce na koma gidan ta saboda mutane." Kai ya girgiza da yayi masa nauyi bai sake magana ba. Dauriya kawai yake yi yana magana saboda ita, amma kansa ciwo yake yi sosai.

Mi™ewa ya yi sai ya yi kamar zai fadi ta zabura ta mi™e tana kallonsa, Omar ganin yadda ta zabura sai ya dake ya ce, "kar ki damu ba wani abun bane, kaina ne yake ciwo kaWan." Har Waki sai da ta raka shi ta tabbatar yana cikin ™oshin lafiya sannan ta fito ta shiga nata Wakin tana tunanin dame ya kamata ta sakawa Nayla alkhairin da tayi mata?.

Washe gari.

Ya ji sau™in jikinsa babu laifi ya daure bai kwanta ba saboda kar hankalin Didi ya tashi, hakan ya saka shi ya fito ya samu tana ta aikace-aikace kamar kullum. Tana ganinsa ta dakata ta ce, "ka fito? Ya jikin na ka?." Šan lumshe ido ya yi ya buWe, da zai iya faWa mata gaskiya da ya ce mata babu sau™i dan ciwon kan bai rabu dashi ba, ga jikinsa gabaWaya babu ™arfi, ga ciwo da duk gaSoSin jikinsa suke masa. Amma da yake baya so ya sakata a damuwa sai ya ce, "na ji sau™i. Kawai bana jin ™arfi ne sosai."

Didi ta ce, "Sannu. Zauna na kawo maka shayi ka sha zaka ji daWi." Zaman ya yi kamar yadda ta ce ta kawo masa shayi ya karSa tana yi mata sannu. Zama tayi a nesa dashi tana kallon sa ta ce, "sannu Omar." Kai ya Wan Waga kaWan yana shan shayin a hankali ba dan yana jin daWinsa ba sai dan saboda ita Win.

Shiru ya ratsa tsakani, tayi shiru shima ya yi shiru yana shan tea a hankali yana kallon wani wajan daban. Didi ta ce, "in ka warware ina so zamu je Kaduna gidan mahaifin Nayla mu yi masa godiya. Shi ne ya yi magana da Sen ya rabu da kai Omar, ´arsa Nayla ce taje tana kuka ta ce don Allah ya yi wani abun ka fito." Omar ya kalle ta ya ce, "to" ya amsa a ta™aice dan baya son doguwar magana.

Ido ta ga ya lumshe ya ajjiye kofin hannunsa ta bishi da kallo kafin ta mi™e ta ™yale shi a wajan tana cigaba da aikin da take yi.


" " " " " "
*England, london.*

Tunda Narma da Najwa suka sauka a ™asar England Najwa ta kasa gane kan Yayarta, domin kuwa ta koma wata iri babu walwala babu dariya babu zaman hira. Ko yaushe tana cikin Waki ta rufe kai ko tana kuka ko tana tunani. GabaWaya zaman bai yiwa Najwa daWi ba saboda ba haka suka saba zaman ba, sun saba su ne yaje su je nan su je can, amma yanzu gabaWaya ta canja.

Narma ta kasa sarrafa kanta akan son da take yiwa Omar, ta rame ta Wan yi dogon wuya saboda tunani. Gangar jikinta ce kawai a England amma hankalinta da komai nata yana Nigeria.

Tana zaune cikin riga da wando masu laushi kanta babu Wankwali ta zubawa waje Waya idanu. ˜arar shigowar message taji kamar baza ta duba ba sai kuma ta duba taga daga WhatsApp ne ta buWe tana karantawa. Ai da sauri ta kira voice call yana Wauka ta ce, "Da gaske ka ke Dad ya saki Faruk?." Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin ta ce, "Shikenan ina zuwa" ta faWa hannu na rawa tana kashe wayar.

Farin ciki ya bayyana akan fuskarta a bayyane ta ce, "Dad ya saki Faruk, Faruk ya koma gida. Wayyo Allah daWi, Allah na gode maka." Number Omar ta nemo babu wani tunani kawai ta kira voice call. Ringing ta dinga yi alamun ba a kunna data ba ta kashe wayar tare da cillar da ita gefe ta ce, "Ko ya yake? Ko yana tunanina kamar yadda nake tunaninsa?."

Najwa ce ta ™araso wajan ta ce, "Ya Narma ga ticket na siya mana zamu je emirate stadium kallon wasan arsenal da liverpool." Narma ta kalle ta ta ce, "Sai kin dawo, ni bazan je ba."
"Meyasa baza ki je ba? Kuma na ga Arsenal shine club Win da kike so, Meyasa baza ki zo mu je ba?."
"Najwa bana jin daWi don Allah ki ™yale ni, bazan iya zuwa ko ina ba."

Najwa bata sake magana ba ta koma Waki ta kira Mum, Mum tana Wauka ta ce, "Mum Ya Narma tana gab da kashe kanta da tunani, tunda muka zo nan bata da wani aiki sai na tunani Mum. Kullum kuka, kullum cikin ganin hotonsa take tana magana ita kaWai. Mum lamarin Ya Narma ya fara bani tsoro wallahi."

Mum ta ce, "kuma kina zama a inda take?."
"Mum bata bani wannan damar, yau ne fa take zaune a falo amma kullum tana cikin Waki ta kulle kanta. Har ticket na siya mana yanzu na zuwa kallon ball amma ta ce baza ta je ba, kuma Arsenal ne fav club Win da take supporting." Mum ta ce, "ki cigaba da jan ta da hira, in abin bata yu ba sai ku dawo kawai." Najwa ta ce, "daman ni na gaji da zaman nan wallahi" ta faWa tana yanke wayar tana mita.KRB2P009
Arewabooks@nanahaleema11
*Nigeria, Abuja.*

Lokacin da Mum ta yanke wayar Najwa kallon Sen tayi da yake jin duk abinda Najwa take cewa, cikin fusata Mum ta ce, "ana cikin wannan yanayi kuma wai ka saka aka sake shi, mu da muke so ya karya asirin da ya yi mata amma ka sake shi ya bar ma Abuja salin alin kamar wanda mu ke jin tsoro. Gaskiya Dear baka kyauta ba sam, baka kyauta min ba nida Narma, abinda ka yi bai kamata ace kayi shi ba. Ka san yadda muke ciki da Narma amma ka iya bari ya bar Abuja lafiya ba tare da wata damuwa ba, ka ga kenan ya yiwa banza."

Dad da yake jinta yana daga zaune ya ce, "Dear ki nutsu mu yi magana."
"Bazan taSa iya nutsuwa ba wallahi, ya asirce min yarinya bata iya ganin kowa sai shi ka ce na nutsu?."
"Calm down please, ki zauna mu yi magana."
"Ina zancen ´ata tana london ta kasa sukuni saboda asirin da aka yiwa mata kana ce min I should calm down!. Wallahi dear in wani abun ya samu Narma, in Narma ta samu ciwo ta wannan dalilin, in Narma ta yiwa kanta illa ta dalilin wannan asirin da ya yi mata ba tiger ba, wallahi ko lion ne sai na ga bayan sa! Wallahi sai na saka an raba shi da numfashinsa gabaWaya!" Ta faWa cikin ihu tana kallon Dad da yake kallon ta.

Dad ya mi™e tsaye ya ri™e ta cikin rarrashi ya ce, "ki nutsu mu yi magana mana." Mum ta ce, "bazan nutsu ba! Duk kai ka jawo wannan abin, na faWa maka kar ka haWa min yarinya da Wan daba amma ka ™i ji. Ga abinda hakan ya haifar nan muna gani ni da kai, kuma ana ™o™arin samun mafita akan kuskuren da ka yi ka sake tafka wani kuskuren ta hanyar sakin sa da ka yi. Anya kaima ba asirin ya yi maka ba?."

Dad ya ce, "Nayi hakan ne saboda tafiyar siyasar mu dear. Ke kin san matakin gov nake nema, kin san yana da tasiri sosai a Sangaren zaSen baya. Barinsa a hannunna in labarin ya fita hakan zai iya taSa carrier ta, sannan shima zai iya sakawa ayi abinda bazan kai labari ba. Shiyasa ana sake shi."

Mum ta ce, "babu abinda zai iya, babu abinda ya isa ya hana babu abinda ya isa ya saka ayi. Waye shi? Waye shi nace!? Ka manta da waWanda aka yi gwagwarmaya ne? Ka manta ta yadda aka yi ka zo wannan matakin ne?."
"Ya isa dear, Dear ya isa. Zai iya taka rawar gani wajan ganin ya kai ni ™asa." Mum ta ce, "Shiyasa ai nace a gama dashi, shiyasa nace a raba shi da numfashinsa amma ka ™i ji. Yanzu me ka ke so ayi? Haka zamu bar Narma kenan?."

Dad ya ce, "Aura mata Ashraf zamu yi a tura shi su zauna na Wan lokaci, in yaso daga baya sai su dawo ayi biki. Hakan shine mafita kuma na tabbatar Ashraf zai yi iya bakin ™o™arinsa wajan ganin Narma ta dawo hankalinta saboda tana sonsa." Tsaki Mum

Please Login or Register in order to submit comment