Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Musliha ta samu kyauta daga wajansu, suna ta yabon ta suna shafa fuskarta.

A nan aka yi meeting suka ™ara tashon contract Win zuwa shekara biyar mai zuwa. Aka yi signing aka yi hoto kamar wancan lokacin. Basu jima a wajan ba suka dawo hotel. Kwanan su biyar a China suka dawo Qatar daga nan suka dawo Nigeria.

Ready to say =ŘKÜ>ŘyÝ
Nana haleematus Sadiyyad'ţKRB3P110

Rayuwa na ta juyawa abubuwa suna ta faruwa da yawa, ciki harda zuwansu Omar aikin hajj shida Nayla da Didi, bayan an kammala aikin hajj aka kai Didi yawon buWe ido a ™asashen turai. Cigaba da samun ™aruwa a fannin kasuwancinsa,  kwanciyar hankali da walwala ta samu wajan zama a cikin iyalansu.

Omar ya sake zama fari tass, ya ™ara kyau da  class na musamman saboda kuWi sun zauna. Yau yana wannan ™asar, gobe in ya dawo zai je wannan, duk akan cigaba da zamanatar da sana'arsa. Ya haWu da manyan masu kuWi, matasa da wanda suka jima da kuWi, idanunsa ya sake buWewa ya kuma sanin waye shi. Har lokacin Didi fama take dashi akan danginsu amma har lokacin ya ™i sakin jiki, an dai samu cigaba tunda za a gaisa kawai amma bayan wannan shikenan baya sake cewa komai balle wani abun ya haWasu.

    Nayla tayi kyau fuskar ta sake yin haske sosai sai dai ta™i ™iba, duk hanyar da zata bi kar tayi ™iba tana bi dan bata so. Ai kam bata yi ba, tana nan ´ar daidai da ita bata gaba bata baya.

Marmerh an yayeta, Omar ya karSe ta ya kawowa Nayla ta haWa da Musliha da take koyan tsayawa. Omar ya sake sha™uwa da Marmerh sosai, dan sai da tayi wata Waya a gidan sannan ta koma. Duk inda ta ganshi ta ce Daddy, shi kuma abinda yake sake sakawa ya ™ara ™aunarta kenan. Har yana mamakin wato su dangin mahaifiyarsa ™aunarsu ne basa yi, shiyasa basa jin wani abu akansu kamar abinda yake ji a kan Marmerh.

      Ranar Laraba da yamma Nayla tana zaune a cikin mota tana ta kuka kamar wacce aka yiwa mutuwa. Sai da ta gaji da kukan ta kalli Musliha da take zaune a gefe tana ta wasa, suna haWa ido da Nayla ta yi dariya irin dariyar yara. Nayla hawaye ya sake sakko mata cikin tausayin ´arta, ta Wauki waya ta kira number Didi. Didi tana Wauka Nayla ta sake fashewa da kuka mai tsanani, hankalin Didi ya tashi cikin kiWima ta ce, "Nayla Lafiya? Me ya faru ki ke kuka?." Nayla ta ce, "Didi kina gida?.

"Bana nan Nayla, na shiga asibiti saboda ciwon cikin nan da nake fama dashi, amma yanzu zan dawo."
"Don Allah Didi zaki biyo ta gidanmu?."
"Lafiya Nayla?."
"Don Allah ki zo."
"To gani nan" ta faWa tana yanke wayar. Nayla cikin kuka ta kunna motar ta nufi gidanta.

      Tana shiga gidan ta ajjiye Musliha akan kujera tana cigaba da zubar hawaye. Ba jimawa Didi ta shigo a gigice ta ce, "Nayla lafiya? Hankalina ya tashi sosai." Nayla ta kwanta a jikinta tana sake fashewa da kuka. Didi cikin tashin hankali ta ce, "Ya rasulillahi! Nayla gabana yana faWuwa, faWa min me ya faru don Allah." Nayla ta mi™a mata takardar hannunta ba tare da tayi magana ba, Didi ta karSa tana buWewa gabanta na faWuwa.

Abinda ta gani ya saka ta zaro ido ta ce, "Nayla ciki ne dake?." Nayla ta kasa magana sai kuka. Didi ta Wan yi tsaki ta ce, "ikon Allah! Yanzu akan ciki kike ta wannan kukan? Wallahi na Wauka wata cutar aka ce kina da ita Nayla."

Nayla cikin kuka ta ce, "Didi Musliha watan ta bakwai amma ace ina da wani cikin?." Didi ta ce, "To daman Nayla indai baki Wauki mataki ba ai zaki yi ciki, ni na yi mamaki ma da aka kawo yanzu baki Wauki cikin ba." Nayla ta ce, "To Didi babu yadda ban yi dashi ba, amma ya ce bazan yi family planing ba, nayi-nayi amma ya ce baya so, ™arshe sai ya ce bai yafe ba in na yi. Didi na shiga uku, ya zanyi?."

Didi cikin kwantar da hankali ta ce, "baki shiga uku ba Nayla, ai cikin halak ne kuma mijinki yana so."
"Didi ai bai san wahalar haihuwar ba ne shiyasa yake so. Tsakani da Allah ko shekara Musliha bata yi ba ace ina da wani cikin? Ga Marmerh har an yayeta ta girma tana zuwa ko ina kuma baki da wani cikin sai ni? Twiny har yanzu bata da ciki."

Didi ta ce, "To Nayla banda abin ki tunda dai kin riga kin yi cikin ai babu batun kuka, kuma tun farko rashin Waukar mataki ne ya jawo faruwar hakan. Gaskiya Musliha tayi ™arama ace an cire ta daga shayarwa yanzu, ko shekara bata yi ba akwai Waukar ha™™i." Nayla ta sake karya murya cikin kuka ta ce, "to ya zanyi? Cewa ya yi bai yafe ba, kuma ya nuna baya so."

"Ai ba lallai sai na asibiti ba, akwai natural da ake yi wanda zaki yi. Da kin sani kin faWa min tun lokacin, sai na san abinda zan yi dan gujewar faruwar hakan. Da ko magana sai nayi masa, ™ar™ari yayi masifar ya gama.
"Hmmm! kin manta waye shi ne kawai, baki ga yadda mu ka yi dashi ba a kai" ta faWa tana goge idonta. Didi ta ce, "to yanzu ya za a yi?."

Nayla ta ce, "tunda bai sani ba ni zubarwa zanyi." Didi ta wara ido ta ce, "zubarwa Nayla? Cikin sunnar zaki zubar?." Nayla ta sake marairaicewa ta ce, "To ya zanyi Didi...? Da rainon ciki zan ji ko da rainon Musliha?. Gab nake da fara exams a makaranta, da me zan ji?. Ga kula da mai gidan, shi kansa kula dashi zaman kansa yake yi dan bai san uzuri ba." Didi ta ce, "Gaskiya babu daWi, amma batun zubar da ciki ki adana shi Nayla bai kamata ba, ha™uri zaki yi ki raine shi Allah zai dafa miki."

Nayla cikin kuka ta ce, "Wallahi Didi ni bana so! wahala zan sha kawai. Ni dai ki amince na zubar, har na zubar ai bazai gane ba. Sai na tawo gidanki tun safe na zauna har dare."

      "Allah ya baki ikon zubar min da ciki, na rantse da Allah in ki ka yi wannan gangancin sai kin yi danasanin sanin Omar a rayuwarki!." A tare suka juya suka ganshi a tsaye ya harWe hannu a ™irji yana kallonsu da alama ya jima a wajan. Fuskarsa taya ja saboda Sacin rai ya bayyana a tare dashi, idonsa ya canja, fuska a cure alamun aljanun Sacin ran sun motsa.

Suna haWa da Nayla ido ta sake fashewa da kuka ta ce, "To ya zanyi? Musliha ko shekara Waya bata yi ba, watan ta bakwai kaWai a duniya, da me ka ke so na ji? Da rainonta ko rainon cikin ko da makarantar da na ke yi?."

Cikin faWa ya ce, "Wannan kuma ke ta dama, makaranta ke ta shafa ba ni ba, ke kika ga zaki iya kika saka kan ki. Abu Waya nake so na maimaita miki, na rantse da Allah kika yi gangancin zubar da cikin nan zaki yi dana sanin da baki taSa yi ba a rayuwarki!. Zaki ji a zuciyarki ina ma baki san mai suna Omar a duniya ba!" Ya faWa yana wara idanunsa yana nuna ta da yatsa.

Nayla itama a fusace ta ce, "Ko Marmerh ba a yiwa ™ani ba sai ni za a ce zan haihu? Ko Didi bata da wani cikin sai ni?." Cikin tsawa da murya mai amo ya ce, "Wannan mijinta ne ya ga zai iya, shi ya ga zai iya asarar yaran da Allah ya bashi amma ni banda ni. Ki daina haWa ni misali da kowa, dan ni ra'ayin wani ba ra'ayina bane, abinda nake so shi nake yi, babu wanda ya isa ya canja ni!."

Nayla kuka take yi sosai, tana jikin Didi da take zaune bata ce komai, cikin fusata da Sacin rai ta ce, "Ni wallahi bana so! Bazan iya sake haihuwa yanzu ba, ko wata goma ban yi da haihuwa ba a ce ina da wani cikin? Wallahi bazan iya ba! Ni zubarwa zan yi!" Ta faWa tana kuka sosai kamar wacce aka yiwa mutuwa.

A fusace ya tako ya zo wajan da take ya ri™o dantsen hannunta ya rabata daga jikin Didi, ya mi™ar da ita tsaye yana jijigata dan ta dawo hankalinta ta kalle shi, cikin fusata da Sacin rai ya ce, "wallahi! Wallahi!! In ki ka yi wannan gangancin....!" Sai ya kasa ™arasa faWar abinda zai ce, ya buWe mata ido cikin tsananin Sacin rai ya sake cewa, "Dan baki da hankali yanzu sai ki zubar min da ciki!?. TaSWijam, da ban san wanne irin hukunci zan yi miki ba, ban san wanne irin mataki zan Wauka a kan ki ba. Abu Waya na sani; sai kin ji ina ma baki zubar da cikin nan ba, sai kin ji ina ma baki taSa sanin Omar a rayuwarki ba!" ya faWa yana sakin hannunta.

Zata yi magana ya zabura kamar zai dake ta yana nuna ta da yatsa ya ce, "kina cewa tak sai ranki ya  sake Saci yanzun nan wallahi, in kina musu ki yi magana Jidda! Ni kuma zan nuna miki bana faWa na canja" Ya faWa cikin tsawa yana zare mata ido.

    Shiru tayi ta koma kan kujera ta zauna tana kuka mai taSa zuciya. Didi duk bata ji daWin abinda yake faruwa ba, tausayin Nayla take ji dan wannan shine ga mari ga tsinka jaka. Ta daure ta ce, "To Omar iya wannan tsawar da ka ke yi mata ma ai cikin sai ya zube da kansa, ka nutsu mana, ka san dole zata ji babu daWi, kwata-kwata Musliha watan ta nawa da za a ce tana da ciki?."

Ya kalli Didi ya ce, "in ma bata yi wata Waya ba bai dame ni ba, ai tun farko na faWa mata ko wata Waya ne Musliha bata yi ba ta samu wani cikin ina maraba dashi, amma dan rainin hankali cikina zata ce zata zubar? Dan shirme da zalla rashin hankali Wan da Allah ya bani zata salwantar min?. Hmmmm! wallahi da ta yi wannan gangancin da baza ta sake marmarin tuna ta zubar da ciki ba a rayuwarta. Ta zubar min da ciki!" Ya maimaita yana kallon Nayla.

      Sai kuma ya kalli Didi a fusace kafin yayi magana ta ce, "Ka nutsu mana, ka yi addu'ar Allah ya inganta shi mana,  sai masifa ka ke yi. Baka da tabbacin cikin zai rayu har ya zo duniya, wannan tayar da jijiyoyin wuyan da ka ke yi akai wata™ila Allah bai nufa za a haife shi ba. Ka cika kawo matsala wallahi, har yanzu ka kasa tsayawa ka fahimci abu kafin hukunci."

Kallon ta yake yi har ta gama magana fuska a haWe cikin kaushin murya ya ce, "Babu abinda zai samu cikina, zai inganta ya zo duniya kamar yadda Musliha ta zo duniya. Ki daina yi min fatan cikina bazai inganta ba, bana son wannan mugun bakin" ya faWa yana harararta.

Sai kuma ya ja tsaki yana kallon Didin ya ce, "Da ke ake haWa biki za a kashe min Wana ko? Da ke ake so a munafurce ni a zubar min da ciki ko Didi?. Har wani cemin ki ke yi wai in bazai zo duniya ba da yake kun ™ulla munafurci dake da ita. To wallahi in har ku ka zubar min da cikin nan daga ke har ita sai nayi shara'a da ku, kuma a inda kuka zubar dashi sai kun je kun kwaso shi kun dawo min da kayana. Allah ya hore min, zan iya rainon yara Wari koda ba nawa ba ne."

     Didi kallon mamaki take masa jin wai sai ya yi shari'a dasu, ko wajan wanne al™alin zai kai su oho masa. Har yanzu halinsa yana nan, fusata da masifa. Takawa yake yi zai bar wajan ya juyo ya sake kallon su ya ce, "Ina maimaita mu ku, aka sake aka yi wannan gangancin wallahi....sai bai ™arasa ba ya girgiza kai ya ce, "dukkan ku kun san bana rantsuwa na karya, kun san sauran" ya faWa yana Waukar Musliha da take ta mi™a masa hannu ya hau sama a fusace.

Nayla ta kwanta a jikin Didi tana kuka sosai ta ce, "Ni fa sai na zubar da cikin nan Didi." Didi tana shafa bayanta ta ce, "Ki yi ha™uri Nayla, ki daina kuka. Ki bar zancen zubar da cikin nan tunda mijinki baya so."
"Kar ya so mana, ™ar™ari in na zubar ya sake ni, shine ™arshen hukuncin da zai yi min. Saki ai ba a kaina aka fara ba, mata nawa ake saki a kullum?. Tunda ba Waukar raina zai yi ba ai shikenan, ni sai na zubar bazan sake haihuwa yanzu ba" ta faWa a fusace.

Didi ta yi dariya jin abinda ta ce, ta san Sacin rai ne ya saka take faWar haka. Didi ta ce, "ki yi ha™uri ki daina faWar haka, zubar da cikin da ba na halak ba ma haramun ne balle cikin halak wanda aka samar dashi ta hanyar aure. Meye laifin cikin? Laifi ai na Omar ne ba shi ba. A kansa zaki huce ba akan cikin da Allah ya baki ba.  Don Allah ki bar batun zubar da cikin nan, ki yi ha™uri ki saka a ranki Allah ya yi zuwan abinda yake cikin ki duniya shiyasa hakan ya faru. Ki kwantar da hankalinki, Allah zai baki ikon rainonsa ki haihu lafiya."

      Nayla dai bata ce komai ba sai hawaye da take yi, wai wata bakwai da haihuwarta ace tana da wani cikin, ita ko shekara biyu bayan haihuwa ta ga mutum ya sake haihuwa sai ta ga kamar bai san ciwon kansa ba. Amma ita gashi ko shekara Waya ba a yi ba ta kwaso wani cikin, gabaWaya haushin cikin ya mamaye mata zuciya, Omar kuwa ji take kamar ta je ta dinga dukansa har sai ta wuce takaicinta akansa.

"Ki daina kuka Nayla, ki daina kuka bana so na ji kina kuka. Sannan don Allah kar ki zubar da cikin nan, kar ki biyewa zuciya ki aikata aikin dana sani." Nayla ta sassauta kuka tana jan numfashi cikin rauni. Rarrashinta Didi ta dinga yi har ta daina kuka, ta Wauko mata ruwa ta bata ta sha tana cigaba da bata baki har ta ga hankalinta ya Wan kwanta sannan Didi ta wuce gida. Amma ita kanta ta tausayawa Nayla sosai.P111

Nayla haka ta kwana biyu bata kula Omar shima baya kulata, ta saka ™in cikin a zuciyarta hakan ya saka ta fara rama saboda damuwa. Sai kuma cikin ya zo mata da laulayi ba irin na Musliha ba, tafara amai ga zazzaSi da ciwon kai. Har lokacin haushinta yake ji itama haka, ba ya ma haWuwa da ita saboda takaici, itama bata zuwa inda yake. In ya tuna ta ce zata zubar masa da ciki sai ya ji haushin duniya ya ishe shi, sai ya ga wacce irin ™iyayya take yi masa da zata zubar masa da ciki? Duk ™aunarta da yake yi da wannan zata saka masa.

     Yau ma Nayla na jikin sink tana amai kanta ya yi bala'in nauyi, Musliha kuma tana gefe tana kuka tana bu™atar uwarta Wauketa amma Nayla bata da wannan ™arfin. Dawowa ta yi ta kwanta a kan carpet tana juya kai ga sanyin da take ji. BuWe ™ofar aka yi, Nayla ta san  mai aikinta ce ta ce, "Salima zo ki Wauketa ki bata cerelec, sannan ki taimaka min da ruwa na sha kaina zai cire."

Omar ganin yanayin da take ciki sai jikinsa ya yi sanyi, tausayinta ya kama shi matu™a, ya tuna wayar da suka gama da Didi take sanar dashi cikin ya zo mata da laulayi sosai.

Nayla jin bata yi magana ba sai ta ce, "Salima kuka take yi ki Wauketa, bazan iya Waukarta ba. Sanyi nake ji, ki Wauko duvet a Waki ki rufe ni." Omar ya sake jin tausayinta ya ratsa shi, ya buWe bedroom Winta ya Wauko duvet mai nauyi da laushi ya rufa mata, ta ja shi har fuskarta ta rufe tana rawar sanyi.

Šaukar Musliha ya yi da take kuka har lokacin ya kwantar da ita a jikinsa yana rarrashinta. Nayla jin har lokacin Musliha bata yi shiru ba sai ta mi™e zaune da™yar ta ce, "bani ita Salima, in ban Wauketa ba bazata daina kuka ba" ta faWa tana dafe kai hawaye na sakkowa daga idanunta. Rauni ya ji ya mamaye masa zuciya, tausayinta da haushin share ta da ya yi kwana biyu ya cika masa zuciya.

Ganin tana mi™o hannu alamun a bata Musliha sai ya kasa bata, ganin yanayin da take ciki kuma ta kasa share ´arta da take kuka sai ya sake jin rauni sosai a zuciyarsa, duk fushin da yake da ita ya kau daga zuciyarsa.  A tausashe ya ce, "Ki kwanta, zan bata da kaina." Jin muryar Omar ta Wago idanunta da suka koma jajaye suka haWa ido, hawaye ya sake sakko mata cikin rauni ta ce, "Tana ta kuka, yunwa take ji sosai, ka bata cerelac ko na je na bata."

"Zan bata, ki kwanta ki huta. Sannu" ya furta cikin tausayi yana kallonta. Komawa ta yi ta kwanta shi kuma ya tashi zuwa kan table Win Wakin, a nan ya ga duk abinda yake bu™ata da zai haWa mata kamar yadda ya saba, da kansa ya haWa mata ya zauna yana bata sai dai duk ya Sata kayan jikinsa itama jikinta haka. Tana gama sha ta sha ruwa sai kuma ta fara kuka tana kiran Mummy.

    Nayla ta fara bacci kenan ta ji ihunta tana kiran sunanta, ya kalle ta ya ga ta buWe ido a wahale ta ce, "bani ita."

"A'a Jidda, baki da lafiya ki bar ni da ita."
"Bazata daina kuka ba, in tana kukan bazan iya baccin ba, ka bani ita kawai." Ajiyar zuciya ya yi ya ™arasa inda take ya ajjiye mata Musliha. Hannunsa ya kai wuyanta ya taSa ya ji zafi sosai ya ce, "Jidda jikinki da zafi, tashi mu je asibiti." Nayla ta ce, "zai sauka, haka yake yi min kullum, zuwa nan da magriba zai daina."
"Haka zaki zauna da ciwo? Ki tashi mu je."
"Bana son tashi, kaina cirewa zai yi."
"To sai na Wauke ki."
"Ka bari kawai, zai daina haka nake yi kullum."

Tashi ya yi ya je ya canja kayansa ya dawo da ruwa da towel ya zauna a kusa da ita, ganin Musliha tayi bacci a kusa da ita sai ya Wauketa ya kwantar akan baby bed Winta da yake falon, ya dawo ya mi™ar da ita ya kwantar a jikinsa ya zuge zip Winta rigarta ya buWe ta baya. Cire mata rigar yayi gabaWaya ya ajjiye ya fara goge mata jikinta da ruwan sanyi.

     Ajiyar zuciya ta yi jin sanyi na ratsa ta ya shafa mata ruwan a fuska, ta kifa kanta a ™irjinsa tana jan numfashi da™yar. Sai da ya ji zafin jikin nata ya ragu sannan ya saka hannu yana shafa bayanta a hankali cikin tsananin tausayinta. A hankali ya furta, "me zaki ci....Uhum?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "babu."
"Ki tuna, me ki ke so a kawo miki?."
"Kunun gyaWa nake so da kilishi."

Omar ya ce, "bara na je na saka ayi kawo miki." Ta ri™e shi a jikinta ta ce, "Kar ka tashi, ina jin sau™in jikina a haka."
"Zan faWawa Salima ta yi miki kunun ne, shi kuma kilishin zan saka a kawo miki."
"Bana so ka tashi, ka zauna."
"To Sannu, ki yi ha™uri ki yafe min. Ban yi niyar saka ki a wannan yanayi ba." Bata iya magana ba ya cigaba da shafa bayanta a hankali, tausayi take bashi amma ko kaWan baya ji a zuciyarsa zai iya ba da goyan baya a zubar da cikin nan.

     A hankali ya ji tayi bacci a jikinsa, ya yi murmushi yana kallon ta tare da kissing Winta a forehead yana shafa kumatunta a hankali.
"Ki yi ha™uri Jidda" ya sake faWa yana shafa kanta a hankali. Šaukarta ya yi ya kai ta Waki ya kwantar da ita ya rufeta ya rage mata ac. A falon ya zauna saboda kar Musliha ta tashi ta yi kuka ta tashe ta. Har aka yi sallar i'sha bacci take yi zuwa lokacin Musliha ta farka tana wajansa. Sai takwas ya sake shiga Wakin da Musliha a hannunsa, ta mi™awa Nayla hannu tana kiran Mummy.

     Murmushi Nayla ta yi idar da sallar ta kenan ta ce, "Musliha!." KarSarta tayi ta rungume ta a jikinta tana shafa kanta ita kuma tana ta dariya. Fita ta ga ya yi bai jima ba ya dawo da tray a hannunsa ya zauna akan gadon ya ajjiye tray a tsakiya ya ce, "ga abinda ki ka ce kina so."

Nayla ta kalli kunun gyaWar ta yamutsa fuska ta Wauke kai ta ce, "ka Wauke, bana son ™hamshinsa ko kaWan." Da mamaki ta ce, "ke ki ka ce kina so."
"Ya fita daga raina wallahi, gwara dai kilishin,
Ka fita dashi kar ya saka ni amai." Bai musa ba ya tashi ya fitar dashi falo ya dawo, ya zauna kusa da ita ya fara bata kilishin a baki tana ci. Kilishin ya yi mata daWi sosai dan yana da yaji ita kuma yajin ne ke mata daWi.

    Ta ci da yawa sosai, ya bata ruwa ta sha ya Wauke tray Win daga tsakiyarsu ya ajjiye a gefe, Musliha tana tsaye a bayansa ta Wafe masa wuyan tana yi masa wasa.

    Hannun Nayla ya ri™e sai ta zame ta mi™e da sauri zuwa banWaki, da sauri ya bi bayanta ya ga gabaWaya kilishin da ta ci ya dawo har ta hanci. Ta gigice saboda yaji, hankalinsa ya tashi ya bata ruwa ta sha ya ri™ota suka dawo Waki ya zaunar da ita ya ce, "Abinda ki ka ci ya dawo, zaki kuma ci?." Ta ce, "Haka nake fama, komai na ci sai ya dawo."
"To ki kuma ci."
"Ko na ci zai dawo."
"Kuma ba ki faWa min mun je asibiti ba?."

Ta kalle shi ta ce, "fushi ka ke yi dani ai, kuma ko mun je asibiti babu abinda zasu iya yi min, laulayi ne kawai." Ya ri™o hannunta duka biyun kafin ya Wora hannu Waya akan fuskarta ya ce,"Amma lokacin Musliha ba haka ki ka yi ba, zan iya irga sau nawa na ga kin yi amai, bakya zazzaSi kuma bakya ciwon kai." Ta kalle shi da jajayen idanunta ta ce, "Wannan ya canja, Mama ta ce daman haka abun yake."

      Ya Wago fuskarta da ta sunkuyar yana kallon idanunta tana karanto tausayinta da yake kan fuskarsa sosai, ta kuma san ya yi rauni duk fushin da yake yi da ita ya kau daga zuciyarsa. A hankali ya kai bakinsa goshin ta ya yi kissing ya sake ri™e hannayenta ya ce, "Allah ya baki lafiya."
"Amin."

"Jidda!." Ta Wago ido ta kalle shi ya ce, "Ki yi ha™uri." Bata ce komai ba ya kuma cewa, "Kwana biyu na share ki, raina ne ya Saci akan batun zubar da ciki nan amma kina raina, kema kin san bazan iya ™yaleki ba. Ban san haka ki ke fama da ciwo ba Jidda, da na sani da na kasance a gefenki a ko yaushe, amma ki yi ha™uri!" Ya faWa a tausahse a hankali yana murza yatsun hannunta.

Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "ni daman wannan wahalar nake gudu shiyasa na ce zan zubar, kuma ga kula da Musliha. Bata yarda da su Salima balle su Wauke ta, daga ni sai kai take yarda dasu, kuma kai ba zama ka ke yi ko yaushe ba."
"Shiyasa na ce ki ha™uri Ashiq, tabbas kina shan wahala ga tsananin ciwo ga kula da ita, ki yafe min don Allah, ina ji kamar ban miki adalci ba. Na yi miki cikin da yake baki wahala kuma na shareki, sannan ga ´ata da ki ke kula da ita."

Ta Wago ido tana kallonsa ya ce, "Eh duka laifina ne, da sai na san hanyar da zan bi na yi miki irin wancan cikin mara wahala." Jin abinda ya

Please Login or Register in order to submit comment