Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce, "Mu bayyana kenan? A kwaso kayan da aka binne?."

Omar ya yi tsaki ya ce, "ina magana kana katse ni?."
"Tuba nake."
"Ko meye zai faru kar ku sake ku fito, na tabbatar ba shi kaWai ba ne, zasu cutar daku dan kasan ku yake nema. Ku zauna, kar ku fito sai da umarni."

Bashir ya ce, "Tiger zasu ga kamar mun ji tsoro ne, ta ya zamu zauna bayan suna ™ofar gidanka?. Baza mu iya zama ba, zamu fito ayi ragas mutuwar kasko." Omar ya ce, "ni dai haka nake mu ku" yana faWa ya yanke wayar.

Nayla ta ce, "Rouhii me ya faru? Su waye wa....." sake dukan gate Win aka yi da wu™a, gate Win ya bada sautin ™all mai ™ara. Nayla ta firgita ta faWa jikinsa cikin tsoro da kiWima. Ya ri™e ta yana kallon gate Win, kafin ya kalle ta ya ce, "ki nutsu."

    "Wallahi in baka fito ba sai mun shigo gidan nan, in baka fito ba ka nuna ka ji tsoro, daman na san tsoro ne ya saka ka zubar da makaman ka, kana tunanin rana irin ta yau shiyasa ka ce kai ka koma mai sana'a. Dan bana cikin gari ne, yanzu kuma na fito. In ka cika Wan halak ka fito!."

Omar ya sauke numfashi, ya kalli Nayla da ta kunna hasken Wakin jikinta yana rawa. Baice komai ba ta ga ya ™arasa bakin gadon, ya Wuka ™asan gadon ya Wauko wata ™atuwar wu™a mai tsaho siririya. Nayla ta wara ido ganin ya mi™e tsaye yana zare wu™ar daga cikin murfinta yana taSa kaifinta. Soketa yayi a jikinsa, ya Wauki riga ya saka a daidai lokacin da aka sake dukan gidan aka ce, "in ka cika kai ba matsoraci ba ne ka fito, ni kuma wallahi in ka fito sai dai a haifi wani ba kai ba. In kuma baka fito ba wallahi sai mun diro!."

Omar ya girgiza kai cikin takaici ya ce, "zan yi maganin ka" ya faWa yana niyar fita. Nayla ta buga tsalle ta sha gabansa a gigice ta ce, "Rouhii ina zaka je? Me zaka yi da wu™a ka Wauka?" Muryarta rawa take yi tana magana.

Ya cire hannunta daga jikinsa ya ri™e bai saki ba ya ce, "ki zauna a nan, kar ki je ko ina."
"A'a Rouhi, don girman Allah kar ka fita, ka ajjiye wu™ar da ka Wauka. Kar ka fita, Rouhii ka taimaka min kar ka fita" ta faWa tana shiga jikinsa tana fashewa da kuka.

   "ka ce baka ji, ka ce kai baka ja da baya, ka ce kai ba matsoraci bane, ka ce kai Damisa ce. Ya ka gaza? Yaushe Damisa ta fara jin tsoro? Yaushe ka fara ja baya!" Sautin da suka sake ji kenan hakan ya saka shi cire Nayla daga jikinsa ya ce, "ki nutsu Jidda, ki zauna a nan, zan dawo yanzu."

"Bazan zauna ba, wallahi bazan zauna ba. Kana jin me suke cewa, kashe ka zasu yi, ni dai kar ka fita!" Ta sake faWa a gigice zata koma jikinsa. Cikin tsawa ya ce, "Nayla!" Cak tayi da kukan tana kallon sa jin sunan da ya kira ta dashi, ya buWe mata ido yana girgiza yatsa ya ce, "Ni ba matsoraci ba ne, ni bana ja da baya, ba a nasara a kaina. Ki zauna a nan, zanje na dawo, babu abinda zai same ni!."

Nayla ta ja numfashi hawaye yana sakko mata ta ce, "Wu™a fa ka Wauka, wu™a ce a jikinka Rouhiiii" ta nuna taga da yatsanta murya na rawa ta ce, "zaka fita wajan su ku yi faWa da wu™a™e ku zubar da jini. Rouhiii kar ka fita, kar ka fita don Allah!."

   Bai kula ta ba dan ya san bazata fahimta ba, ya gyara zaman rigarsa ya ce, "na faWa miki kar ki je ko ina, ki zauna a nan." Ganin yana niyar fita ta sake shan gabansa tana girgiza masa kai tana kuka. Kulle ido ya yi ya buWe a kanta, in ya biye ta kukanta bazai yi abinda ya yi niya ba,  ya saka hannu ya janyeta gefe ya fita da hanzari. Biyo bayansa ta yi tana kiran sunansa, ya juyo a fusace ya ce, "ki koma!." Sai da ta firgita saboda tsawar da ya yi mata, ta zube a wajan tana kuka tana kallo ya fita.

Bata san adadin lokacin da ta kwashe a wajan ba, tana jingine da bango tana jan numfashi cikin rashin sanin abinda yake faruwa a waje. Motsi taji alamun za a shigo, ta zabura ta mi™e ta koma Wakin jikinta yana rawa. A lokacin ya shigo Wakin fuskarsa a Waure, alamun Sacin rai ya bayyana ™arara a tare dashi. Nayla ta bishi da kallo ™irjinta yana bugawa jiri yana ™o™arin kayar da ita.

Kallon ta ya yi yaga yadda ™irjinta yake Wagawa, ya kalli hannunsa da ya yi kaca-kaca da jini, ya kalli rigar jikinsa ya ga jini duk ya lalata ta, ya sake kallon ta yaga jikinta yana karkarwa kamar an jona mata wutar lantarki. Ya san a tsorace take, ya Wauke kai daga kallon ta ya shiga banWaki yana furzar da iska mai zafi.

   Ya jima a ciki sannan ya fito yana goge hannunsa, ya cire rigar jikinsa ya ajjiye, ya zare wu™ar jikinsa ya mayar da ita mazauninta. Wayarsa ya Wauka ya danna sannan ya saka a kunne ya ce, "kun je asibitin?." Shiru ya yi alamun ana bashi amsa kana ya ce, "duk abinda ya faru ka sanar dani" yana gama faWa ya yanke wayar yana jan numfashi.

Kallon Nayla ya yi ya ga ta daskare a wajan, ya san a ruWe take da abinda ta gani, Didi ce kaWai ta saba ganinsa cikin jini kaca-kaca ba ita ba, dole ta shiga ruWani da tashin hankali. Numfashi ya sauke, ya haWWiye yawu ya mi™e yana takowa inda take, yana kai hannunsa jikinta tayi wata irin zabura tayi baya tana zare ido jikinta na rawa. Hannunta yake ™o™arin ri™ewa ta fizge tana runtse ido tana sake ganinsa cikin jini kamar likitan da yayi tiyata. "Jidda!" Ya faWa a tausashe yana kallon ta.

"Kar ka taSa ni, kar ka zo kusa dani. Bana son ganinka, bana so ka taSa ni!" Ta faWa cikin fitar hayyaci tana nuna shi da yatsa.

Ransa a Sace yake matu™a, yana saurarenta ne saboda ya san bata cikin hankalinta. Ya sake takowa ya tam™o hannunta, zata zille ya ri™e ta ™am ya haWata da jikinsa. Wani irin yun™uri tayi sai amaii shaaa, ™arnin jinin da yake tashi jikinsa ya daki hancinta amai ya cigaba da zuba a jikinsa.

   Du™awa tayi a wajan tana amai, ya bi bayanta yana kallon ta tana zubar da abinda taci. Tana gamawa ta yi baya ta zauna daSas a ™asa tana sauke numfashi tana hawaye. Murya a sar™e ya ce, "sannu!." Abinda ya furta kenan yana kallon ta. HaWe jikinta tayi a waje Waya ta cusa kanta a guiwarta ba tare da ta kalle shi ba, ya sauke numfashi ya ce, "ki bar wannan kukan, ki tashi ki kwanta dare yayi sosai" ya faWa yana kallon agogo a lokacin ™arfe uku na dare.

    Zai sake magana ta fashe da kuka mai sauti tana cewa, "FaWa ka yi ko Rouhi? Jinin wani na gani a jikinka, ™arnin jinin nake ji har yanzu. Wani ka kashe? Wani ka kashe ko.....kashe shi ka yi....ya bar duniya......." Omar ya ja tsaki ya ce, "Ke ni ban kashe kowa ba, ki tashi ki je ki kwanta bana son shirme!."

"˜arnin jini nake ji a jikin ka, jinin da na gani a jikin ka na waye? Na waye?. YaMar abinda ka bari ka cigaba da yi? FaWan da ka daina ka koma yi!." Mi™ewa tsaye yayi ya ri™e hannunta ya mi™ar da ita ya ce, "Malama ki je ki kwanta, bana son surutun banza."

"bazan kwanta ba, ni ka cika ni" ta faWa tana fincike jikinta. Ta sake kallon sa ta ce, "Meyasa zaka kashe shi? Sai da na ce maka kar ka fita amma ka fita, ka dawo da jini a jikinka. Meyasa ka aikata haka? Meyasa?."

"Kee!" Ya faWa da ™arfi yana zare mata ido. Ya Wora yatsansa a kan bakinsa idonunsa a buWe ya ce, "shiiiii." Šif tayi tana kallonsa tana jan numfashi cike da tsoro da tashin hankali, ya nuna mata kan gado ya ce, "wuce ki kwanta!."

   Jikinta rawa yake yi sosai, ta kasa motsawa daga inda take saboda tsoro da firgici. Cikin tsawa ya ce, "ki wuce ki bani waje!." A firgice ta motsa zata bar wajan tsantsin aman ya kwashe ta tayi baya zata faWi ya taro cikinta ta tsaya cak, ya sake tamke fuska ya nuna mata kan gado ya ce, "wuce ki kwanta!."

Muryarta na rawa ta ce, "Sallah.....zan......yi...." Ya nuna mata banWaki ya ce, "shiga, in kuma na sake jin bakin ki sai na saSa miki." Da sauri ta wuce banWakin. Dogon tsaki ya ja ya fita ya Wauko abinda zai gyara inda tayi aman ya gyara wajan har lokacin bata fito ba.

˜arasawa banWakin ya yi ya buWe, wata irin zabura tayi ta haWe jikinta waje Waya tana kallonsa alamun tsoronsa take yi. ˜are mata kallo yake yi da alama tunda ta shiga baWakin babu abinda ta yi. Fuskarta ya kalla suka haWa ido, ta haWWiye wayu jikinta yana cigaba rawa.
"Alwalar kenan?." Kamar wacce ya tunawa, ta yi firgigit ta ™arasa gaban sink ta buWe fanfo ta fara wanke hannunta. Jikinta rawa yake yi har ta gama ta fito, ta shinfiWa sallaya ta saka doguwar riga da hijjab ta tayar da sallah.

BanWakin ya shiga ya yi wanka ya fito ya canja kaya, yana kallon ta tana sallah a firgice, kana ganin ta ka san babu nutsuwa a jikinta. Bashi da nutsuwar da zai iya yin sallah shiyasa bai gwada yi ba, ya Wauki waya ya sake kiran Bashir ya ce, "Ya jikin na sa?." Shiru ya yi kafin ya ce, "Okay" daga haka ya yanke wayar. Cillar da wayar yayi cikin Sacin rai, wai shi Tiger aka zo har gida ana yiwa ihu, shi ake cewa yaji tsoro, shi ake cewa ya ja da baya, shi ake Wagawa murya. Ya yi ™wafa a bayyane ya ce, "Bazai kwana da rai ba" ya faWa yana lumshe ido yana tuna baya.

Nayla jin wannan kalmar sai gabanta ya faWi, ta faWi tana faWawa Allah kukan ta cikin sujjada hawaye. Har aka yi sallar asuba yana a haka, ko fita bai yi ba a gida suka yi sallah shi da ita. Tana idarwa jiki yana rawa ta ce, "ina kwana." Kallon ta ya yi ya Wauke kai, ya manta rabon da su yi irin wannan gaisuwar. Da ya dawo daga masallaci take rungume shi sannan su gaisa, amma yau itace take ja baya kamar ta ga dodo.

Bai nuna mata ba ya ce, "ki tashi ki kwanta" ya faWa ba tare da ya amsa ba. Jikin ta yana rawa ta mi™e ko hijjab Win bata cire ba ta kwanta, sabon tsoronsa take ji yana ratsa ilahirin jikinta. Numfashi ya ji tana ja alamun mai kuka, ya juya ya kalle ta ya ce, "ki daina kuka, ki yi bacci." Kamar wacce ya bawa umarni ta rufe ido ruf tare da toshe bakinta da hannunta. Yana zaune a wajan har baccin tsoro ya Wauke ta sannan ya tashi ya fita daga Wakin.


     Da safe ko da farka baya nan, haka ta tashi a gigice ta fita daga Wakin dan bata da nutsuwar gyarawa. Wanka tayi ta haye gado ta rufe jikinta saboda zazzaSin da take ji yana ratsa jikinta. Har azahar tana kwance, jin yunwa ta dame ta ya saka ta mi™e ta fito da™yar ta sha tea a lokacin aka fara ruwan sama mai ™arfi.

   Gidan shiru sai ita kaWai, kuka take ta yi in ta tuna abinda ya faru jiya sai taji kuka ya tawo mata wanda bata shirya ba. Ta rasa abinda yake yi mata daWi, ko ganin Omar Win ma bata taso, saboda tsoronsa da ya gama zagaye jininta. Waya ta Wauka tana kallon agogo ta ga ™arfe uku a lokacin kuma ruwan ya tsaya, hannun ta yana rawa ta shiga lambarsa ta kira shi bai Wauka ba, sai ta rubuta masa text na zata je gidan Didi.

    Tana gama tura masa ta saka hijjabi ta Wauki kuWin mota dan baza ta iya jan mota ba, ta Wauki wayarta ta fita daga gidan. Tana fitowa daga gidan taji wani irin WaWi ya mamaye ta, gabaWaya gidan tsoro yake bata shiyasa take so ta fita ta bar shi. Napep ta tara ta hau sai bayan ta shiga take yi masa kwatancen uguwar da Didi take dan bata san sunanta ba.

    Tunda Nayla ta fito wani da yake can gefe a kan machine yake kallon ta, tana shiga napep ya kunna machine Win ya Waukar waya ya saka a kunne ya ce, "Matarsa ta fita a adaidai sahu" shiru ya yi alamun ana bashi amsa kana ya ce, "An gama, yarinya kwananki ya ™are yana gama faWar hakan ya saka wayar a aljihu yabi bayan napep Win.KRB2P072
Nanahaleema.

Nayla tafiya ake jikinta yana rawa sosai, sai da aka fara shiga cikin unguwar su Didi taji tsoro, dan unguwar shiru gashi an yi ruwa ko abin hawan babu sosai. A daidai gidan ya sauke ta, ta fita daga napep Win hannu na rawa ta bashi dubu biyu ya karSa. Ganin wajan babu jama'a kuma a tsorace take sai ya fito mata da wu™a ya ce, "Kee! kawo wayar hannunki." Nayla jiki ya cigaba da rawa, tsoronta ya ninka na baya, ba shiri ta bashi wayar ya shiga napep Win da hanzari ya bar wajan.

   A guje ta kwasa zuwa ™ofar gidan Didi, buga gate Win take yi a haukace cikin firgici da fitar hayyaci. Bata ji alamun motsin kowa ba ta cigaba da dukan gidan tana neman Wauki amma shiru. A lokacin wata ma™ociyar Didi ta zo wucewa, ganin Nayla a tsaye tana buga gidan sai ta kalli ta ce, "Sannu baiwar Allah, ai Aisha bata nan ta fita tun safe." Nayla ta ja numfashi mai tsaho, bata iya bawa matar amsa ba saboda tashin hankali.

  Kalle-kalle ta fara yi tana kuka a tsorace, babu kowa a akan titi kuma babu inda ta sani a wajan balle ta je, kuma gashi ba mota a hannunta, kuWin hannunta ma su kenan ta bawa mai napep. Jiri Waukarta yake yi cikin tsoro da fargaba, bata taSa shiga cikin yanayin da take ciki ba tunda take a duniya. Machine ta gani daga gefenta an ajiiye, kai tsaye aka yo inda take ana zaro ™atuwar wu™a mai kama da adda. Ba zato babu tsammani aka kaiwa wuyanta sara, cikin kiWima da tashin hankali ta kare da hannunta wu™ar ta shiga cikin naman hannunta take jini ya fara zuba. Wata irin ™ara Nayla tayi saboda azabar da ta ratsa jikinta har ™wa™walwarta.

Ganin bai same ta a inda zai yi saurin kashe ta ba ya saka shi ya ce, "Au ban hallaka ki ba kenan" ya sake faWa yana Waga wu™a zai soka mata a ciki. Cak ya tsaya sakamakon ri™e hannunsa da ya ji anyi, juyowa ya yi a firgice yana kallon wanda ya ri™e shi. Ganin waye ya saka ya kai masa bugu da ™afa a ciki, Tk ya yi baya ya dafe cikinsa saboda dukan ya shige shi sosai. Ya sake yin kan Nayla da ta zube a wajan kamar mara rai jini ya Sata hijjabin jikinta. Cikin azama Tk ya sake ri™e shi suka fara kokawa, ya kaiwa Tk sara ya kauce, ya sake kai masa sara ya sake kaucewa.

Jijiyar wuyansa Tk ya daka da ™arfi, take ya tafi luuu ya zube a ™asa a wajan. Tk ya Wauki waya tare da Waukar hoton fuskarsa ya kai kallonsa ga Nayla da take yashe a wajan numfashin tana yana sama da ™asa. Da sauri ya ™ara kusa da Nayla ganin yadda jini yake tsiyaya daga hannunta ya ce, "Antyn mu, taso na kai ki asibiti."

Nayla jin maganar take yi a sama, ™irjinta yana bugawa tsoro ya gama dabaibaiye mata zuciya. Jikinta rawa yake yi, ga azabar da hannunta yake mata ga tsoro da tashin hankali.

Tk ganin bata cikin hankalin ta ya kalli hanyar, har lokacin babu kowa sannan ga wanda ya sumar a sheme a wajan. Ya du™a ya ce, "Antyn mu ki taso mu tafi, kina zubar da jini sosai, kina bu™atar ganin likita."
"Wayyo Allah! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Na shiga uku, hannuna, jini ne yake zuba" ta faWa a firgice dan maganar Tk kamar farkar da ita tayi daga mafarki.

Tk a gigice yake, so yake ya kaita asibiti saboda jinin da take zubarwa, in wani abun ya same ta ya san mai gidansa bazai Waga masa ™afa ba. Ganin haka sai ya ce, "Antyn mu Didi bata nan, ki zo na kai ki asibiti, zaman ki a nan babu tsaro, komai zai iya faruwa dake a wajan nan. Ki nutsu mu tafi asibiti don Allah." Nayla kuka take yi cikin azabar ciwon da take ji, ta nuna masa hanya ta ce. "sun ™wace min wayata, wu™a ya Wauko yana nuna min. Sun....sun....cire min hannu."

Tk ya runtse ido, ya Wuka ya ri™o hannunta duka biyun zuciyarsa na bugawa, ji yake kamar yaci amanar Tiger da ya ri™e hannun matarsa, amma babu yadda zai yi, taimaka mata yake so ya yi, ri™e ta Win yafi barinta a wajan. Ya ce, "Antyn mu ki nutsu don Allah, ki zo mu tafi asibiti" ya faWa yana buWe mata motar. Kasa tashi tayi, sai da ya Wagota sannan ta iya tsayawa tana jiri, kamar mai taSin hankali haka ta shiga motar ya ja da sauri suka bar unguwar.

   Yana so ya bata waya tayi blocking bank account Winta amma ya san bata cikin nutsuwarta. Kuka kawai take yi tana ri™e hannunta da yake zubar da jini dan ba ™aramin yanka suka yi mata ba. Asibitin da Didi ta haihu ya kai ta, ganin yadda aka ji mata ciwo sai yace masu ™wacen waya ne suka ji mata ciwo. A take aka karSe ta aka yi mata allurar TT. Ana dressing wajan tana kuka mai sauti saboda azaba, bata cikin hankalin ta gabaWaya, azaba ce take ratsa jijiyoyin jikinta. A lokacin Omar ya shigo wajan, suna haWa ido da ita ya sakar mata banzar harara wacce ta saka ta sake fashewa da kuka.

Nurse Win da yake mata dressing Win ya ce, "Ciwon ya yi zurfi, dole ayi mata Winki." Omar ya sauke numfashi yana kallon yadda take hawaye, hijjab Win ta duk ya lalace da jini dan sai yanke hannun hijjab Win aka yi aka fito da ciwon. Šauke kai yayi daga kallon ta, yana jin zuciyarsa kamar zata fito saboda tashin hankali da tausayinta.

Zama ya yi a kusa da ita fuskarsa a Waure ya ri™e ta a jikinsa, ta kwanta a jikinsa tana kuka mai sauti. Kanta yaji da zafi sosai alamun ciwon kai, ya sauke numfashi bai ce komai ba saboda bazai iya magana. A haka aka yi mata Winki tana kuka, kwantar da ita aka yi a asibitin saboda zazzaSin jikinta aka saka mata ruwa. Yana zaune a gefenta yana kallon ta tana sauke ajiyar zuciya cikin rashin nutsuwa, allurar da aka yi mata ya rage mata raWaWin da hannunta yake mata.

Tk ne ya shigo Wakin cikin sanyin jiki ya kalli Omar ya ce, "tuba nake Tiger, na gaza bata kariyar da ya kamata." Omar ya kalle shi da jajayen idonsa ya Wauke kai. Bai ce komai ba, kai ya girgiza yana haWWiye yawu mai Waci, ya Waga masa hannu kawai dole Tk ya fita.

A haka baccin ya Wauke Nayla, ya yi ajiyar zuciya ya mi™e ya dafa goshinta zuciyarsa cike da jin haushinta da kuma tausayinta. Tausayinta yake ji dan ya san bata taSa tsintar kanta a wannan yanayin ba, sannan haushinta yake ji akan laifin da ta yi masa. Ba jimawa Didi ta zo asibitin, ganin yanayin yadda hijjab Win Nayla ya lalace da jini ya saka ta kuka, ya kalle ta da idanunsa da suka ™an™ance saboda Sacin rai ya ce, "ki daina kuka kar ta tashi, ki zauna da ita zan je na dawo" ya faWa muryarsa a dashe saboda damuwa.

Didi ta goge ido ta ce, "me ya faru haka Omar? Waye ya ji mata ciwo haka?."
"Ki zauna, zan je na dawo" ya faWa yana sake dafa goshin Nayla. Hijjab Win jikinta ya cire mata ganin tana gumi, ya kalli inda aka ji mata ciwon yaga tsahon yankan tun daga guiwar hannunta har tsintsiyar hannunta. Ya sauke numfashi ya fita bai kula Didi ba.

Ya jima bai dawo ba, sai goma na dare sannan ya dawo ya ce Didi ta wuce gida zai kwana da ita. Didi suka wuce da mijinta bayan ya saka Bashir ya yi musu rakiya, dan a yanayin da ake ciki komai zai iya faruwa.

A haka suka zauna shi da ita, sai cikin dare ta farka suka haWa ido taga irin kallon da yake mata sai ta Wauke kai dan ita wallahi tsoronsa take ji ba kaWan ba. Sauka tayi daga kan gadon ta shiga banWaki. Alwala tayi tana so tayi sallah amma babu mayafi, shi kuma babu fuskar da zata yi masa magana. Ganin haka sai ya fita dan ya je gidan Didi tunda babu nisa, yana fita suka haWu da mijin Didi ya kawo masa abinci da kuma kaya a leda. Komawa ya yi ya ajjiye mata bai ce mata komai ba. A tsorace ta Wauka ta saka hijjabin tayi sallah.

Wayarsa ya mi™a mata ta kalle shi suka haWa ido, ya Waure fuska ya ce, "ki yi blocking bank account Winki." A sanyaye ta karSa da hannunta da babu ciwo ta yi ta ajjiye masa wayar. Bai sake ce mata komai ba sai abinci da ya nuna mata. A yanayin da yake ciki babu damar yi masa musu, dole ta Wauka taci kaWan ta ajjiye. A haka suka kwana shi da ita, washe gari ba a sallame su da wuri saboda zazzaSin da ya rufe ta, sai gab da magrib suka wuce gida bayan an bata magani.

Tana zaune a falo tana kallon hannunta, abinda ya faru ya dinga dawo mata cikin kanta tsoro ya sake mamaye mata zuciya. Jin ta take yi kamar ba ita ba, ji take kamar ta gudu Kaduna ta huta da tashin hankali. GabaWaya zaman Kano ya fita daga ranta, zama da Omar ya fita daga zuciyarta gida take so ta koma ko hankalinta zai kwanta.

Omar ne ya shigo da sallama, ta amsa a ciki tana Wago kanta. Kallo Waya tayi masa gabanta ya faWi, abinda ya faru a daren shekaran jiya ya faWo mata a rai musamman yadda yanayinsa ya canja mata ya koma mata na wancan Omar Win da ta sani.

   A hankali ya tako ya zo inda take, ya bita da kallo cike sa tausayi ganin yadda ta rame lokaci Waya, duk ta firgice kamar ba ita ba. Ya Wauke kai daga kallon ta, ya daure ya kawar da tausayin ya ce, "Dan baki da hankali, baki da tunani zaki fita ki bar gidan nan ba tare da na sani ba? Ba sai da na ce miki kar ki je ko ina ba?." Nayla bata san ta mi™e tsaye ba, jikinta ya cigaba da rawa tana jan numfashi da™yar ta ce, "tsoron gidan nake....." wata irin zabura ya yi ya Waga hannu kamar zai mare ta ya ce, "wallahi Allah ki ka ™arasa sai na mare ki!." Šuf tayi, numfashinta yana neman Waukewa tana kallonsa a tsorace.
ÿþ

"Uban meye a gidan da zai baki tsoro? Dah ba a cikin sa ki ke zama ba?. Dan kin raina min hankali sai ki Wauki ™afa ki bar gidan nan ba tare da na sani ba, a irin wannan yanayin da ake ciki da an kashe ki fa!?. Kalli ciwon da aka ji miki, da sun same ki a inda zasu kashe ki fa!?" Ya faWa cikin faWa yana nuna mata ciwon hannunta. Tsoronsa ne yake tsirga mata, jinin shekaran jiya kawai take gani a jikinsa, ga wanda ya nuna mata wu™a ya ™wace mata waya, ga wanda ya sare

Please Login or Register in order to submit comment