Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi min, ni kuma na yi miki al™awarin bazan ci amanarki ba har abada!. Ni naki ne ke tawa ce, dan ni aka yi ki dan ke aka yi ni. Wata tarkacen ´ar Sen da ma ko wacce mace bata kai Omar ya kalle ta ba, har yanzu sunan yana nan....Tiger! Har gobe sunana ne. A wajan ki kaWai na canja, amma ga kowa haka nake. Ke kaWai ki ke ganin fara'ata ko a yaushe, shiyasa ki ke tunanin zan yiwa matan kan titi, ki tuna damisar da ki ka sani a baya har gobe ita ce!."

Rungume shi tayi da sauri ya yi ajiyar zuciya yana shafa bayanta ya ce, "kin azabtar dani, rabon da na ji ki haka tun a Abuja, don Allah ki daina haWe min rai Ashiq, kina sakawa ina fita daga hankalina." Nayla ta ce, "ina sonka Rouhii, ina kishinka sosai."
"Son da ki ke yi min wasan yara ne akan wanda nake miki. Ina sonki, Allah shaida ne, ina kishinki wanda ban san iyakacinsa ba."

Nayla ta ce, "Alfarmar wannan gari mai albarka, alfarmar wanda yake kwance a cikinsa baza ka yi min kishiya ba, Allah yasa ka cigaba da sona har a aljanna, Allah ya sa baza ka taSa jin sha'awar wata mace ba sai ni kaWai." Murmushi ya yi mai sauti ya ce, "Amin Jidda, Allah ya amsa addu'arki."

"Amin Rouhii."
Ta yi luf a jikinsa, shima bai ce komai ba idonsa a lumshe kafin ya ce, "Ina kewarki sosai Ashiq, aljanun da suke kawo mana ziyara ma suna kewa Jidda." Ta Wago ta kalle shi taga ya marairaice fuska ta ce, "Didi tana nan."

Ya Wan wara ido ya ce, "sai me? Ta san tunda muka zo tare ai dole sai tana rufe idonta." Murmushi ta yi tana kai masa duka a ™ijinsa ta ce, "baka da kunya ne kawai."
"Ke kina da ita ai." Cikinta yake shafawa a hankali ta ce, "na siyo abinci fa, gashi nan."

Bai magana ba sai matso da fuskarsa da yayi kusa da tata, yana kallon idon ta har lokacin yana shafa cikinta ya ce, "kin san in ka aikata aikin lada a ™asar nan Allah ninka maka ladan yake yi ko? To ki yi aikin lada Jidda!." Nayla ta Wan juya kai ta ce, "Rouhii Didi fa tana tare damu, kuma lokacin sallah ya kusa."
"Ashiq abinda nake so kenan, baza ki yi min ba?."
"Ina so Rouhii, amma....."
"Shiiii! Ki yi shiru." Shirun ta yi tana ji ya fara yamutsa ta ya fara kissing Winta a haukace.

Kukan Marmerh suka ji, Nayla tayi saurin yin baya sai ga Didi ta buWe ™ofar ta fito daga Wakin. Nayla ta yi wiki-wiki kamar munafuka shi kansa jikinsa ya saki ya lumshe ido yana sauke numfashi, bai kalli Didi ba ya rufe ido yana shafa kansa a hankali.

Didi ta ™araso tana kallon su, ganin yanyinsu sai ta ji wani iri, duk da bata gansu a tare manne da juna ba amma sai ta ga kamar akwai wani abun da ya saka suka yi mata shiru. Nayla saboda ta katse shirun sai ta ce, "Didi kin sha bacci, ga abinci ki ci an kusa sallar azahar."

Didi ta ce, "Bacci nayi cike da mafarki Nayla, ki sake yi min godiya a wajan mijinki." Nayla ta yi murmushi Marmerh tana mi™awa Omar hannu tana kiran Daddy kamar yadda Didi ta koyar da ita ce masa Daddy. Jin muryar abar ™aunarsa ya saka ya buWe ido, ya kalle ta ya yi murmushin ™arfin hali ya mi™a mata hannu Didi ta bashi ita, Nayla ta ce, "Bara na kawo mana yaji, wannan shinkafar ta su babu maggi" ta faWa tana tashi ta shiga ciki ba jimawa ta dawo.

Tana zama Didi ta ce, "Nayla me yake damun Omar ne? Naga ya canja." Nayla ta kalli Omar da ya kallon ta, ta kalli Didi ta ce, "Didi kin fa san halin kayan ki, babu abinda yake damun shi." Murmushi tayi kawai bata ce komai ba.

Abinci suka fara ci ita da Didi kafin ya ce, "Mun yi waya da mijinki, na faWa masa inda mu ke ya ce da ´ar tazara da inda yake amma zai zo." Didi ta yi murmushi ta ce, "ka ce ku ne ki ka tsara tafiyar nan a haka?." Omar ya ce, "Jidda ce." Murmushi Didi ta yi, Nayla ta kalle shi ta ce, "baza ka ci abincin ba?."

Ya bita da mayen kallo ya ce, "Kin bani ne?." Nayla ta ce, "baka ce ba ai." Mi™a masa ta yi ya karSa yana binta da ido, ta kawar da kai kamar bata gani ba ta koma suna cin abinci da Didi tana bata labarin yadda aka tsara tafiyar. A tare suka gama ya kalli Nayla ya ce, "Wauko min abinda na baki."

Ba musu ta tashi ta kawo masa, kuWi ne na ™asar da suka canja tun a nigeria, ya bawa Didi ya ce, "Didi duk abinda zaki siya ki yi amfani dashi." Bata karSa ba ya Wora mata a kan ciyarta ya sake bata wani ya ce, "ga na marmerh, in kuma ki ka ci kuWinta Allah yana kallonki." Sai ya bata dariya ta ce, "Omar..!." Ya katse ta a kausashe ya ce, "Didi, ni na gaji da kiran sunan nan nawa da ki ke yi, ko yaushe ki ce Omar kamar ke kika raWa min sunan?." Murmushi ta yi dan ta kasa magana.

A tare suka fita zuwa masallaci don yin sallar azahar, bayan sun idar suka dawo AbdilHamid ya zo suka dinga hira duk da rabi godiya take sakawa ya yiwa Omar. Omar ya ce, "To ka dawo nan da zama mana, akwai Waki ai sai ku zauna tare."

"Ai na riga da na biya Omar, kar ka damu."
"Har na makka?."
"Har shi Omar."
"To ai shikenan." Omar ya faWa dan shi gaskiya yana so ya dawo Win ko dan ya dauke hankalin Didi shi kuma ya samu sakewa da matarsa yadda yake so

Nayla ce tayi musu booking shiga ziyara suka samu permit na shiga bayan sallar i'sha. Anan suke zaune har suka je la'asar suka dawo, da suka je sallar magriba ne Nayla ta ce baza su dawo ba sai sun fito daga ziyara. Didi sabon kuka ta fara Nayla na rarrashi a haka suka kammala suka dawo gida. Nayla ta so su fita yawo amma ya ™i ya ce ta gaji.

˜iri-™iri ya hanata kwana a wajan Didi. ya tasa ta a gaba har Waki, ita kuma kunyar Didi take ji amma ya shafawa idanunsa toka ya ce sam bai san kunya ba. Haka ta dinga zuba masa shagwaSa tana sake haukata shi, basu fito ba sai cikin dare suka yi alwala gabaWayan su suka tafi masallaci.

Washe gari ma haka ne ya faru, da safe sun je ziyarar masijib ™uba, Uhud da sauran wajan ziyara. Da daddare Nayla ta ja Didi yawo suka tafi kasuwa. Ta dinga kai ta waje kala-kala basu dawo ba sai cikin dare sosai.KRB3P094
Nana haleema

Narma tunda ta ga Omar ta tabbatar shine ta sake birkicewa, tafiyar da zasu yi ba kenan sai missing flight suka yi saboda zazzaSin da ya rufeta ruf dole suka dangana ga asibiti. Ruwan da aka saka mata ya sakata bacci, Mum da Dad suna tsaye a kanta suna kallonta sai da ta samu bacci sannan suka fito zuwa wajen Wakin.

Mum ta kalli Dad ta ce, "Haka zamu cigaba da barin Narma cikin wannan yanayi?." Dad ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Lamarinta ya dame ni sosai, da gaske take son shi ba wasa take yi ba." Mum ta ce, "kuma da gaske shine C.E.O Win company nan wai?." Dad ya Waga kai ya ce, "Shine."
"To daman ™arya yake yi a lokacin nan ba Wan daba bane?."
"Ba ™arya yake ba, shine."
"To ta ya zai samu wannan cigaban cikin sau™i haka? Ba shi da ilimin komai fa, taya ya kai wannan matakin a rayuwar shi?."

Dad ya ce, "Ban sani, amma abin ya bani mamaki. Wai Tiger da na sani wanda ko karatun secondary school bai gama ba shine ya kai wannan matakin, shine da wannan matsayin da ni da nake da matakin phd ban kai matsayin ba. He speak an English also, ta ya ya samu wannan cigaban within two years?." Mum ta ce, "to daman ™arya yake maka ya kai matakin da ya kai tun a baya, shiyasa yake dabancin mai tsari. Ni tsoro ma nake yi anya ba Dss ba ne?."

Dad ya kalli Mum ya ce, "ki yarda shine Tiger, a baya bashi da wani ilimi ko wani mataki na rayuwa. Ki dawo hankalinki mana."
"Dole na fita a hankalina, kana magana akan wanda China tayi signing contract da shi fa, kuma yanzu ana zancen shine Tiger wanda ya yiwa Narma asiri, ai dole na ruWe." Dad ya kalle ta ya ce, "Wallahi shine, shine wancan shine wannan."

Mum ta ce, "yanzu meye abin yi?."
"Daman can bashi da tsoro kuma baya tsoron magana, ya kalle ni ya ce shine zai bani appointment ba ni ne zan bashi ba."
"To ai ya kamata a san abinda za a yi kafin Narma ta rasa ranta." Dad ya kalle ta a nutse ya ce, "Kin amince ya aure ta kenan?."

Mum ta ce, "indai zai aure ta Win na amince mana."
"Rayuwarsa ta baya fa? Kar ki manta komai yana nan a rubuce."
"Waye zai tuna wani previous abu? ai present ake kallo yanzu a manta da wanda ya wuce. Ka same shi ku yi magana, na san bazai ™i mace kamar Narma ba."

Dad ya yi murmushi ya ce, "baki kula da matarsa ba ne shiyasa, bana tunanin akwai abinda Narma zata nuna mata." Mum da mamaki ta ce, "har aure ma ya yi kenan?." Dad ya Waga mata kai bai yi magana ba Mum ta dafe kai ta ce, "koma dai meye Narma itace first love Win shi, na tabbatar zai sonta, zai so ya rayu da ita matsayin second wife Win shi."
"Oh kin amince ta je a second wife?."
"I have no choice my dear." Ajiyar zuciya Dad ya yi yana tunanin wannan abu mai Waure kai, Anya Omar zai amince bayan abinda ya faru?.

" " " " " " " " " "

       Mutanen Madina ibada kawai suke yi hankali kwance, su je masallaci su yi ibada sannan su je yawo bisa jagorancin Nayla ko gajiya bata yi indai a fagen yawo ne. Didi addu'arta bata wuce Allah ya ji™an iyayensu, ya sake Waukaka Omar, ya sa Omar ya manta da abinda ya faru ya rungumi danginsa.

Didi ta fahimci kamar tana takurawa Omar baya sakewa da matarsa in tana nan, sai ta tsiri zaman masallaci, in suka idar da sallar asuba zata cewa Nayla cikin masallaci zata shiga bazata koma ba, ko ta ce AbdulHamid ne zai zo ta kuma hana Nayla tafiya da Marmerh.

      Nayla haka zata koma ita kaWai, daman ta fi samu sa a hotel a zaune dan shi bai ma cika zuwa yawon da take kai Didi ba. Da sallama ta shiga ta ™arasa cikin Wakin ta same shi a zaune yana magana da Bashir a waya ta cire hijjabi ta shiga banWaki. Bata jima ba ta fito ta samu har lokacin waya yake yi, ta buWe kayanta ta Wauki ™aramar riga ta cire ta jikinta ta saka.

Tana juyowa suka haWa ido ya gama wayar ta ce, "kwana biyu ban san me Didi take yi a masallaci ba, sai ta je na dawo ita ba yanzu zata dawo ba ciki zata shiga, kuma ta hanani tahowa da Marmerh." Murmushi ya yi ya taso zuwa inda take tana kallon madubi ya tsaya a bayanta ya Wora kansa a kafaWarta yana shafa cikinta a hankali ya ce, "ta fahimci bana sakewa da ke in tana wajan, kema bakya sakewa in tana nan shiyasa take bamu waje." Duk da tana kallonsa ta madubi amma sai da ta juyo ta ce, "Da gaske?."


Ya Waga mata gira ya ce, "Da gaske."
"Kai YaMar! wai kana nufin ta fahimci ™uncin da ka ke yi?." Ya yi murmushi ya ce, "eh mana. Itama ai mijinta na zuwa wajanta in muka fita." Ta madubin ta kalle shi ta ce, "Kai YaMar."
"˜arya na yi?."
"A'a ban ce ba, amma ka dinga jin tsoron Allah."

Dariya suka yi shi da ita, ya zagayo da hannayensa cikin ta yana kallon fuskarta itama tana kallo ya ce, "inda ace hotel Win da mijinta yake shi kaWai ne a Wakin da yake da sai ya Wauke Didi su je can su ™arata, to ba shi kaWai bane suna da yawa. Kuma in ki ka bincika Allah bata masallacin yanzu."

Nayla ta ce, "To tana ina?."
"Wajan mijinta mana, ba kece mai jin kunyarta ki ™i sakewa da mijinki ba...? Ni dan ta ni ba kunyarta nake ji kece dai ki ke kwafsawa." Fuskarsa ta ri™e ta ce, "ni kam ina jin kunyarta sosai." Ya taSe baki ya ce, "Kin manta Didi ce fa? Itace wacce ta farfaWo dake daga dogowar suman da ki ka a daren farkon ki da mijinki." Kallon sa ta yi ta madubi ya kashe mata ido sai ta rufe ido tana dariya.

"Kunyar ta zo kenan?" ya faWa yana kallon ta da murmushi. Nayla ta ce, "Kaine ka bani kunya, wai doguwar suma."
"Eh mana, ba doguwar suman ki ka yi ba?."
"hmmm a dai yi shiru kawai" ta faWa tana murmushi. Ya ce, "ki ka saka hankalina ya tashi na dinga tunanin na kashe ´ar mutane." Nayla da shagwaSa ta ce, "Rouhi.... na ce a dai yi shiru." Yayi dariya ya ce, "an yi."
"Allah ya shiryaka."
"Ya shirya mu dai Jidda, in na shiryu baki shiru ba ai shiryuwa."

Ta ce, "Ka san me? Wai Twiny ce ta ce zata so ta ga abinda zan haifa wai wanne irin kyau zai yi."
"Nima dai ina wannan tunanin shiyasa na ™agu naga kin haihu, duk da dai na fiki kyau amma zan taimaka ta Wan yi kyaun ki kaWan, amma dai na fiki." Nayla ta san tsokanarta yake yi sai ta ce, "to daman ni na isa na ce na fika...? kalle ka fa." Ya Wan murmusa ya ce, "yau kin yarda kenan?."
"Na fahimci musun ka ke so shiyasa na yi maganar." Ya yi ´ar dariya kafin ya ce komai ta ce, "ni bacci zan yi."
"Nima haka." Tare suka kwanta suka yi bacci kafin sallar azahar.

       Haka suka cigaba da rayuwa a Madina bayan kwana goma suka tafi makka suka yi umrah suka cigaba da ibada kamar ko yaushe. Satin su uku da tafiya suka dawo zuwa Nigeria cikin kewar saudia. Mijin Didi ya riga su dawowa da kwana biyu, hakan ya saka shima ya zo Waukar matarsa a airport suka tafi shi kuma suka tafi da Bashir zuwa gida.

       Bayan sun huta da kwana biyu kamar ba tare suka je da Marmerh ba saboda tsarabar da ya yi mata kuma a ranar ne ya kaiwa Didi motar da ya siya mata. Nayla ce ta shiga motar Didin ta™ua, shi kuma ya shiga motarsa suka tafi can. Har lokacin Didi rabon tsaraba take yi, ´a´an mijinta sun sha kaya kamar babarsu ce ta je hakan ya farantawa AbdulHamid rai sosai.

Sun yi mamakin ganin Nayla da Omar, duk da sun saba zuwan dare amma bata Wauka zasu fito ba tunda basu jima da dawowa ba. Nayla ta kalli Didi tun kafin su zauna ta ce, "Didi zo mu je ki ga wani abu." Didi ta ce, "meye?." Nayla ta ce, "Zo mu je dai." Tare suka fito har wajan motar Didi bata gane komai ba, Nayla ta ce, "Wannan motar."

Didi ta ce, "Omar ne ya kuma siya ko ke ya siyawa?." Nayla ta yi dariya ta ce, "A'a, ke ya siyawa" ta faWa tana bata key Win motar. Didi ta kalle ta ta ce, "Nayla kar ku sake ruWa min tunani na kuma suma." Nayla ta ce, "Wallahi da gaske nake Didi, motarki ce, ke ya siyawa." AbdulHamid ne ya ™araso wajan yana faWin, "Kai kai kai! Ma sha Allah, amma mun gode. Wannan tsadaddiyar mota haka? Lallai Aisha kin zama ´ar gata."

Didi ta kalli Omar da yake ta wasa da Marmerh yana Sare mata chocolate Win da ya yi dakon ta saboda ita, kamar bai san me yake faruwa ba. Didi ta ce, "Omar!." Ya kalle ta ya ce, "Didi." Zata fara kuka ya ce, "Allah in ki ka yi kuka bazan shiga gidan ba tafiyata zan yi, ke komai aka yi miki sai kin yi kuka? Na san ai kin ji daWi kuma kin gode, daman na yi dan ki ji daWin ne to meye na kukan?. Bana son kukan nan tun ba yau ba kin sani, amma sai ki dinga yi kuma in nayi magana ki ce na farin ciki ne, Bana son na farin ciki shima!" Ya faWa a fusace cikin masifa dan in ya ™yaleta kukan zata yi.

Jin abinda ya ce sai ta yi shiru tana share hawaye ta ce, "To mu koma gidan." Tare suka koma bayan ya Wauko kayan Marmerh ya ajjiye mata ya ce, "ga tsabar Marmerh." Didi ta yi tagumi ta rasa me zata ce masa sai AbdulHamid ne yake ta godiya yana addu'a kamar shi aka bawa kyautar, Didi kam ta zama kurma sai bin sa take yi da idanu.

Ta buWe baki zata yi magana ya ce, "kar ki ce min kin gode Didi, ki yi addu'a a zuciyarki kawai bana son godiyar. In kuma ki ka yi wallahi zamu yi faWa, zan daina kula ki gabaWaya sai ranar da na ga dama." Didi ta yi dariya ganin ya koma mata Omar Winta na baya, ta share hawayenta ta ce, "ko lokacin da ka ke jan wuya ai baka iya fushi da ni balle yanzu." Ya buWe idonu ya ce, "Har yanzu Jan wuyan ne ai, in kina musu ki gwada ki gani." Dariya ta yi sosai tana kallonsa.

Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Omar ka cika min burina na duniya, duk abinda nake buri a duniya ka yi min Omar, abu Waya ya rage min a yanzu....." Ya kalle ta a nutse bayan ya sassauta murya ya ce, "Didi faWi abinda ki ke so, ki faWa don Allah, ko meye zan cika miki shi in sha Allah."

Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "ala™arka nake so ka gyara da ´an uwan mu Omar, wallahi shine kaWai abinda yake damuna a zuciyata. Fargaba nake yi kar na bar duniya ba tare da ka daidaita da ahlinmu ba, na san in na mutu babu wanda zai saka ka ka yi kamar yadda ka ke yin abinda na ce" ta ri™e hannunsa ta ce, "Don girman Allah ka bar wannan tunanin ya wuce Omar, ka yafe musu ka karSesu matsayin iyayenka. Baka da wasu a duniya sai su Win, su ne ahlin ka, sune danginka gaba da baya. Yayyen mahaifiyarmu da ™annenta inda kana mu'amala dasu zaka dinga ji kamar da mahaifiyar ka ke rayuwa. Maganarsu, kamanninsu duk iri Waya ne tunda jininta ne. Ina jin sau™in kewar mahaifiyarmu a duk lokacin da nake tare dasu, suna bani farin cikin da muka rasa a wancan lokacin."

Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba yana kallonta ta kuma cewa, "Allah ya azurta ka cikin ™aramin lokaci, ya baka Waukakar da mutane dubu basu samu ba. Kana da mota ta kanka, kana gina gidan kanka, kana da ma'aikata sama da hamsin a ™ar™ashinka, kana da mace ta gari harda arzu™in Wan da yake cikinta, to Omar me ka ke nema kuma a rayuwar nan?. Omar in ma da gaske so ake aga ka wula™anta yanzu a wanne mataki rayuwarka take? In so ake aga rayuwarka ta lalace a wanne mataki rayuwarka take Omar?. Balle mutanen nan duk sun yi nadama tun ba yau ba, suna so su jaka a jikisu su nuna maka soyayyar da ka rasa amma ka ™i bada dama. Kar ka zama mai butulci ga ni'imar da Allah ya yi maka Omar, ka zama mai rama sharri da alkhairi. Don Allah ka bar maganar nan ta wuce, ka je gidan ko wannen su ka gaishe shi, duk abinda ya taso ka dinga saka su a cikin lamarinka" Didi tayi shiru tana kallonsa gabanta yana faWuwa.KRBP095
Nana haleema.

Shiru ya yi bai ce komai ba, ya zuba mata ido kafin ya janye idanunsa daga kallonta ya cire hannunsa daga ri™on da ta yi masa. Ya haWe fuska ya ce, "Zan yi tunani." Didi ta yi murmushi ta ce, "to Omar ka yi tunanin da kyau, da ni da kai bamu da tabbacin zamu kai gobe da rai, kafin mu bar duniya ka gyara zumunci nan don Allah, kar ka zama mai yanke zumunci."

"Na ce ai zan yi tunani, ki bar maganar mana" ya faWa ba tare da ya kalle ta ba. Murmushi ta yi Wan ko babu komai an samu cigaba a lamarinsa, tunda gashi bai tashi ya fita ba kuma bai fara yi mata masifa ba.

Ta ce, "an gama gini ko Omar?." Ya Waga kai ya ce, "Eh, kaya ake zubawa."
"Allah yasa a shiga a sa'a."
"Amin." Ta kalli Nayla ta ce, "zuwa yaushe zaku tare?." Nayla ta ce, "zai yi tafiya zuwa Italy next week sai ya dawo."

"Allah ya kaimu, ni na Wauka ma sai kin haihu, ashe a sabon gida zaki haihu. Kai komai inda kuWi ba a Waukar lokaci, gabaWaya ginin gidan nan wata nawa aka Wauka har an gama." Nayla ta ce, "Wallahi nima naga gudun abun sosai Didi." Omar ya kalli Didi ya ce, "yaushe zaki je ki gani?.."
ÿþ
"Ai na je Omar."
"Ki koma." Ta ce, "to zan koma in sha Allah." Omar ya kalli Nayla ya ce, "mu tafi." Tare suka fito gabaWaya motar tana nan inda aka ajjiye suka shiga ta sa motar suka tafi aka bar ya Didin a wajan.

      Radio ce take ta aiki a motar ana wa'azi gabaWaya abinda ake faWa kamar da Omar ake, ta ga ya nutsu sosai yana ji duk da tu™i ya ke yi kuma ba gida zasu tafi ba sabon gida zasu je daga nan zasu wuce gida. Nayla ta ce, "Rouhi inda ace zaka gyara ala™ar nan kamar yadda Didi ta ce da yanzu ka wuce a matsayin da ka ke kai a yanzu, zumunci babban Sangare ne a duniya." Shiru bai amsa mata ba ya cigaba da tafiya.

       Omar ya tafi Italy ita kuma ta tafi Kaduna, sati biyu yayi ya dawo itama a can ta gama kwanakin sai da zai dawo ta dawo gidan. Abubuwa suna ta gaba cigaba na sake wadata da arzu™i suna ta ™ara yawa ga Omar.  A cikin wannan kwanakin suka tafi Maldives kamar yadda ya yi alqawari, tafiya ta yi musu daWi amma ba can ba, saboda cikin Nayla ya girma sun je ne dan ya cika mata alqawari amma ya yi al™awarin zasu dawo in ta haihu.

Dawowarsu aka fara shirye shiryen komawa sabon gida, an gama komai an kuma zuba komai babu abinda aka Wauka a gidan da suke ciki, duk da kayan babu abinda suka yi amma ya ce shi baya da bu™ata, komai sabo yake so ya zuba. Nayla da sabuwar mai aikin da aka bata zasu tafi sabon gidan suna ta haWa kayanta da za a kai can. jin motsinsa sai ta fito zuwa Wakinsa. Tana shiga  ta ce, "Rouhi yanzu duk wannan kayan a nan za a bar su? Yanzu ina zan kai?."

Ya kalle ta ya ce, "na ki ne ai ko? Ki siyar ko ki bayar duk zaSinki ne, ™ananun abubuwa su na amince ki Wauka, kamar frames da kayan kitchen." Nayla ta ce, "meyasa to?." Ya kalle ta ya ce, "ni tun farko ra'ayina kenan, in zan yi aure babu abinda matata za a kawo daga gidansu komai ni zan yi. Kuma yanzu Allah ya bani iko, sai ki bayar da na ki." Murmushi ta yi ta ce, "Rouhii komai na ka daban yake da na mutane, komai naka tsarinsa daban."

Kallon ta ya yi ya Wauke kai bai ce komai ba ta ce, "yau jan ajin ake ji dashi kenan ko? Shikenan na gode." Murmushi ya yi ya ri™o hannunta ya yi mata kiss a goshi, ya

Please Login or Register in order to submit comment