Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya yi kuskure ne kenan. Didi ta ce,  Hajja tare zamu wuce da ita ai, shi wannan ma aiki suke yi na haWa takalman sallah.
Hajja ta ce,  Allah ya taimaka Omar, Takalma suna kyau sosai.
 Amin ya amsa a ta™aice tare da cewa,  Sai an jima ya faWa yana fita da sauri.

Hajja ta girgiza kai ta ce,  Omar kenan. Nayla dai tunda ya shigo bata motsa ba, mamaki ma take yi da ya iya shigowa bata Wauka zai zo ba duk da ta san Didi ce ta saka ta. Kamar ruwa ya tsince ta haka ta yi tsif ko motsin kirki bata yi, duk abinda ya ce tana ji har ya fita.

Diid ta ce,  To Hajja Allah ya kiyaye ya sauke ku lafita ya karSi ibada, ayi mana addu a. Hajja ta ce,  Amin Aisha. In sha Allah za a yi addu a bakin gwargwado. Didi ta mi™e ta ce,  mu zamu wuce. Nayla ma sai ta mi™e ta ce,  Hajja Allah ya kiyaye hanya, ayi mana addu a Hajja.
 In sha Allah za a yi Hauwa, Allah ya baku zaman lafiya da wannan Damisar mijin naki, ya sauke masa wannan abinda yake ji a kansa. Mutum kamar aljani. Dariya Nayla tayi suka fita ita da Didi har Salna da ta raka su gate ta dawo.

Da yake Didi ta cewa AbdulHamid tana gidan Omar yana ™ofar gidan da mota yana jiranta. Da ™afa suke takawa ita da Nayla suna hira. Didi ta kalli gidan su bayan sun fito ta ce,  Nayla Omar ko abinci ba ya ci a gidan ko?.

Nayla ta kalli Didi ta ce,  Didi ni abincin ma nake so a rage ya yi yawa kar ya lalace, ni kaWai ce ba wani abun kirki nake ci ba. Don Allah ki aiko a rage wani abun kar azo ayi asara, ko iya lemo yana nan a jibge ko cartoon ban sha ba har yanzu. Didi jin ta canja maganar sai ta yi murmushi ta ce,  Ai Nayla abincin ki ne ta ya za a rage?.

 To Didi sun yi yawa sosai, ni ko shinkafa ban buSe ba kuma tana nan tafi guda biyar fa. Na dai buWe basmati amma babban buhu ban buWe ba. Don Allah a rage wani abun kar azo ana asara, gwara a rage a bawa masu so. Didi ta ce,  gashi ke kaWai ke ci ko?. Nayla ta ce,  eh wallahi, Ni kaWai ce taya zan iya da abincin nan?. Didi jin amsar da take so ta samu sai ta ce,  Omar baya ci kenan, Allah ya shirya min Omar shirin addini. Nayla ta amsa da amin a zuciyarta.

Didi ta kalle ta suna gab da gidan ta ce,  Nayla na san halin Omar, ki cigaba da ha™uri komai zai zama labari. Wallahi ni kunyar ki ma nake ji. Nayla ta ce,  Babu komai fa Didi, kowa da ™addarar da Allah ya rubuto masa. Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce,  haka ne, Allah ya kawo mana mafita. Ta amsa da amin a lokacin suka zo ™ofar gidan. Nayla ta ™arasa ta gaisar da mijin Didi sannan suka yi sallama Nayla ta shiga gidan ita kuma ta hau mota suka tafi.KRB3P009
Arewabook@nanahaleema.

Washe gari har ta shirya da safe ta fito harabar gidan bata ji motsin sa ba, ban da Allah ya sa ma taji motsi da asuba baza ta san a gidan ya kwana ba. To ta ji an buWe gate har take mamakin daman yana zuwa masallaci ko yanzu ya fara.

Harabar gidan ta ke a tsaye tana kallon motar tana tunanin ta yadda zata fita da ita da baya, ita ta saba da babban gida wanda zata juya mota kawai ta fita ta gaba ba ta baya ba. BuWe gaban motar tayi ta saka laptop ta buWe mazaunin driver ta shiga. Dafe kai tayi tunawa fa ita zata buWe gaye Win, tayi tsaki ta fito ta buWe gate Win sannan ta shiga motar tana fitowa da baya a hankali.

Kasancewar safiya ce babu jama'a sosai kuma babu abin hawa shiyasa ta fito da motar, ba dan haka ba tsaf sai ta bugawa wani motar. Zata fito ta rufe gate Win ta ga Bashir shine ya kulle gate Win ta kalle shi tana cewa, "Sannu, na gode."
"ina kwana Antyn mu." Murmushi ta yi ta ce, "Ka tashi lafiya? Ya ibada?."
"Lafiya lau." Key ta sakawa gate Win sannan ta shiga shiga mota ta bar unguwar.

Wajan aikin ta je tayi duka abinda ya kamata ta yi kafin ta fara aiki a wajan. Sai la'asar suka tashi tana tashi kuma ta Wauki hanyar Arewa24 a address Win da taji an ce suna wajan. Bayan ta je ta faWi abinda ya kawo ta sun yi mata bayanin yadda abin yaketa karSi number su sannan ta nufo gida a matu™ar gajiye ga azumi.

Tana zuwa ™ofar gidan ta hango Omar shida Bashir da kuma Tk suna tsaye da alama magana suke yi. Motar ta faka a wajan ta fito daga motar tana ji kamar zata fika ™asa saboda gajiya da nauyin da kanta ya yi mata. Bashir ya ce, "Antyn mu barka da zuwa." A gajiye ta ce, "yauwa Bashir, na gode." Tk ma ya yi mata sannu da zuwa ta amsa ta buWe ™ofar ta shiga gidan ta buWe gate Win ta cikin gidan ta shiga da motar. Bashir ya ce, "Antyn mu ki huta, bara na shigo miki da motar." Nayla ta bashi key Winta ce, "ai kam na gode sosai." Daga haka ta rufe ™ofar dan ta gaji sosai.

Shigar mata da motar ya yi ya tarar da ita a tsaye daga can gefe ya bata key Win tayi godiya ta ™araso ta buWe gaban motar ta Wauki jakarta da wayarta da laptop ta kalle shi yana niyar fita ta ce, "Bashir yaushe ku ke available gidan tv zasu zo Waukar video na wajan na ku, na gama magana dasu gabaWaya."

Bashir ya ce, "Ai ko yaushe ma muna nan, amma ki ce musu gobe su zo."
"Ka tabbatar gobe kuna nan?."
"Na tabbata Antyn mu."
"Shikenan zasu zo gobe in sha Allah" ta faWa tana shiga ciki shi kuma ya fita.

Nayla wanka tayi ta canja kaya ta zauna tana sauke numfashi saboda ta gaji sosai. Kanta har sarawa yake yi saboda ciwon da yake yi mata. da™yar ta iya samu ta mi™e ta dafa tea ta ji tana son cin bread amma kuma babu, gashi bata da Wan aike balle tayi aike a siyo. Tsaki tayi a bayyane ta ce, "ko meyesa ban taho dashi ba yanzu oho min."

Ha™ura tayi ta soya doya da ™wai ta dawo falo ta zauna lokacin shan ruwa ya kusa. Da™yar ta iya addu'ar gab da shan ruwa saboda ciwon kai, ana shan ruwan ta sha ruwa ta yi sallah ta zauna tana shan tea a hankali duk da kanta da yake ciwo.  Motsi ta ji bata motsa ba dan ta san shine kaWai yake shigowa ba tare da an buga gate ba, ta tabbatar da key Win gidan ya cire yake amfani dashi wajan fita da dawowa.

Daman ta san ba shigowa inda take yake yi ba hakan ya saka bata motsa ba tana zaune tana shan tea Win kamar an yi mata dole saboda ciwon da kan yake mata. Kamar tsayuwa taji a bayan ta hakan ya saka ta juya ta ganshi a tsaye amma kuma waya yake dubawa ba ita yake kallo ba. Fuskarsa take kallo ta ga yayi mata kyau musamman idanunsa da suke kallon waya hasken wayar ya haske idanunsa sai ya bada haske na musamman.

Šauke kai tayi zuciyarta na bata umarnin yi masa barka da shan ruwan, wani Sangare na zuciyarta na hana ta saboda abinda ya ce mata ta san kuma bazai amsa ba. Kallon ta ya yi kafin ya yi magana ta ce, "An sha ruwa lafiya?." Kamar ba zai amsa ba sai ya ce, "lafiya. Ehemm akwai wanda ki ke so?." Da mamaki ta kalle shi ta kasa bashi amsa saboda mamakin tambayarsa. Kallonta yake yi yana ganin mamaki a kwance a saman fuskarta ya wara idanunsa a kan fuskarta ya ce, "kin ji abinda nace ko?." Saurin Wauke kai tayi Allah ya sani in ya buWe ido ba ™aramin tsoro yake bata ba.

Nayla ta girgiza kai ta ce, "babu komai."
"In akwai zaki iya sanar da ni."
"Yanzu dai babu." Ya Waga kafaWa alamun ban damu ba yana niyar fita. Ta kalli abincin da yake gabanta ta ce, "Bismillah ga abinci." Kallon abinda yake gabanta ya yi ya taSe baki ya girgiza kai ya fita daga gidan. Nayla ta dafe ™irji ta ce, "wannan mutum kamar wahainiya ko yaushe canjawa yake yi, wai akwai abinda nake so ka ji fa."

Sai kuma ta yi murmushi a bayyane ta ce, "Ko babu komai ya nuna min ya san ni matarsa ce, hakan ya yi min." Da wannan murmushin ta gama ci ta sha magani aka kiran sallah ta tashi ta tayar da sallah.

Tun daga ranar magana bata sake haWa su ba dan ba bama ganinsa take yi ba, in ta fita tun safe sai yamma shi kuma baya dawowa sai dare wata™ila sai tayi bacci. Kamar yadda suka tsara da Bashir an zo an yiwa company su video ta biya kuWin tayi komai a dan a fara haskawa a arewa24.

Takalman da aka kai Kaduna gabaWaya sun ™are har an sake kai wasu saboda yadda ake rubibin su sosai. Ita kanta wanda ta saka ™afar ta a wajan aiki mutane da yawa sun siya mata da maza, har na yara an siya saboda sallah. Video ™afarta kuwa da take yiwa ko wanne sample Bashir ne yake kawo mata sample tana yi tana tana posting dan tayo log in a dukkan account Win su.

Videon yana Waukar hankalin mutane sosai, ko baza ka siyi takalmin ba in ka ganshi a ™afarta da yadda take Waukar video sai ya burge ka saboda kyaun da yake yi mata. Sun ja hankain masu siya sosai da wannan advert Win da take yi, komai yana tafiya daidai yadda Nayla take so. Cikin ™aramin lokaci suka sake wuce matsayin da suke kai saboda buWin da Allah ya kawo musu ta dalilin Nayla.

Bashir ne kawai ya san me yake faruwa sai su Tk dan tayi musu magana akan don Allah kar su faWa masa. Omar kuma da yake ba kallo yake yi bai ma san ana yin tallah a tv ba, kwana biyu dai ya san yana samun customers sosai daga inda bai yi zato ba amma bai kawo komai a zuciyarsa ba. Manyan mutane daga gari gari suna siyan takalman ana kai musu inda suke. Cikin lokaci kaWan takalmin ya yi suna a social media da kuma tallata shi da ake yi kullum a arewa24 daga ™arfe shida na yamma zuwa shida na safe.

Watan azumi ya raba har an kusa shiga goman ™arshe, Nayla da Omar basu cika haWuwa ba sai dai taji motsin sa amma magana ko ganin sa bata yi. Da yake ta saka addu'a a gaba tana kuma zuwa aiki hakan bai dame ta ba, in ta dawo suna waya da su Salma yana rage mata abinda take ji sosai.

Ranar da aka shiga goman ™arshe aka fara sallar tahajjud kamar yadda ta saba ko wanne watan azumi ™arfe uku ma dare ta ke tashi ta fara sallah har sai an yi asuba. Bayan ta yi alwala ta shinfiWa sallaya sai ta fiton dan ta Wauki ruwa. Kallon ™ofar Wakinsa tayi tana nan a kulle kamar ko yaushe, bata da tabbacin yana ciki ko baya ciki tunda ba jin motsinsa ake yi ba. Zuciyarta ke bata umarnin ta gwada ™wan™wasa masa ™ofa saboda tunasar dashi lokacin sallar tahajjud.

A bayyane ta ce, "Tsoron masifarsa nake ji."  Da™yar ta daure a hankali ta taka zuwa bakin ™ofar ta kasa kunne wai ko zata ji motsi amma shiru babu motsin kowa. Hannu ta kai da niyar ™wan™wasawa kawai aka buWe ™ofar. Baya ta yi da sauri yanayin da ta ganshi ya saka gabanta ya yi mugun faWuwa. Farar singlet ce a jikin sasai brown Win wando three quater wanda bai zo ™arasa guiwa ba, GabaWaya farin jikinsa a bayyane yake, fatarsa har Waukar ido take yi gashi ya lulluSe ko ina na jikinsa.

Ganin ta ruWe tana rawar jiki ta sunkuyar da kai ya saka yake kallon ta. Ita bata yi gaba ba kuma bata yi baya ba, ta tsaya cak kanta a ™asa kamar munafuka. Bakin ta ya fara rawa tana son yin magana tana jin tsoro, shima bai motsa ba kallonta yake yi yana mamakin dalilin zuwan ta wajan har take niyar ™wan™wasa ™ofar.

Nayla ta daure ta ce, "lokacin Tahajjud ne ya yi shine nazo na sanar da kai." Gira ya Wage guda Waya yana Wan girgiza kai ya ce, "oh haka aka ce miki bana sallah sai kin zo kin tashe ni?." Ta girgiza kai ta ce, "tunasarwace."
"Bani da bu™ata, ko kabarin mu Waya da ke?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "to ware."

"Ba a yi masa abin arzu™i, kullum zuciya a wuya kamar ba musulmi ba" ta faWa ™asa-™asa tana juyawa. "Me ki ka ce?." Da sauri ta juyo ta ce, "A'a ban ce komai ba." Bai ce komai ba ya wuce ya Wauki ruwa ya koma ya rufe Wakin. Murmushi ya yi a bayyane ya ce, "Wai kamar ba musulmi ba, yarinyar nan naci gare ta." Kallon sallayar da ya shinfiWa yake yi kana ya ce, "tunasarwa ce" ya faWa cikin kwaikwayon muryarta. Sake murmushi ya yi ya kalli jallabiyar da ta bashi tsaraba ya Wauka ya saka ya tayar da sallah yana murmushi shi kaWai.

Nayla kuwa sai mita take a zuciyarta ta kuma yi alqawarin baza ta sake tashin sa ba komai zai faru. A haka tayi sallah har aka yi asuba, bacci kaWan tayi ta tashi ta yi wanka ta shirya ta tafi wajan aiki.

Shi kuwa Omaar bai fita da wuri ba yana jin fitar ta da mota da yadda take wahalar buWe gate da rufewa, yana tsaye yana kallonta ta window da take Wakinsa yana kallon yadda take kiciniyar rufe gate Win kamar zata yi kuka. Tsaki ya yi ya ce, "shagwaSaSSiyar banza, kalli yadda take taSe fuska kamar wani ne ya sakata zuwa aikin." Tsaki ya sake yi ya bar wajan shima wanka ya yi ya shirya ya fita saboda yanzu aikin yawa yake masa. Yana fitowa falon gidan ya tarar dashi yana ta ™hamshin turaren wuta, ya girgiza kai yana kallon falon dan ya burge shi sosai a shirye tsaf dashi.

Wayarsa tayi ™ara ya Wauko daga aljihunsa yana kallon wayar, ganin ba™uwar number ce sai ya Wauka saboda kwana biyu ana yawan kiransa da sabuwar number. Bayan sun gaisa da wanda ya kira Win ya ce, "Ina magana da C.e.o Exclusive Footwear by tiger?." Omar ya girgiza kai ya ce "shine."

"Kana magana da Usman P.A na Alhaji Mubarak  C. E.O Na kowa Store. Daman akan takalman da mu ka gani muna so ne, muna so a fara kawo mana babban store Winmu da yake Abuja." Omar ya san Na kowa Store, dan a Kano ma akwai store Win, haka yawancin garuruwa akwai Na kowa store. Omar ya amsa ya ce, "babu damuwa, ya za a yi?."
"Ina so mu yi contract ne, amma don Allah kafin mu akwai store ko shop Win da suke karSa a Abuja?."

Omar ya ce, "gaskiya babu."
"Yauwa, Ina so mu zama na farko da zamu fara siyar dashi a store Win mu. Ka bani lokaci da dama ina so na zo mu tattauna."
"Zaka iya zuwa ko wanne lokaci daga yanzu."
"Shikenan, zuwa anjima zan zo in na shigo Kano zan kira ka." Omar ya amsa sannan suka yi sallama ya kashe wayar.

Wayar yake Wan bubbugawa da hannu Waya yana girgiza kai cike da mamaki, cikin kwanakin nan yana ta samu kira daga inda bai yi tunanin zai samu ba, ya rasa ta ya akayi product Win nasu yake trending yana shiga inda bai yi tunani ba. A bayyane ya ce, "ya akayi takalmani nan ya zaga ko Ina haka?." Bai tsawaita tunanin ba ya fita daga gidan.

Da yamma ya yiwa Didi waya ya ce ta bashi address Win gidan ta zai je. Abin ya bata mamaki dan bai taSa zuwa ba hakan ya yi mata daWi sosai. Ko da ya je ™ofar gidan ya sauka daga machine Win Bashir, ya kalli unguwar yana mamakin rashin mutanenta. Didi ta buWe gate Win ta ce, "Omar sannu da zuwa." Murmushi ya yi ya ce, "Haka unguwar ta ke shiru babu jama'a?."

Didi ta ce, "Shigo ciki sai mu yi magana. Bashir ka shigo kaima." Bashir ya ce, "A'a babbar Yaya, barni a nan akwai gidan ™anwata a nan da zan biya. Tiger in ka fito." Kai ya Waga masa shi kuma ya bi bayan Didi.

Gidan Didin ya burge shi ya yi kyau sosai ya zauna yana kallon falon ya ce, "Gidan ki ya yi kyau sosai, kin zama ´ar gayu." Ta zauna ta ce, "abin makamki yau sai gaka kwatsam." Ya yi murmushi kaWan ya ce, "mijin na ki baya nan?."
"Yana nan, yanzu zai fito." Tana magana sai kuwa gashi ya fito yana cewa, "Alhaji Omar, yau kai ne a gidan nan?."

Didi ta ce, "nima haka na ce, yau sai gashi kwatsam bayan dogon lokacin da ya Wauka bai zo ba." Gaisuwa suka yi da Abdulhamid, Omar ya ce, "Daman unguwar da ka kawo min Yayata kenan? Wannan unguwa babu jama'a." Murmushi ya yi ya ce, "gashi muna zaune lafiya kuma ba." Kai ya girgiza bai ce komai ba Didi ta ce, "Ya Nayla? Tana Lafiya?."
"Wace haka?" Ya faWa yana kallon ta.

Harararsa tayi sai ya yi murmushi itama ta yi ta ce, "kayi murmushi mana. Allah in ina ce maka ya Nayla kana cemin wace haka za mu yi faWa da kai." Omar ya ce, "Daman ai faWa mu ke yi da ke tunda ta shigo rayuwata, akanta har korata ki ka yi daga falo, ki ka ce min ina shirme kuma bana aiki da hankali."

Didi ta ce, "Na shiga uku ni Aisha, wai baka manta ba?." Ya kalle ta ya ce, "taS" ya furta a ta™aice yana Wan murmushi. Didi tayi dariya ta ce, "ashe-ashe itace matar ta ka. Narma ta shigo rayuwarka ne saboda ta canja ka, ita kuma ta shigo saboda ta zauna da kai."
"Hmmm" kawai ya ce ba tare da ya yi magana ba.

AbdulHamid ne ya tashi ya fita hakan ya saka Omar ya mi™a mata ledar da ya zo da ita ta karSa ta buWe. Laces ne guda uku masu shegen kyau, sai atampa guda biyu, sai mayafi guda biyu da takalmi irin wanda suke yi guda biyu, sai na AbdulHamid shima ™afa biyu. KuWi ya ajjiye mata ta a gefenta tasan na Winki yake nufi kamar yadda ya saba duk shekara.

Didi da farin ciki ta ce, "Omar wannan duk ni kaWai? Wannan kaya masu kyau da tsada Alhaji Omaar?. Kai amma na ji daWi wallahi, Allah ya ™ara buWi ya Waukaka rayuwarka." Omar ya ce, "amin." Didi ta ce, "Na gode sosai Omar, Allah ya bar zumunci ya ji™an iyayen mu."
"Amin" ya amsa a ta™aice bai sake cewa komai ba. Didi ta irga kuWin ta ce, "Omar har dubu
hamsin na Winki? Bayan wannan kaya da na san ka kashe fin dubu Wari?."

"To Didi in ban kashe miki abinda nake samu ba wa zan kashewa?." Didi ta yi murmushi tana kallonsa ta ce, "Haka ne Omar, wannan shekara tazo mana da alkhairi. Allah ya cigaba da ri™o da hannun ka a duk abinda ka saka a gaba. Lokacin da baka da sana'ar kirki ma ka ke yi min balle yanzu? Na gode Omar." A zuciya ya amsa da amin, Didi ta fuskance shi a nutse ta ce, "Amma ka siyawa matarka ko?."

Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai alamun bai yi ba kenan, Didi ta ce, "Kar ka ce min baza ka yi ba, ha™™in yi mata a kanka yake Omar. Ni yanzu ha™™in yi min Winki ba a kan ka yake ba, ha™™in yi min yana kan mijina, kyautatawa ce kawai ka yi min matsayina na ´ar uwarka. Wacce ya zama dole a kayi mata matarka ce Omar, kar ka yi la'akari da komai ka yi mata domin sauke nauyin da Allah ya Wora maka wuyan ka." Ajiyar zuciya ya yi ba tare da gardama ba ya ce, "To Didi" ya faWa yana shafa kwantaccen gashin da yake kansa. Jin ya amsa kai tsaye sai tayi murmushi ta ce, "Yauwa ko kai fa. Allah ya sake buWa maka, ya sa ka fi haka a rayuwarka."

"Amin Didi." Didi ta yi murmushi tana sake duba kayan ta ce, "Harda su Yallabai kenan? Godiya mu ke mai company Exclusive footwear." Bai ce komai ba ta sake cewa, "kai naga kun bawa Arewa24 advert ko? Ana samun mutane amma ji?."

Ya kalle ta ya ce, "su waye haka?."
"Kai fa ka cika rainin hankali, tashar arewa Win ne baka sani ba?."
"Na sani mana, na ji kin ce talla ne ai."
"Inyee ashe ka san meye advert Win" ta faWa cike da tsokana tana dariya. Tsaki ya yi ya kawar da kai ta sake yin dariyar nishaWi da farin cikin ganinsa a gidanta ta ce, "Allah da gaske nake, talla ake yi kullum ma sai anyi musamman da daddare. Tun shekaran jiya nake so na yi maka magana sai na manta."

"Tallah kuma a gidan tv!?" Ya maimaita yana kallonta. Didi ta harare shi ta ce, "ban sani ba." Ya kalle ta ya ce, "gaskiya baki gani daidai ba." Jin ya raina mata hankali sai ta share shi ta ce, "amma ana samun mutane yanzu sosai ko?."
"Sosai ma, yau ma wani yazo daga Abuja sun siya da yawa zasu saka a store, kuma sun biy  gabaWaya. Ni na yi tunanin ma sai an siyar zasu biya ni."
"Ma sha Allah, Allah ya saka taimaka maka Omar."
"Amin."
"Nima ai ana siya a wajena sosai fa Omar, musamman yanzu da sallah ta zo."
"Bash ya faWa min yana kawo miki."

Zata yi magana AbdulHamid ya shigo ta kalle shi tana cewa, "Kayan sallah Omar ya kawo min har g1da." Da murmushi ya zauna yana taya ta godiya shima aka bashi nasa ya ce, "Har da mu kenan? Na gode sosai Allah ya ™ara arzu™i." Ya amsa da amin yana kallon Agogo. Tashi tsaye ya yi ya ce, "Didi zamu wuce." Ya faWa yana kiran wayar Bash sai ya katse bayan ya Wauka.

AbdlHamid ya ce, "na Wauka yau a nan zaka sha ruwa?." Didi ta yi dariya cikin tsokana ta ce, "Ina magidanci Ina shan ruwa a wani waje?." Abdulhamid ya yi dariya ya ce, "gaskiya dai, kar amarya ta saka mu a ba™in littafi mun ri™e mata Ango." Shi dai bai ce komai ba ko murmushi baya yi.

Didi ta ce, "tsaya na baka sa™o ka kaiwa Nayla." Kafin ya tanka ta shige ciki ya fita shida mijinta yana kallon unguwar ya ce, "Gaskiya da na san haka unguwar nan take Yayata baza ta zauna ba. Ka dai dinga kular min da ita bana so komai ya same ta."

AbdulHamid ya ce, "An gama Tiger." Murmushi ya yi mai sauti jin sunan da ya kira shi dashi shima Abdulhamid Win haka. Didi ce ta fito ta bashi abu a leda ta ce, "ka kaiwa Nayla don Allah." Kallon ledar ya yi ya kalle ta ya ce, "kin san ba a bani sa™o ko?."
"Don Allah na ce ai." Bashi da zaSin da ya wuce ya karSa ya bawa Bashir da yake kan machine dan ya ri™e masa, sannan ya hau suka tafi Didi ta bishi da kallo tana murmushi.

Suna zuwa ™ofar gidan na sa ya tarar Nayla ta sauka daga motar wani, ga ta ta motar a baya wani namiji ya ajjiye ya bata key Win ita kuma tana magana da wanda ya kawo ta Win tana murmushi. Wani abu yaji yana mamaye masa zuciyarsa ba tare da ya sani ba, nan da nan ya sake tamke fuska har suka ™araso gate Win gidan inda suke

Please Login or Register in order to submit comment