Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Daddy baka sake koda nemana ba ta ya zan Wauka kalamanka na gaskiya ne?. Na kasa ha™uri, ina so na ha™ura amma zuciyata ta riga da ta....." HaWa ido suka yi sai ta kasa maganar ta Wauke kai daga kallonsa.

Shi kam Omar bai san me zai ce mata ba kuma, tunda har tana Waukar kalamansa na ™arya ne bai ga abinda zai mata wanda zata yarda ba, gwara kawai ya yi shiru kar ya furta abinda zai tarwatsa mata zuciya. Shiru ya sake ratsa tsakani kafin ya ce, "Kalaman nawa ki ke Wauka na ™arya? Kina tunanin zan zauna a gabanki na yi miki ™arya ne dan na burge ki ko dan ki dawo rayuwata?...Hmm." Nayla ta yi shiru bata ce komai ba, ta Wago ta ga ya zuba mata ido kawai yana kallon ta da alama ya rasa abinda zai ce mata.

Shi kuwa Sacin rai yake ji a zuciyarsa, na farko tana fita bai sani ba, na biyu tana kallonsa tana cewa kalamansa na ™arya ne. Ba dan soyayyarta da yake ji a zuciyarsa ba da kuWi aka ce ta faWa masa abinda ta faWa baza ta iya ba.

Ya girgiza kai ya ce, "ba a haifi wanda zan yiwa kalaman ™arya dan na burge shi ba, haka ba a haifi wanda zan bawa hakuri ba tare da na san na yi laifi Ina so na gyara ba" mi™ewa tsaye ya yi ya kalle ta ya ce, "ki yi tunani yadda ya kamata, ki yi tunani daidai da ra'ayinki da kuma abinda ki ke so. Abu Waya zan sake maimaita miki bazan rabu da ke ba, amma in ki ka yanke hukuncin ki ka ji a zuciyarki kin gama zama dani zan yi abinda ki ke so" yana gama faWa mata haka ya fita dan ransa ya Saci zai iya hargitsewa a gidan mutane gwara ya kama kansa ya bar gidam hakan zai fi alkaihri.KRB3P040
Arewabooks@nanahaleema11.

Yadda Nayla ta shiga a sanyaye ya saka Jidda da Salma tambayarta abinda ya faru. Zama tayi akan gadon ta kalle su ta ce, "Na faWa mu ku kamar baya sona ma gabaWaya." Salma ta ce, "ya taso ya zo gidan nan saboda ke kuma kice haka? Wai kin manta waye Omar Win ne? A ganina tunda har ya zo zancen so ya kamata ki rufe shafinsa." Nayla ta ce, "gabaWaya babu karsashi da zumuWin son dawowata a gare shi, na Wauka zan ga yana zumuWin na dawo amma sai naga ba haka bane."

Jidda ta ce, "me ki ke so ya yi miki a gidan sirikansa?." Nayla ta ce, "Amma yadda ya yi min magana a gidan Daddy daban da yadda ya yi yanzu. Sai Waure fuska yake yi, wai ina fita ba tare da izininsa ba." Salma ta yi dariya ta ce, "ko a nan baki fahimci soyayya bace ba kenan?." Nayla ta ce, "ni kuma na ce har yanzu ban gama yanke hukuncin zama dashi ba, na Wauka zan ga ya cigaba da bani ha™uri sai na ga akasin haka. Domin kuwa cewa ya yi in na gama yanke hukuncin na sanar dashi zai yi abinda nake so."

Salma ta ce, "Wallahi kina da matsala, yanzu meye na dawo da maganar saki kuma don Allah?." Jidda ta ce, "da kin sani kin bari komai ya wuce, dole ya ce miki haka ai Nayla. Duk da dai zhima ya kamata ya nuna miki soyayya a bayyane." Nayla ta ce, "gabaWaya son komawar ma ya fita yake daga raina." Salma ta ce, "Sai ki yi ai." Nayla dai ta yi shiru bata ce komai ba amma gabaWaya zuciyarta babu daWi.

Shi kam Omar da matu™ar fusata ya koma gidan. Ya tsani maganar sakin nan, ko kusa baya so ayi masa zancen saki, amma shi yarinyar nan zata saka a gaba tana yiwa batun saki dan ta ga ma yana saurarenta.

Ko gidan bai je ba, gidansu ya koma ya zauna yana huci shi kaWai. Masifar da take zuciyarsa yake so ya saukewa wani shiyasa kawai sai ya kira Didi. Tana Wauka ya fara masifa ya ce, "Wai me yarinyar nan ya Wauke ni ne? Tana fita duk inda take so ba tare da na sani ba, tana yin duk abinda ta ga dama da aurena a kanta. Yanzu ni take kallo tana sake yi min maganar saki, dan wai tana ganin na je har inda take ne ko? Ni za a rainawa hankali ko Didi? Dan kawai ina sonta ina kuma so ta dawo rayuwata shikenan kuma sai raini ya shigo ciki!?."

Didi da take jin yadda yake masifa da mamaki ta ce, "Omar to ai ba ni ce Nayla Win ba ko? Wannan masifa da ka ke yi min kamar ni ce Nayla Win?."


"Ai faWa miki ke yi, na gaji da Waukar wannan abubuwan da yake faruwa, tana yin abinda take so ne saboda kawai ta samu dama daga wajena. Na kasa sarrafa kaina na kasa tsayawa akan matsaya guda Waya, ko yaushe cikin ™unar rai nake da damuwa duk a kanta. Har faWa min take yi wai kalamaina ba na gaskiya bane, ita an faWa mata ina yin ™arya dan na burge wani? Ko kuma Ina ™arya ne dan wani yaji daWi?. Ni ban ce ta karya min zuciya ba itace zata ce na karya mata zuciya? Ya yi kyau. Ki zama shaida, daga yau bazan sake maganarta ba, in ta ga dama ta dawo, in bata gama ba tai ta zama har a tashi duniya. Rabuwa da ita ne bazan yi ba, duk inda taje babu sanina kuma ita da Allah" ya faWa yana katse wayar a fusace tare da cilar da ita.

Fusata yake ji da ita har a jininsa, gabaWaya kansa ya kulle, zuciyarsa na bala'in bugawa sai girgiza kai yake yi shi kaWai yana cize baki cikin zallan takaici da ba™in ciki. Ranar ko fita bai yi daga gidan ba, a ciki ya kai har dare. Sai daren ya Wan samu zuciyarta sassuta ya fita zuwa shago, amma babu walwala ko magana tsoron yi masa ake yi saboda yanayin fuskarsa.

Bayan kwana biyu da maganar Nayla da Jidda da Salma suka fita su a lallai yawon siyyayar komawar Nayla suke. Ta layin gidan Didi suka zo wucewa kawai suka tsayar motar a ™ofar gidanta suka shiga.

Tana zaune da Marmerh a hannu suka shiga ta da fara'a ce, "barkan ku da zuwa." Suka zauna Salma ta karSi Marmerh ya ce, "masha Allah, Didi Marmerh tana kyau wallahi, amma ni sai nake ganin fuskarta kamar ta Omar." Didi tayi dariya ta ce, "indai kin ga fuskarsa sai kin ga tawa. Sannan ku da zuwa." Jidda ta ce, "Yauwa Didi. Hanya ce ta biyo da mu muka shigo nan."

Didi ta ce, "Sannun ku da zuwa, ku sha ruwa akwai abinci in zaku ci." Umma Saroot ce ta fito ta ce, "Nayla ku ne tafe." Nayla ta yi murmushi ta ce, "mu ne Umma, barka da yamma."
"Barka dai Nayla, ya mai gidan naki? Omar sarkin ´an rigima." Murmushi ta yi bata amsa ba dan yadda take mata magana ba su san tana gida ba.

Umma Saroot ta ce, "Omar akwai rigima, ina jinsa yazo yana ta wasa da ´arsa." Nayla dai bata ce komai ba sai murmushi kawai. Umma ta ce, "in zaku ci abinci akwai." Salma ta ce, "babu komai Umma, mun ™oshi." Ta yi murmushi ta shiga Waki. Jidda ta ce, "Didi wallahi Umma na da kirki sosai, gata suna kama da Omar." Ta yi dariya ta ce, "maza ya ji ki."

Kira ne ya shigo wayar Didi ta kalli mai kiran ta kalli Nayla ta ce, "Mijinki na kira na, ban san da me yazo ba kuma." Nayla bata ce komai ba sai murmushi da tayi, Didi ta Wauka ta saka wayar a speaker dan ta san bazai wuce zancen Nayla ba.

Daga can Sangaren ya ce, "Didi!." Didi ta ce, "Na'am Omar."
"Kina lafiya? Ya Marmerh?."
"Lafiya lau, Na ga baby swing da ka aiko mata dashi, Omar yana da tsada fa, na yi tunanin siya na fasa saboda kuWin da yawa."
"In bakya so ba sai ki ™ona ba, kuma kar na sake yin abu ki ce min yayi tsada, kuWina ne ai ko?."

Didi ta ce, "na ka ne, amma...."
"Kin ga Didi, ba ke na yiwa ba ai ´ata na yiwa, In ke ce zan ma kalle ki ne?." Tayi dariya ta ce, "Ya na jika haka kamar mara lafiya? Lafiya dai ko?."

Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "GabaWaya na zama mai rauni kamar ba ni ba, ko magana bana so ayi min haushin yarinyar can da nake ji da an yi min magana sai na fara faWa, ita kuma na kasa yi mata faWan. Ni da bani da yawan ciwo amma yanzu kullum da ciwon kai da zazzaSi nake yini, ba kuma komai ne yake kawo min ba sai damuwa."

Didi ta kalli Nayla da take kallon Didin tayi murmushi ta ce, "Wacce yarinya kenan?."
"Wa nake da ita bayan ke da Marmerh?."
"Oh ai na ji kace yarinya ne shiyasa. Me matar ta ka ta kuma yi maka kuma?."
"Meye ma bata yi ba."
"Amma ka ce ka daina yi min maganarta, har ka sakko daga fushin?."

Omar ya ce, "na faWa miki na canja, ni kaina canjin nan yana cutar da ni. Didi na kasa mantawa da ita kamar yadda nayi niya, gashi sai da na kira ki dole na yi maganarta. Amma ita Waukar kalamaina take yi matsayin na ™arya, a duniya akwai wanda zan yiwa ™arya ne dan na burge shi... sam babu." Didi ta yi murmushi ta ce, "ni sai ka kira ni kai ta masifa kuma ba ni nayi maka laifin nan ba, Nayla ce ba ni ba."

"Didi!." Jin yadda ya furta a sanyaye sai ta ce, "Na'am." Omar ya ce, "ya zan yi ta amince da gaske ina sonta? Me zan yi da zai tabbatar mata da ina son rayuwata da ita kuma bazan iya rabuwa da ita ba? Me zan yi?."
Didi ta ce, "na ce maka duk kalaman da ya zo zuciyarka shi zaka faWa."
"Ki daina Wora ni a keken Sera, haka ki ka faWa min kwanaki, da na je gidansu na faWa mata abinda yazo daga zuciyata ™arshe kuka ta dinga yi, Bana so na ga tana kuka ko kusa."

Didi ta ce, "Alhaji Omar Wan uwan Aisha, mijin Nayla baban Marmerh. Yanzu me ka ke so nayi maka?." Murmushi ta ji ya yi mai sauti amma bai ce komai ba. Didi ta ce, "Wan soyayya, Ina jinka kayi magana mana."

"Kin raina ni ko? Dan kin ga yanzu na zama wani iri ko? To Tiger har yanzu sunana ne wallahi, kawai wannan matar tawa ce ta Wora min pressure, ko ya akayi ma na faWa da yawa haka oho. Ni fa soyayya bata yi daidai da zubina ba, ban san ya aka yi na bari na yi zurfi haka ba. Allah in aka auna jinina ya hau."

Dariya Nayla tayi dan wallahi dariya ya bata sai kuwa ta ji ya ce, "Waye yake dariya?."
"Ba™uwa na yi tana yiwa Marmerh wasa."
"Amma kamar na san wannan muryar."
"Gaskiya baka santa ba."
"Ya yi. Ba fa ko wanne banza zaki dinga bawa yarinyar nan ba, wasu suna zuwa Waukar yara ne dan su cutar dashi." Didi ta yi murmushi ta ce, "to Omar, ka samu ka yi magana da Nayla Win ko zaka ji daWi."

"Ni bazan kira ta ba Didi, ki barta tayi tunani kamar yadda ta ce min. In bata da ra'ayi shikenan."
"Sai ka rabu da ita Win?."
"Hmm! Inda za a yi tashin hankali dani kenan, Allah sai na tashi garin Kano harda Kaduna garinsu. Na kira ki ne ji lafiyar ki da ta Marmerh kuma na ji, Sai anjima" ya faWa yana yake wayar ta bi wayar da kallo tana murmushi.

Salma ta ce, "Omar kenan, wato shi soyayyar ta sa ma ta musamman ce. Ita da yi masa laifi ke da shan faWa." Didi ta yi murmushi ta ce, "Ranar da ya je gidan Mama yana dawowa ya kira ni, yadda ya dinga yi min masifa sai ki Wauka wani laifin na yi masa. Ya ce na shaida bazai sake yi min maganar Nayla ba, Amma gashi ba a je ko ina ba ya kasa" ta faWa tana kallon Nayla da take murmushi.

Didi ta ce, "Nayla na faWa miki gaskiya? Wallahil azim Omar yana sonki, ban taSa ganin rauni a tare dashi ba sai a kan soyayyarki, Omar in ya ce ya bar abu ya bari amma gashi ya kasa sai da ya yi min zancen ki. Ban taSa ganin halittar da Omar ya bawa ha™uri ba sai ke, babu halittar da Omar ya yi kewa sai ke. Kamar yadda ya ce haka ne, shi ba mai yawan rashin lafiya ba ne, amma a kan ki sai da ya sha fama da zazzaSi da ciwon kai. Kar ki yi tunanin ina faWa miki haka ko dan ki koma masa ko kuma dan Omar Wan uwana ne, kin san ni mai faWa miki gaskiya ce a kansa. Bazai miki ™arya dan ya burge ba kamar yadda ya ce, duk abinda ya faWa miki wallahi ba ™arya yake yi ba Nayla, da gaske ke yana sonki da zuciya Waya da gangar jikinsa. Mace ta farko a duniya da ya so kuma yake so kece, Omar baya Soye min komai nasa, hatta yadda zuciyarsa ke bugawa a kan ki ya faWa min Nayla."

Nayla dai murmushi take yi cike da farin ciki amma sai ta kalli Didi ta ce, "Narma fa?." Didi tayi dariya ta ce, "bazan baki amsar Narma ba, amma daga ranar da zaman ku ya koma na farin ciki ki tambaye shi da kan ki, ki ce masa a wanne matasayi ya ajjiye Narma a kwanakin baya, na tabbatar zai faWa miki."

Nayla ta yi murmushi Jidda ta ce, "samun soyayyar irin su Omar abu ne mai wahala Nayla, komai yana faWa daga zuciyarsa babu ™arya balle ya faWa dan ya burge ki. Nayla ki bar hutun nan haka ki koma, kina sonsa yana sonki me za a jira kuma?."

Salma ta ce, "aji take so ta ja masa, da alama shi kuma tsinka ajin zai yi." Didi tayi dariya ta ce, "ban ga laifin ki ba Nayla, ki tsaya ki yi tunani zama da Omar wallahi sai ka shirya. Halinsa yana na babu inda yaje, sai kun zauna zaki fahimci abinda baki ma san dashi ba. Dan haka ki nutsu, in zaki iya da zafin ransa bismillah, in baza ki iya ba ki kama kan ki ki ja gefe. Abu Waya na sani kawai, Omar yana sonki."

Salma ta ce, "Didi ya ki ke zugata ne?."
"Ba zuga ba ce ba Salma, gaskiya ce. Omar ya wuce duk tunanin ku zama dashi sai da ha™uri." Nayla tayi murmushi ita dai bata ce komai ba amma hirarsa da ake yi ma daWi take ji. Sai magriba sannan suka wuce gidan Mama. Suna shiga falon suka tarar da Mama a zaune da alama su take jira.

Suna shiga ta ce, "Jidda kina da yarinya ™arama ki ta biye musu kuna yawo ko?." Jidda ta ce, "yanzu zan wuce Mama, motata zan Wauka." Mama ta ce, "Daga bara mu je saloon mu dawo sai yanzu magriba ko?." Salma ta ce, "mun Wan shiga siyayya ne daga nan sai muka shiga gidan Didi."

"Ai ya yi kyau. To Abba ya gan ku, ya kira ni yana ta faWa, yana cewa Nayla na da aure ina bari tana yawo. Dan haka umarni ne ba shawara ba, gobe ta shirya ta koma gidan mijinta in ba haka ba da ni da ku duk ran mu sai ya Saci."

Salma ta ce, "gobe kuma Mama?." Mama ta ce, "ni na aike ku tafiya yawon? Zan kira wacce zata yi mata ™unshi gobe da safe, sannan zan aika aje a gyara gidan da daddare sai ta koma" ta faWa tana bar musu wajan. Jidda ta ce, "gashi gobe bana nan zamu fita da Baby." Salma ta ce, "Tunda Abba ne ya ce kuwa sai ta koma goben, dama dai Daddy ne zai iya sakkowa, amma Abba babu wasa. Ki je zamu yi waya" Suka shiga ciki ita da Nayla ita kuma Jiddq ta fita.

Kamar yadda Abba ya ce hakan ce ta da faru, washe gari mai lalle ta zo da safe aka yiwa Nayla ™afa da hannu amma na saman fata, bata cika son wanda ake yi a tafin ™afa da hannu ba ta fi son ba™i ko ja amma na kan fata. Da wuri aka gama yi mata, daga gidan Hajja aka aika aka je gyara gidan.

Da yake da Salma duk wani abu da suka siyo Salma ta saka, daman frames ne da babu a gidan suka siya suka kafa, sai wanda ta ajjiye mata a Waki dan bata san inda zata saka mata ba. Sai kayan banWaki da ta sake siya, towels da sababbin bathrobes, sai kayan ado na falo da kitchen. Aka gyara gidan har aka gama gyaran Omar baya nan suka yi turaren wuta suka koma gida.

Bayan sallar i'sha Mama ta tarar da Nayla ta shirya cikin abaya ba™a mai kyau da tsantsi, tayi mata kyau dan gyaran jikin da aka yi mata ya karSeta. Mama ta kalle ta ta ce, "To driver zai mayar dake, Abba ya ce kar wanda ya yi miki rakiya daman ai ke kaWai kika zo. Nasiha an yi miki tun ba yanzu ba na san duk kin ri™e, abinda ana ce miki kawai ki bar komai ya wuce kamar baki dawo gida kin zauna ba, ki ajjiye komai ki yi facing zaman aurenki. Sai kin yi ha™uri, duk soyayyar film ko ta littafi da ki ke tunani ba ita zaki gani ba, za ki ga daidai misali wacce ta isheki ki faWawa duniya mijinki yana sonki. Sannan kin zauna dashi kin san halinsa, sai ki yi ha™uri akan wasu abubuwan dan aure Wan ha™uri ne Nayla. Allah ya baku zaman lafiya ya Worar da zaman ku har mutuwa, Allah ya sa ki gaji iyayen ki." Nayla ta amsa da amin. Ummimi da Mama suka rakata har mota, a lokacin Abbas yake ajjiye motarsa a wajan.

Mama ta ce, "Abbas ™anwarka zata koma gidan mijinta, ayi mata nasiha." Ya yi murmushi ya ce, "ban da rashin ji." Dariya suka yi gabaWaya ya shiga ciki ita kuma ta shiga motar suka tafi.

A ™ofar gidan aka ajjiye motar ta fita ta bashi kuWin napep sannan ta ce ya kai motar gidan Hajja ya ajjiye. Ya amsa mata da to ita kuma ta buWe gate Win gidan ta shiga.

Sabuwar motarsa tana ajjiye a wajan, Nayla ta kalla ta yi murmushi tana mamakin motar dan ita dai ta san tana da tsada sosai, ta girgiza kai sannan ta wuce zuwa cikin falon. ˜hamshi falon yake yi sosai, ta yi murmushi ta wuce ciki ta ajjiye jakarta da laptop Win da take hannunta.

Šakin ta kalla komai yana nan sai dai an canja komai hatta bedsheet Salma ta canja mata. Ajiyar zuciya tayi ta kalli agogo ta ga tara na dare ta kusa sai ta rasa abinda zata yi. Frame Win da Salma ta ajiiye mata ta gani ta buWe, hoton Tiger ne babba mai shegen kyau, ta buWe baki ha™oranta sun fito waje. Ajjiyewa tayi domin a Wakinsa take son kafawa. Zama tayi ta kira Didi a waya tana bata labarin ta dawo, Didi ta dinga murna da addu'a Nayla na ta murmushi.

Kitchen ta shiga tana sake kallonsa kamar wacce ta shekara bata nan, yana nan yadda yake dan daman ta san babu abinda zai taSa a gidan. Tunani take yi ta yi girki ko kuma ta ™yale girkin dare ya yi?.

Noodles ta Waukota ta kalli bayanta taga kayan miya, irish potatoes da plantain a ajjiye, ta san dai aikin Salma ne ita bata bar komai ba, koda ta bari ai ya ci ace ya lalace. Nan da nan ta dafata ta sai ™hamshi take yi ta samu flaks mai kyau ta zuba yadda baza ta huce da wuri ba.

Tana gamawa ta wanke hannu kenan ta ji motsin shigowa, ta fito ta tsaya cak tana kallonsa yana shigowa yana amsa waya. Yadda yake maganar ta gane da Didi yake waya kafin ta ga ya kashe wayar.

Kallon falon ya yi ya ce, "waye ya shigo gidan nan?." Murmushi tayi da alama Didi bata faWa masa ba kenan. Fitowa tayi daga inda take ta tako ta ce, "Sannu da zuwa." Cak ya tsaya ya Wago idanunsa ya kalle ta suka haWa ido tayi murmushi ta saukar da kai ™asa.

Zuba mata ido ya yi na wani lokaci kafin ya janye idanunsa dan shi a tunaninsa gizo take yi masa. Nayla jin shiru sai ta kalle shi ta ce, "YaMar!." Lumshe ido ta ga ya yi ya buWe, ya kalli inda take ya tsayar da idonsa ™yam akanta yana so ya tabbatar itace ko kuwa gizo take yi masa. Nayla ganin kallon da yake mata ya yi yawa ta sauke ido ™asa tana kifta idanu da turo baki gaba.

Ajiyar zuciya ta ji ya yi amma bai ce komai ba. Waya ta ga ya saka a kunne yana cewa, "na faWa miki gidan nan akwai aljanu, yanzu ba muryarta kaWai nake ji ba" ya jiyo yana kallon Nayla ya ce, "ita nake gani a gabana a tsaye, kuma dan rashin kunya irin na aljani ko tsorona ma bai ji ba kallona ma take yi."

Nayla ta ™yal™yale da dariya ganin da gaske bai Wauka ita Win bace ya Wauka aljana, ganin yadda take dariya ya saka bai ji ma abinda Didi ta ce ba. Sai da ta kira sunansa da ™arfi sannan ya ce, "ina jinki."

Shiru ta ga ya yi sannan ya ce, "wai da gaske ki ke?." Kashe wayar ta ga ya yi ya sake zuba mata ido kamar mai son tantance wani abun. Nayla da ta gama dariya cikin sanyin murya ta ce, "in baka banbance ni Win ba ce ka Wauka kawai aljanar ce" ta faWa tana murmushi murya a sanyaye.KRB3P041

Wani irin nishaWi da daWi Omar ya ji yana mamaye masa zuciyarsa, nan da nan farin ciki ya bayyana har a kan fuskarsa, ya bita da kallo yana ji kamar ya rungume ta amma baya so ta ga ya za™e da yawa ko ta yi masa kalla Wan iska. Murmushi ya yi mai bayyana farin cikin da yake ciki, ya Wan shafa kansa kaWan yana girgiza kai ya ce, "amma an shammace ni." Nayla ta yi murmushi itama amma bata ce komai ba.

Omar ya kalle ta kamar zai yi magana sai ya fasa yana murmushi, ya sake kallonta cikin sanyin murya ya ce, "Yaushe haka?." Nayla taji farin ciki na mamaye mata zuciya, muryar da ya yi amfani da ita wajan yi mata magana bai taSa yi mata magana da ita ba. Ta Wan kawar da kai ta ce, "Wazu na dawo. Har dinner na shirya maka."

Omar ya kalle ta kamar zai yi magana sai ya fasa bai ce komai ba, yana sosa goshinsa kamar yadda ya saba. Nayla a sanyaye ta ke saboda sanin halinsa, amma tana so ta zama wayayyiyar amarya shiyasa take dakewa tunda ba ba™onta bane. Ta koma inda abincin yake ta zuba noodle Win a bowl ta kalle shi ta ce, "ka zauna." Ya kasa tantance adadin farin cikin da yake ji a zuciyarsa hakan ya saka shi ya zauna Win kamar yadda ta ce.

A hankali ta tako ta zauna ta mi™a masa ta ce, "bismillah." Bai karSa ba sai kallon abinda ta mi™o masa Win ya yi, ya kalli hannunta da ya sha jan henna akan fatar hannun. Nayla bata yi magana ba shi kuma bai karSa ba sai kallon hannunta da yake yi.

A kusa dashi ta ajjiye bata ce komai ba, ta zauna kawai tana kallon wani wajan daban tana jin kanta kamar an Waure ta da igiya. Dauriya take yi kawai, amma nauyi da kunyarsa take ji sosai, tana so ta bar komai ya wuce kamar yadda Mama ta ce. Omar ikon Allah yake kallo, gata dai a kusa dashi, amma kewarta yake ji tana shiga cikin zuciyarsa, ya rasa abinda zai yi da zai ji ya gamsu da ita Win ce

Please Login or Register in order to submit comment