Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din tin yana likitansa abin ya karbesa dan haka a yanzu suka gama bunqasuwa.

Ba iya fita aikin Nasir keyi ba sosai yake kulawa da Abbu wanda harya fara samun sauki sosai dan har fitowa dashi Nasir keyi su zagayo yana turasa akan kujera wani lokacin kuma riqesa yakeyi su dan zagayo da kafafunsa da basa wani iya tafiyar arziki.

Fatima kuwa duk da manyanci yaxo hakanan itace komai na gidan ya dawo hannunta itace ke juya masu aiki sai kuma lokutan da dama itace da kanta takewa Abbu abinci musamman data dage tana sake koyar wasu abincinsu bayan wainda ta dade da iyawa daga fammah,

Dr Mum bata zama sosai sbd aikinta ga yawan tafiye tafiye dan haka rayuwa a yanzu tayiwa kowannensu daidai musamman idan dr Mum ta tina da Raheem yana qasar da baya tareda ubansa da dangin jeerahs yana rayuwa da matarsa.

**Nasir bai fara training ba sai da suka share kusan shekara a qasar yana cikin business dinsu ya gama sanin qasa da huldodin komai da rayuwar qasar harma da zama kaman cikakken dan qasa dan haka yafara kokarin shiga training duk da ayanzu sbd Raheem kawai zai shiga aikin,

Bai taba dena waya kowace rana da baba khalil da mommy Zainab ba yana basu kulawansa tareda yi musu aike duk wata zai tura musu kudi masu kaurin kulawa da BABY SANAH da karatun Al'amin wanda karatunsa yake nisa shima dan yana junior class yanzu.

Raheem aurensa wata tara Meenah wahab ta haifi Lafiyayyar babynta wadda bata bar komai na mahaifinta ba wanda zuwa yanzune wani sabon kwarjininsa mai zafi ke qara fidda kyansa da sabon jininsa dake kan lokacinsa,

Fammah shine sunan da aka sakawa babyn kuma haka ake iranta dashi,

Zuwan Fammah duniya ya saka Meenah wahab samun matsayin datake ganin tana buqata a zuciya da rayuwar RAHEEM JEERAH wanda duk da ta zama matarsa uwar yayansa batajin ta samu wannan full satisfaction din a zuciyarta,

Sonsa yayi mata yawan datakejin kaman bata gamsu ba dan hakane shi da kansa ya dade da fahimtar she is obsessed with him dan haka yake bata dukkanin sonsa da kulawansa dan ta samu nutsuwa da jin yana son nata shima.

Dr Mum jin tayi rayuwa da zuciyarta sun sake mata dadi dan kuwa yanzu tasan meenah ta gama samun guri da gurbi a zuciyar Raheem da Ubansa tinda ta haifa musu 'ya,

Sir hakeem jeerah ma tabbas yayi farin ciki sosai da haihuwan tareda tsananin kaunar Fammah din musamman daya taho da ita Nigeria suka dan zauna kusan wata biyu kafin ya tattara su suka koma.

Nasir shine uban 'ya dan kuwa shine ma ya saka mata sunan Dr Mum din.

Dawowa da Meenah akai gida sai datai kusan shekara guda tukuna ta koma sbd RAHEEM da baya zama kwata kwata a dan lokacin rayuwarsa yanzu kusan ta koma ruwa gabaki daya dan yafara taka manyan matsayin da babu sauran hutu a tattare dashi ko kadan bayan rayuwa a cikin inda suke din yanxu.

Meenah ma dole aiki tafara dan debewa kai kewa tareda kulawa da baby fammah wadda tafara wayo da girma.


******Baby SANAAH tafara girma da wayo sosai dan kuwa shekarun sun fara tafiya,
A rayuwarta bayan iyayenta da yaya Al'amin datake tareda su Yaya Nasir dinta shine mutum na hudu dataiwa sanin da zallan kauna ta jinin gaske sbd tin tana qanqanuwa sosai babu ranar da baya kira a ajiye mata wayar yayita mata wasa da magana harta fara wayon ganesa harma a yanzu datai masa sanin sosai dan kuwa a hankali ahankali dashi da Mommy suka tabbatarda ta tashi da wata irin kaunarsa da sonsa a jininta,

Sonsa takeyi kaunarsa takeyi harta kai babu lokacinda bata masa rigimar saiya taho,
A duk lokacinda Zaiji muryanta ko tayi masa yarinta zuciyarsa sake wata irin mutuwa takeyi akanta batareda damuwa da qanqantarta ba garesa,

Anyi anyi yayi aure amma sam ya kasa hakan sbd qwallafa rai da yayi akan Baby SANAAH wadda haryanzu ya kada dena kiranta da baby a cikin sunanta.

A lokacinda Fammah 'yarsa datake girma tareda Baby SANAH bai damu ba dan kuwa bayama iya tinanin aure a lokacin duk da fadan da babansa khalil ke masa na qin aure,SANAH kawai yakeso ita kadai yayi niyar aure koda hakan na nufin zai tsufa ba aure to tabbas zai jirata ita yakeson ta zama matarsa a nan dai duniya.

Kaf iyayensa babu wanda baiso ya fara koda wani aurenba kafin girman Baby SANAAH amma baida raayin hakan dan haka dole aka hakura aka tayasa jira da fatan girman baby SANAAH wadda take sake girma kowace lokaci da kaunarsa a jininta da zuciyarta.

Shine komai nata tinda aka haifeta kaman yanda yafada babu abinda iyayenta suke siya mata da kudinsu saida kudinsa har yanxu datake karatu shine komai da komai nata harma dana yayanta Al'amin.

Baba khalil yariga ya sakawa ransa tinda Nasir yaqi auren to tabbas basai Baby SANAAH tayi girma sosai ba tana kaiwa sha shida ko sha biyar ma zai aura masa ita insha Allah.

*****Nasir ya samu gurbin zamowa navy soldier tini shima sedai basa ma guri daya kwata kwata da Raheem jeerah tukuna sbd Raheem yayi nisan matsayin da bazai taba ma ganinsa ba a bangaren aiki sedai dan uwa kuma shi anan Morocco har lokacin yake.

A wannan lokacin ne kuma katsam Baba Khalil ya samu accident mai muni sosai da motarsa wadda ta Nasir ce yabar masa dazasu baro,

Accident din Baba Khalil ya saka Nasir tattarowa dole ya taho Nigeria sbd jinyar baba khalil din da kulawa dasu gabaki dayansu tinda Al'amin karatu yakeyi sosai ba damar ajewa kuma koda zai iya ajewan dole dai Nasir yazo.

Haduwan Nasir da Baby SANAAH ya taho mata a bazata dan haka sai ta samu kanta da tsananin farin cikin ganinsa da kunyarsa amma sbd yanayin jikin Baban babu damar bayyana zazzafar son da sukewa juna.

Mommy na cikin tashin hankali sbd accident din yayi muni sosai gata sauran kuruciyarta ga babu wasu dangin arziki dan mahaifinta ya rasu yanzu sune suke kulawa da ummanta wadda ta tsufa sosai.

Kafar Baba Khalil daya ta lalace gavaki daya ya rasata dan haka jinya sosai yakeyi Nasir ya tsaya akan komai na ganin ya samar masa jinyar cikin nutsuwa da kwanciyan hankali,
Babbar private asibiti ya kaisa ana zubar da dukiya me yawa gurin kulawa dashi sosai,

Ya jima sosai a Nigeria saida Baba Khalil ya samu sauki daidai misali kafin ya tattara ya koma sbd lafiyar dai gaskia ba lallai ta dawo kaman baya ba.

Kafin ya tafi zafin kaunar dake tsakaninsa da Baby sanah ya qaru sosai dan kuwa tashin hankalin datai dazai tafi sai dayaji inama a aura masa ita a hakan idan yaso yayi renanta ta girma a hannunsa amma yanayin jikin Baba yasaka baice komaiba ya lallabata ya tafi yabarta.

Bayan komawansa ya dena dadewa kwata kwata bai dawoba akai akai lokaci zuwa lokaci yake tahowa Nigeria gurin dubasu sbd Maamah bazata iya xuwaba dan manyanci dan haka ya dage shine ya zama ginshiqin ahalin nasu tinda baba yana zaune ko kwance baya iya fita koina rayuwarsa ta mutu kenan sai abinda Allah yayi.

A can bangare daya kuma nauyi ya sake hawa kansa sbd business din Raheem da suka fara bayyana shine yake kulawa dasu anan Nigeria da Morocco harma da America.

Ya zama wanda yafi kowa zama busy a duka familyn biyu dan hakane ma bai wani yi nisa a aikin navy din ba yayi quiting ya fuskanci manyan abubuwan dake gabansa,

Duk wani sirri da tattalin arziki da kulawa da komai kankantar abun Admiral RAHEEM HAKEEM JEERAH yana kansa bai taba rasa komai qanqatar details na RAHEEM ba,bai taba wasa da abinda ya shafesa ba,
Shine dan uwa daya,rabin jiki daya,kwrgen sirri daya kuma personal person daya dika na Admiral Raheem jeerah da mahaifiyarsa dr fammah wadda komai nata yana hannun Nasir dan hatta komai ma sunansa take sakawa bana Raheem ba kaman yanda dukiyar Abbu ma tana karkashinsa duka.

Shekaru sun sake tafiya sosai Rayuwar familyn Admiral RAHEEM HAKEEM JEERAH ta zama wata rayuwar dukkanin kwanciyan hankali da kauna me karfi da soyayya tareda daula da wani irin tsari na turawan da ilimi yayi mugun ratsawa da yanci,

Da gata da yanci da wata kauna me karfin gaske fammah jeerah ta taso daga Dad dinta ga kuma dayan Dad nata Nasir dayake tsananin kaunarta.

Iyayenta busy suke basa wani zama musamman Dad dinta da kwata kwata rayuwarsa ta kusan qarewa ne akan matsayin dayake akai na Admiral of the Us Navy.
#MAMUH

GANIN IDO
MAMUHGEE
1K
VIP 5K
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

19
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki  Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki  Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce  For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Kauna me tsananin karfin dake tsakanin Nasir da Admiral bata taba ja bayaba saima wani karfin data qara dan kuwa bayan aikinsa dayake da qarfin gaske akai da kaifin raayi da wani irin rashin tsoro ko shakka to Nasir ne wanda yasan asalin cikinsa da wajensa,

Shi a nasa bangaren baitaba yiwa Nasir maganar aure ba sbd yasan ko Nasir din zai mutu ba aure bazai taba auren wadda va yarinyar da shine ya Rada mata suna ba hakama baiga abin tada hankali ko damuwa ba akan yin aure ko fashinsa koda shekaru na tafiya.

*****Baba Khalil jiki ba sauki duk wannan shekarun ga tsufa yana sake tafiyar da ciwon cikinsa dan haka ya yanke shawarar ayi auren Nasir din da baby SANAAH wadda batafi shekaru goma sha shida ba a lokacin.

Hakan yayiwa kowa dadi musamman sbd Nasir din da haka kawai kowa yaji matsuwar son yin aurensa sbd manyancin dake shigosa.

Shi kansa Nasir din a yanxu zuciyarsa ta gama rasa kowane walwala da farin ciki bayan na son Auren Baby SANAAH wadda ta gama tsayar da zuciyarsa akanta dan irin yanda ta kwallafawa ranta da zuciyarta shi,
Bai taba tinanin zata iya masa wannan son ba dayake gani a tattare da ita wanda ya zamana kaman a jininta yake yawo,
Shine ya koyar da ita sonsa ya dasawa zuciyarta sonsa amma ayau son yayi yawan dayake ganin kaman yayiwa zuciyarta yawan da baisan wane irin so zai nuna mata ba yaji zuciyarta ta samu gamsuwa.

Irin zafin son da dayake mata ya saka kowa yake tsananin sonta da kaunar a bangarensa dan kuwa itace macen da zata kawo farin ciki da walwalan da suke ganin yana qasa a rayuwarsa ahankali ahankali dan kuwa ya tashi daga Nasir mai raha da son hayaniya ya koma Nasir shiru shiru walwalansa haka kawai tana yin qasa.

Ana saka date din aurensu wanda tini aka fara shirye shiryensa musamman Dr Mum wadda ta hada kayan auren Nasir dasuke tsananin fatar hakan,

Sun san yarinya ce sosai dan haka suka shirya karbanta su ingata rayuwarta a tareda su kafin ta qarasa girman zama cikakkiyar matarsa.

Dukiya me yawa Raheem ya ware ya tanadarwa Nasir din gidan da zai zauna da matarsa duk da gurin Dr Mum zata fara zama.

Ana saura sati biyar Auren a tsakar dare Allah ya karbi ran Baba Khalil wanda Allah baiyi zaiga aurenba duk burin dayaci na bawa Nasir Baby SANAAH da hannunsa.

A lokacinda Baba Khalil ya cika Nasir na Nigeria a hannunsa ya cika bayan ya rokarwa yayansa gafara a gurin Nasir din wanda tinda yake basu taba maganar mahaifinsa a tsakaninsu ba dan magana ce da babu abinda zaa fada akanta.

Wani irin numfashi me zafi da tsananin mutuwar jiki Nasir ya sake a lokacin daya shafe Baban yanajin wani irin dumi da zafi na ratsa shi,
Wani abu ya tsaya a maqoshinsa idanuwansa sukai jajir ya zubawa Baby SANAAH idanuwansa a lokacinda ta yanke jiki ta fadi a jikinsa jin Babanta ya cika yabar duniyar har abada.

Tinda akai rasuwar Nasir ya kasa cewa komai ya rasa dukkanin sauran kuzarinsa da walwalansa.

Maamah ta iso Nigeria ita kadai sbd dr  Mum batama nan tana Greece gurin wani taron likitoci.

Maamah tayi kukan rashin baba khalil sosai sbd sun rasa ginshikinsu na karshe ,
Nasir a yanzu baida uba baida dangin uba yazama uba a ahalin kenan,

Mommy zainab ta fice hayyacinta itama sbd ta rasa bangon rayuwarta itada yayanta.

RAHEEM JEERAH ya tattara abinda yakeyi ya ajiye ya sauka Nigeria dan jajanta wannan rashin da sukai dan kuwa ya taba Nasir sosai tabawan da baa sake gane kansa ba.

Sati daya akai aka gama zaman gaisuwan daga nan suka koma su kadai,
Maamah bazata komaba sai anyi auren Nasir din kaman yanda baa dagaba saisu tafi da Baby SANAAH din.

Gidan babu wata hidima ko hayaniyar bikin da ake kokarin yi,

A cikin kwanakin SANAAH ta rasa nutsuwanta gabaki daya tafara wata rama haka kawai sbd anyi anyi ta sake ta kasa sakewa musamman da Nasir ya koma musu sabon mutum sai rasuwar ta kasa sakin kowa suka ajeta a rai sbd wanda ya kamata ya zama me yaye musu damuwan ya kasa dawowa shi din.

RAHEEM JEERAH dazai komai tareda Nasir suka tafi zasu dawo tare idan kwanakin auren suka kusanto sosai.

Tafiyarsu a tare Raheem ya shiga mamakin dayafi wanda ya shiga a lokacinda ya fahimci matarsa ta aure is obsessed with him amma a yanxu abinda yake gani a tattareda Nasir yafi kusan abinda yake gani a tattareda Meenah akansa,

Bai taba sanin irin son da Nasir yakewa baby SANAAH ba yakai matakin da hankali ma baya daukaba,
Bai taba sanin ana irin wannan son ba wanda a matsayin cuta yake kallansa,
A yanzu kam ya tabbatarda duk duniya babu abinda zai taba bawa Nasir duka nutsuwan da mai rai yake nema bayan mallakar Baby SANAAH a matsayin matarsa.

Wani irin tsananin tausayi da sabuwar kaunar dan uwansa rabin jikinsa me tsananin gaske ne ta cike kowace bangare na zuciya da gangar jikinsa dan haka ya yanke shawarar Nasir din ya koma kawai shi zai taho idan lokacin auren yazo gap.

Nasir din bai komaba sbd yana buqatan kasancewa da Dan uwansa a lokacinda zaa qaddamar dashi ga sabon matsayinsa wanda sbd shine ya taho dan haka bazai tafi ba zai jira har sai anyi taron wanda zaayisa kwana uku cif before daurin aurensa.

Duk wata hidimar qaddamar da Raheem din dazasuyi ta familyn jeerahs da duk wanda zai taho daga Nigeria da Morocco Nasir ne ya shiga ya tsaya yake gudanar da ita cikin qwazo da farin cikin ganin Raheem din ya kai wannan matsayin da sukai burinsa tare amma shi kadaine Allah ya bawa ikon cika musu.

Sir hakeem jeerah ya iso qasar da kansa dan taya 'dansa farin ciki tarera ahalinsa,
Dr mum ma ta iso tana qasar sbd taya Danta farin ciki da nata iyalin dan haka kusan kowa na Raheem jeerah yana qasar a tareda shi.

SANAAH da Nasir koyaushe suna waya tana tambayarsa yaushe zai dawo an sakata a cikin lalle.

A duk lokacinda tai masa wannan tambayar jin yakeyi inama ba hidimar dan uwansa rabin jikinsa akeyiba da tini ya dawo gareta ya dawo ga hidimar aurensa da shine burinsa a yanxu dayafi kowane buri,
Shine abinda yayi shekaru masu yawa yana jira,shine abinda yafi komai mahimmanci a garesa yanzu amma kuma Raheem da kowace hidimarsa tafi gaban komansa da farin cikinsa dan haka bazai iya dawowa ba sai bayan qaddamarwan.

*****A ranar taron qaddamar bawa Raheem stars dinsa na taka matsayin REAR ADMIRAL a ranar kowa ya sake tabbatarda irin matsayi da girman kaunar dake tsakaninsa da dan uwansa dan kuwa iyayensa ya sarewa ba ba matarsa ba yarsa ba rabin jikinsa ya sarawa tareda qamewa a gabansa saida Nasir din ya dago jajayen idanuwansa ya kafe Raheem dasu yana zubo da wasu irin hawaye a karan farko na rayuwarsa tin bayan girmansa.

Shi kansa Raheem kafesa da idanuwansa yayi har saida Nasir din ya miqe tsaye ya rungumesa da karfi irin na mazan da suke jin karfi da mazankuta.

Anyi taron daya karbi manyan qasar kusan gabaki daya da manyan sojojin kasar gabaki daya kuma anzuba tsoro da asalin mulkin sojoji da wani irin tsarin daya saka taron tabbatarda babu wanda ba wani mai duniya da kanta ba daya halarta.

Nasir shine kaman pa din Raheem jeerah dan haka komai nasa da kulawa da komai nasa da gudanar da komai nasa yana hannunsa dan haka suka sake zama busy a kwana biyun,

A ranar daya kamata su tafi Nigeria wani aikin Raheem me mahimmanci ya sake riqesu kuma Nasir din yana tareda shi,

Ana saura kwana biyu rak daurin auren dukkanin wanda yake qarqashin rear admiral yana gurin wani taron da shine ya tsaidasu kuma iyayensa da duka familynsa na gurin a yau suna gamawa komai dare xasu bi jirgi sauka Nigeria.

Koina akwai tight securities da tsaro da komai ana jiran isowan Rear Admiral Raheem jeerah wanda ya iso tareda securities da Nasir dayake sake duba abubuwan dake rubuce da Raheem din zai tattauna akansu.

Suna shigowa aka rufe koina koina ya sake daukan tsit Raheem ya isa inda zai fara bayani da securities a bayansa.
#MAMUH

GANIN IDO
Mamuhgee
1k
Vip 5k
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

20
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
RAHEEM na bude baki zaiyi magana ko fitowa muryansa bataiba qarar wani mummunan explosion ya watse gurin gabaki daya.

Tsit komai na gurin yayi sbd daukewan ji da ganin kowa dake gurin tareda mummunan yanayin daya karade gurin kafin ihu da kukan mutane yafara tashi ahankali cikin wani hayaqi da zubar qasar bangunan gurin da rufin gurin dake zuba sosai sbd tarwatsewan da gurin yayi.

Cikin mummunan yanayi da tsananin tsoro da tashin hankali kowa dake gurin yake ambatar sunan nasa yana nemansa cikin rashin gani sosai.

Dr Mum ce ta iya bude idanuwanta daqyar bata gani sosai kunnuwanta na bada wani irin sauti mara bata daman jin komai ta kalli inda Raheem yake gurin yayi munin watsewa ta bude baki daqyar ta ambaci sunansa da wani irin sauti kafin ta juya inda Nasir yake shima ta qwala kiransa dukkanin jikinta na wafa irin rawa tana son tashi ta kasa.

Raheem dayake kwance a qasa cikin wani irin yanayi jini na fita gefen fuskansa sosai bayaji sam,

Motsawa yayi ahankali cikin wani irin karfin hali sbd sanin duka familynsa suka gurin,
Iyayensa duka biyu da matarsa da 'yarsa da Nasir dan haka bai iya jiran taimakon daya kamata ya jiraba sbd ko gani baayi sosai.

Rarrafawa yayi ya miqe daqyar yana jin muryan mahaifiyarsa sama sama tana ambatar sunansa cikin matsanancin tashin hankali da sarewa tareda yankewan murya.

Girgiza kansa yayi da karfin gaske har saida jininsa ya watsu sosai ya samu idanuwansa suka dan fara gani ya bude baki daqyar ya ambaci sunanta.

Nasir da yake a yashe gefe fuskansa jini sosai take fitarwa sbd mummunan buguwan da yayi shima motsawa yayi a hankali yana rarrafawa sbd baya jin komai jinsa ya dauke dip hakama ganinsa.

Haske da jijiyoyin jamian tsaro da motocin ambulances ne suka fara gauraye gurin da gaggawa ana kokarin shigowa ta inda ya zube gabaki daya dan fara fidda wainda suka rasa ransu da wainda suka raunana sosai harma da wainda basu raunana ba.

A lokacin ne idanuwan Raheem suka sauka akan mahaifinsa dayake gefe a zube cikin mummunan yanayi sbd babban ginin daya zubo a kafafunsa hakama fuskarsa jini sosai idanuwansa a bude jajir cikin mummunan hali ya kasa motsawa duk da yanajin sautin Dr fammah yana shiga kunnuwansa amma bazai iya tashiba bare bata ceto a cikin mugun halin nan.

Raheem da jiri me karfi ke diba sbd jinin dayake fita a gefen fuskansa da goshinsa dayake shiga har cikin idanuwansa gurin Sir hakeem din ya nufa yana kallan mummunan karfen chandelier nai tsinin gaske dayake seti da Dad din daga sama kuma fadowa yake kokarin yi wanda yana fado masa a tsakiyar kirji shikenan.

Wani karfin halin gaske yayi ya isa ga Dad din yana tattaro karfinsa da jarumta da karfin zuciya yafara kokarin dauke masa bangon daya danne kafafunsa amma sbd yana cikin mummunan hali da jirin jininsa dake qasa kasa daukewa yayi take hankalinsa yayi mummunan tashi dan bazai iya kallan rasa mahainfinsa akan idanuwansaba gashi abin yayo qasa sosai yana qara tahowa tareda wata babban bangon sama.

Masu kokarin shigowa bada ceto suna ganin abinda yake shirin faruwa sauri da gaggawa suka gurin janye manyan banguna dan isowa garesu suna ambatar sunan Raheem din ya janye daga gurin amma sam baida niyar janyewa bare kokarin daukewa mahainfinsa bangon.

Dad din bude baki yayi da wani irin karfin hali cikin azaba yace Raheem din yayi gaggawar janyewa daga gurin,

Bama ya jinsu cigaba da abinda yakeyi yake baa hayyacinsa ba yana jin muryan mahaifiyarsa na ambatarsa da karfi cikin mummunan tashin hankali tana son isowa garesa dan janyesa amma ba hanyar abubuwa da yawa sun raba tsakaninsu.

Tashin hankali mara misali kowa ya shiga da tension din abinda suke ganin zai faru dan haka gurin duk ya sake rikicewa,

Kuka mai tsananin gaske Dr Mum ta fashe dashi tana zubewa qasa tana kiran Raheem din hakama Dad din turesa yake kokarin yi da hannuwansa duka biyu yana basa umarnin barin gurin sbd yanda bangon saman ya rikito gabaki daya tareda tsinin karfin saiti da Raheem din dayake durqushe gaban Dad din bayaji baya gani daidai nan Dr Mum ta fasa qara me karfin gaske tana rintse idanuwanta da karfi komai nata na wani irin rawar gaske....

Dad ma hannu ya saka da karfin gaske zai ture Raheem sbd tsinin ya gama saukowa da karfin gaske sedai hannunsa bai isaba Nasir da basusan daya iso ba gurin ya ture Raheem da karfi daidai nan

Please Login or Register in order to submit comment