Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nutsuwa kafin ya dago ahankali ya kalli inda RAHEEM din yake zaune shima yana dago nasa idanuwan a natse ya saukesu akan Meenah din kafin ya daukesu yana qin kallan Dad.

Murmushin manya Dad ya sake yana dan mayar da bayansa a tsanake yana maida idanuwansa akan SANAAH wadda tayi qasa da kai cikin damuwa da dacin kirji ya bude bakinsa yace

"Babu damuwa a hakan ta tattara ta koma din ni nace"

Sake qasa da kai SANAAH tayi tana jin jikinta na mutuwa gabaki daya sbd batada zabi akan duk abinda Dad din yace.

Da farin ciki sosai Mum tayi masa godia harda fatan qarin tsawon rai da lafiya mai dorewa.

Sallamarsu Dad yayi yace su tafi suje suyi shirye shiryensu kawai.

SANAAH ce tafara miqewa ta a sanyaye ta nufi kofar ta fice kafin su Fammah din suka fito.

Danne tsananin damuwan data shiga take tayi tana dan yaqe cikin tsananin karfin hali a lokacinda suke tafiya Mum din na mata magana da farin cikin shikenan yanxu ba kowace sauran abinda zai hanasu dawowa gurinta dan tana buqatan hakan.

Rabuwa sukai a hanya ta nufi bangaren mommy su kuma suka wuce can din,

Tana isa palonsu dakatawa tayi tareda dan dafe goshinta tana jin kaman zata fasa kuka idanuwanta na sauyawa sosai.

Mommy dake zaune da mamaki ta kalleta tace

"Yaya dai?
Me yake faruwa??

Zaunawa tayi a hankali kan kujera tana sanar da ita abinda ya faru.

Shiru tayi itama cikeda rashin jin dadi sbd harga Allah batason abinda xaije ya dawo ya zama matsala babba amma kuma tinda har maganar takai gurin Dad kuma yace aje babu yanda zasu iya dole sai hakuri.

Miqewa tayi ta shige dakinta ta nufi toilet ta shige ta jingina da kofa tana rintse idanuwanta saida wasu siraran hawaye suka gangaro mata taji dan nauyin daya danne kirjinta ya fada.

Bayan ta fito xaunawa tayi bakin gado tana dan dafe kanta.

Acan ma gurinsu Dad bayan ficewansu babu abinda Dad yacewa Raheem wata maganar ma ya janyo musu sbd yasan shima Raheem din bazai taba cewa komaiba tsabar miskilanci.
##MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

58
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Sai dare sosai bayan fammah ta gaji da jiranta akan kayan baccin sakawanta da zatai shirin bacci ta biyota tukuna suka hada kayansu a luggage biyu Safiya taja musu suka fice.

A cikin iyayenta fammah tayi fira sosai har daren ya qara yi tukuna taje nemo SANAAH din dan Mum ta dauka ma sai goben SANAAH ita zata taho so koda suka dawo da fammah already sun shige itada Dad din.

Bedroom din fammah din suka shiga Safiya ta tsaya fira tana jere musu kayansu a closet tana tsokanarsu da cewa gari yana wayewa zasu fara kewanta.

Firan sukeyi fammah na dan jin ciwon ciki kadan kadan dan haka taje tayi wanka tazo tayi shirin bacci ta kwanta take bacci ya dauketa cikinta na dan ciwo.

Itama SANAAH wankan tayi bayan Safiya ta wuce tayi shirin bacci ta rage hasken dakin sosai taxo ta kwanta.

Tsakiyar dare sosai wani irin mummunan ciwon ciki mai tsananin gaske ya tada fammah kaman zata mutu.

Tsoro mai tsanani da tashin hankali SANAAH ta shiga dan haka ta janyo wayar Fammah din ta bude ta nemo numbern Mum ta saka kira jikinta na dan rawa sosai sbd tashin hankali da tsananin tsoro ganin yanda famman keyi kaman zata rasa ranta.

Har wayar ta yanke baa daga ba dan haka ta sake saka kiran tana rungume famman a jikinta wanda duka jikinta yake neman saki.

Cigaba da danna kiran tayi dayake wayan na silent ne sai a kusan kira na tara sai Mum din ta daga cikin bacci tace

"Yes fammah"

Jin muryan SANAAH da abinda ta fada ya sakata bude idanuwanta gabaki daya gabanta na mummunan faduwa.

Tashi zaune tayi tana yaye lallausan rufan dayake jikinta ta ziro kafafunta qasa batareda tayi tinanin ko tada Fleet ba ta nufi kofa ta fice da wayarta a hannu hankali tashe kafafunta na rawa dan kuwa tsananin son datakewa 'yarta ya wuce yanda take son rayuwarta komai zai iya samunta idan ta rasa fammah.

Hankali tashe ta iso dakin sanye da wasu kayan bacci riga da wando har qasa masu kyau da suka kwanta a jikinta.

SANAAH na dago idanuwanta kallo daya tayiwa Mum din ta sauke idanuwanta cikin damuwa sosai ta sake tallafo fammah din daga jikinta idanuwanta sunyi jajir hawaye na neman fitowa daga cikinsu.

Da sauri Mum ta iso gadon tana kamo fammah da sauri da tashin hankali tace

"Meya faru?
Meya sameta?
Me taci??

Wasu hawaye ne suka fara gangarowa SANAAH ta girgiza kai tace

"Bansaniba kawai ciwon cikin ne ya tadamu,muje asibiti pls Mum"

A rikice Mum din ta sake tattaro Fammah jikinta kafin tace komai famman ta feso wani amai a jikin kayan SANAAH mum na ganin hakan ta sake jan bayanta da karfi wani aman ya sake fitowa.

Saukowa sukai da ita gadon tana sake jin wata azabar.

Fita mum tayi ta nufi bedroom dinta ta hado wasu magani acikin kayanta dan bata rabo da yan maganin buqata ta tinda tasan aikinta.

Tana dawowa maganin ta bude SANAAH taje kitchen da sauri ta dauko warm water ta kawo suka bawa Fammah din daqyar tana juye juye.

Tashin hankali da firgici suka fuskanta a tsakiyar daren batareda sanin kowaba dan ita SANAAH tsoro ta shiga sosai na ganin yanda famman keyi itama Mum din ta fice hayyacinta amma sbd batajin akwai likitan dazata iya barwa duba famman tinda itama karatun datai kenan yasakata kafewa akan dubata din tana bata taimakon da suka kamata har kusan asuba tukuna ciwon ya fada Mum ta kamata itada SANAAH din suka maidata dakin Mum sbd Dakin nasu ya hargitse.

Wani bacci mai karfi ne ya dauke Fammah din take dan haka a tare suka sauke ajiyan zuciya idanuwan SANAAH sunyi jajir tayi kuka harta gaji wanda sai lokacin Mum ta dan rungumeta tana rarrashinta da kulawa tukuna tace taje tayi wanka tayi sallah saita kwanta tayi bacci sbd shikenan kuma insha Allah famman ta samu sauki.

Juyawa tayi ta fice ta koma dakinsu itama Mum wayarta ta dauka ta turawa Fleet dan batason kiransa ta katse baccinsa duk da tasan lokacin tashinsa yayi tinda lokacin sallah yayi na asuba ta rubuta masa sakon Fammah ba lafiya sosai daqyar suka samu takai safiya.

Tana tura masa ta jefar da wayarta kan sofa ta fada toilet tayi wanka sbd duka jikinsu na buqatan wanka.

SANAAH tana komawa dakin itama fara gyarasa tayi cikin sanyi ta sauya beddings din ta fitar da komai zuwa dakin da babu kowa ta kunna humidifier koina ya gyara qamshi na tashi a hankali tukuna ta shiga bathroom tayi wanka a natse har lokacin jikimta a mace yake ga idanuwanta sun sauya sosai sbd dan kukan datai sai ajiyan zuciya take saukewa ahankali.

Tana gama wankan ana tada sallah dan haka ta fito ta sauya kaya ta zira doguwan hijab har qasa akan bayan baccinta data sauya ta tada sallah.

Tana gama sallah addua tayi har lokacin jikinta a tsananin sanyaye yake kaman zazzabi taji zai shigeta da ciwon kai dan haka tana gamawa miqewa tayi ta shige gado a hankali ta kwanta tareda shigewa quilt tareda rufe idanuwansa babu jimawa bacci ya dauketa tana sauke ajiyan zuciya a cikinsa akai akai.

Gari ya dan fara haske kadan ya baro Masallacin cikim villah din da sukai sallan asuba ya nufi bedroom dinsa kai tsaye yana shiga wayarsa ya dauka zai duba sai ya ga sakon Ms Meenah yana karantawa wayarsa ya ajiye a natse ya juya yabar dakin ya nufi bedroom din fammah kai tsaye.

Kai tsaye bude dakin yayi da shigowa ciki sanye da Farar luxury jallabiyar daya dawo sallah da ita a jikinsa.

Bataji motsin bude kofar da akai ba aka shigo sbd baccinta daya dan kokarin karfi yana yankewa sbd ciwon da kanta yakeyi.

Akan gadon idanuwansa suka sauka yaganta a rufe ta bada baya Mum dinta dayayi tinanin samu a tareda da ita yaga bata dakin dan haka daga kafafunsa yayi da tsantsar kulawa da kauna mai karfi ya isa bakin gadon ya zauna a tsanake qamshinsa na fara gauraya dakin a sanyi sanyi.

Hannunsa ya miqa da kulawa ya nufi kanta dashi ita kuma a jin zaman mutum abakin gadon datake kuma a baki baki take ya sakata bude idanuwanta da sukai dan nauyi suna wata irin shigewa cikin sanyi da rashin kuzari ta taso gabaki daya tareda juyowa kai tsaye a tinanin fammah ce shikuma daidai nan hannunsa ya kawo sai kawai ya sauka akan fatar wuyanta ta kallesa da sauri cikin wata irin firgicin daya sakata fasa kuka kawai t hannunta daya na sauka akan kafafunsa ta damqi rifarsa da karfi dayan hannun ta dafe kirjinta daya kusa bugawa da attack na firgita tana rintse ido.

Shi kansa yashiga shock da ganinta amma kasancewansa jajirtaccen jarumin da tsoro baya shigarsa sam ko firgita sai babu abinda ya bayyanarda shock daya shiga ya tsayar da idanuwansa akanta kafin ya kalli hannunsa dayaji dumin fatar wuyanta yana shiga tafin hannunsa na dan zazzabin dayake jikinta ya motsa hannun kadan dan tabbatarda zafin da jikin nata yayi.

Bude idanuwanta tayi tana janye hannuwanta ahankali daga damqan datai masa tareda qin dagowa sbd sai a lokacin takejin dan sanyin tafin hannunsa akan fatarta ta taso janyewa zuwa baya amma tana motsawa kirjinta zai iya haduwa da nasa sbd ya dan rankwafe yake akanta daman gurin tabata tin farko dan haka ta dago a natse ta dago idanuwanta data qi barin su kallesa sbd ta motsa hannunta daya takai wuyanta dan son janye nasa hannun amma ta kasa dora hannunta akan nasa din dan haka dole ta dago idanuwanta da sukai wani iri da kuma hawayen d suka fito cikinsu ta dora akan fuskansa cikin Slow din daya sakasa sake tafin hannunsa sake kama wuyanta idanuwansu na shiga cikin na juna take kamannin da baya iya taba dena tinawa suka bayyanar masa ya dauke idonsa da wata irin kamewansa yana na janye hannunsa daga wuyanta ya miqe tsaye yana dan bude baki da muryansa da sai yau ta shigeta sosai sbd sun kusa sosai yace

"Ina fammah din take???

Kasa bude baki tayi sbd zazzabinta daya ninku ya qara mata yawa take da hannu ta nuna masa gefe alaman dakin Mum tana qin dagowa.

Ficewa yayi batareda sake ko waiwayowaba.

Yana ficewa itama zamewa tayi ta koma ta kwanta tanajin zafi na sake rufe jikinta.

Yana fita dakin Mum din ya nufa yaga bacci sukeyi ya kalli fammah tareda shafa kanta ya juya ya fice da alaman ta samu sauki.

****Dad kuwa da tin jiyan da Meenah tayi masa rokon komawan su SANAAH gurinsu yakeson isarwa da Uwar mijinta sakon da zai sakata daukan matakin da zata kawo kanta Nigeria dan haka ya daga wayarsa ya kira Maamah wadda ta zama kaman yar isar da sako a tsakaninsu tsawon shekarun.

Tana dauka gaidasa tayi suka gaisa kaman yanda suka saba ya fara da cewa

"Masha Allah sannu da kokari Fatima,
'Danki yaji nasihar dana buqaci ki masa dan yanzu haka dashi da iyalinsa duka sun hada kai suna zaune kalau da duka matansa duk da haryanzu Matarsa batadan wacece take zaune da itaba dan haka haka zan sanar mata da kaina tinda babu wanda ya sanar mata haryanzu har shi mijin saiku kara kiranta ku rarrasheta tinda nasan al'adarsu ta haramta musu hakan"

Shiru Maamah tayi cikeda shock da mamaki mai tsananin gaske dan haka batama san yanda sukai sallama ba dashi ta kallo Dr Mum dake gefenta tana aiki da laptop da glass dinta mai kyau ta rasa ta inda zata fara har saida Dr Mum din ta kalleta tace

"Lafiya dai Maamah" dan itama hakan take kirant ita kuma tana kiranta DR

Numfashi Maamah ta sauke tareda sanar da ita komai.

Aje laptop din Dr Mum tayi tana kallan Maamah da wani irin sabon baqin ciki da takaicin dayake danne kirjinta akan Meenah da Hakeem dan kuwa tasan Meenah batada lissafi ko daya tanada wani irin neman a sani da alfahari mai yawa wanda zai iya sakata a tsaka me wuyar da bata sani ba gashinan taje sun hade kai da kishiya batareda sani ba hakama babban tashin hankalin shine zaa sanar da ita a qasar daba tata ba kuma zata iya aikata abinda Hakeem zai kafa hujja dashi ya sama Raheem sallamarta kokuma ma zata iya cinnawa jeerahs wuta ayanda tasan haukanta da tsananin kishinta dayafi nata......

Jin tayi tinanin abubuwa kala kala suna zuwan mata na abinda zai iya faruwa dan haka taji kanta yayi nauyi tsananin baqin cikinta na qaruwa wanda take zuciyar taurin rai da rashin dangana ta asalinsu ta taso mata na bazama ta hakura komai ya lalace ba wata macen ta Raheem daga hannunsu dan haka gwara taje ayi wadda zaayi dole wani auren ya mutu koma na waye ita dai Raheem inde itace ta haifesa bazai zauna da macen da bataso ba.

Aikin datake kasa qarasawa tayi ta dauki wayarta dake gefenta ta nemo Raheem din kai tsaye ta saka kira tana gap da yankewa ya daga kiran kafin ya furta kowace kalma tace

"Ina tafe Nigeria a tanadarmun gidan zama da zan zauna"
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

59
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki  Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki  Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce  For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Tana gama fadan hakan ta yanke kiran tareda ajiye wayar gefenta tana dan dafe goshinta da hannu daya sbd ciwon da kan ya fara a take.

Maamah kallo take binta dashi jin kalaman data isar da sakonsu wanda har abada babu wanda ya saka ran zata sake zuwa Nigeria amma yau da bakinta take fadan zata tafi.

Numfashi Maamah ta sauke sbd itakam daman tana tsananin son samun daman zuwa Nigeria duk da bata hakan taso tafiyar ta taso ba.

Shi kuwa a can nasa bangaren nutsuwa yayi ya aje wayarsa gefensa tareda dan mamakin kalaman Dr Mum din amma kuma shi ba maaboci tambaya bane bare ga Dr Mum dayasan zafi kawai zata qara dan haka koma me zai kawota baida say akai bayan tanadar mata lafiyayyam gurin zama.

A lokacinda kiran ya shigo masa yana tareda Ms Meenah ne da safen zasu fito breakfast dan haka kaman yanda take ta saba bata damu da tambayar meyake faruwaba ta fara jero masa wasu zancen suka fito kai tsaye zuwa dining room.

Su kadai ne a table din sedai ko fara serving dinsa Mum bataiba Fammah ta qaraso dining din jikinta ba qwari sosai amma ta warke kalau bata jin komai bayan kasalan dan hakane ma tana farkawa kusan after 9 kadan tayi wankanta ta saka kaya marasa nauyi ta fito cin abinci sbd samum karfinta ya dawo ganin SANAAH na bacci har lokacin ya saka bata tada itaba ta kyaleta tan tasan tana buqatan baccin tinda basu samu sunyiba da daren a sanadin ciwonta.

Gaida Dad dinta tayi wanda yake kallanta da kulawa mai nutsuwa kafin ya miqa mata hannunsa ta kama tana dan dawowa gefensa ya shafa kanta yana mata sannu da fatan sake samun lafiya mai dorewa.

Breakfast dinsu suka fara sai a lokacin Mum ta dago ta kalli Fammah tace

"Ina Baby SANAAH?
Meyasa bata fito breakfast ba??

Cikin rashin iya daga murya Fammah tace

"Tana bacci haryanzu sbd kinsan sam bata rintsa ba cikin daren kuma yanzu sai kiga tafara zazzabi sbd hakan coz she's too sensitive"

Shiru Mum din tayi tana cewa

"Bare kin daga mana hankali sosai fa a jiyan tayita kuka dole ma zatai ciwon kai"

Shiru suka sake yi kowa na cin abinci a natse har suka gama babu wanda ya sake cewa komai suna baro dining room din kai tsaye fammah daki ta koma gurin SANAAH ta kwanta itama Mum kuwa mijinta tabi zuwa palonsa sika koma.

Bayan kusan awa daya sai ga Imran na knocking kofar palon farko maana main sitting room din tareda budewa ya shigo da wata sabuwar qwararriyar likita itama halfcast ce ya nuna mata guri ta zauna ya daga wayarsa bai kira Fleet ba sbd sanin abinda yakeyi kai tsaye Fammah ya kira.

Tana dauka ya mata ya jiki ta amsa a dan natse kafin yace

"Ga Dr zata duba ku tana sittin room zaune"

Dan shiru tayi tareda kasa fahimtar kalmar "ku" daya ambata sai ta juya a natse ta kalli SANAAH takai hannunta ta tabata taji jikinta yayi wani irin zafi sosai ta kalleta da dan sauri tana mamakin da gaske dai batada lafiyar itama.

Batada kowace irin doguwan nazari da hada lissafin tinanin komai na rayuwa wanda hali ne da Mum dinta data gado dakyau dan haka batai tinanin komai ba na yanda Imran ya saniba ta kalli wayarta tana gyara zamanta a kunnenta tace

"Gamunan fitowa SANAAH dince ba lafiyan yanzu sosai"

Kashe wayarta tayi tareda son tada SANAAH din amma kuma sai ta fasa ta sauk gadon ta fita zuwa sitting room din.

Tana isa gaisawa da Dr din sukai cikin yar kokarin riqe kuzarinta dayake dawowa tace su tafi can daki ta duba SANAAH din.

A bakin gado ta zauna tareda dan miqa hannu ta yaye rufar SANAAH din tana sake taba jikinta zafin sosai yana nan dan har wani hucin zafi ne ya fito daga rufarta data yaye.

Sake shafata tayi tana ambatar sunanta da sanyi.

Ahankali ta bude idanuwanta bayan ta farka daga baccin datakeyi din.

Bata motsaba idanuwanta kawai ta sauke akan fammah din tana jin karfin zazzabinta na qaruwa.

Sanar da ita Dr zata dubata fammah tayi da kulawa tana taimaka mata ta tashi zaune.

Kallan dr din tayi tareda bude baki cikin dauriya ta gaidata tana kallanta.

Dr tasowa tayi ta iso gurin SANAAH din fammah ta bata guri ta zauna gefen gadon tana fara dubata da tsananin kulawa da yan tambayoyi.

Yanda SANAAH din takeda sanyi da rashin sauri ko hayaniya a komai bare yanxu datake cikin tsananin zazzabin ya saka suka dauki time kafin suka gama tukuna ta duba Fammah itama wadda ta sake jinta ta warware sosai batajin komai.

Bayan lokacinda Dr ta bata mai tsayi ta wuce SANAAH ta samu ta sauko gadon ta isa bathroom ta shige tayi brush da sauran abubuwanta kafin tayi wanka da ruwan zafi sbd taji ko zata samu karfinta da abinda takeji na zazzabin ya sauka.

Tana fitowa sama sama ta iya dan shafa body mist na oud mai sanyi da tsada ta saka silk riga da wando marasa nauyi ko kadan ko bra bata iya sakawa ba tasha tea kadan akan tirsasawan Fammah tukuna tasha magani ta koma ta kwanta sbd kanta tsananin ciwon gaske yakeyi.

Tana kwantawa bacci ya dan sake daukanta fammah ta kashe mata wayarta sbd kada a bata kowace irin hayaniyar da zata hana ciwon kanta sauka.

Mum kuwa jinsu shiru ta fito tana waya ta nufa dakin ko data shiga taga halinda SANAAH take ciki dan haka ta nuna damuwanta da kulawanta itama dubata tace su bawa SANAAH din isashen hutunda har sai ciwon kanta ya sauka kada a bata kowace hayaniya.

Fitowa sukai suka barta bayan ta sake samun bacci,
Fammah bangaren Mommy ma takeson tafiya dan tabar SANAAH ta samu hutun itama taje can ta kwanta tayi hutunta acan.

Mum ma gurin Rabin ranta ta wuce acan take sanar masa SANAAH din ba lafiya sosai kaman Dad ne ya aiko Likita ta dubata sedai sai ahankali jikin nata kila zuwa yamma ta warware.

Baice mata komaiba wayarsa dake hannunsa yake ci gaba da dubawa batareda bawa zancenta hankalinsa ba kokuma alaman yamasan abinda take fada.

Safiya ce ta shirya musu dining da rana sukai lunch guraren karfe uku da mintina kafin suna gamawa Mum ta sake zuwa ta duba SANAAH dake bacci har lokacin bayan tayi sallan azahar daqyar ta koma ta sake kwanciya da rufe jikinta duka.

Ganin bacci take ya saka Mum itama barin bangaren bayan Safiya ta sake tattara komai fes ta bar bangaren itama.

Gurin Mommy ta tafi suka baje suna firarsu bayan ta sanar da mommyn SANAAH insha Allah taji sauki tana tashi lafiya kalau zata tashi.

Mommy ma sbd kara bata damuba firar su sukeyi hankali kwance da shagala gashi daman duk taxo bangaren sai dare ko magrib take komawa.

Sunacan sunata firarsu fammah ma bacci me nauyi ne ya dauketa bayan azahar dan baka babu wanda ya sake zuwa dubota.

Bayan sallan laasar wata kishirwa da yunwa mai tsananin gaske ta tada ita daga baccin bayan dan zazzabin ya dan saukar mata dan haka ta farka tayi shiru tana jiran zuwan wani dan tana tsananin buqatan ruwa tasha amma me dumi takeso sbd yanda takejin kaman zatai amai.

Shiru babu wanda ya shigo dakin dan haka ta tashi zaune ahankali da tsananin rashin karfi da da jiri sosai sbd rashin komai a cikinta.

Idanuwanta da sukai wani irin laushi da bayyanarda wata irin kasala da lumshewa akai akai ta juya ahankali ta kalli dakin dayake da rashin haske sosai da aka rage mata taga ba alaman fammah bata ciki dan haka ta hadiye wani numfashi mai tsananin kasala tareda yunkurawa ta yaye duvet din jikinta ta ziro kafafunta qasa tareda dan rufe ido ta bude ahankali tanajin kaman bazata iyaba amma yanda takeji kaman zata mutu ne idan bata sha ruwaba.

Miqewa tayi tana dan dafa bango ta zira soft slippers a kafafunta tukuna tafara takawa ahankali tana rufe idanuwanta da dan dauriya tana budewa jiri takeji sosai da amai na neman yunkuro mata amma haka ta isa kofar bedroom din ta fice.

Palo ta nufa tana tafiya ahankali tana dan dafe cikinta kadan da

Please Login or Register in order to submit comment