Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan sofa ta lafe batada niyar ma ko fita palo bare zuwa dining din data yafe.

Mum ce ta shigo dakin bayan fammah ta gama shiryawa ta juyo zatai mata maganar fita breakfast.

Cikin adonta itama mum din take dan daidai ta iso tana kallan SANAAH din da bada umarni dan kawai ta tilastata fita breakfast din tace

"Ku fito dukanku oya SANAAH taso banason jin komai"

Juyawa tayi zatai fice SANAAH ta bude baki da dan sauti mai nutsuwa tace

"Banajin yunwa ba yanxu zanyi breakfast ba Mum"

Bata juyoba tace

"I dont care dole ki fito daga yau na hana wannan zaman dakin da kike wanda shine yake sakaki jin kewan gida kina wannan kukan"

Ficewa tayi SANAAH da idanuwanta suka sauya da wani irin damuwa da nauyin kirji mai karfi kasa dawo da kallanta tayi akan fammah zatai magana fammah din itama ta juya da sauri ta fice sbd itama batason wannan damuwan da SANAAH ke shiga gwara ta ringa fitowan.

Fammah na ficewa hanyar palon Dad dinta ta nufa gaidasa tana isa yana fitowa daga bedroom dinsa idanuwansa har lokacin babu saukin komai a cikinsu.

Qarasowa tayi tana dan rungumesa tana gaidasa da cewa

"You dont look good Dad,yaya kan?
Ko kana buqatan ganin likita ne Dad"

Girgiza mata kai yayi a natse yana dan kissing kanta yana bude baki wani hayaniya da son doguwan magana yace

"No Doc, alhamdllh insha Allah"

Fitowa sukai tana masa magana yana sauraronta yana saka kai a dining din matarsa datake kokarin zama fasawa tayi tana nufarsa sbd koda ta fito bai tashi ba daqyar ya iya samun baccin ko yauma sbd tsananin ciwon kan daya hanasa ko baccin arziki.

Gurinsa ta taho tareda dan rungumesa itama da kulawa tana cewa

"Good morning my love"

Bakinta takai zatai kissing gefen fuskansa daidai nan SANAAH ta sako kan da akan idanuwansa fes dan haka juyawa yayi ahankali ya kalli fammah yana dan sake mata wani kyakkyawan murmushin daya hana Meenah isowa da bakin nata sbd juyewan da yayi gurin yarsa.

SANAAH kuwa a natse da wata irin kamala ta iso tareda zaunawa a natse batareda ta dago ta kalli ko inda sukeba.

Mum na ganinta tace "yawwa koke fa baby SANAAH"

Wani murmushin da ya sakasa mata wani lafiyayyan kallo ta sake tana dan daukan cup din juice mai sanyin dake gabanta ta shanye a lokaci daya tareda ajiye cup din har saida yayi dan sautin daya sake sakasa dagowa a natse ya kalli idanuwanta da suke a kumbure hakama fuskanta datai ja.

Ko spoon din dake gabansa bai saka hannu ya tababa ya miqe yana kallan time yace bazai samu tsayawa ba ya fice yana barin Mum da hannunta tsaye datakai zata tabasa cikeda wata sakewa.

SANAAH kuwa tinda ta shigo bata kalli inda yake dinba harya miqe ya bar gurin.

Itama bata iya cin komaiba bayan juice din data ringa dirkawa cikinta tana rage zafin cikinta da sanyinsa.

Suna gamawa tabar dining din Mum rana nayi tajasu suka fita yawo.
#MAMUH
09033181070
[11/06, 3:25 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

108
Basu dawo ba sai dare dan haka tana shigewa bata sake fitowaba sai da safe wanda sbd kada ace ta fito dining ya sakata tashi da azumin lada kawai shi kuwa a ranar sbd kada ma kaucewa komai bai fito breakfast dinba haka ya fice saidai a office ya dan ci abincin a luxury restaurant dinsu abinda baima taba yiba.

Sbd tana azumi basu fita koina ba sai washe gari shima ta kuma tashi da azumin da hakanan suka fita din basu dawo ba sai dare shima.

Da safen ma kusan daga shi har ita babu wanda yazo dining dan wannan karan ta daukanwa ranta indai dining ze sakata ganinsa ta ringa azumi kenan daga yanxu har lokacinda zata tafiyarta.

Mum bata gane komaiba harkar gabanta kawai takeyi dan tanata abubuwan yi kafin ace tafiyar zaayi dan haka ta dena zama kwata kwata ita kuma SANAAH ta qauracewa fitowa kwata kwata koyaushe tana daki bata kuma barin ko a wayar yarsa yaji motsintaba,

A cikin azaba da wuya take azumin sbd sam bata iya jure yunwar amma taurin ranta yaqi barinta denawa,

Shi kuwa sati daya akai ana hakan ya hakura ya fara fitowa dining din sbd tinanin ganinta amma sam bata zuwa ta dauke wutarta koina kaman bata gidan.

Sati kusan biyu aka kuma dauka tana cikin wannan halin bai kuma taba sakata a idanuwansa ba ko motsinta bai taba ji ba,

Ana cikin hakan ta sake daga hankalinta gabaki daya ta tada na mutanen gidan da gida takeso ta hana kowa sukuni kaman qaramar baby dan ko mum da batada damuba tashi hankalinta yayi da ganin yanda SANAAH din duk ta rikice da rigimar gida takeso,

Kowa a cikinsu rarrashi da tarairayanta yake akan ganin ta nutsu amma sam ta rufe idonta rigimar da basusanta da itaba ta ringa musu da aikin kuka.

Duka wannan tashin hankalin datake yana sane dashi amma taqi barin ya ganta ko kadan ta saka zuciyarsa a matakin da ko fita aiki ya dena kwata kwata hakama koyaushe yana office din cikin gidan yana bawa Meenah daman futa duk inda takeson zuwa da dawowa duk lokacinda taso sbd ita ta kwantar da hankalinta ko yayane tabari ya ganta yaji abinda yake damunta da rarrashinta amma sam ta bijire karshe ma sbd kada ya ganta Mum din take bi su fita sau dare.

Karshe Dad dinta ta kira ta sanar masa tanason dawowa gida ita.

Dad jeerah dake jiran a tabata yayi musu abinda zasusan da shirunsa na jira ne yanajin ta fada hakan ya sanar dasu su dawo masa da Yarsa dan baisan zama a matsayin me takeyi acanba abasa ita tinda dai haryanxu baiji labarin an bata matsayinta ba.

Sake rarrashinta Mum tayi da fammah amma ba alaman zata hakura dan haka dole aka fara shirin komawan.

Shi kansa tafiya ce a gabansa mai mahimmancin daya kamata yayi tin last week amma ya kasa tafiya koina din dan haka shima ya yanke hukuncin komawan tasu Nigeria din indai hakan zai saka ta sauko ya kuma samu ganinta.

Imran aka saka ya fara shirin tafiyar tasu wadda ta daka Mum zama busy sosai da gaske sbd ta gama duka abubuwan datake so kafin ta tafi din.

Fammah ma duk yanda SANAAH din ta koma musu rigimammiya haka ta ringa lallabata suna fita nasu yawon da yin siyayya da yan abubuwan datake buqatan yi kafin barin qasar.

Ba tareda shi zasuyi tafiyar ba dan shi saiya biya Miami dole kafin ya samesu dan haka ana saura kwana daya su wuce akai musu reserving wani lafiyayyan luxury lounge a wata royal restaurant da zasuci dinner dinsu acan.

Bataso zuwa ba amma babu yanda zata iya qin zuwan tinda kowane zaa tafi dashi hakama tinda na bankwana ne sai kawai ta shirya bawani walwala a tattare da ita suka fito ta dan rame tayi fayau tana sanye da wasu Beige kala riga da skirt da suke straight sun dan lafe mata sai doguwar jacket data saka akai da dan rolling dinta sai jimmy choo takarmin dake kafarta fammah na riqe da hannunta wadda ita kuma riga da wando ne a jikinta dusty rose kala.

Koda suka fito already motarsa a kunne take wadda yana ciki a rufe fitowansu dake jira ya sakasa dagowa da kansa ya kalli kofar da suka fito din da wani lafiyayyan slow ya sauke idanuwansa akanta da suka sauya a take zuciyarsa na warware ahankali daga mummunan nauyi da daurewan datai ya zubawa fuskanta idanuwansa yana mata wani lafiyayyan kallan data fara jinsa a jikinta take dan haka ta dago nata idanuwanta da slow itama ta dauke akan glass din motar wanda idanuwansu suka shiga cikin na juna.

Itace ta dauke nata a natse suna isa motar dake bayan tasa da aka bude musu suka shige a natse aka rufe.

Mum ce ta fito kai tsaye sanye da butter colour free silk gown da rollin din mayafin rigar ta qaraso aka bude mata gefen motar dayake ciki ta shige take aka ja motocin suka bar gurin.

Tafiyar da batafi 30 to 40 min ce takaisu inda zasu din suna isa a bakin kofar shiga aka tsaya dukansu suka fito a da wata irin steez da kamewansa manager da kansa ya fito ya tarbesu suka wuce ciki akaja motocinsu akai gurin parking dasu.

Suna shigewa kai tsaye Vip lounge room dinsu aka nufa dasu wanda suna shigewa security biyu sika tsaya bakin kofar aka rufe ruf.

Lafiyayyan table ne da tsarin da kana shiga kasan sai masu abin dan haka zaunawa sukai dukansu bayan an bude musu electric curtains din babban balcony din lounge din da wani babban swimming pool ke gurin iska da dan sanyin ruwan na bugo musu yana qarawa yanayin dadi da nutsuwa.

Ana zaunawa SANAAH taji tana kasa numfashi daidai sbd kamshinsa daya shigarta direct yana kokarin tado da damuwanta da wargaza kuzarinta.

Shi kansa ita ya kasa daukewa idanuwansa duk da yana sassautawa dan fammah 'yarsa da itama yake jinta cikin rai da jininsa.

Waiters na musamman guda biyu aka aiko wainda Mum ta fara basu ordern lafiyayyun abinci da desserts tareda drinks da suke buqata.

Ruwan da aka fara jerewa SANAAH ta saka hannu ta dauka sbd zufan dataji tana ji a cikin jikinta takai bakinta tasha tareda miqewa tsaye da cup din a hannunta ta nufe gurin da iskan ke kadowa ya dan bugeta dan kuwa wani tense yanayi takeji da kallansa da heat ke taso musu su duka biyun tako ina.

Ma miqewa tayi tana isa gurin SANAAH ta shaqa iskan mai sanyi wanda ya ratsata itama dan juyowa SANAAH tayi ta kalleta kafin ta juya kadan ta kalli inda su Mum din suka idanuwanta ta nasa da suka kalleta daidai lokacin suka hadu taji iskan baya isarta ta ajiye cup din hannunta a hankali gefe tana juyawa da bude baki kadan tacewa fammah she needs washroom.

Mum ce ta iso gurin tana waya da cup a hannunta itama daidai barin SANAAH gurin tazo ta wucesa batareda ta kallesaba tabi wata yar hanyar dake rufe a cikin gurin ta shige washroom dake dakin.

Tana shiga ta tsaya gaban makeken mirror din dayake ciki ta dago idanuwanta zata kalli kanta ba tsammani ta gansa bayanta tsaye ya dago idanuwansa da suka saka tsigar jikinta miqewa ta juyo ahankali tana kallansa da nata idanuwan da suka tsaya akansa cak.
#MAMUH
09033181070
[12/06, 8:10 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

109
Ajiyan zuciya ya sauke mai tsananin sanyi a hankali a kuma bayyane sbd zuwa yanzu dukkanin hakuri da kamewansa tareda riqewansa da duba su Meenah akan su gane duk ya qare masa bazai iya daukaba kwata kwata.

Its kanta zuwa yanzu din taji jiki sbd azabar da zuciyarta ta ringa sha kuma take kan sha dan haka ta dan dauke idanuwanta ahankali daga kallansa tana juya masa baya cikin sanyi tana qin kallansa ko ta cikin mirror din.

Hannunta takai zata kunna ruwan da batasan mema zatai dasu ba taji saukan hannunsa akan nata ya riqo tareda riqewa cikin nasa ya sake sauke ajiyan zuciya tareda juyota gabaki daya yana dan matseta sosai suka jingina da mirror din dayake bangon.

Qin kallansa tayi tayi kokarin janyewa amma sai saukan hannuwansa duka biyu taji a qugunta ya zagayota tareda mannota ahankali jikinsa sukai wata hadewan data sanyata dagowa ahankali ta kallesa tana son bude baki tai magana amma kuma ta rasa abin fadan dan haka zata sake dauke idanuwanta daga kansa ya tare fuskanta da tasa ta hanyat hadesu guri daya suka sake ajiyan zuciya a tare wanda ya sakasa ja da shaqar numfashinta daya ratsashi ya jisa har jikin kwakwalwansa ya lumshe idanuwansa ya bude ahankali yana bude bakinsa da wani sanyayyan sauti yace

"Pls wannan fushi da fadan ya isa haka i can't take ita anymore plsss SANAAH KHALIL"

Rufe idanuwanta tayi ahankali tana girgiza masa kai batareda tasan ma tana girgizawan ba take yaji hankalinsa ya qara rushewa ya dan sake mannota jikinsa suna jikin bangon mirror har lokacin ya sake bude baki daqyar da wani galabaitaccen sauti can qasa yace

"Meye laifin?inason sani,Raheem zai hana fleet sake yinsa just tell me menene matsalan bcoz this is madly killing me...

Qarasa maganar yayi yana shigewa jikinta kaman qaramin yaro wanda hakan ya sakata bude idanuwanta tana kallansa shima ita din yake kalla idanuwansa na mata wata irin kallan dayake bayyanarda galabaituwansa ta dan dauke kai kamshinsa na sanyaya zuciyarta da bata wata nutsuwan da itama ta rasa ta kwanakin amma fuskanta bata nuna hakan ba ta bude baki ahankali da wani sautinta dayake bayyanarda yarinyarta tace

"Ba komai ba wani laifi ni gida kawai nakeson komawa na gaji da nan"

Bakinta ya gangara da idanuwansa ya kalla yanda take maganar tana gamawa ya dawo dasu a cikin idanuwanta tsam suka hade da nata ya bude baki yace

"Ok tinda kin gaji da nan ki shirya zamu tafi Miami"

Kallansa tayi zatai magana ya sake zagayo hannnuwansa da ita yana sake shaqarta yace

"Dole zakiyi hakuri amma zan sanar da Meenah and fammah sbd bazan iya dauka...

Girgiza masa kai tayi cikin sanyi da dagowa ta zuba masa idanuwanta ta bude baki can qasa da murya tace

"Dr Mum tace abari ya koma gida and banason fammah tayi fushi dani"

"So do you intend to kill me ne kafin a koma gidan SANAAH KHALIL??
All this kukan da fushi da hana na ganki da kikeyi this is murder you know?????

Da gaskiyanta ta girgiza kai alaman bata saniba wanda hakan ya sakasa shiga wani fitinannen mamakinta da tsananin kewanta da jinta da matiqar zafi a zuciya,jini,gangar jiki da kwakwalwansa dan daga ya saka hannunsa cikin wuyanta ya kamo kanta ba tsammani ya hadesa da fuskansa ya kama bakinta da nasa cikin wata masifaffiyar kewanta da dagaske illatasa take neman yi.

Wani kyakkyawan kiss mai ratsa kai ya zira bakinsa cikin nata yayi mata yana hade fuskansu da wani kyau.

Kwacewa taso yi amma irin riqon da yayi mata da yanda sonsa yake buge duk wani riqewanta hanata hakan sukai ta dan bude idanuwanta zata kallesa amma cikin nutsuwa ya sake kutsa bakinsa cikin nata yana mata wata tsotsan daya sakata maida idanuwan kawai ta rufe.

Kaman wanda yayi shekara baiyi komaiba ba haka yake kissing dinta da jin babu abinda zaiyi da ita yaji ya ishesa koyaushe kaman ya maidata cikinsa yakeji dan hakanne yake sake jin ko cinyeta yayi bayajin zai taba jin ta ishesa.

Da slow hannunsa daya ya zagaya bayanta yana mata wani shafa da mannota jikinsa kirjinsu na sake wata mannuwa hakama hannunsa daya yana sake manno wuyanta da kanta ga tasa fuskan suna shaqar juna direct bakinsu na hade wani mayetaccan kiss yake mata duk wani lipstick dayake bakinta da kamshin dayake cikin bakin ya tsotse tas har saida bakinsa ya sauya kala sbd lipstick dinta dik da red bane.

Itace ta iya dan janyewa tana bude idanuwanta akansa da suka sauya shima nasa tini sukai wata sauyawan dayake jin ayau matiqar bai sanarwa da Duniya matsayintaba zai iya rasa kansa dan kuwa wannan gasuwan datake masa tafi bataliyar yaqi wuyar yaqa a gurinsa dan gwara ace duk tsawon kwanakin nan yana fagen yaqi da bada wuta sunfi masa sauki akan wannan tashin hankalin da baima taba fuskanta ba ko gani.

Bata bude baki ba da idanuwanta data juya ahankali ta nuna masa kofa alaman akwai wainda ke waje suna jiransu.

Idanuwanta ya kafe da wani mayen fitinannen kallon da itama saida ya tayar da tsigar jikinta duka sbd yanda tai da idanuwan ta nuna masa kofar kashesa tayi daga tsayen dan kuwa saida ya dafa bango tsabar wani shock din dayaji.

Juya baya tayi ahankali tareda zarar tissues ta doge bakinta da duk ya yamutse ta gyara fuskanta da kyau dik da lipstick kam babusa ya fita gabaki daya ya tsotse.

Juyawa tayi ta fice tabarsa a tsaye yana hadiye mata wani lafiyayyan yawu da tsananin sonta da shi dik lamarin bai xo masa da kowace sauki ba neman zama abinda yafi wanda Nasir ya zama so dubu yake.

Tana ficewa lumshe idanuwansa yayi tareda sauke numfashi da ajiyan zuciya yana jin azababbiyar azaba kirjinsa.

Ko data fito har lokacin su fammah ba can tsaye a dan haka bata isa gurinsu ba sbd kamshinsa ne yake tashi a jikinta sosai san baka ta zauna kawai a table tareda daukan apple ta fada ci a natse wanda zai saka ayi tinanin shine ya batar da lipstick dinta.

Fammah ce ta hangota a table din dan haka ta juyo ta nufo gurin hakama Mum daketa faman waya sallama tayi itama tana biyo fammah.

Suna zama fleet din na fitowa shima ya iso gurin fuskansa a gyare shima duk da idan kai masa kallan tsaf da tsaf zaka iya hango sauyawan bakinsa sosai.

Bai kalli kowaba ya zauna a natse tukuna ya dan dago ya kalleta da wani sanyin datajisa har kirjinta itama amma bata kallesa ba idanuwanta na akan fammah wadda take dan nuna mata abu a waya daidai nan ma aka shigo da duka abubuwan da suka buqata ana turowa da jerewa a kan babban table din.

SANAAH kallo daya tayiwa duka tarin abincin ta dauke kanta musamman ganin Mum nata wani farin ciki tana dafa hannunsa da masa magana shi kuwa yana dan amsawa a taqaice.

Akan desserts din da aka jere idanuwan SANAAH suka sauka taji tsananin son cinsu da tsinkewan yawu wanda sai akan idanuwansa daya dago ya kalleta yaga yanda take kallansu da wata marmari da tsananinsu ya maida idanuwansa akansu.

Hannunsa ya miqa akai zai dauka ya bata Mum na ganin hakan ta saka hannunta akan nasa tana karba tareda saka fork ta depo takai bakinsa tana cewa

"When did you start liking deserts and eating them fleet?"

Dauke kai yayi ahankali tareda dan bude baki yace

"No ba nine ke buqata ba its her" ya qarasa fada yana dan kallan SANAAH din wadda tai saurin kallansa da mamaki da jin faduwan gaban kada dai yana kan bakar fadan abinda yayi niyar ayau.

Da sauri Mum din ta maida kallanta akan SANAAH tanajin tsananin mamaki ta bude baki tace

"SANAAH?"

Cikin wani karfin halin gaske SANAAH din ta kalli Mum din tana maida kallanta akan Fammah wadda bata damuba ta kalli SANAAH din tana daukansu ta dawo dasu gabanta tace

"Gashinan"

Mum akan fleet ta maida kallanta wani mamakin na sake shigarta da jin mugun nauyin kirji mai tsanani a karan farko akan SANAAH.

Itama SANAAH din nauyi kirjinta yayi shi kuwa fork ya dauka batareda kallan fuskan kowacensu ba ya saka a gaban SANAAH din yana daukan nasa spoon din yafara cin abincinsa da wata nutsuwa.

Mum sake bude baki tayi zatai magana ya dan kalleta a natse yace

"Pls Mrs jeerah"

Da sauri ta sake maida kallanta akan fammah wadda itama tace

"Mum pls"

SANAAH ta maidawa kallanta wadda itama ta bude baki ta katseta da cewa

"Bana buqatan cin komai I'm ok"

Jin mum din tayi duk kanta ya kulle ta shiga zallan mamakin da ita kanta batasan mema zata ce ba kuma kuma kaman kowa bayason cewanta komai.

Dagowa yayi ya kalleta ya kalli deserts din dake gaban nata zaiyi magana tai masa kallo daya sakasa shiru sbd alaman kada ma ya sake cewa komai.

Cin abincin da chops din da aka jere musu ne masu tsadan gaske sukeyi suna dan magana da fira banda SANAAH da batace komaiba juice kawai take sha kadan kadan duk tsananin son datake wa abinda yake gabanta kin ci tayi sedai kuma ta kasa kalla akai akai wanda duk abinda takeyi yana lure da ita dan haka bai wani ci abincin ba yace ya koshi ya dan miqe a natse yabar table din da tumbler glass cup din red champagne a hannunsa ya nufi balcony din dake lounge room din yana fidda wayarsa yana waya a natse.

Suma saida suka jima suka gama kowa yabar table din Mum ta nufi gurinsa su kuma suka zauna a couch suna dan firar datake sama sama a gurin SANAAH sbd yanda har lokacin yawunta basu koma daidai ba.
#MAMUH
09033181070
[12/06, 11:01 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

110
Sai dare sosai suka baro gurin koda suka fito SANAAH yunwa takeji sosai wadda ta matsu a isa gida kawai take kitchen komai dare jin takeyi sai tayiwa kanta koda qaramin sponge cake ne ta rufesa koina da whipped cream taci.

Mum da fammah kam a gajiye suke sbd sunci abinci sosai hakama basu baro ba sai da aka kawo wani tsadadden fruit island platter da babu kalan fruit din da babu da zuma da wata kakkuran madaran da itama take hade da cream mai dadi haka sukaci suka kuma koshi banda ita da ba abinda yake ranta ba kenan shi kansa baici ba sbd zaqi ba abinda yake sha bane.

Suna isowa kai tsaye kowa dakinsa ya nufa dan gajiyan sosai da bacci ma kowa keji.

Mum mijinta tabi suna shiga wanka kawai ya shige a natse ya fito ya shirya cikin off-white riga da wandon bacci masu kauri kafin ya dora babbar jacket akai ya fito ya wuce office dinsa na cikin gidan duk da dare ne yanada aikin da komai dare zai tura sbd tafiyarsa zata dagu ne saiya samarwa SANAAH da visan tafiya can din su tafi tare.

Mum data ke jin bacci da gajiya sosai bata damu da aikin da zai tafi yi dinba duk da tasan tana buqatansa sosai sbd tafiyar da zasuyi goben su rabu amma koshin datai sosai ya saka jikinta mutuwa dan haka wanka tayi anan dakinsa tayi kwanciyarta take bacci kuwa ya dauketa.

Fammah ma wanka kawai tayi ta saka kayan bacci ta kwanta bacci mai karfi.

SANAAH ma wankan tayi ta saka kayan baccinta ta fito daga dakinta ta nufi kitchen kai tsaye.

Tana shiga kai tsaye fara kokarin hada abubuwan kwaba cake dinta tayi tareda sake jin kwadaituwa da ci tana gama fidda komai ta xuba ta saka hannu da whisker kenan taji kaman motsin kofar babban palon dan haka ta isa gurin hasken kitchen din ta ragesa sosai tabar wanda zata danga abinda takeyi ta dawo taci gaba da aikinta tana gama kwabawan ta nufi inda zata dubo inda zata gasa ta sake jin motsin shigowa daga kofar palon ta dan dakata sai kuma taji kirjinta yayi wani irin nauyi da wani qamshinsa dataji ya ratso hancinta ta juyo ahankali daidai isowansa bayanta har saida kirjinsu yayi wata haduwa tayi baya sedai ko gama bayan bataiba ya zagayota da hannunsa daya yana dawo da ita jikinsa da wani irin slow din da suka kuma haduwa gabaki daya suka kalli juna a tare idanuwansa a cikin nata da sukai wani raurau tanajin kawai kuka takeson masa na halinda take ciki na aikin.

Hannunsa daya ya dago mata ahankali wanda yake dauke da qaton box din data kalla ahankali tana miqa hannunta daya zata taba ya janye ahankali tareda ajiyewa akan kitchen island din dake tsakiyar kitchen din ya dauketa cak ya dora akai itama ya zaunar kafin ya saka hannunsa daya ya bude mata box din wanda idanuwanta suka sauka akan duka deserts din da aka kai musu a dazu wanda wannan ma hadda qarin wasu take taji wani irin sanyi da farin ciki data manta rabon dataji a kwanakin ta kallesa da sauri tareda sake murmushi batareda ta saniba dan kuwa jin tayi hannuwanta na rawan takai bakinta.

Wani murmushin mai kyau shima ya sakar mata yana saka hannunsa da kansa ya dauko yakai mata bakinta ta bude da sauri ta amsa tana lumshe idanuwanta da mamakin kanta datake jin irin hakan akan abinci yanzu.

Cinyewa tayi ya sake saka mata a bakin ta cinye da sauri tana sake karba,

Daga karshe riqe hannunsa tayi a bakinta ta cinye na hannun nasa gabaki daya tareda sake dauko wani da hannunta takai bakinta tareda bude baki tace

"Thank you"

Zuba mata ido yayi yana kallan yanda take ci cikeda jin dadi da qaguwa yana jin kaman ya cinyeta irin hakan shima...

Hannunsa daya yakai gefen lips dinta ya goge mata wanda duk take bata bakinta dashi ya kai bakinsa a natse ya dan tsotse kadan yana jin zaqi kaman yayiwa abin yawa.

Fridge ya isa ya bude ya dauko robar ruwa mara sanyi sosai ya dawo gabanta ya tsaya ya bude mata yakai mata bakinta yana cewa

"Kici ahankali kada ya dameki ok"

Ruwan ta dora bakinta akai tasha tana kallan fuskansa da shima ita yake kalla tana shan ruwan kaman baby ta janye bakinta tareda cigaba da ci yana kallanta batareda dauke idanuwansa akanta ba da suke samun wata irin wadatacciyar nutsuwar ganin yanda ranta yayi dadi sosai da abinda taci din.

Koshi tayi ta bar sauran ta bude bakinta alaman ruwan takeso ya sake kai ruwan bakinta yafara bata tanasha ahankali harta koshi shima ta

Please Login or Register in order to submit comment