Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a natse tana cewa

"Mum sannu da dawowa,ya hanya??

Da murmushi itama ta amsa tana cewa

"Ni naga babyna kaman ta rame,yaya hakane SANAAH? Kinyi kewanmu ko??

Dan karfin hali kawai SANAAH tayi tareda gyada kai tana maida kallanta kan Mommy tace

"Mommy sannu da dawowa ya hanya?

Amsawa mommy tayi da dan kokarin saka a washe a kama wani zancen.

Bude baki SANAAH din tayi tana dan kallan Meenah tace

"Ina Fammah???

Kafin Mum ta bata amsa famman ta fito tana jan hijabinta ta baya da cewa

"Gata anan"

Juyowa tayi da wani irin Murmushi mai girma da fadi daya bayyanarda farin cikinta sosai ta miqe tana komawa gefenta ta rungume hannunta daya tana shigewa gefenta da cewa

"Kuka zanyi ma ni na kewanki danai"

Dariya famman tayi tana kallan fuskanta data narke da kuma farin ciki tana cewa

"Ai nasan kila ma kinyi kukan da bananan"

Daki sukai suna barin palon kowa na binsu da dariya da kuma komawa kan firarsu.

Dr Mum ce ta kalli Meenah tace ta tashi taje ta huta tinda andawo daga tafiya.

Bata fice ba sai data zauna taci abinci a bangaren ta qara bata lokaci sosai tukuna ta bar bangaren ta nufi nasu.

Tana isa wanka tayi tayi shirin bacci ta nufi bangaren miji.

Koda fammah da SANAAH suka gamo suma suka iso bangaren Mum din bata nan dan haka shirin bacci sukai suka kwanta.

Lafewa SANAAH tayi a gadon gefen Fammah tareda lumshe idanuwanta tsawon lokaci ta dauka sosai kafin bacci ya iya daukanta dan haka da safe tayi lattin tashi sosai duk da kusan kowa a bangaren lattin tashi yayi dan fammah ma akwai gajiyan tafiya Mum ma hakan dan haka koda suka tashi ma Fleet baya gidan ya fice ko breakfast duk yanda Ms Meenah taso tayi dashi bata samu daman hakan ba dan kuwa bai bari sun gansa ba.

SANAAH ma sbd kada ta gansa a dining din taqi tashi da wuri sai gashi Mum din ta takura mata da cewan ai shima baya nan kada su rasa ci da junansu tinda shi baya nan dan hakane ta daure taje dining din suka ci abinci tana jin Mum din nata basu labari kala kala amma sam ita jin takeyi ko abincin bata buqata bare.

Suna gamawa bangarensu mommy sukaje suka gaidasu daga nan suka koma dakinsu sunata harkar gabansu da abubuwan da suka jima basuyiba.

Wuni sukai a daki basu fito ba abinci ma sedai anan bangarensu sukaci a dining tareda Mum din ansamu ta zauna yau itama bataje fira ba.

Har dare bai dawoba babu wanda ya gansa dan haka koda ya dawo an shirya dining da kyau dan fammah ce da Mum din yau sukai abinci sbd Maamah datace yau tinda ta dawo tayiwa mijinta abinci sai itama data saka hannu suna gamawa tace su shirya dining dinsa.

Bataje ba fammah ce kadai taje ta hada dining din ita kuma ta tsaya ta qarasa hada masa ginger tea mai tsafta da tsari da Mum din tace ta hada masa.

Da daddaren bayan ya dawo yayi wanka ya fito sanye da wasu black Gucci freesize da suka masa wani irin kyau da fiddo girman murdadden jikinsa na soja tsayayye.

Yana fitowa Ms meenah na shigowa ta kama hannunsa suka nufi dining suna saka kai ciki ya dan janyeta daga jikinsa yana zaunawa a natse idanuwansa na dagowa anatse daidai suka sako kai itada fammah idanuwanta farare tas da wani irin nutsuwa dake cikinsu ta dago ahankali ta kalli Mum din data ambaci sunanta tana cewa ta miqo mata tea din data shigo dashi.

Takowa tayi a natse tabi ta gefensa cikin nutsuwa qamshinta mai sanyi ya shiga hancinsa ya dago da fararen idanuwansa ba tareda ya kalleta ba ya saukesu akan hannuwanta dake dauke da tray din da Meenah ke amsa.

Taji saukan idanuwansa akanta dan haka taqi dagowa ta kallesa tana miqawa Mum din ta juyo a natse ta zauna kusa da Fammah dake gaidasa da kulawa da kewa ta bude baki a natse da sanyayyar sauti mai kamewa da nutsuwanta tace

"Ina wuni"

Sai daya bawa fammah amsa tukuna ya dauke idanuwansa daga kan fammah ya saukesu akanta da wani irin kaifin daya sakata kasa riqe zuciyarta dake jin kaifinsu ta dago idanuwanta masu zallan kyau tai masa wani sanyayyan kallo daya ta dauke idanuwanta tana maidawa akan fammah a narke ta kalleta taji sautin muryansa ta ratsa kunnuwansa yace

"How are you???

Har cikin zuciyarta taji saukan maganar dan haka ta dan ja numfashi mara sauti da bayyanarwa ko kadan ta gyada kanta ahankali sbd bazata iya magana ba dan idanuwansa na karya kowace garkuwan jikinta a daidai lokacin da kaifinsu.

Mum data gama zuba masa tea kallansa tayi taga idanuwansa na kan SANAAH din dan haka babu tinanin komai tace

"SANAAH yi serving Dad dinku"

Dagowa SANAAH tayi ta kalleta da wata irin kasala tana jin gabanta na faduwa sbd kusantarsa a lokacin zai iya hana gangar jikinta amfanuwa.

Ganin babu wanda yabi ta kan zancen dole ta miqe a tsanake tana takawa ahankali ta nufo gefensa daidai nan mum din tace Fammah ta dauko musu ruwa mara sanyi wannan yayi sanyi.

Tana isowa gefensa qamshinta ne ya shiga hancinsa dakyau a tsanake amma bai dagoba sbd yana kallanta yasan zata iya barin da zata illata kanta dan haka ya hana kansa kallanta sai hannuwanta ya saukewa idanuwan nasa da shima anan tajisu.

Cikik nutsuwa ta fara zuba masa brown paster da chicken salad din da aka dafa.

Tana kokarin zuba masa meatballs din dake gabansa hannunta ya dan fara rawa ahankali wanda babu tsammani taji saukan hannunsa a natse da wata irin sanyi da kulawa da kamewa akan nata yana dagowa kai tsaye ya sauke mata idanuwansa da suka sakata tsayawa cak ta dago ta kallesa idanuwanta na neman narkewa.

Janye hannunta tayi tana maida kallanta a natse gurin Mum wadda dago a daidai lokacin batareda ma hankalinta yakai ba.

Magana ya bude baki zaiyiwa SANAAH din batareda damuwan komaiba sai Meenah ta yankesa da dora hannunta akan cinyarsa tana ambatar sunansa da cewa yafara shan tea din.

Janyewa daga gurin SANAAH tayi tana komawa ta zauna sbd Mum din Fammah data dawo tafara kokarin zuba mata.

Kadan ta zuba abincin ta cinye batareda bata lokaci ba tasha ruwa ta dauki tissue ta goge bakinta tana kokarin barin gurin Mum tace

"Fleet gobe inason zamu je spa ni dasu Baby SANAAH sbd fara shirin tafiya bikin Abid dan inason zamu tafi da SANAAH insha Allah banason mu barta saika nema mana izinin tafiya da ita gurin Dad dan Allah pls kaji"

SANAAH dataji maganar kaman daga sama bata tsaya qarasa ji ba ta fice sbd a saninta hadda shi zaayi tafiyar.

Fammah na jin hakan taji wani dadi duk da tasan su zasu fara wucewa kafin Dad dinta din dan haka indai Dad jeerah ya bari to Dad dinta zai taho musu da Dad dan haka ta kalli Dad din wanda ya dago ya kalli Meenah da mamakin yanda kai tsaye take yanke hukuncinta ba lissafin komai.

Bude baki yayi a natse yace

"Bata buqatan xuwa koina"

Bude baki tayi zata sake magana suka ga fuskan hakan dan haka tayi shiru da niyar zuwa gurin Dad da kanta ta roki alfarmar ya bari idan Fleet zai taho ya je mata da SANAAH din.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

78
SANAAH na komawa daki sallar ishai kawai tayi tai shirin bacci ta kwantawanta tana jin bata buqatan tafiyar da ake kokarin sakata dan sam bazata iya binsu ba a qasar da zata zama yar rakiya da takura.

Tanajin Fammah ta shigo itama tayi sallah tayi wanka da shirin bacci ta kwanta tana dan taba wayarta tukuna ta ajiye ta kwanta da wuri dukansu sukai bacci sbd SANAAH din datai sanyi tai baccin da wuri.

Washe gari bata bisu cin abincin ba ta tafiyarta bangarensu Mommy acan tayi breakfast tareda su daganan tayi zamanta anan.

Fammah ma anan tazo tayi breakfast daga baya iyayenta ne kadai sukai breakfast dinsu ayau.

Ita kanta Mum daga baya nan ta taho bayan tabi Raheem din taje ta gaida Dad fammah ma taje da safen ta gaidasa ta jima acanma suka tattauna.

Mum na zuwa bayan ta gaida su Maamah ta zauna tana cewa

"Dr Mum auren Zaid saura wata daya cif amma inason tafiya kafin lokacin kaman nan da Sati biyu nakeson tafiya ni da Fammah"

"Masha Allah,Allah ya nuna mana gashi bana nan zaayi sbd zuwa lokacin bana saka ran na koma gaskia"

"Nima banason ki koma Dr Mum gwara ki tsaya anan tareda mu tinda kusan babu me ranar barin nan tukuna yanxu a cikinmu muma ana gama bikin zamu tafi America amma mu dan qarasa hado wasu abubuwan mu dawo"

Hakan data fada ya saka Dr mum din ta dan kalleta tana cewa

"Zaku dan dade kenan"

"Aa Dr mum ni da nakeson ki dan saka mana baki dan Allah zanje da SANAAH taje bikin hakama acan America ma ba dadewa zamuyiba"

Sai a lokacin Maamah ta dago ta kalleta daga wayarta datake karanta sakon Al'amin daya shigo wayarta ta Whatsapp..

Mommy ma data iso gurin lokacin taji abinda ta fada dan kallanta tayi tana ajiye shayin maganin data dafowa Dr Mum na muran datakeyi ta juya ta koma kitchen tana ci gaba da aikinta da safiya.

Dr Mum kuwa dan basarwa tayi tana daukan maganin ta da mommy ta ajiye tace

"SANAAH kuma?
Kuda zakui tafiya ba qasa daya ba hakama ba lallai me ikonta ya bari ba"

Da dan karfin hali tace

"Dr Mum zai bari zan tambayesa da kaina na roka pls"

Maamah ce ta kalleta gabaki daya dai tana ajiye wayar hannunta tace

"Shi me ikon nata zaki roqa?

"Eh Maamah zan rokesa dan Allah abari mu tafi da ita mana tinda zamu dawo"

Dr Mum ma kallanta tayi da idonta gabaki daya tace

"Komai na tafiyarta bazai hadu ba a lokaci daya kinsani.....

Katseta Meenah din tayi da cewa

"Eh kafin Fleet ya tashi tafiya daurin auren komai ya kammalu sai su tafi tare"

Maamah data fara quluwa da halayen Meenah din itama akan naci tace

"Meenah idan kuma zai biya wani gurin fa kafin ya isa Morocco din yaya zaiyi da ita??

Kallan Maamah din tayi tace

"Maamah Dad dinta ne fa duk inda zai biya ai dai zasu iya lafiya insha Allah"

Dr Mum katse zancen tayi da cewa

"Ai tinda kinaso shikenan tinda kome zaa fada ba fahimta zaki ba Allah yasa abarta tafiyar"

Farin ciki taji tace

"Amin ai insha Allah Dad zai barta tinda tareda ni ne ga fammah ga Fleet din da kansa"

Wata firar suka kama su kuwa su SANAAH suna daki suna tasu firar da wayoyi SANAAH na lafe gefen fammah kaman koyaushe tana kallan fuskanta kaman wata babynta.

Guraren yamma suka fita gurin wata yar siyayya da karbo sabbin hijabs din da suka siya sbd sunason saka dogayen hijabs har qasa indai suna yawon cikin gida sbd basa son kaya mai nauyi ko kadan musamman SANAAH shiyasa take yawan saka hijab da dare indai zata fito daga wani bangaren zuwa wani  bangaren.

Sai magrib suka dawo suka wuce bangarensu kai tsaye SANAAH ce tayi tuqin dan haka key din a hannunta yake suna isa bedroom dinsu sallah suka fara yi kafin suka fito.

Fammah ce ta wuce kitchen ta tadda masu aikinsu suna kokarin shirya komai a dining na abincin da suka kammala dan haka itace ta hada komai na Dad din takai masa SANAAH kuwa bata fito ba shikenan ta shigewanta ko abincin dare bata buqata tea kawai ta buqata aka kai mata da snacks kadan.

Washe gari Mum da kanta dataje gaida Dad ta bude baki ta riqesa tafiyar tasu da SANAAH wadda yaji zancen da mamaki ya dago ya kalleta a natse kafin ya dan yi murmushin manya yace

"Shi RAHEEM din da zaiyi tafiyar da ita kin sanar masa?
Me yace akan hakan??

Murmushin tayi itama tace

"Eh na sanar masa amma kaman dai kai ake jiran amincewanka, dr mum ma na fada mata tace sai abinda kace"

Wani murmushin manyan ya kuma saki tareda cewa

"Shikenan zanyi magana dasu naji"

Godia tayi tareda barowa cikin farin ciki da jin dadin alamar Dad zai amince.

Tana ficewa da daddare wayarsa ya dauka a natse ya saka kiran Dr Mum wadda tana ganin kiransa ta kama fuskanta sosai tana daurewa.

Kaman ba zata dauka ba sai kuma data kusa yankewa ta dauka.

"Barka da dare Likita" ya fada a natse da kwanciyan hankali da muryansa datake ta tsayayyen dattijo data ratseta har cikin kwakwalwanta ta daure fuska tana hana kowace makaminta sassautawa.

Bude baki tayi a tata kamewan tace

"Barka da dare"

Murmushinsa na manya mai sauti ya sake wanda sautinsa ya shigo har cikin kunnuwanta ta kalli wayar a natse tareda sake jin nauyin kirjinta na karuwa da dawowa sabo.

"Yarki taxo ta sameni da maganar rokon tafiya da tawa 'yar wanda nakeson ji daga bakinki kina buqatan na baki aron  'yar tawa kin yadda da amanar 'danki da 'yarki???

Wani numfashi ta hadiye tareda kallan wayar tsawon seconds kafin ta bude baki tace

"Zasu tafi har America daga can kaman tafiyar tayi tsayi"

Murmushi ya kuma sakewa mai tsari da nutsuwa yace

"Amsa daya zaki bani likita daga nan har bangon duniya idan zasuje matiqar 'yata is safe a hannun yarki to shikenan dan kada ku manta auren nan ina nan ina jiran abinda nace sbd babu inda zaije kuma kema kaman matsayar kike jira na rabawa ki koma ko??

Wani siririn tsokin baqin ciki dr mum ta sake mara sauti tana jin maganar tasa a kirjinta direct kuma tasan da gayya yake fadan hakan dan haka kai tsaye amsa daya ta basa tana katse wayar.

Murmushi yayi yana ajiye tasa wayar shima da sake tabbatarwa da kansa akwai dan sauran lokacin daya dibarwa auren yana cika tabbas sauya rabasa koda hakan na nufin kowace bacin rai da kowa zai shiga tinda itama SANAAH din 'ya ce kuma mace ce kaman kowace.

Washe gari dukansu suka fita tareda Mum din wadda itama zatai siyayyar abubuwa da dan dama da kuma gyaran da zata fara yiwa kanta na tafiya qasarta a cikin familynta da itace star a kaf ciki yanzu sbd itace matar wanda yakeda tarin arzikin da babu a familyn da kuma wata irin power da suna hakama dukiyar gaske take sakarwa familyn nata na kusa da nesa sbd nunawa duniya irin daula da rayuwar datake ciki wadda sai mace mai girman saa ce zata samu kanta a cikinta shiyasa kaf familyn suke bata girma da tsantsar tarairaya kaman zasu bauta mata duk da sunada zafi sosai amma ita kam ta zama star din da babu kamanta a familyn duk da akwai maza masu kudi sosai a familyn amma basu kai mijinta ba.

Shopping suka fara yi sosai kowa da abinda yake buqata da kuma so dan haka suka jima tukuna suka gama Mum ce ta biya kudin komai da card din Fleet daya basu kafin suka baro suka nufi spa wanda bayan sun isa Mum tayi magana dasu kudi sukai magana akan a gida zaa ringa zuwa kullum ana musu komai tsawon kwanaki biyar tukuna sukai payment na komai suka bar gurin.

Koda suka iso gida yamma ta dan yi dan haka a gajiye SANAAH ta fada wanka tanayi ta fito tayi sallah tana idarwa fammah na fitowa daga wankan itama taxo tayi sallah a daidai nan Safiya da SANAAH ta kira a waya ta shigo dauke da madara me zafi data dafo mata da zuma da sabon coconut bread daya gasu ta ajiye musu a gabansu tana kallansu da dariya labari kala kala a bakinta ta zauna tana bubbude kayan da suka siyo tana dubawa tana fitarwa tana cewa

"Ni idanma kukai tafiyar nan jikina mutuwa zaiyi kilama hadda zazzabi sai nayi"

Da dariya fammah dake kai bread din mai dadi a bakinta tace

"Ai Saffy kila hadda mutuwa sai kinyi kin dawo tsabar bakida wanda zaki bawa labaran gulmanki musamman na hajiyar Uncle da babu ranar da bakida su a baki"

Dariya safiyar tayi tana qara fidda kayan gabaki daya tana kallan famman da wata sabuwar gulman tana cewa

"Ai ko dazu na ganta ta fito tana waya zata fita a mota sai tsinewa wasu takeyi daman babu ranar da bata tsine tsine fa"

Sai a lokacin SANAAH tayi murmushi mai hade da yar dariya mara sauti tana kallan safiya tace

"Safiya duk ranar da hajiya ta kama ki kila dukan da zata miki akanki zata sauke haushin kaf familyn nan"

Wata dariya me kyau Fammah ta sake wadda ta fiddo wata irin kyakkyawar kamarta da Dad dinta sak musamman idanuwanta sbd yanda zancen SANAAH din ya sakata kwatanto ranar dan haka dariya takeyi da wani irin sakewa itada Safiya din wadda tace

"Wayaga sakwara dan kuwa wlh nima nasan uban duka zanci gashi banda me amsana dan kafin Dad yazo na koma kaman wadda tayi hadarin mashin a digar jirgin qasa"

Wata dariyar Fammah ta sake tana jin kaman zata shide.

SANAAH data kasa dauke idanuwanta ahankali daga kan fuskan famman zamewa tayi ahankali tana jinginar da bayanta jinin kujera daga qasan datake zaune a kasalance tana sauke wata ajiyan zuciya mai sanyin gaske tareda dan lumshe idanuwanta tana ajiye cup din hannunta ahankali tareda kama jikinta guri daya a natse tana kasa dauke idanuwanta daga famman cikeda wata irin kauna da sanyayyar yanayin dake yaduwa a kirjinta tana jin kaunar fammah har cikin jininta.

Sake wata maganar Safiya ke yi tana dariya itada Fammah wadda take jin idanuwan SANAAH akanta ta juyo ta kalleta kadan da kulawa zatai magana SANAAH ta girgiza mata kai cikin wata irin slow da shagwabanta dan tasan abinda famman zata fada.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

79
Dare sosai Safiya takai a dakin nasu tana musu fira suna nishadinsu kaman yanda suka saba tukuna ta baro bayan ta jere musu komai da suka siya a inda tasan ya kamata harna toilet takai ta jere dana gaban mirror da dai komai tukuna ta musu saida safe ta fice.

Fammah kallan SANAAH tayi bayan sun kwanta tana lafe har lokacin a narke batason hayaniya da doguwan magana da kulawa tace

"Ke are you okay wai?

Girgiza kai SANAAH tayi alaman eh bayan ta kalli famman ta dan rufe idanuwanta kadan.

Da mamaki famman ta sake kallanta tana wata dariyar data zo mata tana da neman jin amsa tace

"SANAAH are you inlove? I mean did you fall for me or wat????? Ta qarasa maganar da dariya sosai da tsokana.

Harararta SANAAH ta bude idanuwanta tayi cikin rashin karfi tana kai hannunta daya ta daketa a kafa tana cewa

"You crazy fammah??

"Eeh naji amma ina ji a jikina you're obsessed with ne or my looks,
Kin fara soyayya ne ban saniba girl??
Fadamun waye da bansaniba ya kasheki haka kwata kwata bakida saura ko kadan aswear"

Juya mata baya SANAAH tayi ahankali tanajin tsigar jikinta kawai suna tashi ahankali daga kalaman Fammah din kawai ta lumshe idanuwanta bakinta na sanyin da bazata iya furta ko kalma daya ba.

Fammah na ganin hakan ta sake sake wata yar qaramar dariyar data bata tabbacin maganarta na iya zama gaskia.

"Prof ne??? Fammah ta jefa mata tambayar a kunnenta wadda ta sakata rintse idanuwanta ahankali tana dan qanqame bargon datake rufe dashi sbd tana bude idanuwanta fuskan famman ta gani a kusa da tata wadda murmushin dake kai ya kusan sakata tsayar da numfashinta sbd fuskansa ce sak ta shiga idanuwanta akan ta famman.

Sake maimaitawa fammah tayi da cewa

"Prof ne fadamun sbd idan shine muna cikin murna"

"Fam pls ki kwanta kiyi baccinki ba kowa a rayuwana"

Tsokanarta Fammah taci gaba da yi dan taji harta tabbatarda kaman ba kowa din dan haka suka kwana bacci zuciyarta cikeda sanyi da nauyi na abinda takeji a kirjinta gameda duk abinda famman ta ringa tambayarta.

Washe gari da safe bata fito ba sam tana daki har rana tukuna ta fito taje ta gaidasu Dr Mum tayi zamanta cikinsu har kusan yamma kafin masu gyaransu suka taho wanda Mum dake matar gidan datake ganin kusan duka su Mommy da Maamah harma da Dr Mum itace kadai matar gidan a cikinsu dan itace matar babban Dan Jeerahs kuma wanda yake da matsayin da babu wanda yake dashi a familyn dan haka take sake jin isa da iko masu gyran ma da suka taho haka suka ringa bata girmanta sbd nuna musu datai itace asalin macen Jeerahs family.

Bangarenta aka kaisu aka ware musu daki daya suka shirya komai na aikinsu sai da sukaci abinci suka gama jiranta ta gama yangarta tukuna taxo ta zauna aka fara musu.

Su uku akaiwa gyaran kusan har dare tukuna aka gama sai kuma gobe.

Ana gamawa wanka sukai dukkaninsu sukai sallar magrib da ishai sukaci abinci banda SANAAH da bata iya cin komaiba Dr Mum ta aiko safiya ta kawo mata dafaffiyar madara da zuma da kidney sauce taci tai brush ta kwantawanta.

Su Mum kuwa sbd ta nunawa Fleet adonta data fara acan bangarensa ma tayi wanka bata dawo ba sai washe gari.

SANAAH ko dataje ta gaidasu Dr Mum kai tsaye Dr Mum tace mata kada ta sake fitowa zuwa gaidasu ta zauna guri daya sbd gyaran da ake musun bayason ko yawon tai zamanta kawai sai angama.

Mum ma ta sanar mata hakan amma sam bata iya zaunawa ba sbd duk akai mata ta ringa kaida kawo kenan sbd yanda take ganin tana daukan idanuwan masu ganinta da glowing din data fara.

Maamah ma ta saka an dauko musu mai gyaran gargajiya da zata qara musu da nata idan an gama wannan dan haka a ranar da akai 5days aka gama wannan din a ranar washe gari suka iso daga maiduguri ta jirgi sbd tickets da aka siya musu.

Tin ranar da Dr Mum ta hana SANAAH fitowa bata kuma fitowaba sbd itama gabaki daya bata jin kuzarin yawon daman dan haka tin daga ranar babu wanda ya sake ganinta tana bangaren nasu bata fitowa koyaushe tana daki abinci ma anan take ciki ta dena zuwa sam dining ci tareda su dan haka basu sake ganin juna ita dashi ba tsawon kwanakin.

Ana gama wancan gyaran aka fara musu sabon wanda SANAAH din tace bata buqata sbd jin takeyi abin ya mata yawa amma ko kafin Dr Mum tai mata fadan hakan a waya Ms Meenah tai mata fada sosai tace sam sai anmata sbd bikin dake gabansu dan ita so take ma SANAAH din ta samu miji a can dan akwaima wani dan uwanta datake son hadasa da SANAAH din sbd ya samu shiga a gurin Dad jeerah da Raheem din daya dade yana neman hanyar shiga ahalin jeerahs din dan shima soldier ne matarsa ta farko ta rasu tabar Babynta daya namiji da baifi shekara tara zuwa goma ba dan haka take tsananin son SANAAH din taje kota yaya ne.

Mommy data saka SANAAH a idanuwanta data tafi ganinsu muguwan faduwa gabanta yayi sbd irin sauyin datai wanda ya saka fatarta har wani daukan idanuwa takeyi da kyau da glowing da wani irin fitinanniyar qamshin dake fita daga jikinta jin tayi hankalinta yane neman tashi da tsoro da shakka da fargaban wannan gyaran data ga Dr Mum din sun rufe ido ana mata wanda itaba yarinya bace ta fahimci dole hakan na nufin gyara ne na miji ake mata bayan ga matarsa itama tana cikin gyaran hakama tayaya zasu tafi da SANAAH din qasar da batada kowa batasan kowaba da kishiyar da batasan cewan kishiyarta bace ga kuma miji a tsakiyarsu duk da tasan babu ma abinda zai faru tinda haryanxu a kaman fammah yake kallan SANAAH din kokuma tace matsayin matar dan uwansa da baya raye.

Shirye Shiryen tafiyar tasu ya gama kammala daga Mum din sai fammah SANAAH kuma daga baya Fleet zai tafin musu da ita bayan Dad da kansa ya sanar dashi yayi tafiyar da ita.

Imran ne da kansa yake shirya komai na tafiyar tasu da ita wadda sai anfara ma bikin zasu isa tukuna.

Sati biyu sukai ana musu gyaran daya sauya kowaccensu su duka ukun,

Meenah da Fammah haske sukafi SANAAH wadda itama tanada hasken sosai amma bata kai su ba suda suke asalin larabawan amma kuma kasancewanta ba qal dinba sai tafisu yin kyau da wani irin daukan ido musamman data kasance bata fita koina hakama daman gata da wata lafiyayyar skin da kyan fatar dayafi nasu duk da dukansu hutu ne na gasken gaske yake magana a fatarsu da jikinsu duka.

Ms Meenah dik da ana gyaran tana fita da mota zuwa gurare da dan dama na duka shirye shiryen tafiyarta ga kuma koyaushe cikin tabbatarda mijinta yaga sabon gyaran dayake tattare da ita take tsawon kwanakin.

Kudi masu yawan gaske ya sakar mata na hidiman bikin itada 'yarsa wadda ita kanta ba qannanun kudine a kwance a acct nata ba dan haka koda ya rage sauran kwana biyu su tafi SANAAH narkewa fammanta

Please Login or Register in order to submit comment