Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din wadda itace tayi serving nasu da kalan abincin datasan zasu iya ci sosai su koshi musamman mum dinta da kwata kwata kalan cimarta daban bata saba da abincin Nigeria ba kwata kwata.

Sunyi breakfast din suna gamawa suka baro daidai lokacin ne hajiyar Samad ta shigo palon tareda yan aikin bangarenta guda biyu dake dauke da basket biyu na abincin data saka akai musu itama.

Allah yasa bai shigeba dan haka ya dan dakata suka gaisa batareda ya juyo ba dan baya wani kallansu ko iya samun sakewa da matan mahaifin nasa dan har gwara ita hajiyar Samad din yana ganeta kai tsaye amma Umma bai iya tantance kamanninta sbd babu kowace alaqar datake tsakaninsu bayan gaisuwa kawai.

Suna gama gaisawa tanata neman sake cusa kai da maganar Samad bai biyosa ba ya bata amsar yana wani aiki ne a taqaice tukuna yayi mata godiya datake dabiarsa ya fice ya shige hanyar da zata kaisa palonsa yabarta nan gurin su fammah.

Fammah ta kalla tukuna ta maida kallanta kan Mum din baki a washe da nuna farin cikin zuwansu tace

"Fammah Mum din taki da ita aka iso kenan?
Dazu tinda safe Samad ya kirani ya sanar dani ai sun sauka Nigeria ba shiri nace maza a tashi ahau aikim abincin da zasu ci idan sun iso"

Da murmushi babu wata nuna wulaqantawa saidai kamewan rashin sabo sosai tace

"Yes da Mum aka taho gatanan zaune"

Kallan mum din datake kallan Hajiyan da rashin sani kwata kwata tayi tace

"Mum hajiyan Uncle Samad ne,i mean his mum"

"Oh ok yes" ta fada tana sake fuskanta sosai da murmushi mai kyau tana kallan hajiyan tace

"Mun sameku lfy"

Hajiya na ganin hakan taji farin ciki ta sake sakewa tana cewa

"Lafiya kalau alhmdllh,ya hanya?
Ya America or Morocco zance?" Ta qarasa maganar da yar dariyar sakewa tana kallan Ms Meenah din da kyau wadda itama ba mummuna bace da kyanta sosai duk da tanda zuqeqiyar budurwa gabanta amma bata rasa kyanta da kyan jikinta ba.

Abincin Hajiyar tace akai dining a jera Mum da batasan me zasu ce ba tinda sunci abinci batareda tinanin ana dan kara ba tace

"No no ba buqatan hakan mun riga munci abinci kada a aje mayar ko wani zaici acan,thank you so much"

Wani abu hajiyan ta hadiye na takaici tana kallan bakin Ms Meenah din da jin kaman ta mayar mata da thank you dinta dan takaici amma sai ta washe baki a fili tana cewa

"Ok ba damuwa ashe harkunci abinci,
Ku maida sai anjima ko gobe da sassafe a sake musu wani"

Kokarin dannewa da boye takaicin data shaqa hajiya tayi tana zuba musu hirar da suka matsu ta qare su tafi gurin mommy sbd zaiyi wuya mommy ta shigo bangaren sbd Dad na nan fammah ta fada mata nauyinsa take ji shiyasa ko a waya cikin girmawa da mutuntawa mai tsanani suke gaisawa idan ta hadasu a waya.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

56
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Ganin yanda taketa kokarin jan Ms Meenah a jiki tinda sun riga sun rasa fammah amma kaman kwata kwata basa buqatan hakan dan Fammah ta fice ma Mum din tata kuwa hausar sai ahankali dan haka firar taki armashi yasaka dole tatashi tai mata sallama ta kama tsufanta ta bar bangaren tana hadasu su duka tas tin daga Dad da Dr Mum da Meenah din da fammah dasu SANAAH ta ringa tsine musu da musu fatar masifu da balai kala kala Raheem ne kawai bata tsinewa sbd matsayin dayake dashi a gurin Samad dan Samad bai hadasa da komaiba dan ko ita data haifesa ganin takeyi wani lokacin yafi kauna da ganin darajar Fleet akanta dan haka ta hakura ta bi Allah tabi Raheem din itama.

Tana barin bangaren sai ga Mommy da SANAAH da fammah da safiya a bayansu dauke da tray din fresh fruits masu tsafta da sanyi mommy ta saka an kawo musu.

Dukansu farin ciki ne sosai a cikeda fuskansu suka qaraso ciki itama Mum din na ganinsu farin cikinta ne ya bayyana ta tashi tsaye tana yiwa mommyn sannu da zuwa cikeda kulawa da kauna da sabon da sukai tin a waya dan haka sukai can cikin palon kurya na bedroom din Mum din suka zauna cikeda yar hayaniyar murna da kokarin sake gaggaisawa.

Ita dai SANAAH bata cikin kowane yanayi bayan na nutsuwa da rashin iya hayaniya kawai dai tana kokarin bayyanarda murmushinta kawai ga duk maganar da akeyi hakama ta zaune gefen Fammah datake jin kaman ta hadesu bangare daya su zauns ta lafe gefenta.

Basu wani jimaba a bangaren suka kwasa sukai bangaren su mommyn acan suka zauna da sabuwar hira da tarin tsarabar data kawo musu ta wasu mahaukatan designer shoes da bags da perfumes daga asalin brand stores din designers din.

Godia SANAAH tayi mata a tsanake da girmamawa kafin tabar gurin ta nufi daki dan amsa wayarta da aka kira.

Mum bata bar bangarenba sbd jin ta samu kanta a irin rayuwar da bata taba samun kanta a ciki ba ta mutane sosai duk da ba wani yawa ne dasu ba amma yanda aketa kokarin sabawan da firar ya saka taji tana jin dadin hakan dan haka bata koma ba sai bayan magrib data koma tayi wanka ta sake sauya kaya ana fitowa sallah suka tafi gaida Dad wanda sai lokacin zasu gansa dan yau hadda wuni gida baiyiba yana gurin wasu hidimar.

A gurin Dad ta samu tarban karba gaisuwansa cikin kulawa da mutuntawa haka shima Raheem din dik da zuwan da yayi da matarsa ya saka Dad ya fahimci manufarsa kai tsaye ta gujewa kowace muaamalan dama zaa iya cewa ta hadasa ne da SANAAH dan haka murmushi kawai yayi tareda tabbatarda Raheem bai gama sanin shi waye ba.

Washe gari mommy ce da kanta ta hadawa su Dad din breakfast kaman yanda ta saba hada masa wancan zuwan nasa dan haka koda su kansu su fammah suka tashi suka fito guraren after 9 tini mommyn da safiya sun gama komai dan haka Mommy ta kallesu lokacinda SANAAH ta bude fridge a kitchen din ta dauko sabon fresh guava juice din da aka hada da madaran kwakwa da safen mommy ta hadasa ta zuba a glass ta dauka tana kaiwa bakinta mommyn tace

"Ku dauka ku kai breakfast din tareda gaishes...

Sarkewa SANAAH tayi da dan karfi ta ajiye glass cup din hannunta tana zaran tissue da dan sauri tana goge bakinta tareda neman taqaita tarinta dayake fita tana qin juyowa ta kalli kowannsun.

Fammah datake sake miqo mata tissue cikin kulawa tace

"Lafiyanki kalau dai ko???

Gyada kai tayi batareda ta juyo ba tana karban tissue din ta qarasa goge bakinta ta juyo a hankali tana karban ruwan da safiya ta miqo mata masu dan dumi a cup takai bakinta tasha kadan ta ajiye cup din da dan sake goge gaban rigar jikinta daya zuba kadan.

Kallan Mommy tayi tana kokarin bude baki tafada uzurin da zai hanata zuwa mommy ta kalleta bayan fammah ta dauki basket din daya ta fice ta bude baki tace

"Abinda kikewa fammah bayada kyau da amfani akan duk lokacinda zata buqaceki gameda duk abinda ya shafi iyayenta,
Nasan abinda kike saukewa nima ina kaucewa hakan tinda dai bamusan ma a wane matakin auren yake ba wanda da alamun da suke bayyane babu auren nan dan haka kada ma ki kawo kowane tinani ko wani alaqar auren da tabbas zuwa yanzu babu shi a gaban alaqarku mai tsafta da yar uwarki ki aje komai ki rungumi iyayenta da hannu biyu da biyayya da girmamawa kaman yanda ta karbi naki batareda ma kin bari ta fahimci gudun shiga ko kula iyayenta kakeyiba ki kiyaye sbd duk abinda zaki musu sbd itane zakiyi bawai kodan kowace alaqar ba."

Numfashi taja ahankali mara sauti da sanyi ta fitar tana jin itama daman bata son ko kadan fammah ta fahimci gudun iyayenta takeyi tin ba yanzu ba amma ta rasa yanda zatai ne sbd batason ta shiga cikinsu sosai ya zamana kaman cin amanane tana tareda Mum dinta kuma ace akwai aure a tsakaninta da mijinta gashi alaqarta da fammah ya saka maganar auren zaunuwa a zuciyarta da tinaninta sbd a baya da bata tareda famman mantawa tayi kwata kwata da akwai wani aure a kanta amma yanzu sbd koyaushe tana tareda 'yar wanda auren yake hannunsa ta kasa yakice tinanin auren ta jefar sbd abubuwa da dama babban cikinsu shine kasancewan famman yar uwanta kusan rabin jikinta a yanzu tana tsananin kyamar abinda zai hadata da ita ko samar da sabani a tsakaninsu dan haka ayanzu data kasa cire auren a ranta to zallan kyama da tsanar aurence take ciketa zuwa yanzu.

Hannu ta miqa a natse ta dauki dayan basket din tabi bayan fammah ta fice sanye da riga da skirt na tsafadden brand din AfiaSmith coffee brown sai silk scarf din dior dayake kanta shima brown.

Ko data fito Fammah ma lokacin zata fice sbd wayarta dataje daki ta dauka suka fice a tare suna fira hankali kwance duk da fammah ce mai bada firan.

Suna isa bangaren zuciyar SANAAH taso shiga wani hali amma ta sakawa kanta karfin halin dannewa da daurewa daga yau sbd farin cikin fammah.

Kai tsaye palon fammah ta bude suka shiga suka nufi dining suka jera komai kafin suka nufi dakin Mum SANAAH na kokarin bayyanarda murmushi da sakewa a fuskanta.

Suna shiga kuwa ta gama shirinya tsaf itama cikin doguwan riga dayake sune kayanta tana waya cikin yaren larabcin daya tabbatar musu da yan qasarta take waya dasu.

Zaunawa sukai harta gama ta miqawa SANAAH hannu tana murmushi da kulawa sosai tace

"Baby SANAAH you look fresh and beautiful,yaya kika tashi??

Murmushi mai kyau tayi tana dan kama hannun Mum din ta dawo kusa da ita ta zauna tana cewa

"Lfy kalau Mum,yaya baqunta da kewan America?

Dariya mum din tayi tana cewa

"Masha Allah gaskia da alama zanji dadin zaman"

Fammah ma gurinta ta dawo ta dayan gefen tana maqale hannunta da dan kwantawa tace

"Mum kin tashi lafiya ko?tinda dai yanzu an sauya ni SANAAH kawai kika sani"

Dariya suka yi dukansu banda SANAAH da murmushi me sauti ne ita ta fidda tana cewa

"Fear God fammah"

Sake gaidata sukai ta amsawa dukansu lokaci daya da kulawa tana cewa bara ta dubo Dad dinsu tinda breakfast ya zama ready.

Tare suka fito dukansu kirjin SANAAH na dan nauyin yanda zata iya zama a cikinsu breakfast din da Mum tace tareda su zaayi.

Hanyar xuwa gurin Fleet ta nuna tana fidda wani qamshin turare mai sanyi da dan karfi su kuma suka nufi kitchen dan dauko su ruwan sanyi dasu cutlerys.

Ko da Mum din taje shima ya gam shiryawa yau cikin black Tom ford freesize sweatshirt a jikinsa da khaaki kala trousers na Rugby da suka sakasa fitowa cikakken kakkarfan namiji sbd kusan manyancinsa ya boye kawai kakkarfan Soldiernsa ya fito mai hutu da lokaci.

Mum na riqe da hannunsa ta sana nata a ciki suka fito qamshinsa ne ya fara doso gurin yana dan shiga hancinsu dan haka SANAAH ta tattaro nutsuwanta ta tsayar guri daya tareda tsanakar da zafin kanta tana basar da komai.

Yana sako kai a cikin dining din tana juyowa a tsanake sbd fammah datai gurinsa tana ambatar sunansa dan gaidasa.

Idanuwansa akan SANAAH din da baitaba tsammanin gani ba suka sauka ita kuwa cikin nutsuwa da wata irin basarwa ta sake kyakkyawar murmushin da take kamarta da Nasir tayi waya irin bayyana ya tsayar da fararen idanuwansa akanta Mum kuwa baki a washe da neman cusa SANAAH din tace

"Baby SANAAH zo ki gaida Dad din naku kema"

Wani nauyin kirji SANAAH ta hadiye dakyau tana sake fidda murmushi mai kyau daya sakasa dan dauke idanuwansa daga kanta yanajin wani nauyi yazo ya tokare kirjinsa.

Sake mata magana Mum tayi suna qasarowa suka zauna itama dole ta tako ta nufosu daga ita har shi kirjinsu na wani irin nauyi a lokaci daya tana isowa gabansa nesa kadan ta dakata tareda bude baki tareda dagowa da kyawawan idanuwanta ta saukesu akansa tace

"Good morning Dad"

Yanda kalmar ta fito daga bakinta da kalman DAD data ambacesa dashi kai tsaye shi da ita sunsan kalma ce data ambata akan dole da kuma kasawa da tsarawan Ms Meenah dan haka a cikin wata kwarjini da haibansa ya dago ya sauke mata nasa idanuwan ya kalleta ya bude baki da sautinsa daya sakata sauke idanuwanta sbd strong deep voice dinsa ya amsa a taqaice tukuna Suka isa dining din suna zaunawa.

SANAAH bata iya juyowaba rintse idanuwanta tayi ahankali tareda jan wani boyayyan numfashi tukuna ta juyo tana isowa a natse.

Fammah ce ta fara serving nasu dan haka itama a natse tafara tayata tana kokarin maintaining kanta.

Tea ta zubawa mum tana gama zuba mata kafinma tayi wani Motsin tace

"Ki zubawa Fleet yafi buqatansa before yafara cin komai."

Juyawa tayi ahankali ta isa gurinsa batareda ta kallesa ba ta dan rankwafo a hankali zata zuba masa wani qamshin wani fresh fruits guava da Coconut suka shiga hancinta ya dan dago idanuwansa ya sauke akan hannunta dayake zuba tea din batareda ya kalli fuskanta ba.

Yanda ya idanuwansa suka sakar mata kaifin ganinsu tana jinsu a hannuwanta take ta kasa riqe tea jug din ya kufce mata tafasashin ruwan sukai qasa da karfin daya sakata rintse ido da karfi cikin tashin hankali glass din na isa qasa yayi daidai da lokacinda Mum takai hanunta da wata irin mugun sauri zata janye hannun Fleet wanda hannunta na isa nasa barin gurin ya janye SANAAH din baya unexpected.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

57
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Cikin tsoro da firgitan da SANAAH tayi ta kama hannunsa da duka hannuwanta biyu batareda ta saniba na qanqame tana bayyanarda yar qarar dake hade da tsoro da yarinta.

Fammah ajiye abinda yake hannunta tayi da dan sauri tana nufota,

Mum ma da tana hankalinta da nutsuwanta basu bata komaiba miqewa tayi tana dawowa gurin Fleet da shima ya dan miqe a natse tafin hannunsa hade dana SANAAH din data riqesa.

Fammah ce tayi baya da ita kadan daga glasses din dake fashe qasa tana cewa

"Hope ruwan bai taba ki??

Dagowa SANAAH tayi ta kalleta da fuskanta data narke gabaki daya ta zare hannunta daga nasa tana kama fammah din da gyada kai a hankali tana dan bude baki da sautin daya sakasa dago idanuwansa yayi mata kallo daya ya dauke tace

"No amma naji tsoro sbd na dauka skin dina zai kone"

Dan rungumega fammah tayi tana janyo kujeran datake gefen ta dad ta zaunar da ita tana cewa

"Its ok"

Mum ma Dad din ta dan kama hannunsa tana shigarwa cikin nata tareda cewa

"Thank God babu wanda ya kona tea din"

Zaunawa sukai tana kallan SANAAH tace

"Baby SANAAH kin tabbata you're ok right??

Dagowa tayi tana dan sauke bayayynan numfashin daya buso masa da wani sabon qamshin coconut din daga bakinta data sha sa kafin ta gyada kai tana cewa

"Yes Mum"

Dago da idanuwansa yayi kadan ba tareda ya kalli koina ba ga dan fidda numfashi kadan mai nutsuwa.

A waya fammah ta kira safiya wadda ta iso cikin girmamawa da rashin hayaniya tana isowa ta qaraso ta gaida Fleet kanta aqasa kafin ta gaida Mum itama tukuna ta fara tattara gurin da gyarawa a tsanake.

Tana gama gyarawa fes kaman babu abinda ya zube tabar gurin raje sharp sharp ta sake hado wani tea din a tsaftace da tsari ta kawo.

Shiru Dining din yayi suka fara breakfast kowa hankalinsa kwance banda SANAAH datake jin har lokacin zuciyarta na bugawa.

Bata wani iya cin abinci ba sosai bare kuma daman ba wani sosai take cin abinci ba dan haka fries taci sai juice ta koshi ta zari tissue ta silale tabar dining din.

Tana barin nan bangaren ta bari gabaki daya ta koma nasu tana isa bata wani nuna komaiba tayi magana kadan da Mommy ta wuce bedroom dinsu ta shige.

Bata fito ba tana ciki taji zuwan Fammah da Mum din sun taho suna magana da mommy a palo.

Daki fammah tayo tana bata labarin prof yanata kiranta bata dauka ba sbd tana kan table da iyayenta dan haka bara ta kirasa suji lfy irin wannan kiran hak.

Saka kiransa tayi tana saka handsfree suka gaisa yafara jero bayanin yanda yakeson tai masa hanyar da zai aiko iyayensa gurim Dad jeerah itama tana biye masa da shawarwarin da zasu bi.

SANAAH dake jinsu dagowa tayi da idanuwanta ta sauke akan fuskan fammah ta zuba mata su tana mata wani kallo mai sanyi da kasa dauke idanuwanta daga fuskanta har suka gama wayar bayan tsawon lolacin bata wani gane inda maganganunsa suka dosa ba dan haka bata ce komaiba itama fammah din sbd ganin tana zaune sika tattauna komai kuma tanaji sai bata biyoba da wani bayani takai hannu taja dogon hancinta ahankali tana cewa

"Are you crushing on me girl??

Wani kyakkyawan murmushi ne kufcewa SANAAH mai sanyi daya sakata sake kallan famman tana cewa

"Oh please fammah"

Tana fadan hakan ta fara kokarin sauka gadon tana sake kallan famman da wani naughty murmushi a fuskanta na tsokanan famman da maganarta ta risketa ba tsammani kuma ta sakata jin kunya sosai amma ta fuske bata bari fammah ta gane hakan ba dan hakane ta maidashi wasa.

Fammah kuwa irin kallan da SANAAH din ta qara mata ya sakata biyo SANAAH din da gudu tana cewa

"Akwai abinda yake damunki that i need to check,come here"

Da sauri SANAAH ta nufi kofa da gudu famman ta bita tana kiran sunanta suka fito palon da gudu SANAAH na dariyan da kusan daga fammah sai Mommy da yaya Nasir dinta ne kaf duniya suka san tana irin wannan dariyan datake qara mata kyau da yarinta.

Mommy data saba da wannan halin nasu suna fitowa da gudu kallansu kawai tayi tana kokarin cigaba da zancen datake da Mum sukayo kansu ba tsammani itama bata tantance tai gurin Mum ta maqale ta tana cewa

"Haba Dr tawa,you're too beautiful ne shiyasa"

Mum datake kallansu da farin ciki a fuskanta hana famman taba SANAAH tayi tana cewa Mommy

"Haka suke miki bayan sun zama manyan yan mata amma sunayi kaman yara qanana"

Mommy ma da walwalanta tace

"Ai harna saba tinda basu san sun girma ba kuma iya da junansu suke hakan"

Zaunawa fammah tayi suna shiga firar da akeyi
SANAAH kuwa baro mum tayi cikin dubara sbd bata iya sakewa ta dawo jikin fammah tana cewa

"My Dr"

Hararanta Fammah tayi tukuna ta fara dan shafa kanta suna firar hankali kwance da sakewa.

Suna cikin firar ne Mum ta kallesu tace

"Yanxu dai ya kamata kubar Anty ta huta ku dawo bangarenmu har sai mun tafi tukuna"

Wata mummunan faduwa gaban SANAAH yayi amma bata motsaba bata kuma dago ba bare bayyanarda ma taji abinda aka fadan.

Mommy ma dan shiru tayi tana jin zancen bagatan daga sama saita dan daure tana yaqe kafin ta iya cewa komai fammah tace

"Mum zamu damu Dad fa da hayaniya yanzu"

Mommy karban zancen tayi itama da cewa

"Ai kuwa kinga bazaa damesa ba abarsu suyi xamansu na saba ai da hayaniyar tasu"

Girgiza kai Mum tayi da cewa

"Babu wani damunsa da zaayi yana bangarensa hakama ai mu munyi kewan hayaniyar ai tinda ba yawa ne damuba acan sannan gaskia su barki ki dan huta wa hayaniyarsu ta dan lokaci so kawai su shirya su koma can"

SANAAH data rasa kwanciyan hankalinta lokaci daya kallan Mum din ta dago tayi ta bude baki da kokarin hana kanta bayyanarda tashin hankalinta na maganar tace

"Dad ne bazai barni ba ai sbd ya hanani kwana ko ina tin da dadewa"

Kallanta Mum din tana murmushi tace

"Kada ki damu da hakan ok my baby"

Shiru SANAAH din tayi tana jin kaman zata rasa nutsuwanta dan kuwa bazata iya komawa can bangarenba sam bama zata taba yadda ba.

Daga nan tata firar ta qare ta silale tayi kitchen ta sakawa aikin Safiya hannu sunayi suna tasu firar.

Anan Mum tayi dinner dinta tareda su sai dai aka je can aka jere masa nasa a table.

Da daddare gabaki dayansu su uku hadda Mum din suka nufi gurin Dad gaidasa SANAAH tana dauke da tea dinsa.

Suna shiga cikin rashin Saar SANAAH Fleet na bangaren gurin Dad dan suna shigowa dukkaninsu sukaji qamshinsa dan haka SANAAH tayi ma baya a gurin shiga tana qin dagowa sosai.

Gurin Dad ta nufa gefensa daga qasa ta zauna a natse tana ajiye tray din hannunta akan table.

Gaidasa tayi ya amsa yana kallanta da wata irin kauna da kulawan da bai hada da amsa gaisuwan sauran ba.

Mum itama cikin girmamawa ta gaidasa ya amsa itama cikin kulawan kafin ya amsa ta Fammah da itama yake jinta har cikin ransa ya ambaci sunanta da nutsuwa.

Daman Mum din data shigo mijinta tafara yiwa magana hakama fammah Dad dinta tafara gaidawa.

Kafin a fara kowace magana kaman daga sama sukaji Mum tace

"Dad daman su fammah ne nace su koma bangarenmu da zama kafin mu tashi komawa sbd itama Mommysu ta dan huta daga hayaniyansu so SANAAH tace ka hanata zuwa koina da zama acikin gidan shine nake rokan abarta su koma can din tareda fammah"

Daga Dad din har SANAAH da Fleet tsit sukai cikeda wani irin mamaki da jin zancen kaman shock sbd abune da babu wanda a cikinsu yayi tsammanin ji daga bakinta dan haka Dad datake wa zancen shiru yayi tareda kafeta da kallan

Please Login or Register in order to submit comment