Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

WANNAN KOWA YA SHIGA SABUWAR RAYUWAR DA AYANXU KOWA YAKE KAI CIKIN AMINCI DA KWANCIYAR HANKALI...BISMILLAH.
#MAMUH

GANIN IDO
Mamuhgee
1k
Vip 5k
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

26
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki  Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki  Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce  For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
A daidaita ce tayi parking kofar gidan dayake cikin kuryan karshen layin da har ya zama lungu sbd yawan mutanen anguwan,

Fes layinsu yake da tsafta babu kowace irin kwata ko qazantar bola ko ruwa sbd gabaki daya layin akwai hadin kan tsafta da kiyayewa sbd kusan kowa gidansa ne bana haya ba dan haka babu gayya fes gurin yake hakama babu hayaniya da kwamacalar yara qanana da zaka iya gani ma da irinsu qazanta,

Majalisun manya ne da tsoffin anguwa sau shaguna guda biyu rak dake layin sai masalaccin dayake kusa gap da gidansu,

Koda napep din ta tsaya da yamma ne akwai mutane kusa da kofar gidan a xaune kan babbar tabarmar dake shimfide ta zaman da sukeyi dan haka koda ta ziro kafafunta a natse sanye da black original black crocks bata waiwaya inda sike ba a natse ta qarasa fitowa sanye da doguwar riga black fuskanta sanye da mask da brown jersey veil nade a kanta kudinsa kawai ta ciro daga backbag dinta ta miqa masa tareda wucewa cikin gida kai tsaye tana sauke ajiyan zuciya me sanyi ta isowa gida a gajiye da kuma yar yunwa sbd sam tanada aqidar rashin cin abinci a waje.

Cikin kamun kan datake dashi dayake hade da wani irin sanin darajar kai dayake cikinta kaman ba Marainiya ba ta shigo gidan da sallama me nutsuwa tana kallan Mommy dake zaune a tsakar gidan kan lallausan dadduma me kyau da girma sosai wadda suke zaunawa akai tana dan karanta wasu littafan addini da glasses dinta na qarin gani me kyau dayake dan bayyanarda sauran kuruciyarta itama tayi fresh da ita fatarta ba alaman wahala da tsufa da rashin gyara sbd a rayuwar rufin asiri da kulawa da tattali babu abinda Al'amin ya gaza basu itada SANAAH wadda itama kai tsaye idan ka kalli fatarta da dabiunta da wani irin class datake dashi bazaka dauka ba yar mai kudi bace shiyasa abokan karatunta suke respectin dinta daidai misali ba wulaqantawa hakama kusan da yawansu tana tsananin shiga ransu da shaawan son hulda da ita amma sam ba wata sakewa daga gareta tanada kame kai sosai daga hayaniyar qawance ko yawan muamala me yawa da mutane sbd kusan tarbiyan da Yaya Al'amin din ya dorata akai ne kuma shiyasa ta tsare darajar kanta fiyeda komai sbd ya sadaukar da komai nasa dan bawa rayuwartata darajar da zata wuce kowane irin rashin daraja,

A yanda ya tsaya a rayuwarsu shi tasa rayuwar ta zaka abar tausayi da mamaki dan kuwa kaman mahaukaci akan nema ya koma sedai duk sati haka SANAAH din zata zauna da kanta tayi masa gyaran farce da wankin kafafunsa dan basa kulawan daya kama ace shima yana samu duk da yanada tsaftarsa amma nema na neman haukatasa.

Dagowa mommy tayi a natse tana kallan SANAAH din wadda ta qaraso gurinta tana bude baki da sautin muryanta da shima yake cikeda kamun kai da nutsuwa tace

"Mommy barka da gida"

Da kulawa da kauna me karfi mommyn ta sake kallanta tana amsawa tareda dakatawa da karatun tana matsar da jakar SANAAH din data ajiye mata gabanta tana zare takarminta tace

"Al'amin ya sameki a waya kuwa?
Ya kirani yana tambayar ko kin dawo nace masa aa?

Qarasa zare takarminta tayi tana nufar kofar dakinta tace

"Ya kirani harma yaje ya kaimun daman kudin wani contribution ne da zaayi"

Qarasa shigewa dakinta tayi tana zare kayan jikinta duka ta dauro towel dinta me girma ta fito tana dan lumshe ido sbd wani iska me dadi daya sauka a fatarta da fuskanta datake jin gajiya sosai har lokacin.

Wanka taje tayo ta fito tareda alwala ta koma daki ta shafa mai sama sama da turarenta me sanyi na oud me dadi ta saka doguwan riga mara nauyi da hula ma mara nauyi a kanta ta fito taje kitchen ta sako abinci a plate ta dawo ta zauna gefen mommy tana fara cin abincin a natse suna magana da mommyn dake tambayarta me zaayi da kudin ne na contribution ita kuma tana fada mata suna firarsu hankali kwance cikin jin dadi.

Sallar magrib akai sukai sallarsu ana,
SANAAH na gamawa ta miqe ta shiga kitchen dan dumama abincin sbd Yaya Al'amin dayake buqatansa da zafi dan idan ya fita tin safe baya dawowa sai dare.

Shinfaka ce jallof da cabbage a ciki dan haka sama sama tai masa warming nata tana juyewa a kula ta fito daga kitchen din ana sallar ishai dan haka sallah sukai suna idarwa ba jimawa ya shigo gidan sanye da riga da wando da suka dan tsufa suka kode sosai yana waya da qaramar wayar hannunsa ya qaraso ya zauna akan kujeran dake gefen mommy ta roba yaci gaba da wayar tsawon mintina kafin ya kammala.

Kallan mommyn yayi ya gaidata yana amsa gaisuwan SANAAH datake masa cikin kulawa.

Fira suka dan fara yana dariya suma kusan duk dariyar sukeyi musamman SANAAH da a cikinsu ne kadai take iya sakewa tayi fira da dariyarta hankali kwance.

Wanka ya tashi yaje yayi ya saura kaya zuwa jallabiya yazo ya zauna tsakiyarsu yana fara cin abinci suna sake cigaba da firarsu.

Wayar SANAAH ce dake gefen mommy tayi haske tana fara ringing sunan wanda yake kiran ya bayyana kai tsaye akan wayarta wanda ya saka dukkaninsu kallan wayar suna yin shiru.

Kallo daya Yaya Al'amin yayiwa wayar ya dauke kai yana cigaba da cin abincinsa zuciyarsa na da fuskansa suna sauyawa baice komaiba.

Mommy ma fuskan yaya Al'amin din ta kalla bayan kallan wayar tukuna ta maida kallanta akan SANAAH wadda ta kafe wayar da ido kafin ta miqa hannunta a natse ta dauko wayar tareda dauka a natse ta dora wayar a kunnenta tana bude baki da muryanta dake sake kashe kowace gaba da gangar jikin me kiran tace

"Yes"

Numfashi da ajiyan zuciya me sanyi da nutsuwa dayake tattare da izza ya sauke jin yanda a koyaushe muryanta takeda wani irin karfi ga zuciya da gangar jikinsa ya bude baki da nutsuwa yace

"Ina kofan gida"

Shiru tayi na seconds kafin ta dan bude baki tace masa ok.

Kashe wayar tayi tana ajiyewa ta dago ta kalli yaya Al'amin ta bude baki tace

"AA yana waje"

Cikin yanayi na rashin bawa zancen da wanda ake zancen akansa mahimmanci yace

"A dawo lafiya"

Yana fadar hakan ya dauki ruwan data ajiye masa yana kaiwa bakinsa yafara sha.

Mommy da itama a yanzu ta gama fahimtar abinda yaya Al'amin yake nufi akan lamarin AA dayaqi ci yaqi cinyewa bude baki tayi tace

"Basai ya leqo gaidani ba ina gaidasa kawai."

Ajiyan zuciya SANAAH ta sauke tana miqewa ta shiga dakinta ta sako hijab me girma sosai har qasa akan kayanta yana qamshi me dadi da nutsuwa ta fice.

Wata lafiyayyar BMW ce black me daukan ido ko a cikin dare pake a kofar gidan daga gefe ta nufa tana isa shine ya bude mata motar daga ciki ta shiga a natse ta zauna tareda rife kofar.

Tinda ya bude motar ya zuba mata fararen idanuwansa yana mata wani irin kallan daya kasa dauke idanuwansa akanta har sai data juyo ta kallesa da idanuwanta da suke da haske da wani irin sanyaya gangar jikinta namiji duk zarrarsa har lokacin ya kasa dena kallanta a natse da wani irin miskilancinsa dayake tattare dashi shima wanda yakeda zafin kai da rashin bawa kowace mace mahimmanci ba idan ba uwarsaba amma SANAAH KHALIL ta zama macen dazaice kai tsaye kaddararsa dan kuwa wani irin jinta yakeyi maqale a cikin wani lungun zuciyarsa da bazai iya barin kowane irin namiji mallakarta ba hakama shima bazai iya mallakarta ba sbd zamtowanta yar marasa karfi ko kadan,

Duniyarsa da tata akwai tazara me nisa da karfin gaske da yake ganin duk yanda yake mutuwa da nacin tsananin sonta kaman rai bazai taba iya aurenta ba,
Bazai iya aurentaba sbd background nata hakama bazai iya barin kowa ya aureta ba zata zama tasa har abada koda hakan na nufin sedai tayita zama budurwansa koma macensa amma auren sam yayi yayi da zuciyarsa da raayinsa ya cusawa kansa aurenta ya kasa hakan sbd bai hada girman kansa dayake ganin yanada duniya a hannunsa dayake juyawa son ransa a cikin iko da isa da lokaci ba,
Yanada sunan da girmansa ya wuce ace ya auri macen da batada kowane irin suna da power ba a familynsu,
Yanada tarin dukiya da arziki da kyau da girman ajin data ko ina ya wuce yaqare da auren macen da bakowa bace ta fito daga asali da tarin talauci da kaf danginsu babu wanda zaa daga a kalla a matsayin mutum me daraja da girman da zaace yayi daidai da zamowa sun hada zuria,

Yana tsananin son SANAAH wadda takeda wani irin class da rashin daukan raini daga kowa,
Bata da shakkar kowa akan darajar kanta da sanin class din,
Bata taba zamowa koma baya ba ga dukkanin abinda kowace mace mai class da gata da wayewa da kamewa ke buqata ba,
Tanada wani irin kyau da class na daukan hankalin da bakowane namiji ne zai iya kallanta ma yayi tinanin fara cewa yana sonta ba sai wanda yakeda cikakkiyar zarra kamarsa ba,

Kyanta yakai harya wuce dukkanin inda yake son macensa takai,
Tsarinta da zafin kanta datake dashi dashi kansa bata damu da dukkanin abinda yake dashiba kokuma matsayinsa da power dayake dashiba daqyar ya samu tafara kallansa bayan tsawon lokacinda ya dauka yana bibiyarta da tsananin son mallakarta a matsayin macensa.

Bata tana kula kowane namiji ba sbd sam babu wata soyayya ko namijin da duk duniya yake gabanta sai akansa tin bayan rasuwar Nasir dinta,

Shima aranar daya fara ganinta a school dinsu a ranar zuciyarsa ta mutu kai tsaye akanta da kuma daukan ita din yar babban family ce sbd yanda tsarinta yake sai daga baya ya san ba kowa bace face qanwar datake samun dukkanin gata daga yayanta da baida karatun komai sai ayyukan wahala.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

27
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Koda ya gano hakan gameda SANAAH KHALIL zuciyarsa ta gama mutuwa akanta mutuwan da bazai taba iya dena sonta ba amma kuma bayajin zai iya aurenta ya hada zuria da ahalinta,

Yasha wuya sosoi da sosai matiqar gaske kafin SANAAH tafara basa lokacinta harma saida ya koma gurin yayanta ya samo shigar da kansa tukuna yaya Al'amin din da mommy suka tayasa shigar dashi zuciyarta data fara laushi akansa ahankali ahankali harma ya samu soyayyarta me sanyi da nutsuwa da karfin gaske a karo na farko ta fara son wani namijin bayan Nasir daya zama tarihi a rayuwarta,

Samun soyayyarta shine babban abinda ya bawa zuciyarsa da ruhinsa nutsuwa dan kuwa a yanda son SANAAH din ya zama kamar obsession garesa zai iya komai idan bai sameta ba dan lura da irin mahaukaciyan son dayake mata ne ya saka yaya Al'amin da mommy ganin sun sassauto zuciyarta ta aminta dashi dan daman fatarsu ta samu wanda zai sota sosai da sosai dagaske kuma tinda AA din ya bullo sukai naam dashi dari bisa dari.

A nata bangaren soyayya ce a yanxu zuciyarta kewa AA wadda takejinta a natse me zurfi data shirya zamowa tasa batareda kowace irin damuwa ko kunci ba dan haka suke zuba soyayya sosai,

Ita tata soyayyar me zurfi tanada tsari da control duk da me karfi ce amma tasa soyayyar obsession ce datai yawan da babu control dan hakanne komai nata baida control a zuciyarsa.

Sun dauko lokaci sosai a tare dan tin farkon fara karatunta suke tare kuma yan anguwan gabaki daya kaf sun shedar da irin soyayyar datake gudana a tsakaninsu sbd yanda motocinsa suke zuwa anguwan koyaushe babu kakkautawa,
Babu ranar da baya zuwa gidan matiqar yana gari,
Babu lokacin tafiyarsa idan yaxo sbd irin dadewan dayake yi,
Babu ruwansa da kowa da komai da mutuncin da zai zube shidai idan yaxo baya tafiya sai zuciyarsa ta gamshi ga ganin SANAAH KHALIL,

Hakama koyaushe a motarsa suke firar suke jimawan wanda hakan ya fara kawo damuwa da zubewan mutunci daga idanuwan mutane dake tsananin mutunta Al'amin da jinjinawa tarbiya da jajircewansa,

Ta bangare daya zafin kai da girman kai me tsananin da AA yake dashi baya iya ko gaisawa da kowa anguwan ko mutuntawa ya saka ya fita daga idanuwa da zuciyar kowa suke ganinsa a matsayin wanda sam duniyarsa da duniyar mutane irinsu bama zata taba zuwa daya ba dan haka kai tsaye suka tabbatarda ba auren SANAAH zaiyiba zai bata mata lokaci ne da kuma zubar da mutuncinta da darajar gidansu sai suka fara kokarin fahimtar da Al'amin illar hakan dan lamarin yafara yawan da ya wuce mutunci gwara idan aurenta zaiyi a basa auren nata ayi a wuce gurin yafi wannan rayuwar dasuke yi ta koyaushe tana gaban motarsa suna yawo.

Maganganun tin basa shigar Al'amin sbd yanason SANAAH ta gama karatu kafin aure amma ganin yanda maganganu suke yawo a anguwan harsun zama zunde sun saka mutuncin gidansu zubewa da kuma maida SANAAH abar kyama da lalacewan tarbiya ya saka yayi magana da mommy ya sanar musu zaiwa AA magana ya turo ayi maganar aurensu kawai ayi ta qarasa karatun acan.

A lokacinda yayiwa AA maganar farko kai tsaye AA din ya sanar masa ba yanzu ne zaiyi aurenba,
Mamakinsa hanasa cewa komai yayi dan haka ya kyalesu aka sake daukan lokaci abubuwa sunata sake tabarbarewa dan yakai shima a yanzu ba wani mutuncinsa ake ganiba a anguwan dan haka ya fuskanci AA dakyau ya sanar masa idan har ba auren SANAAH zaiyiba dan Allah ya fita rayuwarta kawai.

Nan ma babu wani sauyi sbd saima qara wata muguwar shakuwa da soyayyar me zafi sukeyi takai hatta shi kansa kunyar kansa da baqin cikin kansa yakeyi idan yaga soyayyar na qara karfi dan haka ya fara daukan mataki sosai akan SANAAH din akan matiqar AA bai aikoba akai maganar aure ya rabasu.

SANAAH bata taba wasa da maganar yaya Al'amin ba dan haka take tai kokarin yanke AA daga rayuwarta duk da wani irin zazzafan son datake masa amma kuma zata iya zabar mutuwa akan sonsa data tsallake maganar yaya Al'amin.

AA yankesa da SANAAH tayi daga rayuwarta ya sakasa jin zai iya rasa komai amma bazaitaba iya rasata ba dan haka ya nemi Al'amin ya aminta da zancen aiko iyayensa maganar auren.

Da wannan Al'amin ya bar SANAAH cigaba da kulasa sedai kuma shiru shiru ba zancen aikowan gashi anguwan take aka hade musu kai gabaki daya hadda kiransa akai masallaci akai masa maganar suna kokarin bata tarbiyar yaran anguwa kanana masu tasowa dan haka duk sai ya shiga sabuwar damuwa mai tsananin gaske data saka yaji ya tsani muaamalar SANAAH da AA kwata kwata auren ma yafita a ransa musamman daya fahimci dakyau babu niyar aure kwata kwata a zuciyar AA.

Shi kuwa AA a wannan lokacin da Al'amin ya dauki zafi sosai ya gama gano babu yanda zaayi ma yanxu Al'amin din ya iya basa wata daman auren SANAAH saiya fara kokarin cusawa kansa raayin auren nata amma girman kansa da ego dinsa ya kasa yaddar masa ya aureta duk da yanda yake jinta a ransa dan haka sai yake jin shaawan son mallakarta a matsayin cikakkiyar mace koda zafin sonta dayake ji zai iya rage masa ya kyaleta.

******Ajiyan xuciya da numfashi me dumi ya sake ahankali tareda shaqar qamshinta me nutsuwa ya dan dauke idanuwansa daga kallanta daidai nan sautin muryanta ya sauka akan kunnuwansa tace

"Yaya Al'amin yana nan bazan dade ba"

Ajiyan zuciya ya sake saukewa yana bude baki yace

"Amma kinsan bazan iya tafiya kai tsaye ba batareda na jima a gurinki ba"

Fuskansa ta kalla da kyau tana bude baki tace

"Idan kasan hakanne meyasa bazakai abinda yakeson ayi dinba?
Meyasa bazaka turo ba?

Dauke idanuwansa yayi daga kanta yana maidasu akan dogayen fresh fararen yatsun hannuwanta data ajiye akan cinyarta ya lumshe ido suna daukan hankalinsa cikin ruwan sanyi ya bude baki yace

"Banajin dukanmu muna cikin gaggawar yin auren,
Idan na shirya yin auren nine zan sanar da kaina bana buqatan kowa yayi rushin dina....

Yana gama fadar hakan kallan fuskarsa tayi tana jin wani irin baqin cikin fara sonsa datai ta hadiye maganar dataso fada masa sbd bama amfani dan haka hannunta kawai ta miqa ta bude kofar ta fice.

Fitowa motar yayi shima yana sake qaramin tsoki sbd duk sun hanasa zaman lafiya ya biyota

Saka kai tayi cikin gidansu daidai nan ya iso gurinta bai tsaya komaiba ya kamo hannuwanta duka biyu tareda juyota da karfi yana dawo da ita daidai nan Yaya Al'amin din ya sako kai gurin kuma akwai nepa ga mutane daga kofar gidan a zaune.

Cikin zafi ta qwace tana kallansa da wani irin zafi zatai magana Yaya Al'amin ya dakatar da ita cikin danne tsananin fushinsa da bacin rai da wani irin baqin ciki kafin ya nuna mata ta wuce ciki kawai.

Wucewa tayi idanuwanta jajir zuciyarta na wata irin tafasa kaman zata kone sbd jin xafin ma zuciyarta datake jin son AA din.

Fuskantarsa yaya Al'amin yayi ya bude baki a natse yace

"Inaga zuwa yanzu dai munkai matakin da indai ka sake zuwa kofar gidan nan zan iya hadaka da hukuma sbd babu wani sauran abinda ya rage a tsakaninka da ita idan ma akwai na yanke shi daga yau babu kai babu ita kayi hkr ka tafi batareda munkai hukuma ta shiga tsakaninmu ba.

Yana gama fadar hakan ya juya yabar AA din a tsaye wanda baijin akwai wanda duk duniya zai rabasa da SANAAH.

Acan cikin gida ma yana shiga gargadi me karfi yayiwa SANAAH akan AA din wanda ya yanke shawarar hadasa da hukuma idan har bai kyale SANAAH ba.

Da wani irin bacin rai da damuwa SANAAH ta kwana na AA data rasa meyake damunsa akan aure.

Haka ta shirya cikin nutsuwa ta fice zuwa makarantar da safen bayan tayi breakfast sama sama.

Tana fita napep ta hau ta wuce,

Wuni tayi makaranta ma wayarta a kashe sbd kiranta datasan AA din zaiyi kuma bata buqata kwata kwata zata cire sonsa ta hakura ta huta shima.

Yamma sosai ta gama da makaranta ta wuce gida,

Bayan isarta gida ma bata kunna wayarta ba dan bazata ganin kiransa ba batareda tadauka ba,

A haka sukai kwana biyu shiru ba AA dan haka ta hakura ta sakawa ranta shikenan ya tafi.

Komawa tayi harkokin gabanta tana maida hankalinta akan karatunta kawai,

Ranar da sukai sati biyu ba tare ba tana dawowa daga school ta tadda sabuwar motar Cclass a kofar gidansu tana daukan ido kai tsaye bugun zuciyarta ya tsaya cak sbd ta tabbatarda AA ne dan kaf layin shine kadai me zuwa da motocin daukan hankali irin wainnan.

Wani nauyi ne ya danne kirjinta a hankali wanda yasakata kama fuskanta sosai ta fito a natse sanye da riga da skirt na atampa masu kyau da suka zauna daidai jikinta.

Sallamar mai napep tayi tana juyawa zata shige gida sai ganinsa tayi a gabanta idanuwansa sun sauya sbd wata irin azababbiyar kunar da ransa ke yi ta kwanakin da yayi batareda jinta ko ganinta ba.

Bata kallesaba saima kame fuskarta datai sosai tana kokarin rabesa ta wuce batareda kowace irin hayaniyaba.

Kama hannunta yake kokarin yi ta dakata cak tana dagowa da idanuwanta tai masa wani kallon daya sakasa bude baki yace

"Inason magana dake pls kafin nayi da Al'amin"

Dauke kallanta daga fuskansa tayi tana son sake wucewa tace

"Kafara magana dashi din tukuna"

Sake tareda yayi yana cewa

"Pls kiyi magana dani tukuna sbd bazan tafi koina ba sai munyi magana ga mutane kinga sun fara kallanmu kuma nasan hakan ne zai baqanta ran Al'amin sosai"

Juyawa tayi ta kalli gefen gidan taga su ake kalla hakama kaman zaa iya jin abinda zasu fada gashi Yaya Al'amin din zaiji.

Rabasa tayi tai shigewanta cikin gida tabarsa a tsaye.

Bayanta yabi da kallo idanuwansa jajir yanajin wani sabon daci da bacin rai me tsanani akan abinda tai masa din a matsayinta na wadda ba kowaba da batada kowane irin matsayi a duniyar itada ahalinta da ko kadan basuyi rabin kwatar daraja da matsayin dayake dashi ba.

Hadiye wani mugun nauyi yayi a kirjinsa yana komawa motarsa.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

28
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5

Please Login or Register in order to submit comment