Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Duk yanda zuciyarsa ke zafi da quna da bacin ran sauke girman matsayinsa da ajinsa dayayi akan son daya qallafa mata daurewa yayi ya nemi Al'amin a daren ya dade yana magana dashi ya kuma tabbatar masa daya shirya auren nata da kuma buqatan a basa ranar dazai aiko iyayen nasa.

Da farko Al'amin baiji lamarin AA din a zuciyarsa da jikinsa ba dan haka yace ya dan dakata tukuna zai nemesa.

A haka suka rabu ya shigo gida ya zauna da mommy ya fada mata komai yana jin hankalinsa na rabuwa biyu akan lamarin amma dashi da mommy sai suka kira SANAAH kai tsaye suka tambayeta akan auren AA din.

Da farko kaman a mafarki taji zancen amma kuma a qasan zuciyarta ta sani tana son AA son datake shirye dayin rayuwan aure dashi sedai matiqar Yaya Al'amin baya son auren bazata taba yinsa ba har abada dan haka dagowa tayi ta kalli yaya Al'amin din babu boye boye a tsakaninsu sun taso da bayyanawa juna komai dan haka ta bude baki a natse tace

"Yaya Al'amin idan bakason auren nima bana sonsa"

Kafeta da ido Al'amin yayi yana jin jikinsa na dan yin sanyi yace

"Kina son AA SANAAH??

Gyada masa kai tayi tana jin haushin kanta da zuciyarta gashi bata iya karya sam bare tace aa bata sonsa.

Mommy ma ajiyan zuciya ta sauke jin amsar SANAAH din dan haka daga ita har Al'amin din take suka sake naam da lamarinsa sbd basa wani tada hankali ko hayaniya akan komai kawai dai yanxu zaije ya samu manyan anguwan sune zasu tayasa karban baqin da bada auren tinda shi kadai bazai iyaba ko dan a bawa SANAAH girma a idonsu.

Sai da aka kwana biyu AA na bin Al'amin kafin ya amince masa daci gaba da neman SANAAH din da kuma basa ranar zuwa neman auren da iyayensa.

Hakan ya dawo da izzar AA da walwalan daya rasa girman kansa ya kuma qaruwa ganin ya sake dawo da SANAAH rayuwarsa itada ahalinta dazai iya juyawa son ransa kuma ya kasa iya yadda da aurenta a matsayin matarsa har lokacin.

SANAAH din bata sake masa ba sun dawo daidai sbd jin zafinsa har lokacin takeyi dan haka sama sama suke ta kama kanta sosai dashi tana ja masa wani irin ajin dayake sake kashesa akanta dan duka manyan yan matan daya sani masu muamala dashi babu wanda tai class da iya jan ajinta da kame steez dinta kaman SANAAH KHALIL dan hakane ta kasa barin zuciyarsa ta moru ga kowace macen bayan ita matsalarta daya inda ta fito da baiyi daidai da inda ya fitoba.

SAMRAH SADEEQ itace budurwarsa daya data gama mutuwa akansa ta rasa nata hankalin da tinanin akansa kuma take daidai da ajin aurensa sbd familynta da suke da tasu power din da suna daidai gwargwado duk da basuyi na familynsa ba amma sunada karfi sosai da aurenta shine daidai shi amma sam ya kasa jin sonta na maitarta kaman yanda yakejin SANAAH gashi ya kasa rabuwa da ita itama sbd tinanin aurenta idan auren ya kama dole.

Ita kanta Samrah tasan yanda ya SANAAH KHALIL take a xuciyarsa babu yanda zatai ta iya cireta amma sanin bazai taba auren SANAAH ba ya saka damuwanta dan taqaituwa sbd yanada wani irin girman kai da bazai taba saukowaba yayi auren da ba kwarya tabi kwarya ba gashi kaf familynsa tin farkonsu haryanzu a tarihi basu taba hada zuria da familyn da masu karfin gaske ba bazai yadda shi ya auro ba hakama mahaifiyarsa bazata taba yadda ba dan hakan ne ma tinda tasan ya kwallafa rai akan yar da ba kowaba ta tsani yarinyar ta tsana me tsananin gaske tareda tabbatarda ta qara masa karfin akidar rashin auren.

Samrah na kishin SANAAH kishi me tsananin da kota auri AA to bazata taba dena kishin SANAAH ba dan tasan bazata taba fita zuciyar AA dinba har abada dan sonta a ransa kaman cuta ce da ba magani.

Daqyar SANAAH ta dawo masa daidai gashi kuma har lokacin zuwan iyayen nasa yayi basu taho ba sai aka qara masa kwanaki a lokacin ne ya shiga wani irin sabon tsananin zuciya daya fara sakar musu wasu irin mahaukatan kudi dasu da yan layin kaf haka ya ringa yi musu barin kudi da barnarsu kaman mahaukaci sbd kawai a dena maganar.

Kwanaki da lokacin aka sake dauka dan haka sai damuwa mai tsanani ta rufe Al'amin da nauyin uba yake kansa ganin irin son da SANAAH kewa AA gashi dai a karo na babu adadi ya sake nuna ba kowane su din ba dan haka sai ya sake kokarin rabasu sbd itama mommy ta fara shiga damuwan abinda ake fada a anguwa akansu.

Manyan anguwa ne suka nema AA din da kansu suka hadu da Al'amin sukai masa kashedin karshe akan SANAAH tareda yanke kowace alaqa wannan karan ko auren kwata kwata an fasa basa baa buqatan manyan nasa ma su taho.

Tinda suka fada masa hakan batareda SANAAH ta saniba zuciyarsa ta shiga duhu da nauyin dacin ganin irin mutanen da suke zaunar dashi suna fada masa magana dan haka yau da kansa yaje makaranta daukan SANAAH wadda ba damuwan komai ta shiga motarsa suka kama hanya.

Kallansa tayi a dan natse tana dauke kai tareda dago wayarta tana duba sako ta bude baki zatai magana sai kuma ta fasa sbd ganin yanayinsa kaman baya hayyacinsa kuma duk yanayinsa ya sauya da damuwa da kaman qunci.

Hanyar daba gida zata kaisu ba ya dauka ta dan sake dagowa ta kallesa tana son masa magana amma ganin yanda fuskansa take hade sai itama ta basar dashi taci gaba da duba wayarta sai data sake dagowa taga anguwan da suke shiga ta wasu gidajen masu karfi a qasa dasuke da tsaro tsit ba hayaniya hakama ba ruwan kowa da kowa koina shiru ne kaman ba muten a anguwan manyan gidaje ne da wasu irin tsarin da ita batama taba zuwa irin guraren nan ba ya sakata ajiye wayarta tana dagowa ta juyo ta kallesa da kyau ta bude baki tace

"Meyake faruwa?
Me nakeyi anan?
Kasan bana zuwa koina ko?
Pls mu juya ka maida ni gida ko ka ajiyeni a hanyar da zan hau napep din wucewa gidan.

Time ta kalla taga magrib ma ake kokarin kusan yi dan hakan taji ma gabaki daya hankalinta na neman tashi dan bata taba zuwa koina ba batareda sanin yayanta ko mommy ba hakama sam bayan makaranta vata zuwa koina tana gida koyaushe.

Baice mata komaiba ya qarasa lafiyayyan mahaukacin bungalow dinsa take yayi horn security dinsa ya fito daga ciki ya bude masa gate din mai kyau da tsari ya shige ciki yayi parking.

Wayarta ta daga zata saka kiran yaya Al'amin ranta a matiqar bace sai AA din ya saka hannu ya karbe wayar tareda jefar da ita yana bude motar ya zagayo ya budeta tareda kama hannuwanta biyu dake rawa sosai ya fixgota daga cikin motar yana kallan cikin idanuwanta da suka ciko da wani irin hawayen baqin ciki da tsananin tsoron da bata taba shiga ba yana jin kaman ya bude cikinsa ya sakata kowama duniya ya rasata sai shi ya gangaro da idonsa a hannuwanta daya damqe sa karfi tana kokarin fizgewa yaji wani tsananin sonta mai hade da shaawa me karfin gaske dayake son sauke mata sbd kawai yaji ko zai rage sonta da kuma idan yayi mata hakan ne kawai yayanta zai hakura ya jirasa ya aureta.

Yace

"SANAAH bazan taba iya barinki ba kaman yanda bazan taba iya aurenki ba,
Bansan tayaya zan iya rabuwa dake ba,
Meyasa dole sai munyi aure yanzu?
Nace ki bani time Insh Allah zan tilastawa zuciyata aurenki kuma zatai sbd tana sonki amma ba yanzu ba pls.....

Turesa da wani karfi tayi tana jin wani baqin cikin dayake neman kasheta yana danne kirjinta da idanuwanta da sukai jajir suna rufewa sbd ko zata mutu batajin har abada ma yanzu zata iya auren AA.

Riqota yayi da karfi yana daukanta gabaki daya tareda rufe bakinta data bude da karfin gaske zatai ihu.

Ciki yayi da ita yana shiga a palon ya jefar da ita a kan babbar lafiyayyar kujeran 3 seater sbd yanda take wani zillo da karfi tana jin zuciyarta zata buga.

Da karfi koina nata yana rawa ta yunkuro zata miqe da sauri,
Danneta yayi yana mata runfa da kirjinsa tareda danneta da hannuwansa biyu yana kokarin kai hancinsa wuyanta dan shaqo qamshinta dayake kashe hankalinsa.


A daidai wannan lokacin Samrah data ga motarsa a daidai lokacin dayake shigowa anguwan tana cikin tata motar biyosa tayi sbd ganin mace a gaban motarsa data tabbatarda SANAAH ce wadda take zuciyarta ta shiga wani baqin duhu da tsananin zafin kishi da hatta idanuwanta wasu zafafan hawayen baqin ciki suka cikosu suna kokarin zubowa ta iso kofar gidan tayi parking daga waje.

Buga gate din tayi take security daya ga itace ta security camera ya bude mata kofa ta shigo kai tsaye ciki tayi batareda ta tsaya ta amsa gaisuwansa bama.

Tana isa kofa bata tsaya knocking ba ta bude kofar kawai ta shiga sbd tasan password.

Cak ta tsaya idanuwanta na rufewa da wani duhu kafafunta na rawa ganin abinda yake shirin faruwa tanajin jiri na neman dibarta.

Tura fuskansa yakeyi a wuyanta tana turesa da karfi tana wani irin kuka mai karfin gaske tana neman ceto da fatar Allah ya dauki ranta kafin AA yayi nasarar yi mata wani abin.

Samrah data rasa me zatayi hannuwanta dake rawa ta daga da wayarta ta ringa daukan abinda yake faruwa idanuwanta na tsiyayo da hawayen baqin cikin kishins AA din.

Juyawa tayi zatabar gurin bata ma gani sosai sai kuma kishinta na barin SANAAH ta rigata sanin AA ya sakata juyowa ido rufe ta dauki qatuwar flower verse dake gurin ta buga masa akai da karfi take ya zube gurin.

SANAAH data gama fita hayyacinta sbd kuka da tashin hankali da tsananin tsoro miqewa tayi koina nata yana rawa gyalenta a hannu da dankwalinta tayo gurin samrah din da sauri bata hayyacinta ta riqeta da karfi tana fasa kuka da neman taimakonta.

Mota samrah ta fito da ita ta turata ciki sbd gabaki daya SANAAH din bata hayyacinta rawa jikinta yakeyi me tsananin gaske.

Suna barin gurin da gudun gaske samrah taja mota bata tsaya koina ba sai kofar gidan su SANAAH din wanda Al'amin ke tsaye yana kaida kawo idanuwansa jajir wayarsa a hannunsa sbd tinda SANAAH take bata taba kai dare a waje ba ga wayarta yanata kira tana ringin baa dauka.

Parking motar samrah tayi wadda ta saka idanuwan duk mutanen dake layin dawowa kansu.

Shima kasa motsawa yayi saida yaga SANAAH a gaban motar jikinta na rawa har lokacin idanuwanta jajir.

Tana ganinsa ta fito motar jikinta na tsananta rawa shi kuwa mutuwar tsaye yayi da mamaki zuciyarsa na wani irin mugun harbawa da karfi sbd kallo daya yayiwa SANAAH mummunan tinanin da gwara ya mutu daya ji hakan akan SANAAH ya shiga ransa.

Ita kanta SANAAH tana fitowa wani irin kuka tafasa mai ratsa zuciya tana fadawa jikin Al'amin wanda koina nasa ke wata irin rawa.

Samrah sauke glass tayi ta kallesa ta bude baki tace

"Idan har bazaka iya bata tsaron daya kamata ba to ka shirya tabbatarda abinda bai faru ba ayau zai faru wata rana"

Tana gama fadar hakan taja motarta ta bar gurin tabarsa tsaye jikinsa na tsananta rawar da hatta kafafunsa kasa daukansa sukai yayi baya saida ya dafa bango.

Dukkanin wainda ke kofar gidan a zaune sunji abinda ta fada dan kowa koina yayi tsit suka kafe SANAAH da idanuwansu cikeda mamaki da tsoro dan kuwa ma a yanzu a take wani kallan suka fara mata.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

29
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki  Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki  Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce  For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Suna shiga cikin gida Yaya Al'amin dakatawa yayi tsaye cak a tsakiyar gidan yana riqo hannunta da karfin gaske har lokacin koina jikinsa rawa yakeyi ya kalleta idanuwansa jajir ya bude baki zaiyi magana ta fasa wani irin kuka tana fada masa abinda ya faru cikin matsanancin tsoro da rikicewa batareda ta jira yayi tambayarba.

Baya yayi ahankali cikin wani irin shock da mummunan tashin hankalin dabai taba shiga ba ko a lokacin daya rasa mahainfinsa,
Wani irin radadi ne yake cike idanuwansa suna sauyawa zuwa jajir ya dafa bango ahankali yana zamewa qasa yayi zaman yan bori tareda rintse idanuwansa ahankali dan kuwa baima iya yadda da rayuwar SANAAH dinsa bata lalace ba,
An lalata mata rayuwar dayake ta kokarin bawa kariya da tattalawa,
An bata rayuwar daya sadaukar da tasa rayuwar gurin ingantawa da bawa kariya da rayuwarsa,
Ya gaza ya zama mara amfanin dayake tinanin yanada shi,
Ya kasa tsare mutuncin qanwarsa da zai gwammaci ace shine aka lalata rayuwa ta karfi akanta.....

Cusa kansa yayi cikin kafafunsa wasu irin hawayen dabaima san suna fitowa suka fara gangaro masa yana jin kaman kirjinsa da kansa da idanuwansa zasu kama da wutar da babu sauki a cikinta,

Ita kanta SANAAH din zubewa tayi a qasa inda take tana fasa wani irin kukan dayake ratsa kunnuwansa da zuciyarsa suna tarwatsa duk wani kuzari da zuciyarsa.

Ita kanta wani irin rawa da tsoro me tsananin gaske jikinta da zuciyarta take ciki dan kuwa tasani rayuwarta ta riga ta lalace ta zama macen da babu cikakkiyar daraja a tattare da ita yan anguwan sunsan an mata abinda shine da wanda ba shine gashi har lokacin a firgici take tanajin AA a jikinta.

Mommy datake zaune ta kasa motsawa ajiyan zuciya ta sauke ahankali jikinta na sakewa tareda komai nata idanuwanta a kafe akan SANAAH wadda alamar jikinta da halin datake ciki da yanda jikinta ke fixga ya tabbatar musu da angama lalata rayuwar tata shikenan.

Wani nauyi me karfi da zafi ne yazo kirjin mommy ya danne mata numfashi ta bude idanuwanta da sukai jajir tana son magana amma ta kasa sai ganin zamewa tayi a gurin tayi kwance tana jin kirjinta da zuciyarta na bugawa ba daidai ba.

SANAAH ce ta rarrafo tayi kan mommyn a rikice tana kokarin fasa wani kukan amma bayama iya fitowa ta fada kanta tana girgiza mata kai da cewa bai nasarar lalata mata rayuwa ba amma sam mommy bata jinta sbd jinta daya dauke take numfashinta ya yanke a gurin.

Kuka SANAAH keyi tana girgizata amma ba alaman motsi ta juya ta rarrafa gurin yaya Al'amin ta fara jijjigarsa shima tana wani irin kukan dayake tayar da tsigar jiki.

Daqyar ya iya lalubo hankalinsa da ganinsa da jinsa yayi kan mommyn yana dagota gabaki daya ya fice da ita da sauri.

Miqewa SANAAH tayi batama gani sosai tabi bayansa tana jan hijabin mommyn dake tsakar gidan ta saka a jikinta suka fice.

Titi sikai anata kallansu cikeda mamaki da maganganun tabbatarwa da SANAAH dai AA yayi nasarar lalata mata rayuwa ta koma fankon da babu me iya kallanta da darajar aure idan ba dan iska mara Mutunci ba irinta dan uwanta ba.

Adaidaita suka tarar suka fada babu bata lokaci akai asibiti dasu har lokacin babu alaman rai a tattare da mommy.

Suna isa aka karbeta zuwa emergency ana tambayarsu meya sameta.

Fada sukai cewan zubewa tayi sbd shock.

Anayin ciki da ita suka koma gefe suka tsaya a rakube har lokacin hannuwansa da kafafunsa rawa sukeyi idanuwansa na tsananta shiga mummunan halin dayake jin kaman ya dora hannu akai ya fasa ihun da duk duniya sai taji radadi da zafin kuncin da zuciyarsa take a lolacin.

Ita kanta SANAAH har lokacin kuka takeyi jikinta na rawa ta qanqame kanta a jikin bango tana kasa dagowa.

Zaman dayafi na daren baqin sukai a wajen babu wanda yace kala sai yanayinsu dayake nan bai sauyaba suna jiran farfadowan mommy da akace shock ne yaso bata attack na zuciya amma da dan sauki yanayin.

Har tsakiyar dare sosai suna zaune cikin tsaka me wuyar da duka suke fatan inama ace sun mutu basu sheda wannan mummunan ranar ba,
Mommyn bata farko ba sai guraren karfe uku saura na dare cikin wani irin yanayi na mutuwan jiki da rashin kuzari ko kadan tareda damuwa me tsananin data saka idanuwanta qanqancewa bata gani sosai itama hannuwanta rawa suke dan yi.

Shiru sukai jigum jigum babu me cewa komai har asuba tayi Yaya Al'amin ya fice sallah.

Suma zuwa lokacin sun dena kuka babu karfin jiki ba sauran kowace irin walwala da kuzari SANAAH ta kama mommyn sukaje tayi alwala da sauransu itama tayo suka dawo sukai sallah.

Suna idarwa sukai sake shiru jigum jigum da shiga tinani ba tareda motsin komaiba.

A hakan yaya Al'amin din shima ya dawo ya bude baki ya gaida mommyn da jiki cikin wani irin sanyi da rashin walwala.

Itama SANAAH bude baki tayi ta gaidasa bai iya amsawa ba sai wani irin nauyi dayaji ya sake dawo masa sabo ya danne masa kirji da zuciya.

Daga shi har mommyn babu me iya kallanta dan kuwa suna kallanta zasu iya samun bugawan zuciyar kallanta a matsayin wadda wani ya ketawa haddi dan haka suke kasa kallanta gashi ita kanta ta kasa dagowa ta kallesu kunyar kanta da baqin cikin ganin halinda suke ciki takeyi.

Gari na wayewa sosai aka sallamosu suka dawo gida,
Koda suka sauka daga cikin adaidaita akwai mutane gefen kofar gidan sosai anata xaman da aka saba,

Kallo aka bisu dashi daya saka Yaya Al'amin din jin duniyarsa na sake duhu sbd rayuwarsu su duka a yanxu ta samu wannan mummun tabon da bazai taba gogewa ba hakama bazai taba barin SANAAH ta samu mijin daya kamata ba anan din dan kuwa abu ne da yan anguwa yanzu suka sani wanda kuma hakan ne sukaita masa gudu akan huldar AA da SANAAH dan haka da alfahari zaa ringa fada da kuma sanar da duk wanda zaizo neman aurenta.

Sallamar mai adaidaita yayi suka shige cikin gida ya rufo gidan sukai ciki.

Suna shiga daki suka kai Mommy wanda tayi weak sosai a dare daya dan jin nauyin kirji da ciwo sosai takeyi amma ta danne.

Ruwan wanka SANAAH da itama takejin batada lafiyar sosai ta hadawa mommy takai mata taxo ta taimaka mata har toilet tukuna ta dawo itama tai shirin wankan.

Bayan fitowan mommyn wanka tayi itama ta koma daki ta kasa komai ta dunqule a katifa sbd wani irin zazzafan zazzabin dayake cinta.

Kayan tea da bread Yaya Al'amin ya fita ya siyo ya dawo da kansa ya kunna dan qaramin gas din dasuke dashi ya dora ruwan zafin tea ya hada komai da kansa ya kaiwa kowannensu a daki ya sakasu tashi suka sha tukuna ya barsu suka kwanta shima yaje yayi wanka ya kasa fita koina ya shige dakinsa ya dunkule dan jikinsa har wata fizga takeyi sbd zafin zazzabin shima.

Wuni sukai gidan tsit a rufe kaman babu kowa sbd babu me lafiyar jiki data zuciya.

Sai kusan yamma kowannensu ya dan samu damar iya tashi suka fito daya bayan daya sukai wanka da sallolin dake kansu a lokacin ne ya sake fita ya samo musu abincin da zasu ci sbd daga Mommy har SANAAH din babu me iya girki.

Haka ya daure ya kula dasu har washe gari tukuna SANAAH ta warware mommy ma ta warware amma ta rasa kuzarinta kwata kwata dan abun ya tsaya cak a tsakiyar kirjinta ya kasa sauka kila harta mutu bazai taba sauka ba ace 'yarta mace daya a duniya anci mutuncinta haka.

Yanda yaya Al'amin ya danne ciwo da radadi da baqin cikinsa ya kula dasu sosai suka dan warware sai kawai shima ya fadi ciwon mai tsananin daya saka hankalinsu mummunan tashi sai gasu a asibiti an basa gado sbd ciwon nasa sosai yayi nauyi ciwon zuciya me tsananin gaske da nauyi.

Ciwonsa ya saka mommy sake shiga mummunan hali sbd shine bangonsu jigonsu,
Ita kanta SANAAH tashin hankali da tsoron da bata taba shiga ba a kusa kusa ta shiga ganin yaya Al'amin din kwance ba kyan gani,

Da kuka take wuni dashi take kwana dashi take sallah dashi take wanka da komai,
Damuwa da kuncin da basu taba shigaba suka samu kansu a ciki sbd yanayinsa,
Ana cikin hakan kuma kudi sukai musu qasa gashi me nemowan ne kwance.

Dole SANAAH ta dawo gida tana dan gudanar da Sanaar da sukeyi ta cikin gida wadda ma kusan sun dena,

Daga baya kuma mommy haka ta daure da yanayinta tana sanaoin SANAAH kuma ta koma itace a asibiti tareda Yaya Al'amin din.

Wata irin damuwa da qunci ne suka saka SANAAH ta fara wata rama da sake komawa wata irin me sanyi sosai da rashin son mutane da shakkar mutane sam bata iya ko zama cikinsu sbd rashin son hayaniya da tsoron abinda zai iya biyowa baya.

Sati hudu da kwanaki Yaya Al'amin yayi a kwance cikin jinya me tsanani kafin ya samu saukin da aka sallamosu suka dawo gida.

Ya rame ya zama kalar tausayi sosai dan kaman wanda yayi jinyar shekara ya koma ga yanayin rayuwar ya sauya musu ya dawo baya dan kuwa a yanxu suna cikin wani halin dasuke buqatan komawansa aiki sosai dukansu.
Sunada abinci da komai amma dai kudi kam sam babu sedai yan canjin da baa rasa ba.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

30
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai

Please Login or Register in order to submit comment