Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iko a gidam Sir hakeem jeerah.

Raheem baida sanayya da kowa dan haka koda ya isa gurin kakanninsa da safe ya gaidasu sukai kokarin gabatar masa da familynsa ya gaisa da kowa batareda ya kallesu da kyauba ya tantance su,

Koda Rana ta qarasa yi tini aka kawo masa mota sabuwa dal da kakansa Alh farouk ya siya masa sai wadda dad dinsa shima yasa aka kawo masa tareda driver dan bazai iya yawo da kansa ba sbd baisan koina ba.

Kai tsaye gidan Maamah da bazai taba mantawaba koya manta da koina yasa driver yakaisa da yamma lis sbd sai a time din ya samu kansa yana tareda kakansa.

Bayan sun isa suka tadda gidan an maidasu shaguna da gurin abinci dan haka maqota driver ya shiga yayo musu tambaya sai gashi kuwa akai musu kwatancen inda su Babak khalil din suka koma.

Koda suka isa gidan Baba Khalil na waje kofar gida yana magana da wasu maqotansa akan harkar masallacinsu na anguwa.

Kai tsaye baba khalil din bai gane Raheem ba sbd girmansa da sauyawansa gabaki daya dan kuwa babu alamar dayake nuna ya hada jini da yan Nigeria dan ya koma mahaifiyarsa sak ga wani irin kamewa da kwarjini da tsananin kamun kai a tattare dashi.

Dukansu shi da maqotan tsayawa sukai suna kallansa tinda ya fito motar cikin nutsuwa da kamewa ya nufosu batareda ta iya kafesu da iso wanda yake dabiarsa ce rashin kallan mutane sosai.

Shi Raheem ya gane baba khalil din shiyasa ya nufosa drivernsa na gefensa.

Yana isowa gabansu gefen baba khalil din yayi kadan yana bude baki cikin hausarsa da bata fitowa kai tsaye sbd ta jiqu da turanci da larabci ya gaida baban kafin ya dan dago kadan ya kalli su malam salisu dake tsaye sun kasa dauke idanuwansu akansa dan kuwa ko kamshinsa kawai daya bugesu jin suke kaman sunbar qasar dan kuwa basu ma taba jin irin kamshi me nutsuwa da dadin gaske ba kaman wannan, qamshi na shigarka kana jin kaman bacci na neman sauko maka.

Baba Khalil na bude baki cikeda mamaki zaiyi magana Nasir na isowa kofar gidan akan mashin,

Numbern motar kadai datake dauke da sunan jeerahs ya sakasa zubawa wanda yake hangowa a kofar gidan,

Gabansa ne ya fadi da karfi dan kuwa abune da bai taba zato dan haka daqyar ya iya dago kafafunsa ya iso kofar gidan suna kasa dauke idanuwansu daga juna cikeda wata irin zallar tashin gashin jiki kowannensu na jin wani numfashi me sanyi na kubce masa.

Nasir ne ya fara ambatar sunansa da wani irin sautin daya saka baba khalil kallan Raheem din sbd sai yanzu ya ganesa.

Ware hannuwa sukai suka rungume juna da karfin gaske irin na maza Nasir na sake ambatar sunansa da karfi.

Wani irin murmushin da babu wanda ya taba gani a fuskansa ya sake yana bayyanarwa cikeda farin cikin da bai taba ji ba dan kuwa wani sanyi ne yake ratsa zuciyarsa da bata saba ba.

Kasa tsayawa Nasir yayi ya kama hannunsa ya jasa zuwa cikin gida gurin Maamah.

Tana zaune tana sauraron redio ta nutsu tana jin labarin wani mutum da aka kama da yara ya sace sai ganinsu tayi suna doso ta hasken fatar Raheem ne ya fara daukan idonta ta zuba masa ido batareda ta kyafta ba tanajin zuciyarta na bugawa da karfi idanuwanta na cikowa da hawaye masu dumin farin cikin ganin Raheem dako girman me zaiyi bazata kasa ganesa ba.
#MAMUH

GANIN IDO
1K
VIP 5K
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

16
Shi kansa Raheem wani shauqi yaji na ganin Maamah a gabansa dan haka a natse ya qaraso gareta tana miqewa tsaye ya rungumeta a hankali bayan ya ambaci sunanta da wata irin nutsuwa da muryansa mai kauri ta namijin gaske dayake cikin lokacin karfinsa.

Wasu hawaye ne suka sauko mata ta bude baki itama ta ambaci sunansa tana sake maimaitawa.

Nasir kuwa duk yunwa da gajiyar daya dawo dasu jin yayi sun bace bakinsa da zuciyarsa kaman zasu fashe sbd tsabar farin ciki da murnar ganin rabin jikinsa ya zuba masa ido yana kallan komai nasa da kowace motsinsa da murmushinsa me kyau bakinsa duka yaqi rufewa farin ciki ya masa yawan da bai taba jinsa ba.

Mommy zainab ce ta taho itama cikeda farin cikin bayyanar Raheem din
Nasir dinta itama dan haka ruwa masu tsafta taje ta kawo masa cikeda kulawa da sosai.

Sun gaisa amma bai iya kallanta ba sosai dan haka itama kasa zama tayi sbd gabaki daya ya cika mata ido bata dauka haka yake ba duk da tasan mahaifiyarsa balaraba ce amma bata tsammaci ganin cikakken namiji kamarsa ba duk da shekararsu cif cif da Nasir amma yafi Nasir zamowa cikakken namiji dan haka ta tabarsu ta koma gefenta.

Shi kansa Raheem idan ba daga shi sai Maamah da Nasir ba baya sakewa da kowa dan haka shima baba khalil yana zuwa suka gaisa tareda yar fira sama sama saiya tafi yabarsu.

Bai bar gidan ba sai dare tareda Nasir suka tafi jeerahs sbd suna buqatar kwana a zaune suna magana.

Acan suka kwana makeken bangarensa dayake dauke da kusan daki hudu da parlours.

Raheem yakai Nasir har gurin kakanninsa duka ya gaidasu hakama ya kaisa gaban Dad dinsa wanda ya nunawa Nasir kulawa sosai da sakewa wadda ma Raheem bai taba gani daga garesa ba

Sai yamma suka fito suka tafi gida a tare wannan karan Raheem dinne yake tuqi Nasir na nuna masa hanya.

A gurin maamah sukaci abincin dare ya hadata da Dr Mum sukai magana sosai harda koke kokensu da maganganunsu.


Dawowan Raheem rayuwarsu ya dawo da farin ciki me yawa rayuwarsu kaman yanda suma suka shigar da wani sabon haske da walwala a rayuwarsa dan haka kusan ma sabuwar kauna da shakuwa ce ta shiga tsakaninsu dan haka aka fara kokarin hada tafiyar Nasir da Fatima amma baba khalil yace a jira sai Nasir din ya qarasa kammala karatunsa tinda saura shekara daya kuma insha Allah kamar yau ne.

Hakan ya saka aka hakura ya gama din dan haka koda Raheem ya gama hutunsa ya koma sun gama kitsa hadewansu navy.

Raheem bai tafi ba sai daya siyawa Nasir din motar hawa da abubuwa da dama na jin saukin rayuwa da karatu hakama Maamah an gyara musu gidan hadda Ac Ac ana saka musu sbd Maamah da duk sauran abun jin dadin da zasu ji dadin rayuwa,
Bawai gini aka sauya ba ko wani abin kawai an zuba musu sabbin furnitures ne bayan an gyara cikin dakunan hadda na Bangaren baba khalil din komai dai da aka sauya musu suma dan haka zainab tini ta siyar da kayan dakinta tsoffin ta zuba a dan sanaar datake yi.

****bayan komawan Raheem dr mum ta fara dakon wani hutun nasa tace Morocco zai taho suma ya gansu amma ana samun hutun Dad dinsa ya basa umarnin bazai sake barin qasar ba sbd yayi girma da matsayinda baa buqatarsa yana barin gurin aikinsa.

Hakan ya saka zuciyar dr mum shiga bacin rai da fushi me tsananin gaske musamman da familynsa suka dauko dabiar kai masa ziyara America din hakama duk yan matan familyn acan America suke hutu yanzu dan haka zuciyarta tafara shiga tashin hankali dan kuwa abinda take shirin gani bame taba yiyuwa bane,

Har abada batajin zata iya barin 'dan data haifa da cikinta yayi aure a Nigeria kuma ma a cikin ahalin jeerahs,

Zatafi son RAHEEM ya mutu baiyi aure ba data bari mahaifinsa yayi masa aure a can sbd sun rabata dashi kenan har abada dan haka kai tsaye ta gama shirinta akan rayuwar danta babushi babu auren wadda ba qabilarta ba.

******ADMIRAL Hakeem jeerah a nasa bangaren tabbas aure a daidai irin shekarun da yayi aure yakeson Raheem yayi aurensa dan haka jira yake yana taka matsayin captain da shine next matsayin da zai taka yayi masa maganar aure yayi shiru ne kawai baice komaiba kuma ya gama shirinsa na nemar masa mata anan cikin family sbd yasan mahaifiyarsa bazata taba son hakan ba kuma a yanda yasanta ya tabbatarda shirin aure a kabilarta take masa dan duk inda yayi aure tabbas zaifi samun rinjaye na rayuwarsa acan dan haka kowannensu yayi shiru.

Raheem a yanzu dayake cikin lokacin hawa matsayi kala kala na career dinsa bai taba tinanin aure ba kwata kwata a rayuwarsa dan babushi a tsari da raayinsa aure a matashinsa.

Dr Mum itama duk yanda take tsananin kaunarsa da sonsa a matsayin 'da bata taba masa sanyi ba zafi da kaifi take basa sbd tanason saka masa tsananin shakka da zamanta kaifi daya da taurin raayi tin yana qarami dan haka itama kaman yanda yake da mahaifinsa babu sakewa bayan umarni da zallar iko da kaifi daya haka yake da iyayen nasa duka biyu,

Dukansu yana iya kokarinsa gurin bawa kowa haqqinsa da girmansa na wainda suka haifesa,
Babu kowace umarninsu da hukuncinsu daya taba dagowa kai ya kalla tin yana yaro haka yake dasu,
Duk kaifi da dacin umarninsu akansa bai taba nuna gazawa ko daci ba haka zai amsa da dukkanin girmamawa sbd yasan har abada alaqarsu da iyayensa bazata taba sauyawa daga hakan ba,
Shine kaf kadai alaqar data rage a tsakaninsu duniya dan haka yasan harya mutu bazai dena karban zafi da wutar mutuwar wannan alaqar tasu ba dan haka ne yataso a jarumin da zai iya hadiye kowace irin daci da zafin hukuncinsu kowace iri ne matiqar bai sabawa ubangijinsa ba,

Rayuwarsa ta jima da zama qwallon da suke garawa da fushi da zafi a tsakaninsu kuma ya amsa ya karbi hakan ya hadiye da jarumtar da bazaka taba sanin yanayinsa ba ko waye kai dan kuwa a yanda zuciyarsa ta jima da tsayuwa a cikin wannan dacin ko Nasir dayafi kowa saninsa ciki da waje baya iya gane komai akan yanayinsa.

******lokaci baiyi karya ba RAHEEM HAKEEM JEERAH yana taka matsayin captain of the American navy Mahaifiyarsa ta gabatar masa da MEENAH WAHAB 'yar aminiyarta da suka taso tare wadda take yar gata gaba da baya kuma cikakkiyar likita ce itama duk da bata aiki sbd batada raayin aikin tukuna aure takeda raayin tukuna.

Meenah kyakkyawar balarabar Morocco mai raayi kusan irin na dr mum dan kuwa tanada tsananin kishi akan abinda take so,
Duk abinda takeso batama son taga wani dashi dan haka ne takeda raayi sosai akan maza sedai daga ranar dataga CAPTAIN RAHEEM HAKEEM JEERAH duniyarta ta tsaya cak ta rasa zuciyarta rasawar da har abada bazata dawo gareta ba dan kuwa so ne mahaukaci mai zafin gaske daya koma kaman obsession dan kuwa komai na Raheem jeerah bibiye take dashi,

A nata bangaren sbd irin mutuwar datai akansa ita ta shirya zuwa Nigeria din tayi zama kowane iri ne indai shine mijinta da zata gama rayuwarta dashi.

A matsayin umarni Dr Mum ta gabatar masa da maganar auren daya jisa kaman tahowan guguwan ruwa,

Yanda ta nuna tsaurin raayinta akan hakan da a shirye take da fuskantar mahaifinsa da duk tashin hankalin da basuyuba shekaru ya saka Raheem amsawa umarninta tareda bawa Meenah wahab dan lokacinsa dayake dashi da mahimmanci sbd hatta umarnin iyayensa yana basa mahimmancin daya kamata.

Ba mutum ne shi mai boye boye ba ko shakka dan kuwa duk ladabinsa ga iyayensa shi mutum ne da babu tsoro a tarihin rayuwarsa babu shakka babu abinda baya iya fada a gaban kowa koda kuwa iyayen nasa ne sun tabbatarda sun shedar da baya shakka idan har ya fada abu to babu shakka zaiyi idan kuwa ya furta ba damar hakan to kuwa kaf duniya babu wanda zai sauya masa raayi dan hakan ne su kansu suke tsananin gudun ranar dazai musu aa dan kuwa aa dince.


Da kansa ya sanar da mahaifinsa Aure zaiyi ya samu matar dayake raayin aure a Morocco.

Tinda Dad din yaji hakan yasan burin dr fammah ne zai cika mata dan kuwa daman yasan bazata taba barin danta yayi aure anan ba hakama shi tinda danta ne tanada iko da umarni akansa bazata taba barin ya qara aure ba har abada bare tinda kabilarta ce matar kenan wani auren ya haramta ga Raheem....

Tsananin daci da baqin ciki harma da bacin rai me tsananin gaske ne ya sake rufe zuciyarsa a karo na biyu tin bayan rabuwarsu amma idan har yaqi aminta da auren da Raheem zai samu matsala dan haka ya amincewa auren amma bazai taba barin ta samu nasarar sakawa danta kabilancinsu ba dan kuwa Raheem jinin jeerah ne kuma a yanxu ba yaro bane da zai zauna akan raayin wani cikakken dan raayin kansa ne da shi kansa yana shakkar irin kaifin da zaiyi da riqon raayi da akida dan haka a yanzu shi kam ya aje makaman zafinsa akansa.
#MAMUH

GANIN IDO 2026
Mamuhgee
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

17
Maganar auren CAPTAIN RAHEEM HAKEEM JEERAH ta bayyana ga family da duniya dan haka aka hau murna familynsa kuwa babu wanda yayi farin ciki ko murnan hakan sbd inda matar ta fito dan haka kusan duka wainda suka mugun saka rai akansa da mutuwa akansa na familyn suka cire rai dan kuwa sunsan kabilar da aka auro da kuma sanin shi din bama me yiyuwa bane yin mata biyu a rayuwarsa sbd miskilancin rayuwarsa yayi bacin da ko mutane baya buqata sosai dan haka babu yanda zai iya mace biyu tinda ta farkon ba sunsan aikin mahaifiyarsa ne bawai yanada raayin auren ba.

A nasa bangaren yayi iya kokarinsa ya budewa Meenah wahab zuciyarsa ko zata iya shigewa duka dan kuwa baima san ta inda zai fara ba kawai dai yasan baisan ya ake so ba idan ta shiga kila zata koyar dashi harma ta samu mallakar zuciyarsa dan matiqar zata iya hakan shi baida matsala tinda itace zata mace daya a rayuwarsa har abada baya buqatan wata.

Aurensa ya saka shirin tafiyarsu Nasir sake kankama dan har service dinsa ya gama ya hada komai na takardunsa,

Shi kwata kwata baa Nigeria zai zauna da matarsa ba sbd nasa raayin kenan sbd ya shirya bawa matar da zai aura dukkanin kulawa da kaunarsa sbd ta rabu da iyayenta da rayuwarta ta zabesa dan haka she deserves dukkanin kauna da kulawa daga garesa shi kadai batareda kowa ya bata kowace irin damuwaba.

Zainab nada ciki tsoho aketa shirin tafiyar tana jin tsananin kewa da kadaicin rabuwa dasu amma kuma tana musu farin cikin tafiyar dan haka ta fidda kudadenta tana musu abubuwa da dama da zasu tafi dasu hakama ta saka hannuwanta da kanta tayiwa dr mum lafiyayyar gyada da cashewnuts da akace tanaso a lokacinda tayi zama Nigeria tace a kai mata tsaraba.

Ana saura sati biyu tafiyarsu a lokacin ne CAPTAIN RAHEEM jeerah ya sauka Nigeria dan daga nan zasu wuce Morocco,

A daren ranar daya sauka din Nasir a jeerahs ya kwana cikin tsakiyar dare guraren karfe biyu da mintina kiran wayar baba khalil ya shigo wayarsa.

Da mamaki da tinani ya dauko wayar cikin bacci daga gefen gadonsa kan bedside drawer yaga baba khalil ne me kiran.

Tashi zaune yayi a natse yana daukan kiran cikin shakka ya ambaci sunan baban.

Baba khalil dake tsaye akan Zainab dake gap da rasa rayuwarta maamah na riqe da ita ajiyan zuciya ya sauke tareda fadawa Nasir din yazo da sauri akai zainab asibiti jikinta yayi nauyin da ankasa karban haihuwan a gida dole asibiti zasu.

Baccin dake tattare da Nasir sakinsa yayi gabaki daya ya ziro kafafunsa qasa ya miqe ya tsaye yana sauya kayan jikinsa cikin sauri ya zari mukullin motarsa ya fice batareda yaje dakin Raheem ba ya sanar dashi.

Kai tsaye gida ya nufa yana isowa suka dauki zainab din zuwa asibiti hankali tashe sbd yanayin jikinta.

Private asibiti me kyau da Nasir ya dauki nauyin tana zuwa awo suka nufa,

Suna zuwa aka amsheta akai ciki da ita sukuma suka tsaya jiran abinda zaa fito ace musu cikin damuwa da tinani kala kala.

Takardun biya wasu abubuwa aka miqo musu bayan mintina da shiga da ita dan haka Nasir ne ya karba ya wuce pharmacy dinsu.

Yar dadewanta tana naqudar datazo mata gadan gadan ya saka lamarin yake neman lalacewa dan haka aka fara dubarun yanda zata haihu da kanta amma abin ya gagara ga bp dinta yana hawa dan haka aka ringa kokarin controlling dinsa.

Cikin tashin hankali da damuwan mummunan halin da mommy zainab ke ciki akai asuba dole aka yanke shiga tiyatar gaggawa da ita.

Kudin komai da komai Nasir ya biya suka wuce lap bada jini da aka nema roba biyu dan haka shi da baba khalil dinne zasu bada daddaya.

Suna shiga lap Raheem ya kirasa dan bai gansa ba a gurin sallan asuba.

Sanar dashi komai yayi kafin suka kashe wayar.

Geamin kadai yayi wanda ya saba kaman cikon rayuwarsa ne datake farawa kowace safiya baya taba missing bai tsaya breakfast ba ya fito sanyeda sweatset riga da wando black na original balenciaga da suka nutsu a jikinsa ya sako hular sanyi black ta bvlgari data boye gashinsa dayake kwance da tsayi sai facemask daya rufe fsukansa da ita itama black sbd bayason yawan kallo kuma duk inda ya shiga a Nigeria idan yaxo kallansa akeyi dan haka bai cika rabo da mask ba, sai sneakers a kafafunsa na Original.

Ko daya iso Asibiti an gama diban jininsu Nasir din suna lab baa basu daman fitowaba kuma da gaggawa ake buqatan shiga da Mommy zainab din dan haka kai tsaye Shi Baba khalil ya cewa yaje kawai ya saka hannu a takardar aikin

Boyayyan numfashi me dumi da nutsuwa ya sake kafin yayi signing a takardun da aka gabatar masa na shiga tiyatar.

Maamah ce a tsaye dashi aka shige tiyatar da ita dan tini likitan da zaiyi tiyatar ya iso asibitin.


Cikin ikon Allah da yardarsa akai aikin cikin nasara ciro mata Baby girl dinda babu abinda ta baro na mahaifinta sai hasken uwarta wadda ana fitowa da ita daga ciki cikin showel dinta fari tas mai laushin gaske Raheem jeerah Nurse ta miqawa babyn cikeda girmamawa da kulawa sbd ganin shine ya saka hannu a takardar shiga da uwar.

Cak Raheem ya tsayar da idanuwansa akan babyn wadda take motsawa ahankali fara tas da ita idanuwanta a rufe yaji zuciyarsa tayi wani irin dum sbd bai taba daukan baby ba a rayuwarsa sau din shi baima taba kasancewa a zahiri da baby ba sbd bayama tareda dangi bare ayi haihuwan da zaije yaga baby,abokan aikinsa biyu suka haihu amma baiga babys din a zahiri ba a waya kawai ya iya ganinsu yayi musu barka dan haka sai yaji kaman bazai iya daukan babyn ba sai da Nasir ya matso gurinsa ya kallesa kafin ya kalli babyn Baba khalil ya bude baki yace

'Captain ka karbeta ai kune iyayenta'

Amsarta yayi a natse tareda sake sauke numfashi mara sauti yanajin wani irin nauyi a hannuwansa da kirjinsa ya kafeta da fararen idanuwansa ya bude bakinsa ahankali ya furta 'Masha Allah' tareda adduoi masu kyau da tsari tukuna ya kalli fuskanta a karo na uku yana ganin kamannin Nasir dinsa akan jaririyar fuskarta.

Nasir da zuciyarsa ta tsaya cak akan tsananin kaunar babyn miqa masa ita Raheem yayi ya karbeta da Bismillahi yana jinta har qasan zuciyarta fiyeda yanda yake kaunar Al'amin yayanta.

Addua yayi mata aka bawa mahaifinta ita yayi mata addua da kiran sallah kafin ya miqawa Nasir ita ya Ambaceta da suna SANAAH KHALIL MUHAMMAD.

a cikin kunnuwanta ya fara kiranta da sunan kafin ya ambata a bayyane take Baba Khalil ya maimaita sunan yana mata adduar girma da gamawa da duniya lafiya cikin aminci da tsaron ubangiji.

Maamah tayi farin cikin haihuwan zainab suna nan dan haka itace tayi jinyarta har akai sati daya aka sallamesu suka dawo gida taci gaba da kulawa da ita kafin tafiyarsu.

Baa bari sati biyu ba akai sunanta sbd idan akai sati biyu kaman yanda wasu keyi idan tiyata ce to su basa nan,

Captain Raheem jeerah ne ya aikowa da baba khalil Manyan shanu guda biyu da raguna biyu na sunan Baby SANAH sbd Nasir daya kwallafa mata rai da wata irin kauna.

Shi kansa Nasir hana baban siyan komai yayi shine ya siya mata duk wani abin buqata da kayan sakawa itada mommyn wadda tace ta cika masa alkawarinsa na cewa itace zata haifa masa mata.

A duk lokacinda suke wannan maganar tasu ta wasa dariyarsu kawai baba khalil keyi sbd yasan wasar ce tinda yaushe Kamar Nasir zai tsaya jiran girman yar Zainab harya aureta tinda a lokacin ai yayi manyancin da bama zai iya aurentaba.

Baby SANAH nada sati biyu cif a duniya Nasir da maamah suka bar Nigeria suka tafi cikeda tsananin kaunarta da kewanta bama kamar Nasir daya tabbatarwa iyayenta shine zai dauki nauyin komai nata komai zaa siyawa baby SANAH a sanar masa bai yadda suyi lalurarta ba ya dauke musu.

*****A ranar da suka isa Morocco a washe garin ranar ne daurin auren CAPTAIN RAHEEM HAKEEM JEERAH da matarsa Meenah wahab wadda tini suka fara hidimar bikim kafin isowan ango da danginsa da suka taho kusan kaf dangin Jeerah sun samu tahowa bikin.

An Daura auren daya samu halarta mutanen da bama ayi tinanin halartarsu ba kuma a cikin kwanciyan hankali da aminci.

Har akai bikin aka gama Dr Mum da Alh admiral Hakeem jeerah basu hadu ba hakama matansa biyu duka sunzo suma babu wanda Allah ya hadata dasu a cikinsu sai da aka gama bikin sukai nacin da saida zuka ganta dan basuda nutsuwa idan ba ganinta a cikin idanuwansu sukai ba.

Babu wata hayaniya kowa ya watse bayan kwanaki biyar da auren kenan kowa ya kama gabansa wanda shi kansa Raheem din babu lokacinda ya bata ya wuce America da matarsa yabar Nasir a nan wanda saiyayi training na dan lokaci kafin ya rafi dashi America din.
#MAMUH
#FLEET ADMIRAL RAHEEM HAKEEM JEERAH
#SEAMAN NASIR IBRAHIM
#SANAH KHALIL
#BEST CRAZY COUPLES CHEMISTRY
#AGE GAP
#CRAZY LOVE
#JEERAHS
#MEENAH WAHAB
#FAMMAH JEERAH


GANIN IDO
1K
VIP 5K
0022419171
ACCESSBANK MARYAM SANI GUMMIGANIN IDO 2026
Mamuhgee

18
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Rayuwar Maamah fatima data dawo hannun Dr Mum tazama abinda ita kanta fatiman batai tinani ba sbd dagaske tamkar uwa daya uba daya ta gabatarwa duk wanda take tareda dashi da ahalinsu na kusa dana nesa daman sun san fatiman a baki da kuma lokutan jinyar fammah din a baya tinda ita kowa ke kira idan zaa yiwa fammah ya jiki,

Abbu yayi farin cikin dawowansu fatiman gurinsu sosai duk da ansha yar wuya kafin samar musu da cikakkun takardun zama amma sbd suna fama da kadaici da rashin kowa a tattare dasu ya saka yake sake jin dadin zuwan nasu musamman Nasir da tini yafara kulawa dashi sbd manyanci babu namijin dazai kula dashi da kyau.

Nasir da baida plans a yanxu dorasa akan huldodin business din gidan aka fara yi yana dan kulawa dasu tinda bame wuya ne sukeyi ba business din gold sukeyi me girman gaske da suka mallaki manyan shaguna a babbar birnin qasar kuma tinfa babanta ya fara business

Please Login or Register in order to submit comment