Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hakeem din da idanuwanta da sukai jajir tana jin wani nauyi na danne kirjinta wanda ya jima a kirjinta ba tin yanzu ba akan alaqar Hakeem din da Dr fammah.

Doctors biyu ne akai gaggawan tahowa dasu dake anguwan sbd dr bushrat ta riga tana asibiti.

Dubata sukai aka dawo da numfashinta daidai suka tafi aka barta a palon kwance cikin da wata irin rashin kuzari.

Dad na shigowa bayan ficewansu zaunawa yayi ya zuba mata manyan idanuwansa da sukai jajir sosai wani radadi da zafi na danne da kirjinsa dayakejin dukkanin riqewa da jarumtarsa ta shekarun tin kuruciya suna tsinkewa daya bayan daya har karshe ya bude bakinsa da wata murya mai tsananin kauri da bayyanarda radadin da kirjinsa yake ciki na abinda ya farun wanda rashin mallakarta ya saka yake kasa bata wata kariya da gaggawan datake tasowa a rayuwarsu idanuwansa a cikin nata ya saka da wannan strong voice din yace

"I cant live without you now Doc,
I can't breathe knowing muna guri daya muna rayuwa amma baa matsayin ke tawa ce ba ni hakeem jeerah....
Ayau ina rokonki Alfarmar da ban nema ba a bayaba,zuciyata bata taba haske da bugawa akan kowace sukuni na rayuwata ba saida kika dawo a cikin gidan danake rayuwa....ki bamu daman qarasa rayuwan datake rage mana a duniya da juna."

Wani irin nauyin dake kirjinta ne taji yana sauka ahankali wasu hawaye na ciko idanuwanta tana kasa dauke idanuwanta daga kansa shi kansa ita yake kalla jan idanuwansa na ciwo da radadin shekarun na dawo masa sabo fil.

Kasa cewa komai tayi sbd ta tabbatarda da son Hakeem zata mutu wanda shine ya sakata rabuwa dashi sbd bazata iya kallansa da wata macen ba amma a shekarun babu ranar da sonsa yabarta da kishinsa da haryanzu tana ji amma a yanzu datake iya ganin radadinsa na shekaru daya boye ya danne bayyane a idanuwansa zata iya basa daman samunta na rayuwar data rage musu.

Umma data kuma dawowa kunnuwanta sukaji abinda ya saka kirjinta dena bugawa daidai juyawa tayi tabar gurin tana jin dana sanin auren Hakeem a karan farko bayan shekaru masu tsayi sbd tin inda aka fito bai taba sontaba zaman auren biyayyar iyaye da hana kansa fidda zafinsa akan ciwon rabuwa da dr fammah din yayi da ita.

Hajiyar samad kuwa tana shiga palonta da Samad kwacewa yayi yana kallanta yace

"SANAAH f.....

Cikin masifaffen fushi ya katsesa da cewa

"Idan ka kira sunanta a nan gurin saina kusan tsine maka sbd zuwa yanzu na gane kaine masifar rayuwata dan tin farko daka riqe kwadayinka akanta da bamuzo nan ba"

Cikin mamaki da jin zafi sosai yace

"Shiyasa kike rufeni kaman nayi kisa?
Tin farkon da kin bari na sameta a ranar danaso samun nata ai da yanzu tawa ce,
Farko Samrah ta hanani mallakarta daga baya kece ku.........

Mari mai zafin gaske hajiyar ta sauke masa tana hanasa qarasa maganarsa sbd meenah din dake tsaye tana kallansu da jin abinda suke fada dan kada ta gane shine wanda yayi fyaden cikin zafi da bacin rai tace

"Ni mahaifiyarka kake fadawa hakan?"

Meenah kuwa da wani mamaki da shiga wani mahaukacin tinanin maganganun samad din da suka shigeta kai tsaye ta kalli Samad din wanda idanuwansa sukai jajir yana kallan hajiyar take ta gane inda zancen ya nufa wani mahaukacin sanyi ya sauka a kirjinta tana jin a karan farko allah ya bata saar da bata taba samu ba ta tarwatsa Fleet da Raheem da baisan sauran qaninsa ya auraba.
##MAMUH
09033181070
[22/06, 2:55 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

134
Dakatawa hajiyar tayi sbd jin zuciyarta gabaki daya ta juye da wani fargaba da zuwan Meenah din bangarenta tinda sassafen dan haka ta juyo tana sake kallanta taga yanda idanuwanta sukai muni sbd ja tasan babu abinda zai saka Meenah magana da hauka bayan jin tafiyar Fleet dan haka ta bude baki tana kallan cikin idanuwanta tace

"Kinsan FLEET da SANAAH sun bar qasar ayau din suma?"

Wani irin kallo Meenah ta sauke idanuwanta akan hajiyar tana mata idanuwanta na cikowa da wasu azababbin hawayen wutar dataji ta kama a kirjinta ta girgiza kai tana bude bakinta dayake yanke magana tace

"Bai tafi koinaba suna can kwance gas yana huda kowace iskar da suke shaqa"

Da sauri Hajiyar ta kalleta tace

"Gas kika saka musu??
Me kike nufi??
Wlh baya nan sunyi tafiya ya tafi da ita sun tafi yawon duniya"

Girgiza kai Meenah tayi da karfi tana jin tinaninta na kasa dauka zatai magana hajiyar Samad dataji hankalinta na tashi da barin jikinta tsabar neman rikicewa tace

"Gas naji kin ambata?
Kunna musu zakiyi kokuwa harkin kunna din??

Cikin zafi ta gyada kai tana cewa

"Me zaki musu?
Zaki sake zuwa ki fasa ihun neman cetone kaman yanda kikai wancan karan?
Karki manta duk abinda nayi yanxu tare muke....

Da wani sautin dayake tafe da tsantsar baqin ciki da tashin hankali hajiyar tace

"Kin kunna dai kenan kike nufi???

"Eh kuma....

Hajiyar bata jira sauran zancenba ta tureta da karfin gaske tana nufar kofa ko takarmi bata iya sanin yaya ake sakawaba sbd yanda idanuwanta suka rufe a take duka jikinta wata muguwar rawa yake dauka bakinta na furta

"Allah ya debe miki albarka Meenah ya kuma debewa larabawan kasarku gabaki daya tattalin arziki,irin masifa irin balai"

Da gudun gaske ta isa bangaren Samad dake kusa hanya daga bayan na Fleet.

Tana isa hannuwanta har rawa suke ta bude kofarsa ta fada tana shiga dakinsa ta nufa tanajin warin gas yana ratsowa har nan dan haka ko gani bataji ta fada dakinsa daidai fitowansa wanka kenan daga shi sai gajeran wandon daya saka ta damqi hannunsa tana janyosa da karfi tana cewa

"Yi sauri kowane lokaci bomb tashi zaiyi a bangaren nan"

Kwace hannunsa zaiyi tai masa wani mahaukacin riqo tana janyosa da daga harshenta cikin tsananin tashin hankali

Rigarsa ya janyo tana jansa yana sakawa ta fito dashi shima a lokacin yaji warin Gas sosai dan haka da kansa ya cira kafafunsa suna barin gurin da gudun gaske.

A cikin bangaren su Dr Mum kuwa tini gas din yafara shiga koina yana shiga cikinsu sosai take oxygen yafara kokarin yanke musu dan haka da wani irin tashin hankali da yajin idanuwa suka fara fitowa a palon sukaji abinda yafi karfin hankali dan haka tini Dr Mum ta zube kasa tana wani irin tarin dayake neman tafiya da ranta.

Maamah ce ta kamata da sauri itama tana jin numfashinta na yankewa ta fara kokarin miqar da ita.

Mommy da Safiya da suka fito ma da gudu Mommy tayi kitchen tana toshe hancinta sbd numfashinta daya fara yankewa.

Safiya kuwa kofa ta isa ta bude da karfin gaske tana dawowa ta bude windows tana jin jiri kaman zai zubar da ita ta fito da gudu ta fita cikin ihu ta nemi jaama wanda ihunta da neman agajinta ya saka securities fitowa sa sauri suna yowa nan daidai nan hajiyar Samad dashi suka fito da gudu suma take kowa ya fahimci abinda yake faruwa.

Da gudu akayo nan.

Mommy tini ta kashe gas din Amma bata iya fitowa ba da kanta sbd jiri da toshewan numfashin daya zubar da ita.

Dad jeerah dake kwance yaji ana ihu da hayaniya sarawa kansa yayi yana rintse idanuwansa da wani irin nauyin kirji sbd da alama an kusa kashesa da bugawan zuciya a cikin gidansa dan haka saukowa yayi yana zira jallabiya ya fito tinda dai baiji ana ambatar mutuwan Dr ba kaman wancan karan.

Koda ya iso tini aka fito da Dr Mum wadda numfashinta yake ya kewa kaman mai asthma.

Da tsananin mamaki da shock yake tambayar kafin ma a basa amsa yaji gas din dan haka take ya bada umarnin koina kada a kunna wuta a villah din.

Bangaren Raheem aka nufa da tashin hankali sbd jin yana fitowa harda tacanma.

Daqyar aka iya shiga aka kashe ana bude koina shima tareda sauke kowace labule sbd ya futa yabi iska da kyau.

Jikin Dr Mum rawa yakeyi sosai tana sake rasa numfashinta dan haka kai tsaye bangarensa yayi da ita yana sakawa aje da gaggawa a kawo masa doctors.

Umma dake bangaren ta shigo kawo masa breakfast kenan ta tadda Dr Mum a palonsa tana taimaka mata gurin dawo da numfashinta ta hanyar huta mata wani iska mai sanyi daga bakinsa zuwa fuskanta yana jin kaman ya sakata jikinta ya basa iskan bakinsa dakyau amma hakan ba dama.

Cak Umman ta tsaya daga inda take a tsaye da kaya a hannunta tana kallan Hakeem din da idanuwanta da sukai jajir tana jin wani nauyi na danne kirjinta wanda ya jima a kirjinta ba tin yanzu ba akan alaqar Hakeem din da Dr fammah.

Doctors biyu ne akai gaggawan tahowa dasu dake anguwan sbd dr bushrat ta riga tana asibiti.

Dubata sukai aka dawo da numfashinta daidai suka tafi aka barta a palon kwance cikin da wata irin rashin kuzari.

Dad na shigowa bayan ficewansu zaunawa yayi ya zuba mata manyan idanuwansa da sukai jajir sosai wani radadi da zafi na danne da kirjinsa dayakejin dukkanin riqewa da jarumtarsa ta shekarun tin kuruciya suna tsinkewa daya bayan daya har karshe ya bude bakinsa da wata murya mai tsananin kauri da bayyanarda radadin da kirjinsa yake ciki na abinda ya farun wanda rashin mallakarta ya saka yake kasa bata wata kariya da gaggawan datake tasowa a rayuwarsu idanuwansa a cikin nata ya saka da wannan strong voice din yace

"I cant live without you now Doc,
I can't breathe knowing muna guri daya muna rayuwa amma baa matsayin ke tawa ce ba ni hakeem jeerah....
Ayau ina rokonki Alfarmar da ban nema ba a bayaba,zuciyata bata taba haske da bugawa akan kowace sukuni na rayuwata ba saida kika dawo a cikin gidan danake rayuwa....ki bamu daman qarasa rayuwan datake rage mana a duniya da juna."

Wani irin nauyin dake kirjinta ne taji yana sauka ahankali wasu hawaye na ciko idanuwanta tana kasa dauke idanuwanta daga kansa shi kansa ita yake kalla jan idanuwansa na ciwo da radadin shekarun na dawo masa sabo fil.

Kasa cewa komai tayi sbd ta tabbatarda da son Hakeem zata mutu wanda shine ya sakata rabuwa dashi sbd bazata iya kallansa da wata macen ba amma a shekarun babu ranar da sonsa yabarta da kishinsa da haryanzu tana ji amma a yanzu datake iya ganin radadinsa na shekaru daya boye ya danne bayyane a idanuwansa zata iya basa daman samunta na rayuwar data rage musu.

Umma data kuma dawowa kunnuwanta sukaji abinda ya saka kirjinta dena bugawa daidai juyawa tayi tabar gurin tana jin dana sanin auren Hakeem a karan farko bayan shekaru masu tsayi sbd tin inda aka fito bai taba sontaba zaman auren biyayyar iyaye da hana kansa fidda zafinsa akan ciwon rabuwa da dr fammah din yayi da ita.

Hajiyar samad kuwa tana shiga palonta da Samad kwacewa yayi yana kallanta yace

"SANAAH f.....

Cikin masifaffen fushi ya katsesa da cewa

"Idan ka kira sunanta a nan gurin saina kusan tsine maka sbd zuwa yanzu na gane kaine masifar rayuwata dan tin farko daka riqe kwadayinka akanta da bamuzo nan ba"

Cikin mamaki da jin zafi sosai yace

"Shiyasa kike rufeni kaman nayi kisa?
Tin farkon da kin bari na sameta a ranar danaso samun nata ai da yanzu tawa ce,
Farko Samrah ta hanani mallakarta daga baya kece ku.........

Mari mai zafin gaske hajiyar ta sauke masa tana hanasa qarasa maganarsa sbd meenah din dake tsaye tana kallansu da jin abinda suke fada dan kada ta gane shine wanda yayi fyaden cikin zafi da bacin rai tace

"Ni mahaifiyarka kake fadawa hakan?"

Meenah kuwa da wani mamaki da shiga wani mahaukacin tinanin maganganun samad din da suka shigeta kai tsaye ta kalli Samad din wanda idanuwansa sukai jajir yana kallan hajiyar take ta gane inda zancen ya nufa wani mahaukacin sanyi ya sauka a kirjinta tana jin a karan farko allah ya bata saar da bata taba samu ba ta tarwatsa Fleet da Raheem da baisan sauran qaninsa ya auraba.
##MAMUH
09033181070
[23/06, 9:19 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

135
Kallan Meenah hajiyar Samad din tayi da idanuwanta da suke jajir tana karantar kota fahimci abinda Samad din ke kokarin fada amma ganin yanda Meenah tayi quri da ido guri daya idanuwan jajir ya sata jin sanyin bata fahimci komai hakama tasan kanta a toshe yake bazata iya fahimtar komaiba dan haka da zafi da tsantsar bacin rai ta kalli Samad din tace

"Wlh tallahi insha Allah inde nice na haife ka bazaka wuce kwanakin nan ba zaka bar qasar nan ka tattara ka koma sbd bazaka janyo mana balain da kanmu bazai iya dauka ba"

Maida kallanta tayi akan Meenah wadda ta juyo ta kalleta itama tana jin wata tsanar Samad din harma da Hajiyar tasa wadda babu son kowa a ranta saina kanta da danta kawai.

Cikin tsananin baqin ciki da takaicin sanin dataiwa Meenah tace

"Wannan haukar taku ta kafirci idan baki koyi danneta ba kina sanin abinda ya kamata kiyi a ruwan sanyi to wlh gwara Allah ya dauki ranki da gaggawa daki kashe mu a banza,
Ke baki san ki ragawa wanda yake sonki ba?
Duk abinda nake miki shine zaki tada wutar da zata cinye har 'dana?
To wlh ko ashana bazaki sake tabawaba a gidan nan saikin sanar min nayi nesa da kaina da ahalina idan yaso ki kona har kanki tinda kin shirya buga haukar da zaki rasa shi wanda kike koman akansa gabaki daya,
Na farko kinyi an yanke shawaran turaki qasarki yanzu kinyi wannan kina tinanin ba dankara miki saki zaiyiba?
Idan har ubansa zai iya dankaramun saki da girmana da 'da a tsakaninmu ke wace da 'dansa bazai iya sakinki ba da 'ya daya,
To tabbas idan kinason zama a cikin auren Fleet saikin aje wannan haukar kisan ki kama wata haukar banda ta kashewa sbd baa kansu abin zai tsayaba,
Kita zabga musu haukarda zasu gagara zaman lafiya amma wlh kika kuma bankawa gidan nan gas ko wuta to ni da kaina zan fara dannaki cikinta kiga kalan haukar data fi taki"

Juyawa tayi da zafi tabar gurin ta shige dakinta gabaki daya zuciyarta tafasa da tiriri take sbd ta shiga tsananin tsoro da tashin hankalinda zuciyarta ta kusa bugawa ta dena aiki.

Samad rintse jajayen idanuwansa yayi yana dafe goshinsa da karfi tareda fidda wani hucin bacin rai da baqin ciki mai tsanani.

Meenah ma kaman zata qone tsabar tafasar da ranta keyi da baqin ciki da zafin maganganun Hajiyar wadda zata tabbatarda ta kirata mahaukaciya dan kuwa zata nuna mata hauka a cikin ruwan sanyin data ambata din dan kuwa zata sauya takun da kowa zaiji a jikinsa batareda kisar ba duk da bazata taba samu sauki ko sassauci a kirjinta ba matiqar SANAAH na numfashi a duniya da uwar SANAAH da dan uwan SANAAH da uban SANAAH wato Dad jeerah.

Kallan Samad tayi da jajayen idanuwanta da har wani radadi suke mata ta danne abinda takejin yana neman kasheta sbd baqin ciki ta bude baki tace

"Ka dena bata ran hajiyarka akan wadda bata cancanci wannan haukan da kakeyi akanta ba sbd yanzu haka ma basa qasar da asubar yau tabi Fleet yawon lalacewa da tabarbarewa tana can tana basa kanta sbd shine abinda ta sani dan nasan kaima da hakan ta jaka"

Qarasa maganar tayi tana dan nuna haushinta sbd sakasa jin abinda taji ya fiddo maganar datake son ji bakinsa.

Juyowa yayi da wani irin mamaki ya kalleta yana bude baki yace

"Sunyi tafiya?
Basa qasar?
Kuma da ita Godfather din ya tafi??

Numfashi ta fitar wanda ya rage radadin wutar dake cin kirjinta ta kuma kallansa tace

"Tare suka tafi babu ranar dawowa dan hakane idan bamuyi hanyar dawowansu ba babu abinda zai rage a jikinta da zaka mora se sauran dan uwanka"

Da baqin ciki ya kalleta yana jin kishi da sonta kaman zai kashesa a kufule yace

"Ba nine zan samu sauranta ba shine ya samu sauran sbd nine nafara samunta a hannuna kafin shi"

A karan farko da Meenah ta samu murmushin baqin ciki da takaici tareda samun sassaucin abinda take ji ya taho mata ta sakesa tana kallan Samad wanda dai daga karshe ta samu jin abinda zai saka mata Fleet rabuwa da SANAAH sbd babu abinda ya tsana a kaf rayuwansa kaman taba abinda wani ya taba dan haka a yanzu kam yanajin sauran kaninsa yake aure wlh bazai taba sake kwana da aurenta a hannunsa ba zai sake.

Abu daya ya rage mata samar da tabbacin da zata gabatar a gaban Raheem dan ya yadda da abinda zata fada din.

Samad kuwa gani murmushin datai ya sanyasa juyowa da kyau ya kalleta sbd ganin kaman bata yadda ba tana masa kallan mara hankali yaji zuciyarsa ta kara daukan zafi da tiririn kalamanta na sauran SANAAH zai samu mijinta ya gama samunta tako ina kashesa kalaman sukeyi kansa ya kara nauyi ya bude baki yace

"Kina mamaki ne?
Kina ganin ban kai bane?
Sbd ni ne ayau shi ya sameta a matsayin mata,
Sbd na gama da ita ne naqi aurenta Dad yayi sadakarta ga mijinki,
Sbd na gama yayinta da biyan buqatata akanta ne ayau ta samu matsayin datake dashi"

Kan Meenah daya kasa daukan duka maganganun datake dauka a wayarta batareda ya saniba ta kashe tana bude bakinta da wani shock da tsananin mamaki da qaguwan datakeyi tace

"Duka wannan zancenka ne sbd babu kalma ko daya datake ta gaskia dan kuwa Dad bazai taba aurawa Fleet sauranka ba hakama idan hakanne meyasa kai da ka lalata baa aura maka itaba aka aura masa gashinan zaka lalata rayuwar Samrah ka aureta bayan ga wadda kakeso din?

Wani mugun tsoki da takaici ya ja yana mata wani banzan kafin ya juya zai fice ta kira sunansa da sautin kulawa tana takowa zuwa gabansa ta ladabtar da kalamanta da nuna kulawa tace

"Samad banason SANAAH da Fleet rabasu nakeson yi,
Bazan iya ganinsu a tare ba zuciyata bazata taba iya dauka ba,
Kaima kanason SANAAH kada ka auri Samrah ka.....

Katseta yayi da dan rintse idanuwansa da budesu akanta yace

"Ki dena maganar Samrah sbd babu abinda bata taba saniba akan SANAAH tin farko har zuwa yanzu,
Tasan menene a tsakanina da SANAAH karshema itace ta lalata mallakar danaso yiwa SANAAH tin farko dan haka tana buqatan zama matata sbd ta sheda da idanuwanta yanda zan auro SANAAH a kan idonta kuma na hukuntata akan abinda tamun so pls kiyi harkanki nayi tawa akan abinda nakeso ko buqata"

Yana gama fadar hakan ya juya ya fice yana barin palon da bangaren gabaki daya idanuwansa jajir.

Meenah dataji wani nauyi mai karfi ya sauka ahankali daga kirjinta na samun cikakkiyar bayani daga samad din cikin rashin wahala ajiyan zuciya ta sauke tana juyawa ta kalli hanyar kofar dakin hajiyarsa tana sake sauke numfashi taji yanzu ba itace a tafin hannun hajiyarba sune a tafin hannunta sbd mutuwa ce kadai zata hanata isarwa da Fleet wannan cikakken bayanin dukansa kaf da zaman SANAAH ragowar kaninsa daya gama da rayuwarta.

Fitowa tayi tanajin komai na kanta ya sauka tinani da lissafinta ya sauya a lokaci daya take dan haka bangarensu ta koma wanda har lokacin akwai sauran dan kamshin gas kowa na zaune a palo koina bude.

Tana shigowa kallo Maamah ta bita dashi cikin rashin kuzari batareda tace komaiba itama Meenah din yi tayi kaman bata gansu ba ta wuce dakinta ta shige batareda ta kallesu ba bare cewa wani abu.

Zaunawa tayi kirjinta nada tsananin ciwo da radadin tareda baqin ciki har lokacin amma maganar Hajiyar Samad ta ratseta dan haka dole a yanzu zata koyi dannewa da riqe kanta dan cimma burinta dan haka shiru tayi a zaune tana rintse idanuwanta dakeda ja sosai har lokacin tanajin kaman ta qyasta ashana da sauran gas din ya tashi kowa ya mutu ta huta da abinda takejin amma dai ta danne dan haka ta ringa sauke ajiyan zuciya me zafi a jere idanuwanta na cikowa da wasu irin hawaye masu tsananin ciwon yanda rayuwarta ta sauya a dare daya a lokaci daya bayan girma ya fara zo mata.

Bata fito dakinba a ciki ta wuni har dare ko abinci bata fito taci ba tana jiyo yar hayaniyarsu amma baqin cikin ganinsu kadai ya kasa barinta iya fitowa.

Sai dare ta fito bayan tayi wanka ta sauya kaya yanayinta ma ya dan sauya dan haka tana fitowa kai tsaye palon datake jiyo muryansu ta nufa dukansu suna zaune banda Mommy datake kitchen ta hadowa Dr Mum ginger mai dadi da kamshi sbd lamarin take ya koma mata mura mai karfin gaske.

Kaman a mafarki ba tsammani suka ganta ta iso gurin yanayinta baa gane yaya yake sam sbd idanuwanta dai har lokacin jajir suke sedai jikinta yayi sanyi a mace yake duk da hannuwanta na dan rawar da tin kwanakin haka take.

Dr Mum bata kalli inda take ba Mommy data iso da tray gabanta ta kalla tana bude baki da kulawa tace

"Sannu zainab"

Murmushi mommyn tayi tana juyawa gurin Maamah tace

"A kawo miki ne Maamah?

Girgiza kai maamah tayi tana cewa "aa" kafin ta maida kallanta kan Meenah data zauna ahankali tana dago kanta kadan batareda ta kalli kowannnensu ba dan idan ta kallesu zata iya jin ta kasa riqe kanta daga tsananin tsanarsu dake cin zuciyarta.

Mommy ma meenah din ta kalla tana bude baki da kulawa tace

"A kawo muki ginger tea din??

Girgiza kai tayi tana dan yin shiru da rasa abin fada saida maamah ta bude baki idonta akanta tace

"Meenah lafiya dai ko?
Akwai wata matsalar ne?

Girgiza kai tayi tana dannewa ta bude baki tace

"Hakuri nakeson baku nayi kuskure shedan yayi nasara akaina amma insha Allah na gane zan gyara ina neman gafararku akan komai"

Qarasa maganar tayi tana kallan inda Dr Mum ke zaune tana fara shan tea dinta ahankali da nutsuwa zuciyarta fes da wata sabuwar nutsuwan data dawo rayuwarta ayau da Hakeem yayi abinda ya kamata yayi shekara da shekaru.
#MAMUH
09033181070
[23/06, 10:34 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

136
Shiru gurin yayi tsit kaman babu kowa a gurin dukkaninsu abune da basu taba tsammanin ji ba musamman Maamah datasan babu hakura akan kishiya a lamarinsu hakama da safen nan taso sake aikasu lahira amma kuma yanxu tana cewa ta gane ta tuba,

Dr Mum da ko kadan ma bata basu hankalinta ba bare tinaninta daukan cup dinta tayi ta miqe tabar gurin batareda ta kalli ko bangaren da Meenah din take ba.

Maamah ajiyan zuciya ta sauke tana jin jikinta na mutuwa hakama ta rasa abin fada daya wuce karban hakurinta tayi ta kalli Mommy wadda itama shirun tayi tana dan dauke idanuwanta daga kallan Meenah din wadda itama har lokacin bata kalli kowannesu ba.

Bude baki maamah tayi da nutsuwa da samun nutsuwa da jin dadin hakan tace

"Masha Allah da kika gane hakan kuskure ne kikeyi Meenah hakama mu daman abinda mikeso kenan tin kafin lamarin yayi nisan da komai zai lalace kuma tinda babu ran da aka rasa allah ya yafe mana gabaki daya ya kuma kara miki hakuri da juriya da tawakkali"

"Amin" Mommy ta fada a natse tana dan kallan Meenah din wadda idanuwanta suka ciko da wasu hawayen da suka gangaro ahankali ta goge tana miqewa tabar gurin sbd kowace lokaci zaa iya ganin ta danne maamah din ta shaqeta har lahira idan bata bar gurin ba.

Dakinta ta koma ta shige.

Mommy ce taje ta hada mata abinci a try ta bawa safiya takai mata har daki sbd ita yanzu babu wannan a tsakaninsu sai komai ya sake daidaita zuwa gaba kila.

Safiya data kai abincin itama a tsorace take da shakka dan haka tana ajiyewa ta juyo ta fito.

Daqyar ta iya tura abincin cikinta tana jin kaman zata amayosa amma hakanan ta tura tana buqatan koyan karfin hali da taurin rai na munafurcin da bata iya dan su basu iya munafurci ba sam shiyasa ko kishiyar akai basa boye kishi idan sun zauna kenan dan basa zama sedai ka zaba daya a ciki ko su ko wata.

Maamah har cikin ranta taji farin cikin hakan da kuma godewa Allah daya kawo sauki a cikin lokacinda basu taba tsammani ba.

Mommy ma da duk hankalinta yake tashe a boye akan yanda SANAAH zatai rayuwa da meenah a matsayin abokiyar zama yau din jin tayi dan wani sauki yafara shiga zuciyarta sbd ba qaramin tashin hankali da tsoro take a cikinsa ba dan idan har meenah zata iya sakawa rai hudu wuta kai tsaye a bayyane baa boyeba sbd kishi tabbas babu abinda bazata iya ba.

Washe gari da sabuwar Meenah aka tashi dan kuwa har daki taje ta gaida kowannensu duk da koda ta shiga dakin Dr mum tana waya a natse bata amsa mata ba dan haka haka ta gaji da zama ta miqe ta fice daga dakin.

Maamah kuwa sosai ta dan sake mata tana sakata tsayawa cikinsu taci abinci tana kokarin cigaba da riqe kanta itama.

Haka ko bayan cin abincin ta dan zauna cikinsu

Please Login or Register in order to submit comment