Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna mata sannu da tambayar abinda yake faruwa.

Cikin nutsuwa ta sanar musu kawai zazzabi ne kwana biyu sbd stress na aiki amma ba komai.

Fatima data fice daga waje bata sake shigowaba sai sai taga doctors sun iso su uku sun shiga cikeda tsananin girmamawa suke gaida Daddyn suna masa bayanin ba wata matsala bace.

Baa wani dauki lokaci ba suka tattara dr fammah din aka koma gida da ita a cikin daren dan haka itama fatima a cikin daren ta tafi gida.

Sati daya dr ta share tana jinya kafin ta warware sosai ta dawo aiki.

Bayan dawowanta aiki fatima tazo har office tayi mata ya jiki cikeda kulawa itama dr taji dadin hakan sosai harma ta tambayeta mijinta da yara tace bata taba haihuwaba tukuna dan auren itama ba wani jimawa yayi ba iyakinta shekaru hudu da auren.

Kokarin janta da har fira Dr tayi sbd tanason ta sauya yanayin rayuwanta ta sabu da mutanen da zasu ringa saka rayuwarta zama me tarin mutane sbd lafiyanta da kwanciyan hankali.

Sun dan jima a tare kafin ta sanar da fatiman ta shirya gobe zasu tafi garin su Aisha dubiyar mahaifinta.

Fatima bata musa ba kuwa washe gari ta taho da dan shirinta tana gama aikinta dr fammah din ta sanar da shugabansu zatai tafiya da fatiman.

Drivernta ne yakaisu dayake ba wani gari ne me nisa sosai ba.

Sunje sun dubosa kuma dr fammah ta bada shawaran dawowa dashi asibitinsu zasu kula dashi sosai.

A ranar suka dawo basu kwana ba amma koda suka dawo dare yayi sosai sosai dan haka kai tsaye jeerah villa dr ta tafi da fatima ta kwana acan sai washe gari suka tafi asibiti tare.

Bayan andawo da mahaifinsu aisha asibitin sosai suke samun kulawan manyan likitoci da kuma ita kanta fammah da Fatima sosai suke shiga cikin masu nunawa kulawa da hidima.

Yanda fatima tafara shigar dr fammah ya saka aisha jin nutsuwa dan kuwa tana iya ganin nutsuwan da dr take samu da ita dan yanxu tana cin abinci a asibitin sabanin a baya sam bata cin komai harta wuni ta koma gida amma sbd fatima data zama tamkar me aikinta ta musamman ya saka take sakewa da aiki cikin kwanciyan hankali dan kuwa office dinta fatima ke zuwa tayi serving dinta abincin da ake kawowa daga gida wanda a baya bata ci sedai ta bayar.

Fatima batada kowa aikinta kawai takeyi dan haka dr fammah tajata a jiki sosai ta yanda har gida take zuwa da ita tana tayata zama da fira da sauran ayyukan sai tayi kwanaki biyu tukuna kafin taje gida ta kwana biyu kuma ta sake dawowa gurinta duk da kullum suna tare a asibiti.

***Ahankali familyn jeerah suka fara ganin sauyin rayuwar dr fammah wadda ta sake yanzu sosai ta fara zama yar qasa ta kwantar da hankalinta sbd fatima data zama tamkar yar uwa gareta tare take xuwa koina da ita.

Ta cire fatiman daga aikinta bata aikin komai yanxu albashi kawai take bata wanda itama fatiman ta dena amsa sbd daman dan rufawa kanta asiri take aikin kuma tinda asirin nata ya rufe sai kawai ya zamana sun zama yan uwa ba biya tsakaninsu duk da dr na tara mata kudinne a gurinta.

Acan gida ma kusan kowa yasan da fatima a rayuwar dr fammah dan itace ta saka ta zama abinda su basu iya sakata ba.
#MAMUH
#FAMMAH JEERAH
#FATIMA
#JEERAHS

GANIN IDO 2026
Mamuhgee

1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

8
_*LADY'S BEAUTY PALACE*_
08169307477
MACE SAIDA GYARA
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ki koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon

To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,

MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,

LADY'S BEAUTY PALACE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Lace
Hijabs
Supplements
Kayan yara da dai sauran Su

Location Katsina state
WhatsApp or call 08169307477
TikTok Hajara Rabiu ( Ladys beauty place)

********
Iyayen dr fammah sun san fatima wadda itama sukaji sunfi kauna akan dangin mijinta sbd itace ta kawo walwala a rayuwar yar tasu da harsun fara dana sanin auren nata tinda wanda ake zaman sbd dashi yana can ya sadaukar da rayuwarsa ga aikinsa yabarta a hannun familynsa da babu ruwansu da kulawa iko da rashin hayaniya kawai suka sani.

Yanda iyayenta ke kaunar fatima ya saka fatima sake jinsu kaman nata ahalin da batada itama dan haka sosai har cikin jininsu suke jin juna,

Masu aikin bangaren fammah tini suka koma sedai aikin da baa rasa ba amma komai ya koma hannun fatima sedai ta basu umarni su cika itace mai cikakken iko akan komai na dr fammah,

Aisha ma tini aikinta ya huta dan kuwa sai abinda ya danganci ilimin boko take nemanta komai nata fatima ce yanzu hakama ta dage sosai akan fatiman ta sauya mata rayuwa itama ta maidata kaman ba itaba hatta mijin fatima dake zuwa yana komawa ganin fatiman ta samu rayuwar data kama sai ya koma yanzu saiyayi watanni bai dawoba daman dawowan dole yake yafison yawonsa akan dawowan dan haka yanci ya samu hakan yayi masa daidai dan kuwa haddda aure ya qara acan batareda sanin fatiman ba.

Fatima ta dade da dawowa gabaki daya jeerah villah sai idan mijin nata ya taho take komawa idan ya tafi ta dawowanta sbd daman dangin mijin kowa ta kansa yakeyi qaninsa ne daya tak da suke uwa daya uba daya yake kulawa da ita daman can inda aka fito tinda yaga ta samu mafita sai bai damuba yabarta tana zamanta a jeerah villah sbd yaga yanda balarabiyar ke kulawa da ita kuma shima tana mutunta sosai sosai sbd ganin shi kadaine mai kaunar fatima da kulawa da ita dan tamafi kaunarsa akan mijin fatiman gashi a gida daya suke daga ita sai shi dan haka suke rayuwar a takure sbd tsoro da kuma sharrin mutune da shedan dan haka zuwan fammah rayuwarsu tamkar rahama ne dan yanzu shikadai ne a gidan ba kowace irin tsoro da gudin bacin suna tsakaninsa da matar yayan nasa.

Hakeem jeerah ma zuwan fatima rayuwar matarsa shine babban farin cikin daya samesa tin bayan aurensu sbd matarsa a yanzu ta zama matar bahausa ta iya abubuwa da dama hakama yana jin dadinsu sbd hakan na basa vibe na kasancewansa bahaushen dayake kokarin sabawa da rayuwarsu shima.

Ita kaunar dake tsakanin fatima da Dr dinta baa magana dan kuwa a yanxu babu sirrinsu da suke boyewa juna sun zama harsun wuce kowace irin girman shakuwa da kauna da kuma kusanci.

Sitira da duk wani abu dazai fiddo mace babu abinda fatima bata mallaka ba,

Saida suka share sama da shekaru biyu a tare kafin kwatsam Allah ya bawa fatima ciki wanda bata gama tabbatarwaba bare ta fadawa dr fammah sai ga dr fammah da ciki itama sbd ita dr fammah din dataso haihuwa a lokacin sosai saita dorasu akan tsarin da allah zai datar dasu cikin a likitance kuma cikin ikon Allah sai ga cikin ya taho musu a lokaci daya.

Fatima murnar cikin cikin dr fammah ya sakata yin shiru akan nata ciki sbd farin cikin da kaf ahalin jeerah ke yi ba qarami bane dan kuwa 'dan hakeem jeerah shine asalin magajin jeerah sbd shi kadaine namiji dan haka dan dazai haifa shine nasu 'yayan diyansu mata kuwa na wani gidan ne.

Alh babbah Ahmed kusan murnarsa da farin cikinsa yafi na kowa duk da kowa na yi dan haka da kansa ya tabbatarda babu abinda dr fammah xata sake nema ta rasa.

Shi kansa hakeem jeerah dawowa yayi sbd tsananin farin ciki,
Iyayenta saida mahaifiyarta ta taso takanas tazo dubata.

Fatima taga asalin kauna da soyayyar dangi da zallar gatan da duniya bata taba ganiba akan cikin dr fammah dan haka kwata kwata bata bayyanarwa da dr fammah da maganar nata cikin ba sbd daman ita kadaice zata fadawa sai kanin mijinta sbd batada kowa bayan su sbd shi mijin ma nata ko nemanta ya dena yi kaman ya gama da aurenta tinda yayi wancan tahowan ya koma kwata kwata babu kauna a lamarinsa da ita yanzu dan haka nata cikin baida kowa bayan shiru.

Bayan captain hakeem jeerah da fammah da iyayenta kusan itace ta uku dake mutuwar son abinda yake cikin fatima dan haka a yanxu rayuwarta ta koma gurin kulawa da fammah kawai.

Mahaifiyarta ta koma ta bar mata amanarta sbd ganinta ya saka ta sake tabbatarda ko basa raye fammah bazatai kadaici ba a duniya na zamanta ita kadai a gurin iyayenta.

Ta zauna dasu ta sake basu amanar juna da fada musu a yanxu su biyu ne yayanta dan haka su zama amanar juna har abada.

Shi kansa hakeem sbd ganin fatiman ya tattara ya koma sbd duk abinda zasuyi na kulawa gareta to fatiman zataisa harma da ninki.

Cikin yana faran diban lokaci ya koma mai tsananin laulayi da tsananin wahala amma duk wahalarsa da azabar laulayinsa baiyi ko rabin na fatima ba wadda ta danne ta jure ta tsayu gurin kulawa da fatiman wadda lauyinta da wahala ta hanata gane halinda fatima take ciki wadda ta fige ta lalace ta rame ta zama abar tausayi sbd nata yanayin amma ta hana kanta hutu ko bayyanarwa.

Bayan fammah ma babu wanda ya taba bada hankali ko bata lurar dazaa fahimci halinda take ciki,

Abincin fammah da kusan a wuni zatai kala nawa itace,
Hidimar fammah dinma itace hakama jinyar fammah din,

Ganin yanda ta lalace ta qare ta fige ta rasa kuzarinta sosai ya saka fammah shiga damuwa duk sai suka sake shiga yanayi mai wuya amma duk da hakan fatiman ce me karfin hali bata taba dena hidimar datake yiwa famman ba.


******a cikin wahala da azaba da mawuyacin hali fatima takai lokacinda cikin jikinta ya bayyana girmansa shima saida yakai wata bakwai daidai dana fammah sedai ita nata bai fitoba shiyasa baa wani san dashi ba sabanin na fammah dayake wata bakwai amma kaman na wata goma ma sbd girmansa.

Bayyanar cikin fatima ya saka fammah da iyayenta farin ciki sai hakeem da shima ya tayata murna sai kuma qanin mijinta daya kasance shine zai zama uban cikin sbd tini mijinta Ibrahim yayi watsi da ita ya rufe babinta a rayuwarsa.

KHALIL qanin Ibrahim mijinta shine wanda yake danginta kuma dangin uban cikinta daya tayata murna da fatan ta sauka lafiya.

Daukewa fatima kowace irin dawainiya famma tayi amma duk da hakan wasu abubuwan fatiman ce dole takeyi sbd babu me iya yiwa dr fammah din komai daidai idan ba ita ba.

Dr fammah ce da kanta take bibiyan lafiyar cikin fatima ya zamana itace likitarsa tinda hutu sukeyi tinda ta samu ciki ta dena fita aiki kwata kwata saita haihu ko zata koma aiki.

*****cikinsu na gap da shiga wata tara dr fammah ta fara fuskantar complications da suka saka ta ringa wata irin rama da zubar jini wanda ya saka aka maidata asibiti kwata kwata dole.

Hankalin captain hakeem jeerah da iyayenta da fatima da duka sauran familyn jeerah tashi yayi matiqa musamman da likitocin suka tabbatar musu da akwai matsala me girman da kowane lokaci babyn cikinta zai iya fadowa ba daidaiba kuma ciresa a lokacin ace zaayi mata tiyata shima akwai dan hadari dan haka dole zasu duqufa da kokarin daidaita lamarin kafin a dauki risk din gaggawar cire mata babyn.

Tinda aka fadi hakan hankalin fatima yayi mummunan tashin datake jin itama akanta ciwon ya fado sbd ita batada masu jiranta ko tashin hankalin halin abinda zai sameta.
#MAMUH
#ABDULRAHEEM JEERAH
#DR FAMMAH
#HAKEEM JEERAH
#BEST LOVE
#FATIMA

GANIN IDO 2026
Mamuhgee
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

9
*_HARGITSI_*
*_TALATU ZAKI_*
+201031621512
*Duk maaboci kuma masoyin karatun littafin Hausa to karya wuce labarin nan bai karantasa ba sbd duk wani tsari da labari yake buqata to akwaisa tattare a cikin labarin HARGITSI Na TALATU ZAKI*🔥
https://chat.whatsapp.com/ERrtA3G4obwBQzBTiJUad3?mode=gi_t

*********
Dr fammah da kanta ta zauna a cikin halinda take ciki ta fahimci matsalarta da kyau ta sauke numfashi tareda ajiyan zuciya tana sallamawa ubangijinta lamarinta sbd tasan haline mai wuya da hadari take ciki da babynta wanda take fatar koda ita Allah yariga yayi bame tashi bace allah ya bawa babynta ikon tsallakewa ya rayu kuma a hannun fatima tabar wasiyar abar mata danta ta rene sa ta shayar dashi ta zama uwarsa har girmansa.

Wannan wasiyar data bari ta saka hakeem amincewa tareda iyayenta dakuma shiga tsaka me wuyar gaske da damuwa me tsanani.

A cikin wannan mummuman halin ne aka sake buqatan hakeem da gaggawa gurin aiki dan haka ya tattara ya koma yabar fatima da fammah cikin tsananin damuwan data sake sakasu ji da kasancewa cikin kadaicin da basuda mafita,

Kowane dare haka fammah zata zauna tayi kuka cikin mawuyacin halin da fatima ma da itace ke jinyar a wahalce zaunawa ta ringa kuka tana rokon Allah ya bawa fammah lafiyar tsallakewa.

Damuwa da qunci da tashin hankali tareda rashin wanda fatima zata zauna ta rage damuwa dashi bayan fammah din wadda zuwa lokacin babu abinda take iya yiwa kanta sai an mata bata gane kowa ya saka naquda tafara taso mata kadan kadan ita batareda shiri ko tsammani ba a hakan still batada wanda zata fadawa haka ta danne tayi shiru tana cigaba da jinyar fammah wadda aka zaayiwa tiyata a cikin kwana biyun.

Acan gida ma yanda iyayenta suka shiga damuwa sosai ya saka ciwon mahaifiyarta tashi kadan kadan dan hakanne ma Abbun fammah din ya hanata zuwa sbd ta shiga mummuman damuwa sosai dan haka fatima da fammah din basa tareda kowa sai familyn jeerah da suma sun tsaya sosai akan fammah din kadai banda fatima da sam bata kanta ake ba.

Ahalin jeerah sun shiga wani mummunan halin damuwa da tashin hankalin rashin mafita bayan duqufa su qasqantar da kai gurin fadawa Allah ya tashi fammah da abinda yake cikinta wanda likitocinta suma suna cikin damuwa sbd dr fammah tasu ce kuma babu abinda take roko bayan allah yasa danta ya rayu a maimakon ita.

A ranar da zaayi aikin fatima bata rintsa ba tana zaune gaban gadon fammah idanuwanta a rufe hannunta akan na famman tayi shiru cikin mummunan yanayi naqudarta na cinta ga wata irin damuwan dake neman kasheta da abinda yake cikinta.

Koda asuba tayi a lokacin azabar datake ciki itama tayi mata yawa amma a daidai lokacin fammah ta dan iya bude idanuwanta ta qura mata idanuwanta bata iya cewa komaiba kuma tana iya gane halinda fatima take ciki na azabar naquda ta bude baki daqyar ta furta mata

'Allah ya saukeki lafiya'

Kasa iya amsawa fatima tayi sbd wasu hawayen da suka gangaro mata na tausayin su dikan.

Karfe 10 na safe zaa shiga tiyata da fammah din amma kafin lokacin yayi mahaifarta da aketa kokarin lallabawa ta gaza gabaki daya ta facce da gaggawar datafi kowace cikin mugun tashin hankali aka shiga da ita lamarin ba kyan gani wanda ya saka fatima kasawa gaba daya itama ta lallaba ta fice batareda kowama ya lura da ita ba.

Daqyar ta iya kai kanta gidansu Allah ya taimaketa Khalil yana gida sedai akai sallama aka kirasa shine da kansa ya kamata sbd baida zabi suka fada cikin gida.

Maqota ya shiga da sauri ya kirawa dattijiwar gidan ta taho da gaggawa ta fada dakin fatiman da yake cikeda wata irin kura sbd jimawan da akai babu kowa a cikinsa.

Cikin matsanancin wuya da azaba fatiman ke naquda me wahalar gaske tana ambatar sunan Allah a zuciyarta hakama da yi musu addua itada yar uwarta fammah tareda yayansu sbd tasan fatima kam bata hayyacinta bazata samu daman addua a lokacin haihuwa ba.

Bata haihu atake ba saida ta wuni tana fama da azabar nakuda mai nauyi kafin Allah ya sauketa ta haifo 'da namijin da khalil aka miqowa shi a hannunsa.

Karban jaririn Khalil yayi idanuwansa jajir da hawaye sbd tinawa da abinda yayansa Ibrahim ya fada daya kirasa akan haihuwan cewa yayi Allah ya rabasu lafiya kawai ya raya mata duk abinda zata haifa.

Khalil nada zuciya dan haka baida niyar sake kiransa tinda daman koyaushe akan fada suke akan irin yanda ya zabi duniya yabar matarsa dan yanzu watansa kusan tara harda kwanaki bai waiwayota ba.

Da taimakon dattijuwa barakah fatima ta kimtsu bayan haihuwan dan kuwa sai data tabbatarda ta taimaka mata tayi komai ta shirya ta ta shirya babyn wanda cikin ikon Allah komai na mahaifinsa ya dauko wanda yake sak da qaninsa khalil dan haka saima kusan duka hasken khalil da kammanin khalil suka bayyana a fuskansa sbd kamar khalil da babansa.

Babu yanda zaiyi haka ya cire yan kudadensa dayake kasuwancinsa yaje ya siyo kayan sakawa kala biyu da dan abubuwan buqata da abinci me kyau ya kawo mata.

Daqyar ta iya cin abinci duk da ta haihu lafiya kalau sumul amma zuciyarta na cikeda damuwan son sanin halinda fammah take ciki dan haka tin kafin ma fammah ta dawo hayyacinta tanason kasancewa a gurin.

Shi kansa khalil tinda tai masa bayanin baasan ta taho ba sai baida niyar hanata komawa inda zata samu kulawa me kyau sosai itada babyn kawai dai yace ta jira ta sake samun karfi da lafiya.

Karban babyn ya sake yi yayi masa adduoi da huduba tareda ambatarsa da suna MUHAMMAD NASIR.

shiru fatima tayi tana maimaita sunan a zuciyarta tana sauke numfashi da ajiyan zuciya sbd ta tabbatada dai 'danta ne ita kadai bada babansa Ibrahim ba.

Hawaye ne masu tsananin zafi suka gangaro mata tanajin wani irin daci da zafi suna danne kirjinta na rayuwar data samu kanta ace ko mijinta da shine kadai danginta yayi watso da ita,
Idan abaya ta zauna a jeerah villa ba goyo tayaya yanzu zata zauna da goyo?.


******
Anyi nasarar aikin ciro babyn Dr fammah,
Babyn da dukkanin familyn jeerah suke jira,
Babyn da wasu daga cikinsu sunfi damuwa dashi,
Babyn daya fito duniya da dukkanin tsananin kauna daga ahalinsa da iyayensa...

Alh babba Ahmed jeerah ne ya karbesa a hannunsa ya rungumesa kafin yayi masa wasu irin adduoi da kiran sallah kafin ya ambaci sunansa da ABDUL-RAHEEM HAKEEM JEERAH.

Kowa a familyn murna da farin cikin samuwar Raheem sukeyi hakama masu jiran fidda labarin tini suka fidda amma har lokacin mahaifiyarsa tana cikin mummunan halinda Allah ne kadai yasan menene matsayin rayuwarta dan kuwa mahaifarta ta fashe ta watse wanda hakan ya saka hankalin abokan aikinta likitoci mummunan tashin yanda zasu iya sanar da ahalin jeerahs da ita kanta fammah din wannan mugun labarin idan ma ta samu rayuwarta kenan to anyi arziki.

Da gaggawa aka sake shiga da ita wani sabon aikin wanda ya saka kowa nutsuwa murna ta dakata tukuna.
#MAMUH
#RAHEEM HAKEEM JEERAH
#MUHAMMAD NASIR IBRAHIM
#JEERAHS

GANIN IDO 2026
Mamuhgee
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

10
*_HARGITSI_*
*_TALATU ZAKI_*
+201031621512
*Duk maaboci kuma masoyin karatun littafin Hausa to karya wuce labarin nan bai karantasa ba sbd duk wani tsari da labari yake buqata to akwaisa tattare a cikin labarin HARGITSI Na TALATU ZAKI*🔥
https://chat.whatsapp.com/ERrtA3G4obwBQzBTiJUad3?mode=gi_t

*********
Duk wannan tashin hankalin da tsananin da dr fammah ta shiga tin kafin haihuwa zuwa bayan haihuwan captain hakeem jeerah bai samu damar zuwa ba duk yanda yaso zuwan babu ko yar qaramar hakan dan haka yana can cikin matsanancin tashin hankali da damuwa amma duk da hakan ya iya dannewa ya fuskanci aikin dayake gabansa mai mahimmancin da zai qara daga matsayinsa zuwa sama.

Iyayenta kam lamarin yayi musu shigar bazatan da zuciyar mahaifiyarta ta kasa dauka saida aka kaita asibitin da dole likitoci suka riqeta dan haka ba damar zuwa ga yarsu duk yanda suke cikin tsananin damuwanta da babynta.

****aikin da akai mata me tsananin hadari da taka tsantsan ne an dauki lokaci me tsayi sosai kafin aka fito da ita tsakiyar dare zuwa private dakin hutun da zata zauna.

Likitoci da nurses sun gama komai akanta sun fice sun bawa familyn daman shiga amma babu kowace irin hayaniya da ake buqata.

Sun shigo da yawansu sun tsayu akanta cikeda addua da fatar warkewanta.

Har asuba su Ummah na dakin tareda ita kafin gari ja fara haske suka tattara suka koma gida aka bar mutum daya a cikin masu aikinta dan kulawa da ita kafin anjima.

Da Raheem suka tafi sbd ko an barshi bata hayyacinta da zata iya basa nono ko wani abin dan haka suka tafi gidan dashi dan aje a shiryasa.

Wuni guda ta sake yi bata farfadoba bare dawowa hayyacinta dan haka likitoci suka sake dunguma da duqufa akanta damuwansu na ninkuwa sbd akwai abinda suke tsananin gudu da kokarin hanasa tabbatuwa.

*****fatima data kwana ta wuni ta tabbatarda ta warware sosai hankalinta bai kwanta ba ta kasa samun nutsuwa haka ta shirya ta fito tareda khalil wanda ya kaita har asibitin itada babyn tukuna ya juya ya tafi.

Ko data iso dakin babu kowa na familyn jeerah dayake asibitin bayan wadda aka bari ta kula da ita dan haka jikinta ya sanyi musamman data sauke idanuwanta akan fammah din wadda duk wata rahama da kyan gani sun bar jikinta da fuskanta dan kuwa tayi wani duhu fatarta ta bushe bakinta ma ya bushe tana kwance kaman babu rai a jikinta.

Silalewa tayi ta zauna idanuwanta cikeda hawaye tana jin hankalinta ya gama tashi gabaki daya daga karshe kasa riqe kukanta tayi ta sakesa ahankali sbd tsoron daya shigeta dan kuwa haka mahaifiyarta ta koma kafin rasuwarta tabar duniya.

Sai datasha wani irin kuka sosai kafin ta iya dago fuskanta ta kalli saratu dake gefenta tsaye shiru itama tausayin fammah din takeyi sbd yanda ta kasa samun cikakkiyar kulawa da kauna daga dangin mijin daya kamata su kula da ita sbd mijinta da baya kusa.

Tambayar babyn fammah tayi
Saratun ta fada mata yana can jeerah villah an tafi dashi.

Wasu hawayen ta sake sharewa kafin ta juyo da kallanta kan fammah tana jin kaman zuciyarta zata dena bugawa sbd damuwa da wani irin daci.

Shiru sukai a dakin tsawon lokaci sai ga likitoci sun shogo tareda Su daddy da kansu da matayensu harma da Raheem an dawo dashi.

Ummah data ga fatima batama lura da goyon danyan jaririn dake bayanta ba ta dan yi mata fadan inda ta tafi tin jiyan kafin ta miqo mata Raheem wanda yake cikin lafiyayyan lallausan bargon babys me fari qal yana bacci jikinsa sanye da fararen bodysuit da hula an nadesa sosai.

Hannuwanta biyu ta saka suna wata yar rawa zuciyarta na bugawa da kaunarsa idanuwanta fes akansa tana masa kallanda da mahaifiyarsa na hayyacinta itace zatai masa ta rungumesa jikinta tana sauke ajiyan zuciya tsananin kaunarsu da sonsu su biyu shida nasir dake bayanta tana ratsota ta gaba data baya.

Ficewa tayi sbd bawa su Daddy guri da likitoci saratu na biye da ita.

Suna fita zaunawa tayi a qaramin sitting room din dake dakin ta sake dago Raheem da kai tsaye zaka san balaraba ce ta haifesa ta zuba masa ido cikeda kauna kafin ta fara rero masa adduar dataiwa danta shima.

Basu wani dauki time ba a waje akace su koma ciki sbd Raheem.

Su daddy sun gama komai kuma an gama jero musu komai na halinda fammah take ciki wadda ta rasa mahaifiyarta shikenan ba ita ba haihuwa har anaba hakama fashewan mahaifiyarta ya janyo manyan matsaloli a lafiyarta da gangar jikinta da ba yanzu ne ba itada lafiya sedai a sannu sannu lokaci zai warkar da komai.

Babu wanda ya iya cewa komai a familyn jeerah sbd lamarine daya girgiza duniyarsu da kowa ya dauke wuta.

Fitowa sukai suka bar asibitin dan komawa a san yanda zaayi a sanar da Captain Hakeem.

Ganin fatima da akasan bayan ita Fammah bata buqatan kowa ya saka baa damuba sedai aka kawo musu dukkanin abinda zaa buqata da sakewa.

Fammah bata farfado ba sai a daren ranar shima iya idanuwanta kawai take iya budewa bata iya ko motsawa me dan karfi bare tashi magana ma bata iyawa sedai kallo kawai.

Fatima ce kadai a tareda ita ko data farfado babu kowa nata babu kowa dangin miji,

Lumshe idanuwanta tayi ta sake budewa a hankali tana jin tama rasa kanta bare sanin menene takeji take cikinsa.

Likitoci suka bawa fatima daman gyarata ta dan sake shiryata aka sake gwaje gwaje da sauran abubuwansu suka gama komai suka fice.

Baa bada daman bata

Please Login or Register in order to submit comment