Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace

"Meenah me kikeyiwa muaamala da wannan matar?
Kina sane da hadda rashin sanin kanki da limits dinki ya sakani zuwa??

Shiru Meenah din tayi tanajin zufa na dan tsatsafo mata na halinda Hajiya ta sakata da kalamanta dan daga farko haka taji saukansu kaman FLEET yayi Aure take nufi.

Ahankali ta bude baki tace

"Smah liya ya Ammi(i'm sorry)"

Juya harshe Dr Mum din tayi dayake kusan duka wainda ke gurin suna ji har Maamah din da fammah ta fara fada sosai tana sauke bacin ran dayake masifar cinta ta rasa inda zata zazzage shi.

Tsit palon yayi larabcin Morocco ne kawai yake tashi hatta masu aiki tsit sukai suna ji,
Hatta hajiyar Samad din data dan bata qarasa ficewa ba tana jin masifar wadda ta sakata jin kaman ta dora hannu akai ta rusa ihu sbd baqin ciki dayake neman kasheta dan tasan ita ake xagi ko aibatawa.

Allah ya tsinewa duka dangi da larabawan Morocco duk inda suke ta ringa maimaitawa tana tattare lifayarta data zame ta koma bangarenta idanuwanta jajir.

Dr Mum kuwa ta jima tana fadan da babu wanda ko motsawa yayi dan sun saba da sanin fadanta da bayada dadi sam.

Tana gamawa ta juya ta shige dakinta ta rufo sai a lokacin kowa ya sauke ajiyan zuciya.

Maamah ce ta zauna kusa da Meenah din tana dan rarrashinta da dorawa da tata nasihar akan ta kasance mai kula da nutsuwa da karantar komai dan nan din a cikin dangin miji suke.

Mommy kuwa da bata taba ganin masifar Dr Mum din ba sanyi jikinta yayi tana jinjina sanyi da nutsuwan RAHEEM kwata kwata ba ita ya biyoba kaman Maamah ce mahaifiyarsa ba Dr dinba dan daga uwa har uban bai dauko kowaba.

Su kansa iyayen nasa sunsan babu wanda ya dauko a cikinsu shayarwar da Fatima tai masa ne ya dauko sanyi da nutsuwanta tsaf sbd Nono yanada bada irin wannan effect din sosai dan hakane haryau basuyi dana sani ba saima farin cikin itace ta shayar dashi nononta shi kansa yana alfahari da hakan dan kuwa da allah ya jarabcesa da dauko zafin iyayensa da rayuwar su ukun baasan ya zata kasanceba.

Babu sauran zaman dazai kasance a bangaren tinda Dr ta shiga bacin rai dan haka kowa kama gabansa yayi suka baro bangaren harda mommyn.

Maimakon ta koma bangarenta bangaren mommy ta bita suka nufa acan suka zauna mommyn na hanata shiga damuwan data ga tana neman shiga hakama fammah ta zauna gefenta suka samu ta warware ta dawo daidai sai a lokacin SANAAH ta fito dakinsu zata koma can inda suke yanxu tagansu a zazzaune ta qaraso tana kallansu kafin ta tsayar da kallanta akan Fammah da ido tace mata

"Lafiya dai??

Da ido ta nuna mata Mum din tana mata alaman taxo ta rarrasheta itama.

Kallan Mum din tayi tana shiga dan mamaki amma hakanan ta daure ta qaraso gurinta ta zauna gefenta daya kafin ma tayi magana Mum rin ta kama hannunta tana cewa

"Karki damu baby SANAAH its ok ya wuce"

Gyada kai SANAAH tayi tana dan zame hannunta cikin nutsuwa da dan tapping hannun Mum din tana miqewa dan baa sake take ba taje ta dauko ruwa ta kawowa Mum din tana bata da kulawa tace

"Kisha ruwa zaki sake jin dama dama"

Karban ruwan tayi tareda cewa

"Thank you"

Kwasa sukai suka koma bangarensu acan ma sallar magrib kawai suka Mum din ta samesu dakinsu ta zauna kirjinta na mata wani irin nauyin data kasa riqewa ta fasa musu kuka mai sanyi tana jin zuciyarta gabaki daya ta rasa nutsuwa da aminci sam tinda hajiya ta fadi maganar sai zuciyarta ta kamu da wannan rashin nutsuwan datake ji.

Daman a duniya yarta ce kawai take zaunawa tayiwa kukan matsalarta dan haka ma ko yanzu tinda sun zama yayanta bataji komaiba a gaban SANAAH.

SANAAH tashi hankalinta yayi sbd batasan meya faru ba kuma ta kasa tambaya dan haka sai jikinta yayi sanyi tausayin Mum din ya ciketa suka ringa rarrashinta da kulawa mai tsanani da kauna.

Sun samu ta sake ta dena kukan suka lallabata zuwa cin abinci.

Suna fitowa ita bedroom dinta ta wuce su kuma suka wuce dining din.

Ga mamakin sanaah Mum din kaya ta sauyo ta goge fuskanta fes ta gyarota kaman ba wadda ta gama kuka ba.

Kallan kayan data sauyo tayi zuwa riga doguwa mara fadi daidai jikinta da ba wani lalacewan da yayi.

Tana kokarin zama Fleet din ya sako kai sanye da qananun kayan Balmain hannunsa sanye da agogon bvlgari black da kudinsa zai siya maka motar hawa gangariya.

Shigowansa ya saka SANAAH dagowa kadan ta kallesa daidai shima din ita ya kallo sbd shigewa cikin muryan Fammah datai ta gaidasa a tare da gaisuwan famman datake masa.

Dauke idanuwanta tayi ahankali tana maidawa akan wayarta datai haske alaman shigowan sako.

Mum hannunsa kadai ta iya kamawa tana dagowa ta kallesa tareda bude baki a natse ta gaidasa.

Zaunawa yayi bayan ya dan kalleta kadan yaga yanayin datake ciki na jiki a mace.

Yau ba fammah bace take serving dinba SANAAH ce sbd ganin yanayin da fammah take ciki na rashin jin dadin ganin damuwa a tattare da mahaifiyarta sbd sun iya maida abu qarami babba haka suke abinda ya kamata su bawa wannan damuwa da lissafin sam basa basa sai abinda ma mamaki zai kasheka suke hadawa karfinsu.

Shi ta fara zubawa komai a natse kafin ta isa gurin Mum din ta zuba mata tana zubawa fammah ta zubawa kanta dan daidai wanda zataji tana kokarin zaunawa ya bude baki kadan ya furta mata

"Thank you" kaman yanda yakewa fammah aduk lokacinda zatai serving nasu.

Dagowa tayi kadan jin kalman tasa sedai bata kallesaba ta dauki spoon ta saka zata fara.

Mum fara cin abincin tayi ta ajiye spoon din hannunta ta dago ta kallesa taji bazata iya nutsuwa ba batareda tayi masa magana ba kawai tace

"Fleet wai zaka iya qara aure...?"

Sarkewa SANAAH tayi da tari mara karfi ta aje spoon din hannunta tana daukan ruwan gabanta takai bakinta tasha tana dagowa ahankali ta kalli Mum din.

Shi kansa daga sama kawai yaji maganar da mamaki mai girma amma bai nuna hakan ba hakama bai dena cin abincin dayake ci dinba sbd koyaushe bata sanin lokutan daya kamata ayi wata managar ta saba kowace magana tana masa a gaban fammah tin acan rayuwarsu dan haka ba komai take samun amsa daga garesa ba.

Yanayinsa ya saka bata sake cewa komaiba tayi shiru hakama su famman ba wanda yace komai din sbd ita kanta fammah bataji dadin tambayar da mum din tai masa ba,
SANAAH kuwa faduwan gaba ta samu mai karfin gaske dan batasan shine tashin hankalin da suketa faman rarrashin mum din akansaba.

Shine ya fara barin dining din fuskansa a kame hakama yanayin zaman da akai kowa yaji tension din zaman a jikinsa.

SANAAH tana gamawa barin gurin tayi sbd ganin fammah ta fara magana da mahaifiyarta.

Daki ta koma tana shiga bathroom ta wuce tayo wata alwala tana fitowa ana kiran sallan ishai dan haka ba bata lokaci tayi sallanta tana gamawa fammah ta shigo dan haka da kulawa ta kalleta tana kokarin mata magana su samu dai kowa ya dawo daidai.

Sallah fammah tayi daga nan suka fada maganganunsu har suka sake da dariyarsu da komai.

Da safe guraren karfe tara ta baro bangaren dan yanda taga Mum ta tashi hankali kwance da farin ciki kaman ba itaba alaman ta shirya da mijin nata kenan.

Batama jira lokacin cin abincin ba tabar bangaren tayi gurin mommy.

Ko data isa suna aikin hadawa su Dr Mum abincin breakfast duk da akwai masu aikinsu acan.

Hannu ta saka aka ci gaba da aikin da ita tana kokarin firarta da Safiya.

Suna gama aikin ta wuce bedroom dinta tayo wanka ta sauya kayanta anan ta saka riga da skirt na soft cotton lace pink da touch of ash kadan mai tsadan data sakasa kwantawa sosai da rashin nauyi ko kadan.

Tana fitowa palon zaunawa taso yi taci abinci Mommy tace ta dauki abincin suje itada safiya sukai wa su Dr Mum.

Batai musu ba sbd daman dole zataje ta gaidasu dan haka wayarta ta dauka a natse ta dauki dayan basket din suka fito.

Koda suka isa bangaren ba kowa a palo sai qamshi da sanyi ne kawai yake tashi.

Hanyar dining suka nufa suka ajiye kayan safiya na cewa

"Bara na shiga kitchen na sanarwa su nafisa"

Fidda kayan daga basket SANAAH tafara kokarin yi saiga Maamah ta fito palon tana waya cikin farin ciki sosai da Al'amin data karbi numbernsa ta kirasa suna waya cikeda farin cikin jin juna tana jin kaman ta janyosa gabanta ta rungume ta saka masa albarka.

SANAAH ajiye abinda takeyi tayi ta iso gurin Maamah din wadda tana ganinta ta sake washe baki tana kamata a natse suka zauna tana cigaba da waya.

Ganin wayar ba gamawa zasuyi yanxu ba ya sakata kallan SANAAH tace

"Kije dakin Dr Mum dinku ki gaidata"

Miqewa tayi ta nufi bedroom din ta dan buga kadan kafin ta bude a natse ta shiga da sallama a tsanake.

Ba kowa a dakin da alama tana bathroom dan haka zaunawa tayi a sofa a natse tana shaqar kamshin dakin mai dadi da sanya nutsuwa na Dr Mum.

Tana zaune tana jiranta aka buga kofar a natse tareda budewa.

Juyawa tayi ta kalli kofar daidai sako kansa ciki shima yana kallan ciki take idanuwansu suka shiga cikin na juna ta dauke nata da sauri tana dan juyowa.

Takowa yayi a tsanake da kwarjininsa ya qaraso ciki tareda sake kallanta kafin ya zauna a gefenta kan sofan datake zaune sbd guda daya ce mai fadi a dakin.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

67
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
EID MUBARAK PROMO PACKAGE
Gara basa gara basa da 7500 dinki
duk wadda ta bari promo nan ya wuceta tayi hasara ba karamaba don wannan ya wuce duk tunanin ku kayan dake ciki ko 50k ka siyesu bakayi hasaraba bare 7500 hmm inba gurin Zuzeam ba wazai muku wannan gatan
1. Tabajen kankana
2. ⁠Gumbar aya da ridi
3. ⁠Tsimin mallaka mai maganin infection
4. ⁠Garin dadi har madiga
5. ⁠Hadin dafa kaza ko Ciccibi ko nama, Kinga yanzun sallah za ai nama ya wadaci kowa hajiya kina iya dafa nama tsoka 7 da maganin ki zai miki mallaka naban mammaki zai ciko miki da gaba zai kara miki dadi da dandano.

Sannan mutun ashirin na farko nada kyautar Turaren tsugunno na mallaka gagara badau 5k

Ina amaren bayan sallah wannan hadin ya dace daku ko mai jego wadda take shirin haihuwa ma Tana iya siya ta aje ko shekara yanayi bai komi
Ina Uwar gida maiji da kayanta wannan hadin nakine
08144015291 For more information say hi,
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
DAHUWAR KAZA
Kin taba cin DAHUWAR KAZA 5in1 wato Ni’ima,Matsi,Chikowa,MAllaka da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya.
INA MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku 08144015291 Zuzeam ventures.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set
08144015291

*********
Motsawa tayi ahankali tareda dan dagowa batareda ta iya juyowa ta kallesa ba ta bude baki tace

"Ina kwana"

Fararen idanuwansa ya juyo ya kalleta dasu kafin ya bude baki kai tsaye ya amsa gaisuwan tata da sautin muryansa daya ratsi kunnuwanta da wata irin nutsuwan data sakata dan sake motsawa tana jin son tashi tabar dakin.

Sake bude baki yayi ya jefa mata tambaya a wata irin gajarcewa da tsantsan ilimi da turai data ratsesa yace

"Dr Mum??

Kai tsaye cikin kunnuwanta maganar ta shiga zuwa cikin kanta da kirjinta sbd muryansa wani strong aura ne da ita da babu wanda zai jita a tsanakenta da kamewanta ba baijita a tsokar jikinsa ba dan haka ahankali ta dan qanqame hannunta daya ta dago idanuwanta tareda kasa hana kanta juyowa a hankali ta kallesa da idanuwanta da babu abinda ya raba kamarsu sak da sak da Nasir.

Jin saukan idanuwanta akansa ya sanyashi sake juyowa ya kalleta da idanuwansa dake fizgar duk ajin mace akansa..

Kasa motsawa tayi hakama kasa fidda numfashi tayi idanuwanta na kokarin daukewa daga kallansa yace

"Menene say dinki akan abinda yake faruwa??
Idan kinada kowane raayi akan hakan zaki iya sanar dani"

Kaman daga sama taji zancen dan haka ta sake kallansa gabanta na dan faduwa sbd a yanxu batada say ko wani raayi akan komai sai yanda akai da ita.

"Karki komai just fadi abinda kikeso akan auren"

Dagowa ta sake yi wannan karan bata iya kallansaba sbd idanuwanta dasuka narke kaman zasu tara hawaye ta bude baki zatai magana kenan Dr Mum ta fito daga bathroom din a shiryenta tsaf da doguwan riga baqa daman tayi wankanta alwala ta koma tayo dan bata son zama ba alwala a jikinta.

Da wata irin sakewa da kauna mai tsananin karfin gaske ta kalli SANAAH tareda bude hannuwanta tana cewa

"Y'allah habebty"

Tasowa SANAAH tayi ahankali ba rashin wayewa ta shiga jikin Dr Mum din tana cewa

"Ina kwana Mum"

Amsawa da farin ciki dr mum din tayi kaman ba itace mai fada da bacin rai ba jiyan itama ta tashi ranta fes batada sauran kowace damuwa bayan ganin SANAAH ta samu right dinta a hannu.

Shi kansa RAHEEM din albarkacin ganin SANAAH ya samu da sakewa da kulawa ta gaisa dashi tana tambayar Meenah da Fammah.

Amsawa yayi da tsanaki kafin ya kalleta lokacin datake zama tareda SANAAH a gefenta tana riqe da hannunta yace

"Maganar gurin zamanki danai miki alkwari ya kammala zaku iya shiryawa zuwa anjima kadan a kaiku"

Kallansa ta juyo tayi babu alamar nauyin komai ko tina komai hankali kwance tace

"Wane gidan kenan??

Kallanta ya dago yayi yana karantar yanayinta na dagaske take tambayar yace

"Gidan da zaki bar nan ki koma"

"Kabarshi kawai na hakura zan zauna anan din"

Kallanta ya kuma dagowa yayi ta kame fuska .

Baice komaiba jin abinda ta fada kawai yayi mata sallama ya fice yabar dakin.

Yana fita ta sake fuska tana kallan SANAAH da kulawa tafara kokarin mata tambayoyi akan karatunta da zaman Gidan.

Anan taji inda SANAAH din take zaune tayi shiru tana juya lamarin a ranta wanda kusan su dukan zasusha wuyar hakan dan gwara Meenah batasan da kishiya take zaune ba ita kuwa data san meenah matar mijinta ce zatafi shan wuyan abubuwan da idonta zai gani ba daman nuna damuwa hakama bazata taba samun daman kebewa da mijinbama.

Fitowa sukai tare tana sake magana da SANAAH din wadda take cikeda jin nauyinta.

Har lokacin Maamah waya takeyi dan haka kai tsaye dining suka nufa inda abincin da suka kawo.

Maamah na gamawa acan ta samesu dan haka acan suka gaisa suna zaunawa su duka hadda SANAAH din da Dr Mum tace ta zauna taci a cikinsu.

Suna cin abincin suna magana da SANAAH din da nuna kulawa wata kauna mai karfin gaske har suka gama.

Suna baro dining din Ms Meenah na shigowa gaida su itama tana ganin SANAAH ta fara nuna kulawa da mata fadan ta dena fita batareda ta tsaya taci breakfast dinta ba.

Da mamaki dr mum ta kalli Meenah din kafin ta amsa gaisuwan datake mata da kulawa alaman ta sauko daga bacin ranta dan haka farin ciki ya cike meenah ta zauna tana gaida Maamah da fara zuba tana nuna ita yanxu ta zama yar gari da nuna iko iko akan SANAAH a matsayin uwa.

Maamah tausayinta taji ya ciketa sosai dan haka ta ringa nuna mata kulawa da kauna sbd a yanzu kam sedai kowa yayi hakuri Dr Mum bazata iya hada kaunar SANAAH da kowaba duk da bazata taba qin Meenah ba sbd itama tatace.

Ita kanta Dr Mum din tausayin Meenah taji tana ji sosai sedai ba yanda zasu iya wata kusan tafi wata hakama soyayya da tsantsar kaunar datake wa Nasir kai tsaye daga jiya xuwa yau ta koma akan SANAAH.

Anan bangaren suka wuni gabaki dayansu sunata walwalwansu hadda mommy nan ta taho suka wuni suna shaaninsu.

Sai dare kowannensu ya watse kai tsaye Dr Mum tace abar SANAAH anan tayi zamanta tukuna.

SANAAH da daman hanya take nema take ta amince da lallaba fammah da dadin baki da shagwaba har famman ta amimce tana tsokanarta da cewa indai dr mum ce kwana biyu zata sha fadanta da saikayi kwana biyu kana zazzabi.

Wani nutsuwa da farin ciki SANAAH taji na baro bangaren dan haka ta sakewanta anan gurin su Dr Mum.

Washe gari itace ta rigasu fitowa ta isa kitchen ta saka hannu a shirin breakfast dinsu tana gama jerawa suna fitowa kusan a tare.

Sunci sun gama kenan saiga Ms Meenah tazo.

Tana gaidasu ta zauna ta kalli Maamah tace

"Maamah dan Allah kiwa fleet magana ko zai amince a bani bangare na daban sbd ko SANAAH ta kasa sakewa sosai a bangaren sbd muna guri daya da Dad din nasu inason inda zamu sake sosai"

Dr Mum dake duba sako a waya dakatawa tayi ta juyo tana kallan Meenah din cikeda mamaki dan kuwa ita kadaice haka a cikin mata tana ganin.

Maamah ma kallanta tayi dakyau kafin tace

"Kina tareda mijinki zaki nema raba guri Meenah?
Kinfi son ki ringa yawon zuwa kullum gurinsa kenan?

Gyada kai tayi tana dan nuna kwantar da kai tace

"Maamah sbd yaran kinga sun zama yan mata muna guri daya dasu gwara a bamu gurimu din zaifimin na ringa zuwan"

Kara bata shawaran tabar maganar maamah tayi tana lurar da ita illar hakan sbd zai iya zamana sun iya fara samun rashin kusanci anan din,

Sam Meenah kasa iya hakura tayi ta nacewa rokon Maamah din ta masa magana sbd itace kadai zata saka ya mata yanda takeso din tinda tayi magana bai amince ba.

Sake magana Maamah tayi amma ina bataji bata gani ita hakan kawai takeso sbd ta samu nata cikakkiyar haqqin tanada nata bangaren bawai na miji ba.

Rasa abin fada Maamah tayi ita kuwa dr mum tinda dai Meenah din ta buqata hakan anata kamota tana zillewa a zance dan haka hakan yayi mata daidai sbd zai kasance bangarensa kowa sai shi kadai sai kuma macen data samesa kenan a tsakanin ita da SANAAH Maamah zata sake tausarta tabar maganar Dr Mum ta katseta da cewa

"Abar maganar zaa mata yanda takeso tinda ita ta buqata"

Maida kallanta tayi akan meenah wadda taji dadin maganarta tace

"Ki shirya ki hada kayanki koda babu bangaren baki ki dawo nan anbar miki mu saimu koma bangaren Zainab hakan ma yafi"

Meenah na jin hakan wani sanyi ya mamaye kirjinta tace

"Ngd Dr Mum, Allah ya saka da khairan ya qara lafiya da nisan kwana"

Murmushi mai kyau Dr Mum din tayi tana saka mata albarka tareda dan kallan hanyat kitchen da SANAAH take can tareda masu aiki suna magana.

Maamah kuwa Meenah ta kuma kalla tana fatar hakan ya zama abinda bazataiwa dana saniba.

Dr Mum kuwa sake jin kwanciyan hankali da farin ciki tayi sbd hakan da meenah tayi yayi mata daidai a cikin saukin da batareda tayi abinda zata saka meenah din jin kunci ba ita da kanta ta buqata.

Tsabar zumudi da farin ciki washe gari ta gama hada kayanta hankali kwance shima baice mata komaiba akan hakan sbd Maamah tayi masa maganar dan haka ya amince.

Dad ma daya samu labarin tashin nata murmushi kawai yayi yana cewa ai shikenan tinda ita ta buqata.

Su Dr Mum basuda wasu kaya bayan suitcases dinsu dan haka take aka gyara musu dakuna fes a bangaren mommy aka kai musu kayansu suka komawansu daman sunfi ma son hakan hakama itama mommyn tayi farin ciki sosai zuwansu.

Sabon parking Ms Meenah tayi a sabon bangaren wanda taji hankalinta ya kwanta ta samu abinda take so dan haka take cikin farin ciki sosai.

Fammah da SANAAH da murna ta koma ciki na ganin ta sake dai zama gurinta dukda da sauki tinda Fleet din baya bangaren.

Da daddare ta gama shirinta bayan kwankanta ta saka kayan baccinta riga da wando bar qasa ta dora hijabinta har qasa shima akai ta fito taje kitchen ta dauko tray na tea din Dad zata fice Dr Mum dake zaune palo dayake a bangaren mum take masa tea dinsa.

"Ina zuwa ne SANAAH"

"Dad zan kaiwa tea dinsa" ta fada tana dan dakatawa cikin nutsuwa wani sanyayyan qamshinta mai sanyi yana tashi.

Maamah ma kallanta tayi cikeda yabawa yanda take girmama Dad jeerah din.

Ms Meenah dake zaune a bangaren har lokacin saka bakinta tayi da cewa kin dafa harda Fleet ko sai shima akai masa tinda yanasha sosai."

Kallanta Maamah tayi zatai magana Dr mum tace

"Idan yanaso to takai masa wannan tinda ita ta shirya,
Ke fammah kije ki dafawa kakanki saiki kai masa idan kun dawo duka saiku wuce gabaki dayanku"

Tana gama fadar hakan ta kalli SANAAH tace

"Wuce ki kai masa"
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

68
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
EID MUBARAK PROMO PACKAGE
Gara basa gara basa da 7500 dinki
duk wadda ta bari promo nan ya wuceta tayi hasara ba karamaba don wannan ya wuce duk tunanin ku kayan dake ciki ko 50k ka siyesu bakayi hasaraba bare 7500 hmm inba gurin Zuzeam ba wazai muku wannan gatan
1. Tabajen kankana
2. ⁠Gumbar aya da ridi
3. ⁠Tsimin mallaka mai maganin infection
4. ⁠Garin dadi har madiga
5. ⁠Hadin dafa kaza ko Ciccibi ko nama, Kinga yanzun sallah za ai nama ya wadaci kowa hajiya kina iya dafa nama tsoka 7 da maganin ki zai miki mallaka naban mammaki zai ciko miki da gaba zai kara miki dadi da dandano.

Sannan mutun ashirin na farko nada kyautar Turaren tsugunno na mallaka gagara badau 5k

Ina amaren bayan sallah wannan hadin ya dace daku ko mai jego wadda take shirin haihuwa ma Tana iya siya ta aje ko shekara yanayi bai komi
Ina Uwar gida maiji da kayanta wannan hadin nakine
08144015291 For more information say hi,
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
DAHUWAR KAZA
Kin taba cin DAHUWAR KAZA 5in1 wato Ni’ima,Matsi,Chikowa,MAllaka da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya.
INA MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku 08144015291 Zuzeam ventures.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set
08144015291

*********
Kokarin kasa motsawa SANAAH keyi Ms Meenah ta katseta da cewa

"Kije ko baby SANAAH"

Daqyar SANAAH ta iya daga kafarta tafara takawa tabar gurin tana jin kamam ta dauko nauyin mota ne a kan tray din hannunta.

Maamah kuwa shiru tayi tana sauraron firar da Meenah ke yi hankalinta a kwance

Mommy kuwa hanyar da SANAAH ta wuce ta dan kalla kafin ta kalli dr mum wadda fuskanta take a kame ba alaman kawo mata kowace zance tana kallan Tv tana jin firar da Meenah keta zubawa da wani alfaharin itace matar FLEE RAHEEM JEERAH.

fammah kuwa kitchen ta nufa tana kiran Safiya taxo ta tayata da fira ko aikin.

SANAAH tafiya takeyi ahankali tana sake jin kafafunta na mata nauyi ta doshi bangaren wanda babu kowa a ciki yanzu bayan mai shi babu kuma wanda zai iya zuwa ciki yanzu sai matarsa da 'yarsa gata kaddara ta kawota batareda ta a tsammanin sake zuwa bangarenba.

Tana isowa kofar bangaren shiru tayi a bakin kofar tana dan dakatawa tsawon seconds tukuna ta motsa ahankali takai hannunta ta bude kofar kai tsaye ta shige tareda rufowa sbd sanin babu kowa aciki da idan ta buga zaaji azo a bude mata sai shi kuma a daidai wannan lokacin ma tasan yana palonsa bazai taba ji ba dan haka bazata bata lokacin tsayawa bugawa.

Palon tsit ya sake samun nutsuwa da kwanciyan hankali sbd rashin kowa hakama qamshinsa ne yake dan tashi kadan kadan dayake shine kadai yake kaida kawo a bangaren yau gabaki daya dan haka gurin ya fara nutsuwa da kamshin nasa.

Tsayawa tayi tsakiyar palon tana kallan Dining da tinanin idan ta ajiye bazai taba sanin ankawoba sedai ya kwana gurin a banza hakama batajin zata taba iya zuwa har palonsa na master bedroom dinsa takai masa.

Numfashi mara sauti ta sauke ahankali tana juyowa a tsanaki ta kalli hanyar palon nasa tana dan sake riqe tray din hannunta tareda sauke numfashi mai zafi tana kokarin juyawa ta nufi dining din kofarsa ta bude yana bayyana tareda fitowa gabaki dayansa.

Dogon wandan kayan bacci ne masu santsi da tsadar gaske a jikinsa bai saka rigar ba iya wandon ne a jikinsa wanda farar fatarsa mai asalin lafiya da kyau da zallan hutu tana daukan ido..

Babu tsammani ko kadan ta sauke idanuwanta akansa zuciyarta da tsaya cak daga bugawa ta

Please Login or Register in order to submit comment