Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita da kaina da hannuna na zama uba kuma waliyin aurenta tareda alfaharin da kowane uba zaiyi idan har zaka bani su sudawo hannuna"

Da slow Al'amin ya dago jajayen idanuwansa ya kalli Dad jeerah din yana jin hawayensa na tsayawa sbd tsananin mamaki dama rashin gane inda zancen ya dosa.

Tayaya zai bada SANAAH da mommy su dawo karkashin kulawan wani bayan yana raye to shi menene amfanin rayuwarsa daga lokacin,
Me zaiyi idan baiyi kula dasu ba?

Sunkuyar da kai yayi shima kai tsaye zai bada amsar rashin Amincewa hakan Dad ya katsesa a nace da dattako da cewa

"Al'amin a yanda kakeson ka kula ka kare dik wani haqqin mahaifiyarka da qanwarka to kana buqatan fara samarwa da kanka cikakken ilimin da zai baka damar hakan wanda zai baka dama ta sanin yanda zaka fuskanci kowace irin rai dazata cutatar da kai a ilimimance koda kuwa hukuma ce,
Nasan waye mahaifinka hakama bayan Mahaifinka Nasir baida mahaifi bayan ni dan haka ka bani su a matsayin ahalin Nasir idan bazaka bani su a matsayin naka wannan shine babban adalci da tsaron da SANAAH zata samu daga duk wani namijin wanda ma ba Samad ba ni kuma ina sake maka alkwarin bata kariyar da duk duniya babu me bata ko bayan aurenta,
Zan turaka ka nema ilimin da duk lokacinda ka kammala kazo zan baka su da hannuna idan har hakan ta kama"

Shiru Al'amin yayi yana tsayar da hankalinsa da tinaninsa akan maganganun na tsoho Dad jeerah wanda kai tsaye maganganunsa suke babu kwana kwana ba bata lokaci kowace magana direct take da jiran amsarta.

Numfashi Dad din ya sauke tareda kallansa yace

"Kada ka damu da komai Al'amin kaje gida kayi tinani me kyau da shawaran da duk abinda ka yanke zan maka hakan"

Mr S ne ya kalli Al'amin din yana nuna masa hanya suka juya suka fice yana zurfafa a tinanin maganganun da duk sunma rikita tinaninsa da hankalinsa.

Har Mr S ya ajiyesa bai fito daga tinani mai tsayin daya shigaba,

Yana shiga gida dakinsa ya shige ya rufe yana tinani mai tsananin zurfi da damuwa,
Har dare baida kuzari yana daki dai magrib ya fito yayo sallah yazo ya zauna cikinsu sukaci abinci suna dan magana sama sama sbd SANAAH da a yanzu take cikin tsananin tsoron rayuwarta kwata kwata sbd Samad.

Ko Mommy a yanxu cikin tsoro da damuwan da babu ranar fita take sai taga anyiwa SANAAH aure gashi mijin ya gagara babu wanda ya taba zuwa ma yace yana sonta kuma bazasu taho dinba sbd suna shakkar Samad jeerah da a yanzu ya fito duniya yayi ikirarin hallaka dik wanda ko kallanta yayi da sunan so.

Da daddare bayan sun rufe gida kowa ya kwanta kusan karfe ukun dare Al'amin yaji ana taba kofar gidan nasu sbd dakinsa ne a kusa.

Shiru yayi yana sake saurara yaji dakyau.,

Magana yaji anayi qasa qasa da motsin daya sakasa tashi zaune daga kwancen dayake ya kasa bacci.

Kaman zai fito sai kuma ya fasa sbd jin andena motsin kwata kwata dan haka ya koma ya kwanta yana rufe idanuwansa ko baccin zai daukesa a lokacin.

Babu jimawa kuwa ya samu bacci ya dan daukesa mai nauyi....

Cikin bacci yaji hayaniya sama sama tana shiga kunnuwansa hartai karfi tareda wani irin azababben zafin dayaji numfashinsa na toshewa da sauri ya bude idanuwansa yaga gabaki daya dakin ya gauraye da wani irin hayaqi mai karfi anata ihun "Wuta Wuta" daga waje.

Miqewa yayi da wani irin rawar jiki da tashin hankali yana nufar kofa ko gani bayayi ya isa setin kofar dakin data dauki mugun zafi tafara kannewa alamar bazata budeba.

Buga kofar yafara yi da karfin gaske yana shiga mummunan tashin hankali da tsoron halinda su mommy suke,

Karfinsa yake tsanantawa yana bugun kofar da gasken gaske ga hannunwansa sun fara konewa sbd zafin da kofar ta dauka na gaske tinda ta karfe ce.

Daga wajen aka fara bugo kofar da karfi suna ambatar sunansa Mommy ne da SANAAH suka dauko tabarya suna dukan kofar dakin ga wutar sai qara karfi take kokarin yi dan harta fada dakin mommy.

Su duka cikin matsanancin tashin hankali suke gashi sunje kofar gidan su bude sbd a shigo a basu taimako amma sun kasa bude gidan sbd an saka musu padlock ta wajen gidan wanda mutane keta kokarin son bugewa a shigo a taimakesu amma kwadon kaman na kofar duniya yaqi budewa.

Mommy ce tafara gazawa ta zube qasa tana dafe kirjinta dan haka SANAAH ta sake shiga rudu itama tanajin karfinta yayi qasa gashi bata saba da wahala ba sam irin haka dan haka tayi kan mommyn tana wani irin jan numfashinta da zafi ya fara yankewa.

Haukacewa Al'amin yaji yana yi a cikin dakin ya fara buga kofar yana ihun gaske yana kiran sunayensu jin shiru...

Koda ya samu nasarar balle kofar dakin duk tafin hannuwansa sun kone sosai amma bai damuba haka yayi kansa yana wata rawar jiki ya sunkuci mommy da duka karfinsa ita kuma SANAAH ya damko hannunta ya nufi kofar ficewa duk da gurin wuta naci.

Daga can waje karfi da gaggawa aka kara gurin balle kwadon amma yaqi dan haka aka fara kokarin bude bangon gurin dan cire kofar gaba daya sbd wuta dai karfin gaske take qarasawa.

Koda aka bude kofar Dukkaninsu su ukun sun sume a maqale guri daya da junansu Al'amin din ya qanqamesu ya gama saddaqar da rayuwarsu daga nan taxo karshen da duka wahala ta qare.

Cikin gaggawa aka fiddo dasu take akai asibiti dasu hankali tashe daga nan yan anguwa suka fara kokarin kashe wutar kafin motar masu kashe wutar taxo.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

35
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Wuta dai ta cinye gidan kusan duka babu abinda ya rage bayan bango hakama a asibiti sai da mommy tayi kwana biyu bata farfado ba sbd ta shaqi hayaqin sosai,
SANAAH kuwa kwakwalwanta abin yakeson tabawa dan zuwa yanzu ganin takeyi ta zama sanadin mummunan kaddarar ahalinta sbd an tabbatarda rufesu akai ta waje aka kunnawa gidan wuta a taqaice ransu akaso kashewa su dukan kuma abu dayane yake nuni da hakan wato Samad jeerah duk da yana jinya.

Kwana biyu sukai a asibiti suna jinyar mommy kafin ta dan dawo daidai aka sallamosu hannuwansa ma a nade inda ya kone.

Rasa inda zasu sukai sbd gida dai ya kone kurmus babu gurin ko rabawa su kwanta gashi bazai iya bari suje a hakan su zauna cikin kangon konannen gidanba sbd Tsautsayin da yayi ajalin inna na faduwan bango akanta lokacin wancan gobarar.

Zafi kansa da kwakwalwansa ta dauka yaji yana neman rasa kansa dan ko kudin komai baida ga uwa uba dare yana neman yi musu suna zaune cikin soron gidan dayake a bude babu komai dagasu sai kayan jikinsu.

Ficewa yayi ya fita bai dawo ba sai dare cikin damuwa da mutuwan jiki yace su taso ya samo inda zasu kwana kafin safe yasamo wata mafitar.

Gidan wani abokin aikinsa dayake can wata anguwa me nisa ya kaisu aka basu wani dan qaramin palo a ciki suka kwana shi kuma ya koma can gidan nasu ya kwana hakanan da tabarmar da aka basa maqota aro.

Tinda ya kwanta bai iya ko rintsa idanuwansa ba har akai kiran asuba na farko ya tashi zaune ya miqe yaje ya kama ruwa yayi alwala ya nufi masalaccin yana zaune a ciki zaune akai kira na biyu yayi nafilarsa har lokacin sallah yayi mutane suka dan fito akai sallah ana gamawa bai miqeba sbd baida gurin zuwa baisan ina ma zai fara wannan rayuwar da masifu sukaiwa yawa ba.

Yayi addua sosai ya fadawa allah ya kawo masa mafitar da zata zame masa alkhairi a yanxu.

Bai fito masallaci ba yana zaune cikin damuwa da tallafe kai idanuwansa jajir shiru har karfe kusan goman safe tukuna ya fito jiri na dan dibansa sbd nauyin kirji dana idanuwa.

Hanyar titi ya kama mutane na haduwa dashi a hanya suna masa jajen abinda ya faru wasu ma dan ciro kudi suna basa yana amsa a sanyaye kansa a qasa yana kasa iya dagowa ya kalli kowa sbd ya gama kai matakin wulaqantuwa.

Kansa a qasa a iso titi hannunsa daya dunqule da kudaden da aka basa wainda yake jin kaman suna ci da wuta a hannunsa.

Tsaye yake a titin ya kasa tsayar da abin hawa hakama ya kasa tafiyar qasa tsawon lokaci kafin ya fara takawa a sanyaye ya nufi hanyar anguwan dayakai su SANAAH.

Koda ya isa har inda suke akai masa iso ya tadda mommy zaune shiru da hijabin da aka bata ta saka sai SANAAH na kwance a gefenta ta shige jikinta sosai kanta na tsananin ciwon da ko idanuwanta bata iya budewa.

Gaida mommy yayi wadda ta dago a sanyaye ta kallesa tuna amsawa da cewa

"Yaya jikinka?
Yaya ka kwana acan gidan??

Numfashi ya sauke me sanyi yana cewa

"A masallacin anguwan kusan na qarasa daren,
Ya SANAAH haryanzu kanne??

Gyada masa kai tayi tana dan kallan SANAAH din wadda jikinta yakeda zafi sosai.

Shiru sukai dukansu babu me cewa komai tsawon mintina kafin ya tashi ya fice ba jimawa ya dawo da ruwan shayi masu zafi da bread da kudin da aka basa ya kawo musu tareda maganin panadol yace SANAAH tasha.

Babu wanda ya iya cin bread a cikinsu shayin suka sha kawai SANAAH tasha maganin daqyar tana komawa ta kwanta.

Shine ya dauki bread din babu tea yafara ci yana turawa cikinsa daqyar sbd komai daci da kaman dutsi yake jinsa.

Fita yayi yaje ya wuni yana yawon neman mafita da qasqantar da kai amma babu abinda ya samu babu kowace mafita dan haka ya kasa dawowa gurinsu sbd sai dare sosai ya dawo din ya wuce gida kawai.

Washe gari tinda safe ma abinda zai kawo musu suci gagararsa yayi dan haka ya nemi guri a tsakiyar rana ya zauna yana cusa kansa a cikin kafafunsa cikeda wani irin qunci da hawayen da baimasan suna fitaba.

Wuni guda basu ci komaiba bai taho ba kunyar zuwa gurinsu babu abinda zai basu yake dan haka basu gansa ba sai washe gari sunyi laushi sosai sun galabaita amma sun daure sun nuna masa juriya da karfin hali.

Rayuwar tai masa daurin minti sama a qulle qasa a qulle babu haske da sassauci ta ko ina ga inda ya kawosu yace kwana daya amma yanzu sun wuce kwanaki biyu ga ciwo yana son zama na SANAAH wadda ta shiga depression ma gabaki daya.

Mommy ma daurewa kawai takeyi sbd kada abin ya masa yawa amma a cikin tsananin hali take.

A yanxu dayakai wannan mummunan matakin na rayuwar da babu kowace madafa baida zabin daya wuce karban shawaran Dad Jeerah dan bawa rayuwarsu kariya da amincin da suke rasawa dama gurinda zasuyi rayuwa a cikin rufin asiri a qarqashin gata da kulawan da akai masa alkawarin basu daga nan har ranar daya samu dama da ikon amsarsu.

Duk yanda yakai ga jarumta saida ya kwana yana zubarda hawaye da wani irin kuka mai cin kirji kaman yaro qarami na radadin rabuwar dazaiyi dasu wadda kuma gwara hakan indai zasu samu amincin daya kasa basu da rayuwar daya kasa samo musu.

Washe gari da safe ya kira Mr S da kansa ya sanar masa yana son zuwa gurin Dad Jeerah.

Mr S da kansa ya aiko driver aka daukosa aka kawosa JEERAHsV.

Kallo daya Dad yayi masa yaji tausayinsa da kaunarsa me tsafta ta shigesa sbd Al'amin jarumin 'da ne kuma jajirtaccen yaya wanda yayi iya kokarinsa da sadaukarwarsa akan ahalinsa amma allah bai basa ikon cimma buri ba yanzu dan haka insha Allah zai zama bangonsa kuma gatansa da zai tabbatarda Al'amin din ya tsayu da kafafunsa dan bawa iyalinsa rayuwar data kamata a gaba batareda saka hannun kowaba.

Bai bari Al'amin din ya fadi maganar datake danne da kirjinsa ba ya bude baki cikin kulawa yace

"Kasani alkwarin danai maka yana nan bazai taba kasa zama ba cikakkeba,
SANAAH zata samu kariyata daga yanzu har ranar da zan bar duniya wannan shine alkwarina,
Nine gatan SANAAH da mahaifiyarka ka saka wannan a ranka kaje ka samu ilimin tsayuwa da kafafunka batareda damuwan komai ba."

Ajiyan zuciya mai sanyi da mutuwan jiki ya sauke tareda bude baki yayi godiya da fatan alkhairi da qarin lafiya da tsawon kwana ga Dad jeerah.

Shi kuwa Mr S a take yafara buga wayar tabbatarda samun gurbin karatun Al'amin din da tini aka samar masa jiran amincewan kadai ake jira.

Koda Al'amin ya tafi gurin Mommy a natse ya zauna cikin sanyi da bayyanarda gamsuwansa yayi musu bayanin komai tareda basu tabbacin hakan shine insha Allah alkhairi da mafitar da suketa roka a gurin Allah.

Mommy da SANAAH sunji shakka da tsoron hakan amma yanda yayi musu bayani da tabbatar musu da zai tsayu insha Allah da kafafunsa ya dawo dasu hannunsa da daraja ya saka su dan sassautowa amma dai sun amince ne bawai dan sun so hakan ba sai dan basa damar yaje ya samu ilimin da wahalarsu ta hanasa samu tintini dan haka suka saddaqar suma zasu tafi sbd ya samu nauyinsu daya maqalesa ya saukar masa.


****Da wannan rayuwarsu su duka ta dauki wata hanyar sabuwar da basu taba tsammani ba ko mafarki sbd rayuwa ce a inda basu taba tsammani ba a cikin wainda basu taba tsammani ba a lokacinda basu taba tsammani ba,

Babban bangare daya dayake dauke da duniyar da basu taba gani ba aka ware musu na zaman dindindin halak malak a cikin JEERAHsV,

Babban palo ne na alfarmar gaske dayake dauke da dakuna uku manya kowanne da toilet dinsa shima babba sai kitchen da dining area da kofar baya da babban balcony na hutawansu,

A cikin bangaren babu abinda ba sabone fil aka zuba ba a cikinsa wanda yake na zallan jin dadin zaman duniya,

Matansa dukansu hankalinsu tashi ya dan yi musamman Hajiyar Samad data saka a kawar dasu a batar dasu shiyasa aka cinnawa gidan wuta sbd suna neman zama kaddarar 'danta wanda a yanzu mahaifinsa ya qara masa iyaka mai karfi akan duk wata dukiyarsa ta Raheem ce kadai yanzu take gatansa da isarsa.

Ganin dawowansu hannun Dad jeerah din da kansa tareda gargadi mai karfi da bada cikakkiyar sanarwar shine uba kuma uwar SANAAH maga isarta sai kowa ya shiga taitaiyinsa tareda mamaki me girma da baqin ciki harma da shakka amma dai babu wanda ya isa motsawa akan hakan tukuna.

Samad jin girmamammen lamarin yayi daga sama saida ya kasa yadda tukuna ya yadda da gaskiyar hakan,

Jin yayi wani irin nauyin dayake kirjinsa ya sauka farin ciki mai tsananin gaske ya cikesa take ya ringa sakawa mahaifinsa albarka dan kuwa SANAAH ta shigo rayuwarsa kenan.

Hajiyarsa tashin hankalinta kashi kashi ne dan kuwa tasan a yanzu da SANAAH ta dawo jeerahs Samad zai iya rasa ransa a kowane lokaci dan kuwa yana kuskaren tabata kila Mahaifinsa ajalinsa zaiyi dan haka duk ta rude ta rasa nutsuwa da sukuni.
#MAMUH
09033181070

GANIN IDO 2026
Mamuhgee

37
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki  Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki  Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce  For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Su mommy kuwa ganin inda suka samu kansu ya sakasu fatar hakan shine alkhairi,
Al'amin ma dashi har cikin bangarensu aka tare dashi kafin ya tashi tafiya karatun da ake hada masa kai tsaye zai wuce a kwanaki kadan.

Mai aiki daya aka basu bangaren wadda zatai hidimar komai na bangaren har dafa abinci wanda shima an cike musu store din dayake lafiyayyan kitchen dinsu da abinci da duk wani abun da zasu buqata naci dana sha da katan katan na ruwa da soft drinks.

Sitirar sakawansu ma sbd magana ce ta kudin da baa san zafinsu ba babu bata lokaci aka tanadar musu sitira da duk abinda akasan zasuyi amfanin dashi.

Mr S ne ya kaisu har bangaren tareda mai aikinsu wadda itace ta shiga har ciki dasu ta gabatar musu da komai a natse da girmamawa.

A palo suka zauna shiru babu wanda ya iya magana tukuna har saida Al'amin yayi karfin halin magana yana boye damuwansa da bayyanarda farin ciki sbd kawai suma su samu kwanciyan hankalin jin dadin yafara yabon Dad din da masa addua yana basu tabbacin a yanxu dukansu zasu samu nutsuwa insha Allah kuma kaman gobe ne zasu ga ya gamo karatunsa ya dawo garesu.

Yanda yake kokarin nuna musu ya sake daga kowace damuwa dan kawai suma su sake din ya sanyasu kawar da damuwa suna nuna masa nutsuwansu da kwanciyan hankalin da zasu samu.

Mai aikinsu da sunanta yake Safiya ta fito daga kitchen ta nufi dakin Mommy ta faro aikinta daga can ta gyara mata duka kayan da aka kawo aka ajiye a kan gado zuwa cikim wardrobe ta jere komai tsaf ta qara gyara dakin ta kunna ac ta fito.

Dakin SANAAH ta nufa wanda shi komai dayake cikinsa na daban ne wanda yake na duka jin dadi da tsarin budurwa mai gata da aji itama kayan ne a aje kan lafiyayyan babban gadonta dayake shirye da tsadaddun beddings ta fara jere mata a wardrobe tana hada kowace riga da gyalenta sbd duka kayan luxury abayas ne kaf masu kyau da rashin hayaniyar ado sai tsada.

Bayan jere kaya turaruka da shoes ne da suma babu abinda akai delay duka an siyosu na amfaninsu da zasu fara kafin idan an nutsu a siya komai akan tsari.

Tana gamawa nan ma tafito lokacin ne SANAAH ta shigo dakin a natse wani sanyayyan sanyin ac ya ratseta ta rufe idanuwanta ahankali sbd har lokacin zazzabi ne a jikinta sosai kuma jiri take gani mai tsananin gaske dan haka daqyar ta isa toilet batareda ta iya tsayawa qarewa dakin kallo ba.

Tana shiga toilet amai me karfi ya kufce mata ta qarasa da sauri tafara yinda a cikin toilet seat tana dafe cikinta dake ciwo sosai.

Sosai tayi aman tana gamawa a galabaice ta zare kayan jikinta ta isa gurin shower ta sakarwa kanta ruwan da batamasan masu zafi ne ta kunnoba sai da suka ringa sauko mata taji dadin hakan ta rufe kyawawan idanuwanta da sukai laushi tana jin ruwan na ratsa fatar jikinta da ita kanta tana buqatan ruwan.

Ta dan jima ciki tukuna ta fito da alwalan sallan laasar da akai tana ciki da jiri har lokacin ta iso tsakiyar dakin daidai nan Safiya ta shigo dauke da tea me zafin gaske dayaji madara sosai ba suga ko kadan ta qaraso ta ajiye akan table.

Bude baki SANAAH tayi cikin rashin kuzari ko kadan tace


"Ki kashe mun Ac banajin dadi sosai"

Cikin kulawa da girmamawa Safiya tace to tana daukan remote ta kashesa tana juyawa ta fice.

Tana fita SANAAH bata iya komaiba sallah tayi daqyar tana gamawa ta zube a gurin dunqule take baccin zazzabin wuya ya dauketa.

Mommy ma wanka tayi mai kyau ta shirya tayi sallah hakama Yaya Al'amin wanda shima hadda shi a kayan sakawan dan haka yayi fes anan yayi sallah bai fita ba sbd baisan koina na cikin villar ba tukuna.

Abinci lafiyayye safiya tayi ta gama bayan magrib tana gamawa ta jera a dining taje har daki ta sanar da mommy,

Basuda zabin daya wuce fitowa cin abincin wanda akai sbd su kawai kuma mai rai da lafiya a tsarin da basu taba cin abinci ba wato kan dining.

Sai a lokacin suka san halin da SANAAH ke ciki dan haka yaya Al'amin dole ya fita a natse da kame kansa sosai tareda bayyanarda irin karfin nutsuwansa ya tafi hanyar zuwa bangaren Dad ya dakata daga waje ya kira mr s a wayarsa cikeda girmamawa ya sanar masa SANAAH ba lafiya sbd baisaniba ko zasu iya tafiya su kaita asibiti.

Mr S baya nan amma saiya kira likita wanda zai taho ya dubata a cikin gidan ba buqatan zuwa kowace asibiti.

A cikin daren kuwa likita mace taxo ta duba SANAAH din tareda bata magani masu kyau bayan tasa ankawowa SANAAH din abinci da tea tasha tukuna tabata magani tasha kafin ta wuce da basu tabbacin gobe zata dawo.

Da damuwan jikin SANAAH suka kwana wadda ta danne damuwan kasancewansu inda suke ganin rayuwar tayi musu nauyin da kaman bazasu iyaba.

Baccin nutsuwa me karfi ne SANAAH tayi a daren wanda yake tattareda kwanciyan hankalin gangar jiki da ruhi dan haka sai latti sosai ta farka a kasalance.

Sallah tayi tareda zaunawa tana adhkar har gari ya qarasa wayewa sosai.

Miqewa tayi sanye da doguwan rigar sallar dake jikinta a natse da sauran rashin karfin jiki sosai ta nufi bedroom din Mommy.

Koda taje itama mommyn tana zaune tana lazimi dan haka ta zauna ta jira tagama tukuna ta gaidata cikin kulawa da kauna.

Amsawa mommyn tayi tana shafa bayanta cikin kulawa da kauna me karfi tana cewa

"Yaya jikinki?
Kin ji sauki sosai?

Lumshe idanuwanta masu kyau tayi tana dan jin jikinta na sake sakewa tace

"Naji sauki kawai rashin karfi sosai nakeji"

Gyara mata rufar kanta tayi tana kallan kyakkyawar fuskanta datai duhu da rama tayi tana cewa

"Shima zai dawo karfin jikin naki indai saukin ya samu"

Yaya Al'amin ne yayi knocking kofar dakin kafin ya bude ya shigo da sallama yana kallansu da kulawa da kauna me karfin shima ya qarasa ya zauna gefen mommyn yana gaidata idonsa akan SANAAH da sai yanzu yake ganin ramarta sosai da duhun datai.

Yaya jikinta ya tambaya bayan ya amsa gaisuwanta.

Maganganunsu sukai na tsawon lokacin daya saka basu samu komawa baccin safe ba saida sukaji shirun yayi musu yawa babu kowa ba motsin komai hakama koina tsit ba wata hayaniya dole kowannensu ya koma ya kwanta baccin

Please Login or Register in order to submit comment