Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Daga airport kai tsaye asalin gidan kakanninsa ya nufa wanda yake na mahaifiyarsa yanzu kuma a ciki yakeda wata kebantacciyar babban bangaren dayake nasa ne komai tsarinsa na turawa da daidai buqatansa ne.

Koda suka iso ansan da yana hanyar zuwa dan haka wangale musu gate akai motoci biyu da suka daukosu suka shige babban gate din gidan suna parkawa a natse Imran ya fito ya bude masa kofa da kulawa da qatuwar ipad dinsa a hannunsa da bai taba rabuwa da itaba matiqar yana tareda fleet sbd baya bata kowace lokaci akan duk abinda zai taso.

Fitowa yayi sanye da Designers riga da wando masu kauri oversized na Prada da black fcap data rufe fuskansa gashinsa ya fita ta baya tamkar sabon matashin dayake early 30s dinsa dan kuwa ko jikin da fuskan babu inda alaman dayake nuna yana budurwar yar datake likita.

Securities da masu aikin gidan kaf haka suka jeru a harabar suna masa barka da isowa cikin girmamawa da rashin rawar jikin dazata bada hayaniya.

Kai tsaye bangarensa Imran ya bada umarnin aka kai kayansa suka wuce nasu masaukin banda Imran din da saida ya gama tsara komai na bangaren da yanda zai buqaci komai nasa tukuna ya fice yabarsa ya huta.

Sai daya huta yanda ya kamata bayan yayi wanka sai yamma ya fito lokacin sallar magrib sbd kusan su Dr Mum basa gidan koda ya iso dan haka koda suka dawo kuma yana hutawa baa sanar dashi ba sai yammar daya fito da kansa.

Kai tsaye bangaren kakansa da shima sai yammar aka dawo dashi daga babban masalaccin dayake zuwa ya wuni a gurin sauraron lectures ta addini sbd ya rage zaman kadaici wasu lokutan ba kullum ba sbd Nasir kusan shine abokin rayuwarsa a komai tinda Nasir ya tafi shikenan ya rasa kusan fiyeda rabin walwalansa na samun abokin fira da mai kulawa dashi yanda ya kama sbd yarsa mace ce sai daga baya aka dauko masa 'dan kanwarsa shima yanada kokarin kulawa dashi da nuna masa tattali da kauna amma ya kasa dena kewa rashin Nasir yau din.

Yana shiga palon Abbun yana zaune da glass dinsa mai qara gani farin tsoho mai farar zuciya da tawakkali da kaunar ahalinsa,

Yana ganin Raheem ya sake murmushi yana sake dubawa dakyau yaga Raheem dinne dai da gaske dan haka ya sake fitarda walwalansa yana bude baki yace

"Fleet of the US navy marhba bik,Nawwart lina dar"

Qarasowa yayi da wata lafiyayyar murmushi mai tsananin kyau da bayyanarda dukkanin sukuni da sakewa da kaunar datake tsakaninsa da Abbu shi kadai a rayuwarsa bayan Nasir ya qaraso ya zauna gabansa yana bude baki da sautinsa mai nuna zamansa namijin gaske da yaren larabcin Morocco yace

"Shoukran,Barak Allah oufik ya jed"

Hannu Abbun ya miqa masa cikeda kulawa da basa girmamawan dayake basa abarsa
Kama hannun Abbun Fleet yayi tareda gaisawa dashi a cikin turanci kuma tukuna yakai hannun bakinsa yayi kissing cikeda kauna da girmamawa da al'adarsu take tukuna ya dago yana kallansa yace

"Kana nan kana zuwa Islamic lectures dinka kenan"

Murmushi yakeyi yana gyara zaman glasses dinsa ya gyada kai yana cewa

"Yaya gida?ya aikinka and your family?

"Duka suna lfy,but fammah na Nigeria daga can nake tace zata zauna na dan kwanaki kafin ta koma America"

"Masha Allah hakan is very very right,
Ya kamata tasan familyn Dad dinta sbd by now ma yakamata ku gyara muaamalanku da mutanen Nigeria ku kama zumunci sbd komai na duniyar ba komai bane ko baa kusa idan ana zumunci kona waya me zuciya zata saku sukuni"

Cikin nutsuwa Fleet ya dan jinjina kai yana cewa

"Yeah insha Allah zamuci gaba da kokarin gyarawan"

"Maamanka ta sanar dani kwanakin baya cewan an baka wata matar acan Nigeria harma an daura aure ko?
Allah ya sanya alkhairi ya bada albarka mara yankewa a rayuwanku ya hada kanku ku dika ya qarawa familynka yawa da farin ciki"

Dago fararen idanuwansa yayi ya kalli Abbun adduoinsa na sauka a kunnuwansa yana jinsu kaman wani lamari mai nauyi sbd shine na farko dayayi maganar auren da zuciyar datake a tsarkake daga kowace irin tinani da manufa,

Ko mahaifinsa bai masa irin wannan adduoin ba akan auren sedai juyasa dayake da manufofi da dama.

A tsanake ya furtawa Abbu "Amin" a taqaice sbd baisan me zai fada ba hakama bayajin akwai wanda zai iya tsayawa yiwa bayanin komai akan auren yanzu sbd baida kowace maganan komai akan matsayi da auren dayake dashi yanzu,
Bazai kuma bawa kowa daman shiga maganarba harsai lokacinda zuciyarsa ta tsayar da bayani daya akan auren da matsayinsa a gurinsa shi dayake riqe da auren.

Bai fadawa Abbu wacece Aka daura auren da itaba sbd duka bai shirya kowace hayaniyar raayin kowa akai ba zai bawa komai lokaci tukuna dan haka suka fara firarsu har saida sukai sallah suka gama tukuna ya isa cikin gida gurin iyayensa mata wainda sunji isowansa tasa.

A babban palon ciki ya tadda Maamah tana zaune tana duba wayarta da alama waya ta gama yana ganinta yaji nutsuwansa ta sake qaruwa sbd bai taba hada kaunarta da girmanta da wasu abubuwanba da dama,

Ba itace ta haifesaba amma itace uwar data shayar dashi ta basa kaunarta da rayuwarta dan haka kowa ya sheda ya sani kaunarta da matsayinta a gurinsa daban ne.

Takowa yayi ya qaraso cikin gabaki daya wanda qamshinsa daya fara kauwa qamshin palon yana maye gurbi ya sakata dagowa tana kallansa a tsanake da wata irin kauna mai tsananin karfi da kulawa tareda kewa fuskanta na cikewa da farin ciki da murmushi da walwala ta bude baki tana ambatar sunansa da cewa

"ABDULRAHEEM"

Shi kansa murmushinsa mai kyau ne ya gauraye kyakkyawar fuskansa datake dauke da haiba ya qaraso har gabanta ya zauna a natse tareda bude baki yace

"Ya Maamah"

"Ya hanya?
Kun iso lafiya ko?
Yasu Hajiya meenah?
Yaya fammah?
Kana lafiya??

Duka tambayoyinta cikeda kulawa da sakewa da farin ciki ta jero masa su tana ajiye wayarta gefe.

Da kwanciyan hankali da farin cikin kasancewa da ita ya fara bata amsar kowace tambayarta a natse da turanci kafin ya dora da cewa

"Fammah kuma tana Nigeria ba yanxu xata koma ba sai daga baya insha Allah"

Kallansa Maamah tayi da mamaki tace

"Nigeria kuma?
Zata iya zama ne acan din batareda ta saba da kowaba?

Dr Mum ce ta fito daga bedroom dinta sanye da wata maroon luxury Abayar da kana kallo kasan sai masu arziki ne ke iya sakata a qasar ma dan kuwa babu kowace hayaniya a jikinta zallan black sequence ne a jikinta da suka qarawa rigar nutsuwa ta zaunu a jikinta da fatarta datake fara qal har tana daukan ido ta manyanta amma kuma tanada sauran kyanta sosai da sosai sbd bazaka ma ce itace ta haifi Fleet ba duk da shima kusan kyan jikinta ne ya dauko sam babu kowace manyanci tattare da jikinsa da fatarsa.

Fuskanta a daure take babu kowace sakewa ko wasa a cikinta wanda wannan halin nata shine halinta da bai taba sauyawa tin kuruciyarta wato rashin yadda da kowace raini ko laifi,bata iya boye bacin ranta ko kadan idan aka tabata ko yi mata laifin daya tabata sosai dan hakane tin ranar da sakon aurensa ya isa kunnuwanta take cikin bacin rai da fushi sosai kawai ta danne ne sbd babu wanda zata saukewa a kusa amma ranta yayi mummunan baci da daukan zafin da ace har Raheem zai qara aure kokuma mahaifinsa zai qara masa wata matar tsawon shekaru amma bai sanar mata ba kila ma harya karba auren yana rayuwa da wata macen batareda sanin su ahalinsa ba,

Kenan itama matarsa datake amana a gurinta tin kafin rasuwar mahaifiyarta ta damqa mata ita amana kuma ta amsa amma gashinan zaa maimaita mata abinda ita akai mata a lokacin nata auren wato auren cin amana dan haka bazata taba yadda ba ko hakan na nufin ta fuskanci Hakeem ne tinda tayi imanin da gangan yayi amma kafin Hakeem Fleet ne zai fara fuskantar bacin ranta.

Tana shigowa palon ya dago kansa a natse ya kalleta ya dauke kansa a tsanake yana kamewa sbd da dukkanin girmansa sbd daman a cikin iyayensa babu wanda yakeda kyakkyawar sakewa dashi ko walwala sosai koyaushe girmamawan ce kawai sai umarni.

Maamah kallan Dr Mum din tayi tana fatan kada ta bawa Fleet kowace irin damuwa tinda dai anriga anyi ko yayane hakuri zaayi indai ba shine da kansa yayi raayin rabuwa da aurenba ya sawwake,
Ita Hajiya Meenah ma take tausayi sbd itace ta gama yadda da har abada babu kowace macen da zata shigo gidanta kuma suma duk sun saka ran hakan amma sai ga wannan tashin hankalin kwatsam ya sauko wanda ya dawo musu da ciwon abinda akaiwa Fammah din a baya.

Zaunawa tayi tana kallansa ta bude baki da mamakinta dayake hade da dacin zuciya tace

"Fammah naji kaman ana cewa tana ina???

Maamah ce ta bata amsa da cewa

"Tana Nigeria,nima mamaki nakeyi ta yanda zata iya zama a cikinsu"

Cikin tsanaki da kwanciyan hankali da kamewa yace

"Barka da fitowa Dr Mum,
Mun sameku lafiya?
Allah ya qara lafiya da nisan kwana"

Bata iya amsa gaisuwansaba duka idanuwanta na kansa tace

"Me famman ta tsaya yi a Nigeria?
Akwai dalilin daya sakata tafiya ne?

Kasancewansa ya saba kuma tasa rayuwar daban take yanada nasa akidar da tsarin maana nasa principles din da baitaba sauyasu akan kowaba harda iyayensa dan haka dan kai tsaye ne babu boyo a lamarinsa kai tsaye yake sbd iko da powern data shigesa hakama baya bayani wa kowa idan ba shine yayi raayi ko ga daman hakan ba shiyasa kaf duniya duk wanda ya tambeyasa har iyayensa suka bai bada amsa ba ya yanke zancen to hakura kakeyi ka tsaya iya nan.
Dan hakanne yake kowace maganarsa da rayuwarsa a tsanake da kwanciyan hankalin da babu hayaniya a ciki sbd rayuwar hayaniyarsa da karajinsa suna a fagen aikinsa ne.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

52
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
A natse da bata girmanta ya bude baki yace

"Daga Nigeria din nake shine ta buqaci abarta can tukuna tana son sake sabawa da mutanen can"

Shiru daga Maamah har Dr Mum sukai sbd mamakin daya sake shigarsu mai girma Dr Mum tace

"Kana Nigeria kenan duk satikan nan?"

"Naam" ya bata amsa a taqaice wadda ta sake sakata shiga mutuwan jiki da tsoro mai tsanani sbd barin fammah ma acan yana nufin komawansa Nigeria guarantee ce.

Rasa cewa komai tayi sbd abinda take hangowa daga kamalansa ma na baya buqatan kowace hayaniya akan komai daya shafi Nigeria.

Wani nauyi ne ya sake danne kirjinta tanajin kila harta mutu Hakeem bazai taba barin ta warke daga abinda yayi mata ba tin tana matashiyarta haryanzu.

Numfashi mai zafi ta fidda wanda yake tattare da damuwa da nauyin zuciya tace

"Nasan kasan zuwa yanzu duk munsan da maganar auren da kake dashi na biyu,
Tambayata ta farko anan itace matarka tasan da hakan?
Idan bata saniba inason kafin ta sani kasan matakin da zaka dauka akan auren kafin kowace damuwa ko fitinar ta taso"

Maamah kallan Dr Mum din tayi tana buqatan sassauci a zancen nata kafin ta maida kallanta kan Fleet wanda babu kowace yanayi a tattare dashi dazai bayyanarda halinda ya shiga najin maganarta mai kama da umarnin sawwake auren.

Dago idanuwansa masu haske yayi bayan dan seconds daya bata na sauke kalamanta ya bude baki yace

"Dr Meenah batasan da maganar auren ba sbd banbawa auren kowace irin mahimmanci ba da time shiyasa ba buqatan ta sani sbd kwanciyan hankalinmu duka amma a yanzu zata iya sani sbd Auren bame warware bane a yanxu"

Da wata irin shock mai karfin gaske daya dakesu su biyun suka kallesa Maamah na cewa

"Daman Saki a auren da bai wani jimaba babu amfani gwara a nutsu a duba"

Dr Mum kuwa jin tayi bakinta ya kasa furta komai sbd kai tsaye yanke kowace magana ce Raheem yayi akan auren.

Ya karbi auren kenan ko me??
Hakeem ya samu abinda yakeso kenan na nuna mata isa da iko ko me?
Ana nufin Meenah wahab kishiyar da basa rayuwa da ita zatai kokuwa itama akan hakan aurenta zai iya zamowa tarihi kamar ita?
Raheem irin abinda Mahaifinsa yayi mata zaiwa tasa matar ta rabu dashi kenan?
Ita tayi karfi da taurin zuciyar zabar rabuwa da hakeem,Meenah wahab bazata iya hakanba dan kuwa zata iya kashe kanta ko Raheem dinma akan ta rasashi ta barwa wata dan haka sam bazata yadda mummunan tarihi ya maimaita kansa ba.

Bata sake cewa komaiba ta shiga tinani mai zurfi dayake cikeda da rashin nutsuwan zuciya da tashin hankali gashi a yanda Raheem din ya yanke maganar idan tace ta bayyanarda nata tashin hankalin mai zafi hayaniyar dazata saka Meenah ta sani ce kawai zata tashi wadda batama son hakan sbd bata kaunar ko kusa meenah ma tasan da maganar yanxu dan itama sbd tana yiwa Raheem tsananin son datasan duk duniya babu macen da zata sosa kaman hakan sedai sbd dukiyarsa da matsayinsa dana familynsa hakama a yanzu daya kai wannan matsayi da girman me zaiyi da wani aure.

Maamah kuwa kokarin jansa da wata maganar tayi sbd ragewa tension din gurin nauyi tana sakewa da kulawa.

Dining tayi umarnin aka hada musu suyi dinner tareda shi sbd suna hakan indai yana qasar ba ruwansu wayewa da ilimi ya ratsa su duka.

Sai bayan ishai sikai dinner hadda Abbu dukansu kuma ko a lokacin saida Dr Mum ta tada maganar auren sbd Abbu ya saka baki amma yanda Fleet din yakame sosai babu kowace walwal ko sakewa a fuskansa da yanayinsa ya saka kowa ya kasa cigaba da maganar Dr Mum ta sake shiga tashin hankali da mamakin me hakan yake nufi kenan.

Washe gari bayan lokacin tashinsa yayi ya tashi yayi wanka da duka abubuwan dayake yi ya fito guraren 11 ya isa bangaren Abbu ya fara gaisawa dashi kafin ya isa gurin su Maamah ya gaidasu babu wanda ya sake kowace maganar data shafi yan Nigeria ma ya fita.

Bai dawoba sai dare ya fita da Abbu zuwa duba businesses dinsa da akeyi a qasar shima na dukiyar daya ware ta harkar zinari,

Da daddaren babu wanda ya gansa sai washe gari.

Maamah ce take kulawa da cinsa da shansa matiqar yana gari duk da yanxi ba itace take aikin komaiba masu aiki keyi kawai dai itace ke bada umarnin komai dan Dr Mum bata wani zama gida kaman ita tana can gurin harkar likitoci dan ita yanzu sun zama manyan da ake komai na harkar qwararrin manyan masana lafiya dasu.

Kwanaki kadan yayi a qasar ya bar qasar wanda ya saka duka iyayen nasa shiga shakkar komaima sbd hakan da yayi shine yake nuna iya girman iyakar dayake son yayi akan zancen auren ga kowa dan haka Maamah ta sauko tareda aje komai ta koma adduar Allah yasa auren nan shine mafi girman alkhairi a rayuwarsa ya kuma kawar da kowace damuwa da tashin hankali da duk zai biyo baya dan kuwa akwaisa duk ranar da matarsa da 'yarsa suka sani.

Dr Mum kuwa duk abinda ya faru shekara da shekaru dawo mata sabo yayi kuncinta da baqin cikinta suka dawo suka ninku sbd wannan abin da Hakeem yayi mata shine karshen baqin cikin dazai mata na janye danta daga gareta ya maidasa Qasarsa cikin hikima hankali kwance.

Daga nan America ya koma dan yana buqatan hutu daga duk wannan tashe tashen hankalin da zaa fara sbd a yanzu abunda ya sani shine wulaqanta wannan auren da zaayi shine zaaga mummunan bacin ran Dad hakama shi kansa yana cikin wani matsatsen daurin da bazai taba iya wulaqanta macen datake zuciyar dan uwansaba ga kuma Dr Mum da itama ya sani bazata taba karban aurenba hakama bazata taba iya saukowaba idan ba sakin auren akai ba sbd batasan wacece matar ba, ga bangaren daya Matarsa da itama yake jin girman sonta da bazai iya hada kaunarta da kowace macen ba kuma bayason hayaniya ko damuwa a gidansa dan hakan baya buqatan tasan komai a yanxu dazai hanasu sukuninsu.

Wannan tinanin da dalilan ya saka ya daukewa kowa wuta har Dad din akan maganar auren ya hana kowa shiga maganar ya barwa kansa komai sbd shine dai mai auren dan haka shine zaisan menene matsayin auren a gurinsa da ita wadda auren yake kanta.

Da wannan duka iyayen da kowama ya danne duk abinda yakeji suka kasa magana da fahimtar ana kokarin kaisa maqurar da kowa bazaiji dadiba.

Ms Meenah da batasan abinda yake faruwa ba sabuwar duniya ta bude ta wata irin soyayya mai zafi ga mijinta wanda tinda ya dawo still hutu yakeyi baya fita koina Imran yayi clearing schedules dinsu na kusan sati hudu dan haka duka masu tsananin son ganinsa Imran suke gani sun ma kasa gane a wace qasar yake yana America ko baya nan sbd babu me iya sanin ina yake idan ba Imran ne yaso ba.

Hutu mai nutsuwa da kwanciyan hankali yakeyi tareda matarsa datake sake jin Raheem jeerah shine rayuwarta da ruhinta da har abada babu namijin dayake da darajarsa a rayuwarta.

Ako yaushe yana kokarin bawa Matarsa daman mallakarsa yanda takeso da bata gamsuwan data riga ta zama Obsessed shiyasa ko kallansa tayi jin takeyi tana sake mutuwa akansa.

A bangare daya kuwa sosai yanzu ta saba dasu mommy da SANAAH sbd Fammah da kullum saisun dauki lokaci suna waya da juna harma da videocall daya saka tasan kamanninsu Musamman SANAAH da ita kanta take yabon kyanta.

Fammah ko Dad dinta babu ranar da bata kiransa tana gaishesa suyi magana sosai amma shi sedai yace yana gaida mommy amma bai tana magana da mommynba awaya bare SANAAH da bata taba damuwa ko bawa lamarin da duk ya shafesa mahimmanci ba dan a ynzu data zama kaman rabin jikin Fammah har abada basa fatar abinda zai shiga tsananinsu dan kuwa lokaci ya tafi sosai sun samu wtaa irin zazzafan shaquwa da kauna mai tsananin da sukewa juna data kasance suna jinsu kaman twins hakama sukejinsu kaman jini daya dan kuwa kusan a yanzu hatta komai nasu iri daya ne sedai kaloli su dan banbanta wanda suma kalolin kayansu da komai nasu basa wuce brown,coffee brown ko Nude kala,

Irin kauna da kusancin dayake tsakaninsu y saka zuwa yanzu babu abinda basu saniba na rayuwar juna wanda gane wacece SANAAH ya saka kaunar da Fammah ke mata qaruwa sosai hakama Ms Meenah tana gane wacece SANAAH ta sake jin nutsuwa da jin dadi alaqarsu da kusanci sosai da Fammah,

Ata kowace bangaren rayuwar luxury suke zubawa cikin zallan gata sbd Dad jeerah kudi sosai ya sakar masu hakama Fleet kudinne yake sako musu,

Mommy kam daman tini ta bawa fammah matsayin da SANAAH take dashi a gurinta babu abinda take nuna mata bayan kauna da kulawa ga yaya Al'amin ma shima ya hadasu sun zama kannensa dayake tsananin ji dasu musamman dayake fammah tafi SANAAH shagwaba sai zamana tana samun kulawa sosai daga garesa fiyeda SANAAH.

Matan gidan su Hajiyar Samad ikon Allah datake gani ya saka ta kusan zarewa abin duniya ya isheta ya sha mata kai jin takeyi kaman zatai zangai sbd son Fammah tasan da wainda take zaune amma tsoron Dad ya hanata magantuwa gashi a yanzu da suka zama aminan juna babu abinda zaka taba iya fada ka sakasu jin tsanar juna a duniya.

Fammah cikin dan lokaci ta koyi abubuwa da dama na al'ada da rayuwan Nigeria duk da su suna rayuwa ne daidai da kaman baa Nigeria din suke ba amma ta samu sauyi sosai a rayuwanta kuma taji dadin hakan musamman da suka samu shiga wasu classes na bayar da qarin ilimin addinin da Yaya Al'amin ya sakasu shiga kuma dad yaji dadin hakan hakama akwai bangaren iyaye da tsofi mata sai suka shiga hadda Mommy 2 hrs ne kullum dan haka sai suke samun rayuwa na tafiya yanda sukeso ga wata tsadaddiyar culinary school da suka shiga sbd dukansu ba wani lafiyayyan girki suka iya ba har gwara SANAAH ta iya irin girkinsu na baya.

***lokaci yayi jan da ake maganar shekara dan haka ya shirya tahowa Nigeria kai tsaye Ms Meenah ta yanke shawarar binsa ta koma Nigeria din itama da zama na dan lokaci tinda yanzu sunada wainda suke kalla matsayin yan uwa dan haka ta nace da rokonsa sbd sam baida raayin zamanta a Nigeria amma ta dage dan haka ya barta sbd baya buqatan hayaniya akan zancen hakama zuwan da ita zai hana mahaifinsa bawa wancan auren daman kebancewa ko wata maganar.
#MAMUH
09033181070
INSHA ALLAH ZAMU GWADA POSTING WEEKENDS MU GANIGANIN IDO 2026
Mamuhgee

53
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki  Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki  Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce  For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Ms Meenah bata samun kanta da farin da tsabanin dokin zuwa Nigeria ba sai yanzu datake jin ta matsu ta isa itama ta zauna cikin dangin Jeerahs duniyar Nigeria taga itace matar mutumin da kowa yake son gani,
Aga matar da itace takeda Fleet Raheem jeerah wanda duka mata bazasu samu ba hakama a kaf ahalin jeerah babu kamar

Please Login or Register in order to submit comment