Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga jikinsa ta fice sbd batason SANAAH ta fito ta tadda ita dan bata son ganinta a yanxu tukuna sedai zuwa gaba kila.

Tana ficewa kai tsaye gurin Dad jeerah ta nufa wanda shima tana shigowa kallo daya yayi mata yaji tausayinta da danne wani irin tsananin zafin mahaifiyarta dayake ji dan kuwa badan Fammah din ba kaf duniya baiga wanda zai sakasa ragawa Meenah ba wadda ya danne bacin ransa mai tsanani ya miqata a duba kwakwalwanta dan kuwa hukuncin doka yaso ta karba na rayukan dataso dauka amma sbd barin lamarin a cikin gida kada ya fita ya sakasa riqe kansa ya tsaya a hakan amma akwai hukunci daya da bazata wucesa ba shine barin masa gida matiqar lafiyarta kalau.

Numfashi ya sauke ya kalli famman ya bude baki yafara da mata bata hakuri tareda mata wata nasiha da sanar da ita daga SANAAH har Raheem babu me laifi sbd shine ya daura musu auren batareda yadda ko izininsu ba sama da shekaru ma kowa yaso a raba auren wanda shine asalin zuwan Dr qasar datai alkawarin bazata taba sake takowaba amma sbd Meenah da kwatar mata aurenta daga wata macen ta tako qasar amma Meenah bata duba itace ta haifar mata mijin ba kuma bata duba kaunar data nuna mata ba ta cinnawa matar wuta.

Shiru Fammah tayi idanuwanta jajir sbd kukan ma ya dena zuwa kwata kwata tana jin maganganunsa da suka sake sakata jin rayuwarta na duhu sosai duhun datake buqatan tafiya daga tsakiyar iyayenta da bazata iya kallansu suna sake zama abinda bazazu taba komawa kaman baya ba har abada.

Dago jajayen idanuwanta da suka bushe tayi ta sanar dashi tana son tafiya hutu koma ina ne kafin ta samu warwarewan kanta ta dawo daidai da kowa musamman SANAAH da ayanzu ko kallan juna bazasu iya ba.

Yayi naam da hakan shima kai tsaye sbd tabbas bazaiso ta ringa ganin abinda yake faruwan ba a tsakanin iyayenta da haukar da mahaifiyarta keyi da kuma hukuncin da zasu iya dauka akan hakan dan haka kai tsaye ya yanke shawarar turata Italy gurin AL'AMIN wanda ya zama dan qasar yanzu taje can zau kula da ita kafin komai ya lafa.

Numfashi ta sauke ahankali tana aminta da hakan tareda masa godia ahankali kafin ta rokarwa Mum dinta sassauci da kuma rokon alfarmar ya kira a bata daman ganin mahaifiyarta idan taje.

Bayani yai mata na cewan bazata taba ganin Meenah dinba sai zuwa jibi idan angama binciken lafiyarta an tabbatarda batada kowace matsalar kwakwalwa gida zaa dawo da ita da kansu dan haka tayi hakuri sbd itama zata samu nutsuwa idan ta tabbatarda matakin da lafiyar mahaifiyar taya yake.

Da wannan sukai sallama ta fito ta shige dakinta ta rufe kanta bata fito ba sai dare da Mommy taje da kanta ta sake bata hakuri da rarrashinta ta fito da ita ta kawo mata abinci da kanta ta bata taci kadan safiya ma tana tareda ita a lokacin suka dan zauna da ita har dare sosai tukuna suka barta ta kwanta.
#MAMUH
09033181070

127
Ita kanta SANAAH cak din data tsaya kasa motsawa tayi sbd Yaya Al'amin dinta duk da tana ganinsa koyaushe a waya suna vidcall a zahiri yayi mata sauyawan da kwakwalwanta ta kasa dauka dan haka ta sake bude baki da sautin daya isa kunnensa daga inda yake tsaye ta ambaci sunansa da tsantsar mamakinda jikinta yake sakewa.

Juyowa yayi gurin dayaji sautin muryan da shima mamakin ne a fuskansa idanuwansa suka sauka akansu su dukan take wani kyakkyawan murmushi ya sauka a fuskansa yana gaurayewa cikin nutsuwa da asalin farin ciki kafin ya tsayar da idanuwansa akanta wadda tini idanuwanta duka ciko da wasu hawaye ya tako zuwa gurinsu yana zare hannuwansa dake aljihunsa ya ware mata hannu ta tafi da gudu ta fada kaman wata baby yana rungumeta itama ta qaqamesa hawayenta na farin ciki na gangarowa tace

"Ya Al'amin" da wata sanyayyar muryan da Fleet yajita ta ratsesa ahankali ya dan dauke idanuwansa daga kansu yana maida akan Fammah wadda itama ahankali ta dauke nata idanuwanta da suke kan Al'amin din tin dazun tana dan kallan Dad dinta ahankali wanda ya dan sake matse hannunta dake cikin nasa yana sakar mata murmushi mai kyau da tsari wanda ya manta rabon daya fito daga fuskansa sbd tashin hankalin da aketa fama dashi a kwanakin.

Ita kanta ahankali ta dan sake murmushin karfin hali suna takowa suka isa gurinsu Al'amin din ya saketa ahankali yana maidata gefen jikinsa ya kalli Fleet da girmamawa sosai da sakewa tareda nutsuwa da wayewa da murmushi akan kyakkyawar fuskansa datake sak data SANAAH yace

"Bansan gabaki dayanku kuke ba,welcome to Italy Fleet"

Cikin basa sakewa da aikata abinda musulunci yace fleet din ya miqa masa hannu a tsanake yana kallansa yace

"Thank you Mr Al'amin"

Hannu Al'amin din ya miqa masa sukai sallama yana kara masa barka da zuwa qasar kafin ya kalli Imran ya miqa masa hannu shima suka gaisa a sake da tsantsar ilimi da nutsuwa.

Fammah ya kalla wadda ta dan sauke kanta daga kallansa tana dan sake dagowa suka kalli juna ya sake mata murmushi mai kyau da sakewa tareda kulawa sosai yace

"Rabin Ran SANAAH barka da zuwa ko?

Murmushin karfin hali tayi tareda dan kallan SANAAH din wadda itama ita ta zubawa ido tana kalla tukuna ta maida kallanta kan Al'amin din ta bude baki tace

"Thank you Yaya Al'amin"

Juyawa sukai gabaki dayansu zuwa mota Fleet ya kalli SANAAH wadda take ta shiga farin ciki sosai tana mantawa da duka damuwa da quncinta tanata faraa da murmushin haduwa da dan uwanta kuma ubanta Al'amin.

Wani sanyi shima yaji ya ratsesa na ganin sauyawanta zuwa farin ciki sosai dan haka dan murmushin da bai fitoba ya sake yana miqa hannunsa ya kama nata ahankali suna tafiyar ta juyo ta kallesa da idanuwanta dake cikeda farin ciki ta sakar masa wata murmushi me kyau tana bude baki kadan tace

"Fammah na kusa fa"

Famman ya kalla wadda take gefen Al'amin ana isowa gurin motocin kai tsaye ta Al'amin din ta nufa wadda kuwa ya bude mata gaban motar da kansa ta shiga ya rife yana juyowa yaga SANAAH ta dan tsaya tana dan kallan motar sbd fammah data shiga idan ta shiga ciki zasu iya komawa yanayinsu dan haka ta dan sake murmushin karfin hali tana basarwa daman Fleet bai sake hannunta ba har lokacin dan haka ta juya suka shiga tasa motar da zata daukesa wadda tini Imran ya bude musu kofa dan haka suna shiga Al'amin ya shiga shima ya tayar baya suka bar Airport din yana wucewa gaba sbd zuwa gidan daya tanadarwa fammah na zamanta wanda a guri daya yake hade da gidansa sedai kowa da bangarensa da kuma kofarsa daban sedai main gate dinsu daya ne.

Baa nan yake ba amma sbd zama a kusa da duk inda zai ajeta dan bata tsaro da kariya ya saka ya siya sabon gidan ya dawo nan kuma komai an tanadar mata an tsarar mata hatta maid da zata tayata zama ya tanadar mata duk da fita zata ringa yi wani program class da aka neman mata da zai hanata shiga damuwa da kadaici.

Tafiya me dan tsayi sukai kafin suka iso gidan da remote ta bude qaramin gate din daya bude suka shiga da motocinsu sukai parking.

Fleet bai fito ba sbd nasa masaukin zai wuce sedai ya kalli SANAAH wadda duka alamanta sun nuna anan takeson sauka tareda yayanta da fammah da ko yayane takeson su samu kasancewa su kadai ko matsalarsu zata qare dan haka itama da idanuwanta da suka dan marairaice ta kallesa tana nun alaman yabarta anan din.

Sakin hannunta yayi tareda kallanta da ido ya mata alaman its ok zata iya sauka anan din dan haka ta sake murmushi me kyau tana bude kofar ta fito.

Fammah ce itama ta fito mota ta nufo motar Dad din sukai bankwana kafin ya sake shigowa dubasu aka ja motocin suka fice.

Su kuwa kai tsaye maid din fammah dince ta fito mai dan duhu da ita ta iso ta fara daukan kayan bayan ta musu sannu da zuwa cikin girmamawa.

Bangaren fammah din suka nufa gabaki dayansu SANAAH na magana da Al'amin suna daga baya tana jin kaman zatai zamanta itama gurinsa sbd mantawa da gudowa tashe tashen hankalin dayake can amma tasan Fleet bazai bari ba.

Suna shigowa cikin palon wanda komai nasa yake da tsari mai kyau da burgewa da rashin hayaniya wanda yayi komai daidai da abinda famman ke so sai kamshi mai sanyi da sanyin aircon ke tashi anan Al'amin din ya dakata yana cewa su huta tukuna zuwa anjima zai dawo.

Kallan fammah yayi wadda ke kokarin isa bedroom din da Ana ta shige da kayanta ya ambaci sunanta yana kallanta da kulawa yace

"Sai anjima ko"

Dan juyowa tayi kadan ta kallesa da idanuwanta kafin ta bude baki tana kokarin sake fuska tace

"Ok Ya Al'amin see you"

Shigewa tayi shima ya shafa fuskan SANAAH din ya juya ya fice yana fiddo wayarsa daga aljihunsa datake ringing.

SANAAH ajiyan zuciya ta sauke tana isa kofar dayan dakin zata shiga sai kuma ta hana zuciyarta hakan ta fasa ta sakawa kanta karfin zuciya ta koma dakin da fammah take ta shiga sbd ta yanke shawaran zama daki daya da famman kaman yanda suka saba sbd dawo da kusancinsu.

Tana shiga famman juyowa tayi ta kalleta da dan mamaki amma ganin SANAAH din taqi kallanta tana isowa ta zauna ahankali tareda ajiye jakar hannunta tana dan dagowa zata kalli fammah din tayi saurin dauke kanta daga kallanta tana wucewa bathroom batareda tace mata komaiba.

Tana shigewa SANAAH ta sauke dan numfashi itama tana miqewa ta fara rage kayan jikinta.

Fammah ta jima a ciki kafin ta fito daure da towel daya daga cikin sabbin towels din da aka jere reras a bathroom din ta wuce mirror kai tsaye.

SANAAH ma miqewa tayi tafada bathroom din tayo wankanta a natse da ruwan zafi masu dan zafi sosai tana fitowa har famman ta shirya tana sallah.

Itama shiryawa tayi ta tayar da sallan tana idarwa kai tsaye ta haye gado ta kwanta bacci mai karfi ya dauketa dan batajin wata yunwa.

Fammah kuwa abinci ta fita ta dan ci kafin ta dawo bata nemi kunna wayarta ba dan tana buqatan layi hakama ko tanada shi batajin zata fara amfani da waya sosai sbd batason kira daga kowa peace takeso tukuna.

Itama hakanan dole taje dakin ta kwanta a dayan gefen gadon take bacci ya dauketa mai karfi wanda batai tsammanin zai taho mata ba sam.

Sun jima suna baccin basu karfka ba sai dare sosai lokacin har Al'amin yazo yaji suna bacci a bakin Ana sai yace abarsu su huta sai safe ya tafiyarsa bayan ya kawo musu tarin sabbin fruits an saka a fridge.

Sallah sukai kusan a tare duk da basawa juna magana suna gamawa SANAAH ce tafara fitowa ta isa kitchen ta samu abinci bata wani ci ba sbd dare ne sosai komawa zatai ta kwanta dan haka fruits taci sosai kafin tasha ruwa taje ta sake kwantawa.

Itama fammah abinda SANAAH din taci shi taci ta koma ta kwanta.

Sunyi lattin tashi da Asuba dan haka SANAAH data fara tashi itace ta tada famman.

Suna sallah basu koma bacci ba SANAAH taso suyi magana amma fammah ta kasa iya hakan dan haka sai bata takura ba ta fito dakin tabarta ta nufi dayan dakin ta dauko kayanta ta kawo dakin ta aje itama kaman yanda suke a baya.

Karfe 9 na safe dukansu suka fito a shirye kuma daidai lokacin ne aka gama hada musu dan simple breakfast wanda suka zauna dole a tare sukaci suna gamawa saiga Ya Al'amin din ya shigo sanye da wasu fararen Armanis da fcap wadda da alama ya saba da ita a kowace shiyarsa qamshinsa mai aji da nutsuwa yana ratsa palon ahankali zuwa koina fuskansa datake tsantsar kyau da hutu dauke da murmushi mai kyau ya kalli SANAAH wadda tana ganinsa farin cikinta ya bayyana ya miqa mata hannu suka gaisa tana qin sakinsa ya kalli Fammah wadda ta dago a natse ta kallesa ta bude baki tace

"Good morning Ya Al'amin"

"Morning doc kin tashi lfy?
Ya bakunta?

Sunan daya kirata dashi din ya sakata sake dagowa ta kallesa da wani sanyi kafin ta bude baki tana dan murmushi kadan tace

"Alhamdllh"

Zaunawa yayi a natse yana tambayarsu idan akwai abinda bai musu ba musamman fammah da aka tanadi koman sbd ita.

Gyada kai tayi tana cewa komai ya mata a cikin kama kai da rashin son shiga huruminsa da SANAAH dan ko ba komai sunyi dadewan da zasu so time din kansu.
#MAMUH
09033181070
[19/06, 1:51 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

128
Fira suka fara mai tsananin zurfi da tsantsar kewan da sukai da juna da abubuwa da dama harma da akan mahaifiyarsu dan haka fammah ta miqe ahankali tana zata basu guri SANAAH ta kalleta tareda bude baki ahankali ta dakatar da ita tana jin dik komai na sake mata rashin dadi ta kalli Ya Al'amin ta bude baki kawai wasu hawaye na zuwan mata tafara fada masa komai hawayenta na tsananta gudu sbd har ga Allah afuwa da yafiyan fammah din takeso sbd kaunar dake tsananinsu bata hada komai da abinda yafaru.

Shiru yayi cikin dan mamakin baisan komaiba sbd baa fada masa komaiba kuma bai taba sanin an boye komai dinba dan haka tabbas yasan baa kyautawa su famman ba musamman mum din tata dan haka ya sauke ajiyan zuciya mai sanyi da nutsuwa tareda dago idanuwansa ya sauke akan fammah wadda ta tsaya cak ta kasa daga kafafunta.

Jin idanuwansa akanta ya sakata juyowa ahankali amma akan SANAAH ta saukar da idanuwanta sbd jin a labarin komai data fada masa bata fada masa wutar da Mum ta saka musu ba harda mahaifiyarsa a ciki ta boye hakan dan haka tayi shiru.

Shi kuwa kiran sunan famman yayi ta dawo ta zauna har lokacin kallan SANAAH takeyi cikeda jin wani nauyi ya dabaibayeta har a kirjinta.

Bude baki yayi yana dan kallan famman ya fara bata hakuri da kansa a matsayinsa na wanda shima kaman mai laifin ne gareta tinda shine ya bada auren SANAAH ga Fleet duk da baisan an boye hakan ba kuma shi a gurinsa duka wannan abin ba abin tayarda hankula bane tinda dai aure ne akai kuma ba wai wata haram ba hakama tin farko baisan meyasa ma aka boye dinba amma koma menene tinda ita famman na ganin anyi laifi ya bata hakuri sbd komai ya wuce.

Sanyi jikinta ya danyi sbd abinda ya fada mata kansa tsaye da nuna duka wannan abinda kowa keyi ba komai bane tinda dai auren ba rabuwa zaiyiba kuma tinda daman kansu a hade yake su hakuri suci gaba da tafiya a hakan bazasu ma ji komai ba ko jin wani banbanci baya da yanzu.

Bai basu daman wata magana ba ya sako wata maganar wadda ta rufe waccan yana kokarin sauya yanayin da ganin kowacensu ta dan sake ta dawo normal.

Yanda ya ringa magana da kowacensu yana hade zance ya saka suka ringa amsawa suna shiga zancen da juna bama tareda sunsan suna hakan ba duk da babu irin wannan sakewan amma sun dan warware da yanayin.

Sai 1 yabar gidan ya fice ya tafi harkan gabansa yana barinsu su sake hutawa.

Bayan tafiyarsa sunyi sallah SANAAH ta sake kallan Fammah bata gaza ba ta sake neman afuwanta wadda wannan karan ta amsata ta kuma bar maganar kaman yanda take fatar ta baro matsalolin komai da damuwan.

Sanyi SANAAH taji tareda samun nutsuwa da saukan nauyi a kirjinta dik da tasan ba lallai yanzu su koma yanda suke ba lokaci daya amma insha Allah tana fatan su koma daidai dan haka bazata takura famman ba zata bi ahankali da kokarin dawo da communication a tsakaninsu.

Ita SANAAH batada waya haryanzu kuma a hakan ma yafi mata duk da tasan dole rayuwar saida waya a yanxu amma for now zata huta da wayar.

Itama fammah sbd batason jin tashin hankali sai batada niyar amfani da waya a yanxu dan haka wuni sukai suna kallo duk da bawai damunsu yayiba karshe ma ciye ciye sikai suna kokarin jan Ana a jiki wadda itama takeda kokarin aiki.

Sai dare Ya Al'amin ya dawo yayi shirinsa cikin kayan zaman gida black ya shigo bangaren nasu yana fidda kamshi me sanyi kafafunsa sanye da slippers da suka fidda hasken kafafunsa sosai yayi musu ordern abubuwan ci da dama baici a cikinsu ba ana kawowa yai musu saida safe ya tafi sbd yanada kamewa sosai ba laifi duk da yanada sakewa da nuna kulawa sosai da iya tattali amma akwai kamun kai dan haka baya wani zama a cikinsu.

Washe gari ma very late ya shigo suka gaisa ya fita office yanada aiki a gabansa dan haka har waje SANAAH ta biyosa suna sake magana da time sosai datakeson ya basu sbd sunfara jin kadaici gashi tsit ko a waya basu ji Dad din fammah wanda ayanxu hankalinta ya koma akansa tana mamakin yanda ya sharesu.

Ko data dawo ciki fammah da itama zuwa yanzu tana buqatan fresh air fita sukai tareda Ana wadda suka saka takaisu grocery store sukai siyayyan shirme taxi ta dawo dasu.

SANAAH hannu ta saka a girkin gidan sbd ta dan ragewa kanta zaman suka ringa dan fira da Ana fammah daga baya joining dinsu tayi sbd jin kaman itama kadaicin nan bazata iyaba.

Sai yamma sosai suka gama suka tafi daki kowa yayi wanka sukai sallar magrib suna gamawa SANAAH ta fita da kanta taje har bangaren Ya Al'amin tana ganin motarsa ta tabbatarda yana nan dan haka bugawa tayi babu jimawa aka bude,
shine da kansa yana sanye da kayan sanyi a jikinsa yana waya da Mommy dan haka shigowa tayi tana karban wayar suna magana.

Sun dan jima suna wayar kafin aka kaiwa Dr Mum da Maamah dikansu suka gaisa tukuna suka kashe.

Miqewa tayi tana kallan bangaren nasa da tsarinsa yake daban na namijin da sam bayason kyale kyale da class komai gwananin shaawa gashi komai nasa brown ne duk da ba duka ba amma kusan komai.

Janyosa tayi suka fito zuwa can bangaren dan suci abincin daren a tare dan haka koda suka shigo fammah na fitowa sanyeda doguwan riga mara ado mara kuma nauyi da hula akai ta kallesu daidai yana kallo gurinta shima idanuwansu suka hadu ya sake murmushi mai kyau yace

"Hi Doc,
Yaya gidan?"

Kallansa tayi tana dan murmushin daya fito sbd batasan yazataiba da idanuwan da suka hada tace

"Alhamdllh,yaya aiki,
Zakai dinner damu kenan"

Isa sukai gurin cin abincin yana cewa

"Yep,zan gwada cin abincin yan matan Fleet i hope i don't end up in hospital"

A tare suka kallesa suna dariya bama tareda sun sanda sunyi hakanba SANAAH tace

"Ya Al'amin ka manta da girkina ka xama babba"

Wani kallo ya mata yana dariya mai dan karfi yana kallanta zaiyi magana fammah tace

"Yes that's a bitter fact Ya Al'amin kada kace komai"

Hannuwansa ya daga alaman ya yadda baida abin cewa kuma suka isa suka zazzauna.

Abincin suka ci Fammah tai serving nasa yana kallan yanda take komai a natse harta gama ta zauna SANAAH kuwa itace tai serving nata kafin tayi na kanta.

Suna gamawa dole suka fita ya kaisu wani gurin da basu fi 40min ba sika dawo.

Washe gari haka suka wuni duk da yadan basu time dinsa sosai sai yamma ya fita.

Kwana biyar suka share basu ga fleet ba basuji duriyarsa ba ya basu dukkanin time din dasuke buqata na warware da juna batareda shiga ba sbd kowacensu rayuwarsa ce.

Ita kanta SANAAH dik da tana tsananin kewan ganinsa taji dadin space din daya basu sbd kada tayi abinda zata taba zuciyar fammah da suke kokarin komawa kaman baya dan yanxu suna magana sosai hakama basu taba sake tado maganar komaiba ta baya.

Ya Al'amin kansa sbd su samu time da junansu sosai da kyau yasaka yake basu time din kuma tinda ya fahimci sun samu fahimtar sai yafara kokarin basu time yana nuna musu kulawansa su dukan da kaunarsa da tattalinsa wanda Fammah take jin hakan sosai sbd bata saba da kauna da irin wannan tattalinba na 'dan uwa sbd ita kadaice batad yaya ko kani ko daya koda na dangi ne.

Ranar da suka cika sati daya cif a da zuwa tini SANAAH taji tanason kiran Dad din famman amma kuma tana hana kanta sbd fammah amma zuciyarta tsananin son jin ko muryansa ne take a yanxu obsession dinta na kallan fuskansa a cikin fammah ya fara taso mata wanda kuma ayanxu fammah data riga tasan komai bazata iya kallanta kaman baya duk da ko yanxu din tanayi amma kunyar fammah bata barinta tai mata kallan daya wuce a taqaice.

Da safe bayan sun gama breakfast Al'amin zai fita office yana sanye da navy blue Armani suite ta fito ta samesa ya dakata yana kallanta dan zai fito kenan ta miqa masa hannunta tana cewa

"Ya Al'amin zan kirasa pls"

Fuskanta ya kalla tana dan sanyi kaman wadda batada lafiya.

Numfashi ya sauke sbd daman kullum Fleet yana waya dashi yana jin lafiyansu.

Wayarsa ya fidda ya saka mata kiransa tareda miqa mata wayar yana barin palon ya koma bedroom dinsa dauko laptop dinsa daya bari.

Saida wayar ta kusan yankewa kafin aka daga cikin wata nutsatsiya kammiyar murya aka daga da ambatar sunan Al'amin din.

Ratsa kunnenta da wayar take kai muryan tayi ahankali ta sakata dago idanuwanta ahankali tai shiru tana kasa cewa komaiba sbd rasa kalman fara fada.

Shirun da akai din da saukan ajiyan zuciyarta me sanyi dayaji can qasa ya sakasa dago nasa idanuwan cikin nutsuwa da tsantsar samun wata kwanciyan hankali da kamewa taci daukan sautinsa kai tsaye yace

"How have you been SANAAH KHALIL"

Wani sabon numfashi taja mai tsananin sanyi tareda jin deep voice din tasa har cikin kanta bata iya cewa komaiba sai data dan sake sauke ajiyan zuciya tace

"Byee"
Kashe wayar tayi daidai fitowan Al'amin ta miqa masa tana juyawa ta fice sbd kenan yana kalau amma baizo ba bai nemesu ba dan haka batada abin fada.
#MAMUH
09033181070
[19/06, 3:58 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

129
Tana baro bangaren Ya Al'amin din ta nufo nasu tana shiga fammah na daki dan haka bata shiga ba palo tayi zamanta tana dan dora idanuwanta a tv da fara kallan da bama wai hankalinta yana kai duka bane kuma idan ta shiga daki a wannan lokacin zata iya kasa kallan fammah wadda zata fahimci kai tsaye itama akwai wani abin.

Sai lokacin sallah ta tashi taje daki tayi alwala da sallah tana gamawa ta hau gado ta bude Qur'an a ipad din fammah tafara karatu tsawon lokaci kafin ta gama sai ta kwanta bacci ya dauketa.

Sai yamma ta farka tai sallah ta nufi kitchen ta tadda Ana na dan aiki sama sama ta janyo kujera ta zauna tana bude drink din data dauko a fridge tana fara sha ahankali da spiced spaghettin da aka dafa da rana tana ci suna dan magana sama sama.

Tana gamawa hannu ta saka snacks din da Ana ke hadawa dan gasawa tana sake qara hada wasu ma.

Kamshin gashin na fara fitowa fammah ta shigo kitchen din tana kallan abinda sukeyi ta saka hannu tana ci suna tambayarta yaya taste din.

Sai magrib suka gama suka fito kai tsaye wanka SANAAH din tayi ta saka doguwar rigar bacci mai dan kauri mara tsayi ta saka abaya doguwa akai tayi sallah.

Sai da sukai sallan ishai fammah tayi shirin bacci ta zauna tana duba abu a ipad dinta SANAAH kuma fitowa tayi ta nufi kitchen ta dauko ruwa a hannunta da cupcakes guda hudu a qaramin plate ta fito kenan aka aka bude kofan palon wanda akai knocking a natse bata jiba.

Cak ta tsaya da kallan kofar da sauri sbd kayan dake jikinta da ko Ya Al'amin ne bai kamata ya ganta dasu ba dan haka zata juya da sauri taji muryansa ta sauka a kunnenta cikin wata zallan nutsuwa da ratsawa da cewa

"Careful Ms"

Cak ta tsaya batareda ta juyoba ta dan riqe numfashinta daya sarqe yana sauya bugawan zuciyarta.

Takowa yayi da wata nutsuwa ya tsaya bayanta tareda jin qamshinta daya rasa na tsawon lokaci ya shigesa ahankali..

Dan shaqar numfashi yayi yana dan riqe kansa da nutsuwansa sbd 'yarsa dake gidan,
Wata kewanta dake cin jininsa da tinaninsa a kwanakin ta masa wata lafiyayyar tasowa yaji idanuwansa sunyi wani nauyi mai sanyi ya ciro hannunsa daya daga aljihunsa ya dora akan kafadarta taji wani irin mutuwan jiki ya shigeta taja numfashi ahankali ya juyo da ita idanuwansa masu haske da wani irin kyau da kwarjini suka sauka akan fuskanta da babu kalan riqewansa da bata ruguzawa ya sauke

Please Login or Register in order to submit comment