Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da karfin zuciya dan kuwa haryanzu mahaifinsa da iyalinsa babu wata shaquwa da sanayya me karfi sbd yanayin rayuwarsu da kowa yake qasa daban yana rayuwarsa da kuma kafiyar raayi dayake tsakanin iyayensa dan kuwa matarsa itama daga kabilar mahaifiyarsa ta fito,kabilar da kusan basu yadda da zama da namiji da wata matar ba dan kuwa tamkar ma hakan a gurinsu baya yiyuwa sbd tsananin zafin kishi da taurin zuciyarsu tareda kafiya tareda iya yadda subar namiji har abada akan hakan dan haka ne yasa mahaifiyarsa takeda wani zafi da kafiya mai zafi akan ikonta da kabilarta.

Tareda iyalinsa yayi sallolin daren basuyi dinner ba kawai snacks suka ci shima yaci pieces biyu sbd ba cimarsa bane,

Tinda ya shige babu wanda dama zai sake ganinsa idan ba Imran ba shima sbd aikin dake gabansa yau bai samu ganin nasa ba saida safe shima sbd isar masa wasu bayanai akan schedules nasa da akai clearing ne da tafiyar dake gabansu wanda kusan komai ya kammala dan daman tafiyarsa zuwa Nigeria kowane lokaci ba matsala bace ko aiki me tsayi dan mahaifinsa dake can koyaushe a aje tafiyar take.

Washe garin matarsa tasan da maganar tafiyarsa Nigeria kai tsaye wadda ta sakata yin shiru tana jin wani irin sanyin jiki sbd tasan dole ba lafiya ba tinda Nigeria ba gurin zuwansa bane a yanzu da tin bayan daya rasa Rabin jikinsa na farko da bayan iyayensa dasu bai hadasa da komai da kowa ba,shine rashin da bazai taba mancewaba harya mutu.

Sanin matsayin mamacin a gurinsa ya saka mahaifin nasa da kansa ya yafe masa zuwa Nigeria din kwata kwata sedai su hade a wata qasar idan yaje wani abin,

Mahaifinsa na barin Nigeria ko tafiyar kwana biyu ce duk abinda yake saiya aje yaje duk qasar dayake ya samesa yagansa wanda hakan ke qara tattabarwa duniya girma da matsayn da ubansa yakeda shi a gurinsa da rayuwarsa.

Numfashi ta sauke me sanyi da sauti sbd Nigeria gurine da suke tsananin son ringa zuwa ita da 'yarta sbd son samun shiga da shaquwa da kusanci sosai da SIR JEERAH wato mahaifin mijinta wanda sukafi kowa sanin yanda yake kaunarsa fiyeda komai to tinda ya aureta take tsananin son kasancewa akwai kusanci da shaquwa tareda kauna me karfi tsakaninta da Sir jeerah din amma bata samu hakan ba dan haka a iya gurin Dr mum takeda kauna me karfi da duka kusancin datake buqata wanda ma harta ke ganin ta gama kama komai tinda ta kasance ta Dr mum.

Batace komaiba akan tafiyar kaman yanda bata tambaya dalilin yinta ba ko tambayar lafiya ita dai muradinta kawai yaje ya dawo garesu dan shine kadai abinda takeso take buqata,

Fammah dataji tafiyar tasa jin tayi tana tsananin son binsa dan kuwa tinda take so daya ta taba zuwa Nigeria din kuma ita a gurinta taji dadinta da har take marmarin sake zuwa harma da fatar ta dan zauna acan dan haka kai tsaye ta roko mahaifin nata tana son zuwa.

Da farko bai yadda ba amma yanda ta sake marairaicewa da fidda kaunarta da kaiwa mahaifinsa ziyara saiya amince musamman dayake bawai dadewa zaiyiba tafiyar kwanaki ce kadan dan haka zuwan da ita ba illa bane dan haka take akai shirin tafiyar da ita wadda ta saka Zuciyar Mum dinta damuwan kadaici da kewansu su biyun tin yanzu dan haka ta marairaicewa Fleet da narke masa gabaki daya akan kewansu da zatai.

*****Kwanaki kadan akai aka gama shirin tafiyar FLEET ADMIRAL RAHEEM JEERAH zuwa Asalin qasar mahaifinsa Nigeria wadda haqqoqa masu girman gaske da dama ke jiransa dan haka a ranar da jirginsa ya daga a ranar can Nigeria aka tanada duk wani tsaro da shirin tarbansa da zaman da zaiyi na lokacin da kuma tanadar da duk wata rayuwar da akasan itace rayuwarsa daya saba da ita.

NIGERIA
Saukar bayan Asuba jirginsu yayi dan haka ko kafin su baro airport gari yayi haske sosai mutane sun fito sosai sun fara kaida kawo,

Motocin securities biyar ne suka daukosa na alfarma sai lafiyayyar BMWi7 ce ta daukosa wadda ba kowane yake tuqata da kansaba face SAMAD JEERAH wato Qaninsa da suke uba daya,
Qaninsa da iya su kadai rak mahaifinsu ya haifa a duniyarsa,
Qaninsa da duk duniya shikuma Yayansa ne wanda yafi masa komai bayan iyayansa,
Qaninsa daya daukesa matsayin uba,dan uwa,madubi,abin koyi,wanda zai iya ajiye masa ransa gabaki daya kuma duniya tasan da hakan dan kuwa hakanne yasaka shine GODFATHER dinsa dayaxo karshen magana akan komai na rayuwarsa.

ABDULSAMAD HAKEEM JEERAH bai taba taka rawa dakowace matsayi da dukiya da komai na mahaifinsa ba sai na dan uwansa kuma godfather dinsa FLEET RAHEEM JEERAH dan hakanne ko mahaifinsa yasan duk duniyarsa babu wani mai girma da matsayin Raheem jeerah duk da tsananin girma da tsayuwar dayake da ita akansu a matsayinsa na mahaifinsu ya sheda girma da matsayin RAHEEM a gurin Samad daban ne hakama ko mahaifiyarsa ta yadda ta karbi hakan dan hakanne ta kwantar da kai ta karbi FLEET din tamkar godfather dinsu itada danta dan a yanzu suna da matsayi da power me karfin da danta ke juyawa a hannunsa cikin qasar Nigeria duka ta FLEET RAHEEM JEERAH ce dan haka suka bi Allah suka bisa duk da baimasan da wannan mutuwar dataiba akansa qaninsa kadai ya sani kuma shima yana kaunarsa kauna me karfi da tsafta dan shine kadai dan uwansa a duniya bayan rasa rabin jikinsa da yayi wanda shine dan uwanda harya mutu bazai dena radadi da kewansa ba.

Motocin a jere kai tsaye daga airport ba hanyar gida suka kama imran ne dayake cikin motar dake gaban ta Admiral din yasa aka juyata zuwa maqabarta da zasu fara kaiwa ziyara kafin isa gida dan kuwa ya gama sanin daman duk ranar da Admiral ya fara sauka Nigeria can ne zai fara isa yakai ziyara.

Samad ma daya san can din dole daman zasu fara zuwa take ya dafe bayan motar gaban suka nufi can din.

Isarsu maqabarta take securities suka tsaya waje suna bude masa hanya tareda tabbatarda tsaro daga waje dan kuwa daga shi sai imran da Samad ne suka saka kai a maqabartar bakinsa da yayi wani irin nauyi dauke da adduar ziyara idanuwansa na sauka akan daidai kabarin da suka tsaya wanda bazai taba manta gurin dayake ba take suka sauya ya sauke su akan sunan dayake kan kabarin..MUHAMMAD NASIR IBRAHIM.
Shekarun baya..........
#MAMUH
#BEST STORY
#FLEET ADMIRAL RAHEEM JEERAH
#MUHAMMAD NASIR IBRAHIM
#LOYALTY
#JEERAHs
#AGE GAP LOVE
#HOT+HOT+ROMANCE

GANIN IDO 2026
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank maryam sani gummiGANIN IDO 2026
Mamuhgee

4
*_IMZEED ENTERPRISES LTD_*
07077532253

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Sisters na ce ba? Wai kuwa Kuna da labarin shahararriyar mai sayar da kayan yara da kayan kicin ɗinnan akan farashi mai sauƙin gaske fiye da kasuwa? Na san dai ko ban faɗi sunanta ba da yawanku kun santa, amma dai duk da haka bari in faɗa muku sunanta. Imzeed Enterprises LTD, ta shahara gurin siyar da kayan yara da kayan kicin kala daban-daban akan farashi mai sauƙin gaske. Sauƙaƙawarta bai tsaya a nan ba, tana yin adashin kayan kicin weekly da monthly ga ƴan'uwa masu niyyar siyan kaya amma basu da dunƙulallen kuɗin a lokaci ɗaya. Abin burgewar shi ne tana da branch a Jihar Kano da jihar Filato (Jos), sannan tana aika kaya cikin ƙanƙanin lokaci a faɗin Nigeria da Nijer. Ku tuntuɓeta a kan wannan lambar wayar domin ku kwashi garaɓasa...07077532253. Muna maraba da masu sayen ɗai-ɗai ko sari.


********
A zamanin da turawa ke kamun baqar fata daga Africa suna tafiya dasu qasarsu wasu ana maidasu bayin bautawa qasar wasu kuwa karatu ake sakasu wasu kuwa sojojin yaqi ake sakasu,
A cikin wannan zamanin ne cikin wainda aka kama aka tafi dasu aka tafi da wasu marayu su biyu da basada uwa sai mahaifinsu wanda ana tafiya dasu da karfi da yaji basu mara ko kwana biyu ba ya rasu yabar duniya.

Antafi dasu qasar turawa ta hanyar jirgin ruwa dan haka koda suka isa kusan da yawansu da aka taho dasu baqin cikinsu da tashin hankalisu yafara sanyi sbd yar nisa da tsarin tafiyar da kusan tin anan kowa yake iya sanin maaunin kaddararsa a hannun turawa.

ALIYU da ABBAKAR su kadai ne suke uwa daya uba da aka taho dasu dan haka kai tsaye suna isa da akazo rabasu sai aka saka Aliyu cikin sojojin yaqi shi kuwa abbakar sai aka sakasa a cikin masu karatu daga nan suka rabu amma suna haduwa sosai sbd camp din bordern qasa suke su dukan.

Aliyu na sauran da aka sakasu cikin bauta da ukubar koyan aikin soldier duk da shekarunsu basuda yawa sbd iyakacinsa shekaru goma sha biyar haka yafara fuskantar wahala da tsantsar azabar zama kurtun soja da ko a gurin yaqi iyakacinsu kai bullet da daukan gawa amma azabar tayi yawan da yakejin kaman bazai iya kai labari ba.

Da farko har abinci baa basu sai duka da bautar aiki kawai wanda ya saka da yawansu sun mutu sbd wahala da sallamawa.

Ganin fiyeda rabin wainda akazo dasu din sun mutu sai turawan suka sauya tsari aka fara koyar dasu hadda ilimin yaren turanci wanda hakan ya fara sassauta zuciyar wainda ke rayen daga sallamarwa dasuke kokarin yi ga rayuwar.

Wannan dan qarin da aka samu ya saka Aliyu fara kokarin daukan jarumtar kowace irin wahala da azabar training sbd samun dan ilimin koda baida yawa zai taimaka masa gurin kasancewa da dan uwansa wanda bayan lokacin daya dan ja anrabasu dan kuwa su abbakar din tini akai cikin qasar gabaki daya dasu dan tabbatarda samuwan iliminsu da turawa zasu ringa amfani dasu dan juya duk baqaqen fata ta hanyar amfani da yan uwan nasu.

Aliyu da Abbakar lokaci yafara ja na rayuwarsu sun gama tabbatarda babu wani sauran maraici da quncin daya rage bayan su dage su zama abinda akeson su zaman matiqar hakan zai saka su samu daman ringa gani da kasancewa a rayuwar juna.

Alkawari ne da suka daukawa junansu batareda sun sake ganin juna ba suka fuskanci komai da karfin zuciya da son cimma manufa,

Aliyu ya tsaya tsayin daka yana koyan duk wani aikin wahalar dake cikin zamowa bawan soja kuma ya kwantar da hankalinsa sosai ya bude kansa dan fahimtar duk wani darasi da koyarwa tareda ilimin dake cikin kowace ukubar da ake basu tamkar dabbobin da basuda rayuwa a jikinsu.

Jajircewansa da qwazonsa tareda wata irin jarumtar shanyewa da hadiye duk wata azaba ga shakaru marasa yawa ya saka ya fara samun attention daga masu kulawa dasu suk maiyar da hankali akansa sosai azabarsa na ninkuwa wanda a nasa bangaren kowace azaba qarin karfin zuciya da juriya a garesa dan kuwa iya bushewa zuwa lokacin zuciyarsa ta bushe sosai.

A ranar da aka fara fita yaqin farko dasu irin tashin hankali da gawarwaki da yanda mutane ke mutuwa mara kyan gani a gaban ido ya saka Aliyu shiga mummunan halin daya suma saida ya kwana biyu kafin ya farfado sbd mummunan abinda ya gani daya saka kukan da baitaba yiba kafin daga baya ya tabbatarda saiya sake zama mai bushewan zuciyarda babu kowace irin tsoro ko fargaba acikinta zai iya tsira harma ya rayu rayuwar da zai iya zama sanadin yancin dan uwansa dan kuwa abbakar daya shiga qasar ya gama zama bawansu na har abada dan kuwa babu wanda zai iya fidda sa qasar.


Tin daga wannan lokacin Aliyu ya fara zama abinda suke son su zama din babu sauki ba tausayi zafi da wuta kawai batareda sanin kowaba da komai bayan qasar turawan.

A bangaren daya kuma kusan shi kadai ne ya tsira da ilimin turancin da ake basu,

Shekaru masu yawa suna sake tafiya Aliyu na sake zamowa cikakken sojan yaqin turawa dan kuwa ya gama sadaukar da rayuwarsa gabaki daya tarihi da kaddararsu yake son sauyawa na tsayawa ya zama soja mai cikakken yanci ba bawan soja ba da zaa kashe a banza ko gurin binnewa bazai samu ba sedai a qona gawarsu kaman yanda ake qona kara.

A lokacinda aliyu yake gwagwamarya da gawarwaki da harbe harben zamowansa soja a filin yaqi a wannan lokacin Abbakar nasa ilimin yayi zurfin da tasa rayuwar shima ta sauya gabaki daya dan kuwa an gama saka masa mummunar akidar tsanar baqar fata yar uwarsa da babu abinda iliminsa bai koyar dashiba na yanda babu amfanin kowace baqar fata a duniya bayan zamowa baiwa.


Bayan shekarun azaba da ukuba da nakasa da fargaba da tashin hankali da rashin bacci da rashin hutun jiki da zuciya da quntatuwa a hannun turawan yaqin kasar amurka ALIYU ya samu damar fitowa a cikakken sojan yaqin qasar mai yanci bayan da kuruciyarsa da samartaka da lafiya da ganinsa da duk suna qare a gurin bautar daya jure dan ganin wannan ranar da zai fito a cikin ayarin sojoji masu yancin da zai iya ganin yan dan uwansa wanda a yanzu yake rayuwar qasqanci a hannunsu.

Bayan duk wannan shekaru da suka shude sama da ashirin da biyar Abbakar ya samu ilimin boko sosai hakama manyanci yafara shigo masa amma baitaba fita daga zamowansa qasqantaccen baqar fatar da suke kalla ba wanda shima yake kallan baqar fatar qasqantattu aiki kawai yake a qarqashinsu kuma zaici gaba ne har qarshen rayuwarsa babu maganar yanci har abada.

Aliyu ya sauya sosai ya shima shekaru sun tafi amma a lokacinda ya amshi lambarsa ta zamowa cikakken soja wasu hawaye ne suka ciko idanuwansa da sukai jajir ya rintse ido yana komawa inda yake tsaye tareda dagowa idanuwansa ya kalli gefen daya tabbatarda ayarin baqar fatar qasar masu ilimi suke dan duba dan uwansa da shima tinda aka ambaci sunan Aliyu jeerah din a cikin sabbin sojojin da aka qaddamar wasu hawaye suka ga garo masa sbd bayan sama da shekaru ashirin kenan dayaji sunan dan uwansa harma idanuwansa suka sauka akansa dan haka kasa dauke idanuwansa yayi daga Aliyu wanda suka taho sunada kuruciyarsu amma a yanzu dukansu yau sun fara manyanta shekaru sun fara rufewa.

Shi kansa aliyu dayaga dan uwansa kasa dauke idanuwansa yayi daga kansa yana jin inama daga wannan yancin nasa su tattara su koma qasarsu wadda baitaba dena marmarin komawaba amma yasan har abada ne wannan.

Zamowan Aliyu Soja bai basu daman gani ko kasancewa da juna ba dan kuwa daga wannan ganin da sukaiwa juna basu sake ganin juna ba sbd Aliyu da aka maida kwata kwata border ta cikin daji sosai dan haka rayuwarsa ta sake zamowa kadaitacciyar da babu kowa a cikinta bayan zamowansa sojan da baisan komaiba bayan yaqi da rashin walwala da farin ciki ko kadan.

Abbakar yafi Aliyu shiga shekarun manyanci sosai sbd baya aikin wahala da gwagwarmaya kaman aliyu hakama lafiyarsa tafara ja da baya dan haka tinda ciwo ya sakosa gaba aka tattarasa aka maidasa inda din da ake aje irinsa can wani qaramin garin da baida kowane irin tsaro a cikin qasar.

Jinya sosai Abbakar yayi wadda ta saka ya samu aikawa Aliyu sakon yana rokon yaxo suga juna na bankwana.

Sakon na isarwa Aliyu ya samu isowa a washe garin ranar bayan doguwar tafiyar kwana biyu a hanya.

Koda ya iso nurses ne dake camp din suke kulawa dashi sosai amma yariga yayi nisan da babu wata doguwar magana a tsakaninsu Allah ya karbi ransa.

Aliyu duniyarsa tsayawa tayi cak sbd yasan shima a daidai yanxu baida kowace burin cigaba da rayuwa sbd duk abinda yayi yaqi ya zama yayisa ne sbd dan uwansa wanda gashinan sun rabu babu kowace sauran kusanci da sanin juna a tsakaninsu.

Ya shiga mummunan hali amma kuma a lokacinda yayi ido biyu da matar Abbakar din da dansa daya tak jin yayi ya samu sauran hope dan haka kai tsaye bayan kwana biyu ya tafi dasu inda yake sbd daman kusan acan din da yawansu sun dauko iyalansu sbd zamane daram a dajin babu ranar barowa shiyasa ya zama tamkar babban gari a tsakiyar jejin.

Bayan ya taho dasu baida zabin daya wuce bayan dan lokaci ya auri baturiyar wadda take ba musulma bace hakanan sbd tausayinta dana 'danta sbd babu inda zasu tinda daman can kaman ba lafiyayya bace aka aura masa dan kwakwalwanta ba cikakkiya bace.

Da farko ya aureta ne kawai dan basu rayuwa amma bayan lokaci me dan tsayu sai ya fahimci rashin lafiyarta nada tsananin tausayi dan haka ya sakawa zuciyarsa sanyi ya amshi auren tareda maidata cikakkiyar matarsa.

Daga shi har ita shekarun sun dan fara tafiya amma cikin ikon Allah ta samu wani cikin ta haifi namiji sai kawai ya saka masa Abbakar dan haka yayansu biyu Ahmed da Abbakar.

Babu komai na tsarin haihuwa kokuma dogon ilimin hakan dan haka ba bata lokaci ta sake haihuwan yara biyu duka maza hassan da husain.

Cikin shakaru marasa yawa ta haifa yara hudu da Ahmed danta da Abbakar sai suka zama biyar.

Duka yaran kalar fatar mahaifiyarsu suka dauko asalin baturiya sai kammnin mahaifinsu dan hakannen aka daga maganar yawan yaran sama take kuwa aka sauya masa gurin aiki daga dajin zuwa cikin asalin qasar America din sbd qasar bata yadda da rashin ilimi daga kowane yaro wannan shine dokarsu.
#MAMUH
#JEERAHS
#BEST STORY OF 2026
#ABDULS JEERAHS

GANIN IDO 2026
1K
VIP 5K
0022419171
ACCESSBANK MARYAM SANI GUMMIGANIN IDO 2026
Mamuhgee

5
_*IMZEEDENTERPRISESLTD*_
07077532253
*ADASHIN KAYAN KICIN A SAUƘAƘE💃🏽.*
Babban burin ko wace ƙasaitacciyar mace shi ne ta ga ta gyara kitchen ɗin ta, ko don ta ƙara kankaro ma kanta kima da daraja a idanun mai gida

Dunƙule kuɗin ki saya ne ke miki wahala hajiyata? Ko kuma kuɗin siyan ne a lokaci ɗaya ba ki da shi? Ko kuma tara kuɗin a hannunki ke baki wahala saboda kina fara tarawa sai wasu hidindimun su saka ki kashe kuɗin?

To ki kwantar da hankalinka ƙawata, IMZEED ENTERPRISES LTD ta gama shirya miki komai ta yadda ke ma za ki mallaki naki kayan kicin ɗin cikin sauƙi da rahusa

Ta buɗe adashin gata, wanda ya fi bashi kwanciyar hankali, akan farashi mai sauƙi, kaya ƴan zamani, masu kyau da inganci. Idan kika gama zubin adashin da kike yi za ki zaɓi duk kayayyakin da kike so, sannan za ta aika miki da shi duk inda kike cikin ƙanƙanin lokaci. Abu ɗaya da za ki dage da shi kawai shi ne yin zubi akan lokaci.

A wannan karon za'a fara zubi 25th April in sha ALLAH . Zubin adashin za a yi shi kashi uku ne👇🏽
20k monthly kayan 100k
10k monthly kayan 50k
3k weekly 15 weeks, kayan 45k
Abin burgewa da adashin Imzeed shi ne ko a adashi kika tara kuɗinki za ta baki kayan ne ba tare da ta yi miki ƙarin ko sisi ba 💃💃

Domin yin adashi da gaske, ki tuntuɓi Imzeed ta wannan number https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1

Domin gani da sayen irin kayayyakin da Imzeed take saidawa, ku shiga cikin wannan group ɗin👇🏽
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt

*********
Dawowan Aliyu Jeerah da familynsa a cikin qasar America ya basu wata yar rayuwa me hasken da basu taba tinanin samu ba bare fuskanta sbd a karkashin militaryn qasar ake musu komai musamman daya kasance jajirtaccen soja da suke buqata duk zamtowansa baqar fata.

Iliminsu da lafiyarsu duka akan karkashin kulawan military suke hakam albashinsa da aka fara basa na aikin sojan ya qaru sbd yawan yayansu.

Yaransu sun fara tasowa da girma a cikin yar nutsuwa da ilimin boko hakama da kwanciyan hankali dan haka mahaifin nasu bai taba jin gazawa ko qyashin aikinsa ba har saida lokacin retire yayi dole sbd tsufa daya sako kai gashi har lokacin sun cikin karkashin kulawa baa taba dena musu komaiba sbd ganin yayansa duka maza ne da ake jiran su zama sojojin qasa suma sbd shine baqar fata bawan farko daya jure harya kawo matsayin sojan qasa mai yanci dan haka akeson ahalinsa suci gaba da jan wannan legacy din.


Matarsa Riyan ta rasu bayan har dansu na farko Ahmed jeerah ya shiga military school.

Rasuwarta ta taba mahaifinsu Aliyu wanda ake kira da A jeerah sosai dan kuwa tamkar ita kadaice makusanciyar dayake da ita wadda yake kalla a matsayin rayuwarsa ta baya da ahalinsa bayan yayansa.

Yayanta ma sun shiga tashin hankali bayan rasuwarta sbd duk da batada cikakkiyar lafiya itace farin mahaifinsu kadai da suke ganin yanada.

Rasuwarta tasake bawa Aliyu jeerah sabuwar yancin da aka amintar masa zai iya fita qasar yaje koina ya dawo sbd tausayawa masa da kuma ganin yanda yayansa da kaf suke gap da shiga military school su samu nutsuwan aikinsu.

A wannan lokacin ne qasarsa ta Nigeria ta samu yanci dan haka bayan ankwana biyu da rasuwar yayansa duka kaf sun shige makarantar sojin ya tafi kasarsa a karan farko bayan shekaru sama da arbain dan haka koda ya taho sedai yazo a matsayin dan ganin qasa kawai sbd baida kowa baida komai baida gurin zuwa.

Karfin hali yayi sbd tsananin son dayakewa qasarsa ya fara kokarin rayuwa a cikinta bayan ya siya gidan kansa da kuma kokarin fara dan business qarami duk da shekaru sun ja amma baida kowa baida mai taimaka masa.

Shekara guda ya share a Nigeria cikeda gwagwarmaya da manyancin ya kasa iyawa sbd zuciyarsa dake kan yayansa dake can hakama dole yana buqatar mai taimaka masa dole ya koma.

Bayan dawowansa babban dansa Ahmed ya fito daga military a kuma lokacin suma qasar ansamu yanci da sababbin tsare tsare da shugabanni dan haka a yanzu yancinsu a hannunsu yake dan haka suka tattara suka sake komawa Nigeria da babban dan nasa Ahmed jeerah.

Bayan komawansu wahala da garari sosai Ahmed yasha gurin iya rayuwa anan din sbd duk abinda suka taho dashi haka yake neman karewa babu kowane tsayayyen aiki ko business din daya samu ga Dad din yana fama da jiki wanda ya saka duk yanda ma sukaso komawa a lokacin ba hali dole yafara maida hankali gurin nema masa lafiya.

A gurin gwagwamaryar rayuwa da mahaifinsa ya hadu da likitar data taimaka masa sosai gurin jinyar mahaifinsu harma ya warke a lokacin ne tayi hanya ta samar masa aiki a kamfanin yayanta.

Fara aikin Ahmed din ya kawo sauki da rufin asiri a rayuwarsu sosai wadda suka saba da ita yanxu,

Aiki tuquri da jajircewansa da iliminsa ya saka cigaba bullo masa sosai wanda daman ya aje aikin soja tini dan anan din ba wannan maganar akeba,

Da kusancin Dr maryam da son datake masa batareda duba da ko kalarsa ta turawa datake bayyane ba ya sakasa samun cigaba da dukiya ya sauya musu gidan da suke ciki zuwa me tsari da walwala.

Baa rufa shekara ba da sauyin muhallinsu akai aurensa da dr maryam wanda auren ya saka yan uwansa tahowa daga can qasar dukansu sun zama soldiers amma biyu hassan da husain basu fara aiki ba dan haka tinda suka taho auren sai suma basu komaba suka zauna tareda mahaifinsu da dan uwansu wanda a yanxu kam shi ya gama zama dan Nigeria.

Farouk da Ashir ne kadai suka koma suka shiga soldiers gadan gadan sbd hakan ya riga ya shigesu.

Anan sun Hasan aiki suka na business din Ahmed dake tafiya yanzu sosai dan kuwa suna cikin rufin asiri sosai sosai.

Haihuwan farko da dr maryam tayi Kafin ayi suna Allah ya karbi ran mahaifinsu wanda ya rasu yana farin cikin ganin shi da iyalansa sun dawo gida abinda dan uwansa bai ganiba.

Bayan rasuwarsa da shekaru biyu Allah ya karbi ran ashir a gurin aikinsa na soja wanda hakan ya girgiza yan uwan sosai suka shiga damuwa sosai dan haka suka maida hankali gurin yiwa dan uwansu addua da dora kulawansu kaf akansa sbd yanzu shi kadaine soldier a cikinsu kuma wanda baya qasa daya dasu.
Hasan da husain duka sunyi aure kuma kowannensu yanda haihuwa da iyali dan haka suke sake jin kulawa da tsananin son ganin dan uwansu shima ya samu rayuwar da zaiyi nasa iyalin amma sam ba damar hakan sbd ya sadaukar da rayuwarsa akan aikinsa.

****AHMED JEERAH shine shugaba a familyn na jeerah a yanzu dasuke tashe gurin business da iya huldar business me kyau da mutane tareda ilimi da wayewa tareda iya gudanar da rayuwa,

Husain jeerah shine wanda ya samu kansa a harkar siyasa shi kuma ta hanyar mutanen arzikin daya hadu dasu tin a harkar business cikin saa shima siyasar tazo masa a cikin aminci dan kuwa sosai ake damawa dashi har yakai ga ya samu matsayin da a yanxu yake kai harma yana kokarin qarawa na gabansa.

Zamtowansu tamkar turawa da ake kallo ya saka suke samun sanayya da suna tareda huldodi da yawa dan hakane daukakansu ke qaruwa.

Iyalansu sun girma sun habbaka sun ginu sai a lokacin ne FAROUK JEERAH yayi aure shi kuma acan qasar dan haka sedai yan uwansa sukaje akai bikin acan tareda matarsa yar qasar Singapore daganan rayuwarsa ta sake daidaita a

Please Login or Register in order to submit comment