Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka ana yin sallan magrib ta SANAAH ta kasa sakewa a gaban fammah din karshe kasa dauka kirjinta yayi ta yanke shawaran zuwa Dad duk da bata jin dadi sosai har wani jiri take ji mai dan tsanani amma dole tana son zamewa idanuwa da kallan fammah.

Sallan ishai sukai suna gamawa ta ta dora doguwan riga mai fadi dosai akan kayan jikinta da mayafi ta silale ta fice zuwa gurin Dad.

Fammah data kasa riqe kanta kwata kwata daga abinda zuciyarta take turata ga bangarensu ta miqe ta nufa kirjinta na wata irin bugawa da sauri tana son hana gangar jikinta da zuciyarta binciken amma ta kasa.

Dakinsu ta nufa tana shiga bangaren tana isa kai tsaye closet ta wuce ta nufi wardrobe din da kayan SANAAH suke a jere ta kalli kayan hannunta na dan rawa takai ga kayan tafara dubawa bugun zuciyarta na tsananin karuwa tana daga kayan gabaki daya saiga jakar datake nema ta tsaya cak tana kallan jakar idanuwanta na dan nauyi kaman yanda kirjinta yake nauyin.

Hannu ta miqa ta dauko jakar tareda budewa kai tsaye idanuwanta suka sauka akan takardun da suke dauke da sunan asibitin jeerahs din ta sauke ajiyan zuciya mai karfi data fito da bugawan zuciyarta.

*****kafin wannan daren kuwa gap da Magrib jirgin Samad Jeerah ya sauka batareda sanin hajiyarsa data wuni a tsaye cikin tashin hankali da tsoro da fargaban isowansa datake zargi,

Babu wanda yasan da zuwansa dan haka ba wanda yaje daukansa airport mota kawai ya hawo ya iso JEERAHsV idanuwansa jajir kaman wanda ya iso a caje sbd yanda idanuwansa sukai dole ma glasses ya saka ya rufesu duk da yamma tayi.

Securities na ganinsa da girmamawa sukai masa barka da sauka suna boye mamakinsu na ganinsa da motar kasuwa.

Yana shigowa mai tsaye uwarsa batasan da zuwansa ba bangarensa ya nufa wanda yake fes sbd duk bayan kwana biyu shima uwarsa ke sakawa ana zuwa gyara bangaren sbd hana qura da yana zama dan haka babu inda yakeda kura koina fes.

Haske kadai ya kunna ya jefar da kayansa ya fada bathroom ya sakarwa kansa ruwa hakanan yakejin kaman jininsa na konewa kwakwalwansa na rasa lafiyarta sbd a iya saninsa tsawon shekarun SANAAH na nan a matar da har abada yadan Fleet bazai taba kallanta a maceba sbd babu qarin wata macen a rayuwarsa data iyalinsa ta ina tayaya hajiyarsa zatace ciki a jikin SANAAH?
Wane namijin ne ya isa ya tabata kokuwa wane namijin ta yadda dashi bayan shi bata yadda dashi ba,

Yabarta ne kaman ajiya ga auren dayake kanta har zuwa lokacinda Dad zai gaji da jira ya raba auren amma yanzu kam bazai iya jiran ba.

Hajiyar na zaune a palo da daddaren bayan ta gama sake danna kiransa bata samu taji an bude kofar palon kai tsaye an shigo ta dan juya dan ganin waye sai kawai ganinsa tayi da sauri ta miqe tsaye tana jefar da wayarta ta isa gurinsa tana cewa

"Wai dawowan kayi kenan Samad?
Innalillahi,
Me kake tunani?
Menene a cikin kanka?
Wace masifar zaka kuma jawomin bayan wadda na shiga ta mutuwan aure da girmana?
To bari kaji na fada maka Samad wlh tallahi babu ruwanka da SANAAH ko da cikin aure ne a jikinta kona shege koma ne menene babu ruwanka da ita"

Wani kallo ya mata da idanuwansa da suka sauya cikin baqin ciki mai tsananin gaske yace

"Idan kina ambatar cikin nan da bakida tabbas akansa kaman zan zare nakeji dan haka ki dena fada.....

Katsesa tayi da karfin gaske da cewa

"Wallahi cikine a jikinta kuma ko zaka mutu bazan bari ka tinkareta ba dan bazaka saka kanka a masifar da zata shudar da labarina a jeerahs ba batareda naga karshensu ba bayan haka so kake ubanka ya kasheka?
Ba shi ba ko Raheem a yanzu kasan zai iya daukan mataki akanka sbd matsayin SANAAH a gurin yarsa dan haka tin kafin ma mu raba hali maza maza a cikin daren nan inason kabar gidan nan ka koma inda ka fito..

Baqin cikin daya gama rufesa hanasa kuma magana yayi ya juya a tsananin fusace zai fice ta riqe hannunsa tace

"Tafiyar zakai ko yaya??

Juyowa yayi gabaki daya ya kalleta idanuwanta na qarasa bayyanarda zallan fushi da baqin ciki yace

"Zan fuskanci Dad din da kaina bayan na tabbatarda abinda kike fada dan kuwa wlh tallahi saina dauki ran ko wanene yayi mata cikin kafin itama ta fuskanci asalin waye ne"

Turesa hajiyar tayi da karfi tana sake cakumo sa tace

"ashe bakada hankali ko?
Ashe hauka ka fara bansaniba?

Fixgewa yayi da karfi yana juyawa yace

"Kece kika fara cinnamun haukar sbd kece kika zabi sanar dani abinda kika gani"

Kofa ya tinkara ta bisa da mummunan tashin hankali ta riqosa tana tsayawa gabansa tashin hankalinta na bayyana gabaki daya ta bayyanarda tsananin tsoronta tace

"Kayi Hakuri kada ka tafi ta koma dakinka gobe zamuyi magana da safe"

Bai kalletaba ya kwace yana futa kofar palon ta biyosa a tsananin rikice tana rokonsa amma sam kaman bada shi take ba dan haka a zafafe tasha gabansa tareda daga hannu ta sauke masa lafiyayyan marin daya sakasa tsayawa cak yana dago idanuwansa da sukai mummunan ja sbd bacin rai da wani sabon radadin baqin ciki ya kalleta zaiyi magana kenan idanuwansa sukai wata sauka akan SANAAH data fito bangaren Dad wanda yake conference meeting a laptop bata samu ganinsa ba.

Bata lura dasu ba sai data kawo daf dasu a harabar gidan dan haka ta tsaya cak gabanta na wata irin mummunan faduwan data sakat kanta muguwar sarawa mararta tai wani nauyi a take.

Hajiyar Samad dinma cikin mummunan tashin hankali ta juyo ta kalli SANAAH din itama take taji hankalinta ya kara tashi ta saka hannunta da sauri ta riqe hannunsa daya tana hanasa motsawa daga inda yake zuciyarsa na wata irin harbawa da azababben zafin ganin SANAAH din a gaban idanuwansa da wata irin sauyin dayake tabbatar masa da maganar hajiyan.
#MAMUH
09033181070
[15/06, 12:38 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

117
Fammah da hannuwanta suka bude takardar asibitin data ciro jakar SANAAH wani irin sarawan da kanta bai taba yiba yayi wani jiri ya dibeta tayi baya da karfi tana zubewa qasa idanuwanta na dishi dishi ta sake karantawa tana jiqewa da zufan da tin daga cikin kanta yake fitowa.

Ciki?
Cikin haihuwa?
Wata biyu da satika?
A jikin SANAAH??

Girgiza kai tayi da sauri tana sake duba gurin sunan dayake rubuce da tsananin sauri hannuwanta na tsananta rawa taga sunan SANAAH dinnne baro baro a jiki.
Dena aiki kowane tinani da kwakwalwanta sukai ta miqe a tsananin tsoroce da kasa yadda dashi dan koma menene bata yadda da result din SANAAH bane zarginta take akan Safiya yakoma sbd ita SANAAH takai asibitin tayi amfani da sunanta dan saka a duba safiya din.

Fitowa tayi kai tsaye tana nufar kofar fita wadda tayi daidai da isowan Mum dinta bata tsaya ko kallan Mum dinba ta wuce hankalinta na da zuciyarta na neman amsa daya daga SANAAH ina cikin ya fito wakeda cikin??
Dan ko saurayin datake fira dukansu basa dashi bare wata maganar ciki ta fito.

Mum bin bayan fammah din da idanuwanta tayi kafin ta juya zata shige sai kuma ta fasa ta biyo bayanta sbd ganin yanda take tafiya kaman wadda bata hayyacinta.

Samad kuwa daidai wannan lokacin ne suka hade da SANAAH wadda ta motsa zata kebesu da sauri ta wuce ya fixge hannunsa daga na Hajiyarsa zai riqo SANAAH din hajiyar ta kuma riqesa da sauri wannan karan jikinta har rawa yakeyi ta juya ta kalli koina taga ba kowa ta bude baki jikinta na wata irin rawa tace

"Ashe bakada hankali muguwar hauka na cinka ko??
Me kake kokarin yi?
Ka tabata ace cikin jikinta naka ko???

SANAAH data daga kafarta zata wucesu cak ta tsaya duk da yanda gabanta yake mummunan faduwa da tashin hankali ta dan juyo ta kalli hajiyar da tsananin mamakin kalamanta sedai kafin tayi magana Samad din ya bude baki yana yi kan SANAAH din gadan gadan yana ambatar sunanta tayi baya tareda juyawa da karfi zata bar gurin Fammah data kawo gurin ta daga mata takardun hannunta a fuskanta idanuwanta a rufe batareda ta lura dasu hajiyan ba tace

"Menene wannan???

Samad ne ya sauke idanuwansa da sauri akan takardun cikin tsananin tashin hankali da wani irin rawar jiki ya damqi takardun yana karantawa bai qarasa ba idanuwansa sika gama rufewa ba tsammani da wani karaji yayi kanta yana cewa

"Ba cikin Fleet bane wann.......

Bai qarasaba aka sauke masa wani mahaukacin marin da saida harabar gidan ta amsa hajiyarsa ta kalli Meenah data sauke masa marin idanuwanta a rufe jikinta na wata irin tsima da rawa idanuwanta jajir sbd jin sunan wanda ya ambata da ciki duk da batasan menene yake faruwa ba.

Shi kansa a rikice ya kalli Ms Meenah din wadda ta juyo da idanuwanta da sauya akan SANAAH wadda take jiri ya dubeta zatai baya fammah ta rikiceta a firgice

Hajiyar samad dataga Jikin samad na tsimar dayake kokarin sake yi kan SANAAH taga bazata iya barin yayi abinda zai rasa kansa ba ta bude baki tana riqesa da karfi tace

"Menene kike tada haukarki tin yanzu ki jira ki fara sanin waye me cikin da ake magana a tsakanin yarki da yar riqonki kuma waye uban cikin duk da babu tabbas amma gatanan ta fada muji idan na Mijinta ne FLEET RAHEEM JEERAH....

Tsit gurin yayi wutar kowa ta dauke daidai isowan Mr Sideeq gurin yana kallan Samad da tsananin mamakin daga inda ya fito saukar yaushe..

Mum kuwa wani dip kunnuwanta sukai idanuwanta a kafe cak akan Hajiyar Samad batareda ko numfashinta ya fito ba,

Fammah kuwa kaman saukan tsawa mai karfin gaske ta ruwan sama taji saukan maganar tayi baya da sauri tana neman faduwa Mr Sideeq ya tareta da sauri idanuwanta na tsayawa cak akan hajiyar itama.

Meenah kuwa take zuciya ta rufeta jikinta na wani irin bari ta damqi wuyan hajiyar tai mata wata mummunan shaqar data shirya rabata da ranta har lahira.

Take Samad yayi wata zaburar daya tura SANAAH da karfin gaske gurin Meenah sbd tayi muguwar faduwan da cikin zai fita koma na waye.

SANAAH na fadawa gurin Meenah din da kafa tai mata wani irin mugun harbin datai baya da karfin gaske Safiya data kawo gurin da sauri ta sake ihu mai karfin daya saka su dr mum dake palo fitowa cikin tashin hankali daidai nan aka tare SANAAH din ta baya da wata irin kyakkyawan riqon daya hanata muguwan faduwa da ko fuskanta zata iya damage.

Fammah data juyo da karfi itama dan tare SANAAH din sai ganinta tayi a hannun Dad dinta daya sake saka kowa shiga mummunan shock.
#MAMUH
09033181070
[16/06, 9:52 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

118
Kasa motsawa fammah tayi tana wata irin mutuwan tsaye hannuwanta dake rawa suna tsayawa cak da wani irin shock daya ratsa idanuwanta zuwa kwakwalwanta da kirjinta tana kallan irin riqon da Dad dinta yayiwa SANAAH idanuwanta nayin jajir..

Shima dago idanuwansa da sukai jajir yayi jikinsa na dan wani jijjigar da yake tsananin kokarin riqe kansa da danne asalin bacin ransa ya kalli Meenah datake kokarin raba Hajiyar Samad da ranta bai kalli SANAAH ba wadda dukkanin jikinta rawa yakeyi tana ficewa hayyacinta sbd tsananin tashin hankali da tsoro da firgici itama batama iya kallansa ba da tsananin rawar jikin ta kalli fammah wadda take shedar da abinda kanta yake kasa dauka bare hankalinta sbd irin riqon da Dad yayiwa SANAAH ba riqone na 'ya da uba riqo ne dayake bayyanar da dukkanin kusanci da sabawa da haduwan jiki dan kuwa a cikin jikinsa sosai da kyau ya tareta yana zagayeta da hannuwansa da basu iya boye asalin tattali da kulawa ga jikin dasuka saba sauka akai.

Rintse idanuwa fammah tayi sbd wani dishi dishi da suka fara gani daidai Su dr Mum na isowa akan Meenah sukai suna kokarin cireta daga jikin Hajiya wadda tafara jin kamshin lahira amma suna isa wani mahaukacin shuri ta kuma bankowa ta buge mommy wadda tayi baya da karfi itama safiya ta tareta Maamah tayi kanta itama haukan ta bugo mata take tayi tashin aljanun da baa taba sanin tanada su ba dan kuwa shaqar dataiwa hajiya an kasa banbare ta Raheem kuwa dayake riqe da SANAAH har lokacin wadda jikinta ke tsananta wata mummunan rawa kafafunta na neman kasa daukanta mararta ta wani irin riqewa kasa sakinta yayi sbd zata zube ne daya saketa dan haka cikin tsananin mummunan bacin rai da fushin gaske ya bude baki da wata tsawar da bai taba yiba ya ambaci Meenah din wadda ta dakata cak tareda juyowa dan jin shine jikinta na wata irin bari da idanuwanta sukai jajir ta sauke idanuwanta akan fuskansa wadda tayi jajir babu kyan gani...

Ahankali idanuwanta suka fara gangarowa daga fuskansa zuwa hannuwansa dake rungume da SANAAH ta gefensa da miqa hannu a cikinta dan bada kariya daga duka haukar da zata taso a gurin...

Sakewa hannuwanta suka fara yi daga wuyan Hajiyar rawar da jikinta keyi tana qara wata irin tsananta idanuwanta da suka fara gani dishi dishi ta tsayat akan hannuwan nasa kafin ta dago ta kalli fuskansa ya mata wata irin zazzafar maganar da bataji ko kalma dayaba sbd jinta daya dauke batajin komai bakinsa kadai taga yana matsawa ta maida idanuwanta akan SANAAH wadda ta rintse idanuwanta tana wani irin kuka mara sauti jikinta na rawar datafi koyaushe....

Dr Mum ce takai hannu zata kamo Meenah din amma ta janye ahankali tana maido kallanta akan Dr Mum din wadda tsananin nauyi ya bayyana a cikinsu da damuwa mai tsananin data bayyanarda guilty dinta take wani kakkaifan yanka ya yanki zuciyar Meenah datai baya kadan tana neman zubewa Fammah da itama jirin take gani ta riqeta da karfi suka rintse idanuwansu a tare kafin Meenah ta bude idanuwanta da jan su yayi munin da kaman jini ma suke kokarin fitarwa ta kalli Maamah wadda ta bude baki zatai mata magana amma ta janye tana daga kafarta datafi nauyin mota a jikinta ta rintse idanuwanta da karfi wani azababben radadin daya wuce hankali yana tarwatsa kirjinta da kwakwalwanta ta bude idanuwanta akan SANAAH ta tsayar tana dakatawa cak bata iya motsawa ba

Kallan Fammah yayi yace su shigo da ita ciki
Yana fadan hakan ya juya da SANAAH din wadda ta kasa ko daga kafafunta sbd ta fice hayyacinta gabaki daya zai daga kafafunsa kenan wani irin duhu yafara rufe idanuwan Meenah datake ganin dishi dishi bugun zuciyarta na neman tsayawa cak jikinta ya sake gabaki daya a jikin fammah zata zube Dr Mum da Maamah suka tareta a tare suna ambatar sunanta da karfi a tare juyowa zaiyi ba tsammani tayi wani irin kukan kura tayi kan SANAAH ta fada kanta gabaki daya tareda shaqar wuyarta da wani irin mugun karfin gaske tana ficewa hayyacinta sukai baya suka fadi da karfin gaske sbd unexpected ta fado kanta bayan sun juya din dan haka ne ta shammacesa.

Da tsananin sabon tashin hankali da wata irin karfi su Dr Mum sukai kanta sedai tini Raheem din yayi mata wata irin muguwar fizgowa amma ta mannewa SANAAH din wadda take ta some sbd faduwan dasukai mai munin data saka Jini balle mata.

Fammah datake sake ficewa hayyacinta da abinda bata taba ganiba da shock din daya girgizata girgizawan da bazata taba kuma dawowa daidaiba da gani dishi dishi taga jinin dayake gangarowa wanda kowa bai luraba sbd tashin hankalin banbare Meenah din daga SANAAH wadda suke tinanin ba ita bace dan kuwa karfin datake dashi ya wuce hankali da qyar ta bude baki tana kallan jinin tace

"Dad,Mum jini.... tana fadar hakan ta xube a gurin a some kanta na kasa daukan komai.

Idanuwansa ne suka sauka akan jinin ya saka hannu yayi mata wata mummunan fizgan data baro jikin SANAAH din ya daga hannunsa dake wata irin mummunan rawan da babu wanda ya taba gani zai sauke mata marin da dr mum ke ganin idan ya mata zaya iya rasa idonta daya ko rasa ranta ma dan yanda jikinsa ke fizga dan haka a haukace Mum din ta riqe hannunsa tana daga nata ta saukewa Meenah din lafiyayyan marin daya sakata dakatawa cak da fixge fixgen datake tana wani irin jijjiga.

Dad ne ya iso gurin da wani irin mamaki da tsananin baqin ciki tin bai iso dap ba Raheem ya riga ya dauko SANAAH din a jikinsa gabaki daya jikinsa har lokacin wata irin wara yakeyi data saka Imran shiga mummunan tashin hankali sbd ko alluran sojansa ta tashi baya taba irin wannan jijjigar da tabbas da hannunsa ya sauka akan Ms Meenah zata iya rasa idanuwan da hakoranta idan kwakwalwanta bata hade da jini ba a take dan haka a rikice da tsananin tashin hankali aka bude mota

Dad kuwa securities yawa hannu da kowa yake tsaye cikin tashin hankali da cewa a bude gate.

Dakatar da Raheem yayi fuskansa babu rahama ko daya baice masa komaiba sbd babu wanda a cikinsu lokacin haukansa ta soja da bata tashi ba da hannu ya nunawa Maamah da Safiya su karban masa SANAAH din wadda jinin yake zubarwa sosai.

Mota aka saka SANAAH din da kansa ya karbi key din motar safiya ce kadai yace ta shiga tana shiga yaja motar bayan shekaru sama da a kirga rabon da yayi tuqi amma da wani mugun speed daya saka securities din villah din kaf miqewa aka wangale masa gate da karfi ya fice yabar kowa baicewa kowa komai ba bai kuma kalli kowa ba wanda hakan ya sake daga hankalin kowa.

Maamah ita gurin fammah tayi ta kwasheta tayi ciki da ita dr mum kuwa hannunta ta wata irin rawa ta damqo hannun Meenah data haukace gabaki daya wani irin ihu da haukan data saka villah din gabaki daya ankarewa da masifar da ake ciki tayi ciki da ita.

Motocin fleet kuwa a jere suka bi bayan Motar Dad wanda shima shine mai tuqin cikin wata mahaukaciyar gudu idanuwansa kallo daya zakai musu kaji jikinka ya dauki rawa sbd rashin kyan ganinsu.

Su imran ne suka bi bayansa da wata motar sbd tsaro dan haka Motocin a jere suke da wani irin gudun da dik inda suka wuce sai ansan Jeerahs ba lafiyaba.

Dr Mum da Maamah ne suka saka Meenah a daki ta karfi duk da kaman tafi karfinsu sbd wani irin karfi ne yake taso mata kusan duka kayansu ta yaga musu da karfin gaske suka sakata suka rufe da key suna jin tanata fasa komai na dakin tana kiran sunan kowannensu da cewa wlh saina kashe SANAAH da duk wanda yasan da alaqar kaf duniya.

Dr Mum da Maamah kai tsaye hankali tashe ko kaya basu sauyaba hijabs kawai suka doro dogo akan kayansu suka fito sai asibitin jikin kowannensu yana rawa da wata faduwan gaba da tashin hankalin kada wani abi ya samu SANAAH da cikin jikinta.

Mommy datake cikin tsananin damuwa da tashin hankalin itama ita aka bari da fammah wadda ta shafawa ruwa yafi so biyar amma bata farfado ba dan haka hankalinta ya qara tashi jikinta na tsananta rawa ta rungume famman tana ta sake kiranta da rawar murya tana sake shafa mata ruwa.


Acan asibiti kuwa Dad jeerah na isa motar Mr Sideeq ce a bayan tasa dan haka da gudun gaske ya shiga ciki ya kirawo dr bushrat wadda ta fito da nurses da masu daukan SANAAH din aka fiddota cikin gaggawa daidai nan motar fleet ta parker shima ya fito kawai sedai imran ne ya iso da sauri ya rufe motar daya bari buden ya kashe ya zare key yabi bayansu.

Take akai clearing gurin aka sallami wainda aka gama dasu aka sallami duk wanda ba patient ba daga gurin emergency din tayi tsit securities din fleet suka tare gurin babu me sake shiga idan ba doctors ko nurses ba.

Imran ne ya gyara gurin zaunawan su Fleet din da Dad da aka tanada suka zauna su biyu kadai babu wanda ya furta kalma ko daya shiru gurin yayi musamman da kowannensu maganarsa bame yiyiwa bane a halinda suke ciki dan Raheem har lokacin jikinsa jijjiga yake hannuwansa ya saka a aljihun wandan dayake jikinsa a zaune sbd yanda shi kansa yasan jijjigar da jikinsa yake zai iya komai a lokacin.

Dad kuwa idanuwansa ne suke bayyanarda asalin zallan fushin dayake cikeda kirjinsa da jininsa da bayajin yanada buqatan cewa komai sunyi yanda sukeso zasuga yanda yake so shima shiyasa ko Raheem din bai kalla ba dan kuwa haukar da matarsa take taqama da ita ba laifinta bane dama aka bata ta hakan dan haka mamaki zai basu matiqar wani abin ya samu SANAAH.
#MAMUH
09033181070
[16/06, 12:47 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

119
Fleet ma a yanda zuciya ta gama cinsa baya buqatan cewa komai ko aikata komai dan lamarin bazaiyi kyau ba dan hakane shima shirun yake yana fatan kada Allah ya kawo abinda Meenah zata bayyana a gabansa a daidai yanxu harma zuwa lokacinda zai dawo daidai dan kuwa a yanxu shi kansa yasan ba shi din bane komai mai muni zai iya faruwa.

Su Dr Mum ne suka iso cikin tashin hankali da tsananin damuwa kirjinta kaman zai fado kasa sbd bugawan dayake ba daidai ba tension din da sukaji ya daki jikinsu da kirjinsu na zaman da Dad da Fleet keyi a gurin ya daka babu wadda ta furta komai a cikinsu gurin zama aka tanadar musu suka zauna suma gurin ya sake daukan tsit manyan gynae doctors na asibitin na ciki da SANAAH.

Acan gida kuwa da qyar kafafuwa na rawa Hajiyar Samad ta isa palonta hannunta riqe da nasa suna shiga ta sakesa ta juyo tareda sauke masa wani mahaukacin lafiyayyan mari tana bude bakinta dayake rawa da jikinta na tsananin tsoro da tashin hankalin mutuwan data shaqa a hannun Meenah a rikice tace

"Bansan cikakken mahaukaci na haifa na shayar ba sai yau"

Wani kallo ya mata idanuwansa jajir yana jin duniyarsa gavaki daya ta kama da wuta ya mata wani kallo idanuwansa jajir sbd a lokacinda Meenah taso kashe SANAAH motsawa yayi da niyar shiga ciro SANAAH duk da tana cikin tsakanin rayuwa ko mutuwa daga shaqar da Meenah tai mata ta saketa bata iya ko hadiye yawu a rikice jikinta na wani irin rawa ta damqosa ta jasa da wani irin rudani sukabar gurin ko gani batayi sosai kafin an ankara dashi dan kuwa babban fatarta Allah yasa babu wanda ya lura dashi a gurin sbd idanuwan kowa ha rufe.

Wani tiriri da daci ya hadiye yana cewa

"To wai me kike nufi dani ne?
Na saka ido ina kallo SANAAH na rasata kenan ko me?
Haryanxu babu tabbacin Fleet ya karbeta hakama ni ko a hakan ina son aurenta yanzu"

Turesa hajiyar tayi ta wuce kanta na tsananin juyawa ta kafafunta har lokacin wata tsananin rawa sukeyi dan kuwa ta shaqu shaquwan data saddakar da rayuwa a hannun Meenah.

Shi kansa Samad din fitowa yayi yayi rai bace ya koma bangarensa yana jiran abinda zai biyo baya da safe.

SANAAH ta farfado amma da wani irin azababben ciwon mara mai tsananin gaske daya sakata cikin mawuyacin halinda duk yanda doctors suka tsaida cikin Allah bai nufa ba haka cikin ya zube akan idonsu wanda ya saka sai da aka buqaci jinin saka mata dan lamarin baixo da sauki ba sam jini mai yawan gaske ta zubar.

Lokacinda dr Akin ya fito ya kallesu da asalin sanyin jiki da tausayawa tareda rashin boye boye tinda aikinsu ne kuma dole haka kowa zai hakura ya rungumi kaddarar kallan fleet yayi yana tsayar da idanuwansa akansa da nutsuwa ya bude baki yace

"Saidai ayi hakuri amma cikin jikinta ya riga ya fita kuma tana buqatan jini da gaggawa"

Tsit gurin yayi babu wanda ya iya motsawa tsabar shock da wani irin baqin cikin duniya daya rufe gabaki dayansu Maamah hawaye ne masu zafin gaske suka gangaro mata ta sauke kanta ahankali dr Mum kuwa jajir idanuwanta sukai kirjinta yayi nauyin gaske har numfashinta na dan toshewa ta dan yaga wuyan hijabinta da hannunta daya sbd shaqewa dataji tana yi zufa na jiqota tako ina.

Fleet kuwa da saida ya sauka a airport ya samu sakon sakamakon SANAAH din daga dr bushrat wanda ta turo baizo ba sbd suna hanya dan haka yana sauka qasar Nigeria din sakon daya fara samu kenan wanda ya sakasa jin duniyarsa ta tsaya cak babu abinda yakeji bayan shiru da tsit sbd abu ne daya dade da cire rai da saddakar da sake samu har abada wato wani jinin nasa a duniya,

Zuciya da idanuwansa babu abinda sukaji duk duniya suna buqatan ji da gani bayan SANAAH KHALIL da cikinsa yake jikinta amma

Please Login or Register in order to submit comment