Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gyara gashi masu inganci da kyau wanda mukeda guarantee dinsa,
Kowace irin turaren wuta na asali na gasken a gurinta ne zaku samu wanda qamshinsa kam har nesa da maqota hakama babu kalan dilka ta gyaran fata data fuska da babu a gurinta,
Kada kubi labari kawai ku siya ku gwada..SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387.

***********
Dad kai tsaye tafiyarsa tareda SANAAH da Dr Mum zaiyita sbd bawa SANAAH daman tafiya itama ta dan samu fita damuwan data kasa cirewa kanta na kunyar kowa da Fleet din da sam ta kasa barin su tsaya a gaban juna.

A nasa bangaren tafiyar tasa shima ta gama kammaluwa dan haka shine ya fara tafiyarsa tafiyar da basu hadu ba sbd ya bari ta sake samun time din kanta ta shirya barinsa ganinta da kansa wanda yake cikin wata irin nutsatsiyar matsuwa da damuwan rashin ganinta a gabansa a cikin idanuwansa dan haka tafiyar shima zata sake saka kansa warwarewa daga wannan damuwan dayake ji na sanin suna gida daya suna rayuwa batareda ganin juna ba.

Bayan tafiyarsa da kwana biyu suma tasu tafiyar ta gama haduwa dan haka suka shirya suka daga aka bar Maamah da mommy wainda zasu tafi Umrah daga can kila zasu iya biyawa kila kuma su tahowansu gida.

Tafiyar SANAAH da Dad da Dr Mum tafiya ce da dukansu suke jinta kaman wata sabuwar rayuwar da bazasu iya hadata da kowa da komai ba sbd tabbatarda cikin dayake jikinta wanda yake 'da ne a gurin 'dansu 'dan da shine jininsu a hade guri daya,
'Da ne da suka riga suka gama sani da tabbatarwa shine daya tak da Allah ya mallaka musu duk irin tsananin son da sukewa juna sunsan bazasu taba samun wani arzikin daya wuce wananna dinba da suka samu kuma suke fatan cigaba da ganin nasa yayan.

Tafiya ce mai sanyi da nutsuwa da tsari da asali rashin hayaniya da wata sanyayyar kauna wadda take gudana a tsakaninsu da ita kanta hakama dayake dukansu a waye suke ilimi da hutu ya ratsa rayuwarsu babu ruwansu da abinda yake gudana a tsakanin junansu sbd soyayyar Dad da Dr Mum din fili take suke kuma dan nunawa ba tareda jin damuwan SANAAH ba hakama itama SANAAH din bata damu ba sam bata ma wani ji abin wani iri ba bayan jin hakanma yana sakata jin damuwanta na dan tafiya sbd tana farin cikin ganinsu a tare sosai dan haka koda sukai kwana biyu a wata qasar kafin suka iso italy babu wanda yaji takura hankalinsu kwance yake musamman Dad dayake jin rayuwansa ta samu nutsuwan da babu a cikinta babu kowa a tare dasu babu kowace damuwa da tashin hankali da hayaniya daga nutsuwa sai kwanciyan hankali.

Ranar da suka iso italy Al'amin ne da kansa yazo airport daukansu da wata motarsa daban kuma BMW X5 fara yana sanye da wasu Ash D&G da fcap bai sako glasses ba sbd girmamawa ga wainda yaxo daukan dan haka koda ya fito ya tarbesu tin daga nesa Dr Mum ta sauke idanuwanta akansa tana sauke ajiyan sbd a take taji zuciyarta ta sake aminta dashi dari bisa dari ga Fammah dan haka da murmushi dukansu mai tsananin kyau da kulawa tareda nuna farin cikin ganinsa suka sake musamman Dad daya miqa masa hannunsa sa sakewan dake tsakaninsu bada shekaru ko matsayiba yace

"Daga karshe dai Mr Al'amin khalil a gabana"

Murmushi mai kyau da asalin nutsuwa Al'amin ya sake yana kallan Dad din da sakewa da kaman amintar dake tsakaninsu ba shekarunba yace

"Welcome to italy Sir Jeerah"

Dariya Dad din ya sake mai tsari suna kama hannun juna da kyau da murmushi akan fuskansu sosai.

Dr Mum data shiga mamakin irin wannan kusancin da shaquwan tasu kaman babu duba matsayi da shekaru a cikinta burgeta hakan yayi taji wani farin cikin ganin ba qaramar kauna da soyayya Dad kenan ya nunawa Al'amin ba da sukai irin wannan kusanci da sakewan da babu a tsakaninsa da yayansa daya haifa.

Cikin girmamawa sosai yana kasa kallanta sosai Al'amin ya juyo ya kalleta yana bude baki da kulawa da nutsuwa da rashin hayaniyarsa ya gaidata yana mata sannu da zuwa ta amsa tana jin kaunarsa sosai na qaruwar mata dan kamewansa da nutsuwansa a bayyane take.

SANAAH datake kallansa ya kalla yana sake mata murmushi me sanyi tareda bude mata hannu ta shiga jikinsa tana sake murmushi da farin cikin data kwana biyu rabonta da shiga.

Juyawa sukai suna dunguma mota a motarsa ya dauki Dad da Mum da SANAAH dake gaba zaune sai Mr Sideeq ya shigo wata motar tareda kayansu suka nufi kai tsaye masaukin da aka tanadar musu na wani sabon gidan dayake kusa da gidansa sosai.

Suna isa gidan da komai da aka tanadar masa na luxury yayi daidai da tsarin da zasu iya rayuwa mai dadi da tsari a ciki dan haka kai tsaye komai aka shigar dashi dakin Mr Sideeq yana can harabar gidan daga gefe daya shima babban room and bathroom mai kyau da girma.

SANAAH ma da dakinta a palon farko sai palon kurya dayake dauke da master bedroom da wani dakin daya daban nasu Dad din da Matarsa.

Daman hutawa daga tafiya Al'amin din ya basu yana tafiya yabarsu zuwa anjima tukuna.

SANAAH wanka tafara yi sbd mutuwan jiki da rashin karfi takeji so tana shiga ruwan zafi ta saka ta fara gasa jikinta sosai kafin ta fito tayi sallan Azahar da time din yayi ta kwanta take bacci mai karfi da dadi ya dauketa bata farka ba sai yamma tana bude idanuwanta ahankali da fammah dake zaune a gabanta tafara cin karo tana zaune ta zuba mata ido tana mata wani sanyayyar kallo mai sanyi da nutsuwa da kulawa.

Itama lumshe idanuwanta tayi ahankali tana sake budewa akan fuskan Famman tana kallan fuskanda take ta narkar da zuciyarta da matar da kaf gabobin jikinta ta sake lumshe idanuwanta batareda ta motsaba ta bude idanuwanta suna cikowa da wasu hawaye masu sanyi tana sauke wata sanyayyan numfashi da jin inama shine a gabanta kaman yanda yace original din ba copy ba.

Fammah da itama kallan SANAAH din takeyi da dukkanin mutuwan jikin rashin ganin Al'amin a kan idanuwanta tsawon kwanaki sbd boyon da sukewa juna yana nesanta kansa da ita sai Dad dinta yaxo ta gansa yaje gurinsa sun hadu shima basu hadu face to face ba bai bari sun kasance tare a gaban na fleet ba sosai ya tafi wanda hakan ya sake sakawa Fleet ganin qimarsa sbd yanda yake kaucewa kowace hanyar da shedan zai iya tasiri akan zuciyarsa da amanar datake kansa na yarsu da suka basa.

Ganin SANAAH a gabanta da asalin kamanninsa akan fuskan SANAAH ya sakata zaunawa tana kallanta da rasa tinaninta da zuciyarta da walwalanta data jima da rasawa akan soyayyar da ita tata wahala ce mai karfi suke sha kawai.

Dauke idanuwanta tayi akan SANAAH tana dan sauke ajiyan zuciya da bude baki daga inda take zaunen tace

"Are you missing him this much ne da zaki mun kuka anan??

Tashi zaune SANAAH tayi ahankali tana kallan fammah da idanuwanta da suka sake marairaicewa tana neman sauko da hawayenta sai kawai ta matso kadan ahankali ta sauko gadon tana zaunawa gefen fammah da shigewa jikinta tana fara mata hawaye da kasa cewa komai sbd harga Allah tayi tsananin kewanta itama datake son fada mata abubuwa da dama amma sbd akan mahaifiyarta ne sai bazata iya fada ba dan wata kusar tafi wata hakama tasan dole har abada bazasu taba komawa yanda suke asalin asali ba sbd uwa ta daban ce.

Rungumeta famman tayi tana dan shafa bayanta da cewa

"It's ok,its ok,Dad ne???

SANAAH batasan lokacinda murmushi ya kufce mata ba ta gyada kai tana sake shigewa jikin fammah din da itama cikin karfin hali tai murmushin tana jin dadin yanda abubuwan suka koma daidai sbd tana waya da mahaifiyarta amma bata fada mata komaiba kaman yanda bata nuna mata komaiba kuma tajita a cikin wani irin sanyi da rashin son hayaniya ko kadan kaman ba itaba hakama Dad din baice mata komaiba shima da alama duka hankalinsu ya kwanta hakama babu labarin kowace tashin hankali da aka kuma yi dan haka takejin nutsuwa da kwanciyan hankali soyayyar Al'amin ce kadai take neman kasheta a cikin sanyi.

Shiru sikai na dan lokaci kafin suka saki juna suna kallan juna da murmushi da farin cikin ganin juna suna fara magana...

SANAAH miqewa tayi tafara shiga bathroom bata wani jimaba ta fito tayi sallah tana idarwa suka fito sbd yunwar SANAAH.

Dining a cike sika samesa Al'amin ya aiko da komai an jere a dinin da fresh fruits dan haka suna sallan magrib gabaki dayansu da Dad da Mum sukai dinner cikin kulawa da kauna.

Suna gamawa daki suka shige suna shigewa Fleet na shigowa gidan sanye da fararen Diors Da suka maidasa kaman sabon matashin da rayuwarsa take cikin shekarun rashin hayaniya da hutu.

Fammah Dr mum taje ta kirawa ta fito Su Dad sukai magana da ita sosai suka kuma tabbatarda raayinta akan aure ta kasa fada musu komai saidai mahaifiyarta datake nuna musu ayi magana da ita wadda jinta kawai Dad yayi yana yanke shawarar ma kawai bazaa jira komaiba zaa daura aurenta da Al'amin din a nan italy idan yaso tana qarasa gama program dinta nan da sati biyar ta koma gida ayi biki acan ta tare kawai.

Dad dinta bai musawa hakan ba dan haka kai tsaye kuwa Dad yanke daura auren Friday nan da 4days kenan.

Fleet na barin gidan Dad ya fara wayoyinsa yana sanar wainda ya kamata su sani musamman Mommy da kansa ya kirata suka jima suna magana itama kai tsaye tayi naam da duk abinda Dad zai yanke akan yayanta tinda shine uba a garesu.

Su Maamah kuwa farin ciki suka shiga mai tsananin gaske suna jin matsuwan ma ta gamo ta dawo ayi biki.

Dr tayi farin ciki sosai da hakan sosai dan haka koda ta sanar da SANAAH take taji duka damuwanta ta tafi farin cikin ganin mutane biyu datake kauna sosai zasu kasance daya.

Washe gari Al'amin a tsanake yazo gidan sanye da Fararen kaftan masu kyau da suka fito dashi wani mutum din daban.

Tareda su yayi breakfast amma banda Fammah da bata fito ba sam dan anan ta kwana tama dawo nan sai ranar da suka tafi kila.
#MAMUH
09033181070
[26/06, 4:09 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

147
*_SHUWA INCENSE AND MORE_*
07042293387/09118783317
Ina masoya kamshi da gyaran jiki na asalin matan da suka amsa sunansu mata?
Kinaso/kunaso ku kasance a cikin kamshin da duk inda aka jisa a tattare dake ko gidanki sai ankasa hakuri an tambayeki?
Shuwa Incense And more itace karshen inda zaki samu asalin kamshi da abubuwan gyaran jiki da mayukan gyara gashi masu inganci da kyau wanda mukeda guarantee dinsa,
Kowace irin turaren wuta na asali na gasken a gurinta ne zaku samu wanda qamshinsa kam har nesa da maqota hakama babu kalan dilka ta gyaran fata data fuska da babu a gurinta,
Kada kubi labari kawai ku siya ku gwada..SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387.

***********
Bayan gama breakfast dinsu Dad zaunawa yayi da Al'amin ya sanar masa da komai da suka yanke take Al'amin din ya dago cikin wani irin slow da nutsuwa ya kalli Dad din wani nauyin dayake danne da kirjinsa tsawon lokacinda zuciyarsa take tsananin azabtuwa da son Fammah jeerah yaji yana motsawa da wata irin sabon nauyin yana qara toshe kirjinsa dayake jin rayuwansa bazata taba moruwaba ayanxu idan ba famman ya samu ya mallaka ba a matsayin wadda zai qarasa rayuwa har mutuwa da ita.

A irin kallan da yayiwa Dad da kasa cewa komai Dad din ya hangi wata azababbiyar soyayyar fammah dake cikin jininsa wadda yake riqewa da dannewa da duk wata karfi da jarumtarsa.

Godia kawai ya iya yi a cikeda nustuwa da cikar burin daya kasa yadda da zai cika din.

Wata maganar Dad ya janyo masa wadda sam ya kasa cirewa da dauke tinaninsa akan maganar anbasa auren fammah jeerah zata mallakinsa.

Ganin hankalinsa ya kasa dawowa daidai sam kwata kwata ya sanya Dad din sakin murmushi yana dawowa akan maganar auren wanda zaa daura a kwanaki kadan Al'amin ya zuba masa idanuwansa yana bin kowace kalma da lafiyayyan nutsuwa da bita daga karshe wani murmushin da baisan yama sakeba ya saki yana sake godiyar data saka Dad shiru yana kallansa da murmushi akan fuskansa yana cewa

"Kodai zamu bar daurin auren nan ne sai ta gama an koma Nigeria gabaki daya?"

Kallansa Al'amin yayi yana dariya mara sauti da girgiza kai yana cewa

"No no ai baka magana Biyu"

Dariya Dad yayi yana cigaba da maganar datake saka bakin Al'amin din buduwa yana magana kaman ba shi dinba da babu hayaniya rayuwansa sam.

Sun jima a tare kafin Al'amin ya fice duniyarsa na buduwa zuwa wata sabon babin dabai taba tsammaniba a lokacin.

Kasa iya kiran Fammah yayi sbd baisan tayaya zasu iya magana da juna ba kaman yanda sukai kwanaki batareda ji ko ganin juna ba.

SANAAH ce ta kirasa sukai magana tana tayasa murna fammah na zaune tana duba abu a waya tana jinta tana kuma jinsa shima baisan me zai fadaba sai kame kame yake nasa farin cikin bame iya rawan kai bane jinsa yake har jijiyoyinsa dabai san yaya zai iya fidda abinda yake jin dinba sedai a cikin tsakiyar idanuwansa da zaa iya karanto zazzafan yanayin dayake cikinsu da babu me iya kallan cikinsi idanba fammah dinba kila itama hakan ba qaramar karya garkuwan jikinta zaiyiba idanma ta iya kallan cikinsu kenan.

Shi kansa sanin fammah na tareda SANAAH din a lokacin ya sanyasa kasa kowace irin doguwan magana hakama itama datake jinsu shirun tayi tana sauraron kalamansa da basuda kowace hayaniya.

Da daddare dukansu haka suka gama surutunsu sukai bacci SANAAH na lafewa damuwanta kowane dare na tasowa na rashinsa dake cinta a ciki kaman zai kasheta.

Washe gari fita sukai tareda Dr Mum wadda zuwa wani tsadadden luxury spa da kusan acan suka wuni gabaki daya ana gyara sai dare suka dawo abinci kadai SANAAH taci ta kwanta sbd dan zazzabi da damuwanta datake tasowa ta rashin Fleet wanda shi kasa hakurinsa ya gama qarewa tako wane bangaren babu sauran kowace nutsuwa a tareda shi dan hakanne ma bai sake zuwa gidanba har aka biya sadakin Fammah din wanda Al'amin dinne ya biya da kansa da dollar kuma sun karba.

Washe gari haka suka sake fita basu wuni ba basu zauna ba sai dare dan haka ranar da akai kwana ba uku basu fitaba koina sbd SANAAH da sam ta kasa jin dadi duk da tayita daurewa sbd kada ta hana komai na hidimar.

Har ayau da ake gobe daurin auren Fammah da Al'amin din basu hadu ba bare yin magana sbd a nasa bangaren ya kasa iya zuwa ganinta sbd nasa son mai zafine da yake rasa kansa gabaki daya idan yana ganinta dan hakanne ya saka yake nesanta da ita tin farko sosai,

Ko a yanzu dazai mallaketa jin yakeyi bazai iya kasancewa a guri daya da itaba har sai anyi bikin da ake buqata an basa ita gidansa.

Wunin ranar gidan da wani irin farin ciki sosai harda Sammy ma tana gidan da wasu abokan karatun famman data hadu dasu anan suka wuni sai dare suka watse.

Washe gari da wani irin mutuwan jiki rashin sanin tinanin yi fammah ta tashi sbd Mum dinta batai maganar aurenba kuma ita ta kasa sanin yanda zata fada mata karshe dai Dad ne ya kirata ya zaunar da ita ya sanar da ita ya kwantar mata da hankali da sanar da ita sai bayan daurin auren kafin ayi biki ta tare zaa kaita gaban mahaifiyarta a fahimtar da ita komai.

Sosai ya kwantar mata da hankali harta samu nustuwa ta fito ta dawo daki tana jin zuciyarta na bugawa da sabon bugu mai sanyi da nauyi na rayuwar da zata hau kanta ayau da zata xama matar wani itama.

SANAAH cikin kulawa da kauna da jin ranar itama har cikin kirjinta zaunawa tayi gefen famman tana dan kwantawa jikinta tace

"Zakiyi rayuwan farin ciki mai dorewa da Yaya Al'amin insha Allah sbd yana miki son dabai san iyakansaba son da baisan yaya zuciyarsa zata iya daukaba"

Numfashi famman ta sake tana hadawa da ajiyan zuciya tareda zubawa SANAAH din idanuwanta sbd batasan me zatace ba dan ita kanta jin takeyi kaman kirjinta bazai iya daukan abinda zuciyarta ke ji ba akansa hakama wata irin kunya ce mai tsananin girma da tarin yawa a tsakaninsu da basusan tayaya zasu fara fuskantar junaba.

Acan Nigeria ma yau da wata farin ciki da hidima sosai suka tashi sbd daurin auren duk da ba anan zaayiba hudimarsu sukeyi sosai da farin ciki sosai musamman Mommy datake jin farin cikinta sosai sbd Al'amin shine nata SANAAH kam tasu Dr Mum ce da Dad dinta Dad jeerah dan haka hidimar gaske sukeyi da biki wanda sukai gayyata sosai.

A bangaren Fleet kuwa mutanensa manya da dama tini suka sauka a qasar tin daren jiyan duk da a kurarren time suka samu gayyatar wadda kusan saida labarin daurin Auren yarsa din ya fita dan haka a take manya da dama suka fara sauka a qasar italy din dan haka baqinsu sosai suka sauka.

Su Abbu ma sun sauka qasar da asuba tareda su Barr Shakur harma da matarsa da yarsa daya.

Karfe 1 zaa daura auren dan haka kusan duk wanda yazo ya halarta babban mosque din da zaa daura larabawa da turawa ne kawai ke shigowa tako ina cikin shigar alfarma da zallan daula dake nunawa daga kowa tako ina.

Al'amin ango tareda Dad suka iso sbd Dad din ne ya biya ya daukesa motar abokansa suka biyo bayan motarsu da Dad din suka iso gurin yana sanye da wani sky blue tsadaddiyar yadi mai tsananin taushi daya zauna akan farar fatarsa da hula da yayi wani irin lafiyayyan kyau asalin Al'amin dinsa ya fito matashi mai ji da kyau da ilimi da hutu da nutsuwa da kamun kai.

Motocin fleet ne suka iso da securities dinsa bayan isowansu Dad din wanda ya fito cikin motar da Imran ya bude masa yana sanye da wani Navy blue tsadaddiyar cashmere yadi a jikinsa daya fidda haskensa da kwarjininsa daya cike gurin tareda wata kamewa fuskansa na fidda wata freshness da nustuwa da calmness tareda izza.

Imran ma fararen kaftan kayane a jikinsa na wani lafiyayyan luxury yadin shima da hular da ita kanta fiddo wani kyansa tayi.

Babu bata lokaci aka daura auren AL'AMIN KHALIL da FAMMAH RAHEEM JEERAH da mutane da yawa suka sheda akan sadakin dala....

Ana gama daurin auren wata lafiyayyar reception luch sukai wadda acan ne hotunan daurin auren suka fita media aka qara sanin da daurin auren jeerahs din da akai a italy daganan kira yafara zuwa tako ina.

Acan gida ma bayan daurin auren farin cikin kowa karuwa yayi suna miqawa Allah dukkanin godiyansu.

Fammah kasa kowace hayaniya tayi tana daki a lafe itada SANAAH duk da su Sammy na gidan har sai magrib kowa ya watse gidan yayi tsit Anna ta sake gyara koina gidan aka kunna kamshi tareda jere abinci lafiyayye a dining da aka hada sbd anan zasuyi dinner yau hadda Fleet da Al'amin din tareda Dad dasu.

Bayan angama jere komai Dr Mum ce ta fito ta leqo dakinsu ta tadda SANAAH tana wanka fammah kuma tana zaune itama ta fito wankan.

Shigowa tayi ta tayata shiryawa tana nuna mata kulawa sosai da wata tarairayanta sbd tin yanxu tafara kewanta duk da dai auren gida ne duka.

Ficewa tayi tabarsu su qarasa shiryawa.

Doguwan fitted rigar data lafe a fatar jikinta dake sheqi tana daukan idanuwa fammah ta saka dark army kala data fiddo haskenta sosai da kuma sheqin datakeyi hadda yar ramarta sai veil daya daj nada tana rufe wuyan rigar dayake V kuma ya shiga qasa sosai.

Koda SANAAH ta fito a kasalance ta shirya tanajin kaman bazata iya fita cin abincinba amma tana jin yunwar da babu yanda zata iya kwana bataci abinci sosaiba.

Straight skirt daya kwanta a jikinta itama ta saka da riga light pink mai kyau daya fidda itama hasken data qara sosai sbd cikin dayake jikinta.

Itace ta fara ficewa zuwa kitchen ta dauko sauran guava drink din data saka a fridge tana kokarin fitowa taji kamshin data dauko kwanaki batajina ya ratsi hancinta zuwa kirjinta dataji wani irin mutuwan jiki na shigarta ta dago idanuwanta ahankali tana kallan kofa da jin bugun zuciyarta na sauyawa zuwa wani mai tsananin sanyin da idanuwanta suka kawo wasu hawaye masu sanyin gaske.

Kasa motsawa tayi saida ta dauko mintina biyu a gurin kafin ta dago kafafunta ta sako kai ahankali ta fito daidai fitowan fammah suka qarasa dining din a hankali a natse da wata nutsuwan da babu wadda ta iya dagowa.

Dad da Fleet da Al'amin da Dr Mum ne a dining din dukansu a zaune...
#MAMUH
09033181070
[27/06, 7:17 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

148
*_SHUWA INCENSE AND MORE_*
07042293387/09118783317
Ina masoya kamshi da gyaran jiki na asalin matan da suka amsa sunansu mata?
Kinaso/kunaso ku kasance a cikin kamshin da duk inda aka jisa a tattare dake ko gidanki sai ankasa hakuri an tambayeki?
Shuwa Incense And more itace karshen inda zaki samu asalin kamshi da abubuwan gyaran jiki da mayukan gyara gashi masu inganci da kyau wanda mukeda guarantee dinsa,
Kowace irin turaren wuta na asali na gasken a gurinta ne zaku samu wanda qamshinsa kam har nesa da maqota hakama babu kalan dilka ta gyaran fata data fuska da babu a gurinta,
Kada kubi labari kawai ku siya ku gwada..SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387.

***********
Wani kallon datake jinsa ne yana ratsawa da kutsawa cikin kowace hanyar tsigar jikinta zuwa cikin jininta taji yana sauka akanta daga idanuwansa da suke cikin wata lafiyayyar kewanta da kadan ya rage tayi ajalinsa dan kuwa bai taba samun cikakkiyar nutsawan tinaninsa da kwakwalwansaba harma da gangar jikinsa a tsawon kwanakin daya share batareda sakata a cikin idanuwansaba tin a Nigeria ya dago dago manyan fararen idanuwansa masu kyau da kwarjinin gaske da sukai wani qasa da wata laushin da baa ganewa ya sauke mata su a wata slow da kamewan da kusan ko iyayensa dake gurin saida sukaji tension din sbd dagowansa ya kalli abu kai tsaye wani abu ne daba dabiarsa ba amma yanda kai tsaye ya dago din yana saukewa SANAAH su saida ya saka Dr mum juyawa ahankali ta kalleta taga kanta a qasa yake bata dagoba sbd a nata bangaren tana dagowa ta kallesa zata iya kasa riqe hawayen tsananin kewansa dake kasheta a kowace daqiqa a wannan lokacin.

Takowa suka qarasa yi suna isowa suka zauna,

Fammah ce ta iya dago kanta ahankali da wani irin sanyi itama tana sauke idanuwanta akan mahaifinta da sai a lokacin ya iya dauke zafafan idanuwansa da wani irin slow daga kan SANAAH wadda taja wani irin numfashi mara sauti ko daya tana jin dukkanin jikinta na mutuwa da wata irin zafaffiyar soyayyarda duke take neman raba ruhinsu da kowace irin nutsuwa da kuzari.

Akan fammah ya sauke idanuwansa da suka sauya a take da wani irin dumi yana dan tsayar da idanuwan nasa akan fammah wadda ta bude baki ta gaidasa tana jin itama jikinta na wata irin mutuwan da daqyar ta qarasa gaisuwan sbd saukan da idanuwan Al'amin sukai akanta da nasa slow din sbd kasa riqe kansu sukai daga sauka akanta sbd muryanta datai masa wata irin ratsa a kunnuwa duk da ya hana kansa kallanta dan riqe composure dinsa a gaban mahaifinta da Kakanta amma muryanta kadai yanke duk wata iyakar jarumtarsa da kamewansa tayi saida ya dago ya kalleta yana sauke wani lafiyayyan numfashin da baida sauti ko daya.

Muryan Fleet din a coshe take da maqoshinsa da yawu ya dauke masa a take da idanuwansa suka sauka akan SANAAH da wata deep strong voice ya amsa gaisuwan yana qin kallan inda SANAAH take tareda sake kamewa da kulawa.

SANAAH dince ta bude bakinta cikin sanyi da sautin daya sakasa dan dagowa bai kalletaba amma ta gaidasa a taqaice tana kin kallansa itama sedai wata ajiyan zuciya me sanyi data sauke mai dan sautin daya isa har cikin kunnuwansa ya bude baki da rashin hayaniya ko kadan ya amsa.

Fammah data rasa yanda zata iya gaida Al'amin shiru tayi kawai tana kasa cewa komai ana dake kawo sauran kayan qarasa jerawa tayi tana barin gurin Dad jeerah na fara magana da Al'amin wanda kowace lissafinsa ta kunce amma ya riqe nutsuwa da kamewansa batareda ya sake kallan inda fammah take ba dan hakan nada damuwa.

SANAAH ce ta miqe a natse tafara serving Dad da Dr mum kafin ta iso gefensa cikin sanyi ta tsaye tana fara serving nasa

Please Login or Register in order to submit comment