Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanayin yayi mata dum kanta ya sara da karfi har saida ta dan lumshe idanuwanta ta bude ta rasa abinyi ko fada ta sauke wata sanyayyar numfashi mara sauti tareda bayyanarda karfin hali ta miqa tana daukan tray din ta fice Dad ya saka mata albarka yace ta tafi.

Duk takunta daya kaman ta dauko dala ba gammo take jinsa harta fice.

Bayan ta fito iska ta dan dakata ta shaqa a natse tana jin bata buqatan bawa kanta kowace irin wuya akan auren wanda bata sansa ba baisanta hakama kaman yanda komai na auren baya gabanta tasan hakanne a gurinsa tinda yanada iyalinsa dayake so hakama itama bata buqatan rayuwa a gurinda baa buqatanta sam koma zaa mata kallan baquwa a cikinsu ko bare.

Numfashi ta kuma fitarwa hankalinta a kwance batareda jin komaiba ta nufi bangaren da bata taba zuwaba dan kuwa komai yanda suke da fammah bata taba rakata gaida Dad dintaba hakama sbd wani irin matsayi da girman da Dad dinta yake dashi a gurinta da rayuwanta ya saka ko baya ganinta bazata iya saba umarninsa ba ya saka kai tsaye ta tafin.

Ko data isa bangaren tsit hanyar babu kowa sai securities dinsa biyu dake gadin hanyar gurin suna ganinta suka kira Imran a waya dan sanar dashi daidai lokacin shima Dad ya kirasa da kansa ya sanar masa wacece SANAAH din dan haka kai tsaye yace su barta ta wuce.

Ko data iso basu tsaida ta ba hanya suka bata cikeda girmamawa ta wuce ta isa kofar kafin ta miqa hannunta zatai knocking imran daya iso ya rigata isar da hannunsa ya bude mata da kulawa da girmamawa mai girma yana kasa mata cikakken kallo na rashin Daa yana danne dukkanin mamakinsa na ganin yarinyar datake daidai fammah a matsayin matar da aka daurawa aure da Fleet da kansa.

"Thank you" ta bude bakinta a tsanake ta furta masa tana daga kafarta cikin nutsuwa ta saka a cikin palon wanda niimtaccen kamshinsa ya daki fuskanta ta dan dago fuskanta ta kalli cikin palon wanda yake tsit tsarinsa da kalar datake palon yake na turawan da basa son hayaniya.

Imran daga waje rife kofar yayi yana barin gurin ita kuwa saida ta dan yi seconds a gurin tsaye kafin ta hangi hanyar Dining dan haka ta daga kafafunta ta nufi gurin tana isa ta ajiye tray din hannunta bata tsaya komaiba kawai ta juyo tareda saka kai kofar fitowa daga dining room din wanda yayi daidai da isowansa zai sako kai shima take suka kusan wata irin haduwan data sakata yin baya da wani irin karfi tana dago fararen idanuwanta a lokaci daya ta saukesu akan wanda yake gabanta fuskanta a kame ajinta da kamewanta na bayyana gabaki daya.

Akan kyakkyawar fuskarsa datake fidda wani irin hasken asalin kyau da kwarjini da wata irin kamewa da izza tareda girman da dole ka sadda kanka idan ka kallesa idanuwansa da suke da wani irin haske da saka faduwan gaba shima sun sauka akan fuskanta kai tsaye yana kallanta a karan farko na rayuwarsa kaman yanda itama karan farko kenan da idanuwanta masu kyau da girma suka sauka akansa.
##MAMUH
#HIS FIONA
#BEST LOVE
#AGE GAP LOVE
#CRAZY COUPLE CHEMISTRY
#FLEET RAHEEM JEERAH
#SANAAH KHALIL
#MEENAH WAHAB
#SAMAD JEERAH
#DR MUM
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

49
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki  Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki  Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce  For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Kamshinsa ne ya rikida niimar gurin tareda shiga hancinta direct sbd yanda suke kusa wanda ya sakata dauke fararen idanuwanta daga kansa ahankali tana dan sake ja da baya cikin nutsuwa da sake dagowa a natse ta bude baki ta gaidasa sbd basa girman mahaifin Fammah cikin sauti mara hayaniya ko fitowa sosai.

Shima dauke nasa kallan yayi daga fuskanta datake kokarin bayyanar masa da kamannin da har abada bazai manta ba amma bazai iya mata kallan tsaf ba sbd kasancewanta yarinya sosai a gurinsa dan haka ya amsa gaisuwanta a taqaice tareda qarasa shigowa dining room din yana kallan table batareda ya sake kallan inda take ba itama data so fadan Dad ne ya aikota sbd clearing tinanin ganinta a nan amma ganin hakan sai kawai taji ma babu buqatan bayanin dan haka ta fice kawai bama tareda yaji ficewan nata ba sbd rashin hayaniyarta ko a gurin tafiya.

Tana fitowa daga bangaren taji ta sake cire lamarin auren kwata kwata daga zuciya da kanta dan haka ba damuwan komai ta isa bangarensu ta fada bedroom fammah dake waya da Mum dinta ta dago tana kallanta da kulawa tace tazo ta gaida da mum din.

Bataji komaiba cikin girmamawa ta dan bude bakinta ta gaidata a matsayin Mahaifiyar Fammah kuma itama kaman uwa a gareta.

Suna gama wayar karatunta suka fara yi da fammah suna shiga wata firar akan karatun bar lokaci yaja suka kwanta.

Washe gari Fammah dataje bangaren Dad dinta taga tray na teaset din da SANAAH take kaiwa Dad a kan dining din Mahaifinta tayi mamaki amma kuma sai tayi tinanin daga gurin Dad dinsa ya taho dasu sai ta tattara ta koma dasu bayan ta jere masa breakfast dinsa.

Bata jira ya fitoba sbd time na fitowansa baiyiba dan haka ta juya ta fice sbd tareda SANAAH zasu fita yau.

Tana komawa shiryawa tayi sukai breakfast a dining su biyu kawai sbd mommy ba yanzu zata fitoba itama.

Ficewa sukai da motan SANAAH zuwa school.

Exams din safe tayi tana fitowa suka sake shiga wata a jere daga nan ta gama ta ranar dan haka kai tsaye shopping din dazasu ke buqata suka wuce.

Siyayya sukai sosai ta abubuwansu na mata da kayan hausa da Fammah din take shaawa su atampa kawai batason lace tace zai dameta so laces din da suka siyo baifi guda uku ba suma masu tsadan gaske ba nauyi ba ado da yawa suka bayar fashion house a dinka suka zube makudan kudi suka dawo da sauran siyayyansu ta tarin undies dasu kayan shafarsu.

Fammah da daddare dataje gurin Dad dinta ta sanar masa siyayyan dinkin da zaayi mata tayi baice komaiba ya qara mata kudi sosai duk da yasan ba lallaiba ne tayi amfani da kayan tinda komawa zasuyi.

Kwana biyu tin daga ranar da SANAAH taje bangaren a bisa umarnin Dad bata sake zuwa gurinsa ba da daddare ta sauya da yamma take xuwa ta gaidasa ta dawowanta dan sam kwata kwata bata buqatan haduwa da mahaifin Fammah dan yanxu wata shaquwa da kusanci ne yake shiga tsakaninsu da bazata iya ma tina auren Dad din fammah ne akantaba.

Fammah ta saki jikinta sosai ta sabu dasu da samun nutsuwa da jin dadi sosai da farin cikin zama acikinsu sbd ta taso daga Dad dinda sai Mum dinta take rayuwa dasu a gida sai masu aikinsu da tsakaninta dasu umarni ne amma anan gashinan tana sakewa hadda safiya datake mai aiki fira da wasa da dariya sukeyi sosai da ita sbd abinda taga su SANAAH nayi da ita kenan,

Samun shaquwansu da kusancinsu dayake qara gaba sosai shine sbd dukansu su biyun babu me kowace kawa ko aminiya a rayuwarta,

SANAAH bata taba yin aminiya ko kawaba duka karatun datai iyakacinta da course mates nata mutunci shikenan hakama Fammah rayuwanta batada qawa ta musamman sai abokan karatunta itama,

Hakan ya saka suke samun shaquwa da kusanci sosai da kuma jin dadin alaqar tasu yanda ya kamata.

Mommy ma yanzu kauna da shaquwa ce sosai tsakaninta da fammah wadda ta zama 'yarta itama dan hakama take nuna mata kulawa kusan fiyeda SANAAH yanux tana cewa itace yar gatanta yanzu.

Duk wani motsinsu Dad na karance dasu dan haka ya kawo ido ya saka musu har akai kwanaki,

Ya gama lura da karantar sam kai tsaye Fleet bai amsa aurenba ba kuma zai amsa ba hakama a shirye yake da yankesa tareda daukan duk hukuncin da zai masa akan hakan amma bazai taba iya ko kallan kawar 'yarsa a matsayin matar da zai iya bawa matsayin macensa ba dan kai tsaye ma kallan babies yake musu.

A bangarensa ya shirya da gaske warware auren kafin tafiyarsa sbd ya bata daman ma samun kula wasu mazan ta samu mijin dazai dace da daidai shekarunta dan haka bai sake ma zaman kowace magana da Dad ba gaisuwa kawai yake zuwa yayi masa ya tafi.

Ana saura kwanaki uku ya koma Fammah ta sanarwa kakanta ita bazata komaba zata zauna anan kuma sbd SANAAH tanajin dadin rayuwa a cikinsu zata koma amma ba yanxu ba tana san ta dan yi rayuwa anan tukuna gashi daman ta gama karatunta kawai dai abubuwan da suka rage mata ne kadan na zama cikakkiyar likita bata yiba zata qarasa idan ta koma kokuma tayi anan.

Hakan yayiwa Dad dadi sosai sbd ta fada masa ne dan Dad dinta bazai iya barinta anan ba ita kadai ba Mum dinta babu shi sbd duk da ta zama budurwa still suna cikin iyayen da suke overprotective.

Dad da daman hakanne abinda yakeda niya sbd riqe fammah anan ne zai saka Dad din nata yawan zuwa yanzu akai akai dan haka kai tsaye ya sanar dashi Fammah zata zauna anan sai ta qara sanin family kafin ta koma kuma itama tana son hakan batason komawa yanzu.

Da farko shiru yayi sbd yanda zancen yazo masa da mamakin yanda fammah zata iya zama a Nigeria ba daya daga cikin iyayenta,
Tinda yafara lura da rayuwan nan din tana shigarta kuma tana jin dadinta yasa yafara tinanin kada tayi raayin xama anan din gashi daga karshe dai tayi.

Baice komaiba akai bayan nuna ba damuwa zata iya zauna din.

Farin ciki da murna tayi sosai dan haka taje har gurinsa tayi masa godia tana cewa zata kula da kanta sosai hakama mommy na kulawa da ita sosai fiyeda SANAAH.

Kallanta kawai yakeyi da idanuwansa masu haske da saka nutsuwa yana sauraronta kawai.

Ana washe gari zai koma ya samu Dad cikin nutsuwa sanye da Ash jallabiya fuskansa da fatarsa sun fidda qamshi da fresh dinsu yana sako kai palon ko shi mahaifinsa yana ganin tsantsar kwarjininsa dan haka yake basa girmamawa so da dama dan haka yanxu ma da nutsuwa yake kallansa harya iso tsakiyar palon ya gaidasa a natse kafin ya zauna a sofa yana ajiye wayarsa a gefensa.

Shiru suka dan yi kafin Fleet ya dago idanuwansa ya kalli Dad wanda saida Dad din ya dauke nasa idon daga kallansa sbd fahimtar maganar Aurensa ce zaiyi ya bude baki ya rigasa furta cewa

"Kafin ka tafi kana buqatan zuwa ga gaisa da mahaifiyar matarka hakama wadda zata riqe maka 'yarka"

A natse Fleet din shima ya bude baki yace

"Ina bada hakuri matiqa tareda fatan zaka mun afuwan hukuncin dazan yanke gameda auren nan bazan iya karbansa ba Dad Allah ya huci zuciyarka"

Shiru Dad din yayi batareda yace komaiba tsawon mintina hakama shima baida niyar qara komai ko sauya kalamansa ya shirya karban fushi da kowace hukuncin Dad din amma aure kam saidai kowa yayi hakuri bazai iya wannan child abuse dinba.

Wani murmushi mai sanyi da dattako Dad ya sauke tareda dagowa ya kalli Fleet da jinjinawa tareda girmamawa batareda yaji komai na bacin rai ba ko fushi yace

"Ba damuwa Fleet ni mahaifinta dana baka aurenta na kuma aura maka ita na gode da bayyanarda hakikanin gaskiyarka hakama zan ajiye wannan kalaman naka na adana maka su zuwa wani lokacin amma dai a yanxu inason ka bawa auren daman wani dan lokaci kankani na xuwa kammaluwan karatunta da fara aikinta to tabbas zan dauko maka su daga adanawan danai maka na baka abinka saika bani hukuncin daka dauka din ni kuma zan karbi 'yata da hannu bibbiyu,
Kuma ina sake maimaitawa dai kafin ka tafi kaje ka gaisa da mahaifiyarta da zata riqe maka 'yarka."

Numfashi a tsanake ya sake tareda bawa Dad din daman dayace wadda daga ita baya buqatan abinda zai sake saka auren kowace macen a rayuwarsa Meenah wahab ta ishesa har karshen rayuwansa.

Fammah Dad ya daga waya ya kira yace taxo ta raka Dad dinta gurin mommynsu su gaisa.

Fammah na jin hakan ta shiga farin ciki mai tsanani sbd daman tana son hakan tinda Mum dinta dai ita tana gaisawa da Mommyn sosai a waya.

Koda fammah ta fito ta isa bangaren Dad jeerah din dukkaninsu sunga farin ciki tattare da ita dan haka Dad dinta yaji ya samu nutsuwan gaisawa da wadda ta bata kulawa da nutsuwa haka.

Qarasa tattaunawa sukai da sallama tareda bada tabbacin kulawa da duk wani haqqin dayake kansa sukai sallama da bankwana ya fice.

Fammah hannunta riqe yake a cikin nasa data saka tana bayyana masa irin kirkin Mommy suka tinkari bangaren imran na biye dasu har kofar shiga palon.
##MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

50
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Itace ta fara shiga Mommy na palon ta sanar mata ga Dad dinta data fada mata zaizo su gaisa ya iso.

Daman kafin ta fita ta sanar mata dan haka take zaune a palon da Hijabinta mai tsayi mai kyau daya fidda kamala da nutsuwanta.

Da murmushi da sakewa a fuskanta ta dan dago tana kallan kofar daya sako kai a natse ya shigo qamshinsa na yaduwa yana sauya niimar palon gabaki daya cikin wata sanyi.

Xaunawa yayi da kamewa da mutuntawa tareda dan dagowa yana amsa gaisuwan datake masa cikin farin cikin sake ganinsa bayan shekaru jikinta na dan sanyi da tinawa da mutuminta amininta Nasir wanda yake abokin shawaranta a komai tinda aka aurota tin tana amarya harya bar duniya shine amininta itama itada Raheem ne aminansa.

Gaisawa sukai batareda ya iya bata cikakken kallansa ba dan kallo ba dabiarsa bane ga mata.

Cikin nutsuwa ta bude baki tace

"Ya su Dr da Maamah suna lafiya kuwa?
Munyita neman hanyar magana dasu muji yaya jikin Maamah tin a baya amma bamu samu ba......

Kalamanta suka sanyasa dagowa da mamaki mai dan tsanani ya kalleta da idanuwansa kai tsaye masu girma da kwarjinin daya sakata sauke kanta cikin jin nauyin alaqar da yanxu itace a tsakaninsu na yana auren SANAAH.

Kai tsaye bai ganeta ba sbd daman ba wani sanin kamanninta yayi ba irin sosai tinda baya qasa kuma bayada sakewa da mutane.

Itama ganin bai ganeta ba tinda ba wani sani a tsakaninsu sosai ya sakata dake murmushi mai sanyi ta bude baki zata fada masa wacece take ya ganeta kafinma tayi maganar da wani irin mamakin daya basa shock mai karfin gaske ya furta sunanta yanda Nasir yake kiranta

"Mommy Zainab??
Is that you?
Mommyn Nasir??

Murmushi ta sake sakewa alaman ita dince

Shi kuwa wani irin bugawa da sarawa kansa yayi yana sake kallanta da dukkanin idanuwansa cikesa da tashin hankali mai tsananin da tin bayan rasuwar Nasir bai shiga irinsa ba ya dan kuwa indai itace mahaifiyar matar da Dad yake magana to batada kowace 'ya a duniya bayan SANAAH din Nasir........

Cak tinaninsa ya sake tsayawa sbd tinawa da sunan matarsa da Dad ya ambata da SANAAH itama.

Fammah ce data je ta janyo SANAAH batareda ta fada mata waye yaxo ba suna shigowa palon tace Dad nata ne yaxo taje ta gaidasa.

Sai a lokacin SANAAH taso tsayawa cak daga gurin amma bataji komaiba kawai dai batada hijab ko rufa me kyau a jikinta riga da wandon bacci ne masu kauri a jikinta da qaramar hulan da bata rufe gashinta duka ba taso juyawa sbd yanayinta amma fammah ta janyota tana cewa

"He is your Dad too kada ki damu"

Magana zatai a lokacin ne mommy ta dago ta gansu tace

"SANAAH zo ki gaidasa mana"

Ambatar sunanta datai ya sakasa kallan direction din a tsanake da wata irin kamewa da nauyin kirji mai tsanani da jin komai ya dawo na yanda duk duniya itace wadda Nasir bai taba hada tsaftatacciyar soyayyarta da komaiba,
Itace Nasir yakewa son da hankali bai taba dauka ba,
Itace matar Nasir daya bar duniya burinsa bai cika akan mallakarta ba,
Itace zuciyar datake bugawa a kirjin Nasir gabaki daya...

Tsayar da kyawawan idanuwansa masu tayar da kowace tsiga ta jikin mutum yayi akanta take kamannin Nasir suka ringa bayyanar masa akan fuskanta da daman can kusan kamarsu dayace sbd jini daya dayake yawo a jikinsu na kasancewan iyayensu uwa daya uba daya.

"Baby SANAAH" itace kalman da Nasir yake fada akoda yaushe.

Kasa qarasowa har tsakiyar palon tayi dan kafafunta da suka riqe a gurin sbd idanuwansa dake tsaye cak akanta suna tada tsigar jikinta daya bayan daya ahankali sbd kallo ne da babu wanda ya taba sauke mata irinsa batareda kowace kalma ko motsi ba.

Fammah daman ta juya zuwa kitchen dan hadowa Dad din tea din dazata bisa dashi suyi bankwana daga can.

Ahankali ta dan dago babu kowane sauyin yanayi a fuskanta na jin komai bayan jikinta dayake gazuwa da karfin kallansa bata kallesaba da muryanta mai aji ta gaidasa a taqaice.

Dauke idanuwansa da sauya zuwa yanayin da babu wanda zai gane idan ba wanda yayi masa sanin gaske ba ya amsa a taqaice shima yana maida hankalinsa kan mommy SANAAH kuwa juyawa tayi tabar palon tayi kitchen gurin fammah dan saka mata hannu a aikin da ba wani iyawa tayiba.

A cikin tsanaki ya sanar da Mommyn yayita sakawa nemansu amma sam ankasa samar masa da address dinsu,

Numfashi mai nutsuwa da murmushi akan fuskanta daya kasa yankewa ta fara sanar masa ai gobara sukai har so biyu suna sauya gurare daga karshe ma sbd rashin muhalli akan gobarar ya saka Dad jeerah dawo dasu nan ya tura Al'amin karatu ma harya gama aiki yake kokarin farawa acan.

Bata sanar dashi mummunan kaddarar data dawo dasu nanba da sanin da sukaiwa Samad yayi musu ba sbd ba buqatan tinawa ma bare wanda yake auren SANAAH din yaji.

Kai tsaye abinda yayi niyar yi ne idan ya samesu yaji daga bakin nata dan haka yaji dadin hukuncin mahaifinsa na dawo dasu nan.

Ya sanar mata Maamah suna lafiya kuma insha Allah zai sanar musu da yasamu ganinsu sbd suma acan sunata neman hanyar da zasu samesu.

Sam baiyi tinanin bata numbern su Maamah dinba kaman yanda bai buqaci tata ba sbd akwai matsala ma kwance kenan a qasa mai girma da nauyi a yanzu dayasan matar rabin jikinsa Nasir ce yake aure,.

Tayaya zai iya yankewa ya datse igiyoyin aurensa daga macen datafi kowace mace daraja da girma a zuciyar Nasir bayan iyayensa?
Tayaya zai iya maida Baby SANAAH din Nasir bazawara??
Dad yana sane ya aikosa haduwa da mahaifiyarta dan ya san wacece yake aure,
Dan yasan matar Nasir ce ta yanda zai fara kokuwa da kalamansa daya furta tareda hukuncinsa daya gama yankewa.

Kasa iya qara wasu sekanni yayi yai sallama da mommyn yafice bayan ya ajiye mata kyautar kudin dollars sbd baida naira sam.

Bayan fitarsa fammah binsa tayi da tea din SANAAH kuwa bedroom ta nufa ta fada gado tana janyo wayarta.

Fammah bata dawoba sai dare sosai tini SANAAH tayi bacci lokacin.

Washe gari da Asuba motocin Fleet suka bar gidan zuwa Airport da securities dinsa da Samad wanda ba zama zaiyiba shima babu bata lokaci aka gama komai jirginsa ya tashi yabar Nigeria zuwa Ethiopia wanda daga can zaibi jirgin Morocco zuwa ga mahaifiyarsa dake jiransa cikin zazzafan yanayin da zuciyarta tarasa nutsuwa tin daga ranar da Alh Hakeem jeerah ya sanar da Maamah a waya cewan 'danta yanada wata matar da Hakkinta yake kansa a Nigeria tayi masa fada.

Kafin Maamah da ita kadai yake communicatin a Morocco sbd itace uwar Nasir da Raheem a gurinsa sai data shiga mummunan shock da tashin hankali mai tsanani ta sanar da Dr Mum wadda a ranar sai da akai mata awon bp da dubawan likita sbd matiqar tana raye babu rayuwar qarin aure da kishi a gida da rayuwar Raheem.

Take ta fahimci dan ta sanine Hakeem din ya sanar da maamah maganar aure. Da yayi shekaru sai yanzu suke ji dan haka ta dauki mugun zafi sosai taiwa Raheem din kiran kai tsaye da umarnin ganinsa dan batason ma matarsa ko kowa su san da maganar auren wanda zaa gamasa batareda ma anfarasa ba dan wlh akan raba auren shirye take tsaf da isa qasar Nigeria bayan shekaru.

Kwana daya sukai a Ethiopia jirginsa ya daga zuwa Morocco wanda ya sauka a tsakiyar dare amma motocin da zasu daukesa shi da securities dinsa sun airport din tini.
#MAMUH
09033181070

GANIN IDO 2026
Mamuhgee

51
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki  Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki  Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce  For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri

Please Login or Register in order to submit comment