Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Bayan sallamosa din duk yanda suka so ya sake hutawa kafin komawa kowane aikin wahala sam baida wannan lokacin yake gani sbd buri ne a kullace cikin ransa da idan bai cikasa ba zai iya mutuwa sbd baqin ciki da zafi,

Baida niya ko daya ta yafewa AA abinda yayi musu sbd ya shirya bin haqqin abinda yayi musu daga nan har kotun qoli koda zai rasa ransa saiya tabbatarda anbi musu haqqinsu koda basu da komai indai hukuma na aiki.

Dan haka koda yayi jinyar kullum da wannan kullin baqin cikin yake kwana yake wuni sbd kusan hakan ya ruguza rayuwarsu gabaki daya wadda suka debo shekaru suna ginawa cikin aminci da tawakkali da gwagwarmaya,

Ga mommy yanzu ta riga ta rasa lafiyarta kila sbd hakan,

Ga anguwan yanzu sunaji suna gani yi akeyi dasu komai fada akeyi akan SANAAH dasu,

Karatunta ya tsaya sbd hakan sbd sam bata iya fita bata iya zuwa koina su kansu sunji sunfi nutsuwa da kwanciyan hankali idan tana gida dan haka karatunta ya samu mummunan matsalar da ba lallai qarasa shi.

Washe garin ranar da aka sallamosa din da safe yayi wanka ya fice daga gida bayan ya zauna yasha ruwan lipton din da SANAAH ta dafa masa da bread yana sha yana kallanta zuciyarsa na sake shiga duhu da dacin tsananin tausayinta dana mommy dashi kansa dan haka duk ya kallesu damuwansa ke qaruwa.

Yana fitowa gida akwai mutane a layin sosai dan haka babu inda ya tsaya yana kawowa a natse zai gaidasu ya wuce batareda ya tsaya ba sbd daman baya tsayawa zama ko fira koina bare yanzu da duka yana iya gani a idanuwansu wani kallan na daban suke masa manya da matasa da samari.

Kai tsaye babbar police station din dake central ya nufa,
Yana isa kaman yanda yaga layin karban cases tsayawa yayi yana dan tsayar da hankalinsa da tinaninsa akan abinda ya kawo sa batareda bawa kowane case dayaji anayiba mahimmanci sbd abinda yake gabansa ya wuce ya tsaya sauraro ko bawa matsalar wani mahimmanci.

Shiru yake a tsaye har layi yaxo kansa ya qarasa har gaban babbar kantar da ake karban case ba.

Numfashi me dumi ya sauke a natse ya jerowa officer din bayanin komai tareda bayyanarda haqqinsu yake son a bisu musu AA ya karbi hukuncin abinda yayi musu.

Gama sauraronsa officern yayi kafin ya sauke numfashi mai nutsuwa yace

"Menene cikakken sunansa shi AA din?
Kuma menene address dinsa da gurin aikinsa da sauran bayanai akansa?

Dago jajayen idanuwansa yayi ya kalli officern yace duka bansan su ba amma dai cikakken sunansa shine ABDULSAMAD ABDULHAKEEM"

da zallan mamaki officern ya dago da duka idanuwansa ya kalli Al'amin din ya bude baki zaiyi magana sai kawai ya fasa yace masa ya basa numbern AA din ya jirasa.

Yana karban numbern miqewa yayi yayi ciki zuwa office din babbansu.

Ya jima a ciki kafin ya fito ya kalli Al'amin yace ya taso ya biyosa.

Tashi yayi yabi bayansa suka shiga ciki.

Suna shiga qare masa kallo tsaf dpo yayi ya bude baki batareda yace ya zauna ba yace ya sake masa bayanin komai.

Sake bayani Al'amin yayi tareda sake tabbatarda neman adalci daidai yanda sharia tace akan AA.

"Mun karbi komai na case din zamu nemeka idan mun taho dashi nan,
Amma ka sani bazaka kai wata qarar ba sai mun tabbatar maka da mun gama komai."

Shiru Al'amin yayi sbd ganin yanda dpo yayi maganar kafin yace shikenan ya tafi.

Daga can gurin nemansa ya nufa bai dawo gida ba sai dare.

Anan ne ya sanar dasu ya saka qarar AA dan haka su sani sharia zasuyi dashi.

Tinda SANAAH taji hakan jikinta ya qara sanyi sbd a yanzu kam tasan kowa duniya zai san abinda ya faru da ita dan haka take taji ta qara tsanar shiga mutane da fita koina.

*****kwana biyu shiru shiru ba kowane bayani ko kira daga police station din dan haka sai kawai ya sake komawa dan jin bayani,

Yana zuwa kwata kwata qin basa dama da mahimmanin bayani sukai a station din gabaki dayansu dan haka ya tafi office din dpo da kansa anan ma kai tsaye dpo ya sanar masa sun watsar da case dinsa dan babu sheda babu ma hujja ko daya dan haka ya tafi kawai yajawa kanwarsa kunne daga bin maza masu kudi.

Shiru yayi idanuwansa jajir jininsa na wata irin tafasa da kunar da idonsa har gani sika rage ya miqe ya fito.

Bai koma gida ba kai tsaye wata police station din ya nufa ya sake saka wata qarar wadda ita anan take ma sukai rejecting din case dinsa suka koresa.

Bushewa yaji zuciyarsa nayi sbd abinda yake shirin tabbatarwa na power ake shirin nuna masa ko me.

Wata station din ya nufa wadda acan ma korarsa sukai,

Bai hakura ba sbd jin yana sake rasa hankalinsa akan lamarin haka ya ringa yawon station a ranar gabaki daya baije gurin kowane aiki ba har dare yana yawon da rayuwarsa ke shiga tashin hankalin abinda yake gani.

Sai dare ya dawo sosai a matiqar gajiye da damuwa me tsanani da mutuwar jiki da wani irin nauyin kirji ga bakinsa a bushe komai nasa ya bushe.

A yanayin dayake ko abinci bai iya ci ba haka ya shige ya rufe dakinsa ya zauna ya fasa wani irin kuka mara sauti yana dafe kirjinsa radadi na gewaye har gangar jikinsa.

Su kansu mommy jikinsu mutuwa yafara yi da yanayin case din dan haka Mommy tace masa su hakura kawai da safe amma bai iya hakura ba haka ya dake bazama yawon kowace station.

Station din daya isa ta hudu a ranar Rufesa ma sukai kawai suka masa dukan tsiya tareda rufesa cikin rashin imani sukace sai anmanta dashi ko zasu sakesa.

Su mommy dake zaune gida shiru shiru ba Al'amin har dare yayi sosai dan haka hankalinsu ya tashi mommy ta kasa barin SANAAH taje ta nemansa saidai suka fita tare a daren.

Dayake sun san case din dayake yawon yi sai kawai suka fara yawon stations a daren nemansa suma.

Dare yafara yi sosai dole suka dawo gida cikeda damuwa da tsoro har gari ya waye suna zaune batareda sun rintsa ba.

Karfe takwas na safe suka sake ficewa suna yawon da duk station din da sukaje kusan sai an gane sune masu qarar da Al'amin din ke yawo da ita.

Basu samu station din dayake ba sai yamma sosai gap da magrib kuma aka qi barinsu ganinsa dan haka anan suka kwana waje suma cikin tashin hankali da damuwa.

Washe gari da safe wani sabon dukan akai masa akan saiya janye karar kuma kada ya sake yawo da ita amma yaqi amince da hakan,

Duk azabar da suka ringa gana masa sam bai janyeba sbd ya shirya mutuwa akan haka amma indai akwai inda zaa karbi qararsa da korafinsa to tabbas zaije.

AA da kansa yazo station din ya tabbatar musu da koda zaa raba Al'amin da duniya ne ayi da abari zancen ya fita sbd gwara yayi ajalinsa daya bari ya fidda abinda zai taba martaba da sunan ahalinsa dayasan akan hakan mahaifinsa ya gwammaci ace mutuwa yayi ya bar duniya daya bata masa sunan da duk duniya take girmamawa da shakka.

SANAAH data gansa a lokacinda ya fito taso zuwa rokonsa akan a saki yaya Al'amin din sun janye kowace qarar amma sam yaqi barin ma ta iso ya bar gurin sbd idan ya ganta a gabansa ya kalli idanuwanta zai iya rasa control na kansa akan zazzafar soyayyarta bayan a yanzu yana cikin siradin da zai gwammaci batar dasu gabaki daya har ita akan maganar nan ta fita ta isa kunnuwan mahaifinsa da zai iya harbesa da bindiga akan hakan.

Mommy ce ta qasqantar da kanta tana kuna ta roki manyan officers din da case din yake hannunsa akan cewa sun janye tayi musu alkawarin bazata bari Al'amin ya sake kai qara kowace irin hukuma ba tukuna suka amince zasu sakesa.

Gida akace su tafi zaa kawosa har gida.

Bayan tafiyarsu sai da ya kuma kwana yaci wata irin azaba a hannunsu kafin suka sakosa aka kawosa da motar yan sanda a wulaqanci a gaban yan anguwa da suka ringa yada wata muguwar zunden.

SANAAH ce da kanta ta fita ta kamosa suka shigo gida yana takawa daqyar sun sauya masa kamannin da ko kuka dasuka gansa kasa yi sukai sbd bushewan kunci a kirji.

SANAAH ce ta hada masa ruwan wanka masu dumi takai masa toilet ta rakasa har toilet din tafito bayan takai masa kujeran zama dan bazai iya tsayuwa ba.


Yana fitowa abincinma itace ta basa a baki yaci kadan ya kwanta.

Da zazzabi ya tashi washe gari dan haka asibiti sukaje aka dubasa aka rubuto musu magani suka dawo.

Yaya Al'amin da zuciyarsa ta gama bushewa da asalin baqin ciki da kunci haka ya miqe batareda jiran warkewansa gabaki daya ba.

Tinda safen rana na uku koda suka tashi baya nan ya fice daga gidan...

Kai tsaye tafiyar kafa yayi doguwa me tsayi da idonsa daya a maqale daya qanqance sbd duka da kumbura da shatin kwanciyan jini.

Gidan Abokinsa dasukai karatu tin a baya tare ya nufa wanda ya zama civil defence yanzu,

Sammakon da yayi sbd kada ya fita kafin isowansa dan haka koda ya iso buga kofar gidansa yayi wanda yake madaidaici dan auren nasa ma bai jima ba sosai duka duka haihuwansa daya.

Kabir shine mutum daya dayake tareda shi tin kuruciya haryanzu da suke mutunci da aminta sosai shima ba wani karfi ne dashi ba kawai dai shi ya qarasa karatunsa harya fara aiki yana lallaba rayuwar sabanin shi dayake gwagwarmaya bayan ajiye karatu.

Kabir dinne ya fito da kansa sanye da uniform dinsa yayi shiri amma ba yanzu ka zai fita ba sai zuwa anjima,

Sunyi magana a waya da Al'amin din kafin zuwansa amma bai gama sanin cikakken bayanin ba saida Al'amin din yayi masa bayanin komai dan haka yayi shiru tsawon mintina batareda yace komaiba tukuna ya sauke numfashi me zafi yana sake nazari kafin ya zubawa fuskan Al'amin idanuwansa yana jin damuwa da dacin irin wulaqanci da dukan dayake bayyane a jikinsa koina da fuskansa duka akan zalincin da sune aka zalintar.

Bude baki yayi bayan sake sauke numfashi a karo na biyu a natse da bawa zancen mahimmanci yace

"Al'amin banajin sake shigar da qara a gurin aikinmu na civil defence shima zai baka adalcin da kake so sbd duka dai abin dayane,
Shi AA din da ake magana akai ba kowa bane face SAMAD JEERAH wanda familynsa keda power din da duk inda zaka bazaa taba sauraranka ba bare baka daman samun adalci wanda wlh tallahi akan hakan ma zaka iya rasa rayuwarka kota ahalinka sbd kawai a rufe zancen nan ahanasa fita,
Akan familyn su bari a samu abin da zaa bata sunansu ko taba martabarsu wlh daukan rai baa bakin komai bane dan haka ka aje maganar qara ko sharia dasu kwata kwata har abada......

Abu daya ne zai iya baka adalcin da kakeso da kuma samun nutsuwan daga abinda akai maka shine samun damar isar da qararka ga wanda shine kadai zai iya bawa zancen dukkanin mahimmanci sbd shine asalin martaba da suna da power din ahalin wanda shine zai baka adalcinka kowane iri ne batareda barin zancen ya sake tashi ba har duniya ta nade wato mahaifin AA din SIR HAKEEM JEERAH."
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

31
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki  Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki  Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce  For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Dago jajayen idanuwansa Yaya Al'amin yayi sun qara rinewa jajir sbd bayan qunci da baqin ciki babu abinda yake cikinsu,

Numfashi kabir yaja yaci gaba da cewa

"Gurin Sir jeerah da kansa gaba daya zakaje wannan matsalar ta qare sbd a matakin da ake kai koda an bar zancen Samad jeerah bazai taba barin SANAAH aure ba zaici gaba da bibiyarta ne kuma yanada power din da bazaa taba iya daukan mataki akansa ba,

Power biyu ne masu karfi hannunsa na familynsa dana yayansa da shine asalin ma power din dayake da ita wadda bazaka taba iya ja dasu ba dan haka a takaice wlh rayuwar SANAAH da kai kanka dake bibiyan case din tana cikin hadarin da komai zai iya faruwa a kowane lokaci dan haka ka isa ga inda zaayiwa tifkar hancin da zaku iya tsira da rayuwarku ku samu yancin rayuwa,

Banda hanyar da zaka ga sir jeerah kai tsaye amma dai zan samo maka hanyar hakan idan kanaso sai ka isa garesa."

Wani zazzafan daci yaya Al'amin ya hadiye tareda yin shiru yana sake zurfafa da wata baqin ciki da dacin jin sunan ahalin da harsun manta ma dashi a rayuwarsu sai yanzu da akai maganar dan haka yaji baqin cikinsa ya ninku dan haka baya buqatan kowa yayi masa hanyar isa ga Sir jeerah zai isa da kansa har gidan ya nemawa ahalinsa adalcin da ko zasu dauki ransa saiyabi.

Dagowa yayi ya kalli kabir ya bude bakinsa dayayi nauyi da daci da bushewa yayi masa godia tareda sallama ya juya yabar kofar gidan.

Hanyar gida ya kama da kafa yana sake zurfi a tinani me nauyi da tsanantar daci da nauyin kirji.

Tafiyar kasa ya kuma yi mai dan tsayi tukuna ya iso gidan.

Yana shigowa SANAAH na zaune a kitchen tana dafa musu abincin rana simple ba hayaniya na spaghetti da yar miyan albasa.

Ganinsa ya sakata zuba masa fararen idanuwanta masu girma tana kalla harya qaraso ta miqe tsaye bayan ta qarasa juye abincin a kula ta fito tana kallansa har lokacin a matiqar gajiye gangar jikinsa take ga lafiyar dama baida cikakkiyar sbd raunikansa babu wanda ba sabo ba har lokacin.

Bude baki tayi a natse tace

"Sannu da dawowa Yaya Al'amin"

Amsawa yayi yana zaunawa a kujera cikin inuwar kofar dakin Mommy dake cikin daki daga bakin kofa tana shan iska.

"Na hada maka ruwan wanka ne?

"Eh" yace yana zubawa guri daya idanuwansa shiru zuciyarsa na cikin tinani.

Mommy da duk ta kalli fuskansa da raunikan jikinsa nauyi kirjinta yakeyi itama kallo daya tayi masa ta dauke ido tana yin shiru cikin damuwa me tsanani da tinani,

Babu abinda suke so dukkaninsu irin tashi da barin anguwar ko garin ma gabaki daya su sauya gurin rayuwar da zasuyi batareda an ringa yiwa SANAAH kallan fanko mara daraja ba amma kuma Al'amin bayada niyar tashin a yanxu so yake saiya fara bi mata haqqinta an dan dawo mata da mutuncinta tukuna su tafiyarsu inda zaa mutunta su.

Ita kanta SANAAH a yanzu tafison su tashi ko inda babu kowane sai su kadai suyi rayuwa ta dena ganin irin kallan da ake mata idan ta fita musamman kowa kallan ita takai kanta sbd kwadayi suke mata.

Hada masa ruwan tayi masu dan dumi takai masa toilet ta dawo ta sanar masa tana kallansa cikeda tsananin tausayi idanuwanta cike da hawayen da sun gaji da zubowa.

Rayuwarsa tayi duhu dif cikin wani irin qunci da baqin cikin dayake neman kashesa a bayyane,
Ya rasa kansa ya rasa tinaninsa ya zama kaman wanda zai kuwwata kowane lokaci sbd baqin cikin dayake yawo a kirjinsa cike da jininsa,
Ya rasa kuzarinsa da iya tafiya nemansa komai ya fice masa arai har rayuwar sbd wannan baqin cikin da Samad jeerah ya kunsa musu a rayuwa da bazasu iya taba mantawaba harsu bar duniya.
A yanda yake jin zuciyarsa da baqin cikin nan da zaa basa fili da Samad zai kashesa da hannuwansa har lahira yakeji.

Sake magana SANAAH tayi cikin sanyin murya ta sanar dashi ruwan na toilet baiji ba idanuwansa jajir a kafe guri daya,

Mommy ta kalla wadda itama dagowa tayi ta sake kallan Al'amin din idanuwanta na dan sauyawa sbd neman zaucewan dayake neman yi lokaci daya.

Hannuwanta biyu duka SANAAH ta durqusa a gabansa ta dora akan hannunsa daya tana kasa magana sedai hawayenta da suka dan gangaro ahankali tanajin duhu na sake dawo mata sabo itama dan itace zata zama sanadin da zai rasa hankalinsa bayan bai ganewa komai na jin dadi da kwanciyan hankali ba a duniyar.

Motsawa yayi a sanyaye yana dagowa ya kalleta baice komaiba ya miqe ya nufi toilet yana tafiya ba daidai ba sbd kafarsa daya da suka kusan karyawa da duka ga tafiya me tsayi yayo.

Wanka ya fada toilet din yayo tareda hadiye dik wata mummunan azabar dayake ji a jikinda.

A gida yayi sallar azahar ya fito ya fice batareda ya iya cin abinci ba.

Basu san ficewansa ba sai da SANAAH taje har dakin ta dubo taga baya nan ta dawo ta shige dakinta ta zame ta zauna a bakin katifa qasa tana dan rufe idanuwanta a hankali tareda yin shiru kaman yanda yanzu gidan nasu ya koma haka.

****yana fita daga gida kai tsaye gurin aikinsa ya nufa ya samu karban aron dubu biyu daga daya daga cikin abokan aikinsa na store din da kullum ake ajiye musu tirelolin kaya suna saukesu tsaf da karfinsu da hannuwansu suna kaiwa babban manyan stores dake jere daga ya gama daga nan zuwa yamma sosai gurin wani aikin na lodi yake wucewa shi kuma har dare tukuna ya tashi ya dawo gida rayuwar kenan dayake yi wahala akan wahala shiyasa wani tsufa yake neman taso masa batareda ya tsufan ba.

Yana karban kudin nutsuwa yayi tsaf ya hau mashin bai tsaya koina ba sai anguwar da tin daga farkonta baa barin masu abin hawan kasuwanci suna shigarta sbd anguwan gabaki dayanta tako wane layi manyan qasa ne a cikinta sai asalin JEERAHsV dayake ciki daga kurya dan haka ma su layin soldiers ne securities dinsu gashi a cikin anguwan akwai manyan sojojin kasar Nigeria suma kusan guda hudu dan haka tako ina anguwan tsaro ne me karfi ga gine ginen cikinta ma kadai abin kallo ne dasuke bayyanar asalin zallar dukiya da luxuries kawai ko a iya gates da tsarin jerin gine ginen.

Tin daga nesa sosai mashin ya ajiyesa ya sauka ya ciro kudinsa daga aljihun wandonsa dayake a kode ya biya ya juya yana kallan hanyar dazai qarasa takawa da kafafunsa dan masu mashin ko napep basa bi sam.

Takawa yafara yi yana jin babu kowace shakka ko tsoro a tattare dashi.

Yana tinkaro asalin checking point din shiga anguwan soldiers biyu sukai dakatar dashi daga inda yake tsaye sukace ya tsaya a gurin da hannu.

Dakatawa yayi a gurin a natse ga zazzabin dayake ji amma ya daure yana shanye kowace irin ciwo da nutsuwa.

Basu bi ta kansa ba sai dayayi kusan awa daya a tsaye cikin tsakiyar ranar kuma bai motsaba a natse kafin daya daga cikinsu ya taso ya iso gurinsa ya tambayesa me yake a gurin.

Dagowa yayi idanuwansa sunyi jajir sbd azabar dayake ji ya bude baki a natse yace

"JEERAHs Zantafi"

Kallansa dakyau soldier din yayi yana bin raunikan fuskansa da kallo kafin yace

"Mezakaje yi a jeerahs din?

Shiru ya dan yi kaman bazai fadaba amma idonsa daya sauka akan uniform din sojan wanda yake da tag a gefe kadan na jeerahs ya sani sauya shawara sbd ya sani a daidai wannan gabar matiqar bai fadi abinda ya kawosa kai tsayeba bazaa taba barinsa shiga anguwanba amma fadar lamarin shine zai saka ayi gaggawar barinsa isa can din sbd kada zancen ya fita ko kadan kuma yaci saar ganin wannan sojan jeerahs ne.

Numfashi ya sauke kafin ya bude baki yace

"Sir jeerah nakeson gani akan kanwata da aka lalata daga familynsa kuma.....

Baya Sojan yayi dashi da wani irin karfi yana masa wani zazzafan kallan daya saka yaya Al'amin din jin rashin dana sanin fada.

Bude baki sojan yayi zai masa tambaya amma kuma sanin hakan laifine mai girma jin abinda bai kamata yaji ba gameda familyn dan akwai wannan dokar me karfi basu da daman jin abinda baa so sujiba komai kankantar abu indai ya shafi familyn jeerahs to sai sun isar dashi batareda bata lokaci ba dan baa barin dama ko qanqanuwa da zata kawo matsala dan haka baice komaiba ya sake kallan Al'amin tukuna ya fiddo wayarsa ya saka kiran babban personal person na Sir jeerah din gaba daya.

Ringing wayar takeyi tsawon lokaci kafin kai tsaye aka dauka.

"Sir daga main checking point ne na gate akwai wani gashinan tsaye a gabana daya zo yana wata magana me dan hadari"

Shiru Mr Sideeq yayi yana sauraron sojan kafin ya bude baki yace

"wace maganar ce yazo da ita??

Dan shiru sojan yayi kafin yace

"Sir yana magana ne akan an lalata kanwarsa"

Tsit inda Mr Sideeq yake ya dauka sbd yana zaune ne tareda Sir jeerah din gabaki daya kuma kai tsaye abinda aka fada ya shiga kunnensa dan haka Mr S ya dago ya kalli Sir jeerah din cikeda mamaki me tsanani na zancen kafin ya dawo da kallansa akan wayar yace

"Menene ya hada maganar daya taho da ita da jeerahs???

Bude baki sojan yayi yana kallan Al'amin zai masa magana Sir hakeem jeerah dayake zaune cikin wata irin nutsuwa da manyancin daya gama kamasa sosai ya dago idanuwansa masu kwarjini da wata irin iko da isa ya kalli Mr S batareda komaiba yace

"Abarsa yazo yayi bayani da kansa"

Hakan daya fada ya saka Mr S sanar da sojan ya kawo masa Mutumin da kansa har nan kada ya bari ya shigo da kansa.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

32
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon

Please Login or Register in order to submit comment