Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qasar cikin aminci da kwanciyar hankali da wadata shima.

Aurensu da shekara biyu ta haifi 'da namiji wanda tinda kansa basu sake haihuwaba har Allah ya dauki ranta ta barsa da 'dansu ABDULHAKEEM JEERAH.

tinda ta rasu tabarsa yaji yana tsananin kewan yan uwansa shima da son kasancewa a tareda su dan haka ya ringa ji shima kaman yanda mahaifinsu ya ringa ji na tsananin son komawa gida amma sbd 'dansa saiya danne hakan ya zauna sbd bawa dansa ilimi da burin dayake buqata ba bazasu taba barin legacy din mahaifinsu ya tafi ba na rasa kowa a soja kowane irin cikin familyn jeerah da kaf familyn babu wanda a cikinsu baiyi soja ba.

Abdulhakeem jeerah yafara karatun soja kaman yanda mahaifinsa farouk jeerah yaso amma shi a sojan ruwa yazo dan haka baban bai damuba ya tsaya tsayin daka ya tabbatarda tsananin kaifi da qwazon zamtowa cikakken navy ya shiga dan nasa.

Bayan shekaru komai na rayuwar navy ta tsayu a rayuwar Hakeem mahaifinsa yabarosa shima ya dawo Nigeria gurin yan uwansa wainda basu duba manyancinsa ba sukai masa aure da wata qanwar hajiya maryam data jima batai aureba.


Manyanci ya kamasu sosai sosai dukkaninsu sbd rayuwa data ja sosai hakama cigaba yazo sosai dan kuwa babu wanda baya kan babban matsayin da duniya take girmamawa a cikinsu,

Hussain dayake babban dan siyasa saida ya taka matsayin gwamnan jaha guda kafin yayi senator tukuna ya tattara yabar qasar shi da iyalansa suka koma Morocca da zama sbd business dinsa dayake tafiya sosai acan dakyau dakyau.

Hassan ma da Ahmed sun bunqasa sunci sun tayar da kai a fagen tarin dukiya da businesses dan kuwa suma basu bar qasar ba sedai basu cika zama ba sbd zama busy.

Farouk dayake retired soldier yanada dukiyar gaske mai yawan daya mallaka tin daga qasar America din hakama dansa Hakeem dayake can yana cikin dukiyar a wadace duk da aikinsa bai taba basa damar jin kowane irin dadi ba ya duqufa ya sadaukar da rayuwarsa kaman yanda kakansa da mahaifinsa sukai sbd shima baida niyar tsayawa insha Allah saiya kai karshen lamba.


********
A cikin familyn jeerah da babu wanda zaa ambata sunansu yace bai saniba kaf Hakeem jeerah ne baa saniba sbd baitaba fitowa duniya tasansa ba yana duniyar ruwa kuma hakan shine alfaharin da mahaifinsa yakeyi cikeda jinjinawa ya zama hakan,

Sauran ahalin zuriar duka mata ne sbd Alh Ahmed jeerah duka duka yayansa biyu rak kuma duka mata ne hakama dukansu anyi musu aure kuma dukansu baa qasar ba suna wasu qasashen.

ALH HASAN JEERAH ma yayansa hudu duka mata ba biyu sunyi aure biyu sunata zuba karatu me zurfin dayaqi qarewa basu shirya aurenba.

ALH HUSAIN JEERAH kuwa yayansa uku biyu mata sai namiji daya,

Dukansu duk da sun kasance haihuwan turai basu wani riqe aladar rashin aure ba dan haka kusan dukansu babu wanda ba matansa biyu ba dan haka sai ya zama kaman al'ada ko Alh farouk daya dawo daga baya a cikinsu saida ya qara auren.

**********
Rayuwa taja,lokaci yaja an samu sauye sauye sabbi da cigaba da qaruwa harma da rashe rashe sbd a halinda ake yanzu Babu Alh hassan jeerah a duniya sun tafi sunbar yan uwansu Alh Ahmed jeerah Alh farouk jeerah da husain jeerah wanda ya tattara ya dawo qasar kuma sun gina wani mahaukacin estate da babu aljannar duniyar da babu a cikinsa kuma duk wani ahalinsu mai amsa sunan jeerah yana cikinsa dan haka suka sake zama sunan da har lokacin babu kamarsa a kunnuwan mutane.

Abdulhakeem jeerah ya zama cikakken captain 1st rank a Lokacin ne ya samu fara gudanar da luxury rayuwar nutsuwa da kwanciyar hankali tareda fara kaiwa kasar mahaifinsa da kakanninsa ziyara sbd a yanzu yakai matsayin tafiya koina.

Zuwansa na farko duniya tasan waye ABDULHAKEEM JEERAH,

Mahaifinsa ya gabatar dashi hakama dayan baban nasa wato alh husain,

Daga nan ne aka fara kokarin gabatar masa da matar aure a cikin dangi yan uwansa amma sam baida raayin hakan dan haka sai aka kyalesa dukda a yanzu cikin familyn basajin zasu barsa auro wata daga waje tin akwai yan mata masu class da wayewan da ilimin dika a cikin family amma dai basason tada masa hankali a natse zaai komai.

Abu babba daya da akasan familyn jeerah dashi bayan dukiyarsu da matsayinsu da kuma tsananin ilimin da suke dashi shine sunada riqo da addini me karfi da aka shede su dashi wanda ya saka hatta bangaren malaman addini basu girma da mutuntawa sukeyi sosai da gaske,

Bayan hakan kuma sunada tsananin girmamawa da tsare mutuncin sunan ahalinsu sbd kaf tinda suke babu wani wanda ya taba bata musu suna ko aikata abinda zaa aibata ahalin sbd tin asalinsu sun dauki suban tamkar rayuwar da baa buqatan mutuwarta.

Babu kowane mai rai dayake ahalin da baya tsananin kishi da kare martabar sunan gidan dan hakane iyayen suke tsaye tsaf gurin hana kowa da komai taba sunan jeerah batareda tsananin girmamawan da har jini zaka jita ba.
#MAMUH
#JEERAHS
#SIR HAKEEM JEERAH
#FLEET RAHEEM JEERAH

GANIN IDO 2026
Mamuhgee
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank maryam sani gummiGANIN IDO 2026
Mamuhgee

6
*_HAXXY's KULI_*
09123227777
Kin taba cin best qulin dayake tamkar alewan madara kokuma muce tamkar ba quli ba sbd dadi da nutsuwan daya samu gurin aikinsa??
Shin kin taba banbance kuli mai capacity da kuli kuli?
To taho ki gwada wannan special kulin da zaki iya cinsa da kuma shansa a komai wato HAXXYs KULI.

Gombe|Nationwide delivery
1500NGN per pack
Muna saida su yajin kuli, man quli, kuli kuli na dunqule da gyadan kunu duka.

*******
Girman matsayin da Captain Hakeem jeerah yake takawa yake qara daukaka sunan ahalinsa wainda a yanzu babu wanda baya alfahari d bugun gaba da matsayin nasa kuma hakan yake sake saka sunan zuwa manyan matakai da abaya ma bai kaiba sbd duniya ta sake fitowa daga zamanin baya sosai da samun wayewa da cigaba tako ina,

Abu daya dayake shima kaman a jininsu shine duk inda suka fara taka matakai sai sunji suna son gida tareda kasancewa a cikin ahalinsu dan qara dabbaka suna da martabarsu da itace abinda babu wanda ya isa kaf ya taba batareda yasan girman masifar daya tarowa ahalinsa ba.

*****
Jirgin karfe hudu ne ya sauka a airport din dake babban birnin Morocco wanda a cikinsa Captain hakeem ne da abokan aikinsa suka fito suma
Motocine kusan guda hudu dana securities suka taho daukansu dan isar dasu masaukinsu dayake tsakiyar babban birnin.

Isarsu masauki yayi daidai da isowar sabbin likitocin da aka gayyato daga qasar Morocco din dan aikin sati biyu da sojojin ruwan da suka taho daga wata qasar.

FAMMAH SAAD tana cikin sabbin likitocin da aka taho dasu da bata wani jima da gama karatu da fara aiki ba sedai tanada kokari sosai dan kuwa tanada wata irin dagiya ne akan duk abinda ta cimma buri kuma ta gado hakan ne itama daga nata iyayen wainda mahaifinta likita ne mai riqaqqen raayi me karfi hakama mahaifiyarta professor ce kaifi dan haka ta gado iyayenta dukansu ta zamo mai zafi da riqon raayi da tsananin sanin yanci da ikon kai da kuma tarin ilimin da bata yadda tayi wasa dashiba.

Da farko ranar data fara haduwa da Captain Hakeem jeerah kusan dukansu zafin kansu ne ya hadasu sbd babu sakewa ko wata alaman sakewa ko kadan a tsakaninta da duka navys din dama sauran abokan aikin nasu dan bashine ya kawota ba a ganinta,

Shi kuwa a nasa ba itaba ko manyanta babu kowace irin sakewan fuska daga garesa duk da shine babba a cikin tafiyar dan haka sai yanayin zafin kansu ya saka suka ankare da juna ta hakan kuma suka dan sabu da juna sbd kallan juna a wainda basa tattareda da shiririnta sakewa ko kadan.

Programs ne kala kala aka gudanar a cikin kwanakin ayyukan nasu kuma ako yaushe suna sake dan samun kusancin magana da juna da hakan ya zamana a cikin likitocin itace wadda yafi magana da ita sosai dan haka sai kusan aka bar mata ta jagoranci programs din har suka gama kwanakinsu aka gama komai.

Bayan tafiyarsu suna dan communicating da juna sama sama har Allah yasa suka sake dawowa Morocco qaddamar da aikin da sukai din wanda a wannan karan ne soyayya me tsananin karfin gaske ta kullu a tsakaninsu wadda ta bawa kowa mamaki daga iyayensu har abokan ayyukansu sbd ganin zafi da kafiyar kowannensu akan duk abinda zai zamo raayinsa dan kuwa a yanzu kowannensu yakeda riqaqqen raayi da rashin yadda ya saka baa taba saka ran zasu iya soyayya mai zafi da karfin gaske da ake ganin sunawa junaba.

A bangaren hakeem jeerah din so ne yakewa fammah din da baitaba jin zaima iya rayuwa a yanzu batareda ita a cikinta ba dan kuwa abu ne da bai taba ji ko sanin haka yake ba,

Fammah kuwa kusan abinda take ji akansa yafi ma wanda yakeji sbd su kam a yanda jininsu yake idan suka kamu da son abu to suna mutuwa ne akansa gabaki daya da zasu iya rasa ransu akansa dan haka ABDULHAKEEM JEERAH ya riga ya shigo rayuwarsu da batajin kuma duk duniya zai iya zama na kowace mace bayan ita tinda har mahaifiyarsa bata raye to ita kadaice macen da zata zauna a zuciyarsa har karshen ransa dan kuwa a yanda tsananin zafin kishi da kaifin zuciyarsu ta asalin larabawan Morocco take zasu zabi mutuwa kai tsaye akan zuciyar mijinsu ta kasance da wata a ciki bare azo akan hadasu da wata a rayuwar aurensu.

Bayan wannan zazzafan zuciyar kishin da suke da ita datai bushewan da babu kowane irin lamarin dazai tausasa musu ita ita kanta fammah nada tata kafaffiyar zuciyar ta daban da batajin zata iya hada Hakeem da kowace mace a duniya tana fatar kada Allah ya nuna mata wannan ranar gwara ta mutu bata duniya.

Iyayenta Dr Saad da mahaifiyarta prof shaarat sunyi farin ciki sosai da samun captain hakeem jeerah a rayuwar yarsu sbd soyayyarsa ta sauya abubuwa da dama a rayuwarta tareda sanyaya abubuwa da yawa dan haka suke sonsa sosai suma.

A nasa bangaren iyayen basu wani yi murnan samo mata balarabiyar Morocco da yayi ba sbd sanin tsananin zafin kishinsu da riqon raayinsu basa wani lankwasuwa sosai amma kuma ganin irin yanda yake tsananin sonta a bayyane ya saka suka amince akan sharadin zai ajeta ne a Nigeria tinda aikinsa baa zaune yake ba duk inda ya ajeta zai ringa zuwar mata hutu ne tinda yana can duniyarsu dan haka gwara ya ajeta a Nigeria cikin jeerahs tinda itama ta zama jeerah idan bata amince da hakan ba itada iyayenta sedai a hakura.

Da farko shi kansa bai aminta ba da hakan amma mahaifinsa shima ya aminta ya tsaya akan hukuncin da yayyunsa suka yanke wato Alh babba Ahmed jeerah da alh husain jeerah
Ya kuma san idan iyeyensa suka hade kai suka yanke hukunci sedai ka mutu ka bar duniya su rufeka amma bazasu sauyasa ba sbd wani irin karfin zuciya da raayi ne dasu wanda acan ya gado harma ya wucesu dan kuwa nasa ya wuce na kowa sedai tinda su iyaye ne haka ya tsaya akan hukuncin nasu.

Fammah da idan tanason abu itama zata iya komai akai bare hakeem da zata iya mutuwa akansa dan haka kai tsaye ta amince da zuwa ta zauna duk inda sukeso matiqar zasu kasance maaurata itada hakeem din har karshen rayuwarsu.

Tana amincewa iyayenta suka amince suma cikeda farin ciki dan haka babu sauran shamaki iyayensa suka taho har qasar Alh babba Ahmed ne da kansa yaxo shi da Alh husain suka nema masa aurenta tareda bada wata irin dukiya me yawan gaske da zinari wanda su larabawa dashi ake biyan sadakin su.

Babu daukan lokaci akai bikin auren wanda yayi suna sosai sbd irin dukiyar da aka zubar da kuma kasancewan Hakeem jeerah shine 'da namiji daya da jeerahs suke dashi da aka fara aurarwa dan haka kusan duka yan uwansa mata dake qasashe daban daban da wainda ke Nigeria ma duka saida suka halarci bikin nasa da dr fammah wadda take cikin tsananin farin cikin da duniya ta shedar da shi daga ita har hakeem duk wanda ya kalli bikin xai fahimci yanda suke tsanani da mutuwar son juna dan kuwa koina basu taba boye soyayyarsu ba wadda ta saka yan mata da yawa jin inama sune dan samun miji kamansa da babu abinda ya rasa a tsakanin kyau,dukiya,ilimi,wayewa,addini,soyayya da kuma zallan daukan hankali da kwarjini.

Bayan bikin kai tsaye Nigeria aka taho da amarya a cikin makeken lafiyayyan bungalow dinta dake cikin JEERAHs VILLAH.

Iyayenta suka kawota da kansu suka inda zatai rayuwa bawai wadatar gurin ba sbd sunsan idan dukiya da daula ake magana a JEERAHs to yarsu zatai dukkanin rayuwar da kowace mace ke buqata ta watada da jin dadi da zallar hutu amma suna son zuwa su kawota da kansu dan su samu kwanciyan hankalin sanin yarsu na qasar da basu taba zuwa ba har ita din sai a yanxu.

Kwanaki biyu sukai a Nigeria suka tattara suka koma bayan sun tabbatar yarsu tana cikin familyn da har 'yayanta da zata haifa a duniya bazasu shiga kowane irin qunci ba.

******sabon babin rayuwar tsantsan soyayya mai sanyi da ratsa jini da jiki Captain Hakeem jeerah ya bude da matarsa Dr fammah wadda ya sheda abu daya shine da soyayyarta zai mutu a rayuwarsa,

Kasancewansa bature kuma wanda bai tashi a tsakiyar uwa da uba ba ya saka bai iya boye abinda yake tsananin so dan haka babu wanda ya taba takura musu rayuwarsu sukeyi hankali kwance tsawon sati shida kafin suka tattara ya koma da ita America.

Babu wanda ya takurasu sbd su samu damar jin dadin amarci sbd tini aka gina mata wata lafiyayyar private asibiti me kyau da tsananin tsarin gaske wadda zatai aikin a nan Nigeri.

Kusan watanni bakwai suka kwashe acan qasar kafin ta dawo ta barosa can sedai ya ringa zuwar musu.

Rabuwarsu ta sake tsananta musu yanda suke jin juna amma hakanan suka hakura kowannensu ya rungumi aikinsa musamman shi da a yanxu komai na aikin ke sake nauyi dan kuwa matsayinsa dake qara gaba sbd jajircewansa da sadaukarwarsa dan kuwa ya qarasa sadaukar da rayuwarsa kaf gabadaya akan aikin batareda tsoron mutuwa ba ko shakka ko daya shiyasa yake tamkar wanda baida zuciya a fagen aiki.

****Dr fammah ma yanda take da kafiya akan aikinta ta sadaukar da rayuwarta akan nata aikin sosai ta zama busy akan aikinta dan shine yake bata nutsuwa da kwanciyan hankali dan haka bata wani zama gida sosai bata yawan shiga hayaniyar family sedai babu wanda bata bawa girmansa a cikin iyayen da yan uwan mijin duk da sunada wayewa da ilimi babu wanda yake takura kowa,

Iyayen mijinta dukansu suna nuna mata kulawa da kauna sosai musamman yanda itama ta tsayu tana samarwa kanta sunan a matsayin dr fammah jeerah batareda jiran sun daga hannunta duniya ta santa ba sosai,

Ba iya asibitinsu take aiki ba tana zuwa asibitin gwamnati tana duba marasa lafiya sosai a duk ranakun alhamis da jumaa dan haka sai ya zamana a ranakun manyan marasa lafiya da case dinsu yake babba ake tara mata tana dubawa tana kuma taimaka musu sosai ga wainda basuda karfin iya nemawa kansu lafiya.

Kadaicin datake fama dashi da kuma buqatar me tayata fuskantar abubuwan da bata san yaya zata iya fuskantarsuba a qasar ya saka da kanta ta nema P.a dinta da hakeem ya samar mata akan ta samo mata me aiki wadda zata rinta zuwa koina da ita sbd masu aikin gida idan sun gama komai sun jere abinci tattarawa suke su koma bangarensu na masu aiki sai kuma gobe dan haka kadaici yana mata yawa sosai duk da batason kowa a tareda ita.

Samo mata me aikin akai amma ko wata biyu bataiba ta sallameta sbd batajin komai na nutsuwa da rage kadaicin datake so daga gareta dan haka sai kawai tace a barshi.

Bata jima da sallamarta ba Hakeem ya dawo ta shiga farin cikin da bata taba shiga ba dan kuwa aikima dena fita tayi kwata kwata sbd samun nutsuwan ruhinta da farin cikinta.

Shi kansa yayi kewan matarsa kaman bazai iyaba duk da karfin zuciyarsa.

Hutu yayi me tsayi kafin ya tattara ya koma wanda a lokacin ne aka sake masa qarin matsayin da duka familynsa saida suka tafi har qasar akai bikin qarin girman dasu musamman matarsa dakejin farin ciki da kuka a lokaci daya sbd harga allah a yanxu jin takeyi kaman zata rasa rants sbd kadaici dake cin rayuwarta na rayuwa a inda ba uwa ba uba ba miji ba kowa ita kadai take rayuwarta a inda bata saba ba dan haryanzu ta kasa sabawa shiru kawai tayi sbd batada kowace irin mafita amma babu daren da bata kwantawa tayi kuka ta fadawa Allah.

Bayan dawowansu rayuwarta ta kadaici da damuwa taci gaba ahaka har depression yafara kamata wanda ya saka ta rage zuwa aiki sosai dan kuwa kanta yafara neman cakewa.

Ranar datai sati uku bata fitaba sbd damuwa da quncin take ciwo ya kwantar da ita wanda ya saka bata fadawa kowaba ta daure ta fita asibiti da kanta acan manyan likitocin asibitin yan uwanta suka kwantar da ita batareda sanin ahalinta ba.

A wannan lokacin ne dole P.a dinta ta saka daya daga cikin maaikatan asibitin masu shara ta kula mata da ita sbd ita a ranar tafiya zatai mahaifinta ya samu accident ya rasu.

FATIMA MUHAMMAD IBRAHIM shine sunan mai aikin wadda ta zauna ta zubawa Dr Fammah idanuwanta cikeda kulawa da tausayi tareda kauna me sanyi sbd dr fammah batada hayaniya duk da kallo daya zakai mata kasan ita din me zafi ce amma tanada tausayi da kulawa sosai ga mutane kuma kowa yasan balarabiya ce aka auro batada kowa anan kaman ita datake batada kowa a duniyar sai mijinta wanda baya tareda ita yana gurin qwadago sedai yazo yayi kwana biyu ya koma kuma itace take tsaye akan kulawa da kanta da kusan ciyar da kanta sbd idan ya tafi yakan dauki lokaci me tsayi kafin ya dawo.
#MAMUH
#BEST LOVE
#DR FAMMAH
#FATIMAH MUHAMMAD IBRAHIM
#SISTERS LOVE
#JEERAHS
#FLEETS

GANIN IDO 2026
Mamuhgee
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank Maryam sani gummi
090331810170GANIN IDO 2026
Mamuhgee

7
_*LADY'S BEAUTY PALACE*_
08169307477

MACE SAIDA GYARA
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ki koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon

To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,

MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,

LADY'S BEAUTY PALACE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Lace
Hijabs
Supplements
Kayan yara da dai sauran Su

Location Katsina state
WhatsApp or call 08169307477
TikTok Hajara Rabiu ( Ladys beauty place)

********
Kasancewan Fatiman batada aikin komai daman bayan na asibitin datakeyi kuma bame jiranta a gida ya saka batai niyar tafiya tabar Dr fammah ba sbd har lokacin bacci take mai karfi cikin yanayi na ciwo.

Wuni guda tayi a zaune guri daya sallah kadai ke tada ita har sai bayan magrib Dr fammah ta farka cikin tsananin nauyin jiki da mutuwan jiki na wunin datai a kwance duk da ta samu saukin abinda take ji din sbd baccin ya taimaketa sosai tinda bata samun yinsa duk yanda taso sbd damuwa.

Akan fatima dake zaune a dakin idanuwanta suka fara sauka ta zuba mata su tana kallanta da mamakin ita din wacece.

Fatima na ganin hakan ta miqe tana dan gyara xaman hijabinta mara nauyi fes dashi sbd saida ta sake wanka a cikin asibitin acan toilet dinsu tayi fes sbd kada tama shigo dakin dr fatiman da kowace irin datti ko zufa duk da itama tanada tsaftar sosai amma tsayuwa ko zama a dakin da ahalin jeerah suke dole ta sake tsaftace kanta musamman dr fammah din datake kaman yau aka haifota sbd wankewa da haske da wani irin daukan ido.

Kallan dr fammah tayi da tsananin kulawa ta bude baki tana fara sanar mata da ita ko wacece tukuna sbd kada ta sakata tinani da cewa

'Ina cikin maaikatan asibitin nan ne haj Aishah ce ta sakani tsayawa sbd ita tayi tafiyan gaggawa mahaifinta ya samu hadari'

Shiru tayi sbd ganin har lokacin dr kallanta takeyi sbd ba komai haryanxu ta iya a yaren hausan ba duka duk da tana ji kuma tana kokarin yi dan ta dage da koyar tin kafin ma aurensu.

Ba duka ta gane hausan ba amma ta fahimci abinda fatiman ke nufi musamman yanda tayi bayanin a natse tana kama matsayinta na ko matsowa ta kasa yi kusa da ita sbd kada ta takurata kokuma ganim takeyi qyama zata bawa dr din.

Shiru dukansu sukai dr fammah na dauke idanuwanta daga kallan fatima wadda take tsaye har lokacin jikinta a sanyaye.

Tsawon mintina kafin dr ta yunkura ta tashi zaune daqyar ahankali kafin ta dago fararen idanuwanta da sukai nauyi ta kalli fatima wadda ke kallanta cikeda tsananin kulawan da zaka gane hakan a bayyane amma kuma ta tsaya matsayinta.

Dr da bazata iya miqewa tsaye batareda an taimaka mata ba sake kallan fatiman tayi idanuwanta cikeda wasu irin hawaye masu sanyi na tsananin kewan iyayenta da mijinta ta bude bakinta a natse tareda miqa mata hannu da sanyi tace

'Help me pls'

Fatima batasan me ta fada ba amma hannun data miqo ya sakata fahimta dan haka a sanyaye ta iso gurinta tana goge hannunta sosai da hijabinta duk da baida komai dan sallah ma ta gama.

Yanda ta goge hannuwanta da karfi sosai ya saka dr kallan hannunta data miqo zata taimaka mata din tana dan shakka taga fes yake ba alaman ma yanada dauda kamawa tayi cikin sanyi tana sauke ajiyan zuciya.

Miqar da ita tayi suka fara takawa ahankali zuwa toilet
Fatima ce ta bude mata kofar toilet din a natse suka shiga har ciki tukuna ta saketa a natse ta fito tareda jan kofar ta fito.

Tana fitowa gyara mata gadon ta sake yi fes tareda shimfida mata komai na sallah dik sa batasan ko sallar zatai ba.

Komawa tayi gefe ta tsaya har dr din ta gama ta fito ta sake komawa ta riqota suna kokarin isa kan daddumar sallah akai knocking dakin aka shigo doctors ne guda biyu.

Da kulawa sosai da sakewa suka fara yimata ya jiki suna maganganunsu cikin  turancin da fatima bata gane komai.

Jira sukai dr din tayi sallolin dake kanta ta gama dayan dr dinne ya bawa fatima umarnin ta hadawa dr fammah din ko tea ne tasha dan haka ta miqe ta nufi inda ya nuna mata bayan taje ta sake wanke hannuwanta ta dawo ta hada mata ta kawo mata cikeda nutsuwa ta bata ta fice dakin.

Sun jima a ciki sosai kafin suka fito suka fice tukuna ta koma dakin,

Tana shiga waya ta taddata tanayi dan haka rabewa tayi ta zauna gefe tana yin shiru.

Gida ne take waya dasu ta sanar da batada lafiya tana asibiti sbd umman ce ta kirata matar mahaifin mijinta ta farko.

Cikeda kulawa da bayyanarda damuwa tace gasunan zuwa sbd sun dauka tana gurin aiki ne shiyasa basu nemeta ba.

Godia tayi kawai ta aje wayar tana ajiye numfashi sbd wannan shine babban matsalan auren nesa sosai inda bakada kowa wani lokacin dan haka ta dago idanuwanta ta kalli fatima wadda nutsuwanta da kamun kanta a bayyane yake.

Bude baki tayi tace

'Zakije gida ne???

Dagowa fatima tayi ta dan kalleta tace

'Aa ba kowa a gida shiyasa haj aisha tace na jira har sai ta dawo'

'Bakida husband? miji??

Gyada kai fatima tayi da cewa

'Baya anan yana zuwa yana komawa'

Fahimta dr rayi ta dan yi shiru daga nan bata sake cewa komaiba hakan da aisha tayi mata yafi mata sbd ba lallai yan matan jeerahs su iya zama da ita a asibiti ba tama san ko su umman bazasu barta a asibiti ba gida zaa maidata sedai likitoci su ringa zuwa dubata acan gida.

Babu daukan lokaci mai tsayi sosai kuwa sai ga Daddy mahaifin hakeem din da kansa tareda Ummah sun iso asibitin tareda Ummi jeerah(cikin yan matan gidan) da mai aikinta guda daya dauke da qaton basket.

Da kulawa me tsanani suka iso

Please Login or Register in order to submit comment