Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganinsa sukai a tsaye idanuwansa tsaye akan Meenah din wadda ta juyo gabaki daya tana kallansa da wani irin zafin kishin daya taso yana kasheta gabaki daya sbd irin sauyawan dayayi ya qara wata haske da lafiya da sauyawa kwata kwata kaman bashi dinba take ta sake waiwayowa ta kalli SANAAH tana bude baki cikin jin kaman zata mutu a gurin tsaye tsabar baqin ciki tace

"Fleet akan wannan duka kake kokarin cireni daga rayuwarka???
Akan macen da wani ya gama da ita ya rage maka kake........

Kafarsa daya ya sako wajen ba tsammani da wani irin mummunan dacin kalamanta dayake kokarin gane me take fada ya mata kallan tsantsar takaici ya daga hannunsa daya ya nuna mata hanyar wucewa yana kasa iya ce mata komai sbd bama zaiyi kowace magana da itaba dan tagama kaiwa karshen hauka.

SANAAH kuwa jin maganar Meenah din wani sarawa kanta yayi da karfi sbd ita kanta zuwa yanzu ta fara yadda babu lafiya kwata kwata a cikin kwakwalwan Mum din dan haka batama iya sake kallanta ba juyawa tayi zata bar gurin tabasu guri Mum din ta fizgota da dan karfin data dawo da karfi tana yin baya ya rigeta da hannunsa daya yana bude baki da kokarin hana kansa bayyanarda fushinsa gabaki daya dayake tasowa yace

"Are you just mad or stupid?
Me kikeyi?
Kina tinanin duka haukan da kikeyi ke kadaice mahaukaciya ko ke kadaice kika iya haukan?
Kada ki kuskura ki bari na bude bakina nayi magana akanki sbd zata zama maganar karshe ne ta har abada"

Hanya ya nuna mata da hannu yana barin sauran maganganun dayake son furta matan sbd SANAAH da safiya dake gurin bayason furta mata su.

Wani hucin baqin ciki mai tsananin gaske ta kuma fitarwa tana yiwa SANAAH kallan karshen tsana da baqin ciki tace

"Duka sbd wannan sauran wanin kakemun wannan Fleet??
Akan macen da saida qaninka ya gama lalatawa baso dayaba,
Akan macen da......

Wata muguwar tsawa mai karfin gaske data saka gidan amsawa Maamah dake kitchen dinsu tana aiki da kofar bayan a bude jin tsawar tayi da tsananin zafin dayake tafe a cikinta ta ajiye abinda ke hannunta ta fito da san sauri tana zagayawa ta hangosu ta iso da sauri daidai lokacin da ya saka hannu zai kai akan Meenah din koina jikinsa na wata irin rawa da fizgan gaske tayi saurin taresa tana kallan meenah din da sauri wadda ta kuma bude baki tana cewa

"Idonka ya rife kenan baka gane sauran wani bane lokacinda ka...

Kwace hannunsa yayi daga na Maamah ya sauke mata lafiyayyan marin data zunduma wani mahaukacin ihun da batasan ta zunduma ba sbd shigarta da yayi hancinta na ballewa da habo ta dago da karfi jikinta na wani irin rawa da jijjigar tashin hankali da baqin ciki taqi yin shiru zatai magana Maamah ta daka mata tsawa daidai isowan Dr Mum gurin tareda Mommy wadda tana ganin fleet a gurin ta dakata tana juyawa Maamah da ranta yayi mummunan baci itama da bacin rai tace

"Ashe bakida hankali da tinani Meenah?
Jahilci ne yake cinki ko me?
Menene kike fada?
Wace mummunan magana ce wannan?
Ashe kema ba mace bace da zakiwa mace yar uwarki hakan??

Idanuwa a rufe tana kasa riqe kanta tako ina da baqin cikinta da zafinta tace

"Dukanku kunsani cewa sbd fyaden da Samad yayi mata Dad ya aurawa Fleet ita da.....

Dr Mum ce ta katseta ta hanyar cewa

"Sai me to??
Mun sani kuma mun yadda mun karbeta a hakan sai me ya rage??

Da wani kallan tsana da takaicin karshen maqura take kallanta ta furta mata hakan wanda hakan ya saka Meenah kallan fleet da karfi tana cewa

"Kaji"

Kallan tsana da baqin ciki da takaici tareda wani azababben zafin dayake danne kirjinsa da rufe jinsa da ganinsa da sukai dif ya kalli meenah din kafin ya kalli Dr Mum da baqin cikinta tini ya saka idanuwanta jajir ya juya gurin SANAAH wadda tayi mutuwar tsaye ganinta na daukewa itama sai ya kasa kallanta ya jikinsa ya dauki wata sabuwar rawa mai karfin gaske kafafunsa na kasa riqesa ya dafa bangon kofar da sauri da hannuwansa dake rawa sosai kaman.

Mommy ma da zancen ya isa har inda take tajisa rufe idanuwanta tayi ahankali hawaye na ciko idanuwanta da wani radadi mai ciwo.

Zamewa SANAAH tayi a gurin zata zube jikinta na rawa itama da wasu hawaye masu zafi da suka gangaro mata ta kalli Fleet din wanda ganinsa ya dauke taji duniyarta ta tsaya cak kawai ta zame Dr Mum da Safiya da tini tafara hawaye itama sukai saurin riqeta Dr Mum na janta da zafi suka juya suka bar gurin.

Maamah ma cikin tsananin fushinta dabai taba fitowaba ta saka hannunta daya ta damqi Meenah zata jata subar gurin Fleet ya bude bakinsa daqyar ya furta

"Maamah a hada kayanta duk abinda takeyi gobe zata koma Morocco"

Maamah datakejin kaman ta rufeta da duka janta tayi da karfi ta tafi da ita har dakinta ta saketa tana bude baki zatai magana sai kuma ta fasa ta juya zuciyarta na tafasa.

Maamah na ficewa cikin baqin ciki hawaye suka gangaro mata ta daga wayarta bata tsaya komaiba ta nemo video din da samrah ta tura mata ta tura masa a wayarsa kai tsaye tareda shiga group din jeerahs family ta turasa batareda tinanin komaiba ta jefar da wayar tana jin gwara kowa ya shaqi bakin cikin da zaiyi ajalinsa.

SANAAH kuwa suna shiga palon dr mum kasa zama tayi ta wuce daki daqyar tanajin kafafunta sunyi nauyin gaske da kirjinta tana shiga rufe kofar tayi tana silalewa qasa ta zauna tanajin hawayenta na tsayawa cak.

Dr Mum ma zaunawa tayi tana kasa cewa komai tsabar takaici da baqin ciki.

Maamah ma haka ta zauna tanajin kaman zuciyarta zata fashe sedai Mommy ce tayi karfin halin shiga kitchen tana qarasa aikin zuciyarta da nauyi sosai itama.

Basu san abinda Meenah tayiba na sakin video din a cikin ahalin jeerahs sbd batasan kowaba anan Nigeria da zata yada masa video din kai tsaye ya tayata yadawa kanta gabaki daya ya toshe.

Hajiyar Samad ce datake zaune tana wayoyinta hankali kwance da dariya tana gamawa ta fara dube dubenta a waya tana isa kan dining zataci abincin rana itada Nabeela yar riqonta tana fara cin abincin idanuwanta suka sauka akan videon wanda ta bude kai tsaye take abincin bakinta yadawo mata da wani irin azababben karfin gaske yana biyowa harta hancinta yayi mata cikin kai shaqe a take tana neman mutuwa jikinta na jijjiga da karfin gaske.

A rikice nabeela ta dauki ruwa tana tasowa ta bata amma basu shigaba dawowa sukai tana wani azababben tarin dake sake shiga kanta da karfi ta qwaci ruwan takai bakinta tana sha da karfin gaske idanuwanta na fitowa gabaki daya atake jajir dasu.

Miqewa tayi da sauri tana sake rarumar wayarta tana cewa

"Allah ya tsine miki meenah,
Allah ya haukatar dake gabaki daya a saka miki mari mu huta,
Allah ya debewa wanda ya auro mana ke da wanda ya kawoki qasarnan"

Da gudu ta fita nabeela na biye da ita tayi bangaren Samad wanda shima yake a zaune hankali kwance yana waya shigowan Hajiyar ya sakasa kashe wayar kafin yace komai ta nuna masa wayar hannunta da sauri jikinta koina yana rawar gaske tace

"Wannan zuriar masifa da balain a ina ta samu wannan abin daya yada?
Ya akai aka samu wannan abin?
Waye yayisa?
Meyasa bansan da antaba yin video dinnan ba?

Wani mummunan sarawa kan Samad yayi yana kallan video din hannuwansa suka dauki rawa ya kalli hajiyar da sauri yace

"Ina ya fito??

Cikin baqin ciki da tashin hankali tace

"Kai nake tambaya sbd wannan meenah dai ta zama masifa da balain da gwara mu taru muyi mata fatan mutuwa kafin ta kasheni da baqin cikinta"

Karban wayar da sauri Samad yayi hannunsa na dan rawa ya kuma kalla zufa na yanko masa tako ina sbd ba Fleet ba ko Dad yaga wannan masifar bazai barsa da ransa ba kila.
#MAMUH
09033181070
[25/06, 11:57 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

142
*_SHUWA INCENSE AND MORE_*
07042293387/09118783317
Ina masoya kamshi da gyaran jiki na asalin matan da suka amsa sunansu mata?
Kinaso/kunaso ku kasance a cikin kamshin da duk inda aka jisa a tattare dake ko gidanki sai ankasa hakuri an tambayeki?
Shuwa Incense And more itace karshen inda zaki samu asalin kamshi da abubuwan gyaran jiki da mayukan gyara gashi masu inganci da kyau wanda mukeda guarantee dinsa,
Kowace irin turaren wuta na asali na gasken a gurinta ne zaku samu wanda qamshinsa kam har nesa da maqota hakama babu kalan dilka ta gyaran fata data fuska da babu a gurinta,
Kada kubi labari kawai ku siya ku gwada..SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387.

***********
Da jajayen idanuwa Samad ya kalli hajiyar yana riqe wayar hannunsa da dan karfi yace

"Kiyi sauri Hajiya kije ki amsa wayarta ki goge kafin kowa ya gani dan daman ba kowa ke duba sako a group dinba dan kowa baida time na shiga group dinma"

Rudewa hajiyar tayi tana cewa

"Tayaya zan goge a wayarta bayan kasan kafirar Allah ce ba bani wayar zatai ba kuma inda ita kadaice a bangaren na mata shegen dukan da ko tashi bazata iyaba na amsa wayar na goge komai ma gabaki daya"

Da sabon tashin hankalin da baya gane komai yace

"Koma ta yaya zakiyi hajiya kije ki gogesa wlh a yanzu da wannan video din ya fita kona tafi nabar qasar ban tsira ba dan kuwa a cikin awanni kadan duk inda nake Fleet zai isa saka a dawo dani,
Ko me zaayi ayi mata a goge wannan abin hajiya"

Sake shiga tashin hankali da rudewa hajiyar tayi tana juyawa da sauri a rikice tana ficewa xuwa bangaren meenah din tana fatar kada ta hadu da kowa.

Shi kuwa wayarsa ya bude yana shiga group din ya kalli videon batareda ya bude ba dan bama zai iya kalla ba zuciyarsa kaman zata fado kasa sbd yanda take wata bugawa da tsananin wani zafi da rasa abin yi kwata kwata dan kuwa dayasan akwai wannan video din da tini yasan yanda zaiyi ya batar dashi daga duniya ko a gurin ubanwa yake.

Hajiyar kuwa tana fitowa a rikice ta isa bangaren nasu Meenah tana hadiye wani baqin ciki da tsananin tsanar meenah din wadda tai alkawarin nuna mata asalin haukar yan Nigeria matiqar ta rasa danta akan abinda tayi dinnan.

Tana shiga palon ko gani batayi dan hakane bata lura dasu maamah dake zauneba ta wuce dakin meenah din kai tsaye ta bude ta fada tana shiga kan meeenah tayi a rikice wadda take zaune tana jin itama gabaki daya duniyar na mata zafi da baqin ciki idanuwanta jajir tana tsinewa sanin dataiwa yan Nigeria da Nigeria din gabaki daya.

Wata damqowa hajiyar tayi mata da karfi tana cewa

"Ashe dai da gaske ke mahaukaciyar ce,
Ashe hauka da rashin hankali kwata kwata a jinin kabilarku yake,
Ashe kece makiyar danake ta mafarki da tinanin wancan tsohuwar dagar ce data zo ta aure mana miji bayan shekaru,
Ina wayarki?
Ina take??
Wlh yi gaggawar goge abinda kika saki ko ayi gawa biyu.....

Miqewa meenah tayi tana kwace hannunta daga riqon da hajiyar tai mata mai karfin gaske bata hayyacinta idanuwanta a rife.

Itama nata idanuwan rufewa sukai ta kalleta da jajayen idanuwa tanajin a yanxu ko Fleet din bataso ta tsanesa kaman yanda ta tsani kowa da komai na qasar tace

"Bazan goge ba,
Bazan taba gogewaba sbd kowa ya sheda Danki kwarto ne dayake neman matar dan uwansa hakama itama kowa sai ya gan cewa sauran samad Fleet ya aura ta yanda har abada bazatai daraja a idon kowa ba kuma.....

Wata mahaukaciyar shaqar mutuwa hajiyar takai mata tana cewa

"Wlh yau ko ranki ne saina dauka na goge wannan abin kafin kowa ya gansa dan ke rayuwar Namiji ne kikewa wannan abin ni kuwa akan nawa dan ke kanki ranki a banza take"

Qwacewa meenah taso yi tana sake qanqame wayarta da batada niyar bayarwa hajiyar ta sake saka duka karfinta tana danneta take wata kokuwa me karfi tashiga tsakaninsu.

Shaqar gaske a haukace hajiyar take sake yiwa meenah tana fara nuna mata malaikun mutuwa da Meenah numfashinta suka fara daukewa ta saka hannunta da karfi a gefenta ta lalabo wani qaton glass fram dake gurin mai kauri sosai ta daga bata tsaya komaiba ta bugawa hajiyar akai wadda ta sake wani gigitaccen ihu mai karfin gaske tana silalewa a gurin ta xube jini na xubowa daga kanta.

Maamah da mommy ne suka iso dakin da sauri cikin tsananin tashin hankali da rikicewan da har ture juna sukeyi suna sako kai a dakin suka tsaya cak cikin mafi girman tashin hankali da wata tsananin tsoro.

Maamah ce ta iya bude baki da karfi itama ta ambaci sunan Meenah din mommy kuwa jikinta na wata irin rawa tayi kan Hajiyar wadda take a zube jini na fita a kanta sosai.

Meenah qanqame wayarta tayi jikinta na wata irin rawa da fizga tana cewa

"Itace taja,itace taso kasheni akan hana kowa ya sheda danta shine kwarton SANAAH"

Maamah data rasa abin fada wani lafiyayyan mari ta sauke mata tana cakumota da tsananin baqin ciki da takaici da danasanin hada zuria da meenah din tace

"Idan kika kuma ambatar sunan SANAAH a bakinki saina tabbatarda da Raheem ya barki har abada sbd haukarki da rashin hankalinki ya wuce kowace iyaka."

Samad ne daya kasa hakura da rashin sukuni da tashin hankalin kada hajiyar ta kasa abinda yace dan haka biyota kawai yayi bangaren shima kai tsaye ya shigo palon daidai nan ne Mommy ta kwala kiran safiya da karfi a rikice tana kokarin kama hajiyar ta tayar jikinta na rawa sosai Maamah kuwa kamo hannun Meenah din tayi xata fito da ita sai kawai ganin Samad din sukai wanda idanuwansa suka sauka akan hajiyarsa dake zube qasa da jini sosai take ya kallesu da wani mahaukacin sauri jikinsa na fara wata jijjigar data saka Maamah saurin isowa gabansa zatai magana ya mata wata mahaukaciyar shaqa yana ficewa hayyacinsa gabaki daya yace

"Kasheta kukai????

Mommy data shiga sabon tashin hankalin da tsananin tsoro sakin hajiyar tayi tana yowa kansa da sauri a rikice tace

"Muma haka muka tarar da ita da meenah....

Sakinta yayi yana yi kan meenah wadda ta sake daukan wani glass din ta jeho musu da karfin gaske wanda take ya hadu da bango yafara wata qara dukansu kusan saida kowa glass din ya sama daya fashe.

Bai dakata ba kanta yayi idanuwansa a rufe da abinda tayi masa da mahaifiyarsa daya tabbatarda ta mutu.

Haukacewa tayi itama tafara daukan komai tana jeho musu da karfi wanda gurin ya rikice da tashin hankalin dayafi karfin kowa.

Safiya ce ta fito da gudu cikin ihu tana neman mutane da kwala kiran Imran wanda tasan shine mai fara zuwa bada taimakon gaggawa.

Su maamah kuwa kan Samad sukai suka riqesa sbd yanda jikinsa ke wata jijjiga zai iya kashe meenah idan ya kamata gashi taqi dena jefo musu komai mai illa dan kuwa glass ne tako ina yake fasuwa a dakin.

Dr Mum ce ta fito a rikice tana debewa Meenah ayau itama sbd tashin hankalin gidan ya kasa qarewa.

Su Imran ma fitowa sukai da sauri suna isowa gurin wanda yayi daidai da isowan Nabeela itama tana shiga bangaren da gudu tana shiga tai ido biyu da hajiya a kwance cikin jini ihu me karfin gaske ta sake tana dora hannu akaai da cewa

"Sun kashe hajiya wayyo na shiga uku na lalace"

Kalamanta suka saka su Imran fadawa da Dr Mum data iso Dad ma tini ya iso bangaren hankali tashe.

Duk wanda yaci karo da hajiya dake kwance cikin jini rikicewa yakeyi ga Samad dake wata irin haukar datai muni dan wani watsi yayi dasu Maamah din yana damqo meenah wadda bakinta bai mutu ba tace

"Wallahi bazan goge video dinkaba sai kowa a jeerah da duniya ya gama ganin yanda ka sadu da matar dan uwank.......

Daidai nan Fleet da baya gani sosai ya iso gurin kalaman na shiga kunnuwansa maamah da bata daddaraba kuwa hannuwanta biyu ta saka da karfi tana rufe bakinta ta baya da danneta Dr Mum kuwa a haukace ta cakumo hannuwanta tana kokarin kwace wayar wadda ta riqe gam gam kaman ranta tana ihu da tsinewa dik wanda yake gidan albarka tana haukace musu gabaki daya.

Mommy ce ta saka hannu tana taya Dr Mum kwace wayar wadda taqi sakar musu ba tsammani sai ganin Fleet sukai a gurin wanda hannu kawai ya miqa mata yana sauke idanuwanta da suke jajir wata wutar masifar da bai taba ji ba tana ci a jininsa ya bude baki da wani sautin daya saka kowa tsayawa cak cikin mugun tension da zifa yace

"Ku saketa"

Sakinta sukai Samad ma jikinsa ne yake wata rawan gaske duniyarsa na kamawa da wuta gabaki daya ya sake motsawa yafison ya shaqeta ta mutu har lahira a rasa me bude bude wayarta sedai take imran ya masa wani mugun riqon daya ringa wata fixga yana haukacewan shima gabaki daya.

Riqe wayarta tayi gam tana tana kallansa da jajayen idanuwanta da har wani ruwa suke tsabar masifa da haukar dake cinta.

Cikin wani irin kuka da haukacewa Nabeela tace

"Video din SANAAH da Yaya Samad ne ta sake a cikin group na jeerahs shine Hajiya tace saita cire akan hakan ta kashe hajiya wayyo na shiga uku na lalace hajiya,ta kashe hajiya wlh..... wani ihun kuka take zundumawa da karfi tana cakumo hajiyar wadda take a some ba alaman rai.

Dad na Jin hakan da wani kafirin sauri ya fita yana komawa bangarensa da sauri ya dauko wayarsa yana budewa kai tsaye kuwa yaga video din amma bai bude ba ya juyo da sauri hankalinsa tashe yana jin kaman hawan jininsa zai tashi.
#MAMUH
09033181070
[25/06, 12:48 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

143
*_SHUWA INCENSE AND MORE_*
07042293387/09118783317
Ina masoya kamshi da gyaran jiki na asalin matan da suka amsa sunansu mata?
Kinaso/kunaso ku kasance a cikin kamshin da duk inda aka jisa a tattare dake ko gidanki sai ankasa hakuri an tambayeki?
Shuwa Incense And more itace karshen inda zaki samu asalin kamshi da abubuwan gyaran jiki da mayukan gyara gashi masu inganci da kyau wanda mukeda guarantee dinsa,
Kowace irin turaren wuta na asali na gasken a gurinta ne zaku samu wanda qamshinsa kam har nesa da maqota hakama babu kalan dilka ta gyaran fata data fuska da babu a gurinta,
Kada kubi labari kawai ku siya ku gwada..SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387.

***********
Tin daga nesa yake cewa maza a karba wayar hannunta kafin kowa ya bude a goge ko zaa datsa hannuwnata akarbe wayar da gaggawa.

Daman Dr Mum tinda taji hakan tayi kan Meenah din tana kokarin kai hannunta ta kwaci wayar Fleet da kirjinsa ya kasa daukan numfashinsa hannu daya yakai idanuwansa a rufe ya mata riqo daya ya bude hannuwanta da ko rabin kwatan karfinsa bataiba ya cire wayar daga hannunta tareda jefar da ita gefe da karfin gaske sbd jin yake hannuwansa na son shaqarta sai ranta ya fita daga dangar jikinta amma tsananin so da kaunar dayake wa yarsa yana controlling dinsa.

Hannuwan Dr Mum na rawa ta bude wayar tana shiga abinda tafara gani ya saka jiri dibanta wayar ta fadi daga hannunta a bude video din na playing wanda idanuwan Fleet din jajir suka sauka akai sedai kafin ya gani Imran da wani irin zafin nama ya dora kafarsa akan wayar jikinsa na wata irin rawar da bai tsaya komaiba ya saka kafarsa daya yakaiwa Samad wani mammunan harbin da yayi baya ya fadi kasa jikinsa na rawa idanuwansa jajir ya dago da sauri yana kallan Dad ya bude baki zaiyi magana imran ya fizgo wata towel qarama dake dakin ya tura bakinsa yana turasa waje yaransu biyu dake kofa take suka bace dashi daga gurin.

Acan ciki kuwa Maamah ce ta dauka da sauri ta shiga ta goge da wata irin sauri tareda dubawa taga hadda Fleet din ta turawa dan haka da sauri ta goge nasa shima tana miqawa Safiya wayar tace ta konata a take.

Dad daman bai iya dake shigowa ba sbd da hannuwansa shi kansa zai iya aika Meenah lahira dan haka ko abinda ya shafeta baya son sake gani har abada.

Cikin kuka mai karfi daya zo mata da wata irin wuta a kirjinta tace

"Idan kun goge video bazaku goge abinda ya faru cikinsa ba har abada wanda yake gaskia ne"

A lokacin ne Dad ya shigo ya kalli Fleet wanda ya bude baki zaiyi magana ya katsesa da cewa

"Matarka gaskia take fada Tabbas Samad yaso lalata rayuwar SANAAH wanda hakan ya saka na aurar da ita gareka,
Wannan shine gaskiyar da haukarta take bata ta fada maka dan haka ni yanxu na fada maka ka sani,
Idan hakan wata matsalar ce da zaa kalli yata da wata fuskan a yanxu basai anjima ba ina son ka sakarmun ita dan wlh tallahi ayau idan nine ubanta danake da iko da ita ta gama zama da matarka da kai"

Cikin wani irin mummunan zafin da basu taba ganinsa a ciki ba ya juya ya kalli Maamah yace

"Wlh tallahi yau yau SANAAH ta gama zama da aurensa matiqar baisan hukunci da matakin daukaba akan haukar da matarsa keyi sbd har abada babu sauyi ko gyara a lamarinsu su dukan"

Juyawa yayi ya fice da zafin gaske zafin daya saka ita kanta meenah kallan Fleet da sauri tana baro inda take tsaye tana yowa gurinsa zatai magana ya furta mata kalman data saka duka su Maamah saurin kallansa da mugun tashin hankalinda ya saka Dr mum juyawa tabar gurin idanuwanta jajir sbd bataso akazo nan ba kodan riqe amanar Meenah dataso amma ayau meenah din da kanta ta yanke igiyar aurenta duk da ba qaramin kokari Raheem din yayiba gurin danne kansa akan abubuwan data ringa yi.

Maamah ma kasa motsawa tayi sbd jikinta daya dauki rawa harya juya da wani irin zafin da idanuwansa da fatar jikinsa sun nuna dan koina jikinsa ja yayi alamar ba qaramar wuta ce take cinsa ba.

Meenah din kuwa hannu ta dora akai zata kurma ihu sai kuma ya kasa fita tsabar abinda taji yaxo ya danne kirjinta da maqoshinta tareda danne jinta da ganinta ta silale a gurin tana kasa ko jan numfashi da kyau.

Nabeela datake cikin nata tashin hankalin itace ta bi bayan wanda suka shigo aka kwashi hajiya zuwa asibiti hankali tashe sbd jini sosai take fitarwa.

Fleet na fitowa baya gani sosai baiyi tafiyar taku biyar ba daga bangaren kafafunsa sukai wata sarewa da karfin gaske ya zube akan gwiwowinsa da karfin da wani irin gudun gaske Imran da securities dinsa suka yo kansa hakama Maamah da bata taba ganin wannan mugun ganin ba tayo kansa tana fasa wani irin kuka a karan farko na rayuwarta bayan rasuwan Nasir tana kallan fleet din wanda take idanuwansa da sukai wani munun gani suka qarasa munana da tashin hankali akai ciki dashi da gaggawa jikinsa na wata irin rawar da komai na jikinsa ke rawa yana wata irin loosing control din kansa gabaki daya.

Hana kowa shiga gurinsa akai a take harsu Maamah da dr Mum sbd babu wanda zai taba iya ganinsa a wannan halin Dad ne kadai ya shiga da Mr Sideeq sai Imran din da kuma aid din gaggawa da aka buqata daga wani babban likitan sojojin dake qasar allah yasa yana garin.

Anan aka shiga sabon tashin hankali da firgicin da baa taba shigaba musamman su Dr Mum da basu taba sheda hakanba saisu Dr da imran da securities dinsa da suke soldiers ne kadai sukasan me hakan ke nufi dan kuwa a wannan halin dayake ciki kome zai iya yi sbd haukan allurar datake kona kowace drop ta jinin dayake jikinsa.

SANAAH dataji abinda yake faruwa damuwanta da tsananin quncinta qaruwa yayi ta kasa fitowa tayi kuka tayi kuka har idanuwanta da karfinta ya kare jin takeyi tana buqatan barin kowa da komai itama sbd a yanxu anriga an sakawa alaqarta dashi tabo tabon da bazai taba gogewaba,
Kowa yaga mummunan qazantacciyar kaddararta datake boye.

Wani irin nauyi da daci kirjinta yake mata da duniyarta tayi duhu dip babu sauran haske a cikinta.

Wuni akai cikin mummunan tashin hankali tako ina a jeerahs din,

Fleet ya sakasu a mummunan tension da tsoron da basu taba samun kansu ba,
Hajiya na asibitin rai a hannun Allah,
Ga Samad bat aka nemesa aka rasa yana hannun yaran imran daya saka a ajesa batareda kowace hayaniyar ba tukuna.

Mommy ta ita kanta tashiga daki tayi kukan data jima batai irinsa ba kafin ta taho bangaren Dr Mum din ta samu SANAAH har daki zatai mata nasihar daukan kaddara sai suka qare da kukan da basu iya cewa juna komaiba har tsawon lokaci kafin ta mata maganganu masu sanyi ta fito.

Sai yamma aka samu daidaituwan Fleet wanda take lamarin ya koma masa ciwo

Please Login or Register in order to submit comment