Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai karfi dan kuwa fever hadda qata fixga da jijjiga yakeyi.

Duk wannan abinda akeyi Imran raba hankalinsa yayi biyu a cikin wannan tashin hankalin ya tabbatarda ya samarwa ms meenah ticket din barin qasar a tsakiyar daren dan haka koda lokacin tafiyar yayi haka ya fito a cikin daren da mota ya tsaya cak dole saida Maamah da kanta ta fito da ita da akwatinta kaman wanda bata gani haka ta fito da ita bata hayyacinta bata iya ko magana batama san me take ba aka sakata mota baice komaiba yaja motar da speed din gaske sai a airport.

A cikin daren bai dawoba sai daya tabbatarda jirginta ya daga tukuna ya dawo gida duk da kowa yasan bata hayyacinta saita sauka kasar Morocco zata san halinda take ciki a kuma Allah ne kadai zai hana mata dawowa.

Shikuwa Dad take ya bada umarni mai zafin gaske cewan duk wani balaraben kasar Morocco idan ma matarsa da danginta ba bazai taba shigowa villah dinsa ba.

Koda gari ya waye SANAAH ma da zazzabi sosai ta tashi sbd muguwar damuwan datake ciki amma babu wanda ya sani sbd bata fitoba tana daki har lokacin,

Fleet ma da safen doctors biyu ne sukazo suka dubasa sbd yafara samun saukin zazzabinsa.

Su Dr Mum sun samu sassaucin damuwa da yar nutsuwa ganin Fleet ya dawo daidai dik da akwai zazzabi mai karfi amma kusan komai ya dan fara daidaita.

SANAAH ma sbd sunsan tana cikin damuwa da kunyar baqin ciki sai baa dameta ba duk da sun bata tabbacin babu wanda ya gani sbd group din sam babu me damuwa da shiga kowa nada abinyi kusan kowa busy yake wasu ma da yawa basa qasar suna kasashe daban daban haka shi kansa fleet din bai ga komaiba sbd shi da kansa ya zabi baya buqatan ganin.

Duk da hakan sam damuwanta bata ragu ba kaman yanda baqin cikinta ya dawo sabo.

Hajiyar Samad kuwa sai da aka aske kanta akai mata dinki har uku akai anata qarin jini da tinanin allah yasa jinin mai shiga kwakwalwanta ba.

Dad ya riga yasan a yanzu hukuncin da bai iya yankewa Samad ba shine zai hau kansa dan kuwa daman yayi masa gudun wannan ranar shiyasa ya hanasa dawowa Nigeria amma daga karshe dai kaddararsa ta janyosa dan haka baima tambaya inda yake ba sbd yasan yana hannun Imran kuma matiqar ba Fleet ne ya tashi ya ce ga abinda zaayiba akansa har abada babu wanda zaisan inda yake a hannun nasu bare iya karbansa.
#MAMUH
09033181070
[25/06, 3:21 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

144
*_SHUWA INCENSE AND MORE_*
07042293387/09118783317
Ina masoya kamshi da gyaran jiki na asalin matan da suka amsa sunansu mata?
Kinaso/kunaso ku kasance a cikin kamshin da duk inda aka jisa a tattare dake ko gidanki sai ankasa hakuri an tambayeki?
Shuwa Incense And more itace karshen inda zaki samu asalin kamshi da abubuwan gyaran jiki da mayukan gyara gashi masu inganci da kyau wanda mukeda guarantee dinsa,
Kowace irin turaren wuta na asali na gasken a gurinta ne zaku samu wanda qamshinsa kam har nesa da maqota hakama babu kalan dilka ta gyaran fata data fuska da babu a gurinta,
Kada kubi labari kawai ku siya ku gwada..SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387.

***********
Sai washe gari again tukuna Fleet ya fara samun saikin daya dawo kansa sosai sedai sam baya buqatan kowa a tareda shi sbd har lokacin konuwan da kirjinsa da jininsa sukeyi badu dena dan kuwa Meenah ta basa tabon da harya mutu bazai dena baqin cikintaba dan ta rama harta zarta abinda sikai mata da wannan haukar tata ta karshe.

SANAAH ma dai zazzabinta ya kasa boyuwa dan dole safiya ta sanar da Dr Mum SANAAH din batada lafiya sosai.

Tashi hankalin Dr mum din yayi ta tafi dakin ta tadda SANAAH din kwance a dunqule jikinta yayi zafi sosai.

Tayar da ita zaune tayi tana kallanta da kulawa sosai tace

"Tin yaushe ne kike fama da wannan zazzabin?

Shiru SANAAH tayi tana sauke kanta qasa kan na mata ciwo sosai.

Da kulawa Dr Mum tace

"Zan kira Dr bushrat tazo da kayan aiki ta dubaki amma ki cire damuwan komai a cikin ranki kinji?"

Dan gyada kai kawai tayi tana jin jikinta na sanyi.

Abinci Dr Mum ta saka safiya ta kawo da kanta ta sakata ci tana taimaka mata da kulawa sosai da wani irin tattali.

Bata barta ba zaunawa tayi tareda SANAAH din da safiya har saida SANAAH tafara jin bacci tukuna ta barta tayi bacci ta fice.

Washe gari ta dan tashi da sauki jikin nata amma damuwarta qaruwa takeyi sbd yanda daga ita harshi basu ga juna ba duk da tasan jinya yake kuma ta kasa iya zuwa dubasa sbd jin daci da radadin abin na dawo mata a duk lokacinda tinaninsa ya taho mata.

A nasa bangaren kuwa haryanxu baya son ganin kowa a tareda shi har ita din sbd bazai taba son ta gansa a yanayin dayake ciki ba zata iya tsorata sosai dan kuwa idanuwansa sam sunkasa komawa daidai.

Dr bushrat da daddare tazo ta dubata ta so mata pregnancy test amma SANAAH din taqi yadda da hakan dan haka ko data fito bata sanarwa su Dr Mum komaiba duk da kai tsaye dukkaninsu sun hango alaman ciki a tattare da ita shiyasa basason matsa mata da kuma tilasta tabbatarwa.

Dad rufe idanuwansa yayi kai tsaye aka gyarawa Mommy bangaren Meenah din a matsayin bangarenta daya gyara ya daka matarsa a ciki dukda ba wata gyara bane kawai sauya mata wasu furnitures din aka dan yi bare kuma Meenah batada komai datazo dashi bayan sitirarta kuma ta tafi da abinta kaf haka Maamah ta hada mata su.

Fleet sai daya dauki kwana shida a rufe babu wanda yake iya ganinsa bayan Imran kafin ya dawo cikakkiyar daidansa kamanninsa suka dawo daidai zuciyarsa da ruhinsa suka dawo daidai da nutsuwansu da suka rasa dan haka bai fito ba sai magrib daya fito sallah tareda mahaifinsa a masallacin gidan sanye da black jallabiya mai kyau da tsada datai masa kyau sosai nutsuwa da kwarjininsa ya fito sosai ya sake zama calm mutum.

Sallah sukai Dad din na farin ciki da ganinsa da kuma hankali da ayanxu insha Allah ya kwanta daga fitintinu.

Tare sukai sallah suna fitowa bangaren Dad din suka tafi acan ya tadda Dr Mum tana bangaren daman kusan ta dawo nan dan haka dukansu a tare suka zauna suna magana a natse da kwanciyan hankali.

Anan ne Fleet ya daga wayarsa ya kira Imran wanda ya shigo dauke da takardu a cikin wata file ya nufosa a natse da girmamawa ya gaida Dr Mum sbd shi Dad suna masallaci yanzu a tare sun gaisa.

File din hannunsa ya bude a natse yana fiddo takarda a ciki ya dan qaraso ya ajiye a kan table dake gaban Dad yana dan komawa bayan fleet ya tsaya yana bude ipad dinsa da take zai qarasa tura cike umarnin Fleet da yana turasa ya shiga inda zai tura angama kaddamar da sakon.

Kallan takardar Dad yayi a natse yana ganin abind yake rubuce a sama na su qasar America,

Shiru yayi kafin ya saka hannunsa daya yakai ya dauki takardar ahankali yana ganin sunan Samad a rubuce baro baro take ya dan sauke numfashi ahankali yana dagowa ya kalli fleet wanda idanuwansa ke kan wayar hannunsa da kira yake shigowa sbd sai yau ya kunna wayar.

Takarda ce ta jefa Samad din aikin soldier na qasar Ameria din wanda yasan abune da samad bazai taba iyawa ba sbd azabar dake cikin aikin amma kuma kaman hakan gyara ne dazai shigo rayuwarsa duk da yana jin shakkar kada a turasa kai tsaye inda sunsan wutar farko da zaa bude Samad bazai kara ko minti daya a kai labari ba.....

Kallan Fleet yayi wanda bai kallesa ba yana zaunen a natse da wata kamewa,
Maida kallansa yayi akan Imran wanda kansa yake qasa yaqi dagowa.

Dan shiru yayi na tsawon lokaci shima batareda kowannensu yace komaiba kafin ya sauke numfashi yana daukan pen dake tareda file din ya saka hannu yana fatan hakan ya zama shiriya ga Samad din da komawansa mutumin arziki.

Dad na aje pen din Imran yayi sendin komai dayake cikin ipad din hannunsa da saka hannun Fleet akan shigarda Samad kai tsaye cikik jerin sojojin yaqin dajin border duhu ta qasar take kuma informations din suka shiga suna isa inda ya kamata su isa a daren.

Juyawa Imran yayi ya fice yana yiwa Dad din godia tareda daukan files din.

Yana fita take ya fara hada tafiyar Samad din wadda bazai bari ya wuce kwanakin ba ya daga.

Fleet kuwa baiyi maganar Samad ko duk wani abu daya faruba ko daya cikin nutsuwa yayi fira da iyayen nasa har tsawon lokaci kafin suka tafi ishai.

Daga masalaccin kai tsaye bangaren su Maamah yaje ya gaidasu itada Mommy kafin ya fito yana nufar bangaren Dr Mum kai tsaye zuciyarsa cikeda wani irin sanyin dayake jin yana ratsawa da shiga kowace tsigar jikinsa.

A palon babu kowa sai safiya data fito daga kitchen zata dakin SANAAH din kai mata abinci dan haka tana ganinsa ta sauke kanta qasa tana masa sannu da zuwa cikeda girmamawa.

Da nutsuwa sauti da rashin hayaniya ya amsa a taqaice.


Hanyar dakin da SANAAH take ta nuna masa tana wucewa dakin takai tray din hannunta ta ajiye tana ficewa.

SANAAH dake kwance cikin gadonta a lafe bude kofar da safiya tayi ya sakata jin kamshinsa ya ratso dakin ahankali da wani sanyi yana shiga hancinta ta lumshe idanuwanta ahankali tana qin budewa.

Safiya na fita ya bude kofar dakin kai tsaye da wata nutsuwa da sanyi yana sako takunsa dayake cikeda kamewansa ya shigo.

Qin bude idanuwanta tayi bare motsawa tana jin idanuwansa masu kaifi sun sauka akanta yana kallanta taji jikinta ya sake mutuwa da damuwa sosai amma bata bude idanuwanta ba dan bazata iya kallansa ba.

Shi kansa cak ya tsaya akanta yana zuba mata idanuwansa da suka sauya take akanta da wata nutsatsiyar sonta da kaunar tareda kewanta mai yawa data ringa dawainiya dashi batareda ya iya barin kowace tinanin komai daya faru dawowa cikin kansaba sbd zai iya mutuwa idan har yabar tinanin wani ya tama dora hannunsa akan jikinta da niyar tirsasa kansa akanta,

A cikin kwanakin da suka wuce na faruwan wannan abin zuciyarsa ta bushe ta mutu babu adadi,
Babu daren da baya kusan dena numfashi sbd bugawan da zuciyarsa take samu da azabar daya ringa shanyewa ta kishin dayake kashesa yana kashe kowace zarrarsa da karfin halinsa,
A kwanakin bai dauka zai tana rayuwaba sbd abinda yaji dan haka ya rufe ya binne ya wanke ya goge ya batar da wannan tinanin a cikin kansa da har abada babu me kuma tayar da hakan sbd shi wanda yayi laifinma tarihinsa zai shude daga ranar daya saka kafa yabar qasar zuwa makomar da suka tanadar masa da shikenan.

Kasa dauke idanuwansa daga kanta yayi tsawon mintina kafin ya sauke numfashi mai sanyi yana juyawa ahankali ya bar dakin sbd ganin baccin datake da bazai iya tayar da ita sbd tana buqatansa dan yasan a kwanakin damuwan data shiga mai girma ce kuma fuskanta ta nuna dan ta fada kadan.

Yana fita ta bude idanuwanta ahankali tana bin kofar daya fita din da kallo me sanyi tana dora hannunta daya ahankali kan cikinta tana jin bazata taba iya rayuwa bada shiba a cikinta sbd bayyanarsa ko yanzu a gabanta duk da bata bude ido ta kallesa ba jin tayi gangar jikinta tayi sanyi mai tsanani da mutuwan jiki.

Abincin ma da aka kawo bata iya ci ba hakanan ta kwana da sanyin jiki da kewa.

Washe garin kuwa Aikin bangarenta da akeyi ne wanda tare a guri daya da mijinta kaman kowane maaurata aka qarawa gudu duk da wani babban tsari akeyi na daban da duk sauran bangarorin duk da kuma sanin cewan ba zaman zasuyiba komawa America zasuyi wannan karan shi da dawowa saiyayi retire dinsa daga aiki kwata kwata tinda tini yayi retire daga filin daga tin shekaru kusan 9 da suka wuce.

Hajiyar Samad kuwa jiki yadan yi sauki sbd ta farfado ta dawo daidai amma kanta kam ba kyan gani sbd askin da akai mata,
Damuwa sosai da tashin hankali take ciki na rashin ganin Samad tinda ta dawo daidai dan haka ta daga hankali tana cika kwana 8 aka sallameta wanda yayi daidai da saura kwana daya a tafi dashi dan haka tana dawowa gida ido rufe tayi bangarensa baya nan,

Kasa hakuri tayi ta nufi bangaren Dad wanda yake zaune tareda Fleet da Mr Sideeq suna magana hankali kwance akan lamarin Al'amin da Fammah daya kira Fleet din zasuyi ayau sbd haryanxu batasan abinda ya faru a tsakanin iyayentaba na rabuwansu.

Hajiyar na shigowa kanta dake gyallin aski Dad ya fara kalla wanda mayafinta ya zame batareda ta saniba sbd ba gashi akai bata ganewa ya kalli kan da kyau kafin tace komai yace

"Wai daman haka sukai miki askin nan??
Amma likitocin nan basu san aikinsu ba menene hakan to?
Ba iya inda zaa dinkaba ake askewa??

Da dan takaici ya qarasa zancen yana bata rai sosai.

Mr Sideeq kallo daya yayi mata ya dauke kai da sauri Fleet kuwa bai kalli ko inda ta shigo dinba.

Cikin damuwa mai tsanani da baqin cikin kalaman Dad da kuma baqin cikin ganin kan nata da sukai tace

"Samad ne banda labarin inda yake wayoyinsa dika basa shiga"

Numfashi Dad ya sauke yana kallanta a natse yace

"Kada ki daga hankalinki yana nan lfya kalau"

Takardun daya aje dan bata daman ya dauko ya miqa mata yana cewa

"Danki dai zai zama solder kaman yanda kike fatan ya zama irin Godfather dinsa"

Hannuwanta na rawa ta karba takardun ta bude tafara karantawa take taji ganinta yana daukewa sbd tariga tasani wlh Samad na tafiya shikenan sbd inda bazai taba dawowa a rayeba Fleet ko yaransa zasu turasa.

Cikowa da wasu hawayen tashin hankali tayi tana dagowa ta kalli Fleet wanda har lokacin baima san da ita a palon ba dan bata samu daman idanuwansa masu daraja suka kalletaba sako yake karantawa a natse a kame a cikin wayarsa.
#MAMUH
09033181070
[26/06, 12:18 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

145
*_SHUWA INCENSE AND MORE_*
07042293387/09118783317
Ina masoya kamshi da gyaran jiki na asalin matan da suka amsa sunansu mata?
Kinaso/kunaso ku kasance a cikin kamshin da duk inda aka jisa a tattare dake ko gidanki sai ankasa hakuri an tambayeki?
Shuwa Incense And more itace karshen inda zaki samu asalin kamshi da abubuwan gyaran jiki da mayukan gyara gashi masu inganci da kyau wanda mukeda guarantee dinsa,
Kowace irin turaren wuta na asali na gasken a gurinta ne zaku samu wanda qamshinsa kam har nesa da maqota hakama babu kalan dilka ta gyaran fata data fuska da babu a gurinta,
Kada kubi labari kawai ku siya ku gwada..SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387.

***********
Kukan tashin hankali da baqin ciki me tsanani Hajiyar takeson riqewa yana kasa riquwa tana kallan Fleet tana sake riqewa amma yana kasawa ta bude baki tace

"Kada kayi masa wannan hukuncin dan girman Allah da manzonsa wlh kaddara ce da mummunan aikin shedan kuma a baya"

Dad daya kalli Fleet ya maida kallansa akanta cikin takaicin askin da akai mata tas ya bude baki yace

"Ga abinda ya kamata kiyiwa kuka kina mace da girmanki da mutuncinki ayi miki aski irin wannan tsabar basuda tinani,
Shi da kikeson yiwa kuka aikin soja ne fa aka turasa ba fagen mutuwa ba"

Kasa riqe baqin ciki da takaicin Dad din tayi sbd a bayyane hukuncin Fleet yake akan Samad inda zaa kashesa ne fit batareda yayi karin ko sati daya a duniya ya turasa ba wai asalin aikin sojan ba amma kowa yayi kaman bai ganeba ana nufin danta ya cancanci kisa kenan akan abinda yayi ko me?
Ya cancanci kisa akan laifin da baima aikataba?
Laifinda a gurinsu ma kamata yayi suce gwara da akai tinda gashinan akan hakan dukansu suka samu SANAAH da ahalinta.

Kuka mai karfin gaske ta fasa tana cusa fuskanta a tafin hannuwanta mayafinta na sake zamewa Mr Sideeq ya sake dauke kai sa sauri Dad kuwa mamaki da takaicin asibitin ne ya kuma rufesa yana cewa

"Ah ah ikon Allah"

Babu tashin hankali da damuwa danshi damuwansa ma da tausayinta akan kanta ne da babu shaawan kalla ko kadan dan shi kam yana kaunar gashi sosai akan mace tin yana lokacin kuruciya dan haka da dan tausasa harshe yace

"Kukan ya isa kije ki kula da kanki tukuna shima Samad din zakiji dadin abinda zai zama a gaba,tashi kije"

Rokon Fleet ta fara yi tana kuka sosai da neman sassauci da yafiya daga garesa sai a lokacin ya dan juyo a tsanake ya kalleta yana ajiye wayarsa gefe da kamewansa mai hade da zallan nutsuwa ya kalleta ya bude baki ya fara bata hakuri da kuma dora mata bayani na kai tsaye sunan Samad ya riga ya shiga Adduarta kawai suke buqata.

Yana gama mata wannan bayanin ya miqe batareda sake kallanta ba dan daman ba wani kallan mata yakeyiba sosai tsoffi da iyaye da yan mata da matasa dan haka maida kallansa yayi kadan akan Dad yayi masa sallama ya fice yabar palon.

Kasa cewa komai tayi sbd yanda zuciyarta ke tsananin radadi da quncin da tinda take bata taba jinsaba dan wlh tallahi ta sani inda samad bazai taba dawowa bane suka turasa wasu zafafan hawaye masu tsananin radadi suka gangaro daga idanuwanta dana sanin aure da rayuwa a cikin ahalin jeerahs na mamaye kirji da zuciyarta a karan farko rayuwarta,

Dana sanin hada zuria dasu da kuma kasancewan Danta jininsu ne ya cika idanuwa da zuciyarta ta sake tsiyayo wasu hawayen tana rufe idanuwanta jikinta na wata irin mutuwa da baqin cikin da shine kila zaiyi ajalinta matiqar Samad ya tafi a goben.

Miqewa tayi tana ficewa batareda ta waiwayo Dad ba wanda ya bita da kallo a natse yana dan tausawa lamarinta da kusan itace matsalar rayuwarta data danta da kanta.

Tana fita ko gani sosai batayi ta isa bangarenta tana shiga ta silale a palo ta zaune a qasa tana fasa wani irin kuka mara sauti mai karfin gaske dayake fitowa tin daga kasan zuciyarta tanajin baqin ciki zai kasheta.

Nabeela data fito itama zaunawa tayi a palon tana sunkuyar da kanta qasa da wani irin yanayi mai daci da damuwa mai tsanani tana hawayen tausayin hajiyar dana Samad dan itama kanta tasan ma maganar yaje wai su sake ji daga garesa bare ganinsa sai wani babban rabo daga ubangiji gashi hajiyar batada kowa sai Samad din ba miji ba 'da ba aure kuma daga karshe dai lokaci yayi dole na barin JEERAHsV dan kuwa babu abinda zata zauna tayi koda baace mata komaiba dan a baya tana sakaran komawa auren Dad komai daren dadewa amma ayanzu da Dr fammah ta dawo rayuwarsa babu kowace macen da zata kuma iya shiga rayuwarsa da Dr famman ce kadai a cikinta tin a farko kuma har a karshe.

Kuka suka zauna suka ringa yi mai ciwo da zallan baqin ciki da dana sani kala kala har tsawon lokaci kafin suka iya tashi kowa ya shige dakinsa.

A cikin daren aka aikowa hajiyar zuwa ganin Samad su gana kafin wucewansa da asuba dan haka jiki a mace hankali tashe ta isa har bangarensa da aka dawo dashi sedai sa securities din da zasu tsaresa har asuba lokacin tafiyar.

Tana shiga a can dakinsa ta taddasa zaune a qasa rakube yana jin bude dakin ya dago idanuwansa da sukai wani mugun zurfin gaske sun bushe kaman wanda aka tono daga rami hakama bakinsa ya bushe sosai kaman wanda yake cin tuwon qasa akan kansa dayake daukan idanuwanta da wani mugun askin da akaiwa kansa sol ta sauke idanuwanta tana jin wani mugun jiri na dibanta ta rintse idanuwanta da karfi tana fasa kuka mai sauti sosai tana ambatar sunansa da isa gurinsa da sauri ta zube qasa tana rungumosa jikinta dake rawa sosai tana sake tsananta kunanta sbd ansauya mata kamanninsa gabaki daya ya koma kaman wanda aka karbo hannun bandits.

Bai iya motsawa ba daga zaunen dayake idanuwansa sunyi jajir babu abinda ya iya furtawa yana jin kukan hajiyar tanayi tana tsinewa Fleet da ubansa da kaf dangin uwar fleet din dana SANAAH tin kakanni tana kira musu balai da masifu.

Yanda take tsine musu ne tana qara daga murya kusan har securities din wajen bangaren suna jinta tanata yi harta dawo rokon Allah ya hana Samad din tafiya allah ya hanasu kaimata shi inda sukeso.

Sai a lokacin ne Samad ya fasa wani irin kuka mai karfi yana sunkuyar da kansa sbd shi kansa yasan hukuncin kaman kisa ne aka yanke masa a dunqule sbd sanin da akai ko gaban ruwa me yawa baya iya tsayuwa zai iya rasa ransa amma aka yanke shawarar aikasa sojan ruwa kuma kai tsaye babu training ba komai zaa kaisa inda yasan wlh bazai taba wuce satiba idan yayi tsanani dan haka yasan babu sauki ko rangwame ko bada second dama a hukuncin sakasa soldier.

Ganin kukan Samad din wanda tinda ta haifesa ya girma ya fara zama saurayi bata taba ganin yayi ba ya sakata qarasa zarewa gabaki daya ta ringa ihu tana kuka tana kiraye kirayen sunaye kaman ta haukace tana tsinewa tana kuma roko dayake dare yayi sosai kusan kaf bangaroran ana jinta tanata wani irin kuka da ihu da neman agajin kada a rabata da danta.

Su maamah da duka kowa yana jinta jikinsu sanyi yayi dukansu sun tausaya mata matiqar gaske sbd a cikin lamarin nata akwai tausayi.

Asubar fari Imran ne da kansa kuwa ya shigo aka fito da Samad din yayi wanka ya shirya a cikin wasu kayan sanyi yayi sallama da mahaifiyarsa datake riqe dashi karfinta tas ya qare sedai idanuwa daqyar aka banbareta daga garesa Dad dinsa yayi magana sosai dashi akan basa tabbacin insha Allah babu abinda zai samesa kuma zai samu sauyi da aminci a rayuwarsa shine fata da adduar dayake masa tareda saka masa albarka a cikin danne komai da kallansa a matsayin dansa jininsa.

Har a cikin ransa Dad bai ji akwai wani boyayyen hukunci a cikin hukuncin Fleet dinba saima gyaran dayake kallo zai kawo a rayuwar dan uwansa dan haka da addua da komai suka rabu shima Samad din yaji ya samu nutsuwa da aminci a cikin tafiyar duk da yana cikin tsoro mai tsananin gaske.

Suna barin gidan hajiyar ta yanke jiki ta fadi a some babu numfashi a jikinta sbd riqe ake da ita har motocin suka fice.

Kwasarta akai aka wuce bangarenta da ita dan taimaka mata ta farfado ta dawo daidai.

Su maamah ma babu wanda ya fito daman bare Dr Mum da tana can bangarenta da SANAAH wadda take tarairayanta akan yanda dik ta shiga damuwa ta rasa walwala da sukuninta gashi tana lura da sam ta kasa yadda ta hadu da fleet din dan haka take kokarin ganin ta sakata dawowa daidai.

Da daddare Dad ya zauna da Fleet palonsa suna magana sama sama akan abubuwan da suka shafi aiki.

A cikin maganar Dad ya dan yi shiru a natse kafin ya dago ya kalli fleet a tsanake ya bude baki yace

"Akwai maganar Fammah da Al'amin wadda take kwance tin bayan zuwanta can wadda bayan nazari da duba akan duka halayyarsu da tarbiyarsu da kuma sanin matakin da kowanensu yake akai na tsarin rayuwa naga dacewansu da ni nake nemawa Al'amin aurenta a hannunka wanda daurin auren kawai nakeso batareda kowace hayaniya ba sbd mahaifiyarta da bazata taba yadda da aurenba bakuma wai dan ana shakkarta ba sai dan zata iya barazana ga yar tata ta hanata yadda da auren"

Shiru Fleet yayi yana dan dagowa a tsanake ya kalli Dad din kafin ya dan maida bayansa ya zauna dakyau ya bude baki ya korowa Dad din bayanin matiqar Famman da Al'amin na kaunar juna da kuma raayin auren junansu he's ok da hakan ya bawa Al'amin din aurenta.

Ajiyan zuciya da numfashi Dad ya sauke yana cewa ya basa daman magana da yarsa kuma shima da kansa a kwanakin zai isa Italy yayi zama dasu da magana dasu mai kyau.

Da haka sukai sallama fleet ya baro bangaren Dad ya isa bangarensa ya daga wayarsa ya kira Imran yace yana buqatan tafiya italy zuwa ga yarsa dan yanada zama da ita dan haryanxu ma batasan sun rabu dashi da mahaifiyarta ba.
#MAMUH
09033181070
[26/06, 1:49 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

146
*_SHUWA INCENSE AND MORE_*
07042293387/09118783317
Ina masoya kamshi da gyaran jiki na asalin matan da suka amsa sunansu mata?
Kinaso/kunaso ku kasance a cikin kamshin da duk inda aka jisa a tattare dake ko gidanki sai ankasa hakuri an tambayeki?
Shuwa Incense And more itace karshen inda zaki samu asalin kamshi da abubuwan gyaran jiki da mayukan

Please Login or Register in order to submit comment