Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana isowa abinda yafara cin karo dashi kenan zubewan cikin da baifi awa biyu da saninsa ba,
Rasa jininsa da baima kai ga tabawa ba bare tarbonsa duniya,
Tsatsonsa dana yarinyar datake breaking kowane record na rayuwarsa,
Tsatsonsa da macenda yakejinta a cikin jini da ruwan jikinsa....

Dago idanuwansa da suka tsananta rikicewa da mugun ja yayi gabaki daya ya kalli Dr Akin bai iya furta komaiba sai kalman

"Muje a bata jinin"

Miqewa yayi har lokacin babu wanda ya iya cewa komai musamman Dad jeerah da rintse idanuwansa kadai yayi ya budesu akan kofar dakin yana fidda numfashi daya mai zafin gaske.

Tashin hankalinsu komawa yayi zallan baqin ciki da damuwa mai tsananin gaske wadda bazasu taba mantawaba anan kowa yafara jin zafin kansa dana Meenah din amma dai babu karfin iya cewa komai sbd kusan hali da dabiar Fleet da mahaifinsa ta idan bacin rai da fushi yayi tsananin da zasu iya illa to basa cewa komai shiru shine abinda sukeyi sbd kaman shine yake bawa jininsu dake tafasa daman control kansu.

Jini aka saka mata na fleet din wanda yayi daidai ana gama saka mata ana kiran asuba dan haka Su Dad gavaki dayansu masalacci suka nufa su Dr Mum kuwa suna dakin.

Daga masallaci suna dawowa gari ya fara haske dan haka motar da zaa maida SANAAH din gida aka tanada ambulance mai kyau ta musamman suka dawo gida da ita anan doctors zasu dawo dubata duk da batama farfado ba yanda ya kamata ta farka amma bata wani hayyacinta ta sake komawa bacci doctors sun tabbatarda insha Allah data tashi shikenan babu wata sauran babbar matsala.

Koda suka iso JEERAHsV koina tsit dan haka kai tsaye bangaren mommy aka wuce da SANAAH sai baa kaita dakin Mommy ba aka kaita dakin Maamah wadda Dad ya kalla da kakkarfan hukuncinsa mai zafi sbd sai a lokacin ya bude baki yace

"A yanzu babu sauran abinda ya rage tsakaninta da 'danku,
Na yanke alaqarta dashi idan har akwai wanda zaiyi jayayya da hakan to wlh zaiga bacin raina da zai raba tsakani da yawa,
Bazance komaiba akan abinda 'yarku tayi sbd ba laifinta bane kune da danku masu laifin dan haka na yanke alaqarta dashi batada hadi dasu a yanzu dan haka duk abinda matarsa zatai yanzu shine zata shiga hurumin dayake nawa"

Yana gama fadan hakan ya wuce hanyar bangarensa yabar su Maamah din cikin sabuwar damuwa mai tsanani da tashin hankali,

Fleet kuwa baya buqatan ganin kowa kaf duniya kuma baa gabansa Dad ya yanke hukuncin ba dan haka bangarensa ya nufa kai tsaye ya shige wanda take imran ya saka aka bawa hanyar tsaro dan kuwa yau ko ms meenah bazaa taba barinta shiga ba haka Imran ya bada umarnin mai karfin gaske kafin ya nufi bangarensa dan kimtsawa tukuna yafara bada lafiyayyan binciken asalin abinda ya faru kafin Fleet ya dawo daidai ya jere masa bayanin komai na abinda ya faru din.

Fammah kuwa tin cikin dare ta farko ta dawo daidai amma ta kasa motsawa tana kwance shiru idanuwanta jajir tana hada tinanin abubuwa da dama da sai yanzu ne take gane menene maanarsu.

Irin kallan da SANAAH ke mata da abinda ya faru a Morocco da yanda SANAAH ta ringa kwana da mahaifinta suna guri daya amma basu taba ganewaba....

Rintse idanuwanta tayi wasu hawaye masu tsananin zafin gaske suka gangaro mata ta kife kanta tana kasa riqe kukanta tafara rero wani irin kuka mai tsananin gaske da ratsa zuciya tana jin kirjinta na tsananin zafin da bazata iya daukaba,

Mutane biyu datake tsananin so a rayuwanta meyasa zasu mata haka?
Meyasa Dad bazai fada mata SANAAH matarsa bace?
Meyasa SANAAH bata fada mata Dad dinta shine mijin da akete cewan tanada shi ba??
Yanzu tayaya zata iya kallansu bayan abinda sukaiwa Mum dinta da tafi jin radadin abinda Mum din ke ji wadda tasan bazata taba iya barin SANAAH ba saita rabata da duniya ko illatata.

Mommy data rasa abinyi ko fada tana jin irin kukan da fammah din keyi ga wani irin kunyar fammah din da kusan itama fammah din tafi kunya ta zauna gefenta tana dan dafata ahankali da bude baki tana bata hakuri da rarrashinta da wata irin kulawa da damuwa.

Har asuba suna cikin wannan mugun yanayin har sukai sallah suka zauna jigum jigum gari na qarasa wayewa fammah din ta fito a sanyaye tabar bangaren ta nufi bangaren mahaifiyarta tana fita suna dawowa da SANAAH din.

Ko data isa bangaren taji tsit babu motsin Mum kai tsaye dakinta ta nufa ta bude tajisa a rife ta kalli kofar sai taga key a jikin kofar ta waje dan haka da sauri ta bude key din tana budewa.

Mummunan faduwa gabanta yayi ganin halinda dakin yake ciki sbd babu abinda bata fasa ba ta buga da kasa.

Rawa jikin fammah ya fara ta shigo dakin gabaki daya tana jefa idanuwanta koina bataga Mum din ba zata juya a rikice futa nemanta taji anbude kofar bathroom din dakin ta juyo da sauri saiga Mum dinta fito idanuwanta da fuskanta sunyi wani irin jan da basu taba yiba ta zubawa fammah idanuwanta da suka sake fammah fara hawaye da sauri tareda tahowa da wani irin sauri ta rungumeta tana cewa

"Mum dan Allah kifi karfin zuciyarki kada ki illata kanki"

Ahankali ta daga hannuwanta da basuda karfin ta rungume fammah din wasu hawaye masu tsananin zafin gaske suna gangaro mata ta ja wani numfashi mai karfin gaske sbd yankewan da numfashinta ke son yi tin jiyan tana riqesa dan kaman ma attack takeson samu amma karfin halinta yaqi bari.
#MAMUH
09033181070
[16/06, 3:23 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

120
Janta fammah tayi suka fito dakin kaman mara gani komai na jikinta a sake yake batada kowane sauran tinaninta da hankalinta sbd ta kasa yadda itace mijinta fleet dinta yake kwana da wata macen bayan ita,
Itace Fleet dinta ya hada jiki da wata macen,
Itace Raheem din data gama tabbatarda nata ne ita daya har qarshen duniya yau cikinsa ya bayyana a jikin wata ba ita ba kuma wai yarinyar datake tareda ita a matsayin yarta da sanin kowa kuma.

Dakinsu fammah ta kaita ta zaunar a kan kujera tareda komawa dakinta ta dauko mata kayan sakawa ta kawo mata sbd ruwa ta sakowa kanta ta jiqa kanta gabaki daya.

Da taimakon fammah ta sauya mata kayan sbd komai nata bata iya motsawa da kanta,
Sallah fammah ta sakata yi wadda ta tabbatarda bata samu yinta ba tana idarwa suka zauna sukai shiru babu me iya cewa komai kowa ya sake shiga tinani mai zurfin gaske.

Mommy jin cikin SANAAH ya fita itama taji damuwa da sanyin jiki duk da ganin SANAAH din a kwance kaman babu sauki a tattare da ita haka ta tafi kitchen kusan tafi ma safiya dan karfin hali haka sukai aikin breakfast suka gama babu wanda ya fito breakfast din kowa yana daki tsit ba motsin komai kusan duka JEERAHsV dinma shiru tayi.

Sai guraren 11 na safe Maamah ta fito taje ta hado tea mai kaurin gaske ta kawowa SANAAH wadda ta farka amma bata motsaba daga kwancen ta bude idanuwanta wasu hawaye masu tsananin zafi suna gangarowa daga gefen fuskanta.

Tayar da ita zaune Maamah tayi tareda kamata ahankali zuwa toilet suna shiga ta hada mata ruwan wanka masu tsananin zafin gaske ta fito.

Batada karfi ko kadan harma da jiri jiri take gani dan haka ta ahankali ta shiga ruwan ta zauna tana sunkuyar da kanta kuka na zuwar mata mara sauti tana fara rerowa kirjinta a cunkushe.

Ta jima sosai a ciki kafin ya fito ta zauna ahankali safiya tana dakin ta kawo mata kayan sakawa sai kuma ga Maamah itama da tea da magani.

Bata iya shan tea din ba kadan ta dan sha aka bata magani tasha daidai nan Dr Mum ta shigo dakin dubata jikinta a matiqar sanyaye zuciyarta ba dadi sam ta kalli SANAAH din wadda itama ta kasa kallanta ta zauna gefenta tana dubata cikin kulawa da bata hakuri sosai akan abinda ya faru.

Bacci ta koma suka fice daga dakin ana gama sallar azahar dr mum da Maamah suka fice zuwa bangaren Meenah sbd ko fammah bata fitoba bare ita.

Suna ficewa shi kuma a daidai lokacin ya iya fitowa ya tinkaro bangaren ya shigo safiya na ganinsa da girmamawa sosai ta gaidasa ya amsa yana bude baki da wata muryansa datai kauri sosai babu rahama ko daya har lokacin a fuskansa ya tambaya inda SANAAH din take.

Dakin Maamah ta sanar dashi cikeda girmamawa bai kalletaba ya wuce dakin.

Koda ya shiga bacci takeyi dan haka ajiyan zuciyan da bai saukeba tinda ya sauka kasar ya sauke ahankali tareda zuba mata idanuwansa da suka fara sauyawa wata wutar radadi na taso masa yana jinta cikin jininsa amma bazaiwa Meenah din komaiba a yanxu zataci darajar yarsu da kuma laifin da akai mata duk da shi laifin zubar da cikin zaibi ta kansa ne daga lokacinda ya samu cikakken bayanin abinda ya faru tin daga farko sbd zai tabbatarda ta karbi hukuncin laifin nata.

Takowa yayi ahankali cikin nutsuwa da kamewansa data kame sosai sbd babu kowace walwala a tattare dashi.

Cikin nutsuwa ya zauna a sofan datake facin din gadon yai folding hannuwansa yana zuba mata zafafan idanuwansa da zafinsu shi kansa yakeji sbd radadin dayake cikinsu.

Bai dauke idanuwansa daga kanta ba yana jin ciwo da radadin dayanzu tana dauke da gudan jininsa haryanxu,

Ahankali cikin bacci taji nauyin idanuwansa akanta ta bude idanuwanta ahankali cikin sanyi da rashin kuzari suka sauka akan fuskansa datake kallan tata ya dan sauke wata ajiyan zuciyan ahankali tareda motsawa ya dawo gabanta ahankali tareda durqusawa ya dora tafin hannunsa daya akan nata ya kama ahankali tareda bude baki yace

"Hi" daqyar muryansa a shaqe.

"Yaya jikinki?
Yaya kike feeling yanxu?

Sake dan hade hannuwansu yayi ahankali yana kallan cikin idanuwanta da suka ciko da wani irin hawaye tana kallansa ta kasa bude baki sai daya daga hannunta yakai bakinsa yayi kissing ahankali tareda kasa cewa komai sbd abinda yake ji ya dan dauke idanuwansa daga cikin nata sbd jan da sukai zasu iya bata tension sabo.

Sake tambayarta yayi yanda takeji ta dan rintse idanuwanta ta bude tareda bude baki kaman kuka zai zuwar mata tace

"Banajin dadi sam,I'm not ok,zuciyana.....

Hannunsa daya da baya riqe da hannunta ya saka ya rufe mata baki yana dan hanata maganar da zata ci karfinta yace

"Ki warke first okay?

Shiru tayi tana janyewa daga hannunsa ahankali tareda juya masa baya ahankali tana shin shiru alaman shima ya tafi kawai bata buqatansa.

Shiru yayi yana kallanta yaga alaman bata son ganin nasa hakanan dan haka ya miqe tareda gyara mata rufarta ya fice.

Yana fita bangarensa ya sake komawa baya buqatan kowa bai kuma bi ta kan Meenah ba sbd har lokacin zuciyarsa bata gama dawowa daidai ba yana tana buqatan tayi nesa dashi.

Su Dr Mum kuwa suna shiga a palo suka samu fammah da mum din tata zaune tana kokarin ganin taci abinci amma har lokacin idanuwanta a bushe suke sunyi wani irin ja bata ce komaiba bata yi komaiba kuma bata motsin komai guri daya take qurawa ido tayi shiru sai wata irin ajiyan zuciya datake saukewa mai karfi akai akai wadda itace take daga hankalin fammah.
MAMUH
09033181070

Mamuhgee

121
Zaunawa sukai dukansu babu me walwala babu kuma wanda yake cikin sakewa ko kadan.

Fammah da jikinta yake tsananin sanyaye cikin rashin kuzari da kasa kallansu ta bude baki ta gaidasu tana dan riqe hannun mum dinta cikin nata data sarqe sbd koma me sukazo fada mata ta bata sassaucinsa duk da su dukan suna buqatan sassauci daga duk abinda zasu ji ayau din.

Maamah ce ta fara bude baki tace

"Fammah yaya jikin naki?
Kada ki sakawa kanki damuwar da zata illata lafiyanki kinji ki lura da kyau"

Gyada kai famman kadai ta iya yi kafin Dr Mum ta bude baki da kulawa duk da suna cikin tsananin bacin rai da baqin ciki da tsananin zafin abinda Meenah din tayi amma kuma zasu danne sbd sun yadda da basu kyauta mata dinba na boye mata komai dan haka ta kalleta cikin larabcinsu tace

"Meenah nasan baa kyauta ba amma kisani duka komai daya faru yazo ne a bazata garemu sbd mu kanmu bamusan da auren ba sai daga baya,
Hakama shi kansa Raheem koda mahaifinsa ya daura masa aure da SANAAH din bai sanar dashi ba sai bayan hakan,
Nice na zabi boye maki sbd naso raba auren da farko kafin daga baya duka muka hakura sbd auren bame rabuwa bane,
Munyi miki laifi kuma duka kowa yayi kuskure amma ki kwantar da hankalinki sbd babu wanda zai taba wulaqantaki ko cutarki a cikinmu sbd kema 'yace da muke kaunarki kinsani."

Maamah ce ta karbi zancen da zayyane mata komai da karawa da tausarta da nasiha.

Dagowa Mum din tayi idanuwanta sun tsananta wani irin jajir hannuwanta na dan rawa ta zuba musu idanuwanta cikin kanta da kirjinta yana ci da wata irin wutar da har a hannuwan fammah tana ji ta bude bakinta dayake rawa tace

"Shekaru Kusan goma da auren da bansaniba"

Wata ajiyan zuciya ce ta kufce mata mai karfin gaske jikinta na qara rawa fammah ta qanqame hannunta a cikin nata tana dan ambatar sunanta kadan sbd bata sassaucin abinda takeji.

Koda Maamah taci gaba da bayaninta babu abinda Meenah din takeji sbd jinta ya dauke dip har suka gama suka miqe suka fice bata motsaba bata dagoba bata kuma sake cewa komaiba.


Bayan fitarsu ta miqe ta shige dakinta ta rife kanta a ciki haka fammah ta wuni ita daya cikin tsananin damuwa da jin tashin hankali itama ta koma dakinta ta rufe kanta.

Gap da Magrib Meenah ta fito daga dakinta ta fice kai tsaye bangaren Hajiyan Samad ta nufa ta nufa idanuwanta basa gani sosai tsabar jan da sukai.

Tana shiga hajiyar na zaune da abun wuya a wuyanta daya kumbura tana ganin Meenah ta miqe tsaye da sauri tana kallanta da daukan wani decor na glass dake gurin dan kuwa yau itama a shirye take da aika Meenah din lahira idan ta tabata.

Samad ne ya shigo wanda shima yanayinsa ba sauki ta kallesu duka su biyun tana bude baki kai tsaye tace fada mata yanda akai auren Fleet da SANAAH.

Hajiyar na jin hakan ta dan ajiye abin hannunta tana kallan Samad wanda kai tsaye baiyi tinanin komaiba ya kalleta yace

"SANAAH tawa ce tin farko kuma haryanxu bazata zama ta kowaba"

Wani irin kallo meenah ta masa hakama hajiyarsa sbd sam baida tinani dan haka tai wuf ta amshe zancen da cewa

"Fyade akai mata sbd ubanta ya rufa mata asiri ya aurawa mijinki wanda aka taru kaf dinsu suka boye miki tareda baki ita kika ringa yawon duniya da ita tana kwanar miki da miji.....

Wani mugun numfashi meenah ta fitar jikinta na sake daukan rawa daya saka hajiyar cigaba da zuba mata maganganun dake zarar mata da kwakwalwa gabaki daya dan haka bata baro bangaren ba sai dare.

Karfe daya da rabi na tsakar daren ta fito kai tsaye ta nufi bangaren mommy da dukansu suke ciki kowa baccinsa yafara nisa sosai sbd lokacin.

Wani tafasa da quna da hayaqi kanta yakeyi batajin zata iya numfashi idan bata raba mutanen da suke bangaren gabaki daya da duniya ba dan haka petrol din hannunta ta fara zubawa a kofar bangaren har zuwa baya ta buga ashana kawai tana jefawa fammah datake zuwa dakinta akai akai dubata dan tabbatarda bataiwa kanta illaba dataga bata gantaba ta fito cikin tashin hankali dan zuwa bangaren Dad dinta sai kuwa ta ganta da gudu ta qaraso tana ambatar sunanta da karfin gaske.

Wuta kuwa a bangaren take ta kama gadan gadan sbd sosai ta zuba petrol.

Hajiyar Samad data kwana da shirin babu alkhairi ko sauki a yanayin dataga meenah din kuma a yanda ta zare da jin abubuwa ta tabbatarda a daren meenah bazata rasa abinyi ba dan haka a kunnenta fammah ta kwada kiran mum din dan haka zumut tayi ta taso ta fito.

Wuta tagani da wani irin zafi ta iso gurin tana kallan wutar na ci tafara wani mazari tana son wutar tashiga ciki sosai tafara cin wanda suke ciki kafin tayi ihun ceto sbd so take akan idon hakeem dr fammah taci wuta ta tafi su huta.

Imaran da baiyi bacci ba a lokacin shine yafara jin kaman motsi sbd wutar tafara girma sosai dan haka kai tsaye ya fito yana sako kai ta sama ya fara ganin wutar take ya qarasa fitowa da tsananin sauri Hajiyar Samad na ganinsa ta dora hannu akai tafara ihun wuta da karfin gaske tana nuna meenah wadda fammah ke kokarin janyewa.

Ihunta ya saka securities fitowa da saurin gaske sunayowa ciki take hanayiya ta tashi.

Dad kaman daga sama ya ringa jin ihun wutar hajiyar na cewa

"Innalillahi Meenah ta kona Dr fammah kurmus.....

Bai san ya akai ba sai samun kansa yayi yana fitowa da wani irin mummunan tashin hankalin da rayuwarsa bata taba shigaba yana nufo bangaren dake ci da wutar sosai....

Isowansa tayi daidai da isowan Fleet a asalin futan hayyaci shima yana tinkarar wutar kai tsaye idanuwansa a rufe kaman yanda na Dad din suke a rufe zasu fada Imran da securities suka riqesu da tsananin karfi hankali tashe

Umma ma tini suka fito Samad na isowa kai tsaye yayi kan wutar yana kwala ihun kiran SANAAH idanuwansa a rufe hajiyarsa ba shiri ta saki zaninta tana yi kansa a haukace da ihun kiran sunansa.
#MAMUH
09033181070
[17/06, 10:29 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

122
Cikin tsananin daga murya mai karfin gaske Imran ya bawa securities dinsu da suka qarasa isowa da gudun gaske umarnin su taru su saka karfin gaske su riqe Fleet wanda karfinsa yake kokarin fin nasu gurin kwacewa dukkanin jikinsa na wata irin zabura da karfin gaske yana kiran sunayen Mum da Maamah da SANAAH wadda yakejin sedai wutar ta kone harda shi daya iya kallan su rasa rayuwarsu a ciki.

Hajiyar Samad ma damqar hauka ta fada gap da wutar tayowa samad daya kusan shiga babu wanda ma ya lura dashi bare ya riqo mata shi data wani irin ihu tana qamqamesa gabaki daya da hannuwanta tana jansa da tsananin karfi hankalinta na ficewa daga cikinta masu aikinta biyu da yar riqonta a rikice suka tayata qamqamesa suna jansa yana wata irin fuzgewa yana kwala kiran sunan SANAAH.

Dad ma da dukkanin jikinsa ke wata irin rawa idanuwansa na neman fitowa da asalin tashin hankalin da matiqar Dr Mum tabar duniya ayau yasan bazai rayuba dan haka ya zabi shiga kozasu rasu ya gwammaci rasuwa tareda ita akan yana gani wutar ta cinyeta yana waje dan haka wani karfin gaske yake nunawa kaman ba babban mutum ba yana kwacewa da son fadawa Su Mr Sideeq da soldiers din gidan suna riqesa yana kwala kiran Dr fammah da basu umarnin suyi gaggawan sakinsa amma sam sun kasa.

Fammah da idanuwanta sukai jajir sun ciko da wasu zafafan hawaye masu tsananin radadin abinda yake faruwa takawa da gudu ta isa gaban Dad dinta daya fice hayyacinsa gabaki daya ya tashi daga fleet Raheem mahaifinta kwata kwata data sani ya koma kaman qaramin yaron dayake kallo mutanen dayake tsananin so a duniya zasu tafi su barsa akan idonsa tafiyar dazai rasasu har abada wani ihun kiransu yakeyi yana nuna tsananin karfi amma mutanen da suka riqesa sunfi su shida sun nuna nasu karfin sun kasa sakesa.

Tana isowa gabansa da wani irin karfi ta fada jikinsa ta qanqamesa tana fasa kuka mai tsananin karfi tana kara riqesa itama dan bazata iya ganinsa ya shiga wutarba ta fara kokarin kiran sunasa amma gabaki daya ya rasa hankali da tinani da ganinsa da jinsa.

Imran ne cikin tashin hankali da tsananin sauri ya bawa sauran soldiers din umarnin buga kofar a budeta sbd wutar bata riga tayi yawa a ciki ba daga wajenne tafi yawa.

Ankira firefighters tini dan haka Imran dinne ya fara jiqa jikinsa gabaki daya da ruwan dake harabar gidan cikin wata kyakkyawar roundabout dake tsiyayar ruwa tukuna ya ja baya sosai ya tafi da wani irin gudun gaske ya banki kofar da kafafunsa amma bata bude ba.

Sauran securities din gidan da duka sauran ahalin gidan maza da maaikata kowa tini ya fito suka ringa shiga ruwan suna jiqa kansu da tsananin sauri suna zuwa da gudun gaske su banki kofar wadda ta kulle ko motsawa batayi amma sbd yanda wannan nayi ya koma baya wannan yazo da gudu ya banka shima haka suka ringa yi hankali tashe da tsananin karfi ga wutar sai qara yawa takeyi imran yi yakeyi yana ihun kada a kuskura a saki Fleet da Dad wanda karfinsa shima baiyi qasa ba ko kadan bai dena tsananin haukan son kwacewaba.

Samad ma bai dena kokarin fadawa ba cikin tsananin haukar data juyar da kansa bayaji baya ganin komai hakama hajiyarsa ihu takeyi suna qin sakinsa tana neman zarewa sbd wutar ta qarasa zafafan gaske zafinta jinsa sukeyi sosai suna wani zufan daya saka suke kasa riqe samad din da kyau ihunta da haukacewan datake yi shi ya sake saka yanayin cikin mummunan rikicewa da tashin hankalin daya fiddo Umma hankali tashe ta iso jikinta na rawa taga yanda wutar ke ciki ta juya da sauri ta kalli inda Dad yake yana rasa kansa da manta shi waye gabaki daya wuyar yake son shiga sbd wadda take ciki data fi masa rayuwarsa.

Jin tayi kanta ya sara yana mata wani mugun nauyi har saida jiri ya dan debeta tana kasa dauke idanuwanta daga kansa muryansa harta fara toshewa sbd karfin yanda yake kiran sunan Dr fammah din wadda acan ciki dikkaninsu sun fito cikin tashin hankali daga dakunansu sbd hayaqi da wani irin zafin daya saka jikinsu wata mummunan zufa take fitarwa kaman ruwan sama sbd azabar zafin wutar.

A palo suka hade hankalin kowannensu a tashe suna kasa isa kowace kofa sbd wutar tariga ta shigo ta zagaye koina.

Dr Mum ce ta riqe SANAAH wadda Maamah ta kamo ta fito da ita jikinta na tsananin rawa hakama ko gani sosai basayi ga karfinsu dayake neman qarewa sbd tari da hayaqin dayake shiga huhunsu zamewa SANAAH tayi a gurin ta yanke jiki ta fadi sbd batada lafiya daman sai ita tafara fara somewa.

Mommy ma fara kasa jan numfashi tayi ta durqushe a gurin tana dafe kirjinta jikinta na kakkarwa
Kafin dukkaninsu su qara shiga mummunan tsoro da tashin hankali Maamah ma zubewa tayi a gurin Dr mum datai kokarin kama dukansu karfinta kasawa yayi itama ta zube gurin tana dafa kowannensu da girgizawa tana ambatar sunansu tafara tari sosai bata ganin komai sbd hayaqi da wani irin azababben zafi,

kofar da ake bugowa da tsananin karfi da tashin hankali ya fara sauka kunnenta ta dan daga idanuwanta ta kalli gurin duk da bata ganin komai ta motsa tanason isa gurin kofar duk da akwai wuta sosai amma ta kasa motsa koda hannunta tana kokarin somewan itama.

Jijjige kofar akai wadda saida akasha wuyar gaske maza sun jigata tukuna ta fadi wani zafin wuta ya bugo wajen a lokacin ne Imran ya sake zuwa da gudu ya jiqo jikinsa kafin ya iso tini Fleet yayi wani irin kakkarfan yunkurin daya fixge gabaki daya ya tafi da wani irin gudun gaske yafada ciki take imran ya zari zanin hajiyar Samad data jefar qasa ya jiqosa da wani tsalle ya fada ciki ya laftawa Fleet a jiki wanda harya isa inda suke baya gani wadda hannunsa ya fara sauka akai ya sunkuto gabaki daya yayo waje da ita sauran soldiers din nata zubowa kofar ruwa dan kashe musu hanyar da zasu fito.

Imran ma sunkuto wata yayi sauran securities dinsu biyu ma tini suka fado ciki kowa ya dauko suka fito ana zubo musu ruwa masu yawan gaske.

Dr Mum ce a hannun Imran wadda idanuwan Dad da sukai wani mummuman ja na sauka akanta aka sakasa ya kwace da karfi ya mata wata irin fizgowa daga jikin Imran din ta dawo jikinsa yana ambatar sunanta da da tsantsar tashin hankali koina na jikinsa jijjiga yakeyi ta bude idanuwanta ahankali dakyar ta kallesa jikinta na sakewa gabaki daya tana somewa.

Wata irin runguma yayi mata da daukanta gabaki daya ya juya yana barin gurin yana mantawa da komai da kansa ma,

Kafin yace komai tini Mr Sideeq ya juya da gudun gaske ya dauko key duk a rikice ya fita ya juyo da mota da saurin gaske tini suka fice villah din da mugun speed.

Fleet ma SANAAH ce a hannunsa da yana fitowa daman bai tsayaba dan ko gani bayayi sunanta yake kira da wani irin sauri yana jijjigata a jikinsa imran ma a haukace ya fito

Please Login or Register in order to submit comment