Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

batareda iya cewa komaiba sbd maganarta na daidai da iya kasa riqe kanta.

Maamah ta roka tai mata iso har gaban Dad wanda yayi mamakin ganin Maamah din da Meenah suka basa hakuri akan Meenah din ta tuba tana neman gafara.

Zuciyarsa Sam bata amsa da kowace maganar meenah dinba amma sbd yarta saiya amsa gafarar tata amma duk da hakan sam bazata taba cigaba da zama a Nigeria ba gidansa dole zata koma Morocco ko America wannan shine hukuncinsa da bazai taba janyewaba dan kuwa ta taba rayuwar macen da bai taba rayuwarta data komai da kowa ba dan kuwa harya bar duniya bazai manta yanayin da idanuwansa suka gani na halinda Dr fammah ta shiga ba akan idanuwansa data kusan konewa har lahira hakama wannan daren shine tsoron da rayuwarsa bata taba shigaba tinda yake a rayuwarsa dan haka abune da har mutuwansa bazai iya mantawa ba.

Hakanan dai jiki a mace Maamah ta sake bata kwarin gwiwan taci gaba da addua da danne zuciyarta zataji komai yazo da sauki insha Allah.

Haka Maamah ta ringa kokarin janta a jikinta tana sake tausarta da nuna mata kulawa da kauna dan bata sassaucin abinda ta lura haryanxu tanaji a zuciyarta na kishi wanda ya saka meenah din itama jin tana samun karfin hali da juriyar iya dannewan tana hana kowa iya gane abinda yake kirjinta da fuskanta.

Ita kanta dr mum sbd yanda maamah ta dage da bata hakuri ya saka ta dan sassauto kadan duk da tariga tasani duk yanda meenah zata hakura matiqar SANAAH da Fleet suka dawo tana ganinsu bazata iya danne abinda takeji ba shiyasa suke tafiyarsu idan har bazasu iya ba dan shine maslaha da mafita tareda zaman lafiyan kowa amma meenah batada niya ko hakurin iya jure hakan.

A cikin kwanaki kadan Meenah ta dawo mutum dinta tsaf ta koma kaman ba ita ba dan kuwa yanzu ta tattara komai ta danna a cikin ranta ta boye ta iya controlling kanta musamman ganin yanda a yanxu duka ta gama saka kowa yadda da tubanta da yafe mata duk da Dr Mum bata gama koma mata kaman baya ba hakama shi Dad sam babu ko daman zuwa gaidasa datake samu,

Hajiyar Samad ta maida hankali sosai akan ganin Samad ya tattara ya koma dan haka ta tattara meenah ta watsar tana jiran ta fara ganin wucewansa tukuna ta waiwayeta ta gyara mata zama,
Itama meenah yanzu ta ajiye Hajiyar cak sbd bata buqatanta lokaci ma ta bata na bari gidan ita da danta.

Maganar maida auren Dad da Dr Mum yafara fita ahankali sbd irin yanda wata irin lafiyayyar soyayya mai sanyi da nutsuwa da manyanci ke gudana a tsakaninsu sbd babu ranar da likita bata zuwa ta duba masa lafiyarta hakama a waya ma yanda yake waya da ita akai akai ya saka ita kanta tafara jin lamarin ya mata nauyi dan haka ta hanasa ganinta kwata kwata dan irin kalla dayake mata duk wanda yake gurin zai iya jin nauyin hakan sbd baya iya riqe kansa daga mata kallan dayake mata tin a lokutan shekarun baya da rashin samun rayuwar kansu da basuyiba tinda sukai aure sbd tinda sukai aure basu zauna sosai ba akazo aka haihu lalura ta biyo baya daga karshe auren ya qare suka diba wannan shekarun ba tareba kwata kwata basu morewa tsantsar soyayyar da sukewa juna ba tinda sukai aure dan hakanne sai yanzu da manyanci yazo kila zasu morewa soyayyarsu ta hanyar zama da juna babu rabuwa saita mutuwa yanxu kam.

Tinda ta hana haduwansu sam kwata kwata yaji zuciyarsa batada sukuni da nutsuwa a ciki duk da a waje kame yake amma a ciki baida kowace nutsuwa dan haka a dan wannan lokacin ne ya shirya tafiya Morocco tafiyar da Umma naji duniyarta ta tsaya cak kirjinta ya kasa dauka haka ta kwanta ciwon hawan jininta daya fara hawa ahankali ahankali sbd damuwa mai tsananin gaske data kasa cirewa kanta.

Dr Mum kuwa dole itama tafara shirin komawa Moroccon tareda su maamah hadda Mommy banda meenah datace zata jira su dawo.

Kafin tafiyarsu aka kammala gyaran bangaren nasu daya kone zuwa sabon gini gabaki daya wanda yake sama da qasa kuma shine kadai ya fita daban da sauran bangarorin kaf,

Duniyar luxuries aka zuba a bangaren wanda ya sake banbanta bangaren da sauran na matan gidan dan kuwa komai nasa na daban ne dan nan ne bangaren Dr mum a matsayin matar gidan macen da Hakeem jeerah ya zuba shekaru yana jiran dawowanta rayuwansa da gidansa.

Fleet ne ya zuba duk wata duniyar dake bangaren yai abinda kowane da ko uba zaiyiwa 'ya ko uwarsa.

Su Dr Mum dinne suka fara tafiya shima sbd jiran visa din mommy ne suka dan dauki kwanaki kafin su tafi.

Suna isowa Morocco da kwanaki biyar cif Hakeem jeerah da tsohonsa da baya zuwa koina sbd manyanci sosai da tsufa wato Baba Hussain da Mr Sideeq.

Suna sauka qasar rayuwan kuruciyarsa yaji ta dawo masa na lokacinda yana neman aurenta da lokacin aurensu wanda yakejin komai yana dawo masa yana jin daga karshe burinsa daya daya kasa cika yanzu zai cika wanda ya debo shekaru yana rokon allah kada ya dauki ransa batareda ya sake mallakar Dr fammah w rayuwarsa ba..

Fleet da shine da Abbu zasu bada auren a cikin tsakar daren suka iso Moroccon shi da tasa matar da kusan kaddararsa shima itace sbd shi a nasa babin bazai taba iya rayuwa babu ita a cikinta ba dan kuwa bama zai iya rabuwa da itaba komai rintsi,
Babu kowace zafin kai da zafin fushin dazai iya sakasa rabuwa da ita dan ita itace tamkar bugawan da zuciyarsa keyi a cikin kirjinsa.

Isowansu da tsakar dare kowa ya riga ya kwanta koina tsit gashi baama san da isowansu acikin daren an dauka saida safe zasu iso dan haka kai tsaye motocinsu na isowa gidan bangarensa suka nufo yana riqe da hannunta tana jin bacci sosai da gajiya dan haka suna shiga bangaren nasa da koina yake fes an gyara wata kamshi me sanyi ne yake tashi koina.

Ac ya kunna nako ina ita kuwa wanka takeso amma batada kuzari sosai sbd baccin datake ji sosai dan haka dole shine ya tayata wankan wanda kusan shine yai mata ma suka fito kayan bacci kadai ta saka tai sallah tana gamawa anan ta kwanta bacci yana dauketa.

Shine daya gama komai ya dauketa ya maidaga akan gadon yana kallan yanda take bacci a jikin nasa kaman baby tana sauke masa wani nunfashi mai dumi na bacci a wuyansa da kanta ke ciki ya lumshe idanuwansa yana dan sake rungumeta ahankali yana rufe nasa idanuwan da fatar wannan karan iyayensa sun hadu kenan sai mutuwa sbd a yanzu dayake jin abinda Dad dinsa ke ji akan Dr mum ya roki Allah ya dauka ransa kafin ya zabi rabuwa da SANAAH KHALIL da kansa.
#MAMUH
09033181070
[23/06, 2:33 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

137
Washe gari babu wanda yasan sun iso a cikin gida sbd babu wanda ya fito yaga motocinsa da aka fitar akaje daukosu airport.

Bacci tayi sosai hankalinta kwance a cikin jikinsa sai asuba ya tada ita cikin wata kulawa da rashin hayaniya harta tashi sikai sallah suna gamawa ta dago ta kallesa bayan ta gama azkar da adduointa.

Kallanta yayi a natse sbd ya gane abinda take buqata sbd ta datayi sallah take shan fruits ko warm milk acan kullum da asuba sai ankawo mata su harsun saba daga masu kawowan har imran mai fita da asuban ya karba ya shigo ya kawo dashi mai bata din da ita mai ci din.

Bude baki tayi cikin yanayi na narkewan data saba masa tace

"Ina kwana"

Amsawa yayi ahankali yana kallan bakinta da yayi maganar a narke kafin ya miqa mata hannu ta kama ahankali tana shigewa jikinsa da wani dan dumin jiki tana bude baki tace

"Zan tafi gurinsu Dr Mum"

Wani dan kallo ya mata yana girgiza kai a natse yana bude baki da sautinsa mai nutsuwa yace

"Ki fara sake hutawa daga gajiyan tafiya tukuna suma basu tashi ba idan kinje yanxu bazaki iya karasa baccinkiba ok??

Dagowa tayi ta kallesa da idanuwanta da sune sabon obsession dinsa dan tana kallansa dasu yake samun kansa a rashin iya dauke nasa daga kanta.

Imran ne ya kira wayarsa da yanxu sbd ita yake kunnawa da asuba.

Tini a duhun asubar imran yaje ya siyo ya kawo dan haka fita yayi ya amso yana kawowa ta tashi daga zaunen datake tana zare doguwar hijabin sallanta daga ita sai wata qaranar wandon baccin da ko cinyarta bai sauka sosai ba sai wata half vest data lafe akan kirjinta koin skin dinta daukan ido yakeyi sbd glowing datake dan bata fita koina bata komai daga hutu sai love hakama shi kansa duk tsawon tafiyar duk inda zai fita da ita basa fita sai dare sbd da safe zuwa rana yana busy.

Wata lafiyayyar shaquwa da fitinanniyar son juna suke gudanarwa hankali kwance da basu taba jin zasu iya rayuwa a yanzu babu junansu ba dan haka koda suka baro can qasar tayi wani irin sabo dashi da yanzu kam zaiyi wuya ta iya dadewa bata gansa ba ko iya danne sonsa.

Zaunawa yayi tareda bata hannu ta kama ta zauna akan kafafunsa yana bude dan babban kwalin da aka jero komai aciki.

Hannunsa daya dauko mata madara mai dan zafi a cup ta kama tana kaiwa bakinta tafara sha ahankali tana dan lumshe idanuwanta yana binta da kallo da fararen idanuwansa masu kyau da kwarjini harta shanye tas ta sake masa hannu da cup din a ciki tana miqa hannunta da kanta ta dauko apple mai girma takai bakinta tana dawowa da idanuwanta akansa ta kallesa idanuwansa akanta basu dauke ba da wani cool love yake kallanta ta sake murmushi mai kyau tana kai hannunta daya akan fuskansa ta shafa tana cewa

"Thank you"

Lumshe idanuwansa yayi yana sauke ajiyan zuciya data jita har ranta ta dan sake kwantawa jikinsa tana cin apple din hankali kwance harta cinye baice komaiba tana gamawa ta dauko wani tana kaiwa bakinsa ya kama hannunta ahankali yana girgiza mata kai da slow kafin yakai hannun nata bakinsa yayi kissing ahankali yana cewa

"Kin koshi??

Gyada kai tayi tana kai bakinta gefen fuskansa ta dora lips dinta ta sakar masa kiss mai sanyi tana sake cewa

"Thank you"

Tana dauke lips dinta daga gefen fuskansa lumshe idanuwansa yayi yana juyowa da fuskansa ya hade da tata ahankali yana dora lips dinsa akan nata yai mata wata kiss me sanyi kafin ya sauke ajiyan zuciya itama ta sauke ahankali tana masa murmushi me kyau dayake sakasa koyaushe kasa cireta daga idanuwansa da tinaninsa ya sake maida bakinsa akan nata din yana bude bakinsa da wata sanyi yana sakawa cikin nata da fara kissing nata da sanyi mai nutsuwa da.

Zagayeta yayi da hannunsa daya yana saka hannunsa daya a cikin wuyanta yana manne fuskansu da kyau da nutsuwa suna shaqar numfashin juna mai sanyi da nutsuwa da bude bakinta yana samun daman qara shigewa ciki yana tsotsanta da wata lafiyayyar sanyi da cool love.

Juyota yayi akansa dakyau suna facin juna kafafunta na zagayesa daga zaunen suka ci gaba da kissing juna yana lumshe idanuwansa.

Anan inda suke suka zuba wani lafiyayyan love daya ratsesu kowace gaba da ruwan jikinsu ta amsa da gamsu da hakan kafin suka shige gadonsa da lafiyayyan duvet dinsa bacci mai nutsuwa ya kuma daukansu.

Basu farka ba saida karfe tara ta wuce dan haka wanka sukai ta shirya cikin wata doguwan riga blue mai kyau sosai da qaramin mayafinta data nado akanta suka fito kai tsaye palon Abbu suka fara zuwa ta gaidasa suka gaisa sosai yana nuna mata kulawa da kauna sosai kafin ta fito ta baro su ta wuce cikin gidan tana saka kai a palon dukansu suna palon suka zuba mata ido da tsananin mamakin ganinta ba tsammani da farin ciki sosai.

Ita kanta wani irin farin cikin ganinsu duka tayi tareda kunyar irin kallan da suke mata ta qaraso tana murmushi mai kyau daya saka Dr mum bude baki tana cewa "Masha Allah" da wani irin kyau da sauyawan dataga SANAAH din tayi.

Hannu Dr Mum ta miqa mata ta miqa nata ta kama tana zaunawa kusa da ita cikeda kulawa da kauna da kewansu datai ta bude baki tana gaida Dr Mum din da larabcinsu daya saka Dr mum din sake murmushi tana amsawa da kauna sosai.

Maida kallanta tayi akan Maamah datake kallanta itama da kulawa sosai da farin cikin ganinta tace

"Ina kwana Maamah"

"Lafiya kalau SANAAH,amma saukan asuba kukai ko sbd har dare bamuji duriyar isowanku ba"

Murmushi tayi tana cewa

"Da tsakar dare ne Maamah"

Mommy ce ta fito daga daki tana isowa ganin SANAAH din ya sakata mamaki da bude baki da farin cikin ganinta tace

"Wannan sammako naku haka"

Cikin wani sanyi da farin cikin saka mahaifiyarta a idanuwanta SANAAH ta kalli mommy din tana kasa riqe kanta ta miqe ahankali ta isa gareta ta rungumeta tana sauke ajiyan zuciya dukkanin nutsuwa da farin cikinta na cikewa da samun kowane farin ciki a rayuwarta.

Zaunawa sukai mai aiki na fitowa kitchen da ganin SANAAH ta saki faraa tana mata sannu da isowa tareda ajiyewa Dr Mum abinda ta kawo mata.

Da sakewa da farin ciki dukansu suka fara tambayarta hanya da firar hidimar data kawo su Morocco din gabaki dayansu.

Abincin breakfast mai kyau da lafiya da wasu hade haden da zasu qara gyara lafiyarta Maamah taje da kanta ta hado mata a tray tana kawo mata ta gyara zama da farin cikin ganin abinci sbd yunwa take ji ta saka hannu ta dauko spoon tafara ci kenan kamshinsa ya ratso palon tareda sallamarsa mai nutsuwa da muryansa data ratsa kunnuwan kowanensu da wata kamewa yana sako kai palon sanye da wani lafiyayyan tausassen yadin cashmere daya nutsu a jikinsa sbd tsadansa da kyan daya masa.

Kallo daya Mommy tayi masa ta dan dauke kanta cikin nauyinsa da girmamawan dake tsakaninsu.

Shi kansa bai iya kallanta sosaiba suka fara gaisawa da nutsuwansa da batada hayaniya ko kadan kafin ya gaisa da Dr Mum tukuna ya maida kallansa akan Maamah wadda take kallansa cikeda kauna da kulawa itama tana sauke ajiyan zuciya tana masa sannu da zuwa qasar.

Murmushi ya mata kyau da itace kai tsaye tafi samun hakan daga garesa sai matansa dan haka amsawa yayi yana dan magana da ita yana zaune a kujeran datake facin wadda SANAAH ke zaune tana cin abinci.

Jin idanuwanta tayi masu kaifi da tasiri akanta sun sauka akanta dan haka ta dago idanuwanta cikin wata sanyi ta kallesa shima ita din ya kalla da wani sanyayyan kallan daya sakata dauke nata idanuwan tana cigaba da cin abincin da jin sonsa na sake ratsata.

Dauke idanuwansa yayi shima daga kanta yana cigaba da magana da Maamah kafin Dr Mum itama ta shiga zancen nasu Mommy kuwa barin gurin tayi kafin SANAAH ma ta miqe tabi ta dakinta suka basu guri dan suyi magana da kyau.

Anan yayi breakfast kafin ya fice bai dawo gidan ba sai yamma wanda a wannan daren ahalin Jeerahs din suka taho gidan Abbu a karo na farko bayan shekaru masu yawa neman aure a karo na biyu.

Fleet Raheem jeerah da Abbu ne suka sake bawa jeerahs auren Dr fammah a karo na biyu wanda su Dad din suka nema kuma a daren suka biya sakakinta wanda Raheem ya amsa da hannunsa.

Neman auren ya tafi a al'adar Moroccon dan kuwa hadda zinari suka gabatar wanda duka anyi wannan al'adar a daren an gama batareda kowace hayaniya ba bakuma tareda sani ko gayyatar kowa dan shedawa ba bayan iya su din.

Koda gari ya waye da wata nutsuwan da bai taba samun kansa ba Dad jeerah ya tashi gashi har lokacin tin a Nigeria rabon daya sake sakata a idanuwansa dan haka a cikin yunwar ganinta idanuwansa da ruhinsa suke.

Ita kanta SANAAH bata koma gurin mijinta ba anan ta kwana cikin gida dan haka ko washe gari ko kayanta bataje dauka ba zamanta tayi anan sedai aka neman mata wasu kayan tana sakawa bai kuma ganinta ba.

Hidimarsu kawai sukeyi dik da babu komai da akeyi jiran jibi kawai sukeyi a daura auren wanda anayinsa zasu kwasa su koma gabaki dayansu.

A cikin kwanakin biyun haka Maamah ta ringa kulawa da komai nasu itada Mommy sbd ita kam batada ma wani moriyan dan kuwa batada kowace kuzarin aikata komai ta saba da shagwabarta da yanda yake mata basa aikin komai sai bata kulawa da tarairayanta.
#MAMUH
09033181070
[23/06, 4:24 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

138
Washe garin ranar da zaa daura auren da wata irin nutsuwa da farin ciki mara hayaniya ko kadan dukkaninsu suka tashi duk da basa jin abinda daga Dad din har Dr Mum sukeji amma farin ciki ne mai dukkanin nutsuwa sukeji da jin kaman yau zaa sauke wani nauyi a cikin kirjin kowannensu.

Karfe 11 da kusan arbain su Dad jeerah suka iso masalaccin gidan wanda daidai lokacin shima Fleet Raheem da Abbu suka iso ciki tareda dukkanin mutanen da zasu halarci daurin auren wanda zaayi bame hayaniya komaiba.

Karfe 12 daidai aka daura auren wanda ana gamawa Abbu ya sauke ajiyan zuciya yana yiwa Allah godiyansa da Allah ya kuma nuna masa wannan ranar daya yanke rahama da gani.

Shi kansa Raheem shiru yayi kafin ya dago ya kalli mahaifinsa wanda idanuwansa suka sauya zuwa jan da jarumtarsa da kaifinsa suka boye abinda yake ji a kirjinsa da zuciyarsa na saukan wani nauyi mai nauyin gaske daga kirjinsa daya sakasa sauke ajiyan zuciya guda uku a jere cikin nutsuwa da kwanciyan hankali tareda kamewa.

Daga can aka watse batareda kowace doguwan taro ba dan haka koina ya koma daidai musamman da akai sallar azahar tini ma su Dad din suka koma masaukinsu.

Shi kansa Raheem Dad din yabi tareda su Alhaji tsohonsu har sai dare ya dawo gida baima shiga cikin gida ba ya shige sedai yayi waya da SANAAH wadda take fama da zazzabi kadan kadan kuma yayi ta bari ya ganta taqi bari kuma nauyin zuwa gurinsa takeyi gasu Dr Mum da kowa a gidan.

Washe gari shirin tafiya suka fara yi har dare hakama washe gari dan haka saida akai kwana uku da daurin auren tukuna suka daga zuwa Nigeria.

Dad baiga Dr Mum ba har lokacin sai a airport da suka hade motocin Fleet sun iso airport dkn da iyayen nasa mata su duka da SANAAH wadda shima sai a lokacin ya sakata a idanuwansa bayan kwana biyu dan haka kallo daya yayi mata tana gefen Dr Mum ya dauke idanuwansa sbd wata fitinanniyar sonta daya taso masa da kewan shaqarta daya xama addiction dinsa.

Ita kanta SANAAH kallo daya tayi masa ta dan sauke kansa tana jin lokacin kaifin idanuwansa suka sauka akanta ya mata wani kallo ya dauke yana qarasawa gurin Dad.

Shi kansa Dad idanuwansa da suka dago suka sauka akan Dr mum wadda take sanye da wata purple doguwan riga mai kyau data fiddo asalin kabilarta da gyalanta dayake nade akanta ta dan fada ma kadan sbd zullumin yanda zatai rayuwa da hakeem din a yanzu baa matsayin matarsa ba ita daya daya hana zuciyarta da ruhinta sukuni....

Kallo daya yayi mata mai nutsuwa da kwanciyan hali dakyau kafin ya dauke kansa yana dawo dashi akan Raheem daya iso gurinsa yana gaidasa ya bude baki yana amsawa cikin tsari da girma.

Babu bata lokaci aka gama komai suka daga zuwa Nigeria.

A jirgi ma dayake can suke first class kusan iya sune dan haka a zaune sike cikin nutsuwa da walwala.

Dr Mum kusa da Dad take tareda shi batareda suna iya wata doguwan magana bama sbd wani kamshinta dayake fita daga kowace motsinta yana hana kansa da tinaninsa sukunin dabai taba samun kansa a hakanba dan haka babu wata magana mai tsaye sosai da sukeyi saidai kallanta datake jin nauyin hakan itama sbd tarin mutanen dasuke tare dasu.

Shi kuwa Fleet SANAAH bata tareda shi sam tana tsakiyar Maamah da mommy sbd baida hakurin dazai iya zama a kusa da ita batareda ya iya kamata yaji hannuwanta a cikin nasa ba ko janyota jikinsa dan haka ya kame kansa yana riqe control dinsa batareda ya iya juyawa ya kuma kallantaba sbd hakan ma zai iya tabasa duk da yana jin idanuwanta masu sanyi da kyau akansa tana sauke masa su tana kwantawa jikin Maamah tana masa wani sanyayyar kallo duk abinda yakeyi tana kallo har bacci ya dauketa mai sanyi.

********
Rayuwar Fammah da Al'amin kuwa ta kai matsayi da matakin da zuwa yanxu wuya ce mai tsananin gaske dukkaninsu suke sha wadda batada magani dan kuwa shaquwa da kusancin da suka samu bame hayaniya bane mai sanyin daya musu muguwar shigar da a yanzu suke wahala ne daga yanda Al'amin yafara janyewa daga gareta sbd hanasu shiga azabar dasuke fama da ita ayanxu.

Har cikin jininsa yake jinta da duk abinda ya shafeta batareda yasan yaushe hakan ta faru ba kawai dai yasan tafara zama illa ga rayuwarsa data rasa suninta da nutsuwanta kaman baya yanda yake,

Mutum ne shi mai principles da kiyayewa sosai tareda tsayawa akan gaskia dan haka tinda zuciyarsa ta gama kamuwa da abinda baisaniba akan Fammah jeerah wanda yakejin kaman he's obsessed with her saiya ja baya daga gareta sosai sbd kallanta kadai sakasa jin yana rasa kowace nutsuwa da kansa yakeyi bare jinta dayake dakatar da komai nasa cak..

Ita kanta yanda a yanzu tagama mutuwa da rasa kanta da tinaninsa da rayuwarta da zuciyarta tasan She is madly inlove with him amma shakka da tsoron makomar alaqar yake sakata jin hankalinta na tashi kaman yanda tagane shima yana janye kansa ne daga gareta dan tsare iyakarsa da duk fitinar da alaqar zata iya janyowa daga mahaifiyarta.

Ya zama busy sosai da sam yanzu basa haduwa sosai duk da suna guri daya a waya ne kadai yake iya magana da ita akan jin yanda take daga nan baya iya doguwan magana yake mata sallama dan haka sai abin ya tabata tafara wata rama sbd damuwa da tsananin halinda take cikin itama.

Suna ci gaba da hakan harta kai ta kwanta ciwon da ita kanta batasan menene yake damunta ba da dole ya bayyanarda kansa a gabanta ya kaita asibiti da kansa sukaga dr wanda ya basu tabbacin lafiyarta kalau kawai damuwa ce da rashin cin abinci.

Suna baro asibitin yana driving a natse idanuwansa akan titi sunyi shiru dukansu har suka iso gida yayi parking yana kasa kashe motar ya sauke wani lafiyayyan numfashi mai nutsuwa.

Kuka ta fasa ahankali tana rufe fuskanta da hannuwanta duka biyu sautin kukan na ratsa kunnuwansa da wani irin yanayin dayaji kirjinsa yayi nauyi ya dan rintse fararen idanuwansa da suka dan sauya ta bude su yana juyowa ya sauke idanuwansa akanta bayan tsawon lokacinda rabon daya sakata a idanuwansa.

Jin saukan idanuwansa akanta ya saka kukanta karuwa ahankali jikinta na sake sanyi damuwanta na qaruwa.

Kasa motsawa yayi bare iya cewa komai yanajin kukanta na ratsasa suna yaga duk wata nutsuwa da karfin zuciyarsa ya bude baki da sautin daya sakata jin nauyin kirjinta na karuwa yace

"Bana iya jin kukan nan pls Doc"

Bude kofar motar tayi tana ficewa ya bude tasa kofar ya fito yana bin bayanta sedai taku biyu yayi ya dakata cak yana riqe kansa daga binta sbd yana ci gaba da jin kukanta zai iya kasa riqe zuciya da gangar jikinsa gareta dan haka ya dafe goshinsa da hannunsa daya sbd yanda kansa ke sarawa da wani bugun gaske.

A cikin daren bai iya rintsawa ba dan haka ya tashi da ciwon kai mai tsananin gasken da bai iya fita office ba daga karshe ya yanke shawara daya da zata hana kansa bugawa da zuciyarsa dake gap da rasa lafiyanta kwata kwata shine rabuwansu a guri daya.

Akwai fahimta da kusanci sosai na maganganu a tsakaninsa da Dad jeerah da kusan shine dansa da yanzu yake maganganu dashi wainda ma bayayinsu da ko Raheem daya haifa bare Samad dan haka sukeda wata irin nutsuwa ta magana da rashin boyo a tsakaninsu dan haka ya kirasa da daddare bayan yaje asibitin shima yaga Dr ya dawo.

Cikin nutsuwa ya sanar da Dad din a lokacin da suke Morocco ya sanar dashi time yayi da Fammah ta dawo gida.

Da farko Dad shiru yayi yana juya zancen kafin ya tambayesa akwai wata damuwa ne da zaman.

Shi kansa Al'amin din shiru yayi kafin ya sauke numfashin daya kusan bayyanarda asirin zuciyarsa ya bude baki da nutsuwa yace

"Babu damuwa amma kadaicin ya fara damunta"

Shiru Dad din yayi kafin ya juya zancen wanda ya tabbatarda kiyayewan

Please Login or Register in order to submit comment