Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannu daya tana barin dayan dan bawa kanta kariyar daga duk inda zata fadi sbd jirin dayake dibanta.

Kai tsaye hanyar kitchen ta nufa bayan bayan ta isa palon,

Tana isa kitchen bata rufe kofar ba ta dakata ahankali tareda dafa kitchen island tana rufe idanuwanta tana fidda numfashi ahankali da ajiyan zuciyan abinda takeji.

Dakatawa tayi tsawon mintina saida ta dan samu sassauci tukuna ta iya daga idanuwanta da suka sake laushi sosai ta janyo electric kettle takai bakin fanfo ta kunna ruwa ya shiga ta kashe ruwan ta jona kettle din tana yin baya tareda da dakatawa ta dan huta kadan daga muguwan mutuwan jiki da kasala da rashin karfi ko kadan.

Numfashi ta dan sake saukewa tukuna ta daga kafafunta har lokacin tana jin jiri ta isa inda fridge yake takai hannu ta bude daqyar tukuna ta saka hannunta daya ta dauko yoghurt dayake ciki ta zuba a cup hannunta na dan neman gazawa ta mayar tareda kai glass din bakinta tasha da wani irin sanyi dayayi sosai.

Bata gama shanyewa ba wani irin amai ya yunkuro mata gabaki daya dan haka cup din ya subuce daga hannunta tayi sink din kitchen da sauri tafara fesa wani irin amai mai sautin yunkurin gaske sbd babu komai a cikinta sai yoghurt din daya shiga cikinta yanzu din.

Wani azababben yunkuri da kakarin amai takeyi mai sauti sosai da tana neman jin kaman zata mutu idanuwanta sun gama bayyanarda azaba take cikinta.

Tsit babu kowa a bangaren dazai jita bare bata taimakon datake tsananin buqata dan ta fita hayyacinta take.

Dawowansa kenan tin bayan daya fita sallan laasar sbd ya dan tsaya ya gaisa da mutane da har ya dan jima kafin ya dawo din.

Yana shigowa palon kafin ya doshi hanyar wucewa nasa palon sautin yunkurin aman ne mai karfin gaske ya fara shiga kunnensa daya sanyasa dakatawa cak daga inda ya dosa sbd a tinaninsa da saninsa babu kowa a bangaren dukan su suna can kuma yanda yaga Meenah din na yi sai dare ko yamma sosai dan haka a natse ya juya zuwa kitchen din cikin takun tsanaki.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

60
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Wani yunkurin ne mai karfin gaske ya sake zuwan mata ta saka kanta tana yi take dan karfinta ya qare jirin datake cikinsa yayi tsananin gaske ta rufe idanuwanta tana yin baya daidai nan ya iso ba tsammani ya tare bayan nata da kirjinsa ahankali tareda saka hannunsa daya ya tarota gabaki daya yana hana jiri yadda ta take wani yunkurin ya taho mata dan haka da kansa ya rankwafar da da ita tana aman wanda baya wani fita,

Yawa azabar tayi mata batasan ma lokacinda hannunta dayake dafe da kirjinta gurin amanba ya sake zai sauka a inda kettle din ruwan ke tafasa ba cikin nutsuwa hannunsa ya riga nata isa ya tare hannun da tafin hannunsa wanda nata tafin hannun ya saukar masa daidai da sake zuwan wani wahalallen yunkurin da batasan lokacinda ta manne tafin hannun nasuba tana qanqamesa zafin dumin dayake jikinta ya ratsa tafin hannunsa daya mannu da nata ya saka hannunsa daya a hankali yana shafa bayanta tana samu aman yana fara fitowa kansa shima a rankwafe sbd irin yanda bayansa shine ya zama kariyar daya baya ta hanata faduwa tinda hannunsu daya yana manne da juna dayan kuma yana shafa bayan dan haka fuskansa take kusa da tata sosai.

Muryansa ce ta fito daga bakinsa ta ratsi kunnenta na dama da bakinsa yake kusan saiti dasu daidai ya furta

"Sannu,Sannu ko" a wata irin tsanakin data bude idanuwanta cikin wani irin slow ahankali sbd aman ya fada mata a take tareda tashin tsigar jikinta ahankali....

Hannunsa da kansa yakai ya zuba mata ruwa nata dayan hannun ta wanke bakinta ya birkito da ita ba tsammani a hankali dan haka ta kasa dago idanuwanta da sukai tsananin laushi ta zame hannunta dayake hade da nasa tana kasa motsawa kuma jiri takeji har lokacin.

Kallo daya yayi mata ya lura da hakan dan haka ya dan juya ya kalli kitchen din dabai san ina zaiga cup ba sai ya dawo da kallansa akan fuskanta ya bude baki yace

"Ina cups??

Dagowa tayi da wata slow na rashin kuzari bata kallesaba ta dan daga kafafunta batareda kallan gabanta ba zata nufi inda cups din suka.

Bata sauke kafarta data dagaba hannunsa daya ya zagayota hannunsa na sauka akan shafaffen cikinta da babu komai na abinci a cikinsa tareda dauketa sama yana dawowa baya da ita sbd glasses din da sauran kiris ta dora kafa akansu na cup din data saki kafin fara amanta.

Jin tayi jirinta na qaruwa sbd wata irin faduwan gaba data shigeta da kuma jin hannunsa zagaye da ita dan haka ta rufe idanuwanta tana jin ya saukar da ita ahankali gefe jikin fridge tareda miqa hannu ya zaro robar ruwa bara sanyi ya bude ya miqa mata a natse da sai a lokacin ya sauke mata idanuwansa gabaki daya yana kallan fuskarta dake kamanninta ke azabtar da wani bangaren na kirjinsa.

Ahankali ta iya dago hannunta dayake cike da kasala sbd tana tsananin buqatan ruwan ta dora akan roban zata amsa hannunsu ya gadu cikin sanyin daya sakasa maida nasa idanuwan akan hannuwan nasu a tsanake kafin ya sake dagowa cikin wata slow ya sake sauke mata idanuwansa yana kallan yanda takesan ruwan suna bin maqoshinta ahankali suna wucewa ba sauti ko daya.

Idanuwansa suka saka ruwan isarta da kuma qara kasalarta dan haka ta zare ruwan ahankali daga bakinta tareda dagowa cikin wata kasalan da bata taba shigaba ta idanuwanta suka sauka akan fuskansa da idanuwansa masu wani irin sakar da kasala da kwarjini tareda haiba mai nauyi suke akanta.

Yanda idanuwanta suka dago tattare da kasalan datake cikinsu ta saukesu akansa ya sakasa kallan cikinsu ahankali take kafafunta jiri ya koma cikinsu suka sake zasu zube qasa ya sake mata wani riqo dakyau cikin sanyi sbd daman tana jikinsa har lokacin tinda ya dauketa bai zare hannuwansa daga zagayewan da yayi mata ba.

Jin tayi numfashinta yana neman yankewa sbd yanayin dasuke ciki da kuma kasa iya daukan kallansa da idanuwanta da gangar jikinta sukeyi ta motsa ahankali tana son zarewa daga jikinsa a lokacin ne ya dauke idanuwansa masu kaifi daga gareta yana kai hannunsa wuyanta ahankali ya dora bisa fatarta datake bayyane take taji tsigar jikinta ta sake tashi sbd batai tsammani ba dan haka ta qarasa zamewa daga jikin nasa gabaki daya tana qin sake kallansa ta juya baya tareda bude baki da sauti mara karfi tace

"Thank you Da.."

Kasa qarasawa tayi tana dakatawa cak shima idanuwansa ya kalleta dasu wanda taji saukansu a kanta dan haka babu wanda ya ce komai a cikinsu suka fice kusan a tare daga kitchen din.

Shine ya fara bacewa daga palon kafin itama tai kokarin xuwa daki ta nema wayarta ta kunna ta saka kiran Safiya cikin rashin kuzari.

Safiya ba bata lokaci taxo ta hada mata tea ta gyara kitchen din ta kawo mata da banana bread tasha daidai cikinta ta sake shan magani sai a lokacin ta dan samu kuzari.

Duk wani motsinta kamshinsa ne yake tashi a jikinta dan haka ta lallaba ta shiga bathroom.

Wanka tayi ta sake samun karfin jikinta sosai tana fitowa ta tadda Fammah ta dawo tana dakin itama wankan tayi jikinta ya sake samun karfi a tare sukai sallan laasar.

Suna idarwa Safiya ta kawo musu simple abinci ta jere musu a dakin.

Fammah dake jin yunwa sosai gurin abincin tazo ta zauna tana kallan SANAAH datai shiru ta zuba mata ido tana kallanta a tsanake da mutuwan jiki.

Hannu ta daga mata alaman "akwai wata damuwan ne??

Numfashi SANAAH din ta sauke tana kasa dauke idanuwanta daga kanta idanuwanta masu kyau na sake saka fammah jin kaman zata dawo mata da zazzabinta ta bude baki zatai magana SANAAH ta girgiza mata kai ahankali tana dan bude bakinta tace

"Kici zanzo nima naci"

"Kin tabbata?" Fammah tace mata da sautin kulawa.

Gyada kai tayi tana dan lumshe idanuwanta tana barinsu a rufe tsawon mintina kafin ta budesu ahankali tareda tasowa ta taho ta zauna gefen fammah din tana daukan spoon ta saka a plate din famman tafara cin abincin.

Kadan taci ta koshi sbd tariga tasha tea ta miqe ta koma kan sofa ta dan zaune tareda miqar da qafafunta akai.

Safiya ce ta shigo tana tattara gurin tana kokarin jansu da zance kaman yanda suka saba har suka dan daure suna bata amsa musamman fammah data warware.

Safiya bata fito dakinba sai da akai magrib ta fice tana dariya suma suna dan yi sbd sai data sakasu firar dole sbd akwaita da kulawa da son fira.

Safiya na ficewa Mum na dawowa bangaren dan haka sallah ta fara yi kafin ta fito taxo dakinsu ta dubasu dukansu tana kallan SANAAH wadda ta kasa dagowa ta kalleta dakyau ita kuma sai sake lallabata takeyi da kulawa da sake tambayar ko zaa kira likita ya dubata.

Girgiza kai tayi a tsanake tareda bude baki tana dagowa ta dan kalli Mum din tace

"No naji sauki Mum,kawai dai rashin karfin jiki ne shima zuwa safe insha Allah zan koma normal.

Dining safiya ta dawo ta shirya da abincin daren dazaa ci a bangaren na lafiyayyan abincin da Mommy ta dafa musu sbd Raheem kaman kullum.

Kafin lokacin ishai suka hau table dinner wanda daqyar SANAAH ta iya fitowa sbd takurawan Mum dan haka doguwan riga mai fadi da gabanta a bude ta doro akan riga da wandon dake jikinta da suka dan lafe mata sai silk scarf data dauro akai dan rife gashinta.

Itace tayi karshen shigowa bayan har sun fara kokarin fara cin abincin sbd Fleet daya qaraso ya zauna qamshinsa na gauraye gurin gabaki daya.

Tana sako kai kokarin hana kanta kowace damuwa tayi ta qaraso a natse tareda zaunawa kujeran gefen Fammah a natse

Tana kokarin dagowa Mum ta katseta da cewa

"Baby SANAAH ki daure kici abinci sosai"

Kallan Fleet tayi wanda ya miqa hannu a natse ya dauki glass din ruwa da lemon a ciki da sanyi kadan yakai bakinsa tace

"Fleet Baby SANAAH ba lafiya fa tin asuba ma, a kwance ta wuni yau"

Dagowa yayi da idanuwansa da hatta ita kanta Ms Meenah din saida zuciyarta tayi wani skipping beat ya saukesu akan SANAAH din wadda itama takai hannu a natse ta dauki glass na ruwa takai bakinta tasha kadan sbd jin spoon din farko na white couscous din data saka bakinta ya tsaya cak a maqoshinta.

Taji saukan idanuwansa akanta dan haka taqi dagowan sai saukan muryansa taji ta ratsi kunnuwanta da cewa

"Allah ya bata lafiya,zuwa gobe Dr zataxo ta dubasu su duka"

Yana fadan hakan Mum ta washe baki tana maida kallanta akan SANAAH da fammah tana cewa

"Allah ya bawa yan matana lafiya"

"Amin" SANAAH ta bude baki ta furta a hankali ita kuma fammah dad din ta kalla tace

"Thank you Dad"

Kallanta yayi da miqa hannunsa daya ya shafi gefen fuskanta yace

"Just get well soonest Mamanah"

Murmushi tayi daya fidda tsananin kamarta da mahaifin nata tana kallan dawo da kallanta akan SANAAH wadda ta dago ta kalleta Murmushinta na qaruwa take SANAAH ta dauke kallanta daga kanta tana cigaba da dan cin abincin sama sama kafin tasha ruwa tace she's full ta miqe tabar dining din.

Da daddare bata iya zuwa gurin Dad ba sedai ta kirasa a waya lokacin ma yana tareda Dad din ta gaidasa ta sanar basa batajin dadi amma da sauki sukai sallama da kulawa.

Dad na gama wayar ya dago ya kalli Fleet wadda bazaka taba sanin akan dad ko aa tinaninsa da hankalinsa yake sbd yanda yake karanta sako a wayarsa a natse da kamewa da wata irin girma da kwarjini.

Numfashi Dad din ya sauke a karo na uku bayan wainda yayi kafin kiran SANAAH ya shigo masa na zancen da RAHEEM yaxo masa dashi.

Bude baki yayi a tsanake sbd dagaske kenan Dr fammah zata iya zuwa Nigeria bayan shekarun baqin ciki da girmama tsanar dataiwa qasar da wainda suke cikinta.

"Babu kowane dalilin zuwanta kaman yanda na santa da dagewa da rashin hakura ga dik abinda ta kudurta bayan akan maganar aurenka da SANAAH ne,
Zata taho ne bazata tafi ba saita tabbatarda babu auren,
Bazata taba hutawaba da zubar da makaman yaqinta ba sai ta raba auren dani mahaifinka na daura maka sbd a koyaushe duk baqin cikin da zata sakamun shine yake sassauta nata baqin cikin na shekaru shiyasa ban taba damuwaba ko jin dacin yanda ta nema maka auren farin sbd na bata daman yin duk abinda zai sassauta baqin cikinta,

A yanxu kuwa tana damara ne da yaqin da batasan kanta zata yaqa da kanta ba sbd matar da zata dauro damarar yaqin fixgewa daga rayuwar 'danta dayake raye itace matar 'danta da baya raye.

Dagowa FLEET ADMIRAL RAHEEM JEERAH yayi da wani irin nutsuwa da slow ya sauke idanuwansa da suka saka Dad din da kansa daukewa ganinsu ya saukewa Dad din batareda yace komaiba.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

61
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Numfashin manya Dad jeerah ya sake saukewa kafin ya yanke nasa hukuncin dayake tareda umarni yace

"Bazaa nema mata masauki a koina ba matiqar a qasar nan kuma nan garin zata sauka,
A cikin matana ne akwai wadda babu aure a tsakanina da ita amma sbd mutuncina da nata mutuncin dana zuriata ban bari tabar JEERAHsV ba tana ciki a zaune karkashin kulawata da ikona,
Hakanne itama a gareta matiqar ina raye da kuma iko bazata taba iya zama ba a inda ba cikin JEERAHsV ba sbd anan ne mutuncinta yake da girmanta da kuma ikonta yake,

Koda babu aure a tsakaninmu ta sani mu ahalin juna ne da duk abinda yake tsakaninmu bazamu taba goge hakan ba dan haka duk gyaran da zaayi mata kasa ayi mata anan cikin JEERAHsV
Akwai bangaren dayake tsakiyar na Zainab da Hajiya khadija a sauya mata tsarinsa zuwa tsarin da zai mata dadin zama a gyara mata ta zauna zan zauna na jira abinda duk ya kawota taxo dashi"

Fleet da baisan mexai iya cewaba sbd hayaniyar iyayensa zata sake tashi kenan duk da sun manyanta amma haka lamarin nasu yake motsawa dan haka baya wani shiga sbd rayuwarsa daban take da tasu,

A tasa rayuwar babu hayaniya da tashin hankali sai miskilanci da tafiyar da komai a tsarinsa na baturen ruwa da bai hada komai da peace dinsa ba,
Sabanin su dasuka kasa hakura da juna indai akan duk abinda zai taso ne kowa zai iya kokarinsa gurin nunawa dan uwansa ikonsa akan dansu da sam basu wani damu da farin cikinsa ba ko amincinsa shiyasa a bangaren ahalinsa a gurin 'yarsa kawai yake samun cikakkiyar sukuni da kaunar da batada kowace irin sirki ko manufa dan ko matarsa tanada manufofinta akan soyayyar datake masa dan kuwa matsayin datake dashi na matar Fleet admiral RAHEEM JEERAH of the Us navy bata hada matsayin da komaiba tana tsananin alfahari da bugun gaba da hakan tareda dagawa da jin bazata taba iya rasa matsayinba ko yadda wata ta amsa irin sunan da sunan RAHEEM JEERAH.

Baro gurin Dad din yayi yana zuwa bedroom dinsa wanka yayi ya fito daure da towel a qugunsa da tabawa daya zaa masa ya warware ya fadi sbd yanda yake daurasa shiyasa kusan matarsa ta riga ta gama mutuwa da shaawansa data zamar mata jarabawa sbd akwai abubuwan dake tattare dashi da matiqar ta gansu bata iya riqe shaawanta akansa dan hakanne ne kusan yawan muaamalansu neman datake masa yafi wanda yake mata dan ko cikin kwayar idanuwansa ya sauke mata take tsigar jikinta take tashi taji tana tsananin buqatan jinta a jikinsa musamman idan ya fito wanka kallo daya takewa murdadden jikinsa da koina kusan jijiyoyin karfi ne a bayyane nan ma bata iya hana kanta tsananin kwadaituwa da mijinta.

Shiryawa yayi cikin kayan bacci dogon wando kawai da wani mayen qamshinsa dayake tashi a jikinsa ya kwanta.

Yana kwantawa Ms Meenah ta shigo dakin sanye da kayan bacci itama masu tsayi har qasa da ciki data sama silk blue kala.

Isowa tayi ta zauna dayan gefen gadon sbd ta riga daman ta gamo komai na shirim baccinta ta haye gadon gabaki daya tana qarasa rage hasken dakin ta matsa cikin jikinsa ta shige masa ahankali.

Washe gari SANAAH da lafiyarta ta tashi dan haka tana yin wanka kafin kowa ya tashi tabar bangaren tayi gurin mommy.

Tana zuwa dakin Mommyn ta shige ta kwanta tana gaida mommyn dake zaune tana waya da Al'amin.

Tana gama wayar da kulawa ta kalleta tana mata ya jiki idanuwanta akanta.

"Naji sauki" ta furta tana janyo mata wani zancen suka fara kafin suka koma maganar yaya Al'amin dayake ta samun cigaba acan ahankali ahankali arziki da damammakin cigaban rayuwa suna samuwa.

Anan ta wuni harma dasu Mum din dukansu anata fira da abubuwansu hankali kwance.

Acan bangaren Fleet kuwa Imran ya sanarwa Dr Mum zata taho a cikin JEERAHsV zata zauna kuma.

Imran dayake shima Dr Mum din ta kirasa ta sanar masa yayi musu shirin tahowa Nigeria din dan haka take ya shiga aikin duka biyu na nema musu komai na tahowa da kuma na aikin bangaren da zaayi wanda kusan zubar dashi akai zaa mata sabon ginin da zaiyi daidai da duk abinda takeso.

Sauran mutanen villah din sunga anata sabon aiki a bangaren wanda yakeda girma shima kuma aikin imran ne a tsaye a akai da qwararrin maaikan daya dauko amma babu wanda yasan aikin na menene dan haka Mum ta fara murnan ko ita akewa bangaren dan tanason ace tanada nata bangaren wanda take ciki sedai ta ringa zuwa bangaren mijinta kwana sbd tana matsayin matar Fleet RAHEEM JEERAH guda da zai iya siye Villa din da yan canjin da ba komai bane a gurinsa ba amma ace batada bangarenta mai zaman kansa dan haka koma ba ita akewa ba to ana gamawa itama zata buqaci gaskia a ware mata nata bangaren su baro na Raheem ya zama tirakarsa ce shi kadai.

Hajiyar Samad dataga ana bangaren abinda yazo ranta shine SANAAH zata tare kenan maganar auren bayyana zatai dan haka ta ringa jin wani irin dadi da farin cikin jiran ganin tashin hankalin da zaayi sbd babu abinda take jira yanzu kaman Ms Meenah ta gane auren ta tsani SANAAH da uwarta wanda ita hakan ne zai bata daman shiri da Meenah din sbd tana neman wanda zasu hada kai su hana SANAAH da uwarta da sukai sanadin mutuwan auren zaman lafiya da kwanciyan hankali.

SANAAH da mommy kuwa tashin hankali da tsoro suka shiga mai girma na ganin aikin da akeyi din wanda zai iya yiyuwa tarewanta zaai magana dan haka suka shiga tinani mai zurfa da yar shakka.

Rage zama sosai bangaren SANAAH tayi sbd zuciyarta da a yanxu batada sukuni sam a bangaren zaman dole takeyi musamman indai zaa hau dining ta ringa jin rashin nutsuwa kenan duk da babu wanda ya taba gane abinda take ciki dan kuwa ko a dining a tsanake take komai.

Tana gaidasa batareda ta iya kallansaba ko bawa situation din mahimmanci ba sbd yanda Mum ke kokarin cusa sabo a tsakaninsu da kaunar dake ganin ya kamata t shiga tsakaninsu sbd ita da SANAAH dinma takeson su tafi idan har zasu koma duk da batajin shaawan komawa koina a yanzu itama zata zauna Nigeria tukuna gaskia.

A duk lokacinda SANAAH ta bude bakinta ta fidda sautin muryanta ta gaidasa a dining sai ya dago idanuwansa a natse ya kalleta dasu taji kaifin su a jikinta tukuna yake amsawa a taqaicen da muryansa ke qara mata kaifi bayan wanda idanuwansa suka sakar mata dan hakane bata iya sake cewa komai a table harta gama tabar gurin sbd tana bude baki a gurin zata iya rasa kalamanta.

******aikin bangaren da akeyi qanda dukiya ce Fleet din ya bada dama ake zubawa kaman baasan zafintaba,

Cikin kwanaki kalilan aka gama komai aka zuba furnitures din da kudi sukai kukan gaske gurin siya aka tsara komai irin tsarin da Dr Mum zatai rayuwan jin dadi da walwala da kwanciyan hankali tareda nutsuwa itada Maamah.

Masu aiki aka tanada guda biyu aka zuba a bangaren kafin ma su iso dan haka tafiyar itama ta kammala komai ya zama ready batareda ya sanarwa Mum din inda zata zaunaba hakama imran bai sanar mata kawai dai an sanar mata komai is ready.

A ranar da jirginsu zai taso tai waya da Ms Meenah amma bata sanar da ita tana zuwa ba dan haka har lokacin kaf bayan Fleet da yaransa sai Dad babu wanda yasan wacece a tafe.

Dad jeerah sabbin gyare gyare da sauya abubuwa da dama na villah din ya saka a sake duk babu abinda ya lalece dan koyaushe cikin kashewa villah din kudi ake dan hakane take kaman ka shiga turai akoda yaushe.

Ana gama komai aka zuba komai Hajiyar Samad farin cikinta ya tsananta ta kashe kunne tana jiran dirar masifa da balain da zai tarwatsa jeerahs.

Mum ma kawai fara shirin tarewa sabon bangare tayi batareda jiran a ce mata komaiba.

SANAAH ma da Mommy ranar da aka gama komai fara jiran abinda zai biyo baya sukai cikin fargaba amma babu wanda yaga alaman kowace damuwa ko nuna ma sunsan da aikin a gurinsu.

Ranar Friday da tsakar dare gap da asuba jirgin da Dr

Please Login or Register in order to submit comment