Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wallahi inji Aisha.
Hajiyan dadi tace da yake gulma ne ba don baku san ciwon ian ku ba wa aka fi aiki balle aiwa mutane rufa ido da sunan aiki ?
Duk falon yai shiru sai Aisha ce tace haba dai hajiya wanan magana ai bai dace ba tace da ita to uwata fada min abindaya dace naji.
Yar uwarta dake aikin banki may yasa bata saya ba sai ita ce za, a ce wai ta sai wanan motar ni dai nai shiru sai Aishan ne tace hajiya ina zaki hada samun Rahama dana Raliya da aikin su na rikici ai ba a ko hadasu ma.
Rahama fa yanzu babban likitace a kasan nan wace ke aiki a maikatar lafiya na kasa baki daya aike surukar ki don dai ba mai rigima bace da kin sani.
Tace may kike nufi tace wallahi hajiya ba a taba hada su ai sai tai shiru sukan suka mike zuwa ganin motar tare da Nasir da ya san komai na motar kamar yunwar cikin shi.
Sai gasu sun dawo suna yaba kyawon motar kai Rahama kin debe takaici wallahi nace ai ban so sayan ta ba ma wata kawar aikina acan ta matsa min na saya.
Kin san mu ma aikata duk movement din mu na kan idon mutane sai ace duk samun ka ina yake shiga ka kasa shiga tsaran ka.
Eh hakane amma ian mutum yana samun tallafi ba wanda baida wanda ya rike mai kan maciji ina yaga wurin wasa da bindin shi.
Kai hajiya ku dai Raliya ta saye ku da amshi ungo din ta yanzu baku ganin kowa in ba ita ba nikan wallahi duk wani barkadon ta bata gaba na don nasan inda gaskiya yake.
Nace hajiya ko baba na nan mu gaidashi mu wuce tace ku shiga yana daga ciki muka aje mata kayan tsaraban da muka zo mata dashi muka mike zuwa gaida Alhajin a falon shi.
Naji dadi kamar kullun ya karbe mu da mutunci sai faman saka muna albarka yake shima muka aje mai nashi tsaraban da abin sallah mukai mai sallama.
Mun koma mun sallami hajiya da su Aisha muka bargidan sai bayan fitar mune suka bude tsaraban nan hajiya jikin ta yai sanyi abinda muka kawo mata din.
Aisha tace hajiya ya kamata ki daina yiwa yarinyar nan haka may ye laifin ta duba kiga yadda yaran nan suka koma fa ko shi ai ya isa ai ta samu sallama a wurin ku.
Yanzu ki duba fa yakai kusan dubu dari biyu wurin nan abinda ta kawo maki fa tace a ina fa ?
Aish tace gasu a gaban ki kuwa sai suka shiga yi mata lissafi tace nikan da ma kudin ta kawo min da yafi ai.
Hajiya wai may zakiyi da kudine haka tace a tambaye ki nema a kan su wa yake karewa ba a wurin ku ba.
Kagin mu dawo gida mun dan yi biye biye a hanya har gidan mahaifiyar Zulfa muka tafi a can muka samay ta a gidan nasu batama san da fitowan mu ba.
Ta tare mu a cikin mutunci tana faman godiya akan irin zaman da mukeyi da yarta sai fadin takeyi adai ta hakkuri zama sai da hakkuri mun biya duk gidajen yan uwan daddy muka juyo zuwa gida don yamma yayi a lokacin.
A harabar gidan naga wasu motoci guda uku nasan cewa munyi baki ne sai da muka karasa shigowa ne naga mata zaune saman fararen roban dake waje da aka aje don shan iska a wurin.
Raliyace tare da kawayen ta wasu irin tantiran mata ne da ganin su ba sai an fada ma ba ko su waye su din don yanayin shigarsu kawai ya nuna.
Gaba dayan su sukayo kaina da kallo har muka fito daga motan tare da duk yaran mun sha kwslliya ba sai na tsaya tsarawa ba don mun tsara da kyau Alhamdullahi.
Magana suke a kan mu sai dai saboda nisa baza mu iya jin su ba a lokacin yaran ba wanda ya bi ta kan su ina gaba suka biyo ni dirr a bayana.
Dayan tace tarkasa ke kice min yarinyar ta bunkasa ne haka hajiya jummai kin ko ga shigar ta daga ita har yaran kuwa ?
Wacce aka kira da hajiya jummai din tace nagani wallahi kayan da muka kasa sayowa matar musa don ne a Dubai fa.
Dayar tace wai tsaya itake da yaran nan masu kama da Larabawa ke nan fa ake nufi ?
Raliya tace a sanyaye itace mana yan so ke nan a gidan nan ba wasu diya bayan su a gidan nan yanzu ai duk inda zai tafi dasu yake zuwa su biyar kamar kan shi aka fara haihuwar diya maza haka farare.
Ke ai dole yaran akwai kyaune wallahi Allah kice dai yarinya ta wuce inda muke tsanmanin ta sai Raliya tace da kike ganin ta a nan shegiya sai bakin wayo kamar ba yar kauye ba.
Yarinyar nan da kuke gani a nukurkushe take mulkin gidan nan in anyi magana ace ai duk babu mai hakkurin ta ta mallake komai da kuke ganinta a wurin nan.
Duk ta inda na biyo mata kafin nakai shegiya ta sani wallahi takai min ko ina don sauran su bakin kishi ya rufe masu ido ba wayau ne dasu ba.
Amma ita yadda kika san diyan wani da wata ko wata tsohuwar yar boko haka take da bakin wayo duk ta rusa min plan dina a gidan nan da kan shi.
In ba ita ba babu mace komai zakigan ta dashi kamar mai aljannu dake fada mata.
Ai ba sai kin fadi ba duba fa ko kallo bamu ishe ta ba a wurin nan balle tasan Allah yayi ruwan mu ta gaida mu.
Dayar tace aiko zama bai ganki ba wallahi Raliya shiga zakiyi ki fita sai kin kifar da ita gaba daya a gidan nan ki nuna mata ira ba kowa bace a zauna lafiya.
Nan dai sukai ta bata shawara ga abinda zatayi sunyi zancen motana da shigana da yarana yafi a kirga zuwan Zarah da hajiyan harka ya kara tsunka su don su ma basu tsaya ta kan su ha suka shige ciki a binsu.
Nan suma aka shiga nasu gonan akai tayi saida sukayi ya ishesu sukai mata sallama suka tafi tare da bata shawaran banza.
Mun dade da su Zarah a ciki muna hira nan hajiyan harka take fada min ko suwaye wa yan nan matan da suke tare da Raliya.
Hiran nasu babu dadi nake mamaki ina ta hado dasu haka sai Zarah ke cewa wai ke halan baki san labarin Raliya yar kadagaruwa bane Rahama ?
Nace nikan ina zan sani tunda ba mutane nake shiga ba kai tsaye tace aiko ya kamata ace kina da labarin su dai kan wa yan nan tantirai ne fa na karshe.
Ni nai mamaki da mijin ku ya aure ta kamar wanda idon shi ya rufe duk matan kwarai dake cikin garin nan amma ya rasa wacce zai aura sai wa yan nan da gari ya gama da su.
Munyi hira sosai da su kamar kada mu rabu amma dare yayi dole mukai sallama dasu suka tafi.
Washe gari da safe na shiga gun daddy na fada mai zan shiga gun iyayyena nagaida su sai dai ba kwana zan yi ba idan na tafi.
A falin yake zaune tare da Raliya sai da na sama yana waya ne nai mamakin ganin ta a falin don dai nasan ba itace da girki ba ranan.
Abinda ban matsa wa kaina ke nan muddin ban da girki ban faye shiga wurin shi har na zauna ba idan dai ba shine ya nemay ni ba da wani magana a nan din.
Sallama yayi bayan na dan tsaya daga bayan kujera na jingina jikina akai ina jiran ya gama wayan.
Sai yace Ragama kun tashi yanzu nake batun aikawa kizo ai don magana aka zo min dashi a kan ki nace to fa ni din nan dai ke nan gashi kuma Allah ya kawo ni yanzu din da ake nema na.
Yace yanzu wanan ta samay ni da maganan da banji dadin shi ba sai dai da yake nasan ba halin ki bane hakan ban damu ba sai naji naki hujjan nayin hakan da kikayi .
Tace jiya kin dawo da yara tana tare da baki daga ke har yaran kukai masu kallon banza da tsuki kuka wuce ciki ba tare da ko kun gaisa da bakin ba.
Ikon Allah nace kafin yaci gaba da maganan shi yace sai kuma tace kin hana Nasir dama duk wasu yara a gidan nan hurda da diyan ta kin ware mata yara a gefe baki bari su shiga gunta.
Nace bakin ki uwayena ne ko mai da ban gaidasu ba yai maki zafi ai ban san ranki ya baci ha da sai na aikata fiye da abinda kika ce na aikata din.
Nace kin gan ni nan ban maka sheri ko shiga harkan ka amma idan kace kai idona yana kan ka to muka zuba da mai shi sai ankai karshe.
Tace naga alama ai don yadda kika kashe Saade har kike kuri da hakan to ki sani wata tafi karfi ki don maye baicin maye sai dai ayi walkabu a mike tare.
Nace wata sabuwa kin tabbatar da cewa nina kashe Saade tace waye ma bai sani ba tai maki halarci kin saka mata da sheri.
Ba damuwa nace da ita don yana zaune baiyi magana ba na juya wurin shi nace dama na shigo ne na fada ma yau zan leka su Inna sai dai ba kwana zanyi ba yau din zamu dawo insha Allahu.
Shiru yayi wurin baiyi magana ba na juya na fara tafiya zan fita yace Rahama nace naam idan kun shirya kizo sai naji tace za a aje ai bakar asirin da aka saba yi a can ke nan ko.
Murmushi nayi sai bayan fitana yace kin gama abinda ya kawo ki ko , tace may nagama ai gaskiya na fada ba karya ba.
Yace amma kin san tun kan Rahama tazo gidan nan Saade ke fama dz kan ta ke nan itace ta sako mata kafin ta zo din na kyale kine don nasan halin Rahama ba wai shirun banza tai maki ba ko da kikaga ta kyale ki yanzu.
Tace tayi abinda zatayi din mana an fadi batayi bane komay waye hai sani ba duk garin nan yace ok kawai ya kayale ta ta fice tana fada cikin son fitina
Yadda daddy ya kyale bai yi magana ba ya kara tunzura zuciya na har naje na dawo raina a bace yake ranan tun da safe kuma na shirya da yara already dama na fadawa Sani zancen tafiyan mu tunda safe nake son tafiya.
Duk wanda ya tashi ya sama babu gidan mun bar garin daga ni har yaran daddy ya kira waya na daidai ma mun kusa shiga Abuja yake tambaya na kuna ina ne wai naga part din ku a rufe.
Nace gamu zamu shiga Abuja insha Allahu ko ka manta na fada ma yau ina da wacce zanwa aiki da karfe goma sha daya.
Sai yai shiru nima na kashe wayan yara kawai muka sauke nace da Sani mu fita muna barin gidan nace sani kaini kotu mugani ko sun dawo yace sun ma dawo ai yau aka koma aiki ko ina.
Ina zuwa nai karan Raliya tare dz kunna oudio din da tai magana da duk ta fada min take aka buga mata sanmaci na bayar da kudin zuwa kano kai mata sanmacin alkali yace da goma na safe ake bukatan ta kotu gobe.
Dan sakon da yakai sako ya samu wani sabin tashin hankali a gidan don Awal dan ta yayi shaye shaye yazo yace sai ya bankawa gidan daddy wuta baki daya.
Sai kuma ga dan sako ya sallama yace daga Abuja yake kotun magistre ake neman mai suna Raliya nan kuma aka koma kan shi.
Idan hankalin daddy yakai dubu ranan ya tashi sosai yace Rahama tai kara ko may ?
Tunda zan shiga theater na kashe waya na ban kunna ba sai dare sosai na kunna wayan ban dade da kunnawa ba kiran Zulfa ya shigo min a wayan.
Tace Rahama may ke faruwa ne kika wuce ban sani ba sai kuma ga sanmacin an turowa Raliya tace yau aike dai bari maganan ki ya tabbata don matar nan taga jaiba a gidan nan.
Nan take fada min abinda ya faru da dan ta sai kuma ga sanmaci an turo mata ana neman ta kotu yanzu dai suna nan tafe tace yau har Alhajin babba saida yazo gidan nan.
Don daddy yace ita data fada taje ta kare kan ta bai zuwa ko ina ta ishe shi a rayuwa don ba wani kwanciyan hankalin da ya samu kan ta.
Nace ya samu kan Anty a gaban shi fa ta fada min magana yana zaune bai ce komai ba kin sanni da record din magana don mantuwa va su san na danna ba ne.
Tace aiko tashiga uku nace zata dai shiga barta dani take wasa wallahi ko daddy yazo ba zan jaye karan nan ba Anty.
Ta shiga zugani ni dai ina jin ta ban ce komai ba har tayi tagama abinda zata fada mukai sallama nace kai kishiya a raina.
Zakace a Abuja suka kwana don uban samakon da suka bugo sai dai duk samakon su basu samay ni a gida ba lokacin gashi anzo da mutane.
Har asibiti suka samay ni sai akace dasu ina cikin theater room ina aiki sai zuwa sha daya zan fito yadda ma tagani asibitin yasa ta fahinci ko wacece ni a wurin .
Ganin zasu bata lokaci suka wuce zuwa amsa kiran mai sharia don kada suyi laifi kuma again kan rashin zuwa da wuri.
Aiko suna zuwa Alkali yace a saya ta bayan kanta sai gobe zai yi sharian mu nan hankali ya tashi bayan an saya tane sai ga sun dawo wurina asibitin daidai na fito ina cikin office dina ina wanke hannu.
Suka shigo office din nai masu sannu da zuwa tare da nuna masu wirin zama da zasu zauna Bashir yace kai kaunata kin samu cikin wani hali wallahi.
Nace an dai sani nida akaiwa batanci a gaban ku baku dauku mataki ba yace ba wanan ba yanzu dai gamu munzo wanan yaya ne ga Raliya wanan kuma dan uwanta ne sai maigidan naku.
Don haka munzo ne don Allah Rahama kiyi hakkuri ki janye karan nan don yanzu haka tana can a rufe banji dadi ba a raina amma a fili nace dashi don Allah ku bari na daukawa kaina yanci don wanan kazafin idan ba anyi iyaka dashi ba ban san ina zai tsaya ba haka.
Mun dai ji don Allah ku bari a sasanta a gida a fahinci juna tsakani ba sai an kai ga hukuma ba zancen kishi ne ai bai kai haka ba.
Nace hakane fa zancen kishine da kazafin kashin kai yanzu sai a bari alkali yai huluncin shi ai muji in wanan magana ya shafi kishi.
Dama alkalin muna tare da yar shi Fatima kawa na don haka na samu daurin gidi Fatima ta zuga shi aiwa Raliya ladabi ta shiga hankalin ta.
Aikuwa da kyat suka ci saata na fito muka tafi kotun mun samu ance alkali yai tafiya zuwa Nasarawa state duba wasu case a can sai ya dawo.
Don haka dole sukai hakkuri muka dawo gida sai alkali ya dawo da yamma zamu koma ira dai tana can a tsare.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , ,

95
Daddy bai min magana ba nima haka nasan dai zaiyi zai gama ai tunda agaban shi mukai komai yai zaune kamar ba namiji ba.
Nasan haka rayuwan shi yake abune mai wuya idan ana sa,in sa a gaban shi yai magana iya maganan shi shine ya isheni haka fa ko zan bata maku rai shine maganan shi shi.
Alkali bai dawo ba sai dare don haka zata kwana a ciki hankalin su yai matukar tashi sosai dole ya aje girman kan shi ina daki sai gashi ta shigo dakin sallah na idar a lokacin.
Ban ko iya gaida shi ba sai yace dani ke Rahama ki sa a sako Raliya haka na don ba zan yarda ta kwana can ba ko yanzu dai ai ta horu don haka ki sa a sake ta da daren na ba sai ta kwana ba.
Banyi magana ba har ya fita daga dakin na daga waya na kira Fatima nake fada mata yadda mukayi da shi tace ba matsala bari ta kira tace idan sunzo a basu bellin ta.
An kira an bada belin ta din baban na fatima ke fadin Fatima na dai gane har da kishi ga alamarin naku.
Tace baba so muke ai muna maganin ta tasan mu ba sa, an yin ta bane da zata dinga shiga gonan mu bamu damu da su ba sun saka mu s gaba.
Anje anbada belin ta cikin dare ta dawo gidan kamar bata ciki shiru kake ji ba wani motsi a wurin ta.
Da safe na shirya zan fita sai gashi saye da kayan barcin ajikin shi yake cewa ina son yau kuje ku jaye karan nan.
Da sauri na dago ina kallon fuskan shi da mamaki nai karfin halin cewa a gaban ka fa tai min mumunan kazafi kana ji baka dauki mataki ba yanzu kuma zan daukawa kaina kace na jaye ?
Indan na jaye ya zama gaskiya ke nan maganan ta ya tabbata gaskiya ke nan ya zama dole na kwatarwa kaina yanci wanan karon .
Ina fadin haka na juya na bashi baya naci gaba da abinda nakeyi yace ke nan ban isa nace maki ga abinda zakiyi kiyi din.
Sai nai shiru bance dashi komai ba ya juya ya fice daga dakin sun tafi kotu alkali ke fada masu nace a janye karan amma su sai sun daukawa mai hakki hakkin ta.
Don kazafin kashe mutum ba karamin kazafi bane sai ga Raliya na kuka tana roko alkali yace ko taba da taran dubu dari biyar ko taje gidan wakafi na wata uku.
Daddy yace dama ya fada masu kwandalan shi ba zaiyi ciwon kaiba ga zancen ko zuwan da yayi akan tursasawan mahaifan shi ne yazo.
Nan fa kudi ya gagara a gunta sai waya take bugawa a turo mata babu kudin, karshe dai shidi ya biya kudin ta dawo gida tsurutsuru da ita.
Sauran sun iso daga kano nan aka hada mu falo ranan dukkan mu munga bacin ranshi yai rantsuwa tafi a kirga akan duk wacce ta sake jawo fitina ita kadai zata tafi.
An dai sulhunta a zauna lafiya sai kuma zancen yaron ta da ya fara kawo wani harkan banza a gidan yace sai ta mayar dashi gidan uban shi.
Nan ma taita magiya tana roko ba kunya tace don Allah Rahama kusa baki mana ku bashi hakkuri.
Sai kowa yai shiru zulfa tace gaskiya bazamu bada hakkuri ba ya fara haka ranan da maigidan bai gari fa ya dauko muna magana yaya ake so muyi.
Hindatu tace garin kwashe kwashe an dauko muna fitina a cikin gida muna zaune zaman zaman mu.
A, a ku dakata a gaskiya tarbiyan shi idan ta mayar dashi inda bata kusa akwai matsala gara dai yana kusa da ita dai.
Tace ka taya ni tsawata mashi a tarbiyan shi amma idan aka mayar dashi abin kuma lalacewa zaiyi azo kuma ana da an sani.
Ya juya gunta yace kin gani ba kin gani yanzu kin dai ji abinda ta fadi kuma gaskiya ta fada idan ya koma can din sai yafi haka lalacewa.
Amma kin rufe ido kina mata yankar kauna ido rufe don wasu banzan kawayen ki da basu da amfani a gunki.
Nan kika shiga matsala aka rasa wacce zata ara maki ko kwandala a cikin su karshe sai ni kika sa nai hasaran kudina gun belin ki.
Yace kuma sai kinyi hakkuri don shi tarbiyan yaro ba wai kai kadai da ka haife shine nauyin haka ke kan ka ba kowane da ake tare hakan ya shafa.
Hindatu tace niko nasan haka don hakan yai min dadi don nagani kan ihisan yanzu dan mannewa yaran nan da takeyi ina hanata sai gashi naga faidar abin a rayuwana.
Wanan zuwan kano da mukayi Nunu taje kauyen su itace na samu take muna komai har muka dawo nan.
Yace yanzu ke bakiji kunyar fadin wanan maganan ba da bakin ki kike fadin Rahama na bautar da yaran nan ne kawai ba rikon arziki take masu ba.
Kai ko dear akwaika da tashin tashin wallahi sai abu ya wuce ka dinga tuna shi ana zaune kalau kuma yace Allah yasa a zauna kalau din dayafi maku alheri a rayuwan ku.
Nan dai akai ta mayar da maganan abinda ya dace ina zaune ina sauraren su dama nasan bawai zai kori yaton bane a gidan shi barazanane kawai na maza a gaban matan su.
Dakina na koma na samu wuri na kwanta don han son damuwa hutu nake nema kawai a wanan lokacin.
Ban sake fitowa ba sai da safe da yake morning duty nakeyi kafin kowa ya fito nabar gidan ko a lokacin.
A wurin aiki Fatima take kara labarta min yadda aka kwashe a kotu tace ashe ita duk barazanar banza ne ko mai ma bata dashi dan kudin da zata belli kanta ma ya bowaye ta.
Murmushi nayi nace ni fatima kin san ba don ke da kika bani karfin gwiwa ba da taci bulus tace da gaba wanda zatai maki sai yafi wanan da tayi din.

********* ********* *********
Nasha zagi da gori wurin hajiyan su daddy kan karan Raliya da nayi kotu tace abin nawa yayi yawa sai gashi ta bugo min waya tai min tasa ni dai sai hakkuri nake bata kawai.
Har tayi ta gama ban daice da ita uffan ba har cewa take na fake ga kula da yara ina cutar su yadda na cuci uwar su na aure mata miji.
To komai tsiya na dai ba zan taba zama ni kadai ba yadda nake so a gidan daddy dole in bude ido inga wasu tunda ba don ni kadai akayi shi ba.
Nace na sani hajiya kiyi hakkuri don Allah ba za a sake ba insha Allahu tace don dai ma shi ya zama mai naci ne ni inba jaraba ba irin na maza na rasa may yaron nan kewa wanan rawan kai haka a kanki kamar kin fi sauran matan nashi ne.
Ta kashe wayan nabi wayan da kallo tare da sake murmushi una sauke ajiyan zuciya na mayar da kaina saman filo tare da lumshe idanuwa nace Allah gani gare ka.
Kowa dai Rahama dai Rahama dai may nayiwa mutanen ne haka basu sona basu kauna har uwar miji a kishin mu.
Wani hira akayi dani kan matsalolin mata dake yawa yanzu inda nice akaiwa interview din kan abinda ke haifar masu da wanan matsalan a yanzu.


Please Login or Register in order to submit comment