Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko ga zaman ku in akwai rayuwa bazaki kwadayin kema kiga kin saka wa yarinyar nan ba kada fa ki matan da irin halarcin da kukaiwa junan ku abin gwanin ban sha, awa daku.
Jikin ta yai sanyi da kalamin mahaifinta sai dai gaskiya hudubar Falmata ya riga yayi tasiri a zuciyar ta sai dai zata rage wani abu don bin umurni kawai.
Da Abba ya fito sunyi mai rakiya hindatu nagani tasan da akwai magana don Abba baya zuwa gidan haka a banza kai tsaye.
Can ta samu Zulfa da zancen duk da ba dadine a tsakanin su ba take cewa da ita mutanen ki fa ina ganin zumunta ya watse a tsakanin su don akwai magana koma may ye ai ji zamuyi muna zaune don sai na gano komai ke faruwa din inji Zulfa take fafin hakan.
Ranan dana karbi girki har lokaxin bana jin dadin jikina daurewa kawai nakeyi gashi da dare jikina yai wani irin mugun gashewa da zafi amma daddy bai sani ba.
Hakana nake daurewa har na gama girki na gashi ba wani daddy tsakanina da anty sai dai dan saukin anin ina gaishe ta ta karba min harda tambayana ya school tanayi.
Sai dai ba wani dogon hura a tsakanin mu kamar da can baya bani dau gajiya da zuwa gurin ta gaida ita duk da na fahinci bata son hakan.
Matsala kuma yar aikin ta kazama ne ko girki bata iyaba gashi part din duk ya lalacemata kullun sai sunyi fada da daddy ya kasa cin abincin abin ya fara damunta sosai sai rikice ya fara samuwa a tsakanin su take cewa wai ya dai gaji da ita ne kawai yake kirkiro mata matsala a tsakanin su.
Ranan suyi rikici sosai har ya daga hannu ya mareta fada sukayi ba dadi a tsakanin su sosai harta jefo zancena a cikin maganan fada sukayi take fadin wallahi sai taga bayana a gidan nan.
Ranan kan makiya sun dara don tabar abin fada a garesu hankalina yai matukar dagawa sosai nake cewa da ita nikan anty zanbar gidan don dama kece sillar shiga na a ciki.
Nan na barsu nafice falon da aka taru masu ban tsaya ba su gajiye da fatima na bani hakkuri na dauki handbag dina na fice daga gidan ban masan inda zan nufa ba sai can dabara ya fado min na wuce zuwa gidan Amina course mate dina na kuma roketa kada tafadawa ko Zarah ina gurin ta zaune.



ZAINAB iDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON ONLINE NOVEL NE WANAN BA A YAFE BA, , ,

61
Gajiye ce tsaye a waje cikin tashin hankali tana jiran dawowan maigidan daga masalaci wurin sallah magriba daya fita.
Tana ganin shigowan shi ta tare da sauri tafara gaida shi a cikin tashin hankali take fadin Alhaji dama uwar dakin mu ce tun safe kuna wanan rikicin da hajiya ta fita bata dawo ba har yanzu.
Ya juyo da sauri yana cewa da ita wa kenan Rahama ko wa tace dashe ita Alhaji yace ina ta tafi har wanan lokacin tace wallahi ban sani ba don bata kai war haka a waje.
Yace da ita yaji ya shige ciki kawai ya barta tsaye a gurin dama duk yinin wanan ranan rayuwan shi a bace yake sanadiyar fadan da sukayi da anty din.
Yana shiga ya furzu iska daga bakin shi yana fadin a fili ina wsnan yarinyar zata shiga kuma har wanan lokacin haka?
Wayan shi ya ciro daga aljihun gaban rigar shi ya shiga kiran layina duk iya kokarin shi bai samu layin ba gaba daya.
A Lokacin ne hankalin shi yai mugun tashi azaton shi ko ina gidan Abba ko na mahaifan shi ne sai yai dabaran kiran su da sunan gaisawa dasu amma har ya gama gaisawa da kowan su baiji an sako mai zancen Rahama ba.
Haka yasa ya dan shiga cikin damuwa sosai don shi baiga dalilin da zai sa na saka kafa nabar gidan ba don badani akai fitina ba ai suna na ne kawai ta shigo cikin zancen su.
Har dare sosai bani ba labarina a gidan dole ya hakkura ya kwanta cike da damuwa gashi anty ce da girki bata shigo gidan ba.
Ita ko uwar gaiyyan bata ma san cewa bani gidan ba har lokacin tana can ta dauki fushi da kowa a gidan don tana ganin an mata tozarci a bainan jamaa.
Tun da safe ya buga kofan part dina Gajiye ta bude kofan tambayan ta yayi da ta dawo kuwa ?
Cikin damuwa tace dashi wallahi bata dawo ba Alhaji ko gida ta tafine dai yace an ya ban tsan manin zata tafi gida don da sun bugo waya ai.
Cikin ikon Allah yana komawa part din shi sai ga maigari yakirashi suka gaisa yaji yana tambayan shi muna dai lafiya ko ?
Wanan yasa ya kara tabbatarwa da ina cikin garin dai na samu inda na boye je kawai amma ai duk inda nake zai gane.
Anty suna gaisawa da Falmata take fada mata abinda ya faru Falmata tace bana fada maki ba wanan yarinyar annobace a gare ki .
Don ta riga da ta asirce ki ta ko ina ba ki da sauran motsawa dole ne asama maki makarun abinda tai maki tun kan ki cutu da yawa.
Sunyi da ita zata shigo gidan su kara tataunawa zuwa rana don su san abinyi akai a cewar ita falmata din.
Sai dai suna gama wayan a bangaren Falma sai ta sauke wani shu,umin murmushi kawai tana magana a zuciyar ta ita kadai.
Daddy ya kira Bashir yazo nab yake labarta mai abinda ke faruwa a gidan shi har da barina gidan danayi bai san inda na nufa ba.
Nisawa Bashir yayi bayan ya gama sauraren abokin nashi yace watau su dai mata haka halin su yake basu da tabas akan halaiyan su ?
Yanzu ita Saade harta manta da irin halarcin alherin data shuka da Allah ya baku rabo tsakanin ka da Rahama aida ankai ga diya biyu a gidan nan da ita.
Nan dai suka yanke shawara akan su shiga school tunda sun san a wanan lokacin da nake ga ganiyar gama karatuna babu inda zan tafi na bar karatun nawa ai.
Sun shiga school din da tambaya suka isa department din mu inda suka rasa wa zasu tambaya sai ga wata daga cikin dalibai tafito da ganin ta yarece ita don tai kama da kabila suka gaida ita.
Nan Bashir yake tambayan ta ko tasan wata Rahama anan department din tace da hausa gaskiya da wuya da nan san abinda take karantawa ne sai lokacin daddy yai magana yace matar aure ne tana yawan shiga CRV assh color tana shekara na shidda ne yanzu.
Tace ok nagane ta wata fara kyakyawa mai kamun kai bata da yawan hayaniya sosai kawar Zarah Ko ?
Yace ita,
Tace nadai ga shigowan Zarah din dazun amma ban san ko ita tana ciki ba don ko tana nan baka ganin ta sai idan sun fito zuwa sallah.
Tace dasu tana zuwa ta juya zuwa ciki daddy yai tsuki yace wasu akwaisu da surutun tsiya wallahi wanan dogon bayanin waya tambaye ta ne wai ?
Bashir yai dariya yace ai ta taimaka muna koba komai munji wani abu gamay da Rahama din anan suna cikin magana suka hango fitowan ta da Zarah tana saye da hijjab daidai gwiwan ta.
Tana ganin daddy tai mamakin may ya kawo shi kuma gashi yau bata ga na fito ba ko ba lafiya ne dai yazo complain.
Suka gaisa sai yaji tana cewa ince ko lafiya daddy yau banga mutumiyar nawa ta fito ba nayi kiran layin ta har ba iya ka ban samay ta ba tun jiya.
Ganin wanan yarinyar ta farko taki tafiya takuma tsare su da idanuwa yasa shi cewa lafiya kalau wallahi dama mun zo ne mu ganki jin haka yasa lydia barin wajen tai masu sallama zata tafi bashir yace ta dakata ya bata dubu biyu ta wuce tana masu godiya.
Bayan tafiyan ta Bashir yace doctor Zarah dama kawar ki muka zo nema a nan don tun jiya tabar gida bamu san inda ta shiga ba kuma.
Munyi zaton kuna tare ne sai gashi kuma munji kina fadin ke ma kina nemanta ne yanzu ?
Cikin faduwan gaba Zarah tace bata gida ina ta tafi kuma ?
Daddy ne yai magana wanan karon yace ko akwai wata kawar ta da kika sani ko zata tafi can gurin ta anan garin ?
Tace wai da wuya wallahi don Rahama bata faye shiga mutane ba in dai ba wacce ban sani ba ne amma kuma an tambaya can gida kauye ko tana can.
Yace da wuya don munyi waya dasu suma suna tambayan lafiyan ta dazun da safe kin ga bata can ke nan.
Nan dai tai masu alkawarin cewa zata taimaka ta bincika duk inda ta san na sani tagani ko Allah zai sa a dace.
Sukai mata sallama suka tafi kasa zama tayi anty Amina tana ganin ta take tambayan ta ko lafiya ?
Tace anty kawatace ke cikin dan matsala yanzu mijin ta yazo nan ya wuce Allah ya sauwaka tace tabar ta bata kara magana ba.
Koda ta dawo gida ta samu na gyara mata ko ina na gidan har girki nayi mata don daga ita sai kaunar ta ne zaune kuma duk suna fita zuwa makaranta yaran ta da mijin ta basu garin suna can Enugu zaune inda mijin ta ke aiki karatu ya tsayar da ita a kano sai ta samu hutu take zuwa.
Ina zaune a falo ta shigo gida da yamma kamar yadda muke dawowa a wahale tace kai kai kai lalai yau gidan nan yasan yayi bakuwa kan.
Nagaida ita muka zauna ina tambayan ta abinda akayi tai min bayani can tace Rahama maigidan ki fa yazo neman ki a school yau shida abokin shi.
Kawar ki ma naga ta shiga damuwa don bata ma zauna ba nace Allah sarki nasan Zarah tafi da haka wallahi.
Nan mukai magana sosai da ita kan matsalan abinda ke faruwa dani take cewa ni yanzu Rahama banga abin tashi ba anan ?
Tunda dai mijinki bai maki komai ba matsala dai da kishiya ce don may zaki biyewa rudin shedan ki baro dakin ki ?
Nace anty Amina gaskiya barina gidan shine alheri gara dai na bar mata mijin ta a zauna lafiya tunda kinga matan nan tai min halarcin da ba kowa ce mace ne zata iya yiwa bawa shi ba.
In dai nice zan kawo mata matsalan farin cikin ta gara dai na barsu kowa ma ya hutu tace a naki tunanen ba ina zaki kai son mijin ki a zuciyar ki ko shi yaya kike son yayi da ran shi a rashin ki ?
Gashi kwana daya har ya fara yawon neman ki a gari haka ni idan zakibi ta nawa kiyi hakkuri ki koma dakin ki ki share kowa taita haukan ta ita kadai.
Don ko batace ba dama Allah yayi akwai aure a tsakanin ki da shi tun farko ki daina wani tunanen wai don ita tasa ya aure ki ta dawo kuma tana cuta maki haka ?
Dole fa sai kin nuna mata kema din mace ce tunda kikaga ta fara wanan halin idan ba kunyi fito na fito ba ba zaku taba zaman lafiya ba yadda kike so da ita.
Don ko yaushe magana ya tashi cewa zatayi ai a dalilin ta ki ka aure mata miji gashi mata fara zargin kun dade tare dashi tunda tana bakin ciki ya nuna yana son ki haka.
Watau ita so tayi ki ta zaman takura tana juyaki yadda ranta yaso ki zauna baki da incin kan ki ko kadan sai yadda tayi dake ke nan ?
Nace ba hakana bane Anty da farko fa zaman mu gwanin ban sha, awa ne don ko makara nayi ban tafi gurin maigidan ba zokiga yadda take bata ranta akan hakan yaran ta kuma tana matukar son yadda muke muamula dasu .
Shigowan wanan kawar nata ne a rayuwan ta ya kawo muna duk wanan matsalan da muke ciki da ita a yanzu din.
Tace kai haba Rahama in har son Allah da Annabine ai babu wacce ta isa ta shiga tsakanin ku irin yadda kuke da ita din nan.
An dai tarar da hali dama akwai wata a kasa kece dai da kike zaune da ita Allah ma,aiki kike ganin ba wani abu a zuciyar ta amma kawa ruwan ta ta tofa ciki kawai akwai hali dama can.
Mun dai tattauna sosai da ita tana kara koya min dabaran da kuma yadda zan zauna a cikin kishiyoyi na zamani .

********* ********* *********
Horn ake a kofan get maigadi ya taso ya duba yana ganin motan matar da maigidan yai mashi kashedi ne akan kada ya kara bude mata get idan tazo gidan .
Tana ganin shi gashi sai faman horn take ya bude mata amma yaki dole tafito daga motan ta cikin hasala ta nufi kofan tana fadin kai wani irin dan rainin wayo ne kana ganin kana kuma jin ana hirn bazaka bude wa mutum kofa ba ?
Yace na jiki na kuma ganki sai dai umurni ne aka bani akan bazaki kara shigowa gidan nan ba tace wani dan kazan uba ne ya haka wanan umurnin a kaina haka.
Yake cewa da ita maigidan ne yabani wanan umurnin a kan ki don haka kibar wurin nan kagin na kira maki yan sanda.
Tace har ni akewa barazanar kiran yan sanda wayan ta ta ciro takira Saade take fada mata abinda maigadin yai mata take ran Saade yai matukar baci sai gata tafito a fusace daga cikin gidan.
Ta nufi get din tana fadin malam musa rainin wayo ne yau kuma akaina ko may ko kana nufin kabi bayan Gajiye ne kaima ?
Yace hajiya ba hakana bane maigidan ne ya umurce ni da yin hakan kuma yace idan ta shigo gidan nan a bakin aikina wallahi.
Can ta fita suka ga juna da ita sun jima har maigidan ya dawo ya samay su a wurin ya shige ya barsu yasan malam musa ya fake aikin shi ke nan.
Da yamma anty ta shirya takai karan daddy da kukanta gurin mahaifinta ya daga waya ya kira daddy din yazo ya samay su anan.
Bai dauki lokaci ba ya iso aka kirata tafito nan takawo maganan da tazo dashi ra kara maimaitawa a gaban Abba da daddy din.
Daddy yace tabas shiyaba malam musa maigadin shi wanan umurni don Falmata ba matar arziki bace.
Yace tun baya sun taba samun wanan rikicin akan ta tun kafin suyi aure da kyat ya samu ya rabasu.
Sai gashi kuma yanzu ta sake dawowa cikin rayuwan su da manufanta akan su inda ta dawo da tsigar tarwatsa mai farin cikin gidan shi ga bakii daya.
Yace Abba na rasa ko Saade wata irin yarinya ce ita da bata da fahinta ko kadan wanan falmatan sam bata kaunar ta da alheri amma ta kasa fahintar hakan ita.
Gashi ta cusa mata mugun halin banza a rayuwan ta har takai ga zubar da mutuncin ta ga abikiyar zaman ta da suke zaman lafiya a tsakanin su.
Yanzu hakka Abba Rahama bata gidana yau kusan kwana biyar ke nan na tafi duk inda nake zaton zata tafi ban samay ta ba can.
Nasan kuma tayi hakane don ta nisanta kanta da mu don irin maganganun da taji Saade ta furta a kanta ranan.
Abba yace subbahanallahi yanzu ina yarinyar mutane ta shiga ba a sani ba shine kai kuma bakazo ka fada min ba a bincika ko zaa ganta.
Ya juya gurin Anty yana cewa kin gani kinga iri abinda kika jawo wa yarinyar mutane da kika dauko amana yanzu may gari ya waya akan wanan hadin ?
Kina ganin wanan yarinyar zata kara ganin ki da daraja a idanunta ko may tun da kin zubar da kimar ki a gareta ko ?
Ta dago kai cikin nadama tana cewa ni wallahii Abba ban ma san bata gidan ba tsawon wanan lokacin haka ?
Yace ina zaki sani kin dauki mugun abu kin sa a ranki wai ke kishi baki ji kunyar fadar cewa baki san yarinyar nan bata gidan nan ba tsawon lokaci haka ?
Har kina nufin kin manta da irin dawainiyar da yarinyar nan tayi na jinyar ki ko may ke yanzu kina ganin ita wanan da kika dauki amanan kan ki kika mikawa zata iya maki abinda wanan yarinyar tai maki a rayuwa ni nasan akwai abinda mijin ki ya sani yake boyewa akan wanan kawar taki amma ke hauka ya hanaki ganewa tai maki hudubar shedan kin hau kai kin zauna.
To ki sani mudfin kikace bazaki bi umurnin mijin ki ki zauna lafiya da kowa ba zamu raba gari dake baki fatan mu rabu lafiya dake ke nan .
Hawaye ne ya zubo mata take cewa don Allah Abba kayi hakkuri insha Allahu zan gyara ba zan kara wanan rayuwan ba Abba .
Yace yanzu ai zabi a gareki duk inda kika san yarinyar mutane ta shiga maza ki nemota a garin nan don ba zaki maidani mutumin banza ba.
Abamu yarinya don darajana amma yanzu kizo ki tsiro wa mutane shegan taka irin haka ?
Nan dai suka dawo gida har lokacin ba wani shiri a tsakanin su kowa najin dan uwa a ran shi.
Tana fita bata tsaya ba ta shige part din ta kawai ya bita da kallon takaici shima ya shige nashi wurin.
Yana shiga wayan Zarah na shigo mai ya dauka da sauri bayan sun gaisa take tambayan shi babu wani labari dai har yanzu ko ?
Yace wallahi Zarah ba labarin komai don har garin su na tafi amma bataje can ba ina dai sa rai da tana nan cikin garin akwai inda ta boye kawai.
Sukai sallama ta kashe wayan tana kashewa kirana na shigo mata da saurin ta ta dauka tana cewa Rahama kina inane haka ?
Rahama ina kika shiga duk kin dagawa mutane hankali don Allah ina kike yanzu wai ?
Nai murmushi nace haba Zarah baki ko tsayawa ki tambaye ni zaki shiga tambayana haka ina nan inda nake mana.
Munyi magana da ita nake fada mata tazo gidan anty Amina ta samay ni don Allah kada ta fadawa kowa ko ita akwai maganan da nake son muyi ne shiyasa nakirata.
Bata bata lokaci ba sai gata gidan dariya muka shiga yi mata tace amma anty Amina baki kyauta min ba yanzu ashe Rahama na gurin ki baki fada minn ba ?
Tace alkawari na dauka akai don haka babu yadda zan fada maki hakan kin ga na karya alkawari ko ?
Harara ta watsa min tace to yanzu ke may kike anan da kika bar dakin ki ?
Nace abinda kikaga inayi mana tace wallahi kin dai ji kunya Allah kuwa Rahama yanzu akan kishiya zaki bar dakin ki da mijin ki ?
Kin bar mutumi bawan Allah duk ya haukacewa mutane an rasa gane kan shi duk ya tsayar da aiyukan shi akan ki.
Nace yadai so ne amma ai bani kadai bace mace gare shi ke gara na bar mashi matan shi ko za a zauna lafiya yafi min.
Kin dai san daddy ba zai taba sakin ki ba batawa kan ki lokaci kawai kikeyi anan in zaki koma dakin ki ki koma tafi maki.
Anty Amina tace abinda nake dafada mata ke nan kullun wallahi tunda tazo gidan nan kishiyar may can kowa tashi ta fisheshi mana ba shike nan ba amma ita taki yarda.
Munyi magana dasu sosai amma basu shawo kaina ba daga karshe anty ke cewa dama kiran da mukai maki test muke son yi shine tace ke zaki iya koba abin yi yanzu dau dan duba min ita please ko maganan ku zaizo daya da nata.
Da sauri ta dago kai tana kallon inda nake tace ku fada min dan Allah may ke gudana ne wai ?
Yanzu dai dubata mugani please da sauri ta mike zuwa inda nake ta jawo hannuna ta dan rike kamar mai nazari can ta dago tace two months da kwanaki Rama ?
Na runtse idona a hankali ta jawoni da murna a jikin ta tace Allah mun gode ma yan bakin ciki kunyi kunya wallahi.
Bude bakin ki mu gani na bude mata duk wani abinda ya dace sai da tai min duk da nima na san dashi.
Yan zu may ye abin yi ta tambaya tana kallon anty Amina don taji may zatace da ita din .
Kunga wanan matsalan bai san dashi ba nace ba wanda yasani kuma dawowan shi daga chaina ne nasan na samu cikin nan don ga lissafina haka din ne.
Mun dauki lokaci tai muna sallama don dare yayi a lokacin ta tafi tun a hanya ta kira daddy din wanda ke zaune tare da Zulfa a falon shi.
Bayan sun gaisa ne take fada mai cewa daddy yanzu daga wurin Rahama nake tana kuma lafiya a inganttacen wuri.
Mikewa yayi ya ma manta a gaban Zulfa yake yake cewa tana garin nan ke nan tace tana nan daddy a gidan wata kawar mu take zaune.
Sunyi magana sosai sukai sallama yake cewa da ita gobe zai shigo ya samay ta yaji komai.
Ranan yayi barci kwanciyan hankali don yasan ban bata ba ke nan sai dai har lokacin anty tana bashi mamaki sosai.
Nayi kyau na kara murjewa dani dan dan cikin dake ajikina kyauna ya kara baiyyana duk da ba komai ne nake iya ci ba sosai.
Muna zaune da Anty Amina a falon ta mukaji an dana bell din gidan hakan yasa muka san anyi baki ke nan.
Ta tashi taje ta duba na jawo hijjab dina na saka hankalina yana gun tv ina canza Chanel sai kamshin turaren daddy ya daki hancina.
Da sauri na dago kaina mukai arba da shi yana tsaye saye da coth baki ya kura min ido baya ko kiftawa.
Inda Zarah take na kalla cikin bacin rai sai ta ware min hannayen ta alaman ina ruwan ta ita.
Bissimillah zauna mana Alhaji inji anty Amina take cewa dashi hakan ya samu wuri ya zauna suka fara gaisawa dashi.
Can ya juyo inda nake yace Rama yaya akayi kika zo nan bada sani ba kika zauna shiru nayi mashi kamar badani yake magana ba.
Yace bakiji may nake fadi bane halan dake shiru kowa yayi a falon can anty Amina ta mike ta shige tare da kiran Zarah tabi bayan ta.
Tashi yayi ya dawo inda nake zaune yana batun rugumay ni nace cikin wani irin murya dont dear touch me , kaje kaji da matan ka please ?
Murmushi yayi yace kina hauka ke nan kema kin shiga shirmay sauran ke nan tunda har kika bari shedan ya shiga zuciyar ki ya samu wurin zama.
Ba wani shedan sai gaskiya kayi min abinda suke so a zauna lafiya bazanyi sillar shiga hakkin kowa ba a rayuwana in wargaza mata farin cikin ta bayan irin halarcin da

Please Login or Register in order to submit comment