Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take cewa tana son ta dora wutan miyan rana ne nace danyi hakkuri na dafawa Nasir idonmie yanzu zan baki guri.
Ta bata rai wai zamu bata mata lokacinta rana yayi bata karasa da wuri ba.
Duk da raina yabaci ban yi magana ba na hada komai da ake bukata sai na kunna gas din komawa nayi daga bakin kitchen din nai tsaye ina jiran ya dahu na juye yaron na daki a bakin gadona yana game da waya na.
Idanuwa suna Lumshe na hada hannaye a chest dina nabi bango kamar mai tunane har suka karaso inda nake ban sani ba sai jin muryan su ne yasa na sauri bude idona a dan cikin firgici don ban san da su ba a gurin.
Ramana lafiya may yafaru kuma kika dawo nan kika tsaya tunanen may kikeyi haka a tsaye hsr baki san inda kike ba anty ce ke magana sai shi dake ta bayan ta yana kallo na.
Sau daya na kalli inda yake tsaye na dukar da kai ban sake dago kai na kallesu ba gaba dayan su kara maimaita tambayan da taimin tayi.
Rama may ya faru kin dawo bakin kitchen kin tsaya nace ba komai anty dama ina jiran indomie ya dahu ne na juyewa Nasir na tsaya a nan.
Daddy ina kwana nace cikin dan rusunnawa kadan ashe kina gidan nan Rahama ?
Ya tambaya anty kuma cewa tayi yanzu don indomie din Nasir kika dawo nan kika tsaya ke kadai kai Rahama kina dai shagwaba yaran nan wallahi anya kuwa ashe sai kuma tai shiru.
Sun wuce store din kayan abincin mu suka nufa a tare suna dubawa daga can ta kwala min kira na shigo take cewa dani kin gane ne kayan nan don Allah duk a kwashe su Rama daddy zai kawo muna wasu kin san azumi ya gabato wanan din a fitar su waje sai mu kyautar dasu za, a zuba muna kayan azumi ne.
Nace to Anty bari na gama da Nasir nazo na gyara gurin da kaina yanzu kai wake Nasir dai Nasir dai yanzu ne ma masu kawo kayan zasu shigo muna dasu nace ba matsala ai ya dahu yau my boy yace baya shan tea kin san shi hukuma ne sai lalashi ko indomie din da kyat na samu zai ci wai shi masa yake son cin.
Ai fa nikan maigari ya dauko min fitina wallahi da yaron nan bai san masa ba amma tun zuwan kauye ya dawo min da zancen masa da kosai a bakin shi.
Heart beat ni zan tafi indan sunzo sai ki fito ayi yadda ya dace kowa akai mata nata part din ta na basu lanban ki zasu kiraki idan sun iso.
Rama wai ko kin gaida daddy da dawowa nai saurin daga kai na dan saci kallon shi ya wani daure fuska dama haka yake indai ba yana tare da yaran shi bane baka taba ganin annurin fuskan shi.
Cikin daurewa yake cewa ni ban ma san rabona da ganin kaunan taki ba yanzu kin san yar University ce ba a ganin ta kai tsaye yadan yi min barkwanci don wani lokaci yakan min wasan kaunan mata idan yaso.
Nai murshi kawai nace anty ni ban ma san daddy ya dawo ba wallahi sai yanzu dana gan shi .
Amma baki da kirki daddy yau kwanan ahi biyar fa da dawowa kasan nan mutum ya share kusan wata uku bai kasan.
Daga inda nake labe a bayan ta nace sannu daddy da dawowa sai abin yabata dariya tace ina ruwan mai dole.
Yace nina fita ba tare da ya amsa min ba tace ai kinga shima yayi fushi tunda yaga sai da na roka kika tare shi .
Nasir ne yafito daga daki yana kwala min kira Anty Anty nace daga bayan ta my boy bari na kawo ma.
Gurin daddy shi da yagani ya nufa rike da waya na a hannun shi yana cewa daddy kaga irin game din da nake so ka saya min anty tace idan naci na daya kona biyu a class din mu zata saya min shi.
Rike shi da yaron yayi adole sai yaga game din yasa shi karban wayan a hannun yaron.
Komay yagani sai naga ya juyo yana kallon inda muke tsaye da anty daga can yake cewa Sa, ade amma kinji kunya yanzu wayan yar university ke nan waya duk ta kode haka ?
Tun da nazo gidan ban taba jin ya kira anty da sunan ta ba sai yau kuma akan waya na yakirata da hakan.
Tace kasan halin mutumiyar wayan ma ai kusan na Nasir ne ita ba abokai ne da ita ba ko sauri sai aukin yin game ko yaushe.
Dan dube dube yake a wayan wanda muke zato games din wayan yake kallo Nasir nata zuba mai surutu ya dan rage tsawon shi daidai yaron suna magana.
Mutuminnda yace yana sauri zai fitane ya buge kuma ga hira da yaro kai daddy akwai son yaran shi wallahi.
Na shiga kitchen na juye mashi indomie din suna gurin har anty sai dariya suke gwanin sha, awa naba yaron indomie karshe dai ni ban san inda suka nufa ba ashe suna falo tare sukaci indomie din da yaron.
Sai gaf da zan gama gyara store din ne yaron yazo inda nake yake cewa anty da daddy mukaci fa yacinye min abincina yace wai anty ta iya dafa nudulles sosoi.
Ina aiki ina mamakin yadda daddy yaci wanan jagwalgwalen har yanawa yaro santi.
Nagama har nai wanka na saka dogon riga baka da gyalen shi na daure kaina yaran ma nayi masu wanka muka dawo falo muna kallon program din yara a tv.
Nace Amira dauko min jinior taje sai anty ta koro ta wai bata iya daukan shi anty ta biyo bayan ta tana cewa haka kawai zaki turo min wanan mai rawan kan tsiya daukan min yaro nace haba Anty tun yaushe su Amira ke daukan shi tun fa yana jariri.
Bako a gaban idanuna ba don bazan yarda ba yaron nagani na ya shiga washe min naki yana miko hannu na dauke shi wai.
Nace zauna can tunda an hana ma anty na daukan ka nima yau ba zan dauke ba zauna gurin mummy.
Rama don Allah ki karbe shi kada ya balla ni ina fadin naki ina mai wasa shi duk ya tattaro karfin shi gare ni ya matsu na dauke shi din.
Wayan ta dake hannunta ya kara ta miko min yaron na katbe shi muna wasa naji tana fadin gani nan zuwa tafice daga falon.
Shiru shiru bata dawo ba har kusan minti talatin can naji hayaniya ya kaure a waje da sauri gajiye ta shigo falon tana cewa dani Rahama fada fa ake kuma da yar uwarki ake fadan nace subbahanallahi .
Da sauri muka fita gaba dayan mu daga falon zuwa waje matan gidan da yan aikin su duk suna gurin a tsaye ga kayan abincin su shimkafa taliya tomatoes maggi mai taliya indomie an kasa kashi ukku sai dai kashi daya yafi sauran yawa sosai.
Ashe akan shine ake fadan sunce don may kadon anty zaifi yawa watafi da za, a bata kaso mai yawa haka ?
Ina jin ba,asin maganan nasu kawai na mikawa Amira jinior nacewa Gajiye duka mu kwashe kayan kawai.
Sai gani sukayi na fara daukan kayan aiko sai ga Zulfa tayo cikina tana kokarin bangaje ni da zafin nama na juyo saiko ta kwada min mari kayauuuu.
Zafin marin danaji nikuma na kwashe mata kafa sai gata a kuca tafadi aiko tana tasowa ta shakeni nace maman hanifa sake ni taki sai bugu take kai min bugu daya nai mata Allah yaban saan fuskan ta tasaka wani irin ihu mai karfi.
Hindatu ta daga waya tana kiran maigidan yazo ga fitinan da ya haddasa a gidan shi takai har na doki Zulfa .
Tare suke da Bashir a lokacin yace duka fa tace kazo kaga shahidi mana danbe sosai mukayi da ita na nuna mata karfin yan kauye sai da taji jiki duk ta yakushe min jiki da cizo niko na dake sosai Allah ya ban saan ta ranan.
Gaban masu kawo abincin mukayi shi da ita zagi da gori na sha shi a wurin su kuma na kwashi kayan na shige dasu part din mu.
Anty hankalinta yai mugun tashi sosai a lokacin amma ai ita suka so dukan da farko don ashe dama sun kitsa su bata tsinanen kashi ayi abin da za ai masu.
Sai gashi hindatu ta jaye ta barta ina kakwasan na karshe hindatu ta rike min riga saida ya yage aiko itama na wanke ta da mari kayauu har sau biyu take idon ta yai mugun ja a gurin.
A bakin mazan da suka kawo abinci yaji ba,asin maganan ya samay su a kofa ran su a bace.
Ya shigo gidan kamar namijin zagi gaba daya yan gidan ya hada mu har yan aiki dakowa yai muna mugun zagi sosai.
Zagin matan shi yafi yawa yace dubi abinda yarinya karama tai maku dube ku don Allah hindatu tace dashi ai ba sai ka zage mu ba Man don ba yau ba na fahinci kana son yarinya nan tunda duk cikin yan aikin mu babu wanda kake kyautatawa kamar kwana ki har motar shigan ka ka bayar aka kaita har kauyen su dashi.
A hasale ya juyo gareta yace hindatu sherin naki har yakai yau ki kalli idona kice ina son kaunar Saadatu a gidan nan.
Ni ke son Rahama Saade ni zakiyiwa wanan kazafin haka don ki bata min suna ki hada ni fada da matana da mutane ?
Daga inda anty take zaune tace wallahi Besty in ma kace kana son auren Ramana na ne ni bani bata rai nafi kowa farin ciki dajin haka a rayuwana.
Kan shi ya dafe take idanuwan shi suka kada sukai ja yai shiru falon ma kowa shiru yayi a cikin sa.
Can ya dago rinanun idanuwan shi yace hindatu ba a taba min kazafin daya kona min rai ba irin wanan.
Amma ki sani ni yusuf Rano ba mazinaci bane ban mata taba tunanen yin shi ba a rayuwana don ni ba dan akuya bane.
Idan a gidan ku ake haka to ni ba ai min wanan tarbiyan ba a gidan mu zaki gane kin min kazafi mai zafi haka ku tashi ku bani guri.
Aka watse falon kowa ran shi a bace sai faman kuka nakeyi don wanan mugun kazafin da akai min damay yai kama haka ?

****** ********* ******
Kuka nakeyi sosai a dakin mu take wata zuciya tazo min mikewa nayi na fara hada kayana dake cikin mamakeken wradrove din dakin ina kuka wiwi.
Amira ce ta sheka kiran maman su Nasir kuma yana kwance saman gado ya kifa cikin shi tare da kura min idanuwan shi.
Sai ga Anty ta shigo dakin tun daga kofa take fadin may ye kuma haka Rama kin tayarwa yara da hankali Amira ce fa ta samay ni da kukan ta wai ga can kina kuka kina hada kayan ki.
Ban daina abinda nakeyi ba har sai data karaso inda nake ta dafani cikin hasalan da ban taba ganin ta ciki ba tai min magana.
Wai badake nake bane may kikeyi haka kina nufin sin samu galaba akan mu ke nan dama zaman ki gidan nan ya kai masu ko ina sun yi gulma sunyi tsegumi sai wanan kazafin ne zai bata maki rai Rama.
Sai lokacin na juyo idanuna danaci kuka sunyi ja sun kade nake cewa anty saboda Allah wanan wani irin rayuwa ne ni maman husna zatace wai daddy na so na ?
Daddy yayi may dani don kazafi kawai suna son na bar masu gidan su shine zasu yi min wanan kazafin haka su hadani fada dake ?
Dawa zasu hadaki fada Rama ni Allah dai ya sauwa wallahi akan may zan dauki zafi dake ni ko ba su suka fadi haka ba ai bani fushi balle su suka fadi .
May ye kishiya bata iya fadi a kan ka don ta bata maka rai kan shi ni wallahi in ma sunyi ne don naji haushi ni kan dadi ma naji da besty zai taimake ni ya aure ki ai nafi kowa farin cikin hakan.
Wani kallon mamaki nayi mata kamar zanyi magana sai na juya naci gaba da kwasan kaya na kawai.
Take cewa wai ba zaki ji abinda nake fada maki bane Rama ki daina wanan kwasan kayan da kike yi babu fa inda zaki.
Zanyi magana sai ga gajiye ta shigo dakin tana cewa hajiya kiji wa yan nan matan da basu da tsoron Allah.
Yanzu naje kai wanki naji suna fadin wai dama ke suka so duka amma Rahama ta kwabsa masu shiya su kuma sukai mata wanan kazafin dan kiji haushi ki koreta su samu su gasa ki yadda suke so.
Anty tace to ke kinji ni dama ai nasan sherin su ne hakana barsu nan inda kika gan su an sherin mutana ne.
Tace ai naji wallahi suna can har yan aikin su suna dariya wai ai dole yanzu Rahama ta bar gidan don koke ko mai gidan dole ku koreta.
Allah yafisu yafi sherin su babu inda zata sai ma suji haushi wallahi don yanzu ma zan sa aima Rama abinda basu taba zato ba a gidan nan tunda haka suke so.
Gata nan mara wayo wai ita barin gidan zatayi tunda sunce maigida na son ta ko yace yana son ki ba mace kike ba halan kuma sun san kifi su da komai wallahi.
Sai kibar gidan suji dadi su zuba ruwa a kasa su sha niko ki barni da bakin ciki ba shi ke nan ba tana fadin haka ta juya ta fita daga dakin ta barni nan tsaye na rasa abinda zanyi a lokacin.
Sai Gajiye tace Rahama kiyi hakkuri idan kin tafi ai dadi zasuji ki mayar da kanyanki ki maida komai ba komai sai bakin ciki ya kashe su kin dai ji abinda hajiya tace ai.
Indan kinyi haka baki kyauta mata ba kije ki samay ta ki bata hakkuri a wuce gurin don Allah nan na durkusa ina kuka wiwiwi raina kamar zai fita.
Nasir ne ya taso daga inda yake ya rugumay ni yana fadin anty yi shiru kinji kyale maman Husna sai na halbe ta da bindagana.
Najawo yaron a jiki Amira ma tazo tasa hannayen ta tana share min hawaye tana fadin nai shiru sai taba hanifa da husna kashi tunda maman su sun sani kuka.
Kuka nake sosai sai ga anty ta dawo dakin takawo min jinior daya damay ta da fitina tasan gurina yake son zuwa lokacin yadda yake mata.
Yadda ta gan mu sai muka bata tausayi yaron ta miko min tafice itama kukan takeyi a lokacin.
Haka na wuni cikin bacin rai yaran ko suna manne a jikina duk inda nake suna saman jikina.
Muna falo zaune nake saman one seater amma haka suma suka manne min ga jinior saman jikina mu hudu mun makure a guri daya anty na dakin ta cikin bacin rai.
Daddy ne ya shigo part din wanan katon ya sauya kayan jikin shi zuwa kananan kaya wando baki da yar rigar tieshirt ja an rubuta mai THE KING da ruwan zaiba a gaban rigan.
Idanuwan shi a kan mu ina saye cikin digon riga light blue mai dogon hannu sai hulla da na dora a saman kaina.
Yaran na ganin shi suka mike zuwa gare shi suna daddy Nasir ya rike shi yace daddy please dont live anty to go.
Ya shafa kan yaron yace to go where ?
Yaron yace she said she is living us soon.
Inda nake ya kalla yace kada ki ruda yaran ki Rahama inkin yi haka baki kyauta masu ba kin ga sun shiga damuwa sun ganki a cikin damuwa.
Daddy wai zaka auri anty inji mummy husna harda mummy mu inji Amira take tambayan uban nata.
Shafa kan ta yayi yace mummy husna bata da hankali karya takeyi jinior ke mika hannu uban ya dauke shi wai.
Ya karaso inda muke ya dauki yaron yana cewa big boy may ke damun ka haka kake wanan raman ina mummy tana ciki ko ya juya da yaron zuwa cikin daki inda anty take ya samay ta.
Ta na kwance ta dunkule a guri daya jin shigowan shi dakin yasata dago kan ta idanuwan ta da taci kuka ya rine yayi ja dashi.
Yace kema kukan kike yi kamar yaran ko may kina son jawa kanki matsala kuma ko bayan kin san ba lafiya ya ishi jikin ki ba.
Yanzu abinda Matanka sukai wa yarinyar nan don su fashe haushinna akan ta sun kyauta ke nan besty ?
Yace ai ba ita sukai wa kazafi ba ni sukai wa sheri ni maigidan da sukaiwa zatlrgin sheri amma zasu gane kuren su ai sun san halina.
Shiru sukayi sai can anty tace Besty may zai hana ka auri Rahama ne shi kadai zakayi min ka fashe min haushina idan sunyi ne don naji haushi sai ya koma masu .
Babu daya daga cikin su da zata taba zaton jaka zai iya faruwa tunda sunyi ne don sheri dama.
Kina da hankali kuwa Saade nine zakice na auri Rahama may zanyi da wata mace kuma kosu ba dai da rabon aure bane a tsakanina dasu da kuma takuran magabata.
Mata uku ma yaya na iya daku balle na kara dauko wa kaina magana shin kin ko san naiyin maganan da kikayi yanzu kuwa besty da wani ido kike son yarinyar na ta kalleni da kuma duniya.
Tace an so what ba aure bane kuma Allah ya halasta maku auren mata har hudu a rayuwan ku, kana kuma da karfin yin hakan ta ko ina idan ka so yin hakan.
Ban son jin wanan maganan please gashi har yara sun san abinda ake fadi yanzun nan su Amira suka tare ni da zancen a falo ina dadin haka please.
Ai sai ki kori yarinyar a gurin ki bayan kin san irin taimakon da take maki a rayuwan ki a gidan nan.
Tace ai don tai makon da take min ni da yaran nake son taci gaba da zama damu a cikin gidan nan ko ba komai ko bani nasan zata rike min diya na yadda ya dace ai.
Dan Allah ki rabani da wanan tunanen yaran naki ko kema kin haukace ne irin na sauran ban sani ba ban son na kara jin wanan magana daga bakin ki kuma please.
Yaron ya aje mata ya fita daga dakin a hasale komai jin shi yaka yai mai baki kunci ya mamaye mai zuciyar shi yana tunanen may zai yi ya bata wasu hindatu rai akan haka.
Hajiyan shi ke neman shi can ya nufa amsa kiran mahaifiyar tashi tafe yake a motan shi yanayi yana shafa sajen fuskan shi a hankali.
Tunanen maganan da sukayi da Anty yakeyi ran shi na kara mai kuna a lokacin harya kawo gidan mahaifan nashi.
A falo ya samu mahaifan nashi su duk suna tare sai Aisha da ya samu tazo gidan a lokacin ganin su nan suka gaisa ya samu guri ya zauna.
Ya fuskanci mahaufiyar tashi yana cewa hajiya gani kince kina nema dazun da rana bani gari yanzu na dawo shine na shirya nazo.
Hajiya batason magana a gaban mijinta ba amma kuma babu yadda zatayi dole tai maganan a ga ban su hakana.
Alhaji yaya akayi haka kuma yar aiki ta daki matan ka kuma baka dauki mataki ba a gidan wanan ai raini ne da wullakanci kajawa matan ka hakan ?
Yace yar aiki hajiya ?
Ba yar aiki take ba may take a gidan ina matarka ce ta dauko ta kalar dangi ta zauna da ita samun wuri kuma yasa har takai hannun ta ta daki matan ka kamar wata yar chaina da ita tai masu kaca kaca da jikin su.
Suma ai taron banza ne suka kasa taruwa suyi wa yar banza duka tsiya sai ta kasa motsi a gurin gobe ta kara gigin kai hannun ta duka wani kuma.
Hajiya Rahama ba yar aiki bace na fada maki haka ba yau ba kaunar saade ne ta dauko ta taimaka mata.
Duka kuma ita Zulfa ita ta fara dukan yarinyar ita kuma ta rama hindatu taji haushi ta yaga mata riga ta mareta itama ta rama hakan.
May zance in ba fadan karya zanyi ba tunda daurin hannu ke garesu daga magana sukai wa yar mutane duka don suna takama sun fita.
Dariya Aisha dake gefe tasa tace Rahama ta zama shago ke nan duk ta watsa su amna anyi kattan bamza wallahi.
Amma dai basu kysuta ba inji Abba dake sauraren su koni ne tunda su suka fara bazan ce komai ba ai.
Haba Alhaji ka bari ai mashi magana haka bai dace ba wallahi yaya zata doki matan gida su da gidan mijin su ina ruwan ta da fadan kishin su da zata saka bakin ta ciki.
Yace hajiya har ni Hindatu zata kalli idona tace wai ina tare da Rahama ta sani ba yau ba.
Ni zatai wa zargin sheri da kazafi irin haka don ta raina ni ko may saboda suna ganin suna iskanci son ran su ina kyalesu idan mace nake so kasa nawa nake zuwa ina ganin mata iri iri ban nema ba sai kaunan saade zan nema kuma.
Ni hajiya yaran nan sun kai min ko ina wallahi saboda ku fa nake zaune dasu haka na amma ba wani jin dadin zuciya da nake samu garesu.
Kai mata ho idan ma kana son ta aiba abin boyo bane ko tunda Allah bau haramta maka yin hakan ba sai ka auri abinka shike nan.
Mahaifin daddy ne ke fada mai hakan yace in har akwai alheri ga auren yarinyar kaje ka aure ta ni nace gobe su kara kazafi da kyau kuma.
Haba Alhaji wanan wani irin shawara zaka bashi haka kuma ana neman mafita ga yarinya tazi ta addabi mutane da gidan su.
Ko ni nan ta taba min rashin kunya saida na hada ta da yaruwar nata nai masu tas tashiga hankalinta.
Don haka bani son zaman yarinyar nan a gidan man kaje ka sallamay ta tabar masu gidan su takoma inda tafito kaji na fada maka.
Ni kuma nace babu inda zata kinji hukunci na wai may yasa ku mata baku da hankali ne komai girman ku ai idan ta tafi sai a dauka da gaske ne haka maganan yake son ta yakeyi din.
Ba, a aure mukasa su ya aure su baiso hakan ba a lokacin ban son maganan shirmay dama don wanan shiriritan ne kika kira shi yabar abinda ke gaban shi yazo nan.
Ni mahaufin ka na baka baki jeka auri yarinyar in har haka shine mafita a gareka suje su mutu yaran banza kawai da basu san arziki ba tashi kafita na sallamay ka.
Aiko da ka auri yarinyar nan yayana daka more rayuwan ka tun da matan ka kaf babu mai zatin ta a gidan ka kishin haka ne yasa suke zargin ka kawai.
Gata da tsabta ga kirki ga girmama na gaba wallahi yarinyar tayi hundred

Please Login or Register in order to submit comment