Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bacin rai kullun namiji sunan kuna zaune kalau amma baida aiki sai na kadin aure.
Kamar wanda bai samun jin dadi gun iyalin shi irin wanan ma ai sai duniya ta zagi mutum don baza mu fita sai ace mune bamu gamsar dashi ga wanda bai san halin shi da raayin shi ba.
Sai naji Inna tace kinga ta nan tun dawowan ta na fahinci ba dadi tsakanin ta da shi don ko yawan shigowan da take dubamu ya rage.
A, a haba dai Rahama may kuma kike so a duniya yanzu ilimi da daukaka Allah ya baki ga miji na gwadawa tsara kin samu ga zuria dayyaba Allah yabaku a tsakani may kuma kike nema Rahama ?
In dai don wanan auren da yake yawan yi ne sai ku barshi da halin shi tunda auren nasa bawai yana takura maku bane ko wani abu.
Gaskiya in har hakane abinda uwarki ta fada baki ko kyauta ba don banga abin damuwa ba ga wanan dai.
Bafa a kan ku matan ke zama ba ke ku godewa Allah ma da ba irin mazan nan bane da idan sun dauko wata a gida ke ra gida dake da babu duk daya kuke a wurin shi.
Iya hakkuri bawan Allah nan yana dashi a gare ku iyalin shi ki duba irin tsiyar da yaran nan hindatu da zulfa ke shuka mai amma yana hakkuri yana takewa yana kuma zaune dasu lafiya.
Duk masu shigowan nan ni a ganina kaddaran aure ne a tsakanin shi dasu inba ita wanan daya aura mara tarbiyan ba bayan mutuwan diyana waya haihu dashi ?
Balle ita wanan uwar guzumar daya kwaso yanzu ai ba batun haihuwa a gare ta ma mufa a zamanin mu bamu kishin komai inba na haihuwa ba ki zuba in zuba kowa ya cika gida kuma babu wani abindake ga namiji in dai ba wanan din ba.
Nace mama ni ba wai auren shi bane ko wani abu ke damuna yanzu fa ba irin da can baya ne aure haka a zamanin nan abun tsoro ne ga namiji don zamani ya canza lafiyan mutum akewa tsoro.
Haba yar nan har ke kin fishi sanin hakan ko kin kaishi sanin abinda duniya ke cikine wai inna tace fada mata dai mai kuli yarinyar nan bata ji ne tun bata dawo kasan nan ba mukai wanan maganan da ita.
Ashe ita da manufa a zuciyar ta yanzu kinji inda ta bullo wai ita malamar lafiya dariya inna tabani nace inna ba haka bane ku baku ganewa ne shiyasa.
Bafa ganin mutum yanzu haka lafiyyaye shine lafiya ba ciwon ba a goshi ake ganin shi ba nan dai nai masu bayan komai kan irin cutar da nake gudu gare shi ga yawan auren da yakeyi.
Na kara da fadin yanzu fa ki duba waban matar da ganin ta irin yan duniyan matan nan ne dake zaman kasu a wani kasan bama a na kasan ba kawai.
Nan nake fada masu yadda mukayi da ita ranan da muka dawo garin mama tace yo ga yar iska ita kuma dashi ta shigo watse gida ko may ?
Nan dai suke min nasiha da kuma fadakar dani irin halakan da nake daukawa kaina na wanan zaman doya da manjan da mukeyi dashi a gidan.
Maganan su ba wai ya shigeni bane sosai don ina a kan bakana na sai naga takardan gwajin da sukayi da ita kafin auren su dashi.
Baya gari da ya dawo ya shigo gaida su nan yake magana akan tafiyan inna da zatayi ga jibi sai inna take cewa dashi Alhaji mun gode kwarai da kokarin ka a gare mu ko yaushe don Allah adai ta hakkuri da iyali.
Murmushi yayi yace Inna ai hakkuri ya zama dole tun da an zama daya yanzu suna dauka na ban san may nakeyi bane shi ya kawo haka kawai.
Hakkuri za ayi don mu mata dama sai hakkuri balle ga wanda ya aje mace fiye da daya ko biyu a gidan sa.
Ya mike yana fadin barsu ai mun saba in dai halin su ne komai zai wuce ne insha Allahu.
Da dare na shiga falin nashi don na fada mai ina sin ni da kaina zan mayar da inna gida idan zata tafi do ina son zuwa na duba jikin mahaifina.
Ya dago kai yana cewa dani ashe ina da darajan da za a nemi wani alfarma a guna nace ni ba wana ya kawo ni ba yanzu.
Yace ban amince ba in dai nike da wanan dokar a hannuna nace ba matsala Allah ya bashi lafiya don ban tsaya jan maganan ba .
Namike zan wuce yake cewa dani kina ganin wannan matakin da kika dauka a gare ki shine daidai ko kina min daukan mara hankali ne wai ?
Nace namay kuma nifa auren ka ba wai ya damay ni bane kawai dai magana ta daya ne a nan shine naga takardan ku na gwaji da kukayi da wanan yar duniyar matar tunda abin bana kai sake bane nake gani.
Ko makaho ai sai ya lalaba yake taka wuri ba wai tafiya yake babu lalabe ba mutum tun yana dauko abinda duniya ke iya dan kallo har ya koma dauko abinda za ai mai dariya don bakin jaraba kawai.
Na sa kai zan bar falon naji yace dani Rahama nine yau kuma jarabbabe ko may ?
Nace ai haka din ne don in ba jaraba ba banga abin gani gun wanan curarar matar daka dauko ba a gidan nan ban da magana babu abin ganewa a nan.
Yace a ganin ki ba ni abin dake min na dauko kune baku ganewa kawai nace sai kuje kuyi ta ganewa kai da ita ku da jaraba ya dama a rai.
Ina fadin haka na juya na fice daga falin dakina na nufa kai tsaye na fada saman gado siffan wanan matar dana gani mai kiba wai amarya nake tunane da yace shi yana gane abin sa.
Nace a raina to may daddy ya gani har yace mune wai bamu ganewa a nan dayake fadi ni dai banga wani tsiya ba a gunta in banda muni sai ko launin jikin ta da ya nuna mai take shafawa na zamani.
Shima na barshi can yana tunanen magana na abin ashe ya bata mai rai yace watau ke nan ina nufin baida hankali ko may da zai afkawa mace irin haka kai tsaye shiko Niima da ya aura a budurwa bata shigo gidan shi ba sai da sukai gwaji da ita.
Balle wanan dashi kan sa yasan zaman barikin da tayi a waje dama nan kasan don ba diyar kowa bace ita irin matan nan ne kawai masu sai sunyi kudi da karfin tsiya ko ta wani hanya.
Shi kan shi wani lokaci yakan yi mamakin yadda ya aure ta ba dai tsari takai ko wace mace dake gare shi a gida ba balle auren dai ne yazo masu don ta dade tana bin shi amma sai gashi haduwan su da ita a kaduna yaji yana balain sha awanta shiko ba zina ya iya ba don haka tana gabatar mai da zancen aure yaji ya amince mata da suyi din ba adauki lokaci mai tsawo ba aka daura auren.
Abinda bai sani ba sai da tai mai zaman kashi na shekaru tana aiki a kan sa duk wani shige da ficen shi ta sani a kasan shiyasa bata sha wani wahala ba wurin samo kan sa.
Namiji baida wuyan kamawa gun mace ta wanan fannin sai idan Allah ya kare shi kawai daga kaidin ta gashi ma ita kan ta da ganin Rahama hankalin ta yai balain tashi sosai don yanzu haka a cikin rikici suke da ita.
Don ya tsura ta taja waya tana fadin itafa hankalin ta ya tashi ga matar don ko diyan ta fa cewa tayi takwas dashi kawar da ita kawai zanyi don ina ganin ita ce aka fada muna dama bazan iya da ita ba a gidan a kawar min da ita kawai kowa ma ya huta.
Bai san may ake fada mata ba a wayan dago kan da zatayi sai kawai ta gan shi tsaye a bayan ta nan ta shiga kamay kamay tana fadin ai na fada maki wanan hadizan yar iskace ni maganin ta zanyi idan bata dawo min da kudi na ba.
Ta kashe wayan tana wani fadan borin kunya sai taji yace da ita a gidan nawa nake da hadizan data ci maki kudi har kike son a kawar da ita a duniya ko may ?
Tace dashi tunda ba kunya gare ta ba a gidan ka kamar ya kasan da wace nake waya ne balle kace wai a gidan ka ?
Yace ke dakata kiji duk abinda ya samu daya daga cikin iyalina kema ya samay ki don duk abinda kike fadi tun dazun a kunne na yake gaki ga matan nawa sai ki kashe ta tun yau mu gani.
Ya juya ya fita ya barta tana fadan borin kunya don duk jikin ta yai sanyi har ta tafi basu shirya ba do ta rasa gane kan shi abu ya taru yai mashi yawa a zuciya sai kuma.
Wanan shigowan nawa yanzu ya fahinci inda na dosa da zaman mu dashi da muke yar tsama tun dawowa na.
Ya nisa tare da furzo da iska daga bakin shi yanisa yace halin mace ta waye ke nan ai su wa yan nan basu ko kai zuciyar ga wanan maganan da nayi ba sai fadan kishi da ya damay su kawai.
Ban sake magana akan bin Inna ba zuwa duba mahaifina da yan uwana a gida sai da safe ina daukan waya naga text din shi yana fadin na shirya nakai ina gida tafiya ya kama shi baya samun zuwa ya maidata.
Kamar nace na fasa amma kuma sai naga wanan ne lokacin da nake dashi a yanzu kuma ko banza mahaifiya tace zan kai ba wata ba.
Don haka a gurguje na shirya tafiyan sai gashi ya shigo yi wa inna din sallama ya kawo sako envelop biyu ya bata daya takaiwa maigari dayan na mahaifina nane.
Godiya sossi inna ta shiga mashi ba laifi a gurguje nake ta shiri ya shigo dakin ya samay ni a hakan nai mashi ina kwana ya amsa ba sakin fuska kudi ya bani masu yawa akan tafiyan da zanyi din na ansa da godiya.
Nan yake fada min zancen tafiyan shi da zauyi zuwa kasan Kuwait inda zai kwana biyu a can don wani harkan mai da suke son yi a can din.
Zuwa wani kasa shi da wasu da suka hada hannu dasu nai mashi fatan alheri tare da rokon Allah ya bada saa ga tafiyan.
Bayan na gama maganan ne sai dan shiru ya biyo bayan va wanda yai magana a cikin mu can naji yana cewa dani yanzu haka zaki barni na tafi babu ko tausayawa ?
Nace kamar ta kuma aini na gama zance akai ko don na fada ma matsala kuma na zauna inda Allah ya aje ni ko.
A ina aka aje ki nace matar da bata da wani biyan bukata aji dadin ta sai na waje da ake hangowa a gare su ne hutu yake da jin dadi ko.
Wanan kuma maganan ki ne abin siri ne mai daki shi yasan inda ruwa ke yoyo ai ba wani ne yasan cikin zuciyana ba.
Auren da nake kuma kaddaran ubangiji nane wanan don haka Allah ya kaddaro min a rayuwana nace da sauri kuma da niyyan yin hakan ba.
Yace haka dai kika ce amma ai ko duniya tasan banda macen da tafi min Rahama a yanzu, in ma yin auren da nakeyi ne ai kina da kamisho a cikin sa tunda kulawan da nake samu da a wurin ki yanzu aikin ki ya hanani samun shi kamar baya.
Kin mayar da rayuwan ki akan aikin ki fiyye da bani irin kulawan da kika saba bani a baya.
Yaya kike son na zauna a gida ni kadai kulun kamar maraya babu mai bani kulawa yadda nake so ai min.
Nace ta nan kuma za a bullo min yanzu su matan dake gida ba mata bane ko ni kadai ne mace a gidan wanan maganan ma kada ka bari wani yajita don Allah don sai ai maka wani fahinta na daban can.
Mutum mai mata uku a gida zai tsaya yana fadin irin wanan maganan haka ai abin kunyane a gare ka aji hakan daga bakin ka.
Yace ga wanda baisan mai aure yake nufi ba zai min wanan fasaran ko amma wanda yasan aure da kulawan shi ai ba zai ce wani abu ba kan magana na.
Nace ni dai ban ja ba kawai takardan gwaji nake son gani shine karshen magana na dakai yace kina min dan kan mai ciwo ke nan yanzu ko kuma wani wanda bai san kan sa ba can ko ?
Nace wanan wani magana ce mara evidence kake son fadi don ni magana daya na kawo idan naga amsa sai komai ya wuce a guna amma bani gani mace haka yar duniya ta gama karade duniya da tun da kurciyar ta yanzu ta dawo nan ta cuta muna don hainci kawai.
Ya girgiza kan shi tare da fadin Rahama ban san may kika masheni ba yanzu har abin yakai ga ban san zafin kaina ba da zan fadawa halaka don idona ya rufe da aure ko may ?
In ma wani abune na fada maki kece mai babban kamishi ga yin haka a gare ni nace da yake ita Raliya daka aure ta lokacin ina aikine ko ?
Yace au baki aiki ko ya murmusa yana fadin ni zan tafi don ina ga daga can zan wuce nace Allah ya sauke lafiya yace to ba kaji ba rakiyar ma itama yanzu bana samun ta dai ke nan nace ai wanan ba matsala bane idan ka gama sai ka kirani na fito.
Nace mun kuma gode da alherin da akaiwa iyayye Allah saka da alheri yace ba don ki nayi ba albarka nake nema don banga dalilin da zanyi don ki ba nace ko a hakan ma mun gode ai.
Yace tare da dan juyo ya nufo inda nake zaune da sauri na mike tsaye dariya ma nabashi yace ashe abin naki da gaske ne nace ka dauka wasa nake ashe.
Wanan uwar guzumar da ka kwaso ku karanta can da ita don ba zan yarda ta kwashe min current din na ba ta karawa tsufarta .
Dariya sosai yake ya fice yana fadin ni kinga tafiyana sai na dawo da sauri na bi bayan shi ina fadin Allah ya tsare a tare muka fito daga dakin.
Mun fara tafiya nake cewa dama ina son tambaya nadawo kuma naga har yanzu zulfa bata dawo garin ba bai takan ni ba sai rike hannun Anty da yayi suna magana da yaran kasa kasa ban majin abin da suke fadi ba.
Mun fita tare har haraban gidan inda na samu har wanda zai kaishi yazo yana jiran shi nan muka taru har yaran muna mashi a dawo lafiya.
Ya tafi yana daga muna hannu muka juya muka shige gidan tare muna hiran ko ina amaryan tashi ta shiga kwana biyu hindatu take cewa wata kila ta tafi balaguron ta.
Allah dai ya kyauta nace da ita tare da jan hannun anty muka shige ciki na bar yaran maza suna wasa a haraban gidan sai na dan juyo ina fadin yau fa kano zamu zanje na maida Inna gida insha Allahu.
Tace ashe gidan zai koma mu kadai ke nan a yau din nace gaskiya kan don zamu kwasa gida yayi kira yau din nan insha Allah kano zamu dira.
Ban wani dade ba nagama shiri na muka kama hanyan kano ni da iyalina idan sai biyar muka sauka garin don haka nan Gajiye ta shiga dawainiya damu.
Zulfa ta shigo ta tare mu munyi yaya bayan rabo da ita muka dan taba hira ta barmu mu huta na shiga da wainiya da yarana.
Sai washegari tun da safe Inna ta sakani a gaba don tana ganin kamar zance da ita ta kara kwana a kano saboda hankalinta ya koma gida sosai.
Da kyat na samu ta amince min na dan shiga kasuwa don sayo tsaraban da zamu tafi dashi saboda a can ban samu sayen komai ba na tsaraban da zan kaiwa yan uwa na.
Sai bayan munyi sallah a zahar muka kama hanyan kauyen mu nida yaeana baki dayan mu don zamu dan kwana biyu a can kamar yadda nake son idan da hali.
Mun isa a lokacin yan ma ta danyi kadan bayan la,asar mun samu taro kamar yadda muka saba samu idan muzo a cikin karamci.
Wanan karon ban sauka dakin kowa ba dakin mahaifiyata muka sauka daga ni har yaran inda da kaina na shiga gyaran dakin ina fitar da duk wani abinda bai dace ba a dakin.
Inna tana faman fada amma nasa aka fice dasu nan mutanen gidan suka shiga tsintar abinda suke bukata daga ciki sai da naga dakin ya koma yadda nake so na shiga wanka ina fitiwa ne wayana yai kuka masu motar kayan dake bayan mu sun iso nan na fita da kaina na bada umurni da su shigo da kayan komai na dakin sabo aka saka ba mama ba har abokan zama nata sai dai na mama din yafi nasu tsada ne sosai.
Nan gida ya shiga murna kowa aikin nasa ake yi don da masu haka kayan akazo kafin wani lokaci har sun gama aikin su ko nan na sallamay su suka tafi komai har kayan kallo sai da a saka masu do yanzu mun samu wuta a kauye da safe za a kira min mai wearing yazo yai masu.
Zuwa washe gari komai ya kammalu yadda nake so a raina ban samu shiga wurin mahaifina ba don aikin da muka sha yasa na dan gaji sosai.
A nan gidan Inna ta Suwaiba ta samay ni duk cikin yan uwa namu yafi zuwa daya da ita sosai nan ta taya ni fitarwa yan uwan mu da abokan arziki tsaraban da mukazo masu dashi.
Sai yamma ta shirya zuwa gida inda na yafa muka fita tare da ita a kafa muke tafe muna hira tana bani Labarin sabon bazawarin da Rukaiyya ta samu wai zata aura.
Nake cewa da ita ta dai bi a sannu ga yaran ta kanana ne gun wa zata barsu don tasan halin maza yanzu ba son dan wani suke ba tsakani da Allah.
Indai ba dan abinda aka bar masu bane yake hasashe yake son ya aure ta idan ya cinye ya gudu ya barta da wahala kuma ga yara kanana.
Tace ai kafin yaci mama ta cinye rabi don kullun sune zuwa gidan boka da malam wai tana son su mallake komai da Jatau din ya bari iya wasu.
Nace kai haba har yanzu ita mama bata daina irin wanan halin na bawa boka da malamai amana ba duk wanan wayewan kai da malamsi ke bamu haske akai.
Tace mama kan bata da ranan barin wanan halin don ko ciwon kai taji yanzu zata yafa ta je gun bokan ta tace wani ne yai mata asiri.
Nisawa nayi tare da fadin Allah ya kyauta ya ganar damu hanya madaidaiciya tace amin yar uwa.
Mun rabu da ita akan da safe zata shigo mu zagaya garin mu gaida yan uwa da abokan arziki da aka kwana biyu ba a gana ba.
A dakin mama Abu na yada zangon muka dan taba hira da ita sai da akai kiran sallah nabar dakin nata.
Washegari Suwaiba koda ta shigo ta samu har na shirya muka garzaya sai gidan mahaifin mu mun samay shi a gida don yanzu babu inda yake zuwa saboda sugar da yasa shi gaba.
A kofan gida muka samay shi tare da yarana muka zo gidan namu ya nuna farin cikin ganin mu nan yayi yayi da yarana akan suzo gun shi amma sai suka ki.
Na ce dasu a cikin tsawa kuje gun grandpa sai suka tafi ya rugumay su a jikin shi yana dan hira dasu na tambaye shi lafiyan jikin yace dani Alhamdullahi.
Ai abin yazo min da sauki tunda ina samun kulawa daga gare ku keda mijin ki Allah dai ya saka maku da alheri.
Nai murmishi tare da fadin amin baba ya juya gun Suwaiba yana cewa ashe kina gunta haka nake son ganin ku da baku biyewa wanan uwar taku da har yanzu bata san Annabi ya faku ba hassadan ta a kullun kamar karuwa yake a zuciyar ta .
Na rasa ko wata irin mutum ce Laure da bata girma kullun jiya iyau take Suwaiba tace baba ni yanzu ai ba zan taba yarda mama ta hadani da kowa ba tunda na gane halinta bana kai mutum ga alheri bane ko yaushe.
Nace tashi mu shiga mu gaida su mama mu wuce zuwa sauran gidajen sai dai kafin na shiga saida muka leka mama Altine bata nan ta fita zuwa unguwa.
Kamar kullun yadda mama Laure ta saba tarona babu yabo ba fallasa hakan ne ma yau a fuskan ta don tunda tace a, a mutanen birni ne yau a gidan namu bata sake bi ta kan mu ba sai Suwaiba ce ta shiga ta dauko tabarma ta shimfida muna a waje cikin yar rufar dake daga kofan ta da akayi.
Amaryan baba tafito da murna tana muna sannu da zuwa na karbi danta dake goye a bayan ta take cewa jiya mukaji labarin kin shigo kin dawo da yaya a wurin mai kuli.
Nace mun shigo mama aiki ne ya dan yi min yawa da mutanen dake shigowa yasa bamu samu shigowa wurin ku ba a jiya din.
Tace to yaya hanya andawo lafiya Allah yasa abinda akaje nema ya amfana ga kowa ai kina da kokari wallahi duk da baki kasan amma aike ko yaushe baya katsewa a gare mu.
Nace kai mama ai hakan ya zama dole nayi mata gaisuwan mahaifinta da na samu labarin ya rasu bana kasan .
Dama haka ake so ai a dinga bin masu hannu da maiko idan sun shigo kamar za a fadi ana ladabin shegu gare su.
Na dauka ma dani take sai naji amarya na cewa bakin halin wasu kuma bai bari hassada ya sa suci arziki ai gara nabu naci arziki dana zauna hassada ya kashe ni a daki.
An girma ba a san an girma ba har yanzu mugun hali ya hana a tuba a koma ga Allah sai yawon bin boka da malam a ka iya.
Nace da yarana su mike mu tafi na mika masu tsaraba da bazo masu dashi harda yaran amaryan babana sai kuma mama ta hau fada wai har yanzu ina nuna mata kiyayya a fili.
Ita may yasa ban ban ta wani abu ba kari akan wanda nabata amma na uya sakowa kannena har da agolan gida tsaraba.
Allah sarki dadi inji barawon takanda an daiji kunya wallahi ai sai ki bari diyan ki da kika hana su nuna yara jinin su ne amma ba wacce hassadan ki ya zamawa taki ba a duniya.
Don rashin ta ido wai yau har kina fada kan

Please Login or Register in order to submit comment