Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shine Allah yabaki naki rabon a gidan nan nima naga jinin ki a cikin gidan nan kamar kowa.
A cikin raina na karba mata da amin amma a fili murmushi kawai nai mata nace kai haba anty muje kiga kayan a falo kada mu bata maki guri nan.
Tana fitowa taga kayan take cewa kai kai kai Rama wanan kayan haka duk a lagos kika samo su haka waya na daga na kira Fatima nake cewa duk su kwaso sauran kayan su kawowa anty ta gani.
Nai mamaki danaga tana jidan kayan kitchen din da nazo dasu sai bayan ta gama zabe tana ta yabawa da kyaun kayan haka .
Take cewa kin san ina da amare har biyu shiyasa na zaba masu ba sai munje saya waje ba daga baya.
Amare a ina kuma anty tace gajiye da Fatima mana Rama ai dole nice uwar amaren dai ina ce.
Shiru nayi mamaki ya rufe ni na hali irin na anty ko ni da Fatima take guna banyi wanan tunanen ba haka.
Amma saboda salihanci irin na anty sai gashi ta ita tayi wanan dabara ganin nayi shiru naji tana fadin Rama kin fasa abinda kaiwa wani a duniya shine rabonka a lahira walau sheran ko hairan don haka don Allah ki barni na samu wanan ladan na alheri dana sawa raina.
Wanan shine kadai abinda mutum zaiyiwa wani mai bukata na kasa dashi ya tsira ga ubangijin shi.
Don haka gobe zan baki kudin kayan ki sauran list din abinda nake bukata garesu kuma akan su duk kece zaki sawo Rama na saya a gurin ki wanan alkawari ne naiwa raina hakan.
Shiru nayi duk imani da tausayin ta ya kamani sosai sai tunane nake wai ita wata irin mutum ce a duniyan nan cikin mata ?
Bata fita ko ina tana gida anty time tana bautan Allah da auren ta haka kuma abinta ban taba ganin ya rufe mata ido ba ita a rayuwan ta.
Sai naji tana ta faman yaba kyawon les din da na sayo muna tace kuma kayan yara sun matukar burge ta a rayuwan ta.
Muna cikin fira sai ga maigidan ya shigo fuskan shi a daure murtuk dashi dagani har wanan lokacin ranshi a bace yake mai.
Gaishe shi muke yi daya bayan daya yana amsawa kamar baya son amsawan a lokacin.
Tambayan ko kayan may ye wanqn haka yayi take cewa kayan da Rama ta saro a lagos ne mana.
Inda nake ya juya yana cewa ke har yaushe kika samu sayan wa yan nan kayan haka cikin mamaki ?
Nake cewa dashi da muka tafi da matar Adebayo ne ta kaini na sayo su a can.
Yana tafiya yake cewa kada fa ki ce zaki fara shiga Dubai wanan abin dana gani haka fa ?
Dariya duk wanda ke falon yasa saboda maganan shi sai anty ke cewa aiko bataje ba sai tai oda kuma su shigo mata yanzu akwai hanyar bussines ai a cikin sauki masu yawa.
Ya har falon mukaci gaba da harkokin mu sai dare na koma ni da su Fatima part dina gan kwanta ba karatu na shiga yi ina nazari saukina abinda na koyo da muka tafi chaina dashi ne akayi bana garin.
Washe gari ban tsaya ba na loda kaya a mota na fice gidan Allah ya taimakeni tun a mosque da mukaje sallah nai ciniki sosai an kwashe lace din dana fito dasu ranan gaba daya har ana nema don kyaun su.
Na dawo gida nagaji mukai kicibis da Zulfa yarta na wasa a haraban filin gidan ina ganin ta na ja burki sai da aka dauke yarinyar na karasa inda nake aje mota na.
Na fito ganin Zulfa duk da nine na fito unguwa ya kamata tai min sannu da zuwa a lokacin amma na san bazan samu hakan ba a gareta na daure na gaida ita da gida.
Maimakon ta amsa min sai cewa tayi amma tukin naki Rahama ya zama na ganganci zaki shigo kin san akwai yara a gidan zaki kwaso haka a guje nikan ki rufa min asiri kada ki mayar dani baya please ?
Mu koma dani dake ba maishi a gidan mun zama daya ke nan a hakan don Allah ki rufa min asiri please.
Mamaki ne ko takaici ya rufe ni na tsaya rugumay da takardu a hannuna ina kallon ta nace haba anty mai yai zafi haka kuma da wanan maganan haka ?
Aiko da ban taba haihuwa ba nasan zafin yaron don ina da imani a zuciya ban ga dalilin da zan dauki alhakin karamar yarinya irin baby ba haka ?
Daga can bayan mu naji ance damu aiko jaririya ce sai a kashe akan kishi tunda mutum na bakin ciki da diyan mutane tunda shi bai haifa ba saboda hassada.
In haihuwa banza ne ai mace ta haifi nata mugani mana amma sai kai ai kokarin salwantar ma da wanda Allah ya baka kuma saboda bakin hassada.
Murmushi nayi nace sai dai ku sani ni baniwa Allah garaje akan abinda ya boye da haihuwa da rashin shi duk ikone na ubangiji ni ko a hakan da nake nagodewa Allah na kuma ko yaushe ina cikin gode mai ga irin ni,imar da yai min wanda kowa bai taba zaton haka ba a gare ni.
Zama mace ta hudu a wurin mijin irin daddy aiko ba hahuwa alhamdullahi don babu abinda na nema na rasa sai dai nagodewa Allah na a hakan.
Tunda mijina bai taba banbatani da masu diya agidan ba kuma rasgin haihuwa ba wai ya damay shi bane don ina juya cikin ku ashe ko Alhamdullahi tunda daidai nake ga kason kowa ko ban haifa ba an haifa min kuma ina da iko yadda naso dasu.
Ban tsaya jin amsan su ba na shige abina na barsu nan suna ta faman haushi kamar mahaukatan karnu ka.
Zan shiga naji hindatu na fadi lalai yarinyar nan wuyan ki ya isa yanka ashe don kina ganin kamar kin kai kowa ne a gidan yanzu.
Na juyo nace har akwai may wata kama na kwarai ne can na daban ana ko kuwa taron cushe inda za, a bar mutum yayi zabe ai ba mai zaben ku cikin gidan nan kuma kun san da haka sai dai ku godewa Allah abin ya zama na sadaka ne gaba daya.
Na shige abina na barsu nan kamar ran su zai fita wurin jifana da bakar magana ni dai banji ba balle naji zafi suko sunji nawa dana fada masu.
Don basu taba zaton nasan cewa ba shine ya nemay su da aure ba bashi su akayi ya aura a dole.
Sunji matukar haushin wanan kalamin harda cewa wai a bari maigidan ya dawo ai dole ne a zauna dashi.
Har dare ina jiran kira banji komai ba kuma ban ma fito hira ba fun anty don damuwan da ya kamani kan wanan yawan gorin da suke min na rashin haihuwan da banyi ba kuma ban fadawa anty abinda ya faru ba tsakanina dasu.
Washe gari cikin kuka nake fadawa Zarah irin gori da habaicin da suke min idan magana ya hadani dasu.
Hakkuri ta bani tace kada nasa zancen a raina don Allah bai mata da ko wani bawan shi ba sai take cewa dani na samu miyar kuka koda yaushe na zauna na shashi sosai don yana sa mace samun haihuwa idan bata haihuwa.
Tun wanan ranan zan hada kuka yaji daddawa da kayan yaji na zauna na shashi sosai.
Kuma ina hadawa da bissimillah kafa dari daya da goma sha uku na shafawa kasan marana.
Sai kusan bayan sati daya ranan daddy ya shigo ina zaune saman sallaya muka gaisa yake cewa dani Rahama idan zaki shigo gida ki daina gudu da mota haka don gujewa kaddara.
To daddy nace dashi insha Allah bazan yi godu ba har ya fara tafiya sai naji yace amma kuma nai mamaki don ban san lokacin da kika fara tukin ganganci ba haka ?
Na ce cikin murmushi daddy ni bani gudu kaima ka sani ka kuma sheda hakan gare ni ai sai dai zan kara tsarewa insha Allahu.
Ya ke cewa dani matar Adibayo tace a fada min kayana zuwa tuesday zasu shigo hannuna insha Allahu.
Nace ai min godiya wurin ta sosai yake cewa yana gani wani sati zai wuce zuwa Bangkok akwai taron da zasuyi acan din.
Nace amma ba dadewa zakayi ba ko daddy naso kafin kai tafiyan asan matsaya akan Gajiye da Fatima yace haka nake planing nima kafin dai na tafi hakan za, ayi insha Allahu don shawara ne mai kyau wanan.


Kuyi hakkuri da wanan da kyat na samu na dan rubuta maku shi don har yanzu ina jin jikina wallahi nagode kwarai da kulawan ku gareni yan uwa wanda na bata ma rai ga jina shiru suyi hakkuri don Allah dani halin jiki da jine hakan nagode da fatan zaku fahince ni yan uwa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON ONLINE NOVEL NE BA A YAFE BA , , ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA KEDA ALLAH YAR UWA DON ONLINE NOVEL NE, , ,
58

Daddy bai bar garin ba sai da ya tabbatar da komai ya ian kama akan zancen auren Fatima da hamza gajiye da maigadin gidan shi.
Har dukiyan aure sai da ya biya tare da duk wani abinda ya dace ayi a kan aure na fannin maza yabar garin.
Wanan karon daddy bai tafi dako wace mace ba shi kadai yai tafiyan shi batare da ya tayawa kowa ba gashi s n sa rai cewa ,
Daya daga cikin su ne za, ai wanan tafiyan da ita zuwa waje don haka kowa a cikin shirin tafiya take amma sai ganin shi kawai sukayi yazo sallaman su akan zai tafi.
Yakawo kudi yabawa kowa wanda zatai amfani dashi bayan kayan abincin da ya sayo muna, masu yawa ko wani part aka shiga dashi equally,
Da ganin irin wanan tafiya tafiya ce mai muhinmanci a gare shi zai tafi ya dauki lokaci acan har sai ya gama shige da ficen abin da ya kaishi kasan zai dawo gida Nigeria.
Gashi yanzu bakin kishi ya jawo wa kowa hasara yai tafiya shi kadai suna kallon ba wacce ya tafi da ita.
Sana,a ta nake da karatu ba wasa Allah kuma ya taimake ni ina samu sosai a wanan fanni,
Ba karamin haushi da takaicina matan daddy ke ji ba saboda wanan tafiya din da akayi bada su ba.
Daga karshe sai ga shi ranan Saturday tunda safe sun tayar damu da fitina a tsakanin su akan fadan yar wurin hindatu wai ta dauki baby sai ta yar da ita daga hannun ta, da gangan .
Allah ne ya kama su don suna tsaye suna magana a waje kan tafiyan daddy din ita hindatu ke cewa da ita wanan ai sheri ne da makirci kawai irin namaza don ya ga bada ita zai tafi ba.
Suna cikin wanan gulman ne sai ihisan ta dauki baby din daga hannun uwarta tana wasa da ita daga gefe.
Sai kawai ta sake ta a kasa ta fadi cikin wasa maimakon uwar tai mata magana sai tana dariya ga har bakin yarinya ya fashe tana tsala ihu ita ko zulfa taji haushi takaiwa Ihisan bugu sosai take fitina ya fara a tsakanin su don kowa bai kawar da ido ga danshi.
Fada sosai suke wanda wanan halin ba abin mamaki bane a tsakanin su tonon asiri suke cikin daga murya na fito don raka yara na samay su a hakan su gajiye da sauran yan aiki na daga dayan barin suna sauraren su.
Kukan da yarinyar keyi ga bakin ta da hanci najini a gurin da ta bugu yasa na kasa wucesu nace da uwar ki duba wanan yarinyar anty bakiga jini yadda yake zuba mata ba ne ?
Ta mayar da kallon ta ga yarinyar jini ne sosai yake zuba da sauri na karasa gurin na bude bakin yarinyar take hankalin kowa ya tashi nace da fatima yi sauri dauko min kada a first aids box .
Abin ba dadi yadda nake cusa kada a bakin yarinyar ina fitar mata da jini a cikin sa ashe harshen yarinyar ne ya hakori yai mugun datse shi yake fitar da jini.
Da kyat na samu jinin ya tsaya nace maza ta kaita asibiti a duba ta zaifi don ai mata alluran T,T .
Hankalin mu duk a tashe don ko ita hindatun jikin ta yayi sanyi sosai dole yarinyar na ajikina muka tafi asibiti mu uku hindatun ce take jan motan ina dafe da bakin ta don jinin bai tsaya ba har lokacin.
Ba karamin ciwo taji ba ni da kaina nai treating din yarinyar yarda ya dace muka dawo gida.
Nikan muna fita mota nai masu Allah ya tsare gaba na shige hanyar part din mu.
Na samu anty na falo zaune tace dani har kun dawo Rama yanzu dana fito Gajiye ke fada min abinda ya faru ai.
Rama sai nake ganin kin fini saukin kai a wani fannin har yaushe suka gama maki kazafi akan yarinyar nan don kawai su bata ki ga maigidan Allah ya kare kawai bai dauki zancen su ba.
Nace ina zama wanan kuma don kan su ai yarinyar taban tausayi ga yarinya a wani hali amma don hauka wai fada sukeyi su.
Ai idan kan yara ne su basu kunyar hakan gare su, shiyasa nake jin dadin yadda ki kaiwa yaran nan training ba ruwan su da shiga wurin kowa yanzu balle su dauko min magana ina fama da kaina.
Anty idan kasan halin mutum sai kaci maganin zama dashi ai ba sai sun gansu ba balle suce ga abinda sukai masu kuma.
Ashe maganan bai kare ba zuwa rana ni dai ina barci sai jin hayaniya nayi ashe yan uwan Zulfa ne suka shigo gidan.
Fada sosai akayi tsakanin su da Hindatu ranan inda suke cewa sun fahinci dai so Hindatu takeyi ta kashe yar zulfa din tun tana ciki.
Sai ita ma hindatun ta buga waya ba a dauki lokaci ba sai ga nata yan uwan sunzo take gida ya koma kamar gidan wasu yan tasha can .
Ban tsaya ba na ja yara har gajiye uwar son jin kwam muka shige na rufo kofan mu muka bar su can suna ta fitina tsakanin su.
Ban san waya buga mai waya ba sai gashi ya kira waya a cikin fada yake magana da anty naji tana fadin ni may kake son nayi a kai tunda ba saurare na zasuyi ba.
Hajiyan daddy ashe sun shigo gidan ita da mama laraba da sauran yan uwa fitina sosai akayi ranan.
Hajiya tazo har kofan mu da kanta zan iya cewa tun shigowa na gidan da sunan aure yaune zuwan ta na biyu gidan tun haihuwar yarinyar da tazo barka sai yau ina ganin kuma maigidan ne ya sa su zuwa gidan.
Jin itace ke buga kofa yasa muka fito amma nai warning din yaran da kada wanda ya fito waje daga cikin su.
Nan muka shiga gaidasu ina duke a bayan anty muka gaidasu a cikin ladabi anty tace hajiya ashe kin shigo gidan.
Tace yo ba dole ba yar nan tunda na fahinci so suke su kashe min da da ran shi ni kuma ba yarda zanyi ba da hakan.
Yaro yana tsaye yana nema maku abin rufin asiri amma ku kullun kuna gida sai bakin fitina ba karewa a kan ku ne faraun din zaman kishi ko may ?
Hajiya sai hakkuri don ko nai magana ba jina suke ba yanzu Rama ce ma ta kaisu asibiti don ba ko ta kan yarinyar da taji ciwo sukeyi ba don hauka.
To kiji fa inji mama Laraba tace ina shekaran jiyan nan ita wanan mara hankali ta hau ta da fitina wai zata taka mata ya da mota kuma da aka bincika ashe zancen ba haka yake ba ma sheri ne kawai irin na kishin hauka.
Hajiyan daddy tace bakinji ba nifa Laraba halin yaran ya isheni ace gida kullun cikin matsala kamar akan su aka fara zama da mata hudu a gida.
Mama Laraba tace ga kwanaki wai gorin haihuwa ma su kaiwa wanan yarinyar amma yau ki duba itace ta taimaka aka kai yar nan asibiti kuma.
Hajiyan daddy tace wanan kishin nasu ai son kaine baka taba jin matsala ya faru ka samay su da gaskiya.
Ita wanan ta tashi a gidan su uwarta ce kawai mata a gidan ubanta shi yasa take da gurin fanin sai ta watsa kowa a gidan ta zauna daga ita sai yarta kawai.
Mama laraba tace yanzu ashe kin gane abinda na dade ina fahintar dake akan wanan yarinyar duk wani makirci a gidan nan itace mai kulla shi.
Ita ko wanan shashan bata da wayo sai ta hau ta zauna bayan tasan cewa ba don Allah take zama da ita ba.
Hajiyan daddy tace ni gaba dayan su duk wace ba zata bawa yarona kwanciyan hankali ba a rayuwan shi ashirye nake da ya sallamay ta nagaji da goyawa karya baya haka.
Duk wacce bata iya zama da kishi hanya a bude yake gare ta ba zan yarda su tsiyata min yaro ina ji ina gani ba haka.
Yanzu ki duba a baya ina jin hauahin wanan yarinyar Saade akan gaskitan ta Zaliha ta hana na fahinci komai a gidan nan don son kai irin nata da yarta ke yar naki da ko wayau bata dashi.
Da zulfa na da wayau yau gidan nan wa yakaita kusanci da yaron nan amma wai da ita ake hada baki a cutawa dan uwanta jifa wanan maganan yau babu dadin sauraro ko kadan.
Daga inda anty take tace ayi hakkuri hajiya anyi kuskure sai dai a gyara kawai.
Cikin bacin rai hajiyan tace idan ma bazasu gyara ba kowa ta fice ta bar mi yarona nagaji da fitan su haka wallahi.
Duk wanan maganan da ake tsaye suke daga kofan shiga part din anty sukeyin shi don basu shiga daga ciki ba.
Sukai muna sallama suka tafi muka rako su har gurin motan su sai faman fada hajiyan daddy keyi tace don hauka kowa ta kwaso yan uwanta a cika gida kamar gidan danbe kuna zubawa mutane shakiyanci haka yaro nacan gurin nema maku abin rufin asiri sam bazan lamunci wanan halin ba a gidan nan.
Mu dai muna tsaye ni dai ban tanka su ba har suka fice hakan ma masu fitan sai da hajiya taga ba kowa a gidan suka ja motar su suka tafi.

********* ********* *********
Tun wanan lokacin na kula da kowa a gidan sha,anin gaban shi yake yi ba mai yi da dan uwa a tsakani wanda nasan na kwana biyu ne kawai mai hali baya fasa halin shi ai.
Na dawo school agajiye na shigo gidan na zauna gun anty muna dan hira take cewa dani gaskiya Rama nikan wai yaya za, ayi na samu wanan maganin da kika kawo min na dada sha.
Don naji dadin shi kwarai wallahi kin ga na daina jin wanan yawan taunan jikin da sauran su gashi yanzu har nai barcina normal har safe.
Nace masha Allahu dama haka ake so kasha magani da zuciya daya batare da ka tsaya kwankwanto a kan sa ba.
Nace niko kinga da shakku ma nakawo maki shi wallahi don ban zaci cewa zaki sha ba anty yadda mutumin ya dinga gidada maganin shi yasa na sayo shi gashi kuma da kudi kalilan akan dubu biyu na karbo shi fa.
Tace kaji ikon Allah ba ni kan ai yadda zan samay shi yanzu naci gaba da shan shi don yai min dadi sosai wallahi.
Waya na ne yai kuka na ciro shi daga hand bag dina da sauri ina kokarin duba wanda ke kirana a lokacin nan.
Daddy ne na gaida shi a cikin mutunci tankar yana a gurin ne tare da mu yake tambayana kina gida ne Rama na amsa mai da eh daddy.
Yace don Allah kije part din Zulfa ki duba min yarinyar nan bata da lafiya wai inji uwar, don na fadawa doctor yace ai maki magana zaki fahinci komai akai.
Ina sauraren shi jikina yai sanyi na dai amsa mai da tau a sanyaye na kashe wayan.
Anty ce ke tambaya na may nene ya faru kuma don ganin yanayi na a sanyayye.
Nace da ita wai baby ce bata da lafiya naje na duba ta a part din su yanzu doctor yace na duba naga may ke damun ta.
Tace to ai sai ki tashi ki tafi tunda yai maki magana kada kiyi laifi kuma gurin shi.
Daga part din anty na wuce zuwa wurin yarinyar dan na dubata na gani na shiga part din gabana yana faduwa don yaushe rabo dana shiga gurin su.
Sallama na biyu kamar babu kowa a part din sai can dana sake wani sallama naji yar aikin ta ta amsa min.
Ta karaso muka gaisa da ita takewa dani lafiya dai ko tambayan ya dan sosa min rai amma na dake ina cewa ina babby din da bata da lafiya din.
Tace tana ciki bari na fada masu ta shige ta barni nan a tsaye ta jima bata fito ba daga ciki can sai gata tana cewa dani wai ki jira tana tafe yanzu .
Na kusa kai minti talatin ina tsaye a inda nake sai ga ta tafito da yarinyar a kafadar ta tana faman wani ya tsunar fuska dagani dole ne ta fito din.
Nace da ita ashe baby ba lafiya kuma haka tace eh gata doctor yace wai na kiraki ban san ko zaki fahinta ba ma yadda take din nan.
Murmushi nayi na karasa zuwa inda taja ta zauna saman kujeran dake kusa da kofan fitowan ta dakin.
Nakai hannuna a saman jikin yarinyar najishi radau ya gashe mata sosai nace subbahanallahi ai fever yai mata yawa na duba bakin ta da idon ta gabana ya fadi.
Miko min ita nan nagani kamar ba zata bani yarinyar ba na dai karbe ta na fara cire mata rigan dake a jikinta a hankali.
Take cewa zafin jikin dashi ta kwana haka na bata magani bai sasauta mata ba har yanzu.
Nace miki min towel da ruwan sanyi wani kallo ta watso min tace may za, ayi dashi kuma nace cikin daurewa zan goge mata jikin ne ta dan samu relief.
Tace a yadda take din nan kuma a daba mata ruwan sanyi a jikin ta nace shine saukin ta a yanzu ai.
A, a gaskiya ki barshi ba zan yarda ba a zuba mata ruwa masu sanyi a jiki yadda take din nan a haka ?
Aiki baka haifa ba ka tausayawa wanda ya haifa tunda ba a jeji na dauki ta ba ko a jejin ne ma sai da nasha wahalan zuwa ai dauko ta din.
Allah ya baki hakkuri nace da ita tare

Please Login or Register in order to submit comment