Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kau taji mari masu zafi har biyu ya sauka mata a fuska yace da ita stupid idiot munafuka kawai kin zaci kowa macucine irin ki idan bani nai mata cikin ba uba wa yai mata cikin ?
Kila kin san sherin da kikayi ne na bazatai ciki dani ba yasa kika fadi hakan babu kunya a gabana don baki da mutunci.
Har lokacin tana dafe da kumatunta inda ta sha mari don bata taba zaton haka ba a gareshi irin yadda ta daure shi tana ganin sai abinda tace yake aikatawa a ganin ta sai yadda ta juya shi yanzu.
Sai gashi taga bazata daga gareshi take kuma gaban ta ya fadu wani tunane yazo mata tace a ranta kodai ya gane dan bakan da tai mashi tsakanin shi da Rahama ne ?
Yaushe har tai sakacin da wanan abin ya karye bata sani ba bayan duk ranan girkin Rahama sai ta haka shi don kada komai ya kasance a tsakanin su.
A dadafe taja kafanta zuwa dakin ta ta fada saman gadon ta wani kuka ne yazo mata a lokaci daya ta jawo wayan ta tana kiran mahaifiyarta cikin tashin hankali tana kuka.
Uwar na dauka tace mama na shiga uku na lalace zulfa da ciki ga kuma Rahama da wani ciki ga shi wani auren zai kara mama wai may ke faruwa ne dani haka a lokaci daya sai ta sake wani kuka mai ban tausayi.
Uwar tace kiyi shiru mana muyi magana na fahinta kina ta faman kuka haka may zan gane har mu san mafita gare mu.
Dole ta tsagaita kukan nata take fadawa uwar a tsanake abinda ke faruwa da ita a gidan sai uwar tace da ita amma hindatu kin kai sakariya wallahi.
Yanzu duk kudin da na kashe kina nufin na kashe su abanza har kika bari wanan shegiyar yarinyar ta sake kumsa wani ciki a gidan nan ke ki na zaune da ya daya tilo kina mata hakon gida ita da mijinta suna fita neman na kansu.
Tace mama na shiga uku na halaka wallahi ga zancen auren nan ba fasawa zaiyi ba don ko wani sati yanzu sai ya shigo kano da wuya ta tsalake sati bai shiga kano ba gun bazawarar tashi.
Uwar tace ni abin ma duk ya daure min kai wallahi ban san ta ina zan fara ba ma wallahi duk bakin sakacinki ne ya jawo muna ganin wanan balain son mijin kike kawai a baki kina nufin a haka har zaki samu ki mallakeshi ke kadai yadda kike so.
Mun samu waccan ta tafi muna murna yanzu saura ita wanan hatsabibiyar yarinyar mai kama da shuuma ashe ita.

Don Allah ayi hakkuri dani bazaku dinga jina ba don matsalar waya da nake dashi sai jefi jefi har zuwa lokacin da Allah zai kawo min mafita na samu waya.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,
86

Abubuwa sun daurewa kowa kai a lokaci daya wai daddy zai auro banker mai aikin a bankin manoma na kasa.
Matar wata yar bariki ce don ba yarinya bace sun taba soyayya da ita don unguwar su daya dashi unguwar iyayyen shi ke nan.
Ita da kanta tai nai tayi bayan rasuwan anty da wasu kwanaki tace tana son ta maye gurbin anty idan ya amince a gidan shi.
Gani take yanzu tafi karfin shi irin yadda ta waye tai kudi yadda yake jin labarinta a gurin Bashir, don haka koda ta bukaci hakan sai ya ce ta bari zaiyi tunane akai.
Amma yawan turo mashi da sako da nuna kulawan ta yasa ya fara mayar da hankalin shi gareta.
Hindatu ta shiga matsanacin damuwa sosai a lokaci daya abu ya taru yai mata yawa a ranta ga kishiyoyi da ciki ga kuma zancen auren da miji zai kara yi.
Sai hauka take ta saci lanban Raliya a wayan shi ta kirata sukai cin mutunci sosai da ita abin ba dadi tsakanin su don sun zagi junan su sosai.
Haka ma Zulfa suke fama da ita acan ba dadi kishi suke nunawa sosai a tsakanin su.
Ranan suna hira da daddy kan abinda hindatu tai mata sai Raliyan ke cewa yanzu saura ita dayar matar taka naji nata kalar kishin a kaina su wa yan nan naji nasu ko.
Daddy yai murmushi yace wai kina nufin Rahama ko wa tace sunan ta ke nan ashe yace da baki sani ba ashe ?
Tace ni ina zan sani tunda ba ruwa na dasu sune suka damu dani da sun sani su kwantar da hankalin su don ni basu gabana sam.
Yace indai Rahama ce kuwa ban tsan mani zaki taba jin bakin taba ga wanan zancen don ni kaina har yau banga wani canjin fuska ba a gunta kan wanan zancen.
Tace man kabar cika baki akan mace yadda sauran sukai min ko ita nasan zata aiwatar da nata don haka itama ina jiranta inji nata kalan kishin a kaina.
Bayan sun gama waya ne take tunane ko dai a cikin matan shi yafi so na ne da gaske kamar yadda take ji din tunda gashi da bakin shi taji ya yabe ni cewa ba na kishin ta in ba so ba may zai sa ya yabeni ni kadai haka dole ne ta fahinci waye wanan yarinyar da kyau ta san ta inda zata fito min da nata halin.

********* ********* *********
Kwana biyu bana jin dadi haka nake ta faman nukurkusa gashi ba dadi tsakanina da hindatu zaman kawai muke na doya da manja ba ruwanta da ni nima haka ba ruwa na da ita irin mugun kishin nan muke gudanarwa a gidan na kowa tashi ta fishe shi.
Daddy ya dawo da rana don sudan yaje yai sati biyu a can yana dawowa ya samay ni cikin wanan halin na rashin lafiya sosai ya dauke ni sai asibiti don a dubani duk dana fada mai ina treatment a gida.
Bai yarda ba sai da mukaje asibitin namu ya kaini an dubani anmin duk abinda ya dace ai min din don doctor Fatima muka samu tana ta min sheri.
Muna hanyan mu na dawowa gida wayan shi yai kara har ya katse bai daga ba ni dai ina lafe a seat din da nake abu ya damay ni.
Can aka kara kira ya dauka yana cewa hanya nake ina driving nakai Rahama asibiti ne ba lafiya nadawo na samay ta a kwance.
Ko cewa tayi ya bani mu gaisa sai naga ya miko min wayan na gane may yake nufi na karba gabana sai faduwa yakeyi.
Muryan ta kawai da naji sai da gabana ya kara faduwa sosai da sallama muka fara take tambayana ya jikin ance banda lafiya nace Alhamdullahi tace Allah ya sauwaka nace da ita amin.
Nagode nace tace babu komai wanan baby yana baki wahala da yawa naga ko yaushe baki jin dadi murmushi nayi mata kawai nace haka yazo min wanan karon kuma.
Tace Allah ya sauwaka nace amin nagode mukai sallama na mika mai wayan sukaci gaba da hiran su har muka kai gida nafita na barshi yana wayan shi.
Duk da naji wani iri a raina ban dai nuna mai komai ba a fili na dake ne kawai na ciki na ciki a raina.
Shi ya biyo ni da maganin lokacin har na kwanta don barci nake ji Alluran da akai min ya fara aiki a jikina ya kawo min maganin da aka bani har dakin nawa don dana rude a mota na bar mashi shi.
Ina kwance yake cewa dani kisha maganin kafin kiyi barci na ce ai zan sha kawai na gyara kwanciya na yace dani tashi mana kisha nai shiru kamar banji shi ba.
Murmushi yayi ta gane raina ne ya baci ya juya ya fita sai gashi ya dawo da goran ruwa mara sanyi ya kawo min.
Yana fadin tashi ga ruwa kisha maganin na mike da kyat shi ya bara min ya hada min yadda aka zana min yabani na sha ina sha na koma na kwanta abina ya fita daga dakin.
Bayan fitan shi ne Aisha ta shigo da Haidar wai yana kuka na ce ta miko min shi ta bani abincin shi in bashi.
Yaron sai kuka yake na rugumay shi a jikina nasan nono yake so ni kuma so nake ma na yayye shi daga nonon.
Kuka yake sosai dole na bashi nonon ya sha san nan aka samu lafiya dashi har yai barci a jikina tare mukai barcin dashi har tsawon wani lokaci.
Dawowan yaran ne yasa muka falka nan suka cika ni da surutu dole na tashi na biye masu muka shiga yadda muka saba duk da ina jin jiki sosai.
Na samu maganin da nasha yai min aiki sai dai bakina ne babu dadi ko kadan a lokacin amma dole na biye masu do ba barina zasuyi ba na huta daga mai kawo kara sai mai neman abu guna haka nake fama da lalurar su koda yaushe idan suna gidan.
Na samu naji sauki na dan fara fita gashi zance tafiya mu sai karasowa yake amma har lokacin ban san may nake ciki ba ni da tafiyan ko zai barni na tafi ban sani ba.
Kwana biyu naji zancen auren shi ba wani motsi haka yasa na dauka kila sun watse ne ni dai ba tambaya zanyi ba balle naji may ake ciki.
Abban Anty baida lafiya wanan dalilin yasa muka shiga kano muka duba shi na zagaya dangin ta dasu suka gansu nan na barsu na shiga kauyen mu a gurguje ban kwana ba na gaida su.
Nake fada masu zancen tafiya na da zanyu zuwa karo ilimi a kasan turawa sunyi murna sosai da jin haka sai dai maigari ne ke tambayana yaran a ina zasu zauna su nace dashi shine dai ban sani ba amma dai duk yadda za, ayi zanyi naga anyi yadda ya dace sunyi min nasihohi yadda ya dace akan auren da sukaji yana batun karawa din.
Ina ta ce keta kara kwantar min da hankali kan zancen auren ta tausa na da kada na yarda na nuna komai na barsu suci kan su tace dani.
Kin dai san ba fasawa zaiyi va tunda ya riga da ya saba da zama da mata hudu ko da bai auri wanan din ba wata zai auro maku kuma dole ku zauna da ita din don dole tunda ra ayin shine kuma zaman shi kukeyi din.
Kedai karamace a cikin su duk ita ma wanan din da zai auro din ance ta girmay maku ga shekaru dukkan ku.
Don haka keda kike karamar su ki zama may hangen nesa a kan su kece zaki zamo may sanin ya kamata kada kice zaki ja da hukuncin ubangiji akan abinda ya halasta akan mazasuyi wanan dama ne da Allah ya basu akan may mu mata baza mu dinga daurewa ga hakan ba mu tsaya a matsayin mu na mata akan su.
Kada ki yarda ki zubar da kimar ki a idon wace zata shigo din wurin nuna kishin ki a fili harta samu daman da zata shigo dake a ran ta.
Haka shine ke kawo baraka a rasa samun zaman lafiya a tsakanin abokan zama gida ya koma kamar gidan da babu tauhidi ha cikin sa.
Tunda inna ta fara min wanan nasihan kaina yana kasa ina hawaye don nasihan nata ya ratsa min jikina sosai don gaskiya inna take fada min ba karya a cikin sa.
Nace inna na gode insha Allahu zaki samay ni yadda kike so da yardan ubangiji ba zaki ji wani abin assha ba daga gare ni.
Mun rabu lafiya dasu duk da a gurguje naje ji nake kamar kada na barsu a ranan mukai masu sallama na barsu lafiya muka dawo kano washe gari muka kama hanyan Abuja ni da yaran da driver daya kawo mu gidan.
Mun iso duk na wahala a hanyya saboda warin petur din motan da yake hawa min kai wanka nayi kawai na samu wuri na kwanta sai barci.
Daddy baya garin yaje calabar wurin wani aiki don haka nake da isasshen hutu nai barci sosai sai dana falka ne na iske miscalled din shi har uku a wayana.
Wanka na yi nai sallah magariba da isha, i na fito ko zan dan iya cin abinci na samu Aisha ce ta girka masu abinda zasuci don ita matar gidan ko kallo bamu isheta ba ma.
Na zauna naci sosai don jelof din yai min dadi ai inda naci nan na kwanta sai barci don duk jikina yana min ciwo sosai.
Mun kai kwana hudu da dawowa ya dawo garin yana zaune da yara sun kewaye shi na fito daga dakina nazo yi mashi sannu da zuwa dutyn yamma zanyi a ranan don haka ban zauba ba na wuce zuwa shiryawa.
Karfe uku bai min a gidan ba nai masu sallama na tafi aikin mu a kwai dadi akwai wahala don idan duty ya zagoyo kan mutum tun dai na dare shine matsala babba a gin mace.
Tun daddy na fadan hakan har ya gaji ya kyale ni tunda yasan haka aikin ya gada dama.
Ga tafiya yazo sai shiri nake don ya yarda da tafiyan nawa kwatsam sai naji zancen wai auren daddy da Raliya za a daura a karshen watan da muke cikin sa.
Haukan kishi kan na gane shi a gun matan daddy don sai da ta zare masu yai muna kaca kaca hardani da ban fitar da nawa a fili ba ya hada yai muna tas ranan.
Yace duk wacce bata iya zama hanya a bude yake mata zata iya tafiyan ta idan bata iyawa.
Nidai ina zaune shiru banyi magana ba har ya gama na mike na shiga dakina na kwanta raina ya baci amma ina gudun in magana in bata batun tafiya na don ni buri na shine naga dai na samu tafiya karo ilimina don shine mafita a gare ni.
Don shi na fahinci ba mace a gaban shi in zaka zauna ka biye mashi babu abin da zaka tsinta banda bacin rai da takaici kawai .
Wanan auren kamar wanda zai auro budurwa yake jin shi don yadda naga yake rawan kafa akan shi.
Sai kuma kyalewan da nayi wai bai mashi dadi ba nan kuma ya samay ni daki ina kwance na dawo aiki na gaji ban dai fara barci ba a lokacin.
Yai tsaye a kaina yana cewa wai ke may kike nufi ne naga ana magana har yau banji may kikace ba kan maganan koke baki da wani shiri ne akan hakan.
Na dago cikin natsuwa nace dashi daddy ni yanzu may zance kuma aure daine kayi niyar yin Allah kuma ya halasta maka yin shi ni wacece da zance wani abu ga hakan.
Ba a aure ni aka auro ni don may zan tsaya ina tayar da jijiya kan abinda bai shafe ni ba ta shigo mana Allah ya kawar da shedan a tsakanin mu kawai.
Shiru yayi yana kallina sai can yace naji amma idan kina da wani magana you are free to talk about it.
Nace ni da ke shirin tafiya daddy har wani shiri zanyi kan hakan sai dai idan Allah ta dawo damu lafiya in naga ina son wani abin sai nayi.
Yace haka kika ce nace shine kawai magana na ubangji ya bamu hakkuri da junar mu kawai yace yayi Allah yasa mu dace nace amin.
Duk yadda yaso yaji bakina kan maganan ban yarda na furta komai ba shine yake wa tantama anya kuwa ma ina son shi kuwa kowa ya tayar da hankali amma ni ko gezau bai taba jin na furta kalman komai ba da anyi magana na kawo mai nawa hujjan ya rasa bakin magana.
Su kan an yi lissafi har sai da yai mamaki may ye wanan haukan haka da suka lissafo mai duk da sabbin kujeru ne a gidan amma sai da hindatu ta lussafo wai a sake wasu kayan gidan dana kitchen.
Ya fada masu gidan ta daban zata zauna amma hakan bai sa ta yarda ba da shi don dai a zauna lafiya yace yaji za, a sake wasu.
Nan kuma suka bullo da cewa basu yarda da zancen zama wuri daban ba ai yaudara ne wanan ta dai zo inda kowa yake a zauna ana ganin komai.
Nan yace wanan kuma tsarin shi ne va nasu ba don haka yadda yake so ke nan haka kuma za, ayi din ba zai kawo ta nan ba inda muke.
Ni dai nawa dasu ido sai daga baya ana gap da daura aure wai hindatu tana neman shiri da amarya akan su hade min kai.
Take cewa wai dama ita ba komai takewa rigima ba sai don kada ta shigo tai masu irin yadda nai masu don yanzu in bani ba daddy baijin kowa a ranshi.
Harda fadawa amarya wallahi ta shirya sosai don mu yan kauye a shirye muke wai har gida naje na shiryo a kan ta don kawai zancen ya ruguje.
Da yake mu mata hankalin mu kadan ne in anzo ga maganan kishi sai ta yarda da shirin su ta hau ta zauna a kai cewan da sukai mata wayon tsiya ne dani shiyasa ba aji na furta komai ba.
Ranan ina kwance sai ga waya da bakon nomba na dauka da sallama na ba ko gaisuwa sai naji ance dani Rahama ko nace eh.
To na kira ne na fada maki aure da yusuf ba fashi a tsakanin mu don dani ya dace bada ku ba don banga wata dafa cikin ku data dace ace tana matsayin matar shi ba.
In kyau kike takama dashi nafiki in kurciya kike takama dashi nafiki in kuma dan aikin likitan da baikai yakawo bane kin san nafiki don ni yanzu kiris ya rage na zama manager.
Zataci gaba nace to Allah ya taimaka ni bani takama da komai sai Allah da manzon shi dama ba sai kin fadi ba dake din ya dace don ni bakowa bace sai boyar Allah mai tsoron shi kuma diyar tallakawan kauye don haka kiyi hakkuri idan ma wani abin kikaji nayi maki har kike wanan magana.
Tace ke rufa min baki munafuka kawai kina wani simi simi kamar ta kwarai dake sai dai ki mashi shida kika shanye amma bani ba.
Kashe wayan nayi don ban iya ci gaba da sauraren wanan kalamin nata Aisha na daga gefe na duk abinda take fadi tanaji tace dani anty amma matar nan bata da hankali ne ko ?
Nace da hankalinta Aisha hakan wai shine kishi ni bata gabana don nasan inda na aje ta tun farko matsalana daya shine shi daddy din ya nuna min wani abu.
Amma tunda bai nuna min ba kin ga may zai damay ni da haukan ta bakina kawai take son ji kuma batajin shi indai nice.
Ban nuna mai komai ba don ban fada mai ba ita da bakin ta da hira yai mata dadi take fada mai ai ta kirani ta zageni don taji abinda nake shiryawa a kan ta.
Sai ranshi ya baci ya kashe wayan dip tai kiran duniya yaki dauka na shigo dakin bayan sun gama wayan.
Yabini da ido a zaton shi zan fito mai da zancen sai yaga har nagama yi mai komai daya dace na samu wuri na kwanta bance dashi komai ba.
Bayan na kwanta sai naji yace dani Rahama na amsa da naam yace Raliya ta kiraki ne sai nai murmushi kawai bance dashi komai ba.
Yace tambayan ki nayi ta kiraki ko bata kiraki ba kuma yaya kukayi da ita din data kiraki din.
Nace ta kirani daddy yace yaya kukayi nace kawai magana ta fada min nace da ita kuma nagode shike nan.
Bazaki fada min abinda ta fada ba ke nan nace daddy ba komai bane ai sai neman baki a yadda na dauki maganan don tace ga abinda nai mata kuma.
Sai naji ya rungumoni yana sauke ajitan zuciya yace ba zan dauki wanan halin ba na fada mata tun farko kuma wallahi sai ta fada min da maganan ya fito harta samu nombanki ta kiraki.
Nace daddy indon ta nice kada ka dauki maganan da zafi abinda aka fada mata akaina ne tai amfani dashi ba tare da ta gani ba.
Yai shiru ya fara bin lafiyan jikina ni ba ma wani dadin kimai nake ji ba har yayi ya gama mukai barci.
Washegari tayi kira harta gaji yaki daukan wayan abu wasa wasa taga zance nadon baci a tsakanin su haka yasa ta shirya taje gidan mahaifan shi takai karan shi gun su hajiya.
Nan hajiyan da ake jikawa ko yaushe ta kirashi tana fada dashi wai zai watsa masu kasa a ido sai da yaga lokaci ya gabato shine zai masu hakan.
Yace hajiya idan ba ta fada min wanda ya fada mata maganan nan ba wallahi sai dai mu watse sai ta fada min wanda ya bata nomban Rahama da har zata kira min mata taci mata mutunci.
Ahaka take son na sata cikin iyalina gashi tun bata shigo ba sun fara fitina dakowa gaea dai ayi hakkuri kowa ya hakkura ba zan daukowa kaina wani fitina ba bayan wanda nake ciki.
Jikin su duk yai sanyi nan hajiyan ta tursasa ta sai da taga da gaske zata rashi ne tace itafa hindatu ce ta kirata ta fada mata kuma ta bata nomban don ta gwada Rahama din ta gani.
Sai bayan sunyi wayan ne amsan data bani ya sa na fara fahintar ko dai shiri ne kawai sukai min gashi yanzu zata ja min tsiya .
Hajiyan tace kin san halin shi idan ya hau don haka kikirashi ki fada mai komai a fahinci juna don kada su ja maki tsiya.
Dole tai mai text akan zata fada mai komai ya dauki wayan ta kirashi tafada mai duk yadda sukayi da hindatun a waya.
Tsuki ya ja ya kashe wayan batare da yai mata magana ba hankalin ta ya kara tashi sosai dashi duk kuma yana mata ne don ta shiga hankalin ta dama don shima ya kamu da son ta.
Ina daki da dare ranan yace nazo fali yana nwman mu na mike dakyat na fita zuwa falon na samu hindatu a zaune ya daure fuskan shi ba rahama a gare shi.
Gabana ya fadi na samu wuri na zauna na gaidasu ya amsa min da kyat gabana ya fadi don ban san may nayi ba kuma.
Can yace hindatu ta amsa a bashe dashi yace may kika fadawa Raliya gamay da Rahama ?
Tace may ta fada maka nace da ita yace abinda kika fadi yanzu zuwa gidan da yarinyar nan tayi duba jikin mahaifin marigayiya shine kikace wai taje gida yin shiri kan auren mu.
Tace ita Raliyan ta fada ma na fada mata hakan yace in kina mussune na kirata ta maimaita da bakin ta.
Tace in tace na fada na fada din karya nai mata wani abin taje yi in ba shi ba can din ko may ye bamu sani ba kaine

Please Login or Register in order to submit comment