Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda tace daga kasan bargu na kayanji.

********* ********* *********
Ranan dai nace bari na kira anty mu gaisa don kwana biyu ban kira ba bata kirani ba kuma dama dai nice mai kira din ba ita ba.
Ga mamakina sai bata dade ba ta dauki wayan na fara gaida ita tare da tambayanta lafiyan yaranta.
Mun dauki lokaci muna dan hira wanda duk akan yaran ta ne mukayi shi normal ba wani matsala a ranan haka yasa bayan mun gama wayan naiwa Allah godiya kan hakan.
Tun wanan lokacin nakan dan kira wayan ta mu gaisa tunda ta rage yawan daure min da takeyi a baya gashi har zata tambayi lafiyan baba wani lokacin abinda a baya batayi.
Abinda ban sani ba yanzu ta fahinci zama dani ba karamin rana ne gareta ba don barina yasa ta fahinci cewa ni ba kishi nake da ita ba sai taimako amma ta biyewa son zuciya tana musguna min haka.
Gashi tsakanin su duk da miji baigida kullun da irin matsalan da zai bullo a tsakanin su sai iyayye sunzo sun shiga ga maganan.
Don raini dama sun riga da sun raina tako tun baya wanda ba komai yaja mata haka ba sai son kai da suka fahinci tun farko tana dashi ashe ?
Ga gori dan abu kadan zasu rufe idon su suyi mata gori akaina kuma su zageta fes shikuma mijin dake goya mata baya yanzu yafita zancen ta .
Shiyasa taga ta shirya da Rahama kila zai kawo mata saukin zaman doya da manjan da ke tsakanin su tunda dama shine matsalan nasu.
Haka yasa take kokatin ganin ta taushi zuciyar ta akan kishina da take ji a zuciyar ta ko za,ta samu sauki a rayunta.
Ban dai yarda na sake sosai da ita ba kamar baya don bana fada mata komai na sirin daya shafe ni yadda muke da ita a baya can.
Koda yaran ne suka bulstiye mata zata kirani ta fada min nai masu magana kuma suji tundai ma Amira dake yawan dauko mata magana a gidan yanzu.
Nakan wa yarinyar magans maikama da Nasiha a cikin hikima kuma ta fahinci magana na ta bar abinda takeyi din.
Cikin jikina ya girma yanzu sosai don har ya fito watan shi bakwai da kwanaki haka nake ta fama dashi ni kadai nake kunshe da abina ba wanda ya san da shi bani ma fatan wani yazo daga fannin daddy har ya fahici hakan.
Shima muna waya dashi amma ban taba sanar dashi komai ba akancikin don haka baisan dashi ba tare dani sai dai nasan ranan da zai gani da akwai rikici kan gaskiya ban damu ba an dai riga da anyi din ko.
Ya bugo waya zai dawo cikin wani sati don watan shi uku acan da kwanaki kenan baya kasan sai da yaga komai da suke so ya kammalu masu shine zai dawo gida.
Naso bashi sakon kayan baby amma kuma may zance dashi ga hakan sai kawai nashiru sai yazo ya ganewa idon shi zai san yadda yayi ai da hakan.
Anty da kanta ke kokarin sanar dashi shiryawan mu da ni da ita sai dai idan tai magana a waya yayi murmushi don yasan tuban mata na mazuru ne dan abu kadan zai sa ta koma wa halinta tunda ya fahinci abin a jini yake muna.
Sai dai ya fahinci tunda muke ni baitaba jin nai mai wani korafi mara dadi akan kowacen su ba bani kuma sukan su gaban shi koda kuwa sun bata min rai na.

********* ********* *********
Da yamma ya dawo ya iso gida da biyar da wani abu lokacin ina daki ina kara shirya duk da dogon riga ne a jikina light blue na daura dan kwalin shi a kaina sai cikin daya turo a jikin rigan yai tsiri dashi.
Nafito da fara, a na don na manta da baisan da zancen cikin ba ni da murna na samu yaran gidan suna taron shi nace daga kofan da nake fitowa din da daddy oyoyo.
Ido ya zuba min bai iya karba oyoyon danai mashi ba a lokacin sai idon da ya zuba min har na karso inda yake tsaye sagale da corth din rigan shi a kafadan shi.
Da hannu ya daga yace dani dakata Rahama da sauri naja wuri daya na tsaya kamar yadda yace min din.
Kallona yake cikin mamaki idon shi akan cikin nawa, yace Rahama ciki ne dake komay nake gani haka ajukin ki ne wai ?
Murmushi nayi nace kai wallahi har naji tsoro na dauka wani abune wallahi, ina karsowa inda yake a tsaye sai su Aisha suka fara sulalewa falon.
Ya kara kallo na yace yaushe har kikai ciki a gidan nan har ya girma haka ban sani ba Rahama ?
Nace daddy wani ciki kuma kai mutum bai kiba sai kace ciki kuma humm naji yace kawai tare da kara bina da kallon mamaki ?
Boye min kuma kikeyi ko may Rahama da har ciki zai zauna a jikin ki yakai haka ni uban cikin ban sani ba saboda may zaki boye min wanan irin maganan da ba karami ba haka.
Na rugumay shi ina sauke ajiyan zuciyan ganin shi ya dan dafa bayana tare da kai hannun shi ga cikin take kuwa dan cikin yai wani bul bul daga cikin riga.
Yace tabbas kuwa cikine dake Rahama, don gashi naji motsin shi yanzu ai.
Na sake shi ina fadin daddy sannu da hanya yaya aiki yaya jama, a kuma da sanyi ?
Yana dai tsaye yana kallona daga inda yake bai motsa ba yace abin ya daure min kai wallahi yadda har mace zatai ciki yai girma haka ace wai ban sani ba don may zakiyi min hakane wai ?
Zama nayi don banda jimirin tsayuwa mai yawa yanzu da kyat na kai zaune ya kara kallona a cikin mamaki.
Ganin baida niyar zama nace ka zauna mana daddy ka huta tukun kafin muyi wani magana dakai ko.
Yace dani barni a nan tunda banda wani amfani a gunki har zaki iya boye min alherin da ubangiji yai min haka banyi mai godiya ba.
Nace afuwa yallabai tuba nake nayi kuskure amma may zan fada ma tunda lokacin da zaka gani yayi ko .
Kallon mamaki ya sake min daga haka bai sake magana ba sai ya fara tafiya zuwa part din shi ran shi a bace mai.
Bin bayan shi nayi da kallo daga gurin da nake zaune na sauke ajiyan zuciya bayan naga shigewan shi ciki.
Ban iya tashi ba don tashi wuya yake min sai da na dauki lokaci mai tsawo na mike nabi bayan shi zuwa dakin.
Na samu har ya fito daga wanka ya saka dogon riga mai laushi a jukin shi ko jin nashigo bai sa shi ya juyo inda nake tsaye ba.
Daga inda nake tsaye nake cewa dashi abinci na falo yana jiran ka ya dan juyo tare da zuba min idanuwan shi a kan cikina.
Yace ba yanzu zanci ba sai nayi sallah zan zauna naci abincin nace daddy ko ruwa baka sha ba fa tunda ka dawo yace No ki barshi a koshe nake ai.
Sai banji dadin yadda ya daure din ba na juya don barin dakin cikin jan kafa na da kyat don bani da wani lakkan kwarai yanzu.
Muryan daddy naji yace Rahama may ye dalilin ki na boye min cikin dake a jikin ki, kika ki fada min kina da ciki tsawon lokaci haka ?
May kuma kike nufi da hakan da kikai min kika hana na godewa ubangijina da ya azurta ni da samun karuwa a gidana ?
Shiru nayi ba amsa ya dago yana kallo na ido da ido da sauri na dukar da kaina a kasa cikin jin nauyin shi na rasa may zance dashi din.
Ya sake cewa ba dake nake bane baki jini bane ki may tambayan ki nayi akan wani dalili kikai min hakan ?
A sanyaye nace daddy ni bana nufin komai ga yin hakan da nayi a gare ka na dau yi shiru ne don ban san yadda zan fada ma ba a lokacin ganin ina shayar da yaro dan wata goma bai isa yaye ba.
Amma ni bayan wanan bani da wani manufa akan hakan kuma nayi haka ne don gujewa maganganun mutane akan hakan.
Nace amma don Allah kayi hakkuri tunda ranka ya baci ga yin hakan da nayi din ba da wani manufa naki fadawa kowa ba ni.
Yace ashe baki da hankali ban sani ba Rahama cikine zaki boye har yakai tsawon wanan lokacin kina nukurkusa dashi a jikin ki batare da wani naki ya sani ba ?
Ko kuma kin dauke ni ban san abinda nakeyi bane saboda wani hujja can naki na banza mara dalili,
Ko waye baisan hikimar ubangiji ba idan ya tashi yin ikon shi akan mutum zaki dauki ciki har yakai wanan matsayin kina fama dashi a tare dake kin yi gum idan kika cutu ga hakan da kikayi laifin wa kike tsanmanin za, a gani ga yin hakan.
Shiru nayi mai har ya gama fadan shi nace don Allah daddu kayi hakkuri nasan nayi kuskure babba nima.
Bai min magana ba sai saka kai yayi ya fita daga dakin kawai na dade a wurin da nake a tsaye a cikin damuwa daga baya nabi bayan shi na fito daga dakin nima.
A falo na samay shi zaune yana waya na samu wuri na zauna sai faman wayan shi yake ya nuna baima san ina wurin ba sai baba ne da yazo yana dan jana da hira nake bashi amsa kawai cikin gwalancin shi na yara.
Sai da akai kiran sallah na mike na shiga dakina nai sallah ban fito ba don a gida yai sallah shima na idar da isha,i da shafa,i da wuturi na kara dan gyara jikina na fito falon na zauna.
Tun kan na kai zaune yace dani mikon min abinci nan naci a nan na mike zuwa wurin da abincin yake a table na dauko zuwa inda yake na jera su a gaban shi.
Sai da nagama har ya fara ci na samu wuri a gefen shi na zauna ban dai yi magana ba har lokacin don nasan nayi laifi babba.
Cin abincin shi yake hankali a kwance da gani abincin yai mai dadinci don ya dade yane kewan abincin gida irin haka.
Nan dai na zauna ina amfani da waya na ban bi ta kan shi ba sai can batare da ya kalle ni ba yace dani wata nawa ne cikin naki yanzu yake ?
Shiru nayi tare da dakatar da abinda nakeyi da wayan na dago kai ina kallon shi sai kuma nai saurin dukar da kan nawa a sanyaye nace dashi takwas da kwana ki ke nan yanzu.
Amma gaskiya rashin hankalin ki yai yawa wallahi ashe da sai dai kawai naji haihuwan ki idan na dawo ke nan da ban dawo ba a yanzu ?
Shiru nayi shima ci gaba yayi da cin abinci shi har ya gama ya jawo roban da na aje mai ruwan wanke hannuwan shi yafara wanke wa sai naji ya ce dani.
Amma ki sani wallahi, idan kin sake maimata min irin haka bazaki ji dadin matakin da zan dauka akan ki ba nan gaba.
Saboda wani hujjan ki can na bazan mara gamsuwa zakiyi kokarin cutawa kanki dana tare dake irin haka ?
Abinda yasa kuwa zan bar wanan maganan a yanzu don kawai yanzu na dawo kasan bazan yarda na shiga yan uwa na da bacin rai ba haka.
Na rasa ke wani irin tunane ne akan ki duk wanda zaiyi magana yaje yayi mana abin kunya ne halan gare ki da da uban shi ki cuta muna haka ?
Na sake cewa don Allah daddy kayi hakkuri nayi kuskure na sani nima ka yafe min don Allah yace naji amma gaskiya banji dadin hakan ba wallahi.
Nasan banda gaskiya don haka na lafe ban kara yin wani magana ba nai shiru har ya gama na kwashe kayan abincin zuwa kitchen.
Ko da ya shiga sai da na dauki loiaci na samay shi har ya kwanta a lokacin ko nima kwanciya nayi sai naji ya dan sauke ajiyan zuciya tare da juyowa yana fuskantar inda nake kwance yace.
Ni ban ma san ta ina zan fara gwada babyn nawa ba wanan girman da cikin nan yayi haka duk da nasan ba laifina bane ga hakan.
Yana kewar matan shi dole ya manta da bacin rai da ya tarar a gidan ya biya bukatan shi sai dai ba yadda yaso yi din ba.
Washegari gaba daya jikina ya dipge min hakana na daure na fito na shirya mai abin karya tare da namu gaba daya da taimakon Aisha na samu na gama komai na jera mai bai dade ba yafito daga dakin ya ci ya fice daga gidan.
Bayan fitan shi wanka nayi na samu wuri na kwanta sai barcin wahala ya kwashe ni ban falkaba sai gab da sallah azahar na tashi inda na samu har Aisha ta hada abincin rana .
Naji dadin hakan don ta taimaka min kwarai da gaske saboda koda idona biyu ma bazan iya komai ba yadda nake jin jikina din.
Bai dawo gida ba sai bayan karfe biyar na yamma nan ya zauna yaci abincin kafin ya tashi sai ga yaron shi sani nan garin ya na shigowa da kayayyakin abinci nau,i, nau,i.
Komai na amfanin gida sai da ya sayo muna yakuma ce na duba idan da akwai wani abinda nake so wanda ba a sayo ba din a ciki don kada na tashi nace komai an sayo.
A dan kwana biyun da daddy ya dawo ya fahinci bana cin komai sai kunu na koko da nakan zauna nasha sai na koshi, .
Duk lokacin daya shigo zai ganni da cup a hannu yace may ye wanan sai nace dashi koko ne nake sha ranan dai yace dani wai Rahama ban gane wanan yawan shan kunun da kike ko yaushe ba ko so kike kijawa kan ki wani matsala ne kuma?
May na rasa a gidan nan da zaki zauna dare da rana baki da aiki sai shan koko akai akai haka sale salin kija min zagi ko ki haifi da da rama ace ba, a baki kulawa ko may ?
Na dago kai daga inda nake zaune ina fitar da zufa na dan kalle shi a hankali nace daddy ba wai don wani abu nake yawan shan koko ba kawai shine zan sha na zauna lafiya.
Yace to na fada maki bana so ki dinga hada tea ko dan abinci mara nauyi mana kina ci bana son yawan shan kokon nan ni.
Don ba zan yarda ki cutar min da abinda ke acikin ki ba in ke baki damu da kan ki bane haka ?
Mamaki ne ya kamani kaman wanda bai san lalurar ciki ba ko may yanzu ne ma nake dan iya shan kunun a baya sai ruwan bakin liptop nake sha kawai ai.
Yagama fadan shi ya shige daki banyi magana ba may ma zance ina a wanan stage din har zai tsaya min fada irin haka.
Tun wanan lokacin idan zan sha sai dai na shige can dakina nasha na fito waje kamar ban sha komai ba.
Sai da yai sati uku ya shirya zuwa kano inda kafin nan ya sha korafi sosai a gun matan shi inda kafin nan yasha korafi sunyi fada sosai har a waya sai suke ganin ya makale ne a guri na kawai muna jin dadin mu a Abuja.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,
74

Subbahanallahi kowa da abinda yake fadi akan wanan matsalan wasu suga laifina wasu kuma gaba dayan mu suke zagi wasu kuma ita hindatun ce suke zagi.
Alokaci daya abin duniya ya taru yai min yawa akai ni kadai duk da ba a gari daya muke ba haka bai sa na tsira ba daga zargin mutanen duniya.
Tun faruwan wanan abin gaba daya ya sauya ya koma wani zaki mafadaci da kowa a gidan shi haka yasa kowa ya shiga hankalin shi dashi.
Ni da a kullun nake kusa dashi abin ya shafe ni don ya dauki zafi da kowa bai magana na tsawon lokaci da kowa sai idan shi yaga daman yin hakan zai dan zauna dasu mama a falo su danyi hira kafin ya fita.
Waya ko ko yaushe hindatu cikin bugowa take tun ban fahinci ita bace har nazo na gane cewa itace take yawan bugo mai wayan ako wani lokaci.
Na dai san baifi ban hakkuri takeyi ba haka muke mata sai mun bata da gangan sai mu dawo daga baya kuma muna bin muna ban hakkuri da dodofa a dawo damu yanzu wanan abin ina ranan shi ?
Lokacin da take cin mutunci ta manta cewa ba a hannunta auren yake ba kuma iya hakkuri dai daddy yana dashi akan iyalin shi don ba duk maza bane zasu iya hakkurin da yake kullun ya dawo gida daga wurin neman hakkin shi da irin fitinan da zai samu na jiran shi a cikin iyalin shi.
Don ma yana namijin duniya ne ya san yadda zaibi da ko wace mace a zauna lafiya da ita.
Yau ba fita kasancewa weekend ne yana gida yana barci har goma da wani abu na safe nima barci na nayi sosai na tashi nai wanka na shirya nafito ganin rana ya soma yi bai karya ba.
Sai na fita zuwa dakin shi na samay shi har lokacin kwance yana barci kada na damay shi yasa na juya zan bar dakin.
Rahama naji yace nace naam daddy na juyo zuwa inda yake a kwance tsakiyan gado, na karaso gap dashi nace dashi antashi lafiya yace Alhamdullahi yaya ku ka kwana nace lafiya kalau, yace kin shigo kuma zaki fita mana ?
Nace eh daddy dama naga rana yayi ne shine nazo na duba naga baka karya ba har yanzu sai kuma na samu kana barci shine zan fita.
Yace yanzu nake son na tashi dama nai wanka aina dan huta yau don dama ina da gajiya nace haka na gani shiyasa zan fita na barka ka huta din.
Yace ai kin barni na huta din don ba a damay ni ba yace barin yi wanka na fito na ce bari hada ma ruwan wankan kafin ka tashi.
Yace barshi kawai a yadda kike din nan ai gwara ki huta barshi kawai zan hada idan na shiga ai.
Nai murmushi nace ai zan iya hada ruwa ba wani aiki bane ai yace gashi kinyi kyau yau kamar ba mai tsohon ciki ba dake.
Na dan mai kallon mai wata irin tsiga nace daddy yau kuma zolaya ce abin yadda na koma wata bushuma dani haka kamar wata uwar mata komai ya bude min haka dani ?
Yace yana dagowa kece ke ganin haka ni dai ban gani ba nace gadai masu kamar kwarai can a kano suda basuyi nauyi ba ka barsu.
Ya mike zaune yana cewa ai ba sai kin gwada min su ba keda ke gabana yanzu nake magana ba wa yanda basu kusa dani ba.
Cikin ya hanaki daukan dawainiyan kato kama nane ko may da zakice wai duk kin koma wata kala dake to ni dai ban gani ba ke kika fada yanzu don ni wata yar shar nake gani a gabana cikin bai sa kin jagule ba tunda bai hanaki yi min kwaliya in gani ba.
Nace cikin jin kunya kai haba dai daddy ina kwalliya a nan haka kamar wata bosa dani.
Dariya yai min ya mike tsaye yace barin shiga wankan ko su mama bamu gaisa ba yau dasu don ban fita ba.
Sai ya kamoni zuwa jikin shi yace ko za a taimaka min ne na dan yamutsa wanan kwalliyan da akai min ?
Da sauri na dago kai na na kalle shi nace don Allah daddy rufa min asiri yadda nake din nan ina zan iya daukan double share jiya da yau haka.
Yace kai wanan dai akwai ragguwa wallahi ko ba cikin ma ai haka zakice dani niko gani da bukata ga mace nace ai Allah yabaka su yadda zaka shanye kwadan ka.
Murmushi yayi yace baki ganewa ne ke don haka abar zancen tunda ba a bari na kara more weekend dina.
Ya shige bandaki ni kuma na juya na fice daga dakin kafin yafito a falo na samu su mama zaune na gaida su nan mama ke cewa nace yau ko asubanci dan nan yayi ya fita ne bamu gaisa ba da shi.
Nace ya na nan mama bai fita yanzu naje na tadashi ya karya rana yayi bai karya ba yau weekend ne bai zuwa aiki sai in ya kama yakan fita irin ranan yau din.
Tace bari ai maza na kokari wallahi mutum ba hutu ko yaushe kamar agogo wurin neman na kai ace kuma wanda ke gida a zaune shine mai fitina haka.
Nasan inda maganan ta ya dosa sai nai saurin kawar da zancen don ban son aci gaba da yin shi ba dadi magana daya kullun.
Nace mama kun karya kuwa ko akwai abinda za, a kara makune wanda kuke son ci ayi maku shi yanzu.
Tace a, a a haba dai ai Alhamdullahi munci mun sha mun gode wallahi ni zaman nan ma baka aikin komai har ya soma isata wallahi.
Ka saba da yi wanan yi wancan a gidan ka nan ko kana zaune wuri daya ba baki ba fari sai kallo tv da cin abinci kawai shine aikin mutum.
Nai murmushi nakai zaune ina fadin to mama Allah ya kaiki ga hutu danki ya kawo karfi ai sai a godewa Allah dama haka ko wata uwa ke fatan gani ga zurianta hutu daga tsatonta.
Muna ta hira dasu suna bani dariya daddy ya fito yau kanan kaya ya saka a jikin shi ida ya nuna dan tunbin girma daya fara ajewa a jikin shi.
Nan ya karaso suka fara gaisawa dasu mama nacce akawo abincin nan ne ko a table zakaci yace batin tafi can naci yacewa Attu tsohuwa yau sai ki shirya muje yawo ko naga baki saba zama wuri daya ba haka.
Tace rufa min asiri barni anan wanan gari naku ai sai ku dake cikin sa nikan ai in kaga fitana a gidan nan gida zan koma.
Yace a, a kada muyi haka dake mana idan kin koma dan tsohon mijin ki ya tambaye ki labarin abuja may zakice dashi kuma ?
Yau kan zan fita daku kuga gari son ita wanan yanzu sai a hankali tayi nauyi da yawa balle ta kaiku wani wuri.
Attu dai ra nace babu inda zata nace aiba ke kadai bace ga mama gashi kije kiga gari don Allah ko ki koma mijin ki yaga an wayar dake sai akasa dariya daddy ya mike nufi gurin da abinci yake.
Yana tsaka da cin abinci mukaji wayan shi yai kara

Please Login or Register in order to submit comment