Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na dago kaina naga dai a zahiri mu take kallo sai dai da alama tayi zurifi ga tunane ne .
Nace Anty bakiji bane sai naji ta sauke ajiyan zuciya tace may kikace ne ?
Nace kinha Jinior da wanan hannun nashi wai sai ya saka min abinci a bakina kuma make shi zanyi.
Kallo mai kama dana hararan wasa tai min tace kin taba jin mata ta doki mijin ta bayan yana son kuyi soyayya dashi.
Bata kaji dama ai kaine angon kai ya dace kana bata abinci har ta koshi kamar yaji yako yi ksina wai sai ya saka min abaki har kasa muka kai sauran yaran sukayo kaina suka tayashi tura min abincin a baki su anty nata muna dariya.
Ina cikin dariya naji tace Rama wanan kayan sun matukar karban jikin ki wallahi wanan ai idan angon ki ya ganki haka baza mu gane kan shi ba kuma.
Da sauri cikin kunya na daga yaron a jikina na jawo hijjab dina dake gefe ina sakawa tace yau ga tsiya may zaki wani rufe jiki kuma?
Bari kiji haka nake so idan besty na gari ki dinga yi mai kwaliya da kaya matsatsu yana jin dadi sosai a ranshi, mune dai bama yi mashi kwalliya yadda yake son gani.
Nace anty aiko kina kwalliya mana tundai idan ma kece da girki tace ni har yaushe nake wani duty abin daga bara sai bana.
Da dare ta sakani gaba wai dole a part dina zan kwana har da kuka nayi mata amma tai kemaymay sai da taga na shiga ta saka suka rufo part din su suka barni ni kadai a part din.
Haka na kwanta ga tsoro ga kuma tunane barkatai da nake ni daya kamar manya har barci ya dauke ni.
Da safe mun tashi da wuri kamar jiya hamza driver ne ya dauke ni zuwa school ban dawo sai yama yau biyar na dawo gidan.
Na shiga muna zaune da anty a falo muna hira saiga yar aikin Zulfa da gudun ta ta fado part din hankali a tashe take magana.
Wai anty tazo uwar dakin ta zata mutu anty tace dani taso mu tafi da sauri muka bi bayan yar aikin zulfa din.
Kwance take shamay shamay kamar bats motsi muka karasa inda take kwancen hindatu na tsaye tana waya hankalin ta a kwance.
Ban san lokacin dana duka da sauri ba na tallabo hannun ta ba tare dan saurarawa na dan lokaci ta bude idon ta ta sauke a kaina zatai magana na nuna mata da hannu irin na yara da shiii sai tai shiru.
Nace da ita rufe idon ki ki dan shaki numfashi a hankali sai ki sauke har sau uku bataki ba tayi abinda nace da ita.
Duk suna tsaye suna kallon mu bayan tayi kamar minti daya sai tai wani irin ajiyan zuciya a hankali.
Nace jini yana zuba maki ne a kasan ki ?
Ina ruwan ki da wanan tambayan kuma inji Hindatu cikin fushi.
Kibari mana tayi aikin ta mugani tunda shi take karantawa ai ban bi ta kanta ba na sake maimaita tambaya gare ta.
Tace yau da safe dana tashi na danga sign din jini amma ba sosai ba na sa hannuna ta bayan ta nace dago kadsn mu gani please ?
Tana dagawa ashe kwance take cikin jini na juya kan su cikin tashin hankali ina fadin yanzu tana cikin wanan halin ita bata san inda take ba ku kuma dake tare da ita baku taimaka mata ba.
To Docter yi muna fada na juya gurin anty nace cikin ne a jikin ta kuma yana barazanan fita ne a ko wani lokaci iyanzu.
Gaba daya hankalin su ya tashi a dakin zama nayi da kyau har numfsshin tana shiga nawa ina dan shafa mata daidai kugunta a hankali kamar ina mata massage din shi.
Hindatu na fadin a kira likita yazo da sauri can kuma tace bani guri na daga ta mu tafi asibiti kawai.
Cikin wani murya nace da ita kada ki soma ki daga ta bata a kwance tukun a wurin.
Nace anty ta dago ido ta dan kalleni lokacin ne uwarta da yarta suka shigo dakin a gigice suke suma.
Nace daure ki dan kara shakan iska irin na dazun kinji ta sake maimaitawa a hankali yadda nace tayi din.
Yanzu haka zamu zauna da ita ana wanan shirmay haka ai mu tafi asibiti kawai antyna tace da Hindatu ai wanan ba shirmay take mata ba.
Nace idan mun daga ta a haka jini zai iya balle mata ko wani lokaci don akwai abinda tasha wanda ke barazana a cikin nata.
Hankalin su ya kara tashi cikin hikima irin na likotoci na samu stress din ya dan lafa mata a hankali numfashin ta ya dawo daidai nace wanda zaiyi tulin ya ja a hankali haka kuma idan zaku dauketa ne ku daga ta a hankali.
Sai dai da zakubi tanawa a bari likitan yazo gida ko luma na rubuta magani a sayo ai mata allura.
Sai duk sukace adai kira likitan zaifi sun kira likita yace bai samun zuwa adai kawota asibiti na nuna masu yadda zasu kamata zuwa bakin mota.
Mama Zulai tajuyo gareni tace don Allah ki taimaka mu tafi dake ina ga zai fi ai na juya gurin anty tace ga hijjab saka ku tafi Allah ya bata lafiya muma gamu nan tafe yanzu.
Filo na aza mata na tare jinin yadda maranta ba zai motsa ba ko kadan muna tafe ina mata sannu anty har muka shiga asibitin yatta ke jan motan.
Muna shiga na kamata yadda ya dace bamu sha wuya ba nai masu bayanin komai likita na dubata abinda na fadi shiya fada muna nace dashi ga alluran da za, ai mata zaifi sauki tunda da alaman akwai poissing a jikin ta ai.
Sai bina suke da kallo yace yaya akayi har akakai wanan lokacin abin bai fita jikin ta ba na fada mai taimakon da aka bata tun agida.
Yace good hakan na da kyau gado aka bata tare da mata allurai ta samu barci kuma Alhamdullahi jinin ya bar zuba.
Nace da mutane don Allah ayi hakkuri a dan fita daga waje a barta ta dan samu hutu please.
Muna fita naji mama Zulai na fadin may Zulfa tasha cikin jikin ta ke son fita ni dai nace dasu mama zan tafi gida Allah ya bata lafiya.
Muka juya nida Anty bamu tsaya ba don asibitin ya fara cika da yan uwanta a lokacin sosai.
Muna hanya Anty tace dani Rama kikace abu tasha cikin ke son fita nace gaskiya akwai wani abuda tasha ya kawo hakan gareta.
Tace dani amma kuma yadda Zulfa ke son ciki haka har ta tsaya shan abu don cikin ta ya zuba kuma ?
Wayan maihudan ne ta shigo mata don haka taci gaba dayi mai bayani a kan komai yace gashi nan dawowa ga gobe idan Allah ya kaimu.
Tace Allah ya kawo ka lafiya suka kashe wayan nikan a bangarene gabana naji ya fadi ras ras don ban ki ma ace yai ta zama ba acan har abada a lokacin.
Sallah da ban samu yi ba nayi tare da jero shafa,i da wuturi gajiya da kasala ke damuna a lokaci guda na samu guri na dan kwanta ashe anty ta shigo ta samu ina barci taja min kofa ta fice dakin.
Washe gari na dan makara da sauri na mike nai sallah na jero adduoi na namike na nufi part din Anty.
Na samu Gajiye ta hadawa yan makaranta abinci na taimaka muka shirya su nima nakoma na shirya na nufi gurin anty na sallamay ta.
Bayan mun gaisa take cewa dani jiya ai nashiga muyi magana na samu kin yi barci nace nima koda na falka naga biyu na dare kuma an rufe min kofana.
Tace ki saba da rufe kofan ki Rama gidan nan sai a hankali wai kin san kuwa tun jiya ina tunane akan matsalan Zulfa.
Nifa sai nake zargin da wata a kasa fa Rama don a sanina dai Zulfa bazata sha abinda cikin jikin ta zai fita ba wacce ke nema ido rufe Allah ya bata.
Allah ya sauwaka nace ina kokarin wucewa naji tace yau dai kin san maigidan zai dawo ina fatan kin shirya taron shi dai ko ?
Nace anty wani taro kuma gaku tace may kike nufi wai bani fa son shirmay wallahi kada ki dade ki dawo da wuri ki shirya mai abinci.
Fuskanta babu alaman wasa ga maganan ta tace naso kikara shiryawa kafin ya dawo gashi lokaci ya dan kure muna wallahi.
Amma dai duk da haka zan san abinda za, ayi akai nima zanyi wanka na tafi asibiti na dubo su can.
Idan zaku dawo sai Hamza ya biyo dake ki duba su a can nace to anty na fice abina ban tsaya ba .
Tunanen duniya ranan nayi shi kafin mu shiga school sai dai muna zuwa na manta da komai nashiga harkana kawai.
Sai Four na kira Hamza driver yazo ya daukeni muka fara zuwa asibiti duba zulfa .
Asibitin makil yake da yan uwan ta da ma wasu dangin mijin su gaba daya idanuwan su caa akaina ni dai na gaidasu na shige gurin ta.
Ina shiga cikin dakin ma mutane ne na gaidasu tare da karasawa bakin gafon nace sannu anty yaya jikin naki ?
Cikin wani ya mutse fuska tace dani da sauki baki shigo ba tun safe sai yanzu ?
Nace yanzun ma daga school nake don naji likita yace kina bukatan hutu yasa banzo ba da safe kada na damay ki.
Nace jinin dai ya tsaya ko ya daina zuwa kafin ta bani amsa wata yarta tace aniyar maishi tabishi mukan ai Alhamdullahi tunda cikin bai zube ba ai.
Shiru nayi mai maganan taci gaba da sake bakaken magana ina tsaye ina sauraren ta harda cewa haihuwa daine sai anga Zulfa nayi shi gida Yusuf kamar ko wace mace don sai tai dozen da yarda Allah.
Nace Allah yasa sukace amin mama zulai data shigo take cewa Rahama kece tafe ai tun safe likita ya tambaye ki yace ba karamin taimakawa kikayi tun a gida da cikin ya zube ai.
Nace cikin murmushi mama ai ina dubawa nasan magani ne tasha a lokacin idan munce zamu dagata haka zai ba abin dama samun hanya fita shiyasa na hana a dagota na dan yi mata dubara yadda yadace ai mata.
Don na sani badon haka ba gaskiya cikin zai fita kuma ta samu matsala ita ma sai dai abin da mamaki don kwayan da tasha mai karfine sosai adai kiyayye gaba don Allah.
Zulfa tace dani Rahama ban sha kwaya ba don likitama haka yace dani nace zaki iya tuna abinda kika sha awa daya daya shude ko kafin lokacin?
Sai tai shiru tana tunane nace koma may kika sha shine sanafin faruwan wanan abin haka gare ki nai masu sallama ban kai ga fita ba naji wata na fadin au itace ta taimaka a gidan gako Asiya har rana sake mata magana.
Zulfa tace yarinyar ta taimakeni ai mama sosai don badon taba gaskiya ban san inda nake ba a lokacin zuwan tane da tabani taimako har na gabe gun da nake a dakin.
Gida na nufa na samu har gajiye ta dora girki ina shiga anty tace Gajiye bar mata tayi tunda ta dawo yanzu.
Hijjab kawai na cire na juyawa gurinta nace anty may za, a girka ne ta dago tare da tsura min ido tace yau naji ikon Allah ga Rama .
Ke da mijinki zaki tsaya tambayana may zaki girka kuma ai dabara ya saura gare ki yanzu.
Rugumay ta nayi cikin shagwaba yadda na saba nace don Allah Anty may za, a girka maku please ?
Tace kin dai san anty tin tuwo yake so shi don haka sai kiyi yadda ya dace dashi ko abinda kika san zai burge ku.
Ni dai jiki ba kuzari na shiga kitchen din tunda tace anything tuwo don haka nai tuwon semo da miyan yauki sai jan miya danayi masu daban na hada zobo mai kauri na saka a fridge na hada ferfesun kifi danye yaji kayan kamshi kafin magariba na hada komai nace da ita na hada.
Zan je nayi sallah don gaba daya yanzu ta hanani zama part din ta kamar kullun, amma hakan bai sa na bari ba din.
Wanka nayi na dauko wani riga na saka robane rigan zai iya matse mutum daidai size din jikin ka yana da ado a gaban shi sosai na sa na rufo kofa bayan na gama komai na nufi gurin ta.
Abinci na samu tana ci tana ganina tace Rama ashe kin iya keta ni dai baki taba min tuwo hakan nan ba duk zaman ki dani.
Fada mata nayi a jiki ina dariya nace kai anty ashe kin gane baiyi dadi ba ke nan bake kikace nayi tuwo ba shine niko nai maku shi haka.
Tace wai kina nufin keta kikayi dama ko may to wallahi yayi dadi sosai tambayi gajiye kiji leda nawa nacinye yanzu.
Gajiye tace wallahi na biyu ke nan take ci tana zuba santi nima dariya kika samu ina mata nace oya Nasir zo ka zauna aci abinci kada kai barci.
Yace little mumm kaina ke ciwo a razane na juya gurin anty nace anbashi magani anty ?
Tace wa yasani in ba yanzu da yake fada maki ba ke ne dai zaifadawa dama don shi bai yarda da kowa ba ai.
Mikewa nayi na shiga daki na dauko magani sam baison shan magani da kyat na samu yasha magani sai mukaji hadari ya taso alaman akwai hadari ana son yin ruwa.
Yaron yana lafe a jikina ina lalashin shi sam bamu ji dirin mota ba balle mu san shigowan daddy gidan.
Sai ganin shi kawai mukayi a tsakiyan falo suit ne a jikin shi fari da wandon shi ya saka hannun shi daya ga aljihun wandon shi.
Besty ashe ka iso yanzu naji hadari nake tunanen ko kana ina haka by this time ?
Yace ana magariba na shigo na tafi asibiti ne dubo maijikin .
Nan muka shiga gaidashi da dawowa ga kamshin turaren shi duk ya cika muna hanci gavana sai wani mugun faduwa yakeyi faf, faf,faf.
Cin yar siririyar murya nace daddy sannu da dawowa kamar wanda baison amsa gaisuwan ya amsa min tare da dago kai ya dube mu ina zaune rashe rashe a saman kafet Nasir ne kwance saman jikina ya lafe bayan ya sha magani.
Kallon Nasir yake don bai tare shi yadda ya saba taron shi ba yace da yaron my friend my kuma ya samay ka kai ?
Anty tace cikin tabe baki gashi nan ai ga uwar shi yanzu ne ma da yaga ta shigo yake cewa da ita wai kan shi ke ciwo.
Da sauri tun bata karasaba yace subbahanallahi tare da nufo inda muke ya rage tsawon shi dukowan da yayi a gabana gurin yaton yasa faduwan gabana ya kara tsanan ta sosai.
A hankali nake kokarin gyara wuyan rigan dake a jikina yadda ya dan fado kirjina kusan a fili yake lokacin.
Magana yake wa yaton kasa kasa suke maganan su ya mika mai hannu ya dago shi daga jikina tare suka fice daga part din da yaron.
Anty ta juyo inda nake tace dani may ye haka kinyi zaune kuma baki tashi ki bishi ko an fada maki haka akewa miji idan ya dawo.
Na turo baki gaba idanuwa na atake suka ciko da kwalla nai shiru ban mike ba.
Tace bazaki tashi kije ki taimaka mashi da ruwan wanka bane ko may kin yi zaune ana magana da ke.
Maimakon in tashi sai na saka kuka mikewa tayi cikin tsuki ta tashi ta fita daga dakin tabi bayan shi.
Tana fita gajiye tace dani haba Rahama kada fa kikai iyakar matar nan kin dai san abinda ya dace kiyi amma tana magana kin wani basar da ita ki tashi ki dauki abinci kikai mashi mana.
Allah ya taimakeni har na gama jera abincin suna ciki basu fito ba a lokacin na saurin barin falon sai da suka fito ne suka samu na jera abinci na fice daga falon.
Tace yaushe har Rama ta kawo abinci ban ji ta ba nan shi dai ya zauna yaci abincin shi suna hira da ita sai dai kafin ya gama ruwa ne da iska mai karfi ke zubawa ga cidan da akeyi.
Ban tsaya part din anty ba na koma daki na rufe sai na samu kaina da bin shawaran Zarah na tsarki da ruwan dumin da tace dani tunda rana nake hakan.
Sai dana gyara jikina nabi lafiyayyen gadona na haye na kwanta naji ana dukan kofana gabana ya fadi dam.
Na mike na nufi kofan anty ne tsaye tace badai wai rufe kofan kikayi ba kuma Rama ?
Zan mata aikina kuka sai ta raba ni ta wuce daga ciki ta barni a tsaye kofan dole na juya nabita ciki.
Na samu ta zauna saman kujera ta tsura min ido sai kuma ta juya tana bin ko ina da kallo tace ki shirya zan je nazo maki da angon ki yanzu nasan dai ba zai tsaya a nan ba .
Nadai fahinci so kike sai ya sai bakinki kamar na ko wace amarya kila zaki daina ja mashi aji haka.
Ki tashi ki samu rigan barci mai kyau ki saka ki gyara jikin ki ko ina da kamshi da dakin gaba daya part din ki saka kamshi ta ko ina.
Ganin ban da niyar yin abinda ta umurce ni ta shiga bed room dina ta bude kayan ta ciro wani rigan barci mai shara sharan hannaye rigar kamar raga yake ta dauki room fresh da turare ta feshe dakin ko ina rigan ma sai da ta turare kusan kala biyar a jikin shi naga tabi ko ina da kallo sai ta miko min riga wai na saka ajikina.
Kallon rigan nayi na kalleta tace shiga maza ki wanka ki tabbatar kin gyara jikin ki tsab kafin na dawo.
Yadda tace haka nayi har ma abinda batace ba sai da na gyara ko ina nawa tsab na koma saman gado na kwanta ina jero addua a bakina.
Falon daddy ta koma yana zaune don an dauke wutan gari an tayar da gen din gidan zaune yake tana waya Hindatu daga gefen shi zaune.
Tana ganin anty ta shigo ta bata rai don bata kai ga maganan daya kawo ta gare shi ba shima dai fuskan shi a daure yake tamau dashi.
Guri ta samu ta zauna a gefe tana jiran shi ya karasa wayan da yakeyi.
Hindatu na ganin anty ta zauna ta mike tabar falon don tasan bazata iya fadin abin da ya kawo ta ba anty na zaune don sun fara magana dashi aka kira shi ga waya ya dauka.
Yana ganin zatafita ya dakatar da wayan yace ina kuma zaki muna maga ai ki zauna ayi da ita tunda itama maganan ya shafe ta ai.
Tace ba sai da ita ba don ban tsanmani ita ya shafe ra ba ni dai daya shafa nazo naji kan maganan.
Kallon mamaki anty ke masu tana son jin wani magana ne ake akai haka taji yace da ita ke Saade fada mata wai tabayana tazo tanayi wai yau wake da girki a gidan don kwanakin girkin Rahama ya kare ko da nai tafiya.
Anty tace haba Hindatu idan munyi haka ai bamuyi masu adalci ba anan yarinyar nan fa ko sau daya bai shiga dakin ta ba tafiya ya kamshi.
Yanzu kuma muce bazamu barshi da amaryan shi ba ai bamu yi masu adalci ba gaskiya.
Haka dai kika ce mu wa yai muna adalci kuma tasan yana da mata ai ta nace sai da ta aure shi to tashigo tazo ta dandana abin da take son ji gareshi.
Ni ba ruwana da wani rashin adalci can mijina nasani nice ko ke tunda zulfa bata gida zamuyi girki yau.
Kafin anty tai magana yace da ita to bazakuyi ba in ke baki san Allah ba nina sani bazaki halakani ba na dauki alhakin yarinyar mutane ba.
Tace haka kace yace eh na fadi jeki fadawa wanda zaki fadawa tace ban fadawa kowa amma Allah ya saka min sai tafice daga dakin.
Yabi bayanta da fadin noses idiot yarinya kullun ita bata bari a zauna lafiya sai ta samo fitinan da akayi.
Ganin ranshi a bace ne anty ta mike tana fadin muje na rakaka dakin matar ka ni ina son in kwanta ne dare yayi ga sanyi an soma kasan ba bashi yake bani ba wanan yanayin.
Yace ke kuma kamar yaya ki rakani dakin matana itace da girki din yau ne ?
Yace wanan matar hauka take ni you are ok for me anan zaki kwana ba ruwana da wata wai amarya can yarinyar da bata masan gaida mutum ba sai kunyan tsiyane ko girman kai waya sanan mata ?
Tace kana dai zance malam don Allah tashi ka tafi dare ya soma kada tai barci kaga yau yanayin akwai sanyi sosai a garin.
Ya dage da cewa shifa itace zatai girki ganin baida niyan tashi tai fushi tare da kara mikewa tace idan kaga dama sai ka samay ta kai kadai ni kaga tafiya na barci nake ji.
Niko a lokacin ma nayi barci a cikin bargo na don yanayin sanyin garin ga kamshin kasa mai dadi na damana yana tashi ko ina a hancin mutane.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON ALLAH NAGANI MAI TSORON ALLAH TA KULLAH DA HAKAN DON ALLAH..


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH NAGANIN CIN AMANAN DA KIKAYI YAR UWA DON ALLAH MUGUJEWA SABON ALLAH MU KOMAI KANKANTAN SHI, , ,

41
Tana fita daga falon yabi bayan ta da kallon tausayi kawai yasan duk abinda takeyi na karfin haline takeyi don idanuwan ta ya nuna hakan a yadda ya riga ya fahince ta sosai.
Ya mike ya kashe kayan wutan dake aiki a falin dakin shi ya koma ya kara yin wanka yai shafe jikin shi da turare ko ina ya kulle kofan part din ya nufi part dina.
Ya fitowa yaji wani sabon iska ya gauraye garin alaman wani hadari aka kara hadawa kuma again ya lumshe idanuwan shi a hankali yake takowa zuwa part din.
Ya tura kofan da farko ya dauka rufe kofan yake saida ta murda ne yaji kofan a bude ya sa kai ya shiga wani kamshi da sanyin Ac ya ziyarce shi a lokaci guda zuwa yayi ya kashe AC da ke aiki a falon.
Yabi ko ina da kallo tsab part din yake yace a ranshi wanan yarinyar badai tsabta ba kan Allah yasa ta dore a haka kada tazo ta zama irin su zulfa daga baya da kazanta.


Please Login or Register in order to submit comment