Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NR, , ,
88

Alhamdullahi zance komai nawa yanzu ya kammala a gare ni sai hamdala da godiya ga ubangiji a gare ni.
Naje da niyan yin shekara daya da watanni sai gashi zan yi shekara uku a can da watan ni lokacin zan zama babba likita cikakkiya idan na dawo sai course da zandinga zuwa yi don ci gaba na.
Saan dana samu shine wanan auren da daddy ya kara komai baya gaban shi sai amarya da lalurar ta sune yasa a gaban shi.
Duk da bana gida ina da labarin komai a kunne na don duk abinda ake ciki yana dawowa gare ni ina jin komai a inda nake.
Wanan dalilin yasa na kara neman hanyan cigaban karatuna a can nai zamana da yara na matsala shine Amira da ta dauko wani hanya na makirci tasawa kanta.
Nai alkawari a raina idan na dawo zan jata a jiki na ga rayuwan ta bai salwanta ba don bata da kunya ga makirci da son wullakanci sosai.
Zamana a can ya matukar tsonewa amaryan daddy ido sosai sai dai duk samo kan shi da tayi bai sa ya yarda da ta dinga kawo kushe ga matan shi ba don haka yake shi idan ba an hadu da halin maza a kai ba.
Sai ta nemi hadin kan sauran don burinta kawai taga ban dawo kasan da auren daddy ba don tafi hindatu iya makirci gun kishiya.
Saboda ita hindatu tana hadawa da hauka ga alamarin ta don datayi sheri rawan kan ta zai sa ta tona kanta akan abinda tayi din.
Ita ko wanan akwai wayo da ilimi a gare ta sai tai masu sheri ta dawo ana zagi da ita kamar ba itace tayi ba.
Haka take faman cuta masu amma basu ganewa dama ita zulfa ba wai ta yarda da ita bane don ta san ta tasan komai nata tun baya.
Ta gwanmace da tai hurda da ita gara dai ta daure ta jani a jiki yafi mata alheri ga yin hakan dasu.
Tana yawan kira na tun ina dari dari da ita sai dai har nazo na sake jiki da ita zan kirata ko ta kirani mu dauki lokaci muna hiran mu da ita .
Sai dai bana yarda ta dauko min zancen abinda ya shafi gidan namu na rikici idan ta fara nakanyi dariya nace Anty Zulfa a dai ta hakkuri wata rana sai labari insha Allahu.
Da sannu har na fara saro kaya dubai ina turo mata tana sayarwa don kayan da nasan zasu shiga nakan shiga na saro na turo dashi ita da hajiyan harka.
Cikin ikon Allah sai gashi ta fara dagowa ita ma ta samu abinyi yanzu don tana samu sosai a wanan fannin sana an namu.
Wanan ne kuma ya kawo wani sabon tsegumi a gidan har ya kai matar daddy ta fara zuga shi kan wai ina nake samun kudi nake facali haka.
Tunda yace shi yana ma dadewa bai muna aiken wani abu ba ji fa duk da yaran shi na a wurina amma bai sa ya mayar da hankali ya kula damu yadda ya dace yayi.
Gulma yasa hindatu ke fadawa zulfa ai shegiyan nan ta kusa dawowa tunda naji Raliya na fadin sai tayi abinda zaisa ya dawo da ita kasan nan tunda batafi kowa bane ai.
Suna gama waya ta kirani take sheda min yadda sukayi tace na fada makine don ki san abinyi kuma don Allah kada sunana yafito ciki Rahama.
Haka yasa na shirya ma maganan ina jiran ya runkare ni na bashi amsa don likacin nayi nisa ga karatuna sosai ga yan yara na duk sun tasa sun girma gwanin sha, awa dasu ga duk wanda ya gan su.
Kwana biyu shiru banji yai min magana ba sai kamar bayan sati uku ya bugo waya naji yace dani ke nifa ina son ku dawo gida hakana fa.
Don zaman ku acan ya fara isa ta hakana, a raina nace anzo wurin ke nan nace haba daddy kwana nawa ya saura na karasa karatun .
Hakkurin da kayi na taimaka min nazo ai bai kai wanda zaka yi yanzu ba so nayi na samu yaran nan su hada karatun sun tunda sun kusan gamawa nagani.
Yace kin dai ji na fada maki ku shirya zan shigo ku dawo gida hakana ban son zaman nan cen da kukeyi.
Amma dai ai ba zaman banza nake ba ko abinda zai amfane ni nakeyi a can kuma da yardan ka nazo nan din ba wai a cikin rashin yarda bane nazo.
Ni na yarda da farko amma yanzu ban amince ba zan shigo ku dawo gida hakana cikin yan uwa.
Daddy waban maganan kane ko dai na wani na tambaye shi da hakan, aiko take ya hasala dani yace kamar yaya magana na ne ko na wani wa ke aurar min ke da zai min zaben akan matana?
Nace a gaskiya i iya dan sanin da nai maka nasan abinda zaka iya nasan wanda baka iyawa amma wanan maganan daji ra, ayin wani ne a kaina.
Don may shi bai kaunar cigaba na ko kadan yasa ya tursasa maka wanan ra, ayin a kaina don ya shiga tsakanin mu saboda yasan ba abu bane da zai yuyu kai tsaye.
Saura shekara da wata bakwai na kammala karatuna duk hakkurin da kayi da rashin mu a gidan sai yanzu ne wanu magana zai bullo kuma daga baya ?
Kin dai ji na fada maki idan zaki shirya kafin nazo to idan kuma baki tashi shiryawa ba ni zanzo na kwashi diya na nadawo dasu gida.
Nace Allah ya kawo ka lafiya Allah dai na tare da mai gaskiya ko yaushe ya kashe wayan ba tare da yai min magana ba.
Zarah na kira nake fada mata komai har yadda mukayi da zulfa data kyankyasa min zancen tun farko kafin ya kirani.
Tace Rahama tunda har Allah yasa kinji sai kin jajirce akan haka kada ki tsaya sanyi aimaki sakiyar da ba ruwa abinda kowa ke neman wanan daman ke Allah ya baki shine za, ai maki sheri don haka wallahi kada ki yarda da zancen dawowan nan sai kin kammala nuna mashi kema kin iya.
In yaran ne ya kwaso su su mana ai sun samu na samu a can kice ya hada harda na goyen ya dawo dasu gida din mana ki gani idan zai kwaso su din.
Dama gidan shi akwai zaman lafiya ne nasan zai iya kwaso su yakawo wa matan shi amma gida ba dadin yau balle na gobe ya kasa tsawata wa matan shi shine zai ce zai maki hakan.
Ta min maganganu sosai da suka kara min kwarin gwiwa naji ko kadan bana jin shayin komai a kan maganan idan yazo din.

********* ********* *********
Ya shirya yai sallama da iyalin shi akan zai dawo damu idan ya tafi take aka soma gulma da dariyan keta akan dawowan nawa bashiri.
Har suna fadin yanzu suga wanda zanwa wani sallon tsiya tunda karatun ma nawa ban hada ba balle na dawo na samu wani cigaba a nan da nake tsanmanin zama nan gaba.
Ya iso da dare ban nuna mai komai ba na tare shi a cikin mutunci da girmamawa sai washe gari bayan ya karya yaran sun fita zuwa makaranta ne yake tambayana shi baiga kamar na mun shirya tafiya ba bayan ya fada min zaizo mu koma tare dashi.
Nace komawa ina kuma daddy yace ke Rahama kada ki mayar dani mutumin banza fa na fada maki zancen komawan ku gida kina son mai dani karamin yaro.
Nace daddy kayi hakkuri amma ni babu inda zan tafi sai na kammala karatuna nan da watanin masu zuwa insha Allahu.
Yace ok good yayi kyau kila zaman kanki kikeyi ban sani ba yanzu ?
Nace ba duk zaman kaina nake ba nasan dai da yardan ka nazo wanan karatun ba dakin amincewan ka ba sai bayan nazo ne naga sauyi daga gare ka duk ina hakkuri ina shanyewa don a zauna lafiya.
Amma duk hakkuri na hakan bai maka ba daddy sai an turoka ka shiga rayuwa na anga ka tozarta ni hankali zai kwanta.
Wakike tsanmanin ya turo ni na dauke ki ke nace koma waye ai ka sani don haka idan do na koma kawai na zauna ana fitina a tsakanin mu ne ni bazan tafi ko ina ba sai na kanmala abinda ya kawo ni nan din tunda ba zaman banza nakeyi ba nan din.
Lalai abinda mutane ke fadi yau nagani da ido na tun ba aje ko ina ba kina son ki nuna min kinfi karfina yanzu Rahama.
Nace ko daya ni ba zan taba fin karfin ka ba kai ma ka sani rashin adalci ne naga yai min yawa duk abinda ake min ina hakkuri ina hadewa a zauna lafiya baka gani daddy yanzu yakai har sai wata mace ta tursasa maka ra, ayi a kaina kuma kabi don kawai ka gyara mata ran ta taji dadi.
Aiko nan ya shiga fada inda yake shiga ba nan yake fita ba harda cewa har may na zama da nake ganin nafi karfin shi a yanzu.?
Na tuna a karkashin shi nake kuma in yaga dama karatun da nake takama dashi sai ya ruguza min shi aikin ma ko na gama bazan yi ba don na sani.
Sai lokacin nai magana nace daddy nagaji nagaji wallahi na dai yi hakkuri naga alamar ka gaji dani ne kawai ka tsiro min wanan halin ba yau ba don haka a watse kowa ma ya huta tunda abin babu gode balle na gode
Duk yadda nake ma kokari baka gani sai ka rufe ido kai min cin mutunci yau har da goranta min in kai kadai kasaura namiji a duniya nabarka daddy daga yau.
Yace haka kika ce nace shi yafi muna sauki dani dakai tunda banzo nan ba sai da yardan ka yanzu anzugo ka kazo kana min tujara irin haka ido a rufe nafasan komai tun kan kazo dama ina jiran wanan lokacin.
A karshe yace tunda ban tashi ba zai tafi da yaran shi ne shi, nace a sauka lafiya sai dai a hada har da Abdul a tafi don banga abinda za a bar min shi yiba a guna.
Ranan Allah dai ya gyara don kamar zai sake ni Aisha da taji hayaniya yai yawa tafito tana bashi hakkuri tana kuka.
Yafice ya bar gidan cikin kunan rai da mamakina don bai fadi in fadi a sanin da yai min amma sai gashi ranan mun yi kaca kaca dashi.
Washe gari ya kira mama laraba da fada a hasale yake fadin wallahi mama zan saki Rahama na gaji da wullakancin da yarinyar nan take min haka.
Salati mama ta saka tace Yusuf kan ka daya kuwa yau kake fadin wanan maganan haka ?
Rahama fa kake fadin zaka saka da bakin ka kake fadin wanan mumunan kalamin haka may yarinyar tai maka yai zafi haka ne ?
Yarinyar da ta rike ma diyan ka amana ta kuma zauna dakai da zuciya daya da kowa naka tun shigowan ta gidan ka ban tabajin wani abin assha ya shiga tsakanin ku ba haka ?
Yace mama hakkuri fa duk lokacin na nakeyi da yarinyar nan tunda na kara aure ta canza min kwata kwata ba dadin ta nake ji ba sam, hakkuri kawai nake da ita kawai.
Yanzu may tai maka mama din ta tambaya cikin son jin abinda nai mai yai zafi haka da muni.
Yace mama har ni zanzo daukan su mu dawo gida tace dani wai bata zuwa nace idan bata tashi ba zan dawo da yarana gida tace na dauka har Abdul mai shan nono din.
Watau ta nuna min yanzu ita idon ta ya bude ko tasan duniya ko may wallahi zan gwada mata ni banga wanan matar ba tukun a rayuwana.
Da har zance ga raa, ayina tace dani bazata bi ba sai nata ra, ayin take so yi nagaji wallahi mama tunda ita bata san ana tausaya mata ba ko kadan.
Tace baba babaka saurare ni wallahi wallahi idan kayi gigin sakin yarinyar nan kan dan abinda baikai ya kawo ba zakayi dana sani yafi dubu kuma ka sani kai keda hasara ba ita ba.
Don ita ta debi rabon ta gareka ko ta haihu da kai ta samu ilimi ta samu karuwa kaiko fa ko rike maka yara nan wani sabon aiki zai zama maka wacce ma ansan uwar su rasuwa tayi sun kasa rike maka su dan dagawan yarinyar nan gidan ka balle wacce suka san uwarsu na raye da ran ta.
Wallahi kada ka bari shedan ya rude ka kazo kana da kasani daga baya don shi za, ayi ina laifin wanan yarinyar karatu fa tajeyi amma sai da ta kwashe yaran nan kaf ta tafi dasu can suma su karu.
Idan kai ma Rahama kan kara itama tai maka na itace yanzu dabara ya saura gare ka zan kuma fadawa yaya halin da ake ciki ta sani tunda ba zuwan girma da arziki kai masu ba sai ta kashe wayan nata dip.
Nan kuma ya shiga damuwa maganganun mama din yana dawo mashi a rai ya ja wani tsuki ya dade zaune inda yake kafin ya mike din .
Yara kan na shirya su tsab nagama shirina na dauke Atika da Aisha muka fice na bar mai note da cewa idan ya tashi ya kwashi yaran shi ya tafi dasu kamar yadda yace nima aure ne ban yi na fasa ko shi kadai ya rage namiji a duniya na barshi har abada ke nan.
Tashin hankali yana gama karantawa ya kalli yaran dake barci sai da wani zufa ya tartso mashi a goshi.
Tun ba aje ko ina ba ga maganan mama yafito mai shi ina zai kai wanan yaron yanzu haka tundai na goye ke bashi tausayi idan ya falka yaya zaiyi dashi yanzu.
Sai ko ga yaron ya falka ya fara kuka Nasir ya tayar Allah ya taimake shi yaron ya iya abinda Aisha ke mai tare sukai renon yaran ranan.
Hankali a tashe yake nemana ko ina a garin gashi bai san inda zai gannin ba abinka da wayayyen kasa take aka gano inda nake can cikin asibitin da nake karatu.
Ban yarda na karbi yaron ba sai da ya jajibo min manyan kasan mu suka saka baki na karbi yaran amma na dage ban zama dashi kuma.
Shima sai abin nawa ya fara bashi mamaki yadda na hau fiye dashi a yanzu duk yadda aka so fir naki yarda nace nagama zama dashi ke nan tunda har ya rufe ido yazo min cin mutunci a kasan mutane.
Ni kaina nai mamakin kaina yadda na iya rufe ido nai mashi tas haka a kasan mutane batare dana yi dubaiyyan akan baya ba.
Ya samu an lalaba na karbi yaran amma bamu shirya ba tsakanin mu don kowan mu ya hau sosai.
Bayan tafiyan shi ba wani shiri na canza layin wayana gaba daya na ma canza muna mazauni nabar maigidan shi baki daya.

********* ********* *********
Ya sauka a lagos sai daya huta ya samu natsuwa ya karso Abuja lokacin Raliya tana gari tazo tana jiran zuwan mu ta samu na fada min taga yaya muka dawo.
Sai ganin shi tayi shi kadai babu mu take ta nuna bakin cikin ta a fili tace sun dawo kuwa shiru yayi ya shige dakin shi bai tanka ta ba.
Bata hakkura ba bayan ya tashi ya fito ta sake tambayan shi da kai kadai naga ka dawo mana yace a tsawace Raliya will you keep quaint please.
Nagaji na fahinci kina son mayar dani mutumin banza don kinga ina biye maki kin san kin fadawa mutane kece kika tasani a gaba shine kika bari naje naji kunya ga hakan.
To ki sani kafin ma naje Rahama tasan komai da kuke kitsawa a nan keda masheranta yan uwan ki.
Kin zubar min da mutunci ga yarinya ta mayar dani mutumin banza mijin tace kawai don komai da kika kitsa min a nan tas naji shi a bakin Rahama a can.
Nagaji nagaji wallahi daga yau kada na sake jin wani zance akan wanan yarinyar a gidan nan ko rayuka su baci.
Kada ku mayar dani mutumin banza mana haka abinda wanan yarinyar take min ko kadan baki iya min shi ina nan na dauko Amira na kawo maki amma kika kore min ya tabar karatun ta ta koma kano.
Kina ganin abin bai min zafi bane ko may yanzu ita kuma wanan dabaki ko zauna da ita ba kin dauki tsanar duniya kin sa a kan ta ba don Allah ya gyara ba da kin kai ga hakon ki akai.
Ya fice ya barta nan da mamaki ina naji wanan maganan haka har yakai a kunne na kodai aljanace ni bazanji shi ba a inda nake.
Daga karshe taita tunane tace ko hindatuce ta fada min tace ina hindatu ai tafi ta son ma na dawo gida din bazata fada ba to ina naji wanan magan ne wai ?
Kwana biyu sun rasa gane kan shi gaba dayan su ya dauki fushi da kowan su da yake ta iya bariki ranan da tai wani zuwa ta nemi shiri dashi.
Har kasa ta duka wai tana neman gafara a wurin shi ta marairaice murya tana fadin ita bada wani manufa ta fadi hakan ba ta daiga ya kamata ne ace mun dawo gida hakana tunda ance na gama karatuna shiyasa tai maganan.
Bai tanka taba har ta gaji ta mike don shi idan ya tuna da cin mutuncin da nai mai na barshi da yara har gobe abin na bata mai rai.
Nikan bayan tafiyan shi naji ba dadi amma naga hakan yafi min sauki ko ba komai zan kara samun natsuwa ga jeraban dake tafe min .
Don namiji idan ka biye mai baka taba samun natsuwa a zuciyar ka shi baiji kunyan goranta min ba nima haka yasa na rufe idona na dauki mataki akan abinda suka kulla suyi min din.
Ba mai wani contact dina nima bana kiran kowa naci gaba da harkokina na watsar da komai balle namiji irin daddy daya cika mata a gida kowa da nata kalar sallon data iya.
Ya neme ni daya sauko don yaji lafiyan yaran shi amma layin bai shiga sai daga baya ya fahinci kila na canza layi ne hakan yasa ina nan akan bakana dashi ke nan ban sauko ba.
Niko nasan zanji surutun mutane akaina sosai amma hakan bai damay ni ba don ba zan zauna da kurciyana sunnun namiji ya kashe ni ba a raina.
Don ni kadau nasan irin hakkurin da nake a gidan ba a gani saboda hakkuri na sai gani ake nice ke yadda raina yaso ba a san cewa na zamay irin matan da akewa kirari da MARUCIN KAN DUTSE bane.
Kafin ya tofo sai an dauki shekaru bai tsiro ba a gani hakan ke sa ana daukan alhakin wasu mata ake ganin suke shanawa a gidan miji don hakkurin su.
Hakkuri idan yai yawa yakan baci ga dan adam don wani lokaci yana zama cuta haka yasa na dauku matakin don nuna mai nifa mutunce mai jini a zuciya ba wai ruwa kawai nake sha ba na zauna hakana.
Sannu sannu kwana nesa sai gashi na gama karatuna lafiya har Nasir da Atika sun samu kammala nasu karatun.
Sun so rike ni a kasan nai aiki dasu amma hakan ba zai yuyu ba don kaucewa zargi irin na mutanen mu don haka na daure nai aiki dasu na wata shidda kafin na karbi komai na yaran mu tattaro mu dawo gida gaba daya.
Ranan labara ranan saa muka sauka gida Nageria ni da yaran lokaci har Abdul ma yana tafiya da kafan shi ya fara karatu a can don shekaran shi biyu da dan kai.
Sai da muka huta a lagos har kwana uku don nisan tafiyan da muka kwaso muka dan huta anan.
Shigan safe mukayi Abuja a gidan da aka tanadar min na sauka na ma, aikatan mu nan na sauka ni da yarana baki dayan mu.
Na canza na koma wata matar manya ga aji ga class komai na tara a rayuwana bana shayin kowa kuma a halin yanzu ta fannin kishiya.
Sai washe gari na saka layin dana saya na nan gida Nigeria don an min wellcome back.
Na fara kiran yan uwa da abokan arziki muna gaisawa dasu don su san na dawo gida a lokacin.
Ban san dan gulman daya fadawa daddy cewa muna cikin Abuja ba mun sauka ni da yaran .
Yai matukar mamaki sosai don shi dama a hakane ta hake min zaiga yadda zan dawo gidan don yasan dai dole gidan shi zan dawo banda wani wurin zuwa kuma.
Sai gashi yana zaune mama laraba ta sake kiran shi tana cewa ashe Allah ya dawo da yaran nan lafiya jiya da dare Rahama ta kirani take fada min sun sauka lafiya sun dai iso lafiya ko ?
Wani iri yaji a ranshi amma a fili yace lafiya suka iso mama tai min addua ta kashe wayan sai lokacin ne ya ke tunane may wanan yarinyar take nufi ne wai dani ?
Daurewa yayi ya kira bashir din ya fada mai halin da muke ciki na dawo kasan ban nemay shi ba.
Bashir yai matukar mamaki sosai yace dama mai hakkuri bai iya fushi ba don haka kaida iyalinka ke hannunta ba fushi zakayi ba da su.
Daurewa zakayi kaje kanemayta ku sulhunta a tsakanin ku tun maganan baiyi nisa ba sosai don kaga yanzu fa ba da bane.
Rahama na da ilimi tawaye tasan duniya don haka juyata yadda kake nufi tunda ta hau haka kabita ka lalabata kawai a wuce wurin.
Ya dauki shawaran abokin nashi don ya nemay ni amma ban daga wayan ba, hakan bai mashi ba sai gashi ya nemi gidan da muke yayi zuwa yakai ukku amma naki yarda ya ganni.
Don ko yaushe gidan namu a rufe yake bamu fita ko ina mutum ma bai sanin akwai mutane a ciki don muna bakin shiga don da gidan empty yake ba kowa a cikin sa.
Hankalinshi ya tashi gashi ko yaran shi na hanashi ganin su balle yaji dan sanyi a ran shi idan ya gan su din.
Ganin baida wani mafita ga matakin da na dauka yasa shi yanke shawaran da zai fishe shi kawai don haka.
Kano ya nufa ya je kauyen mu ya sanarwa iyayyena halinda muke ciki ni dashi abin yai matukar basu mamaki sosai.
Kin san halin iyayye da rufe ido su ba yarsu laifi nima hakan ne ya kasance da nawa iyayyen don laifina suka gani ga zancen.
Tare suka shirya zuwa Abuja da daddy anyi tafiyan ne da maigari da mahaifina da liman da wani abokin babana.
Gidan da aka bani

Please Login or Register in order to submit comment