Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi a zahiri.
Gashi ko ai gaskiyan tayi halin ta tunda dai su bazasu iya wanan kulawan da ita Rahama keyi ba ai.
Ai ke dai bari wallahi tun wancan zuwan na rege halin su don na fahinci son kai na tsiya a gun Raliya sai dai kiga yaranta nacin abu muko ta saka yan aikin ta suyi muna kwababen miya muci cikin mu ya burkuce muna.
Dariya suka saka ma hajiyan tace don haku san irin halin da na shiga bane a zamana dasu wancan karo ita wanan hindatun ma aiko kallo ba isheta ba don bata da kunya idan an kawo muna kuma ta zauna ta cinye.
Mikewa nayi don jinior dake ta kwada min kira ina fita muka ci karo da daddy a falon mu ya shigo wurin mu yana ganin na fa jinior na fadin mummy abamu abinci muci wanan da kikaiwa su hajiya yanzu zamuci
Duk yan uwanka bazasu zubama ba sai ta zuba ma da kan ta baka ganin tana fama da nauyin dan uwanka ne a jikin ta.
Da sauri yaron ya dago kai yana kallona sai dai ya kasa fahintar maganan uban nashi yace Daddy ai Abdul da su Haidar duk suna can suna kallo tare ma zamuci dasu.
Uban yace mummy bata sanar da kai zuwan sabon babyn din ku bane nace kai daddy wanan fallasan kuma fa haka ?
Shi Jinior may zai gane ga yaron a tsaye ya tsura min ido yace mummy wai da gaske muma za mu samu baby ga ihisan ko yaushe tana muna sallo wai in mummy ta ta haihu bazamu dauki kanin ta ba itama.
Kyaleta kafin ta dauki nasu kai zaka fara daukan naku kaji kai zakai mata sallon ai ba ita ba.
Ni dai naja kafana da kyat na barsu a wurin suna shirmay su na fito dauke da tire din dana zubo miya a plate's nace yaron ya karba yakaiwa yan uwan shi ta dawo na basu bread.
Aiko yana shiga sai gashi da yan uwan shi da murnan su wai mummy kema zaki haihu harda Nasir a bayan su nace ku tambayi daddy shi daya fada mashi ai.
Da ido ya nunawa Nasir ne sai ko yaran suka dauki ihu murmushi nayi nace kai daddy baka barin dai a zauna lafiya yanzu na shiga ukku da damuwar Jinior wallahi.
Yai murmushi yana cewa wayon da kikai min a baya kikai min surprise kike son yiwa yara ki ma yanzu ko ?
Daddy wayon may kuma can dan Allah dai ?
Kafin ya magana sai ga Zulfa dake barci ta fito tana cewa wai ihun may yaran nan keyi haka ne wai ?
Nace su da daddy sune suka abin su jinior yace da ita daddy ya fada muna mummy mu zata haifa muna babby muma.
Kallon daddy tayi tace har kuma da yara ake irin wanan maganan kuma yake cewa wani irin magana ke nan fa ?
Tace Allah dai ya taimaka kowa na dashi da mutum ya ga takaici take ranshi ya haci yace da ita may kuma ya kawo wanan magana haka ?
Fadawa yaran shine kuma abin bacin rai ko may da har zaki fadi hakan ?
Tace nikan kada ka lake min barni naji da abinda ke damuna yace ashe keda na fadawa su baby ranan haushi nags kinji ba dadi ba ?
Wai may yasa ku baku kunyan fadin magana akan kishi tace kajika kuma zaka wani daure ni daga agana nace don Allah dai ku bar wanan zancen haka ba kyau mana a gaban yara kuma ?
Mikewa yayi ya shiga dakin su hajiya ya barmu a wurin nima ban tsaya ba na shiga dakina kwantawa nayi don na huta barci ya fara dauka na sai gata tashigo dakin .
Take cewa dani kin kwanta ne ashe nace eh batare dana dago ba ta samu wuri ta zauna daga gefe na tana fadin.
Watau na miji dan hadin fada ne Rahama daga fadin magana sai ya juya min magana na kawai nace humm m anty don Allah dai mu bar zancen jan don babu yaro a cikin mu ai.
Abinda dama nake son magana ke nan don naga ranki ya baci sai lokacin na dago ina cewa da ita raina ya baci kan wanan maganan da ba yau aka fara irin shi ba a gidan nan.
Ni dai nasan da zuciya daya nake zaune da kowan ku a gidan nan bance ban kishi ba amma dai ba irin wanda kuke gwada min ba haka wanan maganan banga abin kishi a cikin sa ba don kowa na dauke da wannan abin a jikin shi.
Allah na tuba ma ciki har abin tsayawa wani kishine a kansa ayan kayan wahalan dake ajikin mutum kawai.
Tace to don Allah kiyi hakkuri ni dai bada wani manufa na fadi magana ta ba don dai naga yara ne kawai nace nifa ban dauke shi wani abu ba can anty.
Tace na sani amma dai naga ai ranki ya baci ga maganan nace dole ne don bana jin dadin irin yadda ake gwada min tun dai ke anty duk fa zaman abu daya muke gaba daya a gidan nan.
Halin maza kuma kowan mu ya san yadda yake yau a kan kane gobe ga wata to may ye abin jin haushi a cikin sa kuma.
Aisha data shigo ta samay mu take cewa kai kuna nan ashe har dakin ki nake ai bakya ciki sai yara dake kallo kawai.
Mun zauna da Aisha sai ga Fatima hira mukayi dasu sosai har muka manta da halin da muke a ciki nan cikin hiran nake fahintar wasu magana akan Zulfa din a baya gata ashe gwanace sosai wurin shan kayan mata yadda suke hira da Aisha suna kyalkyalan dariya.

********* ********* *********
Waahegari su hajiya da yaran ta suka shirya komawa gida nan dan yai mata sha tara na arziki inda shi da kan shine zai mayar da uwar har gida harda mota sabuwa ya saya masu ita da mahaifin shi.
Sun tafi a cikin dadin rai duk muna tsaye a kofa munyi masu rakiya gaba dayan mu gidan in ka debe yaran Raliya da suka ki fitowa raka su kawai.
Suna dagawa sai Raliya tace munafunci dai baiyi ba wallahi ra juya zata fara tafiya sai Zulfa tace waye muna fukin yanzu a nan ke nan ?
Ta juyo tana cewa da ita wanda duk ya damu dashi nakeyi aiko nan fada ya barke a tsakanin su Hindatu tace da ita wanan maganan da kikayi ai dole ne a tambaye ki ko.
Tace kai nifa duk wanda ya saya na sayar mashi waye ba munafukin ba ko waye bai san munafuncin da akayi ba anan.
Duk dai tsiyan mutum sai ya ganni a gidan nan kuma na aje yadda kowa ya aje nashi sai dai a mutu da haushin kura.
Don ta Allah bata mutum ba an dauka ko mutum juya ne duk bakin ciki da hassadan da ake min kallon kowa nake wallahi.
Yanzu ai sai kiyi da wanda kika gani Juya a cikin mu ko don Allah ya raba gardaman shi ko a nan saukin abin yaba kowa ba maiwa wani gori kuma .
Kai fadan nasu yai tsanani har takai zasu fara dangwaran junan su nace haba haba maman Ihisan kin manta da halin da kike cikine kada kiyi soma motsa jikin ki haka zaki iya samun matala yanzu kuwa.
Da sauri hindatun ta dan juyo ta kalle ni tace kedai fa dama ko yakai wa kowa ko ina zan biyewa wanan yar kakagidan mu lalace tare ta baya taji an shako mata wuya sai ko kokuwa ya kaure tsakanin su sosai ikon Allah.
Ni da nafisu watan ni ne na samu na raba fadan aiko sai ga jini ya balle wa hindatun take a wurin nan kuma muka shiga wani sabon fitina.
Yadda nake da haka na gigice nasa su Amira suka kama min ita zuwa mota don ita Raliya ma bata tsaya kan ta ba mun isa asibiti da ita duk wani abinda ya dace muke mata.
Da kyat da sudin goshi na samu cikin ya tsaya amma mun yanke cewa idan bai tsaya ba zamu cire mata baby din don anyi scaning mace ce a cikin ta.
Ina kan ta har garin Allah ya waye har isowar daddy da iyayyen ta muka dora da su daga karshe dai dole zamu cire cikin don lafiyan shi da nata ita uwar.
Nai mata aiki na fitar da yar baby da bata kosa ba muka kaita dakin adana irin su don kulawa tasha matukar wuya sosai a lokacin.
Uwarta sai bina take duk ta rude tana fadin don Allah Rahama a taimaka yarinyar nan ta rayu kada ta mutu nace da ita.
Mama duk abinda na sani shi mukeyi idan Allah yayi zata rayu zata rayu din don haka Allah ya rubuto mata wanan matsalan.
Cikin yardan ubanginji uwar taji sauki itama yar babyn na samun kulawa sosai tana dan murmurewa a hankali
Sati uku ban huta ba gashi watana na tara na batun tsaya min haka ga bakin kano na tashigowa duba jikin hindatun don an sallamota sai dai baby din dake asibiti har lokacin.
Ranan ina kwance na dan samu hutu sai ga mahaifiyar hindatu har dakina take cewa nazo don Allah wai babyn nan kamar bata da lafiya da sukaje bata nono haka na daure na mike muka nufi asibitin lafiyan yarinyar kalau bayan an dubata nace mama ku kwantar da hankalin ku idan an shiga sati mai zuwa za a bamu ita mu dawo da ita gida insha Allahu.
Daddy ma ya iso don an buga mai waya yake cewa don may baza a bar ni muyi aikin mu ba ba a ganin nima halin da nake ciki ne ya kamata su tausaya min hakana mana dai.
Ni kaina wanan fitinan ya fara isata haka wanan haukan yai yawa a gidan nan na yau daban na gobe da ban wai kuma duk a kan kishin mutum daya ake wanan abin haka.
Ina son yin transfer na koma kano da aikina na barsu nan amma basu yarda ba wai sai dai lagos ko portherqut zan iya komawa ba arewa a ciki inda zan iya komawa din yanzu.
Fitinan ya isheni haka ko da yaushe a cikin tashi hankali harda batun salwantar da rayuka gashi kan wanan zancen har yau daddy baiyi wani magana ba akan zancen.
Tun kowa na jiran matakin da zai dauka har akaji shi shiru ba wani magana kuma ga Raliya na girkin ta daidai da kowa lafiya lau ba wani fitina.
Da haihuwa yazo min a satin da duk aka dawowa Hindatu da yarta gida satin naji haihuwa yazo min daga Amira sai Aisha da sai mama Altine na dauka muka nufi asibiti da su.
Don daddy ya tafi kano duba jikin hajiyan shiko da na bar gidan duk suna barci ba wanda yasan fitina da asuba.
Tara na safe na haihu lafiya sai dai nima haihuwan yazo min a bazata don dama ina zargin hakan a gare ni.
Macen ta fara fitowa sai namijin da ya dan dauki lokaci ya biyo baya ta duk kan su kuma a cikin koshin lafiya sukazo duniya.
Sai da komai ya kammala na kirashi ina sheda mai na haihu daddy yace what ko dai kin fadi ne nace gasu kaji kukan su ai.
Yace may kike nufi nace tau ga su dai ai kaji su ko yace Rahama tagwaye kika haifa murmushi nayi kawai ban ce uffa ba dai.
Tare da doctor Fati muka dawo gida nan kowa yake mamaki da haihuwan sai dai duk wacce taji biyu na haifa sai fuska ya sauya a wurin.
Ba wacce bata sauya fuska ba daga cikin su ranan daddy ya dawo garin shi da mama Laraba suka shigo tare.
Da farin cikin shi ya karaso dakin don gani kyautan da ubangiji yai mashi a kwance suke saman gado yayin da mama Altine take zaune bakin gadon ta mimike kafafuwan ta duka biyu ina ban daki fitowa na yai daidai da zuwan su.
Sannu da zuwa nake masu amma hankalin su na kan yaran dake barci nade a cikin towel suna saboda sanyin da akeyi a lokacin.
Idon daddy kyam a kaina ya kalle ni ya dubi yaran yace dani so da gaske kike Rahama tagawaye ne dauke a cikin ki ashe baki fada ba.
Nace na shiga uku daddy wallahi nima ban tabbatar ba sai yau don ban taba zuwa scaning ba don in ga may zan haifa sai dai ga yana yin zaman su nakan yi hasashen hakan dama amma kuma naga ba wacce ta taba haifa ma su sai nake ganin baku da kwansu a gidan nan ai.
Mama laraba tace waya fada maki shi Alhajin mahaifin shi ai haka suka fito mace da na miji ne macen ta rasu gun haihuwa ne shiyasa.
Sai mama laraba tace kunga ita ma din ai ai ubanta tagwaye yake biwa maza kuma duk suna nan da ran su a akauyen su.
A hankali daddy ya karasa bakin gadon ya dauki daya daga cikin su yana fadin wanan macen ne ko na mijin sai mama tace dashi namijin ne ka dauka ga macen can ai yanzu nake wa uwar sheri duk tabi ta makale mata kasan mu mata da son diya mace.
Mama Laraba tace ai nima sai da na fadi nace yau yar nan ta fado a inda ake son ta Rahama da son diya mace.
Addua yake baiyi magana ba sai da ya gama ya mikawa mama yaron ya dauko yarinyar yana binta da kallo.
Mama Laraba tace yaran nan ai sun yankewa mahaifin su kauna ana cewa Abdul yafi kwaso uban ga wanda suka kwaso shi da tushe har da dan bakin tabon dake hannu shi sai da yaran nan suka dauko.
Yana addua yana murmushi ya karasa ya rugumay yarinyar yana fadin Allah ya raya muna su a tafarkin musullunci ya sa masu albarka a rayuwan su duniya da lahira.
Yace ina yaran suka shiga ne mama tace ai suna school basu dawo ba har yanzu sai sun dawo muga hauka yau kan.
Hajiyan daddy ce ta kirani a waya na dauka ina saka kaya a jikina muna waya da ita take cewa sannu yar nan ashe an sauka lafiya ga Alhaji na gaida ke yace kin zama maman shi kuma yau.
Murmushi nayi na kara gyara kwanciya na ina fadin hajiya a gaida min dasu Aisha munyi sallama da ita mama ke cewa dani naga kin kwanta ai da ki tashi ki dan ci wani abu hakana Rahama tun dazu fa ban da tea ban ga kin sha komai ba fa.
Mama Laraba tace haka take haihuwan Haidar ai mun sha fama da Attu da ita nace kai Attu ta faye fada komai tace mutum sai ya ci shiyasa wanan karon na dauko mama bakina alaikum balle tana fama da tsufanta yanzu wani moriya zatai min kuma.
Daddy da zai fita yace dani Hamza zai zo da ita ai don ban tsaya daukan ta ba amma na bar sako yazo da su.
Abinda yabawa daddy mamaki shine har ya kwana ba matar da tai mai barka a cikin matan shi har ya fita yaje muna shopping ya dawo.
Yana zaune da yaran shi a falon shine Zulfa ta shigo wurin su tana tambayan shi wai kayan da aka shigo dasu rabawa za, a yi ne ?
Kamar yaya rabawa zakuyi har yaushe na sayowa kowa kayan amfani wanan baki ga na mai lalura bane ga tada jama, a a tare da ita.
Tace dashi gani nayi har abinda babu a namu ka sayo ai yasa na tambaya yace Zulfa na sayo nafa fahince ki a harkan nan.
Ke batulu ce ta karshe idan har kika bari Rahama ta fahinci ba da zuciya daya kuke zaune ba zakiji kunya ke kan ki kin sani.
Tace ban gane ba yace zaki gane ai idan har kishi ya jaki kika gane cewa duk abinda kikeyi Rahama na sane dake.
Amma kana bani mamaki wallahi Rahama rayuwana ne ko may ko uwata ce ko ubana yace da ita kada ki kawo min diban albarka a nan yanzu ran ki ya baci maki.
Don iskancin ku ya soma isata haka na kaya dai ne nace na mai haihuwa ne ku gunta nace Sani ya kai su.
Tace to shine may idan an hana muna kayan ai ba yau aka saba yi muna haka ba a gidan nan.
Take ran shi ya baci yace sai ta fada mai lokacin da ya taba ba wata wani abu ita bai bata ba a gidan.
Zata wuce yace dawo ai ba tafiya zakiyi ba tace gara na natafi don naga dama a jirace kake dani ai.
Yace kina tafiya wallahi yau baki kwana a gidan nan ido ta fitar tana mamakin shi nan yai mata tas sai da ya gaji ya kyale ta.
Barci nake a cikin barci nake jin muryan shi yana fadawa su mama zai mayar da ita kano ne dama idan yaje yana bukata wata acan don haka ra shirya ta koma kano da zaran an gama suna.
Mama Laraba fada take sosai tace shine matsalan Zulfa bata da wayo wallahi na lura ko dakin nan sau daya naga ta shigo shi ashe ita da manufa take hakan.
Ina jin su ban motsa ba don ni ba bakon abu bane a guna bayan fitan shi ne na tashi na kira Aisha da Amira da suke gida nace ta taimaka a gyara kayan su kai komai inda ya dace su aje.
Yan barka na shigowa harda ma wanda ban zata ba sun shigo gidan ganin yaran don fari jini irin na tagwaye.
Banyi mamakin rashin shigowan yaran Raliya ba don ko ita uwar sau daya ta shigo inda muke har gashi ana zancen suna yan kano sun fara cika muna gida ko.
Yaran sunci sunayen Saade da daddy kowa yai mamaki kara saka sunan shi da yayi yace a haka suka zo dama naja bakina nai shiru nan sabon gulma ya tashi kuma again.
Sunan yayi kyau sosai don har walima su Fati suka hada anyi rabon abubuwan daya dace sosai a wurin.
Naga kishi a gun matan daddy kamar cikin nan ba kowa keda shi ba a gidan ni Zulfa tafi ban mamaki wai a haka shiri akeyi sai tazo taga abinda akayi zata koma gefe tana magana kuma.
Yan uwa na sunzo min sosai don haka na kebe dasu nace mama zata zauna dani wanan karon don Attu bata zo ba.
Da zasu tafi kamar yadda ya saba yi masu alheri ko yaushe wanan karon ma haka yai masu ya ba kuma Suwaiba da Rukaiyya alheri su samu sanaar yi idan sun koma gidajen su.
Gida ya rage daga mu sai su mama dake zama damu din tun mama Laure na shan jinin ta har tazo ta sake jiki don komai sai ince uwata nima fa uwata a tare dani.
Munyi arbain ya shirya su mama suka koma gida suma da tarin alherin su mama Altine ce dai ya hana komawa tace a nan zata zauna da mu.
Sati na biyu da arban sai gashi da visaza zamu tafi umurah har yaran nawa gaba daya wanan abin ya dan kawo rikici a gidan sosai.
Ba fashi muka shirya din an shiga dogon zango na hutun makaranta muka wuce ba saudiya muka fara zuwa ba sai da muka tafi Egypt don jinior ya matsa yana son zuwa yaga gawan firauna da ta gani a waya.
Satin mu daya muka juyo saudiya nan muka samu wani gida mukai masauki zaka ce don mu akai gidan dama sai bayan zuwan mune na fahinci akwai aikin da shi kan shi maigidan yazo yi acan dama don baya zama a garin yana shiga wurare da dama a can don business din shi.
Wasa wasa sai da muka kai wata biyu a can waya kan da fitina daddy ya sha su a gun matan shi amma ko a jikin shi bai damu ba da komai da zasu fada muna can Raliya ta haihu na dauka zamu dawo ne sai da muka share sati hudu bayan haihuwan ta muka fara shitin dawowa gida a lokacin.
Dagani har yaran duk mun canza munyi kyau don itin daulan da muke a cikin sa mun dawo gida mun samu anyi wa gidan gyara na sosai don ashe bayan mu suma sai da suka koma kano a kai gyaran wuri yanzu part dina daban na Zulfa daban haka ma sauran suke.
Kwanan mu biyu a kasan bamu damu da muje mu yi wa Raliya barka ba don har yaran ban tsanmani sun tafi ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,
101

Tun daga wannan rikicin da mukayi na kara fahintar alamarin kishiya dai abin tsoro ne duk dadin ki da kishiya ki tabbatar da kin boye sirin ki na yan uwan ki dana kawayen ta a gare ki.
Don da ace ni irin rayuwan Zulfa da ta shige min jiki kamar aminiyar gaskiya ke gare ni na yawa sake maganan duk wanda yazo mata a rai ba yan uwan ta ba ba iyayyen ta ba kawaye ba da miji.
Da na sha matukar wahalan zama da ita don nasan dan abu kada ne zai hada mu tafito tsakar gida tai min gori a gaban wanda nai maganan shi da ita ko ta samay shi gefe tace ai Rahama tace da kai abu kaza.
Amma sai Allah ya taimake ni duk zaman mu na kama bakina a gare ta bana zama ina sakin maganar kowa kamar yadda ita take zaman yi mun.
Ban yi ba ma tana koma gefe tace nayi din inaga nayi mata da yawa bani ba nasan muna samun irin wanan matsalan ga irin su da son shigewa mutum a jiki kamar da gaske son ka suke tsakani da Allah.
Don Allah mata mu kula kafin mu yi sauri yarda da mutum mu auna halin shi mu gane irin kalar mutumin da muke zama dashi don wata zata dade tana cuta maka amma bazaka san cewa ita bace ke cuta maka don irin su Allah ne ga baki fir,auna ga zuciya suke.
Ba wata kishiya a zamanin nan da zata ce tana kaunar ka da zuciya daya dole na ciki na ciki a zuciyar ta da kai.
Nima bawai bana kishin kishiyoyina bane ina yi sai dai ba can ba irin yadda su suke min din don har yarana sai na fahinci akwai hassada da bakin ciki a tsakanin su da su.
Tun dai yar Sa,adene da take karama na dauki son duniya ni da uban ta mun kwallafa ma yarinyar kamar yadda fita goma zanyi sai na sayo mata wani abin don shi abin yara mata avalable ne ko yau she zaka ga lates din abin kwalliya na diya mace haka uban ma yake da yarinyar yana kiran ta da sweeting shi mu kuma muna kiran yarinyar da

Please Login or Register in order to submit comment