Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk tare da yaron nan da yace min sunan shi habib ne dan gidan mai faci.
Sai yamma Alhaji ya shigo gidan daga shiyana ina zubawa yaron abinci naji muryan sabuwa tana cewa yau wani sabon cin amana ne da muna funci ya taso a gidan nan kuma ?.
Kamar yaya kuma ya tambaya tace duk munafuncin da kake a gidan nan nabawa yarinyar nan kayan dadi taci don ta yarda dakai ta kwantar da hankalin ta ka murje ra yadda kake so nagane ka.
Mu sai ka tura muna tuwo ita ko daga shinkafa sai taliya kake bata bata taba cin tuwo a gidan nan.
Ga kowa yai cirko cirko yana sauraren ta yace cikin daka tsawa ke sabuwa ban son sheri ni kike kira da munafuki yau.
In ma har munafunci ne ai ake nakeyi don ke ce munafukan kullun a gidan nan ba mai bani bani sai ke, ke, kenan kullun yin karya da ciwon yara ba ranan da zan fita baki karbi kwabona ba a gidan nan karyan yau daban na gobe daban.
Kaji kuma na sayo mata don itace mai girki su nake son ci shiyasa na sayo ke ranan da zan sayo bacewa kikiyi wai nabaki kufin ba ki sayo da kanki dana baki na dawo cewa kikayi n sace kudin ai.
Nawa nake ba wanan yarinyar a gidan nan ko bata nayi yadda nake bata sai dai tace na sayo mata duk abin da ya dace idan na fita.
Sabuwa nan ta hau borin kunya akan wai Allah dai ya kama ka yau kila ma har gashin dare kake kawo mata kai a dole gaka mijin yarinya ko ?
Sabuwa yau dai na gaji da sherin ki a gidan don haka na fada maki akan yarinyar nan zan iya saba maki kifice min daga gida.
Ahayye nanaye abin kunya wai aure da mara kwabo yace balle da kwabona ko kin manta kwabon kika gani a baya kika lake min da aike da komai har na yarda kika shigo gidan don haka yau ko wayai maki tsaye a gidan nan wallahi baki kwana min a gida.
Maimakon ta ci gaba da gudan da takeyi sai kuma jikin ta yai matukar sanyi sosai don tasan takan mashi fiye da haka amma bai taba yanke irin wanan hukuncin ba a kan ta sai yau kuma akan yar karamar yarinya.
Nan dai mama hausi ta saka bakin ta tace asha Alhaji da baka biye mata ba halin sabuwa ne kuma bako a gare ka yau.
Yace bari hausatu nagaji da sherin yarinyar nan yau ta kaini kat ne ita bata ji kunyan yaudara na ba sai nine zanji kunyan ta.
Ina kazan nan a kowan ku da yai girki sai da na saya mai aka girka min naci amma don wanan yarinyar na da girki na sayo zatai min sheri tace ai ba biyu ka saya muna ba kamar nata.
Bai kula ta ba ya shige dakin ta da kan shi ya kwaso kayan shi na kwan ciya ya fito daga dakin nata.
Hankali yai matukar tashi sosai a lokaci don nasan halin kauyen mu yazu labari zai sha banban ace daga shiga na na fara watsa matan gidan da na samu.
Hakana jiki ba kwari na dinga aiken wanan yaron da Allah ya hadani dashi yau yana kai wa kowa miyan duk sai da na kusa rabe naman don yawan gidan.
Mama hausi dake zaune tare da sarakan ta matan diyan ta su uku ta ce kungani ba yanzu ga naman ma karshen ta duk ta rabe shi gare mu.
Har ya fita zuwa sallah ya dawo bata bar gidan ba kamar yadda ya bukata haka yasa shi zuwa har kofanta ya daga labulen dakin yace.
Sabuwa may kike jira ne a gidan nan wai ai tunda gidan nan bana ubanki bane yau na fada maki wallahi baki kwana min a gida ki tafican gidan ku kikarata can.
Idan kuma kin ki fita yanzu na turo masu karfi aja min ke da karfin tsiya har waje.
Ganin haka tasan kuma da gaske yake yi yasa ta fara tattara kayan ta tana kuka wai saboda karamar yarinyar da kokwai bai aje da ita zai koreta gidan shi ita dake da yara bakwai a gidan.
Haka tafice daga gidan bakin ta bai mutu ba ta nufi gidan su a cikin dare kowana na kallon ta a wullakance.
Sai bayan tafiyan tane na fahinci ashe halinta ya ishi kowa agidan sai fadin aibunta kowa keyi.
Nan naji abubuwa da dama akan halinta ashe shiyasa take ganin an auro ni zan karbe mata power da take dashi a gidan da gurin mijin su.

****** ********* ******
Washegari tunda safe na shiga gurin mama bayan na gama aikin da nakeyi na kwashi kayan wankin ta sai aune tayi dani ina wanke tufafin ta.
Ta saka salati tana cewa haba amarya ai sai kina ace muna bautar dake ko iyayyen ki suka samu labari bazasu ji dadi ba gaskiya.
Nace daidai danta babba yana shigowa gidan dauke da dan karamin yaron shi a kafadan shi haba mama don nai maki wanki shine za, ace kina bautar dani kefa uwatace mama ba kishiya ba kamar yadda naji ana fada.
Ko a gida nike wankewa su innata har da mama kayan su idan yai dauda don wanan kayan da baida yawa ma.
Girgiza kan shi yayi yana cewa a ranshi ikon Allah yanzu baba wanan karamar yarinyar daya kwaso kurciya zalla haka may zai gane a gurin ta ne wai.
Nan dai dole uwar ta barni da wankin na wanke su fes na shanya na koma dakina ina jiran su bushe na kwashe mata.
Yaron nata mai suna yaya sani ya shigo dakin mahaifiyar tashi ya samu guri ya zauna daga gefen ta yace.
Mama dazun sai nake jin ki da amaryan ku a bakin rijiya kuna gaddama kuma akan wanki.
Tace bari kaidai ni kurciyar yarinyar na ya fara daure min kai wallahi bata tasan kyashi ba ko hassada a rayuwan ta komai haka zata zage tayi shi tsakani da Allah.
Yace haka naji nima sai dai mama gaskiya sai kunyi da gaske gurin rike amana tun da dai ba sanin ciwon kan ta tayi ba yarinyar gashi uwarta tai mata tarbiyan da ya dace duk uwa ta gari taiwa yarta.
Tace insha Allahu haka nake kokarin ganin nayi yo har ma may mutum zai cuta a wanan gurin kuma ?
Nan dai sukai ta zancen su har suka fado kan maganan sabuwa da irin hallin gallaza masu data dinga yi a zamanin ta a gidan.
Mama hausatu tace don yaran ai ayi hakkuri ta dawo dakin ta gashi kuma bazan so ace don wanan yarinyar tabar gidan nan ba.
Kada azo a shafa wa yar mutane labbo bata ci ba tasha akama zarginta ga banza kasan haln mutanen yanzu da dauka su dagwarawa kan su maganan da bata shafe su ba.
Dan nata yace hakan yana da kyau mama indai wanan mara mutuncin ne aiko ta dawo ba dainawa zatayi ba.
Gara dai tadawo dakin ta din zaifi don kaga yanzu idan tafice gidan nan nauyin diyan ta duk akaina zai dawo gasu ba tarbiya ke garesu ba.
Yadda mama hausatu tai shawara da danta haka akayi da yamma da Alhaji yadawo gida ta sanya shi a gaba tana bashi baki akan yayi hakkuri ya daure sabuwa ta dawo dakin ta hakana ko don yaranta.
Yace wai hausatu ke ce ke auren ta ko ni da zaki isheni naje nayo bikon ta ina indai sabuwa ce koke bata bari a gidan da tsufanki kuwa ?
Mama hausatu tace kadai yi hakkuri Alhaji kodan yaran ta ta dawo taci gaba da duba abinta.
Yace yara ai bada su tazo ba anan ta samay su kuma a gidan iban su suke ko ?
Ya ja tsaki ya dauki buta ya fice daga gidan.
Gaba daya yaran Sabuwa sun ishi matan gidan da rashin kunya idan ka cire shi Alhajin da basuyi a gaban shi don tsaye yake akan iyalin shi.
Don haka shi zaman su ma babu uwar su a gidan ko a kwallan shi bai taba damuwan shi ba don dan ficewan ta har ya samu natsuwa tare dashi.
Satin ta daya shiru babu labarin dawowan ta gidan har wanan lokacin ganin maganan wasa zai zama gaskiya yasa.
Mama hausatu samun wani dan uwan Alhaji kuma amin shi akan zancen sabuwa din don yaran sun ishesu ba hutu gareta.
Bayan sun gaisa ne tayi mashi bayanin komai akan matsalan da ake ciki tsakanin sabuwa da Alhajin.
Malam shehu yace a gaskiya ba yau ba Alhaji hakkuri yake da al, amarin sabuwa ke ma kin sani .
Don ko jiya muna tare nan dashi yake min bayanin komai don iyayyen ta da yan uwan ta sun damay ni da zariya agida.
Amma tunda kinzo ba komai insha Allahu anjima zan samay shi muyi magana idan ya dawo.
Mama tace don Allah malam a taimaka a sa baki ga alamarin a gyara tun bai baci ba kodon yara.
Daga haka sukai sallama ta tafi tana godiya don sun saba dashi sosai akan matsalar gidan su.
Duk yadda ya raya da Alhaji akan yai hakkuri Sabuwa ta dawo dakin ta yaki yarje mashi.
Don haka ya kyale shi malam shehu ya nemi wani amin shi da magariba suka shirya sai gidan wan sabuwa inda take zaune.
Lokacin da suka isa gidan sun samu wan nata baya gida dole suka dan jira shi don ba nisa ya tafi ba.
Bayan sun gaisa ne suke cewa da shi dama mun biyo bayan sabuwa ne don Allah ayi hakkuri ta koma dakin ta hakana.
Don sabani akasamu kuma yanzu kowa ya gane kuresa don ko tsakanin harshe da hakori ana samun sabani balle mutum da mutum don gaskiya iya hakkuri kukan ku kun sani Alhaji garbati yana iya hakkurin shi da sabuwa a gidan shi.
Yayan nata yace hakane amma naso ace shi Alhajin ne yazo nan da kan shi don na kara bashi hakkuri saboda nima dan zaman ta cikin iyalina nasan yana hakkuri sosai.
Malam shehu ya jinjina kan shi yace hakane amma da zuwan Alhajin da namu duk kusan guda ne don a madadin shi muka zo mu.
Koma may nene ai yanzu ta san ta fara kaishi bango don baka kallon babban mutum kamar Alhaji garba tsakiya iyalin shi tace mai munafuki.
Yayan nata yace don Allah akara bashi hakkuri kafin nazo har gidan na bashi.
Yayan yace kafin ku tafi bari na kirata taji da kan ta don ku kara ja mata kunne mace da girman ta kamar Sabuwa ace wai ta saura yaji don rashin hakkuri irin nata.
Bai jima ba suka fito a tare yana gaba tana bayan shi ta samu guri daga gefe ta tsugun na.
Yayan nata yace sabuwa ga malam shehu nan sunzo bikon auren ki a madadin maigidan ki.
Ta dukar da kai cikin kunya da nauyi zatayi magana malam shehu yace da ita.
Haba Sabuwa yanzu lokaci yayi da za, a san girma ya kama a daina wasu halaiya kuma.
Don Alhaji ya auro wanan yarinyar bai kamata ace daga gareki ne ba a samu zaman lafiya ba idan kin yi tunanen irin zaman da kukayi ke dashi har takai kina ci masa mutunci a tsakiyan sarakan shi hakana.
Don haka idan kin koma dakin ki da fatan komai zai sauya daga gareki yanzu shiga ki dauko kayan ki basai gobe ba mutafi na mayar dake dakin ki.
Zatai magana yayan nata dake zaune a gefe yace ya katseta cikin bacin rai da cewa .
Kin sani sarai bana son tashin tashin kije ki shiryo ku tafi.
Ba don taso ba ta tashi ta shiga ciki can sai gata tafito da lulubinta dauke da dan ledan kayan ta suka kama hanya.
Ko da suka iso gidan sun samu Alhaji a kofan gida shi da baba salla zaune suna hira.
Yacewa Sabuwa shiga gida ta shige simi simi ciki shi kuma ya tsaya wajen su Alhaji dake kallon shi a cikin mamaki.
Nan ya zauna ya dinga bashi baki akan yayi hakkuri ya taushi zuciyar shi akan iyalin shi.
Yace babu komai tunda taci albarkacin shi zai kula ya saka ido ga komai a gidan insha Allahu.
Muna zaune kofan mama gaba dayan mu gidan ga hasken farin wata ya haske ko ina anyi gungu gungu ana hira.
Sai ganin shigowan ta kawai mukayi gidan da kumshin kayan ta babu ko sallama.
Kowa ido ya saka mata wasu sun gane cewa itane musanman ma yara ta da suka hau ihu eh mama mama da murnan su.
Nan dai duk da batai sallama ba aka shiga gaida ita tana amsawa cikin basarwa ta shiga dakin ta.
Ganin akwai duhu a dakin sai gata tafito tana cewa mama yaya ara min fitilar ki na haska naga guri don Allah.
Mama tace a dauko mata ta amsa fuuuu ta juya zuwa dakin nata daya daga cikin sarakan mama tace bisimillahi Allah matsala ta dawo ke nan kuma.
Kowa nan suke fadin albarkacin bakin su akan dawowan nata kuskus kus daya bayan daya muka watse gurin kowa ya kama gaban shi.
Da daddare can sai gashi ya shigo gidan dakina ya nufo don nice da girki a ranan.
Ya samu kujeran da yake zama kafin ya kwanta ya zauna na gaida shi da dawowa yace.
Amarya kinga wanan fitinanan ta dawo gidan ko ?
Nace wa wai maman Suwaiba ?
Yace ita ,
Don haka abinda nake so dake kikama kan ki daga gareta daga ita har yaranta ba tarbiya ne dasu ba.
Nace insha Allahu zanyi kamar yadda kace Alhaji bazan shiga tsabagan taba ko na diyan ta a gidan nan.
Ashe sabuwa tun shigowan shi gidan tana hankalece wai ita a zaton ta tunda ta dawo ranan a dakin ta zai kwana don haka takeyi wa sauran matan nashi a baya.
Tana ganin ya wuce zuwa dakina wani tukukin bakin ciki da kishi ya rufe mata zuciyar ta a lokaci daya.
Don haka tafito fuuu zuwa dakin mama hausatu tafada mata daki tana haki tace yaya kinga wanan mutumin baya son a zauna lafiya a gidan nan ko ?
Mama tace da akayi may kuma Sabuwa ?
Tace amma ai yasan na dawo amma ya iya wucewa ko dakina bai leko ba yana nufin cewa yarinyar nan itace zatai girki ko may ?
Ke sabuwa wai yaushe zakiyi hankali ne ke ki san jiya ba fa yau bane ?
Idan mu dacan kin samu kina muna yadda ran ki yaso yanzu baki tunanen cewa wata tazo gidan ne.
Gara ki rufawa kan ki asiri ki zauna dakin ki ki dubi yaran ki zai fi maki sauki wallahi .
Aiko da dakike muna hakan idan kin dawo kema kin san ba hakkin ki bane yin hakan don dai a zauna lafiya muke saka maki ido kawai.
Yanzu kuma wata tazo yarinya danya sharaf kice zaki tauye mata nata incin kinga haka zaiyuyu kuwa.
Gara ki kama kan ki da mutunci ki a gidan nan tun bakija wa kan ki raini ba ga yar diyar cikin ki da ko uwarta kin girma ga haihuwa.
Nan dai taga ba ci idan tace zata ja gashi da kyat ta samu tadawo dakin ta tun ba, a kwana ba kuma ace wani matsala ya taso a gareta haka ?
Ta juya cikin kwafa zuwa dakin ta tana faman mita da ace tasan zaman da muke da mijin nata da take ganin na anshe mata data bawa kanta lafiya.
Don idan tace taja wani fitina da daren nan wani sabon tonon asirin ta ne zai a bainan jama, a don yanzu maigidan nasu akan yar karamar yarinya baijin ass.
Don a dole banda yadda zanyi nake zaune gidan gashi har takai iyanzu na saba da komai ina zamana hankali a kwance tunda ba takura.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WA WANDA BAI BIYA BA ALLAH NA GANIN KI DON AMANA NE, , ,

8
Izuwa yanzu komai na gidan ba matsala saboda kakausar kashedin da manyan diyan Alhaji suka taru a tsakar gida sukayi.
Kan abar masu mahaifin su ya samu lafiyan shi don yawan futinan da aje saka shi zai iya jawo mai wani sabon matsala kuma.
Sunyi barazanan daukan mataki akan duk wace take kawo masu yawan tashin hankali a gida.
Wanan dalilin yasa gidan ya samu kwanciyan hankali na kwana biyu.
Gashi dai zan iya cewa Alhaji yana cikin mazan dake kokarin ganin yaba iyalin shi kulawa don bai make aljihun shi ga iyalin shi.
Kwanciyan hankalin da na samu ba fitina ba tsangwama yasa na sake murjewa nai kyau nai haske sosai.
Nan kan kula da yanayin Alhaji idan yana dakina sai naga ya tsura min ido kawai can naji ya sauke ajiyan zuciya a sanyaye.
Ban daukan wanan a komai sai dai naga kamar wani abune ya shige mai a duhu yake saka shi a tunane.
Ban sani ba ashe tausayina ne yake ji yana ganin kamar ya shiga hakkina da yawa.
Yakawo ni gida ya girke ba biyan bukatan komai a kaina bai san ni haka wani gata ne Allah yai min ba da hakan.
Allah bai barin bawan shi mai hakkuri ya tabe banza a duk inda yake watarana sai kaci riban hakkurin ka insha Allahu mudfin kayi shi da zuciya daya.
Ranan na tashi da safe na shiga nai wanka bayan na gama yan aiyuka na sai ganin nayi jini yana zubo min a gabana.
Tun ina bini bini kewayawa na wanke har tsoro ya fara kamani gashi naki sakin jikina ko cikin gida naki shiga na taya su aikin komai a ranan.
Sai bayan sallah azahar da naji kowa ya shige dakin shi na idar da sallah na nufi gurin mama hausatu.
Na samu ta idar da sallah tana zaune tana lazumi ita kadai a daki tana ganina tai dan murmushi a fuskan ta tana cewa Amarya .
Yanzun fa nake zancen ki a zuciyana yinin yau banga kin fito ba tun safe da muka gaisa nake cewa ko dai lafiya kuwa ?
Nakai zaune tare da cewa wallahi mama yau banda lafiya akwai matsala shine nazo na fada maki.
Cikin sauri tace subbahanallahi may ya samay ki kuma yar nan ?
Shiru nayi ban san may zance da ita ba a lokacin sai dai kaina dana sada a kasa kawai.
Tace may yafaru amarya gaya min mana nifa ban dauke ki a kishiya ba matsayi diya ta ta cikina nake daukan ki.
Na kara dukar da kaina a kasa nace mama dama sai nai shiru can kuna na dago na kara cewa a sanyaye dama yaune naga jini kawai yana ta zuwa min a karkashina tun safe da na tashi ga marata sai ciwo yake min.
Nace barin fada maki ko zanga likitane tun cutar bai min yawa ba ?
Tace cikin mamaki ikon Allah Rahama dama baki fadi bane sai yan zu ?
Na dago kai da sauri na dan kalle ta tace wanan ne karo na farko da kikaga haka ko may ?
Nace mata a sanyaye eh mama.
Tace to ki saurare ni kiji da kyau wanan abin da yazo maki zan iya cewa ba cutane ba kuma cuta bane alama ce ta girma yazo maki da hankali da samun natsuwa.
Duk ko wace mace da kike gani tana yin wanan abin a rayuwan ta wace bata yi kuma to tana da matsala kuwa babba.
Wani irin ajiyan zuciya na sauke taci gaba da fadin kada ki tsorata da hakan nan tafara yi min bayanin yadda zan kama kaina a lokacin da nake cikin wanan laluran na fashin sallah.
Kamar yadda uwa zatai wa yarta bayani haka ta zauna tai min bayani sai daga karshe tace da zaran kin gama zakiyi wanka kamar yadda kike yin wankan janaba.
Nace wankan janaba mama tace eh idan kin kwana da mijin ki ba kikan yi wankan tsarki ba ?
Nace eh kawai ba tare dana fahinci may take nufi ba tace to shima hakan zakiyi sai dai gurin niyya ya banbanta ne wacan janaba zaki ce wanan kuma haila.
Nan dai ta kara koyar dani komai nace nagane mama a makarantan boko dana islamiya duk an koya muna shi na kuma rike.
Nace mama dama wanan jinin shine jinin hailan da ake nufi tace shine amarya sai jinin haihuwa shima tai min bayani da kwanakin da ake son mace tayi ta fara yin tsarkin shi.
Na gamsu sosai da bayanin mama akarshe take ce min sirina ne daga ni sai mijina kawai daya zama dole ya sani ake son ya sani idan ma ina fashin sallah naga kowa ya tafi sallah na shige daki nima kada na zauna a waje kowa ya fahinci ban salla don siri ne babba ga mace.
Nai mata godiya tare da mikewa na wuce zuwa dakina na kimtsa jikina kamar yadda tai min bayani nayi.
Ina fita na bata tausayi sosai sai dai bata ga laifina ba sai na iyayyena dake da alhakin haka akaina.
Gashi yar karama dani a wanan zamanin an min auren cushe ga miji, mijin kuma babban mu kamar alhaji gashi ashe ko hankalina ban gama mallaka ba.
Kamar yadda mama ta fadakar dani hakan ne nayi na gyara jikina tsab mai makon na ma dinga shiga mutane sai kawai na dinga nisanta kaina da jama, a baki daya gani one two one ta na kewaya na gyara jikina.
Da maigidan ya shigo gida ne mama ke fada mashi cewa ashe amarya sai yanzu ta fadi yau ta samay ni cikin damuwa take fada min don bata san kaiba.
Shima yai mamaki kwarai jin sai a lokacin na fadi ashe kuma ban san komai ba akan faduwa hakan na nufin ke nan har yanzu ina a matsayina na cikakkan budurwa as a virgin .
Tausayi na ne ya kara kamashi a lokacin ne yai daya sani shiga rayuwa na da yayi da wuri haka nan.
Ke nan zancen da kishiyar mahaifiyana ta fada mai nacewa gara ma da yazo nema don ni watsatsace ban da kamun kai na san maza ko zan iya zama dashi ai ban ganin tsufan shi tunda maza nake so a rayuwana.
Wanan magana babu inda ya hango kamshin gaskiya a cikin sa don dai halin rayuwa na ya nuna mai ta ko ina ni yarinya ce mai mutunci da kima nasan darajan kaina da iyayyena.
Don haka dole ne yai min adalci akan zaman da nake dasu don ya fahinci yarinya ce ni sharaf ban san komai ba na duniya.
Wanan dalilin ne yasa ya kara jawo ni jikin shi sai naga yana haba haba dani fiye ma da farko da yake min.
Mutanen gidan ganin kwana biyu bana yawan fitowayasa suke shigowa daya bayan daya suna tambayana may ke faruwa dani ne wai ?
Sai cewa masu nake banda lafiya ne bana jin dadin jikina na ne shiyasa.
Su daukan su na samu cikine, wai, sai naji suna cewa Allah ya ingata ya kawo muna mai albarka.
Jin haka yasa Sabuwa ta fara dan sake magana tana fadin an dai ji kunya wallahi .
Karshen muna funci ya baiyyana ace muna ba, a da lafiya amma sai ga shi an iya

Please Login or Register in order to submit comment