Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa dani haba Rama.
Don Allah kiyi hakkuri ki yi biyayya fa mijin ki mijin ki mutum ne mai murdaden hali sai a hankali zaki fahince shi.
Yana da yawan bukata wanda nasan sai a sannu zaki saba da hakan gareki.
Don Allah Rama ki daure ki fahinci beasty zakiji dadin zama dashi sosai indan kin fahince shi.
Rama nasan zaki iya insha Allahu don nasan halinki nasan na besty na don haka idan kin kwantar da hankalinki abin zaizo maki da sauki sauki sosai.
Don haka daga yau ina son ki sake jikin ki ki zama kamar kowa a gidan nan don kin dai san halin matan gidan nan, sarai da son raini wayyo, ba zan so ace kin bari sun fara kawo maki raini ba don ba fashi za suyi hakan don ko halin su ne ba son suke a zauna lafiya, ba.
Ni dai ina sauraren abinda take fadi ziciyana sai fal, fal nake ji wanan wa,azin da anty ke min anya kuwa zan iya hakan da take so dani.
Tace ban san may suka saka maki a cikin kayan lefe ba don bani na sayo masu ba su Aisha ne yaba kudin suka sayo mashi.
Don ni lokacin da akai sayayyan mun dan samu matsala dashi kan zancen auren naku.
Na dago kaina da sauri ina kallon ta cikin mamakin jin abinda ta fadi wai akan aure na sun samu matsala da mijin ta.
Kada ki damu zan maki wanda ya dace idan na samu lokaci zan dan shiga na sayo maki abin daya dace ayi.
Idan na danji sauki sai mu zauna mu tsara yadda abubuwa zasu tafi muna anan a cikin part din cikin rufin asirin mu.
Nidai ban ansa mata ba haka ta dinga dan jana da hira nasan tanayi ne don na sake jikina kawai.
Muna nan zaune saiga yan makaranta sun dawo gava dayan su sukayo kaina da murnan su.
Nai masu sannu da zuwa tare da rugumay su a jikina nakaisu dakin tare da cire masu kaya nabasu abinci suna ci muna hira dasu.
Time din islamiya nayi na shirya su zuwa Islamiya suna ficewa na kara gyara gidan tsab anty tana fitowa ta ga ina aiki take cewa dani.
Rama don Allah kibar aikin nan kibar gajiye ta dinga aikin nan yanzu hakan ba naki bane.
Murmushi nayi naci gaba da aikina kawai ban daina ba sai dana gama na koma part dina naiwan ka tare da bin dakin da kallon mamaki duk wanan gurin wai yau mallakina ne.
Wanka nayi na shirya cikin daya daga cikin kananan kayan da Nafisa ta sayo min bayan na idar da sallah ne na nufi gurin anty don wayan da Zarah ta bugo min muna da test a school.
Zaune take tana waya sai daga baya ne na fahinci da msigidan take wayan amma bata jima ba ta katse wayan.
Ta juyo gare ni tana cewa Ramana yaya gajiya da kewan su Attu suna dai gida yanzu kan.
Nan na dan duka cikin murmushi nace Anty dama nazo na fada makine muna da test ranan tuesday in Allah ya kaimu shiyasa nake son na dan leka school din.
Allah sarki Rama kin san yanzu ikon ki yafita a hannuna hakkin ki na karkashin mijin ki don haka shi zaki kira ki fada mai.
Da sauri na dago kai ina kallon ta mai ma, ana wani ?
Nace a hankali anty ba zan iya magana da daddy ba gaskiya ina jin nauyi da kunya anty na fafi a shagwabe take cewa dani.
Kikirashi ki fada mashi muji abinda zai fadi kin ga idan ya yarda sai ki shirya ki tafi ko.
Nace anty bazan iya ba wallahi kuma ni ban ma da nomban daddy a wayana gaskiya.
Taimako dayan zan maki zankiraki na baki wayan sai kiyi mashi magana muji.
Ta daga wayan ta ta kira shi bayan sun danyu magana take cewa Amaryan ka ce dama ke son magana da kai besty, ban san may yace mata ba naji ta kwashe da wani irin dariya tana miko min waya.
Na karbi wayan a sanyaye a hannun ta don ban san may yace wa anty ba take wanan dariyan irin haka.
Ina karba a sanyaye nake cewa cikin wani murya daddy ina wuni shiru naji yayi bai amsa min ba.
Nakara fafin haka a karo na biyu sai naji yace hmmm, wace irin amarya ne da bata damu da jin lafiyan mijin ta ba.
Rama ko baki damu da angon naki bane haka zamuyi dake ko haka kikaga anty ki tana min bata damu da damuwana ba sam.
Mamaki da imanine ya kashe ni a lokaci daya wai yau ni daddy ke kokarin yiwa magana irin haka a rayuwana.
Kai watau maza dai basu san kunya ba a duniya ke nan ko may yasan kuma anty na gurin amma yake kokarin yi min magana irin haka kamar wanda bai san kunya ba.
Jin nayi shiru ne ya kara cewa ko baki jin abinda nake fafi ne wai naji kin yi shiru ba amsa ke nan dai ko ?
Sai da na dan daga ido na kalli anty naga bata sauraren mu tana can tana wani tsabgan gaban ta hankalinta bai gurin mu.
Nace a hankali dasdy yi hakkuri don Allah, yace bazan yi ba sai naji hujjan ki na yin hakan ?
Shiru nayi yace dole ne na hukuntaki da yin hakan da kikayi don ni ba ai min laifi na yafe kai tsaye kin sani.
Nace ban sani ba daddy amma don Allah kayi hakkuri yace bazan yi ba na fada makii sai kin biya bashin yin haka idan kuma kin sake sai nai doubling din yin hakan.
Yanzu ina jin ki nasan kina da bukata ne kika nemay ni ko ?
Nace daddy dama test ne muke dashi ranan tuesday shine nake son shiga school don an dan wuce ni dama.
Yace kibari zanyi magana da Saade zakiji may na yanke a kan haka nai mai sai anjima na mika mata wayan na daga nabar dakin don suci gaba da wayan su.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU DON BA, A YAFE MAKI HAKAN BA DABARA YA SAURA GA MAI TSORON HADUWAN SHI DA ALLAH KAN HAKKIN WANI, , , , ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA NA ROKI ALLAH YA SAKA MUNA AKAN KI DON BAKI DA AMANA DUK MAI FITAR MIN DA NOVEL ALLAH YA DAUKAN MIN FANSA AKANTA, , ,
38

Sin dauki lokaci zaune a dakin ba mai iya yiwa wani magana a cikin su don tashin hankalin da suke ciki.
Can mama ta nisa take cewa amma may yasa baki fada muna wannan matsalan ba naki tun tuni sai yanzu.
Nan dai take cewa zata tafi ta gwada maganin gargajiya ko Allah zai sa a dace kallon ta kawai anty ke yi tana murmushi kawai.
Masu gyaran guri suka shigo gidan kan jagorancin Habbib brother din maigidan ta wurin uwayen su .
Sanin ko shi waye yasa daya shigo gidan da masu gyara ba wanda yai magana daga cikin matan gidan.
Kafin kwana biyu an fitar wa kowa da nata tsofin kayan an saka sabbi angyara komai sai gurin ya koma kamar a lokacin ne suka tare a gidan gashi badama su dan yi korafi akan komai yanzu habbib yaci masu nutunci.
Maigidan baya gari yai tafiya koda akai gyaran gidan duk bayanan akai komai sai daya dawo ya samu an gyara ko ina neat har part din shi sai dai ya samu matan gidan suna cikin hasala sun cika fam dasu.
Sai bayan sallah ishai ne yake cewa dasu yana da magana kowace ta karasa yanga da jan aji tazo falon amsa kiran maigidan.
Gurin da Anty oe zaune ya dan kalla sai yaga yadda ta dan samu zugi gurin mama Altine tasauya mai baki dayanta ya kasa fahintar ta.
Yace dama ba wani abu bane yasa na kira ku nan sai akan zancen wanan aure dana kara .
Naso ace kafin auren ne labarin yazo maku amma Allah bai nufi hakan na sai gashi anyi shi a bazata muna zuwa nema aka bamu tare da daurawa don darajan iyayyena.
An dai matsu da ita dama ana neman kai abaka daga tayi wani kallo yaiwa Hindatu tare da kada kan shi.
Sai Zulfa da tace ai zata gane kuren ta zata san tayi gigin shigowa, inda yafi karfi shigan ta.
Ya dan yi murshi yace ko ashe anfi karfinta a nan gamu gani ke nan yana magana yana kallon fuskan anty Saade wacce tun safe yau yake ganin sabanin halinta a fuskan ta.
Maimakon ita da ta hada ta bashi full confedence kan zancen amma sai tai wani kicin kicin da fuskan ta a lokaci daya.
Abinda bai sani ba shine tasha zugi fam gun mama Altine dake ganin kamar tun farko asiri naiwa mijin anty da anty suke matukar sona da kauna na haka.
Yace cikin daure fuska ba wai na taraku don son jin ra, ayin ku bane na kiraku ne don naji bukatan kowa kan kayan fadar kishi da zan maku kudin zan baku ko kayan za, a sayo maku.
Har suna hada bakin su, su biyu gurin cewa kudin muke so abamu ya ce ke saade may kikace a hakan ta wani tabe fuskan ta tana cewa ni duk yadda akayi duk daya a gareni.
Nan ya kirga kudi kowace sai da tai mamakin kudin daya basu a lokacin.
Sai bayan komai ya lafa ne ya mike ya samu Saade a dakin ta zaune take saman salayan da ta idar da sallah take zaune sai nadama da dana sani take auki yi a zuciyar ta afili ta yarda cewa bai yuyuwa ace gaba dayan su suna matukar son Rama haka dole akwai kamshin gaskiyan maganan mama a cikin zancen.
Tana jin shigowa shi amma bata dago daga yanayin da take zaune ba ta fuskance shi ta a yadda ya samay ta a, zaune a dakin.
Tana ganin shi taji wani tsanar shi ya shigeta lokaci daya yau mijinta masoyin ta shine daga tai mai tayi ya zake akan maganan har tana son finta zakewa ma yanzu yadda taga yana rawan kai haka.
Baki jin nashigo gunki ne amma ko ki daga kai ki kalle ni dago kai tayi ta dan kalleshi a nakashe wanu haushin shi ne da tsana taji ya ziyarci zuciyar ta.
Kai maza baku da tabbas wai yau besty ta ne ke rawan jiki akan Rama yarinyar data tayar tankar diyar da suka haifa.
Wanan gaskiyan maganan mama Altine ce tace dama renon kan shi yaiwa Rahama a gidan don bukatan shi shine yai amfani da ita cikin saukin kai yayi mata dubara har ta yarda da zancen auren da kan ta.
A hankali ya tako zuwa inda take zaune yace ban fahince kiba don tunda na dawo naga wani canji daga gareku haka.
Wani kallo ta watso mai daidai lokacin da take gyara zaman ta da kyau sai ga hawaye shar shar suna biyo fuskan ta tana kokarin tare su.
Tsayawa yayi ya kura mata ido cikin mamaki yace Saade kinga abinda nake wa gudu ko ?
Tun farko abinda naiwa gudu kenan muna zaman lafiya kin kawo muna sabun fitina da zai tayar muna da hankali.
Dama nasan a karshe nice zaki bari a cikin zancen ina zaman zamana kika dauko minbsabun fitina a rayuwana .
Kece kika sakani yin auren banda ra, ayin karin mata a rayuwana ammakika sakani gaba da kai karana gurin magabata na har nakai ga amincewa da zancen.
Da kikasan bazaki iya hakkurin hakan ba da saiki barwa Allah al, amarin ki yai muna mafita da kan shi.
Amma yanzu gashi kin saka ayi abu kin kuma dawo kin tayar da hankalinki kin kasa samun natsuwa muma na tare da ke mun kasa samun namu.
Ya juya a fusace zai bar dakin sai ga mama tana shigowa dakin take cewa yaka mana Alhaji may kuma ke faruwa yau ina jin harshen ka har falo.
Mama may Saadatu take son mayar danine don taga ina tausaya mata shine take ganin kamar zata iya juyani yadda ran ta ke so, bafa tsoron ki nakeji ba, abubuwa da dama yasa nake matukar tausaya maki ina maki ragowa akan su.
Amma akan may kike son mayar dani wani bi can kamar mijin hajiya a gidan nan auren yarinyar nan kece fa kika tasa ni gaba zuwa gun magabata na .
Yanzu kuma Allah yayi abin kina kokarin tayar min da hankali so kike na zama mutumin banza ko may nace eh, na dawo kuma nace a, a komay ?
Wani kuka ne ya zo mata a lokaci daya tana fadin besty nayi nadama wanan hadin na cuci kaina da kaina besty.
Yanzu na fahinci nayi gangancin hada ka da Rama danayi a rayuwa na na fahinci yin hakan babban kuskure ne a rayuwana.
Kallon mamaki yake mata cikin rudewa yake cewa yanzu kina nufin dai kin jaye zancen auren ta a ranki sokike na sake ta ko ?
Da sauri mama ta cabe zancen tace shine saukin sakin wanan yarinyar don bai yuyuwa ace kamar Rama ta zaman kishi da Saade.
Wanan abin bayin kan ku bane kai da ita sihiri ne ke aiki akan ku kawai da zaka daure ka saki wanan yarinyar salin alin tun bata cinwa manufanta ba akan ku da zaifi saukin rufin asiri agare ku.
Kunga aniya makomiya ke nan amma ina Rahama ina shiga cikin ku , yar tallakawa lis da ita , ni ban taba yarda ba cewa ba sihiri suke a kan ku ba dama.
Wani irin abu yaji ya tokare mai makogwaron shi a lokaci guda ya gama fahintar mama tai amfani da lafazin tsofin mata akan Saade taji galaban ta, har kiyyayya ya tsiguru a zuciyar ta na Rama.
Take yaji idon shi ya canza launi yana jin kalamin mama kamar saukan aradu azuciyar shi da mama tasan kalaman sakin da take kira yaiwa Rahama yadda yake jin shi a ransa da bata kara furta ko a ba daga haka.
Yaya mama zata sa Saade ta mayar dashi mutumin banza mai magana biyu idan da yar tane ko jikan ta akaiwa haka zata ji dadin yin hakan da akai masu.
Lokaci daya anty ta fahinci rayuwa mijin ta yai matukar baci yadda mama ke ra fadin mugun kalami a kaina.
Ganin halin da yake ciki yasa ta fara tare mama dake ta faman zuba shar kamar ruwan sama.
Tace mama don Allah kibar zancen nan haka bai kamata kina fadin haka ba a gaban kowa.
Yace No ki barta ta fadi yanzu na fahinci komai dake gudana kuma na gane amma ki sani ke Saade idan wanan yarinyar bata da amanan ki kukai mata haka don tozarci Allah ba zai kyale ki ba.
Kin sani bani da ra, ayin karin aure a rayuwa na amma kika sakani gaba da fitina sai da na amince har Allah ya nufa aikai wanan abin.
Don haka ba asiri tai muna ba ko dauri tai muna bazan sake taba har abada gara ma ki kwantar da hankalin kafin yarinyar nan ta fahinci sauyin rayuwa a gare ki ki sha kunya ga hakan don mutuncin ki ne zai zube gareta.
Ina ilimin ki da imanin ki yau yashiga da har dan lokaci kadan shedan zaici galaba akan ki haka , ?
Kin bani kunya Saade kin kuma bani mamaki yau duk tarin sanin Allah ki harki bari shedan ya rude ki wai ke an maki asiri idan halintane yin haka ke kinfi kowa sanin hakan gareta.
Don kece ke zama da ita kin san komai na rayuwan ta ba sai wani ya fada maki.
Yadda yake magana yasa gaba daya jikin ta yai sanyi nadama abinda tayi yazo mata a lokaci guda hankalinta duk ya daga .
Ita kanta mama kunya da wani irin nauyin shi duk ya rufe ta saboda tasan ya gane itace ta zuga anty take hakan.
Yafara tafiya yana cewa yau din ba sai gobe ba zan samu su Abba na kuma basu takardan yarinyar nan basai ta tare min a gida ba.
Anty najin haka tamike da sauri ta tari gaban shi tana fadin dakata don Allah besty ka bari muyi magana ta fahinta dakai please?
Yace maganan may zanyi dake ke kika hada kin kuma ce a,a yanzu basai kowa ya kama kansa ba yafi sauki.
Kwata kwata ni dama wanan maganan baya a raina saboda kece nake komai da kikaga inayi din farin cikin ki yanzu ko ya kare ai.
Daga haka ya juya ya fice daga part din ta ranshi a bace zuwa nashi part din hasale yake don gaba daya kan shi ya daure ta ko ina ba dadi gare shi gaba daya matan sun sawa kan su bakin kishin yar karamar yarinya a duniya.
Amma kuma da yai nisan tunane sai yaga wannan abin duk jerabawan ubangiji ne hakan.
Allah kadai yasan hikima da albarkan dake cikin wannan aure da Allah ya nufe shi dayi batare da ya shiryawa hakan ba a rayuwan shi.
Ita Saade ya fahinci inda matsala ke taso akan ta zai yi kokari yaga ya magance wanan matsalan kada ta samu raunin imani a rayuwan ta abinda baida kyau zuwa gurin wanin Allah boka ko malam kan neman yayewan bukatan ta.
Don yadda ya fahinta ko wani lokaci mama na iya cin galabanta zuwa ire iren irin guraren nan na shirka.
Cikin kwanakin nan duk yadda Anty taso su shirya da shi abin yaci tura saboda ya dau zafi da ita sosai.
Ya dauki abin da zafi so sai a ranshi har takai ta fara shiga wani yanayi don gaba daya ya tsamany taga duk wanibal, amarin shi ya juya mata baya yana harka da sauran matan shi da yan uwan shi.
Ko zancen kai lefe gidan mu ga bakin mama laraba da Aisha ta samu labari hankakinta ya kara dagawa tasamay shi da zancen a falon shi.
Yace cikin murmushi eh dole ne nayi taka tsantsan dake yanzu Saade .
Don na fahinci sauyin rayuwa a gareki don ban taba tunanen zaki yi rayuwa irin na masu yarda da shirka ba.
Yanzu ke da kanki kin sani ke kika kawo zan cen yarinyar nan amna kika bari shedan da mama suka rude ki kan karya bayan kin san komai kece kika hada abinki.
Why zakibi rudin shedan ki hau ki zauna idan har wani yaji maganan nan in har yau Rahama na asiri kema tabbas kinayin asiri don kowa a tare ya san ku ai .
Nadama ne yazo wa Saade a lokaci daya tabbas ba karya ya fadi ba duk wanda taji maganan nan dole itama za, a ce tare suke wanan halin dubun su ne yacika ita da Rahama din kaikayi ya koma ga mashekiyar ta.
Tace don Allah besty kayi hakkuri wallahi mamace duk ta kaini ga haka kan dalilin ta mara tushe .
Ni dole inwa Allah godiya tunda na gane gaskiya kafin Rahama ta tare a gidan nan nazo naji kunya.
Yace dole ne na jaye don kada nima ki dulmiyar dani kamar yadda ke kika dulmiye kanki.
Idan zaki fadawa mama gaskiya don azauna lafiya ki kuma yi istigifari ga Allah ki roki yarinyar mutane gafara.
Kuka sosai Anty keyi tana mai nadama aranta tace nasan Allah naso na besty tun da har bai yarda naci galaban ka ba akan hakan.
Ka bijirewa bukata bamu taru mun cutawa yar mutane ba bayan tauye mata rayuwan da nayi na hata zabin kan ta kuma nabi bayan ta da kazafi da sheri.
Alhalin nasan haka ba halin wanan yarinyar bane da iyayyen ta don haka yau ba sai gobe ba nima zan zauna da mama idan ta gane wala ba, asa idan batagane ba ni dai babu hannuna ga duk abinda zatayi.
Tai mashi godiya ta fita zuwa nata sashen sai dare ta samu zama da mama cikin hikima da kuma kawo mata Allah ta ja hankalin mama.
Tace mama kin fini sanin halin yarinyar nan mama akan kishi zamu bari shedan ya yaudare mu mu cuci Rahama duk irin halarcin da yarinyar nan tai muna a rayuwan ta .
Mama dai ta fahinci gaskiya anty ke fadi dole taji nadama yazo mata bai kamata ba ta bi son rai ba taiwa yar mutane mugun kazafi haka ba.
Rahama mutum ce Saade gaskiya nima yanzu nayi nadaman abinda nai mata dole ne na nemi yafiyan wanan yarinyar.
Anty tace mama kina ganin yau in bani a gidan nan zaki shigo gidan nan koda da sunan ganin jikokin ne akarbe ki da mutunci ?
Amma idan Rahama na gidan nan tankar nice a gidan zaki zo kiyi yadda kika sabayi duk lokacin da kika ga dama ganin su.
Kuka mama ta fashe dashi sosai tana nadaman abinda tai min tace gobe zan koma gida ayi komai dani yadda aka saba ba zan yarda har akawo Rahama ba ina gidan nan dole ne naje ayi komai tare da ni.

********* ********* *********
Attu da nake gurin ta sai fanan shiri takeyi a kaina tana kara nusar dani yadda zama da kishiya yake tare da abinda zan wa miji na jan hankali.
Sai faman bani wasu jike jike takeyi tare da yi min wankan lalle akai akai tana kuma yi min hayaki da ban san ko na may ye ba ga ruwan rubutu da take faman kin kima min ina sha dare da rana.
Kashin rakumi naji tace a samo mata da kanunfari sai tasa na dinga tsugunawa ina hauakin jikina dashi.
Da nayi wanan hayakin za anji gaba daya alaura na ya wani ciko min yana min kamar kaikayi ko susa a lokacin.
Dutsen tama naji tace a tsinto mata naga ta jika a kwano duk zata dibi wanan ruwan da ta jika duwatsun tama a cikin shi ta hada da garin shasha tau da manta uwa da bita zaizai da shashatau tanika su guri guda tace na shanye su.
Ni kaina duk da ba abinci nake ci sosai ba nasan na samu canji sosai a jikina.
Ana gobe za, a fara shagalin buki ne naga tashigo dakin bayan magariba take cewa dani da mayafin ki kizo mu shiga nan gidan makwabtan mu.
Ban bata lokaci ba muka shiyar muka fita daga gidan gidan makwabcin su malam Musa muka shiga mun samay shi a zauren gidan shi muka gaidashi cikin mutunci.
Yace Attu kun iso tace dashi eh malam ga yarinyar nan nazo ma da ita na gaidashi a cikin mutum ci yace da Attu yaya sunan ta tace Rahama take.
Yace suna mai ma,ana ga musulunci kiyi amfani da martaban sunan nan naki a gidan mijin ki kikai mashi Rahaman dake cikin sunan ki a gidan shi.
Naga mijin naki mutum ne kamili mai addini a yadda nagan shi ga bincike na sai dai yana da murdade hali tare dashi ba matsala bane hakan idan har

Please Login or Register in order to submit comment